WASU Zawarawan
WASU Zawarawan
@2021
~Mallakar zeesardaunerh~💜🖤
Allah yai dadin tsira ga Annabinmu Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam da Ahalinsa tareda
Sahabbansa baki daya
Ina rokon Allah Mabuwayi Gagara misali yadda ya bani ikon fara wannan littafi mai albarka ya
gwadamin na gamashi lapiya
Allah yasa kasa Al'ummar musulmii su amfana da da russa na kwarai dake cikin wannan littafi
kuma in akwai mai irin wadannan halayyan Allah yasa ta daina
Ina ma masoyana fata Alkhairi a ko ina suke 🙏❤️❤️❤️❤️
_Wannan shafin na kine ummu_ _munaifah( Ayshert_ _sardaunerh)_ ~godiya dubu~ ~tare da fatan
Alkhairi Allah~ ~barmu tare~ 😻😍🥰
_________________
______
𝗶𝗿𝗶𝘁𝗲
𝗺
𝗿𝘂
𝗮 𝘀𝘀
𝗱
𝘁𝗲
𝗶𝗮
𝗰
𝗼
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*page* 1~~2
Zaune take bisa tabarma tana tsintar shinkafar hausa tana sauraron wakar hamisu breaker, a gidan
redio da yar karamar salularta. Akalla baza ta wuce shekara talatin da takwass ko Arba'in ba sai
mita take yi "ohni saudatu ni wlh na gaji da wannan rayuwa a ce ko yar shinkafar ga ta gwamnatii
dai mallam ya sayo mana mu tuka amma yakiya a'a, ko da yaushe sai dai yace babu babu kamar
kansa a ka fara talauci ko wurin abokanansan nan yaje ya aro koda bashine dai ya sayo muci
kamar yadda su laure kayi, amma sai dai yace Ayi hakuri wata rana sai labari ni gsky na gaji da
hakurin nan mssssstwwwwwssss". Ta k'arashe maganar tana jan dogon tsaki. Alokacin da aka turo
kyauren gidan tare da sallama ciki ciki inna saude ta amsa sallamar yayin da naga wata mata
shiyar budurwa wadda ba za ta wuce shekara goma sha bakwai ba ta fito a cikin wani dan madai
dai cin daki sanye da wata kodaddiyar atamfa, ta yo wurin wannan mutunen da ya shigo wanda
akalla zai kai shekara hamsin amma idan ka kalleshi so daya baza kace yakai hakan ba domin irin
jikin fulani ne dashi daka gansa zakace tabbass bafulata ni ne ta durkusa tace "bappa sannu da
zuwa ya kasuwa?". Dadai lokacin da yazauna bisa tabarmar tare da amsa mata da cewa "yawwa
mamana da fatan na same ku lapiya". Tace "lpy lau baffah". Yayin da ta tashi ta nufi wurin tulun
su ta kawo mai ruwa mai sanyi, ya karb'i ruwan yace" nagode mamana Allah ya miki Albarka".
"Ameen Baffana". Ta fad'a tana murmushi.
Bayan ya gama shan ruwan ne yace "Hala ina auta naga bangan ta ba". wannan yarinyar da ya kira
da mamana tace "inna ce ta aiketa gidan su inna laure ta anso mata kuka". yace "tou". tare da nufar
dakinsa a yayin da ko kallo bai ishe inna saude ba balle ai maganar gaisuwa dan haushinsama take
jii yanxu shiya takasa yi masa magana yau kenan ko naman dari biyun bai riko asa a miyaa ba
Guduu kawai yake a mota da'alama sauri yake domin gudu yake shararawa a bisa titi Allah ne
kawai yakai shi gida lapiya domin yayi mantuwan wasu files a gida gashi kuma urgently ake
bukatarsu yana isa bakin wani makeken gate yai parking ko motar bai shiga da ita cikin gidan ba
ya bude marfin motar ya zuro kafafunsa waje da dan sauri sauri mashaallh shine abunda nace a
lokacin da nai tazalii da kyakkyawar fuskar sa ma'abociya haiba da kamala matashin saurayi
kenan maiji da kyau da kudii Aliyu muhammad Ahmad da daya tilo ga Alhj muhammad Ahmad
mai xinaree Shahararren mai kudin da yayi suna a fadin nigeria yana da companies a garuruwa da
dama za kujii cikaken labarinai nan gaba
Noking din gate din yayi Ila mai gadi ya bude ya shiga ko saya amsa sallamar mai gadii bai yiba
yai cikin gidan direct da sallama ya shiga cikin palon da sallama kamar yadda yasani haknne ko a
yanxun zune take bisa kujerun da suka kawata dakin tana charting a wayar ta kirar iphone 12plus
karar takalmi da tajine alamun an shigo yasa ta dago kanta tare da daga yan yasunta tayi waving
dine maana hiiii taci gaba charting dinta bai kulata ba dan inda sabo yaci a ce yasaba da halin
suhailat direct uptchers ya nufa tareda shiga room dinsa after 3mint ya fito tare da files din ya fita
ko adawo lpy bata masa ba gaba daya ma bata san ma ya fito ba yaja motarsa tare da nufar A.M.A
COMPANY .................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh*
( ~yar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
#share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Page* 3~~4
Da isar sa A.M.A COMPANY direct office dinsa ya nufa bai tsaya b'ata lokaci ba yakira waya
bayan yan mintutka akayi noking "yes come in", cewar Aliyu wanda ake kira Haidar mik'awa
mutumin da ya shigo files d'in yayi ya ce "ya kaiwa accounter bayan fitar", mutumin ya duba time
yaga 2:15 dafe goshinsa yay yace "oh Allah!", tare da nufar toilet din da ke cikin office d'in na sa,
tsayawa misilta muku yadda toilet din yake bata lokacine domin komi na Aliyu haidar yana yinsa
ne a tsari Alwala yayi bayan ya gama ne ya shinfid'a darduma ya kabbarta salla domin tawucesa
balle yace yy a masallacin companyn.
"Aleeya! Aleeya!! Aleeya" shine sunan da naji inna Saude na kira kamar mai shela a anguwa da
sauri wadda naji an kira da Aleeya ta fito daga dakin su, matashiyar buduwar nan ce ta d'azu da
mallam Yusuf ya cewa Mamana "masha Allah fata barakallahu Ahasanul halik'in", kyakkyawa ce
ajen karshe duk da talauci ya nakasar da kyawunta kallo d'aya xaki mata kice wannan ta had'a jinsi
da larabawa bai wai dan kyanta yayi yawa bane aa irin sihirtaccen kyawun nan gareta wanda idan
mai kallo ya tsureta da ido domin wai ya gano muninta to Allah kyawu zai ga ta k'ara masa tanada
round face irin wacce ake so ga zara zaran eyelashes tareda dogon hancii had'i da pink lips,
bakinta dan k'arami dashi zaka iya rantsewa hannun ta baza ya shiga ciki ba Allah ya mata diri mai
kyau kamar ita tayi kanta shiyasa bata fita da gyale, a rayuwata ako ina take tana saye da hijab
wani time ma harda liqab, a yanzun ma hakanne sanye take da hijab d'inta wanda ya wuce mata
guiwa ta durk'usa kusa da inna Saude tareda cewa "dan Allah Inna kiyi hak'uri koda kika kirani ina
sallah ne shiyasa ban amsa da wurii ba", tsaki inna taja "msssttwwwssss", tare da cewa "kedai kika
sani kin shige d'aki kin dunkule salon malam yazo yace an maki wani abu nidai dan Allah tashi ki
had'a wuta ki d'ora sanwar tuwo kinga uku ta kusa" da "to", ta amsa tare da nufar wani gun da
alama kici ne..............................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh*ce*
# _Comment_
# _like_
# _share_
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*page* 5~~6
Itace tadauka tasaka cikin murhu ta fara hasa wuta domin daura sanwar tuwon, yayinda inna
Saude Ta shige daki abunta.
Wani kololon bakin cikine ya to kare masa wuya alokacin da ya shiga palon da ko arzikin
shara bai samu ba.
Zaune take bisa karfet tana karatun littafan hausa da ta saba yi .
Ya yi sallama har sau ukku kafin ta amsa domin hankalinta ya tafi a karatun littafin da take.......
"Abban Khaleel Nidai gaskiya ka rage yi min wannan kallon na kuriila haba kamar na
chanxa maka" cewar Azeema Kenan ya yin da take turo bakin ta cikin dan shagwaba,yanda takeyi
baza kace ta haifi yara biyu ba.
" Soory dear baxan kara ba kinjiii" cewar Abban Khalil,
"ok najii kar ka sake, ko jiya haka kace baza ka koma ba amma gashi yanxu ka sake yiii"
" Ai kedin ta da ban ce shiyasa ako da yaushe bana gajiya da kallanki, dear ko da yaushe kara
zama yarinya kike kamar ba kece kika haifi khaleel Da khaleela ba".
"Eh mana ai na fahimce so kake na tsufa ka kawomin wata .." tafada tana bata fuska Alamu bataji
dadi baa.
"Sorry ba haka nake nufi ba dear, ai daga ke ba karii, kece Uwar gidana kuma Amaryata
inshaallah ."
"Humm Abban Khaleel karkasa na sakankance da zantukanka rana tsaka najii kace Aure zaka
karaaa nidai abar maganar kawaii "
" Najii amma kesan irin tarin san da nake miki ko??
Kina ganin cewa akwai wani gurbi A zuciyata bayan nakiii ?
Ke kadaice muradin zuciyata, ban rasa komii a wajenki ba to karin aure namii?
Kisa a ranki ni Abubakar Na kine ke kadaiii har abadaaa.
Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, ya yin da ta afka cikin kogin tunani....
Shiyasa a koda yaushe take alphari da jarumii kuma gwarzon sahibintaaa,shi tafara so a duniya
kuma har karshen rayuwarta hakanne da yardar Allah.
A duniya bata tantamar kaunar da Abban Khaleel Ke mata, shiyasa bata sama ranta cewa ita
kad'ai zata zauna dashi ba kamar yadda *WASU MATAN* Keyi idan suga miji na son su sosai.
Tasan cewa Aure lokaci gare shi kuma muddin na Miji ya yi niyar kara Aure to ba fashi sai
wani ikon Allah.
Guiwar ta tana sanyi ne a duk lokacin da ta tuna cewa Uwar Mijinta ba son ta ta take yi ba.
Bawai tana tsoron kishiya bane,a'a tana dai tsoron Abunda zai rabata da Mijinta Abun
Alfaharin ta.
A Wannan zamanin da muke ciki da mutane ba tsoron Allah a zukatan su, bata san wace za'a
kawo mata ba.
