Filin wasa na King Power
Filin wasa na King Power | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Birtaniya |
Constituent country of the United Kingdom (en) | Ingila |
Region of England (en) | East Midlands (en) |
Ceremonial county of England (en) | Leicestershire (en) |
Unitary authority area in England (en) | City of Leicester (en) |
Coordinates | 52°37′13″N 1°08′32″W / 52.620277777778°N 1.1422222222222°W |
History and use | |
2015 Rugby World Cup | 2015 |
Ƙaddamarwa | 23 ga Yuli, 2002 |
Mai-iko |
King Power (en) TIAA (en) |
Wasa |
rugby union (en) ƙwallon ƙafa |
Occupant (en) |
Leicester City F.C. 2002 Leicester Tigers (en) 2005 - 2009 Leicester City W.F.C. (en) |
Maximum capacity (en) | 32,261 |
Contact | |
Address | Filbert Way, Leicester LE2 7FL |
Offical website | |
|
Filin wasa na King Power (wanda kuma aka sani da filin wasa na Leicester City a dalilin kuwa dokokin tallafawa UEFA kuma wanda aka fi sani da filin wasa na Walkers) filin wasan ƙwallon ƙafa ne a Leicester, Ingila.[1] Ya kasance gida ga kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta Gasar Premier tun daga shekara ta 2002 kuma filin na da yawan kujeru 32,261. Tun daga 2021, filin wasa kuma ya kasance gida ga kungiyar kwallon kafa ta matan Leicester City.[2]
Tarihi
Fage da gini
Filin wasan Leicester na baya yana kusa da Titin Filbert, wanda ya kasance gida a garesu tun 1891. An inganta shi a hankali a karni na 20th kuma tare da zuwan Rahoton Taylor a watan Janairun 1990 yana buƙatar duk kungiyoyi daga buga manyan gasa guda biyu su sami filin wasa na kowa da kowa a watan Agusta 1994, darektocin Leicester City sun fara binciken gina sabon filin wasa a farkon shekarun 1990s, amma sun yanke shawarar ɗaukar zaɓin sake fasalin ta hanyar gina sabon fili a ɗayan gefen titin Filbert da kujeru masu dacewa a cikin sauran wuraren da suka rage, yana ba filin wasan damar zama 21,500 gabaɗaya ta lokacin 1994-95.