Isa ga babban shafi
ZANGA ZANGA

Tabbas na shiga zanga zanga a baya, amma ta lumana - Tinubu

NAJERIYA – Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yace tabbas ya shiga zanga zanga a baya domin kawo karshen mulkin soja, amma ba ta tashin hankali ba ko kuma wadda ta kai ga rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © Bola Ahmed Tinubu - X
Talla

Tinubu ya bayyana cewar zanga zanga na daga cikin tanade tanaden da dimokiradiya ta samar, amma babu wata gwamnati da zata nade hannun ta domin zuba ido wajen kallon zanga zangar da zata kai ga rasa rayuka da kuma lalata dukiyoyi.

Shugaban ya ce lokacin mulkin soja, yana daya daga cikin wadanda suka daga muryoyin su wajen adawa da gwamnatin amma ta hanyar lumana, da zummar ganin an samu dimokiradiyar da ake cin gajiyarta yanzu na shekaru 25.

Tinubu da yake wadannan kalamai lokacin da ya karbi sabon jakadan Amurka Ricahrd Mills a ofishinsa, yace Najeriya za ta ci gaba da jagorancin Afirka a matsayin ta na babbar kasa kuma abin koyi.

Sabon Jakadan Mills wanda ya gabatar da takardunsa na aiki, ya jaddada muhimamncin Najeriya ga kasarsa, da kuma bayyana yadda kasashen biyu ke mutunta dimokiradiya, tare da alkawarin taimaka mata.

Jakadan yace ya zo ne ya bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar dimokiradiya da kuma tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.