Isa ga babban shafi

Tinubu ya gana da Sarakuna da Gwamnoni kan shirin zanga-zangar matasa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shafe ranar jiya Alhamis wajen ganawa da bangori daban-daban na ƙasar, a wani kokari na daƙile zanga-zangar da matasa suka sha  alwashin gudanarwa don neman kawo ƙarshen gurɓataccen jagoranci da kuma tsadar rayuwa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. © Daily Trust
Talla

Bayan ganawa da gwamnonin jam’iyyarsa ta APC, Tinubu ya kuma gana da Sarakunan gargajiya fadar Aso Rock.

Sarkin Zazzau mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli na daga cikin waɗanda suka samu halartar ganawar da shugaban na Najeriya, wanda yayi wa ‘yan jaridu ƙarin bayani kan wasu daga cikin batutuwan da suka tattauna akai.

01:03

Sarkin Zazzau mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli

Bayan ganawarsu da shugaban Najeriyar, Sarakunan sun shawarci masu shirya gudanar da zanga-zangar neman gyara lamurra da su tattauna da gwamnati domin zayyana buƙatunsu domin kaucewa fargabar da ake yi kan yiwuwar shirin wasu miyagu na yin amfani da fitar ɗangon da matasa ke shirin yi wajen haddasa tashin hankali.

 

Gabanin ganawa da Sarakuna da shugaba Bola Tinubu yayi, gwamnonin jihohin Najeriya suka gudanar da nasu taron, wanda ya samu halartar mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribaɗu da ministocin kuɗi da tsara tattalin arziƙin ƙasa wato Abubakar Bagudu da kuma Wale Edun.

Batun gagarumar zanga-zangar da matasa ke shirin yi dai na cigaba da ɗaukar hankali a ciki da wajen Najeriya, inda da dama ke ganin a baiwa ‘yan ƙasar ‘yancinsu na bayyana rashin jin daɗin ƙuncin rayuwar da suke ciki, yayin da wasu ke bayar da shawarar bai wa gwamnatin ƙarin lokaci kafin zartas da aniyar da matasan suka ɗaura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.