Tasan halin *WASU MATAN* ba Imani gare su ba shiyasa take jin tsoro.
Gidan Mallam Abubakar Kenan shida matarsa kuma y'ar uwar sa Azeema Tare da y'ay'an su
twins Khaleel da Khaleela.
Mallam Usman Yana da Mata biyu Y'ay'a biyar Hawwa'u Da Hadiza Sune Matansa.Inda
Hawwa'u Keda Y'ay'a hudu duk mata. Aisha,Fatima,Firdausi,Fareeda , inda suke kiranta da Mama.
Itako Hadiza d'a d'aya Allah ya bata Abubakar, suna kiranta da umma.
Mama ta kasance mutum mai hakuri da kawaici ,Umma kuwa masifaffiyar mace ce ta bugawa
da jareeda ga shegen kishin tsiya .
Allah bai had'a jinin ta da na maman Azeema Ba, dan kawai suna mugun shiri da mama.Itako
ana ta tunanin duk mai son mama mak'iyin ta ne.
Malam Abubakar Mallamin Islamiyya ne acikin unguwar su Aleeya Mabera A Garin Sokoto.
Ya kasance d'an uwa ne ga Azeeema.
Yan zu haka shekarar su biyar da Aure da Azeema Kawar Aleeya; Kuma ya kasance shi ke karba
musu hadda a Islamiyya.
Tawannan hanyar ne soyayya mai zafi ta kullu tsakanin sa da k'anwar shi Azeema har ya kai
ga sunyi aure Allah ya albarkace su da y'ay'a biyu, yanxu haka shakarar yaran hudu da watanniii .
Rayuwar Gidan abun burge wa ce ga kowa domin zallar soyyayya suke shinfidawa a cikin
gidansuu.
Matsala dayace suke fuskanta Arayuwar Auren su;wannan matsala kuwa itace k'iyayyar da
Ummarsa ke wa Azeema Tayi yawa bata san Azeema Ko kad'an; dan k'awai takasance y'ar
aminiyar umma.
Da Mahaifinsa da Mahaifin Azeema Uwar su d'aya ubansu d'aya; su yan Asalin garin sakkwato
ne (A karamar hukumar wurno ).
A lokacin da Umma ta matsa masa ya fidda mata yayi Aure bai dace ya zauna haka ba tunda
ya Kammala Digree dinsa a fannin computer,kuma yana Koyar Wa a Islamiyya yana samun
abunda ke shigo masa; "yace mata ai Azeema ce zabinsa"," fada ta dingayi ba ka'kk'autawa, a duk
cikin y'ay'an abokannan ta dake sansa baza yazabi wata cikin su ya aura ba sai yace wai sai
Azeema Baa Azeema Ba wallah uwarta ita da ta haifeta. "Dallah tashi ka bani guriii dan neman
shanyayye kawai an wanke an baka ka ka shanye dan anga kai d'aya ne gareni,to bara a bid'i
hanyar ra bani da kai"," tasss ta masa tare da ce wa kar ta sake jin maganar".
Mama na jinsu ko k'ala ba ta ce ba ta sa musu i'do kuma ta hana ya'yan ta tank'awa musamman
Aisha Uwar jidali.
Ha kuwa a kayi Abubakar bai k'ara tada maganar ba sai da ummansa tayi tapiya, bayan
tapiyar ta k'auyen su buki y'ar d'an uwanta ne Abubakar Ya tunk'ari mahaifinsa da maganar kuma
ya yi farin ciki sosoi har da sa masa Albarka, k'oda Umma ta dawo ta iske har an yana ka sadakin
Abubakar da Azeeema. Ranar gidan sai da ta tashi hank'alin kowa na gidan ta hana su barci lafiya
tace danta baza ya Aure waccan abar ba.....
Shiko Malam Usman Yace mata tayi karya wallahi dan aure tsakanin Abubakar da yar d'an
uwansa anyi angama, in ko tace bahaka ba saidai takoma gidansu da zama, da taga malam yadau
zafi da yawa har da batun sakii sai ta hakura amma tayi alkawarii sai Abubakar ya aure binta diy'ar
k'awarta Hinda wacce ita ke kara tinzira ta.
Haka akayi bukii Uwar Ango bata so balle k'auna kuma har yanxu ta tsane Azeema fiye da da
dan cewa take sun shanye mata d'a kuma tanan kan bakan ta na Abubakar sai ya kara
Aureee ...............................✍️✍️✍️
Tofah wai matar d'an sanda ta haifi barawo, ku biyoni domin ganin yadda wannan chak'wakiyar
zata k'aya.
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*page* 7~~8
Duke take a bakin murhuu tana fitar wutar itacen duk hayak'i ya cika gidan sakamakon itacen da
take amfanii dasuu dan yu ne, duk idanunta sun cika da kwalla, fita kawai take amma wutar taki
kamawa sai dan banzan hayakin da takeyiii "sallamar k'anwar ta Salamatuu Tajii tana k'walawa
inna Saude Kira, inna inna ga kukar na k'arbo miki, kuma tace nace tana gaishekiii"
Inna Saude Ce dake fitowa daga ciki dakin ta, "tace yanxuu Salamatu Dan kin rainani shine
baza ki shiga ciki ki mik'amin shine kike ta k'wallamin kira haka", maganar tace ta katse a lok'acin
da hayak'ii ya mata maraba.
"Innalilla'hi wa inna ilaihi raji'oon tafada tare da rafka salati",wanda yasa sai da Aleeya Ta mike
tsaye da sauri, "yayin da inna Saude Tace, yanxu Aleeya kina zaune gidannan ya cika da hayak'ii
amma ko ki heta wutar nan".
"Wlh inna ita ce nake hetawa tun dazuu cewar Aleeya amma taki kamawa", "ok to bara nazo na
heta miki k'ar ki ci gaba da hetawar"cewar inna Saude Tana kok'arin komawa cikin d'akin.
Maganar Salamatuu Ce ta katse mata hanzari yayin da take cewa "ni gaskiya inna nace miki
kidaina cemin Salamatuu".
"Salmaat ne suna na fah, amma k'in ki barin kirana hakan, kin maida min suna sai kace na
tsoffi tafada cikin shagwabaa".
" Yi hakurii auta bazan k'ara ba kinji", "murmushi salamatuu tayi", "inna Saude Tace ko kefa
autaa, tare da shiga cikin dakin ta da ko arxikin ledar kasa bai samu ba balle ai maganar kujeruu....
Salamatuu Ko nace Salmaat Ce ta nufi wurin Aleeya Tana cewa "Addana sannu da aikii",
"Eh tace tare da cewa Addana wannan wutar ba kamawa zatayi ba,naga da alama itacen nan
danyu ne, bara na k'arbo kudii wurin inna na sayo miki yanga", (tafada cike da tausayin y'ar
uwarta kan hayakin da take sha).
"Aa Adda bara na k'arbo dai tafad'a tare da nufar dakin inna Saude, ko sauraren Aleeya Bata
tsaya yi ba tashiga dakin tana cewa inna bani kudii na k'arbowa Adda yanga, itacen chan basa ci
suna bata wahala sosai".
"To ni dai kiyi hakuri dan Allah" kan wannan dalilin tasan halin innar ta ta cewa zatayi batada
su, dan shegen son kudin tsiya gareta,shiyasa ma bata biyema fad'an da take mata ba ta bata
hakuri, tare da cewa" ni dai dan Allah inna ki bani na sayo mata mana, kinga lokacii na tapiya
hudu ta kusa gashiii kuma 5:30 zamu tafii makarantar dare".
Bata rai salmaat tayi dan Allah ya sani tatsane wannan abun da innar ta kema bappan su sai dai
ba yadda ta i'ya ne,mai hali baya fasa halinsa in da sabo yaci ace ta sabaa.
"Naji nidai in kina bani ki bani kawai basai kinsaya kina zagar min uba ba cewar salamat cikin
baata rai wlh auta kin cika rigima da yawa, girma kike bakya hankali kin mai dani sa'ar ki, ko nace
kakar ki, ungo nan dan ALLAH ki fice ki bani gurii" ta fada tare da mika mata naira hamsin.
k'arban kudin tayi tareda fita a dakin tana cewa mungode innataaa.
Nufar wurin murhun tayii da yake cikin fillin gidan domin taa nunawa Aleeya kudinn.
"Addana kinga inna ta bada hamsin a sayo yanga"!
" iyee cewar Aleeya cikin sassanyiyar muryar ta, tana cewa munko gode ALLAH ya kara
arzikii, yayin da salmaat ta fita domin sawo yangar wurin idii mai kayan miyaaa.
Aleeya kuwa cikin ranta Alhmdllh take cewa dan bata sa sanmanin inna Saude ta bada kudin
yangar ba, domin kowa yasan halin inna saude da mugun son kudin tsiya.In tana tanadin naira
hamsin sai kin dauka nera dubuu ce.
Allah ne ya dubeta da idon rahama ya rage mata wannan wahar hashin wutar, ya yin da take
saka itace a dayan murhu domin ta d'aura sanwar miya take wannan zancen a zuciyar ta.
Ta amsa sallamar ranta a bace, tana cewa.... "haba haba yaya kabeer a gaskiya ni ba ka
kyautamin wlh kayi sallama kaji ban amsa ba ai sai kamin uxurii ko? amma sai kayi ta rangada
sallama sai kace mai shela a garii, haba dan Allah taja wani wawan tsakiii.
Duk fadan da yayi niyar yi mata suna hada ido sai ya kasa cewa komi, domin in yana tare da
maryam mance komii yake, baya iya tabuk'a komiii sai abunda ta sashii.
"Cikin kwantar da murya yace mata kiyi hakuri" dauke kai kawai tayi ta ci gaba da karatun
novel dinta.
kusa da ita yaje ya zauna yana cewa "haba maryama gimbiyar mata ki hakura mana! na bakii
hakuri kinkyaleni."
"Inshallah bazan koma ba" (ya fada cikin lalama) "daya fi ma dai" cewar maryam.
Gidan su ya nufa dake cikin unguwar Runjin samboo domin ya gaida iyayensaaa.
Abangaren A.M.A(haidar) kuwa,bayan ya tashi daga aiki a company,tafe yake cikin motar sa
kirar Benz yana waya cikin zazzakar muryarsa, Ahankalii yake driving kamar wanda baya son yin
tukiinn.
Waya yake ki da'alama da mahaifiyarsa ce, domin sai narke mata yakeyi kamar mai waya da
budurwarsa; chan najii yana cewa "ok momy zan shigoo Abuja inshaallah before next week"shiru
yayi a dayan bangaren tayi magana, sai cewa yayi "dear yanxu ina kan hanya ne" banjii mi tace
masa ba "najii yace ok bye luv u much my dear" tare aje wayar.
