Tibi
Tibi | |
---|---|
Specialty | Infectious diseases, pulmonology |
|
Tibi (TB) ko Tarin fuƙa: wata cuta ce, wadda ake kamuwa da ita daga kwayar cuta mai suna “mycobacterium Tuberculosis”(MTA). Tb cuta ce da ke shafar Hunhu amma tana iya shafar wasu gaɓoɓin jiki kuma. Yawancin cututtukan tibi ba su nuna alamar kasancewarsu a jiki ba. Kusan kashi 10 (10%) na cikin dari na tibi ba su nuna alamar kasancewarsu ba, suna iya zama ciwo idan ba a magancesu ba, zai kashe kusan rabin masu dauke da cutar idan ba a yi jiyyarsu ba. Mafi alamar cutar tibi su ne: tari, majina da jini, zazzabi, da zufa da daddare da kuma ramewa ko rage nauyi. Kalmar “ci” an samo ta dalilin ramewa bisa ga tarihi. Shafar wasu gabobbin jiki na iya nuna alamomi da dama.
Ana baza cutar tibi ta iska yayinda masu shi na tari daga huhu, tufa miyau, yi magana ko atishawa. Mutane masu dauke da kwayar cutar da bai zama ciwo ko ba, ba su baza cutar ba. Ciwo mai tsanani kan auku ne ga masu dauke da kwayar cutar sida da kanjamau da kuma masu shan taba. Ana yin binciken ciwon tibi ta daukar hoton kirji, da yin amfani da madubin likita, da kuma nazarin ruwan jiki.
Tsare kamuwa da tibi ta hada da gwajin wadanda ke da hadarin kamuwa da cutar, ganowa da sauri da kuma shan rigakafinta “bacillus Calmette-Guerin vaccine” na taimaka wajen magance cutar. Ýan gida, ofishi, da sabowa da jamaá masu tibi na da hatsarin samu ko kamuwa da wannan cutar. Jiyyar wannan cutar ta bukace amfani da maganin rigakafi na tsawon lokaci. Rashin jin maganin rigakafi na tsawon lokaci damuwa ce da ke kara rashin aukin Maganin-Tibi (MDR-TB).
Ana tunani kashi daya cikin goma na alúmmar duniya na da cutar tibi. Kashi daya cikin dari na mutanen duniya na sabowar kamuwa da cutar. A shekara ta 2014, an samu masu cutar Tibi miliyan tara da dubu dari shida (9.6 million) wanda ya kai ga mutuwar mutum miliyan daya da rabi (1.5 million). Mutane fiye da kashi tasain da biyar cikin dari (95%) sun salwanta a kasashe masu tasowa. Tun shekara ta 2000 an samu raguwa wajen kamuwa da cutar. Kusan kashi tamanin cikin dari (80%) na Kasashen Asiyawa da na Afrika an same su da wannan cutar sannan biyar zuwa goma na mutanen Majalisar Dinkin Duniya an same su da kwayan cutar. Kasancewar tibi na nan tun dá.
-
yadda ciwon tarin tibi yake bata huhu
-
alamomin tarin Tibi (TAB)
-
TB