Isa ga babban shafi
Gasar Olympics

Ana gudanar da bincike kan harin da aka kai birnin Paris

Kamfanin da ke kula da sufurin jiragen ƙasa na Faransa  SNCF, ya ce wasu da ba a san ko su waye ba, sun kai hari tare da lalata sassan titunan jirage masu tsala gudu, yayin da ya rage sa'o'i kaɗan a buɗe gasar wasannin Olympics da birnin Paris ke karɓar baƙunci.Tuni aka fara gudanar da bincike don gano tushen wannan harin.

Jami'an ƴan sandan Faransa
Jami'an ƴan sandan Faransa © AP - Michel Euler
Talla

Yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, kamfanin na SNCF ya bayyana farmakin a matsayin babbar barazana, la’akari da tasirin da ya riga yayi, domin tilas aka soke jigilar jiragen ƙasa zuwa sassan Faransa da dama, wanda kuma sai an shafe hutun ƙarshen mako kafin kammala gyara layukan dogon da aka lalata.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren rahoton Nura Ado Sulaiman

Kamfanin Kula da Sufurin Jiragen Ƙasan na Faransar ya shawarci fasinjoji da su ɗage lokutan da suka tsara na yin balaguro, su kuma ƙauracewa zuwa tashohin jiragen ƙasa har zuwa lokacin da za a tabbatar da tsaro.

Harin dai yafi shafar titunan jiragen ƙasan masu tsala gudu da ke jigila zuwa yankunan Arewaci da Gabashin ƙasar, yayin da jami’an tsaro suka daƙile yunƙurin da aka yi na lalata titunan da ke sadarwa zuwa yankin Kudu maso gabashi.

Kimanin ‘yan wasa 7,500 ake sa ran sun hallara a birnin Paris domin nuna bajintarsu a gasar Olympics, yayin da ake kiyasta yawan ‘yan kallo zai kai dubu 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.