Area dinsu ya nufa dake cikin sama road,wasu jerin gidaje na gani masu mugun kyau, wurin
makeken gidan nan na d'azu naga ya nufa tare da danna order, da hazarii mai gadii ya wangale
katon gate din gidan ya cilla kan motarsa ciki.
Bayan mai gadi ya kulle gate din da guduu yazo gurin motar haidar dake kokarin fitowa ya
durkusa yana mika gaisuwa, amsa masa yayi tare da wucewa cikin gidan,shiko mai gadi ya wuce
zuwa aikinsa.
Cikin makeken palon ya nufa tare da sallama kan lips disa, duk da yasan da wuya ta kasance
cikin palon koda ma tana nan baza ma taji mi yace ba,hasashen sa ne yazama gaskiya A lokacin da
ya isa tsakiyar palon, bai saya bi takanta ba dan duk a tunaninsa tana room dinta.
Uptchairs ya haye tare da nufar room d'insa, yana shiga cikin palon da yafi na d'azu tsaruwa da
haduwa nace wow mashaallah... ina mai bin katoton palon da kallo tsaya misilta muku yadda
palon haidar yake bata lokacine,bangama karewa dakin kallo ba dga ya nufi wani room na daban a
cikin palon, da hanzari na bi bayansa.
Hmmm da ace kudii na magana a duniya da sai sun maganta a wannan dakin, bawai dakin
ma kad'ai ba, gidan ma baki daya zai maganta.
Zaunawa ya yi a bakin lallausan bed dinsa yafara cire takalminsa, tare da zare zara zaran yan
yantsun kafarsa dake cikin safa ya cire suit dinsa ya daura towel.
Bathroom room ya nufa..... hmmm komi na haidar daban yake, duk da da bathroom din
tamkar ka shiga wani palon ne na daban,fita nayi nabashi gurii.
Ina cikin room din ina kalle kalle naji alamun ya fito direct gurin miro yanufa ya zauna bisa
kujera yana shafa lotions, shafa wancan..fesa wanchan,sai da ya kwashe 30mint kafin ya nufi wani
gurin da duk glass ne baza ka d'auka akwai wani abu a wurin ba.
Hannu naga yasa ya danna wani abu red a gurin, take wannan wurin ya bude, (hmmmmm in ana
salla ba'a magana) kunsan mina gani kuwa? wani karamin .........................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
plss kuyi voting and comment shike karamin karfin guiwa
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Page* 9~~10
part d'in jallabiya ya nufa tare da d'aukar milk colour,the same thing yadanna abun nan na d'azu
sai gurin ya koma yadda yake.
Bayan yasa jallabiyar sa ne ya fesa turaren sa Imperial Majesty(the most expensive male perfume
in the world) ya ma jikinsa wanka da perfume kamar ba gobe bcox Allah ya yisa mutum mai
masifar son kamshi;lallausan takalminsa yasa a kafarsa masu masifar laushi tare da nufar
palon,gurin fridge ya nufa tare d'aukar one bottle water ya fita.
Part d'in Suhailat Ya nufa ya mird'a handle din kofar ta ta yaji a kulle, dama yasan a rina (wai an
sace zanen ma haukaciya).
Suhailat Ce zata zauna a gida ba tare da ta fita ba,ya d'an tabe cute pink lips d'insa tare da cewa a
ransa "whether tana nan or not duk uwarsu daya tunda bata san darajar aurenta ba".
Fita yayi daga part d'in, because lokacin magrib ya kusanto direct masallacin da ke cikin gid'an
ya nufa, a gurin ne ya hadu da ila mai gadi cikin husky voice d'insa yake tambayar sa"Suhailat ta
fita ne?" "eh dazu bada jimawa ba, bayan ka koma office" "ok" yace lokacin da suka shiga
masallacin.
"Salmat Yi sauri mana kinga time na tafiya kar muyi latti","gani zuwa adda littafaina ne na
dauka"cewar Salmat Yayin da take fitowa daga cikin dakin su,"ko kefa,kina son muje ne mallam
Nura Yamana bulalar latti?"
"A'a adda,kuma kinsan baida mutunci bulalarsa mugun zafi ke gareta."
Dariya Aleeya Tayi saida gav teeth din ta ta bayyana tana cewa"Aiko saina gaya masa abunda
kikace", "sorry Addana karki gaya masa kinji,amma gaskiya na fada ai ko?"
Murmushi kawai Aleeya tayi tare da jan hannun k'anwarta tace"nidai mutafi kinga time yana
tafiya", "ok" Salmat Tace suka nufi dakin inna Saude .
Sanye suke cikin tupapin islamiyya ash colour,riga da wando ne sai dogon hijab white colour
wanda ya wuce guiwa amma na Aleeya har kasa yake,suna cikin tapiya suka hadu da kawar
Aleeya mai suna Amina Tare da k'anwarta Bilkisu Yar kimanin 13Years,suka hadu waje guda
suka nufi makarantar.
Bayan sun isa makarantar ne kowa ya nufi class dinsa.Aleeya Da Amina ajinsu guda a both boko
and islamiyya,haka ma Salmat Da Bilkisu.Gidan su Amina yafi kusa amma basu da wani tazara
tsakaninsu da su Aleeya.
"Sallama" sukayi a ajin sauran yan class din suka amsa, sit dinsu suka nufa suka zauna tare
da mikawa sauran frnd dinsu hannu suka gaisa.
"Ai na d'auka ko yau sai kunyi lattin"cewar Ummi(Maryam) d'ai daga cikin frnds d'insu," dariya
sauran suka sa Rahma Ta ce "kinsan Aglaa(Aleeya)da shegen tsoron bulala ko kad'an bata san abin
da zai taba lafiyar ta ai", "da gaskiyarta wlh wake son a taba masa lapiyar jikinsa, hardai waccan
malamin mai shegen zafin hannu" cewar Aisha, Amina tace "wlh ko" duk dariya suka sa,A lokacin
kuma malami ya shigo ajinnasu.
Aglaa shine sunan da frnds dinta ke kiranta dashi,Aglaa kalmar larabci ne ta na nufin(Mai
tsada),suna kiranta da mai tsada ne saboda baiwar kyau da dirin da Allah yai mata,ga kuma
nutsuwa da kaifin basirar da Allah ya bata.
A yanxu haka Aglaa hizib dinta Arba'in da harda,kuma ta sauke Alqur'ani mai girma tun
bayan shekara hudu da suka wuce , a cikin littafai kuwa ta kammala Usulull-
fiqihu,Ahdari,Ishimawee,yanxu haka tana cikin iziya.Bangaren boko kuwa tana ajin karshe SS 3
kenan.
Allah ya mata baiwar basira hakanne yaja mata farin jini ga malami maza da mata da kuma
dalibai;yanxu haka ita ce food prefect (mai kula da tsaftar abincin dalibai).
cikin ransa yake cewa daga gaisuwa "toh Allah sawwaka" ya tashi ya fita.
Wurin abokanansa ya nufa suka d'anyi fira kafin yace" bari na tafi gida karna biye ma
gwauraye"ya fada yana dariya,"mun daiji,muma ai lokaci na nan tafe"cewr daya daga cikin
abokanansa,guda kuwa cewa yayi "gwara ka tafi tun bata fara cigiyarka ba tunda ka koma mijin
tace" dariya sauran suka sa masa"nadaijiya kumi za kuce" ya fada yana hawan mashin din sa
Ko da ya isa gida tsare shi da tambaya Maryama Tayi tana cewa "daga gidan ubanwa kake" "lfy
dai ko?" ya tambayeta "lafiyar ce ta kawo haka" tafada tana jijiga jiki.
yarasa ma wace amsa zai bata,wai kamar shi da gidansa dan ya fita sai an tambayeshi daga
gidan uban wa yake?
Bai san lokacin da ya ce mata ba daga gidan Uban................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like__
# _Share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Page* 11~~12
"Ubana?"
"Ubana kace fa?"
"to waya sani" tapada tana jan tsaki, "tou wai tsayama mika je yi a chan din??"
"kamarya? banfahimci tambayarki ba"
"ai nasani bazaka fahimta ba, tunda kana chan tare da wadan chan makirran..." bata karasa
maganarta ba ya tari numfashinta cikin bacin rai yake cewa "su waye makirran??"
"kafini sani ai"cikin ranta kuwa mamaki take taya kabeer ya samu kwarin guiwar da zai tsaya yana
ja'inja da ita anya...
maganarsa tadawo da ita duniyar tunanin da ta lula.
"Na fiki sani? Uwar ta wace makirar ko k'annena?" ya fada cikin muryar da ta d'an tsorata ta
amma sai ta waske bata nuna ba tayi k'asa da muryarta tana cewa" duka "tare da tabe baki.
Da tsauri ta dafe kunchin ta saboda wani azababben zafi ne ya ratsa shi da zuciyarta tare da kai
ziyara a k'wakwalwarta,batare da ta dawo hayyacinta ba taji wani zafin a dayan kunchin, bata ma
san lokacin da ta lailayo ashar ba tana nuna kanta tare da cewa "ni!ni!!ni kabeer ka mara? marin
ma har biyu?"
Cikin karfin hali tare da danne a bunda ya keji a zuciyarsa yace mata....
"To tsaya kiji ba'ayi halittar da zata zagar min uwa a gabana in kyaleta ba wlh! kika kara gigin
zagarmin uwa na rantse da Allah sai makiyin ki yaga tausayinki" yafada yana shigewarsa cikin
dakin sa.
Tsaye take mamaki,Al'ajabi,rudu tare da tashin hankali suka dirar mata bayan tadawo
hayyacin ta daga marin bazata da kabeer yayi mata ko motsin kirki ta gaza yi ga maganganun da
ya gaya mata!
"Dole nagaya ma inna mu koma gun boka dajjal in ba haka ba to wlh akwai matsala, wanki
hulla na neman kaimu dare.
"ita zaka ba hakuri bani ba,kuma kar na sake jin ka ce mata karya take,kana jina ko?"
"eh Umma"
"Anty khaleela kiyi hakuri kinji bazan sake ba" "kinyi hakurin?
"eh"
"Khaleela zo nan"
"a'a"
"shine ke kuma kika balla masa nasa ko?miyasa baki da hakuri ne Khaleela?Khaleel ba kanin ki
bane,idan baiji sanyi gunki ba gun wa zaiji ? banasan irin wannan abun kina jina ko?
