Jump to content

Marcio Rosa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Marcio Rosa
Rayuwa
Haihuwa Praia, 23 ga Faburairu, 1997 (27 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
G.D. Chaves (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga

Márcio Salomão Brazão Rosa (an haife shi a ranar 23 ga watan Fabrairu 1997) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Cape Verde wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasa mai tsaron gida a ƙungiyar Montalegre ta Portugal.

Rosa ya fara buga wasan kwallon kafa tun yana da shekaru 8 tare da Escola de Preparação Integral de Futebol a Cape Verde. Ya koma kulob ɗin Portuguese Chaves a shekarar 2015, kuma bayan shekara guda a makarantar matasa ya koma kulob ɗin Montalegre a matsayin aro a shekarar 2016.[1]

Ayyukan kasa da kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

An kira Rosa don wakiltar tawagar kasar Cape Verde a watan Mayun 2018 don buga wasanni biyu na kasa da kasa.[2] Ya buga wasansa na farko a bugun daga kai sai mai tsaron gida 0-0 (4-3) akan Andorra a ranar 3 ga watan Yuni 2018.[3] An sanya sunan shi a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su fafata a gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2021 lokacin da kungiyar ta kai zagayen kungiyoyi 16.[4]

  1. "Criolos no Estrangeiro: Márcio da Rosa emprestado pelo chaves ao Montalegre". www.criolosports.com
  2. Seixas, João. "Cabo Verde: Márcio Rosa chamado à seleção" .
  3. SAPO. "Andorra vs Cabo Verde - SAPO Desporto" .
  4. "Cape Verde include veteran quartet for AFCON". ESPN. 23 December 2021.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]