Jump to content

Mujiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mujiya
Scientific classification
ClassAves
SuperorderNeoaves (en) Neoaves
order (en) Fassara Strigiformes
Wagler, 1830
Geographic distribution
General information
Babban tsaton samun abinci European Rabbit (en) Fassara
Wata Mujiya ta zare idanu a bisa bishiyar Ɓaure
mujiya ta buɗe ido ƙwala-ƙwala
Wata ƴar matashiyar mujiya
mujiya su biyu akan bishiya
mujiya da ƴaƴansu

Mujiya tana daga cikin jinsin tsuntsuyewadda take da matsakaicin girma, tana da manyan idanuwa. Ƴan'uwanta tsuntsaye, da suke cin nama sune kamar shaho, Angulu da dai sauran su. [1] Sai dai duk da girman idanunta bata gani da rana, shiyasa ma bata yawo sai da dare, saboda idan ta fito da rana tsuntsaye da sauran dabbobi zasu kashe ta, don kuwa basa shiri ko misƙala zarratin. Itama mujiya bata barin su (tsuntsaye) da sauran ƙananan dabbobi irin su Ƙadangare saboda tana farautar su da dare tana cinye su. Akwai wani kalan kuka da mujiya take yi da dare, to idan har tayi kalan kukan dole ko wane tsuntsu ya nemi mafaka. Haka masana sun bayyana cewar ita mujiya tana Kuma da gira har guda uku (3) ta farko tana amfani da ita wajen goge ido, haka akwai wadda take ƙyafta ido, sai kuma girar da mujiya take bacci da ita, shi ya haɗa gira uku kenan. Wasu kuma suna asiri da mujiya kamar ƴan indiya. Haka kuma a ƙasar Hausa a na yin wani karin magana wai "Reshe ya juye da mujiya" [2][3][4][5][6].

  1. Lanzendorfer, Joy (15 September 2015). "15 Mysterious Facts About Owls". Mentalfloss.com. Retrieved 7 July 2021.
  2. "Abubuwan al'ajabi da ba ku sani ba dangane da dabbobi". BBC Hausa. 22 May 2020. Retrieved 7 July 2021.
  3. Qureshi, Imran (7 December 2018). "Me ya sa ake asiri da mujiya saboda siyasa a Indiya?". BBC Hausa. Retrieved 7 July 2021.
  4. Saddiq, Mustapha (16 May 2017). "To fa! An yi wa sarkin Kano asiri da mujiya". legit hausa. Retrieved 7 July 2021.
  5. Usman, Jamil (24 January 2020). "Tirkashi: Mujiya ta kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue hari a coci". legit hausa. Retrieved 7 July 2021.
  6. "Da Na Kowa Ne 08: Reshe Ya Juye Da Mujiya". dw hausa. 15 August 2019. Retrieved 7 July 2021.