"eh"
"dama nasan kece baki da gaskiya sai shegen bakin kawo kara" tafada tana hararar ta "kar na
kuma ji, fice ki bani guri."
Bayan ta gama ne ta gyara dakinta,palon ma tazo ta gyara,taje dakin Abban Khaleel Shima ta
gyara masa,ta share harabar gidan bayan ta kammala ne ta ma su Khaleela wanka,ta shiryasu cikin
kaya kala guda matsu kyau tace musu "oya kowa yadauko home-work dinsa yayi"
Abaya ta zura tare da d'auko hijab dinta da darduma domin an fara kiran sallah.
koda ta fito har Khaleela tasa hijab dinta sun shinfida dardumarsu irin ta yara, ita ma shinfidawa
tayi suka fara bin masallacin unguwarsu.
Bayan Azeema ta i'da da sallar ne tasa su kayi azkar dinsu,wanda basu iyaba ta cigaba da koya
musu cikin ma Allah yayiwa y'ayan nata basira ga wayo hadi da girman jiki dan ita suka dauko
fannin zafin girma,idan kaga twins dinta zaka dauka sun kai six or saven year hardai Khaleela da
take mace.
Suna nan zaune tana koya musu karatu da azkar akayi kiran i'sha, suka sake bin masallacin.
Da suka idarne ta tashi ta nufi room dinta domin ta gyara jikinta because lokacin dawowar
Abban Khaleel ya kusa.
Lotions ta murzawa fatar ta mai mugun kamshi ta saka riga da siket na atamfa, ta shafawa
fuskarta powder tare da sakawa idanunta kwalli,ta murzawa lips din ta lips glow,ta na cikin daurin
dan kwalin ne ta juyo muryar su Khaleel suna cewa................✍️✍️✍️
*Zeesardauner ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 13~~14
Alokacin da ya shigo cikin gidan wani sanyayyen kamshi ne ya doke hancisa tare da masa sannu
da zuwa.k'ayataccen murmushi ya saki yana kara gode ma Allah da ya mallaka masa Azeema A
matsayin matarsa.
Da sallama ya shiga cikin palon yayin da yaransa suke masa sannu da zuwa,amsa musu yayi
yana shafa kansu.
Wani sihirtaccen kamshi ne ya ziyarci hancinsa yayin da Umman Khaleel ta fito daga kuryar
dakinta zuwa in da yake tana rusunawa tare da cewa...
"Abban Khaleel Sannu da zuwa ya hanya?"
"yawwa Umman khaleel "da murmushi a fuskarsa yake cewa "hanya Alhmdllh, kina tambayar
hanya kamar wani gari naje"
Chan kasa da muryar yadda yaran baza su jiba tace "a wurina wani gari kaje kam har na kosa ka
dawo"
"Abubuwa "
"ko"
"eh mana,amma muje ka fara watsa ruwa sannan"
Murmushi tayi tare da yin fari da i'danunta ta kashe masa daya tana cewa "muje ka fara wankan"
Allah yasani har cikin ranta taji dadin yabon da ya yi mata .
Ruwan wanka takaimasa bayi,ya shiga domin watsa ruwa koda ya fito ta fiddo masa kayansa tare
da fesa musu turare,ita ta taya shi sa kayan kafin suka fito palon domin cin abincin dare.
A cikin plate daya ta zuba musu ita da hubbynta sannan ta zubawa su Khaleel na su a dayan
plate,bisimilla sukayi tare da fara cin abincin.
Ba yan sun idar ne suka danyi fira har yaran sukayi bacci.
Dakinsu takaisu wanda ke kusa da nata,Addu'o'i ta musu tar da lullube su da bargo becouse
lokacin sanyi ne,ta fito tare da rufe musu kofar.
Dakin ta ta nufa, ta dauko duk wani a bunda zata bukata kafin ta wuce dakin Abban Khaleel.
(Ni ko nace Asubah ta gari lovers)
Bayan sun isar da sallar magrib bai fita a masallacin ba sai da ya yi sallar isha'i sannan ya fita.
Room d'insa ya nufa ya sauya dressing zuwa kananan kaya,yasa facing cap dan baya san yawan
kallo.
Gurin motarsa ya nufa ya shiga,mai gadi ya bude masa gates ya cilla kan motarsa waje.
*Shanghai Bakery and* *Restaurant* ya nufa dake cikin garin na sakkwato,bayan yayi
parking ne ya nufi ciki, Already sunsan da zuwansa bai tsaya b'ata lokaci ba ya fito tare da ledar
take-away "tsaki yayi saboda i'danun da yan matan wajen suka zuba masa.
Bayasan yawan kallo a rayuwarsa.
Mortarsa ya shiga tare da cilla ta bisa titi yana tuki slowly.
Allah yasan baya san abincin restaurant,amma ba yadda ya i'ya ne, Suhailat bata jin magana ko
girki bata iya ba kuma ta koya taki,wai ita ba yar wahala bace kuma ba aikatau aka kawota ba. Ya
kori yan aiki dan kawai tayi girki da kanta but nothing change,Alway's yana Restaurant.
Shine a bunda yafi kona masa rai a rayuwa in ya yi magana mommy tace mai yai hakuri
kuruciya ce ke damunta dat's why yasa mata i'do yaga iya gudun ruwanta.
Part dinsa ya wuce,ruwa yad'an wasa kafin yasa sleeping dress ya hau bed d'insa.
Duk inda ake san namiji yakai to haidar yake,Allah ya masa baiwar kyau,kwarjini tare da haiba,
ga karfaffan jiki, dole duk macen da ta gansa ta rufta kansa bcox ya chan-chanci haka.
Abuncin yad'an tsakura yaci sannan ya d'auko system d'insa tare da rufe kafafunsa da blanket
mai taushi, ya jingina kansa a gadon tare da daura system din a kan laps d'insa .
Agogo dake manne a bangon dakin nasa ya kalla,almost 12am amma bata dawo ba.
Bayan an tashi islamiyya ne su Aleeya suka nufo gida da yake ba wani tazara tsakaninsu da
makarantar da kafa zuka iso kuma kodama akwai tazarar to basu damu ba dan sun saba abunka da
talaka da ke bid'ar abunda yaci.
Da guda guda duk abokanan tafiyarsu suka nufi gida ya rage daga Aglaa sai salmat,Amina and
Bilkisu.
Suna isowa garkar gidan su Amina su ka shige suna musu sai da safe,ya rage daga
Aglaa(Aleeya ) sai salmat.
Bakinsu d'auke da salama suka shiga cikin gidan,bappa suka samu kishingide yana
hutawa,"Bappa barka da dare"Aleeya tace tana durkusawa itama salmat yanda ya'yarta tayi hakan
itama tayi .
"muna nan munayi "inji salmat yayin da take nuna mai hadisin da aka musu.
Dakin inna Saude ta shiga tana cewa cikin muryarta mai sanyi "Assalamu Alaikum"
"wa'alakissalamu"inna Saude Ta amsa mata,dukawa tayi tana cewa "inna mundawo" "tou"tace tare
da gyara konciyarta tana cewa"Abincin ku na nan cikin madafi ku d'auko kuci "
"tou inna " Aleeya tace tare da mikewa tsaye.
Dakinsu ta nufa ,ta cire uniform na islamiyya kana ta saka na gida.Wata doguwar riga tasa wadda
bata ji jiki sosai ba tayane kanta da mayafin ta,ta nufo waje .
Abincin su ta d'auka ta nufo inda salmat take tare da bapannata tana cewa...................................✍️
✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
_Nagode da Addu'o'in ku a gareni_ my fans _ _na ji sauki_ _sosai Allah ya bada__ _lada_
*Page* 15~~16
"tou Addana"ta fada tare da mikewa tsaye,bayan ta wako hannun na tane ta zauna kusa da
Aglaa,bisimilla tayi suka faracin tuwon.
Da suka kammala cin Abincin ne suka zauna kusa da bappa suna fira yana basu labarai kala-kala
masu sa nishadi da ban dariya,salmat Sai dariya take ita ma Aglaa Murmushi takeyi.
A duk lokacin da suke firar dare tsakaninsa da yaransa wani lokaci da inna Saude sai yaji a
ransa inama tana raye,inama ace a yanxu hakan suna tare.da zai iya dawo da hannun a gogo baya
da ya gyara kuskurensa da zai sanyata farinciki fiye da misali,
Ajiyar zuciya ya sauke ya dubi su Aglaa Yana cewa "mamana kutashi ku tapi dakinku ku kwanta
da wuri kar da safe ku makara zuwa makaranta"
"tou bappa sai da safe komi munka yima ka yafe mana"suka ce suna mikewa tsaye
"ameen bappa"
Bayan bappa ya kulle gida ya nufi dakin inna Saude,su Aglaa kuwa suka nufi nasu dakin.
*WASHE GARII*
Tun da bappa ya ta dasu sallar subahin bata koma bacci ba tana zaune tana azkar bayan ta idar
da sallah, jin bappa ya dawo daga masallaci ne ta fito tana cewa "bappa ina kwana"
"yawwa, na dauka haryazun batayi sallar ba ne "yace yana shiga cikin dakinsa .
Ayyukan da tasan wajib ne tayi su ta fara,dan bata san ta makara a makarantar bokon.
Gidan ta fara sharewa ta masa tas sannan tayi wanke-wanken k'wanuka, ta daura ruwan damun
kunu.Da suka ta fasa ta dama kunun sannan ta d'aura zazafen tuwo.
Dakin inna Saude ta nufa ta gaya mata ta gama abincin karin kumallon tazo ta raba.
cikin dakin ta shiga da sallamarta, inna Saude ta hango tayi reshe-reshe bisa katifarta tana
shakar baccinta.
A ka'idar inna Saude ba'a tada ita bacci,kuma ko waye yayi gigin tada ita yasin sai yaga cin
mutunci kala-kala,Bappa d'ai ne dai-dai da ita dan tana shakkunsa wani lokacin amma wani lokaci
inta tashi rashin arzikinta harda shi take mawa.
fita tayi a dakin ta nufi madafi, raba abun karin kumallon tayi ta sama Bappa nashi a k'wanikan
shi,inna Saude Ma haka,ta dibi nasu sannan ta fito daga cikin kicin d'in.ta kai ma Bappa nashi a
dakinsa.
