Gaga da Nakaruma sun nishaɗantar da mahalarta gasar Olympics
Fitattun mawaƙan nan Aya Nakamura da Lady Gaga sun gabatar da wasan kaɗe-kaɗe da raye-raye a yayin buɗe gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics a birnin Paris na Faransa a wannan Juma'ar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Nakaruma wadda ke da ruwa biyu, wato ƴar ƙasar Faransa da Mali, ta kasance shahararriyar mawakiyar da aka fi sauraren waƙoƙinta a ƙasashen da ke magana da harshen Faransanci, yayin da ta gabatar da kayataccen wasa duk kuwa da irin caccakar da take sha daga wasu masu tsattsauran ra'ayi.
Matashiyar mai shekaru 29 na shan suka ne sakamakon wakarta ta "Djadja", inda a ciki ake zargin ta nuna rashin girmamawa ga harshen Faransanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu