Jami'ar Umaru Musa Yar'adua
Jami'ar Umaru Musa Yar'adua | |
---|---|
| |
To learn and to serve | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Umaru Musa Yar'adua University |
Iri | jami'a |
Ƙasa | Najeriya |
Laƙabi | UMYU |
Aiki | |
Mamba na | Haɗakar Ƙungiyoyin Ma'aikatun Jami'o'i da Ƙungiyar Jami'in Afrika |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2006 |
umyu.edu.ng |
Jami’ar Umaru Musa Yar'aduwa, dake cikin birnin Katsina wacce akafi sani da suna Jami’ar Jihar Katsina, a ƙarƙashin Dokar Jihar Katsina mai lamba 7 na watan Satumbar, shekerar 2006.[1] Dr. Umaru Mutallab ne Shugaban Jami'ar, yayin da Farfesa, Sunusi Mamman mataimakin shugaban jami'ar wato, (Vice Chancellor).[2]kuma ya gaje shugabancin ne daga hannun tsohon shugaban Prof. Idris Isah Funtua.
Tarihi.
[gyara sashe | gyara masomin]An kirkiro Jami’ar a shekara ta 2006 a Jihar Katsina. don zama tushen ci gaban tattalin arziki, fasaha da siyasa na Jahar ta hanyar samar da ƙwararrun masaniyar ɗan adam ta hanyar salon koyarwa na fuska da fuska da na nesa. Burin gwamnati ne da al'ummar jihar Katsina su kafa jami'ar da zata shiga jerin kwararrun Jami'oin duniya ta hanyar sadarwa na zamani wato(ICT). Jami'ar ta fara shirye-shiryen karatun ne a cikin watan Janairun, shekarar 2007 a wani rukunin lokaci na wucin gadi wanda ke Hassan Usman Katsina Polytechnic, Katsina.[3]
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yanke shawarar canzawa makarantar suna daga "Jami'ar Jahar Katsina" watau (Katsina State University) zuwa "Jami'ar Umaru Musa Yar'aduwa, Katsina" (Umaru Musa Yar'aduwa University, Katsina) a ranar 08 ga watan Aprelu, shekarar 2009.[1] Anyi hakan ne don nuna yabo na musamman ga tsohon gwamna kuma shugaban ƙasa na lokacin, Umaru Musa Yar'aduwa - Matawallen Katsina.[1] Bayan kwana ɗaya da canjin sunan makarantar, shugaban ƙasan Nijeriya na lokacin, Marigayi Umaru Musa yarduwa ya bada fili mai girman hekta 1029.33 akan hanyar Dutsin-ma, don gina jami'ar a wurin na dun-dun-dun. Anyi taron buɗe makarantar a ranar 09 ga watan Aprelu, shekarar 2009.
Tallafin Naira Biliyan 4
[gyara sashe | gyara masomin]Ranar 2 ga watan Nuwamba, 2022 Gwamnatin Tarrayya Ta Tallafa wa Jami'ar da Naira Biliyan 3 don ƙara bunƙasa ta gami da yin sabbin Gine-gine a Jami’ar.
Har wayau kuma Gwamnatin jihar ta ƙara Naira Biliyan 1 akai don fara aiwatar da aikin gadan-gadan.
Gine-ginen dai da za'a yi sun haɗa da gidajen wasan kwaikwayo na lacca, da shingen gudanarwa, ɗakunan gwaje-gwaje, wuraren kiwo da sauransu.[4]
Tsarin Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An tsara makarantan don bada Ilimin digiri tun daga digiri na farko (Undergraduate degree), digiri na biyu (Masters degree) da digiri na uku "Daktanci" (Doctoring degree) har zuwa digiri ta qoli "Farfesanci" (Professorship). Akwai fannuka daban daban wanda suka hada da; # Fannin Kimiyya,
- Fannin fasaha
- Fannin Karatun Alqalanci, da
- Fannin Karatun Koyarwa
- Fannin Likitanci
Fannin Kimiyya Wannan fanni ne da ya kunshi sassa na karatun binciken abubuwa masu rai da marasa rai dake cikin duniya da wajen duniya. Ana kiran wannan fanni "Science", kuma wannan fanni a wannan jami'a yana da sassa kaman haka;
- Sashen lissafi (Mathematics and Computer Science),Biology,Chemistry, Physics da kuma
- Sashen karatun Geography. Ana kiran sakamakon wannan fanni " Bsc" wato (Bachelors of science) kuma anfi sannin wannan Fanni a turance da "Faculty of Natural and Applied Sciences".
Fannin kimiyya da Fasaha Wannan fanni ya kunshi kwasa-kwasai da suka jibanci fasahan rayuwa da kuma ilimin zamantawar dan-adam. Wannan kwasa-kwasai sun hada da;
- Karatun Tarihi (History), Yaruka (Languages) kamansu Turanci, Larabci, Faransanci da sauransu.
- Har wa yau akwai sashen karatun addinai,daban Dayan kamar Musulunci da kuma Kiristanci wato "Islamic Studies" da kuma"Christian religious Studies". Ana kiran sakamakon wannan fanni da " B.A" (Bachelors of Art).
Fannin karatun Alƙalanci Wannan fanni anfi saninshi a turance da " Faculty of Law" wanda ya jiɓanci karatun alqalanci ko lauyanci. A karkashin wannan fannin akwai sassa kaman,
- Sashen Alqalanci na Shari'ar Musulunci (Islamic Shari'a Law)
Fannin Karatun Koyarwa Wato "Faculty of Education" a turance. Wannan fannin ya jibanci koyar da ilimin malumta ko koyarwa. Wannan fanni ya shafi horar da malamai a fannin kimiya da fasaha da kuma Alqalanci baki daya.
Darussa
[gyara sashe | gyara masomin]A ƙasa akwai jerin kwasa-kwasan da jami'ar ke bayarwa bisa ga faculty ɗin su;
Faculty of Humanities
[gyara sashe | gyara masomin]- Arabic Studies
- English Language
- French Language
- Nigerian Language (Hausa)
- History
- Islamic studies
Faculty of Natural and Applied Sciences
[gyara sashe | gyara masomin]- Biochemistry
- Biology
- Chemistry
- Industrial Chemistry
- Computer Science
- Geography
- Mathematics
- Physics
- Microbiology
Faculty of Education
[gyara sashe | gyara masomin]- Education and Arabic
- Education and Biology
- Education and Chemistry
- Education and Economics
- Education and English Language
- Education and Geography
- Education and Hausa
- Education and History
- Education and Islamic Studies
- Education and Mathematics
- Education and Physics
Faculty of Law
[gyara sashe | gyara masomin]- Islamic Law
- Common Law
Faculty of Social and Management Science
• Accounting
• Business Administration
• Economics
• International Relations
• Political Science
• Public Administration
• Local Government and Development Studies
Additional programmes
The National Universities Commission has approved for the establishment of fourteen (14) new programmes in the university as follows:
- Medicine and Surgery (MBBS.)
- Forestry and Wildlife Management (B. Forestry)
- Integrated Science (B.Sc. (Ed.))
- Business Studies Education (B.Sc. (Ed.))
- Primary Education Studies (B.A. (Ed.))
- Early Childhood Education (B.A. (Ed.))
- Special Education (B.A. (Ed.))
- Computer Science Education(B.Sc. (Ed.))
- International Relations (B.Sc.)
- Environmental Management (B.Sc.)
- Local Government and Developmental Studies (B.Sc.)
- Meteorology (B.Sc.)
- Agricultural Science B. Agric)
- Fisheries and Aquaculture (B. Fisheries)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Brief History – Umaru Musa Yar'adua University Katsina". Retrieved 2021-04-12.
- ↑ "UMYU Appoints Sanusi Mamman as New Vice Chancellor". Allschool. 2020-07-05. Retrieved 2021-04-14.
- ↑ https://www.umyu.edu.ng/index.php/2017-03-24-22-03-38/about-umyu/283-introduction[permanent dead link]
- ↑ https://katsinapost.ng/article/32993/gwamnatin-tarrayya-ta-tallafa-da-naira-biliyan-don-yin-gine-gine-a-jami-ar-umyu