Wanka taje tayi sannan ta tada salmat domin tayi wankan"Allah Addana kwanan nan bai ishe ni ba
wlh kika tadanii"tafada cikin muryar bacci da shagwaba
"murmushi Agla tayi tana cewa "ok sorry y'ar k'anwata tashi ki shirya sai muci abincin mu wuce
makaranta kar mu makara kinjii"
Wankan itama tayi sannan tazo ta shirya cikin uniform d'in su na *G.G.S.S mabera*
( *GOVERMENT* *GIRLS SECONDRY SCHOOL* )da ke cikin unguwarsu.Bayan ta shirya a
tsakar gidan ta samu Aglaa zaune bisa ta barma,zaune tayi suka fara karya wan atare,ba wani
abincin kirki Agla taci ba ta mike tare da wanko hannunta,kunun ta dan shan bada yawa ba amma
yafi zazafen da taci yawa,salmat kam hani'an tayi sannan ta mike tare da wanko hannun ta tana
cewa
"Alhamdulillahi Rabbil Alameen,yanxu kam naji garau Adda,zamu iya tapiya na ba mallam
hakkinsa"
"a'a bansanshi ba,wai ba inna tace kibar kula samarii ba y'ar yarinya dake dudu fah bakinki 14yers
"tapada cikin fada-fada amma in mutum baisanta ba bazaice fadana take hakan ba
kumshe dariyar da kesan kufce mata salmat tayi tana cewa"eh tace ,kuma Allah Adda shike
damuna wai ai nabashi hakinsa idan ba haka ba yai ta damuna,kuma kinga in anka ganeni ai baza
ace min yar shekara sha hudu ba ko ?"
kasa ke Aleeya tayi tana kallan salmat chan tace "hakki kuma mine ne hakkin nasa?"
Ganin yadda Addan nata kebin ta da wani kallo yasa ta kwashewa da dariya tana cewa "yanxu
Adda Aleeya Baki fahimce wane mallam nake nufi ba"
kallo kawai Aleeya Ta bita dashi hakan yasa salmat kara kwashewa da wata dariyar tana cewa
"yasinn ni ba wani malami da nake nufi face *CIKINA*naci abunci na basa hakinsa shine nake
nufi tafada cikin dariyar da take.
"Murmushine ya kwacewa Aleeya tare da sauke aziyar zuciya tana cewa "lalai salamatu kin girma
yanxu nizaki mayar abokiyar wasarki ko? yamiki kyau "
"sorry!sarry!!my Anty daya tamkar da dubu karkiyi fushi da yar k'anwarki mana,kiyi hakuri nasa
kinyi mutuwar tsaye"ta fada har yanxun dai dariyar take tana kwatanta yadda Aleeya Tayi.
Itama Aleeyar Saida ta dara tana cewa "zanka maki ne Salmat Harda koyon yadda nayi ko"
"Alqur'an yadda kinka yine yaban dariya sosai wlh"
"ok yayi kyau ki ci gaba da dariyar sai mun makara"tafada tana nufar dakin Bappa.
Da gudu Salmat tabi bayan ta suka shiga dakin a tare "Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikusallam" Bappa dake kishingide bisa katifarsa yana jan tasbaha ya fada
"tou Allah yatsare ya kiyayemin ku,ya maido ku lafiya"yafada yana miko musu naira dari "ungo
wannan kwasai wani abu in lokaci cin abinci yayi."
Da ameen ameen suka amsa Aglaa(Aleeya)na cewa "Bappa mun gode Allah kara budi"
"Ameen"
Salmat Ta bude baki zatayi magana ta hangi inna Saude zata wuce sai ta d'an daga muryarta tana
cewa "Bappana mungode Allah karo arziki mai albarka ko innata na daina ma wulakanci tunda
taga baka da kuddi,Allah bappa ifan kayi kuddi ka kara aure"tafada tana kumshe dariyar ta.
Murmushi Bappa Da Aglaa sukayi domin daga jin wannan maganar sun san da inna Saude ne
takeyi,aiko sakon da ta isar ya isa dan inna Saude masifa ta dinga zubawa domin dai Salmat ta
tsokanota.
Bappa kuwa yayi kunne uwar shegu da ita domin yasan komi iskancin da takeyi mai bata
kaunar ace ya karo aure,tana tsananin sonai shima haka yana santa amma halayyarta ne na son
kudi ke rage santa a zuciya tai.Sanadin san da ya kema ta ne ya yasa ya tabka babban kuskure
arayuwarsa da duk lokacin da ya tina yana jin ba dad'i.
Da suka ma mata sallama za su wuce masifa ta dinga yi musu hardai Salmat,tana cewa wai anya
auta ba musanya min ke a asibiti akayi ba ?
"Haba inna yanzu dan nace Bappa ya kara aure zakice an musanya miki ni "tafada tana kwabe
fuska
"dakuwa inna saude ta mata tacewa "kinci gidan ku nace wato kara maimaitawa ma kike,to wuce
ki bani guri tun ban ji miki ba yar nema da bata kishina"
Hannun Salmat Aleeya taja dan wallahi suna iya kaiwa takwas ita da inna Saude sunayi kuma ba
bari zata yiba tace "inna Allah ya huce zuciyarki, mun wuce makaranta"
buta inna ta dauka tare da kyaro mata ita da gudu ta fita wajen gidan tana dariya,Aleeya ta bita
abaya tana daura nikab dinta ,Bappa ya bisu da fatan Alkhairi.
Gidansu Amina Suka nufa ,abakin kofar gidan suka taras dasu suka wuce makaranta salmat na
basu labarin yadda sukayi da Aleeya da inna.✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 17~~18
Dariya Amina Da Bilkisu keyi don sallon yadda Salmat Ke basu labarin ma abin dariya ne sannan
kuma suna jinjina masifar inna Saude Ga shi Allah ya bata d'iya mai tsokana.
Da sunka idar da sallah ne ya tsaya ya gaisa da masu aikin gidan kamar yadda ya saba sannan
ya nufi cikin gidan.Shirin zuwa hospital ya fara yi becouse ya na da patient din da zai duba sannan
akwai abubuwan da yake sonyi a chan kafin ya tafi company.
Bayan ya kammala shirinsa ya sauko kasa part din Suhailat ya nufa amma har yanxu bata
dawo ba,cikin ransa yake cewa "it means ko ina taje a chan ta kwana" tabe baki yayi tare da daga
shoulder dinsa alamun i don't care ya fice daga part din baki daya.
Kichen ya shiga ya hada tea ya dawo palon ya zauna yana sha tare da amsa calling da ya shigo
wayarsa,ya jima yana waya kafin yatashi ya fita.
Motarsa ya shiga yadan na order,da gudu Ila Mai gadi yazo ya bude masa gate din yana cewa
"Alhaji Allah yatsare ya kai ka lafiya"
"Ameen"yace yana fita daga gidan.
U.D.U.TH ya nufa,da isar sa direct offices d'in sa ya nufa yana amsa gaisuwar da nurses and
doctors ke masa.
Bai jima da zama ba yana duba wasu files na maras lafiya akayi noking "yes,come in"yace
yana cigabah da abunda yake .
Turo kofar Dr.Abdallah yayi yana cewa "Dr.haidar harka isone?" "eh wlh,nama jima amman ba
sosai ba, dama koda mukayi waya dakai zan fito ne daga gida" "ok" Dr.Abdallah yace yana mika
masa hannu sukayi musabaha,ya zauna bisa kujerar dake cikin office din yana cewa "saura
30mint mushiga theater " tsadadden agogon dake hannunsa ya duba yana cewa "ashe ma lokaci
yayi kusa sosai","eh wlh yanzu kasan lokaci ba yada wuyar tafiya","hakanne kuma"nan suka
cigaba da tattaunawa kafin lokacin ya cika.
Suna cikin tattaunawar ne akayi noking,"yes"wata nurse ce ta shigo,d'an rusunawa ta gaidasu
kafin tace "sir dama lokacin theater yayi ne shine Dr.Aysha tace nazo na fada muku"
"okey, we are coming" Dr.Abdallah yace da ita , juyawa tayi ta fita.
shirin shiga theater room sukayi sannan suka fita.
A bangaren Kabir Kuwa,da bakin cikin abunda maryama ta masa ya kwana shiyasa daya tashi da
safe bai nemeta ba kamar yadda ya sabayi ko wanne lokaci,shirinsa ya hauyi ya fita.
Gidansu ya fara biyawa domin ya gaida iyayen nasa,a kofar gida ya hadu da Allhj sa'id
mahaifinsa suka gaisa sannan ya shiga cikin gidan, sashen umma ya wuce,koda ya shiga cikin
palon nata ba kowa a ciki ,kuryar dakinta ya wuce domin yasan da wuya ta wuce chan,zaune ya
tadda ita bisa darduma tana lazimi ta gama sallar walha;durkusawa yayi yana cewa "Umma ina
kwana antashiya lfy"
"lfy lau Muhammad Ya iyalin naka"
cikin boye abunda ke damunsa sanadin maganar maryama da tayi yace "tana lfy "
"mashaallah haka ake so.Allah yakara tsareka"
"Ameen Umma"
"Kana cigaba da addu'a ko?"
"eh,sosaima","yayi kyau ka kara dagewa ba'ason mutum ya kasance mai sakaci da ibada da kuma
addu'a,koda mutum baya cikin damuwa,bakinciki,tashin hankali tou ana son yakasan ce mai
yawan ibada da neman kariyar Allah;basai ana cikin wad'annan abubuwa sannan zakace kayi
addu'a ba,a'a ita addu'a makamin muminice.Duk wanda ke jifar ka da sharri ko sihiri muddun ka
tsare addu'a sannan ka tsalkake zuciyarka ya kasance ba ka bibiyarsa da sharri tou ba'abun da zai
sameka sai abunda Allah ya kaddara."
"Ohh na tina"ummm..
"da wani abun ne?"
"cewa nayi za'a dan samu wani abu",
Murmushi tayi irin nasu na manya tana cewa...........................✍️✍️✍️
*Zeesardauner ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 19~~20
Murmushi tayi irin nasu na manya tana cewa "ka duba dining baza'a rasa ba"
"godiya nake umma Allah kara nisan kwana,"dining d'in ya nufa,soyayyen arish da kwai ya zuba
cikin plate ya na ci sannan ya hada tea mai kauri ya kora dashi,sai anjima ya yima Umma ta amsa
tare da masa Addu'a ya fita daga dakin nata ya nufi chemist dinsa da yake tsayar da magunguna.
Inna Dije da ke labe cikin dakinnata tun shigowar kabeer, ta kasa ta tsare sai da ta ga yafita daga
gidan sannan ta lalibo wayarta ta dannawa Maryama Kira.
Abangaren Maryama Kuwa, itama ba wani isashen baccin kirki ta samu ba sakamakon kiran
innarta da tayi domin ta sanar da ita abunda ke faruwa amma bata samu ba,hankalinta ya tashi
sosai da yadda kabeer din yayi mata,hakan ke nuna cewa abun da sukayi a kansa yana neman ya
warware musu.
Karar wayar tane ya tashe ta daga baccin hasarar da takeyi, domin ko salla bata samu yi ba
gashi har wuraren 9:00 (A'uzubillah) dagawa tayi tare da kara wayar a kunnenta duk atunanin ta
Babar tace;murya inna dije da ta jine yaganar da ita ba innarta bace,zuwan da kabeer yayi gidan da
tsawon lokacin da ya d'auka a dakin Umman sa ta sanar mata tare da kara tinzirata hadi da zugata
kan ta tashi tsaye, in ba hakanan ba akwai matsala, domin alamu sun nuna aikin dake kansa ya fara
warwarewa in ba haka ba "saidai kiji ana guda,kuma in baki yi saurin daukar mata ki ba sirrin
boye zai fito fili"
"ok naji da yardar Allah ma hakan bazai faru ba"sannan ta kashe kiran.
Abu goma da ashirin, kan Maryama ya kara d'aukar zafi sosai fiye da da,domin inna Dije ta
kara hautsina tinaninta sosai,tabbas ta san cewa muddin aikin farko da akayi a kan kabeer ya karye
to tabbas a ranar aurenta ya kare.Ita kuma bata shiryama hakan ba.
Sake gwada kiran innarta tayi amma number bata shiga,jifa tayi da wyar kan gadon ta dake
harmutse,bama shiba har dakin a hargitse yake tana cewa "Dam it"mike damun wayar inna ne
wai,Ni maryama ya zanyi yanzun
tafada tana dafe kanta...!
Bayan sun tashi ne daga barci ta tada yaran sukayi sallar subhi ita kuma tashiga cikin kitchen
lokaci na tafiya sosai gashi yaran sun kusa makara zuwa makaranta.
Breakfast ta d'aura bayan ta kammala ne tazo ta musu wanka ta shiryasu cikin tufafinsu na
makarantar boko,palon ta fito rike da hannuwansu tace"kuzauna bari na kira Abbanku"
"tou Umma"suka ce then suka zauna bisa carfet din.Dakin Abban khaleel ta nufa,sallama tayi ya
amsa ta shiga ciki.
Sakin baki tayi tana kallansa,ya kamla shirinsa cikin yadi bowl milk colour yasaka hullarsa,sak
ya fito hausa fulani,ba karamin kyau ya mata ba kamar tace yau kar yaje kasuwa, bata fuskarta
tayi tana cewa "shine ka kwashe ladar ka ko dan kar ka jirani nazo na shiryama"
"no ba hakan bane Ummu Khaleel ai lada ko da yaushe cikin ta kike,naga aikin yamiki yawa ne ga
breakfast ga shirya yara, ga nawa shirrin ma shine fa na rage miki tunda yau mun makara bamu
tashi da wuri ba"
"ka taba ganin inda lada tama mutum yawa Abban Khaleel"
"a'a Umman Khaleel,domin da tanayi y'ar kyawwar matata zata farama bcox yar aljanna ce da
yardar Allah "
Fadawa tayi bisa faffadan kijinsa tana murmushi take cewa Allah ka barmu tare har a aljanna
firdausi mijina"
"Ameen matata"jan hannunta yayi suka fito palon inda yaran suke.
Gaida Abbannasu sukayi ya amsa yana tambayar sun tashi lafiya"lfy lau Abba"
"mashaallah"ya fada yana zaunawa kusa da Umman Khaleel.
Sarving d'in kowa tayi sannan suka fara karyawa,abin karin take ci amma hankalinta na kanshi
sai kallon shi take yi,kusa da kunnenta ya matso yana cewa "yadai an mata"yafada tare da dage
mata gira,murmushin da bata shirya yi ba ya subuce mata,yadda ya dage giran yasata sakin
murmushi itama cikin rad'a take cemasa"uwar y'an mata dai tana kashe masa ido daya"murmushi
shima yayi yace"eh hakane kuma,to ya akayi naga sai kallona kike kona chanza miki ne?"
"sosaima kuwa jina ke kamar ace yau kar ka tafi kasuwa katsaya nayi ta kallanka har sai nagaji
banason ka fita wasu su ganka"
"hhh kice kishin ya motsa"
"dolene ai in dai akan ka ne"
murmushi yayi ya cigaba breakfast dinsa domin yasan muddin ya biye mata tabbas zata hanasa
zuwa kasuwa yau.
Bayan sun kare karyawar ne ya mike yana cema su Khaleel............................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 19~~20
Murmushi tayi irin nasu na manya tana cewa "ka duba dining baza'a rasa ba"
"godiya nake umma Allah kara nisan kwana,"dining d'in ya nufa,soyayyen arish da kwai ya zuba
cikin plate ya na ci sannan ya hada tea mai kauri ya kora dashi,sai anjima ya yima Umma ta amsa
tare da masa Addu'a ya fita daga dakin nata ya nufi chemist dinsa da yake tsayar da magunguna.
Inna Dije da ke labe cikin dakinnata tun shigowar kabeer, ta kasa ta tsare sai da ta ga yafita daga
gidan sannan ta lalibo wayarta ta dannawa Maryama Kira.
Abangaren Maryama Kuwa, itama ba wani isashen baccin kirki ta samu ba sakamakon kiran
innarta da tayi domin ta sanar da ita abunda ke faruwa amma bata samu ba,hankalinta ya tashi
sosai da yadda kabeer din yayi mata,hakan ke nuna cewa abun da sukayi a kansa yana neman ya
warware musu.
Karar wayar tane ya tashe ta daga baccin hasarar da takeyi, domin ko salla bata samu yi ba
gashi har wuraren 9:00 (A'uzubillah) dagawa tayi tare da kara wayar a kunnenta duk atunanin ta
Babar tace;murya inna dije da ta jine yaganar da ita ba innarta bace,zuwan da kabeer yayi gidan da
tsawon lokacin da ya d'auka a dakin Umman sa ta sanar mata tare da kara tinzirata hadi da zugata
kan ta tashi tsaye, in ba hakanan ba akwai matsala, domin alamu sun nuna aikin dake kansa ya fara
warwarewa in ba haka ba "saidai kiji ana guda,kuma in baki yi saurin daukar mata ki ba sirrin
boye zai fito fili"
"ok naji da yardar Allah ma hakan bazai faru ba"sannan ta kashe kiran.
Abu goma da ashirin, kan Maryama ya kara d'aukar zafi sosai fiye da da,domin inna Dije ta
kara hautsina tinaninta sosai,tabbas ta san cewa muddin aikin farko da akayi a kan kabeer ya karye
to tabbas a ranar aurenta ya kare.Ita kuma bata shiryama hakan ba.
Sake gwada kiran innarta tayi amma number bata shiga,jifa tayi da wyar kan gadon ta dake
harmutse,bama shiba har dakin a hargitse yake tana cewa "Dam it"mike damun wayar inna ne
wai,Ni maryama ya zanyi yanzun
tafada tana dafe kanta...!
Bayan sun tashi ne daga barci ta tada yaran sukayi sallar subhi ita kuma tashiga cikin kitchen
lokaci na tafiya sosai gashi yaran sun kusa makara zuwa makaranta.
Breakfast ta d'aura bayan ta kammala ne tazo ta musu wanka ta shiryasu cikin tufafinsu na
makarantar boko,palon ta fito rike da hannuwansu tace"kuzauna bari na kira Abbanku"
"tou Umma"suka ce then suka zauna bisa carfet din.Dakin Abban khaleel ta nufa,sallama tayi ya
amsa ta shiga ciki.
Sakin baki tayi tana kallansa,ya kamla shirinsa cikin yadi bowl milk colour yasaka hullarsa,sak
ya fito hausa fulani,ba karamin kyau ya mata ba kamar tace yau kar yaje kasuwa, bata fuskarta
tayi tana cewa "shine ka kwashe ladar ka ko dan kar ka jirani nazo na shiryama"
"no ba hakan bane Ummu Khaleel ai lada ko da yaushe cikin ta kike,naga aikin yamiki yawa ne ga
breakfast ga shirya yara, ga nawa shirrin ma shine fa na rage miki tunda yau mun makara bamu
tashi da wuri ba"
"ka taba ganin inda lada tama mutum yawa Abban Khaleel"
"a'a Umman Khaleel,domin da tanayi y'ar kyawwar matata zata farama bcox yar aljanna ce da
yardar Allah "
Fadawa tayi bisa faffadan kijinsa tana murmushi take cewa Allah ka barmu tare har a aljanna
firdausi mijina"
"Ameen matata"jan hannunta yayi suka fito palon inda yaran suke.
Gaida Abbannasu sukayi ya amsa yana tambayar sun tashi lafiya"lfy lau Abba"
"mashaallah"ya fada yana zaunawa kusa da Umman Khaleel.
Sarving d'in kowa tayi sannan suka fara karyawa,abin karin take ci amma hankalinta na kanshi
sai kallon shi take yi,kusa da kunnenta ya matso yana cewa "yadai an mata"yafada tare da dage
mata gira,murmushin da bata shirya yi ba ya subuce mata,yadda ya dage giran yasata sakin
murmushi itama cikin rad'a take cemasa"uwar y'an mata dai tana kashe masa ido daya"murmushi
shima yayi yace"eh hakane kuma,to ya akayi naga sai kallona kike kona chanza miki ne?"
"sosaima kuwa jina ke kamar ace yau kar ka tafi kasuwa katsaya nayi ta kallanka har sai nagaji
banason ka fita wasu su ganka"
"hhh kice kishin ya motsa"
"dolene ai in dai akan ka ne"
murmushi yayi ya cigaba breakfast dinsa domin yasan muddin ya biye mata tabbas zata hanasa
zuwa kasuwa yau.
Bayan sun kare karyawar ne ya mike yana cema su Khaleel............................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*comment and vote dinku shike karamin karfin guiwar typing* 💋
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 21~~22
Yana cema su Khaleel"kutashi mutafi kun kusa makara"mikewa sukayi suna "Umma muntafi sai
mundawa"
"Allah ya tsare ya kiyayemin ku,kuyi karatu sosai banda mugun wasa da jan fada"
"tou Umma"rakiya ta musu sai da suka hau,machine din yadaka daga gidan sannan ta dawo cikin
palon nata.
Breakfast dinta ta'ida saboda d'azu bata ci abun kirki ba sannan ta fara kimtsa gidan.
Cikin amincin ubangiji sunyi theater lami lafiya ba tare da wan problem ya afku ba,yanxu
haka patient din tana bacci .
Office d'insa ya nufa domin ya gaji sosai,ruwa ya d'auka yasha tare da zama bisa kujerar sa ya
hutawa.
Bayan hour guda ya kammala diba files na maras lafiya da zai dubaa sannan ya fito,bisa hanya
suka hadu da Dr.Abdullahi zamau "wurinka ma zanje ashe har ka fito"
"eh inason ne na biya company "
"ok dama batun file din matar nane"
"wace matar?"
"wadda keda matsalar heart,Allah yasa dai ka duba bayananta"
"oh..!na manta ne,eh na duba bayananta now thursday sai monday za'a mata aikin"
"ok,Allah kaimu"
"Ameen"yace yana nufar motarsa
"Dr.Haidar"bai jiyo bcox ya shaida wacece ,sake kiransa tayi ganin bai amsa ba amma ya mata
shiru shi bai amsa ba kuma bai shiga motar ba.
kusa dashi ta zo ta tsaya cikin karya murya tace "Dr.Haidar Na kiraka ka kyaleni nama wani
laifine ?tafada cikin alamun tausayi.
"Kunne keji ai,if u don't have something to say please leave here,i have something important to do
"ya fada ba tare da ya jiyo ya kalleta ba,iya shaka tou Dr.Aysha Ta shaka,wulakanci da Dr.Haidar
Kemata ya yi yawa amma duk da hakan bata jin zata hakura dashi,cikin dakewa da nuna abunda
yace mata bai mata zafi ba tace "no dama cewa nayi idan ban ta kura maka ba ina son kad'an
ragemin hanya "
"i can't akwai abubuwan da nake son yi alot d'an haka banida time d'in westing,kina iyama
Dr.Abdallah Magana sai yayi dropping dinki" ya fada yana shiga motar sa ya bata wuta.
Wasu hawayen bakin ciki ne suka cika mata i'do,muryar Dr.Abdallah taji yana cewa muje nayi
dropping d'inki "no barshi kawai Thanks ta fada tare da nufar motar ta.
Dage kafada Dr.Abdallah yayi irin damuwarki cikin ransa kuwa cewa yake "rashin aiki ne
yamiki yawa Aysha da kike tsayawa westing time d'inki akan haidar, mutum yanuna baida intress
kanki amma kinki ki fahimta,
always bakya tsakanin abuja,kano,sokoto duk inda yayi sai kin bishi, taya zai so ki haka abu ba
class,bansan mike damun y'an matan mu na arewa ba wlh,mata kunya aka sansu da ita amma
yanzu everything sai kaji ance zamanine"wani tsaki yaja tare da komawa cikin asibitin, dama
rakiya ne yayiwa Dr.Haidar.
Cikin motarta ta fada tare da bata wutaa,zuciyarta gaba daya a chinkushe take,data isa bakin wani
tampatsetsen gate ta rika zuba order kamar hauka da sauri maigadi yazo ya bude mata domin daga
jin wannan order kamar za'a tadda gidan yasan cewa hajiya karama ce it daice a gidan ke irin
wannan motar parking tayi cikin makeken parking space dake cikin gidan,direct room dinta ta
nufa wanda ya kawatu sosai da sosai fiye da tinanin mai tinani.
Bisa Royel bed dinta ta fada ta sake wani marayan kuka maiban tausayi,miye aibunta da Aliyu
baya santa ne,mikewa tayi ta nufi glass ta tsaya taa karema kanta kallo bata wata makusa ,to
miyasa shi bata burgeshi,miyasa baya santa ne ,tana da masoya da yawa a ko ina,duk abunda
Haidarke mata sansa ko kadan bai ragu a zuciyarta ba sai ma haw hawa da yake yi,a ko da yaushe
a ko wace sa'a.
Ta wulakanta samari da yawa kala-kala masu kudi da diyan talakawa wadanda ke daukowa
kansu abin da yafi karfinsu in bahaka ba miye hadin ta da wani talaka mstwwsss dan ya renata
yace yana santa,ta wahalar da samari masu yawa amma ace wai ita Aysha Mas'ud mai nera
soyayya ke wahalar suwa ,akace idan da ranka ka sha kallo amma ai Haidar yakai matsayin da
kowace mace ta gansa zata iya afkuwa da sonsa .Mahaifinsa na cikin mayan masu kudin kasar nan
ko ina ana damawa dashii sannan shima kansa yana cikin matasa masu kudi wad'anda suka jika da
naira ga uwa uba kyau da Allah ya bashi, tabbass Haidar kyakyawane sosai shiya take bala'in
sansa kuma inshaallah sai ta mallakeshi a matsayin mijin .
Har yanzu tana cikin damuwa gashi wayan ummanta yaki shiga,agoon dakin ta kalla karfe daya
ta buga amma bata samu damar koda share gidan nata ba bare tayi batun aza girki,wani murmushi
ne ya subuce mata,alokacin da taga...........................................✍️✍️✍️
*Zeesardauner ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa _
Muna taya ku murnar cika shekara ɗaya da kafuwa *(AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION)*
Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ina miƙo gaisauwa tare da jinjina agareku marubuta *Al'umma*.
🥳🥳🥳🥳
Allah ya ƙara muku basira ɗaukaka tare da dunbin mabiya marubutan Al'umma, haƙiƙa wani
kayan sai amale, muna matuƙar alfahari daku, Allah ya kare daga dukkan sharri, Allah ya ci gaba
da dafa muku cikin al'amuranku, Allah ya ɗaukaka ku, Allah yasa ku kasancen cikin jerin da
al'umma zasuyi alfarhari da ku, bisa faɗakar dasu da kuke yi, Allah ya biyaku afsa faɗakarwa da
kuke yiwa al'umma, Allah ya tsare gabanku da bayanku ya shiga cikin lamauranku duk duniya
tasan daku.
Haƙiƙa mu ƙungiyar *Jarumai writer's association* mana matuƙar tayaku murna tare da tarin
jinjina a gareku bisa ga namijin ƙoƙarin ku, Allah ya ƙara basira haɗe da hasken makaranta.
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 23~~24
Murmushi ne ya subuce mata a lokacin da taga number innarta ta shiga,ringing ukku ta d'auka,
handsfree Maryama Ta sa sannan takara a kunnenta dadai lokacin innarta ke cewa" ya akayi ne
shalele dafatan kina lpy,"
"mssstwwwssssss"cikin kwabe fuska ta cigaba da cewa "ina ko lfy inna,tin jiya fa nake ta kiranki
amma wayar ki ta ki shiga"
"miya faru ne shalele"
"akwai matsala fa inna dan ina tinanin aikin da mukayi kan kabeer ya warware"Cikin kidima da
tashin hankali inna tace"whattt...!
kamarya ya warware?duk aikin da nasa akayi kansa!
Cikin yanayi na mutummen dake son yin kuka take cewa "Allah inna ya warware,kinga harda
dukana yayi"
"duka kuma,yi hakuri kinji zai dawo hannu ne,duk sai kin rama abunda ya miki"
"tou inna,amma yau ne zamuje wurin dujjal ko?
dan gaskiya bana san na rasa kabeer"
"ki kwantar da hankalinki shalele ,indai ni hjy hawwa ina da rai da numfashi bazaki rasa kabeer ba
har abada ko da kuwa zanyi yawo tsirara ne"
"yawwa mamata ta kaina shiyasa nake matukar sanki wallahi"
"nima ina matukar sanki 'ya ta"
"umm.. yau waccan matar saida ta kirani"
"wace matar?"
"dije mana ta gidansu kabeer"
"oh na tina ta,mi tace miki hala?"
"wai cewa tayi na tashi tsaye in ba haka wai sai dai naji ana gudaa"ta karishe maganar cikin
takaici .
"To mi take nufi"
"ina na sani nasan bai wuce wadancan shashashun uwayen nasa susa ya kara aure,tunda ba so na
suke ba"
"bai isa ya yimiki kishiya na kyaleshi ba wlh,na shiga na fita na hana ama 'ya'yan wasu kishiya
bale tawa 'yar "
"shiyasa fa mama bandamu ba,saboda nasan ina da ke,abunda yafi tad'an hankali shine kar aikin
da akayi masa na farko ya warware,kinga ma yanxun yana yawan zuwa inda mahaifansa"
"ki kwantar da hankalinki shalele bana san kinasa damuwa a ranki,yanxu yaxunan bada jimawa ba
zan dau hanyar niger "
"yawwa ummata,kinsan ance da zafi-zafi ake dukan karfe"
"hakan kuwa,sai kinjini"
"ok bye" ta katse wayar.
Wani sanyayyen murmushi Maryama ta saki,gani take matsalarta ta kau yanxun,sanadiyar
sanar da mahaifiyarta da tayi.
Abangaren hajiya hawwa wato mahaifiyar maryama kuwa suna gama waya da maryama ta mike
bedroom d'inta ta nufa,mayafinta ta d'auka ta fito,da Nafeesat karamar yarta suka hadu tace "inna
ina za kije yanxu"
"inda kika aikan"
"a'a ni ban aikeki ko ina ba,kawai naga baki dade da dawowa ba,Allah yakai lapiya"
"Ameen"tace tana nufar parking lot.
"Allah ya shiryaku keda sis gimbiya inkuna da rabon shiriya" tayi shigewarta dakin su.
Karfe biyu dai dai aka tada su daga makaranta suka dawo gida.Bayan sun gaida inna saude ne
suka wuce domin yin sallar azahar,alwala sukayi tare da yin sallah bayan sun idar sukaci abinci
sannan salmat ta wuce gidan Fa'ixa kawarta(Idan mai karatu bai manta ba inna saude da inna laure
abokanan juna ne) Gidansu na da tv,chan take zuwa tana kallon wani shiri da ake cewa wai
*DADIN KOWA* salmat na isa gidan suka hadu da inna laure zata fito waje,durkusawa salmat
tana cewa "inna barka da yini"
"barka dai Salamatu kina lpy"
"lpy lau inna"
yanzu kuwa gidanku zanje,dafatan innarki na nan?"
"eh tana nan inna"tafada tana shigewa dakin inna laure,duk haushi ya cika ta na saida ita da inna
tayi.
Dakin ta shiga da sallama,da sauri Fa'ixa Ta taso inda take tana cewa "k'awalliya ya ankayi
kika jima gashi har an fara shirin"
"kedai bari k'awas wlh tun dazu nazo innarki ta tsai dani a waje"
"ok,naganta zata fita tace gidanku zataje"
"eh wai hakan naji"suka maida hankalinsu kan shirin da ake.
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 24~~25
Ga wata shawarar"mi zai hana ki barta ta ringa tara samari kamar yadda hindatu keyi...!
"wa ni rufan asiri irin wannan abun da hindatu keyi abu sai kace a kuya...
"y'ar tawace a kuyar ?
"nidai bance ba kama kawai nace,kuma walla koda mallam bai hana ba ni bazan barta tayi ba
wallahi,ko da ba yata ce ta cikina ba ai hannuna ta tashi,so kike hala innna fita a dunga nuni ana
cewa ga babar wance chan,ina ni gaskiya wannan shawarar bata yiba,ni da keson in na fita a dinga
nuna ni ana cewa ga hajiya saude nan amma kina wannan batu,balle ma yarinyar da ko gyale bata
fita dashi har zakice in bari ta tara samarii...chanza wata dai.
"hmmm ni Saude wace shawarar kuma zan baki..yanxu gabana kika zagi y'ata wai kamar
akuya ko kunyata ba kiji ba sannan kike batun wata shawara"
"ke laure matsalata da ke abu bai wucewa gareki wlh,kinsan halina sarai bakina bai haila bale jinin
biki,sanin kanki ne in abu baimin ba fad'a nake kar na cuci kaina,da nayi gulmarka bayan ka gara
nayi gaban ka ehhe,ai ba karya na yi ba duk unguwar nan maganar hindatu ake yi,in yau mai kalar
waccan mota yazo gobe wani zai zo shine abinda ake ta fada a unguwarnan kunki yi mata aure sai
dai bata nan bata chan"
"duniya munafukai sunyi yawa wlh,in banda munafurci me yasa baza azo a taras dani a fada
gabana ba sai dai a bayana"
"nima dai shi nagani shiyasa banason wannan abun dan kinsanni sarai bana daukar reni wlh domin
duk y'ar iskar da tace ta zagan ni da itane ba kyalewa zanyi ba.
"tou ai shikenan tunda wad'annan shawarwarin basu miki ba sai nemo wata shawarar da kanki dan
ke ba'a iya miki"
"hhhhh baki fadi karya ba laure,amma ai nasan zaki sake bincikomin wata,Laure tawa ni da ke
muta karaba"
Dariya inna Laure tasa tana cewa "wlh Saude baki da dama,kinsan yadda zaki tunzura mutum
lokaci guda kuma ki sashi ya sawko"dariya itama inna Saude ta saka suka ci gaba da firar su.
kiran sallar la'asar ya tada ni daga baccin da ya d'aukeni,dama ni bana da nauyin bacci kamar
salmat sometimes da an kirani nake farkawa,ko da nafito daga d'aki haryanzu inna laure na nan
bata tafi ba.Alwala na d'auro domin nayi sallah,bayan na idar ne nayi azkar dina sannan na fito
domin na d'aura tukunyar abinci,anan waje na riske su inna Saude Suna alwala,kara gaidasu nayi
sannan na tambayi inna miza'a dafa yau"tuwo da miyar d'anyar kubewa"da "tou"na amsa na nufi
madafi.
Wuta na hasa sannanna fara d'aura tuwon shinkafar kamin salmat ta dawo ta siyomin saura
kayan miyar.
Ina wankin shinkafa Salmat Ta shigo gidan,labari ta fara bani na wasan kwaikwayon da suka
kalla a gidan inna dije wani abun in tafada sai nayi murmushi muna cikin haka inna ta fito zata na
bayi taga Salmat"ke y'ar albarka da samu yau she kika dawo gidan?"
"la tund'azu na dawo ai,nadai tsaya ba Adda labarin abunda na kalla"
"tou, na d'auka yanzun kika shigo ai"
"a'a"
"zo ki amnashi kud'i ki sayo mata kayan miya"
"tou inna"tafada tare da bin bayan inna Saude da tayi hanyar d'akinta.
Kudin ta karbo na lisafa mata a bunda zata siyomin,duk da kudin ba wani yawa ne da su ba
amma zasu isa girkin mai karamin karfi ba tare da ya takurawa kansa ba,fita tayi domin siyo
abunda na lisafa mata ni kuma naci gaba da kimtsa gidan,tas na share tsakar gidan sai kyalli yake
na d'an kimtsa dakin mu duk da ba wani hargitsewa yayi ba na d'auko yar kwalbar turarena na
fisawa gidan .Aduniya ina mahaukacin son kamshi fiye da tinanin mai tinani,Allah ya shiryamin
son kamshi a rayuwata amma duk da haka bana sa turare in zan fita domin hakan bai dace ba ko a
addinance,ko minti biyu banyi da zaunawa ba bayan nagama shara sai ga Salmat Ta shigo "yanzu
nake zancen ki a zuciyana ina cewa wai ina kika tsaya haka"
"Allah Adda kinsan wajen layi ke gareshi saida na jira"
"ok,kin siyo kayan magin?"
"i'm sorry my Adda wlh mantawa nayi gaba daya bari nayi sauri yanzun nan na karbo miki"
"ok plss kar ki jima kinji"
"inshaallah Adda"
Abangaren Abban Khaleel kuwa ya na ajiye su Khaleel a school d'in su mai suna ( *JAMA'A*
*NUSERY AND PRIMARY SCHOOL* )dake nan mabeera bayan ya tabbatar da sun shige class
d'insu ya wuce direct gidan su ya nufa domin jiya bai samu damar zuwa ya gaidasu ba.
Cikin gidan ya shiga da sallama mama dake nan waje ita da Aisha suka amsa durkusawa yayi
yana "cewa mama ina kwana antashi lafiya"
"lfy lau Abubakar ya kabaro iyalin naka dafatan kowa lafiya"
"lfy lau suke mama,Azeema tace tana gaida ke"
"ina amsawa,ina kishiyata hala sunmin yaji sun bar zuwa"
Murmushi yayi yana cewa"duk suma qalau suke mama,inshaallah zasu zo muku weekend a
satinnan"
"tou Allah kaimu"
"ameen mama"
Juyowa yayi inda Aisha dake cewa "yaya barka da safiya"
"barka dai Aisha,ai na d'auka yau baza'a gaidani ba "
"a'a babban yaya,nama isa..!baka dai ji bane amma tin d'azu na gai da kai"
"ok na yarda,ina su fareeda ne bangan su ba"
"sun tafi makaranta"
"ke miya hana miki zuwa?yafada ya tsura mata ido becox ko kad'an bayasan kannen nasa na wasa
da karatu,musamman Aisha gashi ba lafiya bata ishe taba"
"bana jin d'adi ne yaya,idan ma baka yadda ba tambayi mama"
"kinci arziki nad'auka karya kike haka kawai ne kika ki zuwa da na saba miki"murmushi kawai
tayi cikin ranta kuwa Allah take godewa da yasa mama bata karyata taba da kashinta ya bushe
wurin yaya Ab,
tasan halinsa sarai bayasan wasa da karatu gashi ko wane hukunci zai musu mama goya masa baya
take.
mikewa yayi ya wuce dakin Umma(mahaifiyar sa kenan)da sallama ya shiga dakin nata,zaune
ya risketa bisa kujera ta cika tayi fam kamar ta fashe take ji,miyasa Abubakar baya jin maganarta
ne,tace bata san alakarsa da mama Hawwa ko kad'an, bata son ya rabesu amma baya jin
maganarta,tun da ya shigo gidan ta fito daga kuryar dakin ta tana jiran ya shigo domin dama tana
nemansa amma shine ya shareta ya kusan kwashe rabin awa inda hawwa da shegiyar yarinyar
chan fitsararriya ma'ana (Aisha),ita yabari zaune tana jirainai (niko nace ikon Allah,baima san
tanayi ba)duk inda rai ke baci na Umma Hadiza ya baci a yau,bai ankara da yanayin da take ciki
ba ya sake maimaita sallama domin duk a tinanin sa bataji bane amma har yanzu shiru ta matsa
"Umma barka da safiya an tashi lafiya"ko kala batace masa ba duk da hakan ya kara maimaitawa
cikin muryar dake nuna bacin rai da hasala take cewa"ban..................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on facebook*
https://www.facebook.com/groups/465546087828286/permalink/465546091161619/
*Page* 29~~ 30
Wannan shine dalilin da yasa ta jigata da yawa adalilin d'adewar da ummanta tayi.kuma inshallah
yau take sammanin dawowarta sokoto, shiyasa take cikin farin ciki a yau sosai,ba abunda takeso
irin kabeer ya shigo hannunta kamar da sai yadda tayi dashi.yanxu haka ma sunyi waya da umman
nata bcox a Illela ta kwana,nan bada jimawa ba zata iso Sokoto.
Da misalin karfe hudu hajiya hawwa ta dira a gidan su kabeer,lokacin yana chemist dinsa,futawa
tayi sannan ta dauko kulin magani ta bata daga wanda zata sa masa a ruwa wanka sai wanda zata
samasa a abinci sannan layukan da zata sa cikin pillow dinsa sannan ta kara mata bayanin abunda
boka dajjal yace na batun aiki na nan bai warware ba amma ta kiyaye taba iyayensa sannan ta kula
wurin gudanar da wannan aikin domin wannan karon kabeer yabar wasa da addu'a shiyasa aka
kara wani aiki mai karfi a kansa,to"umma yanzu ya za'ayi nifa bana masa girki wlh balle ai nakai
masa ruwan wakan ta filllow ba damuwa zansa amma wad'annan akwai matsala"
"nikam zan wuce gida yanzun, kyasan yadda zaki yi nidai nagama nawa aiki saura naki"
"ok umma sai munyi waya,in na samu nasarar aikatawa zan sanar dake"
"Badamuwa na wuce,shin wai ma tsaya yaushene zaki zo daukan maleek ne?yaron yana kewan
iyayensa fa"
"gsky umma kibarshi gun ki kawai domin ni bazan iya da kukan sa ba kuma damuna zai dinga yi"
"ohk ba matsala na wuce"rakiya Maryama Tayi mata har bakin da madadaicin gate d'insu sannan
umman ta tashiga motarta ta wuce its kuma ta koma cikin gidan tana tunanin ya zata aikata sauran
ayyukan bokansu.
A.M.A kuwa bayan ya baro offices d'insa kamar kullum gidansa ya nufa time na sallah nayi yaje
yayi kamar kullum yadda ya saba sai da ya gabatar da isha ya fito daga masallacin,part d'insa ya
nufa ruwan brown coffee kawai yasha domin bai iya d'aura wani abun yanzu kuma baza ya iya fita
restaurant ba now,abubuwan da su zamar masa al'ada yayi bayan ya gama wanka ne yayi brush ya
kimtsa kansa cikin kayan baccinsa pink colour masu matukar kyau sannan ya kwanta tare da
cigaba da aikinsa a system d'insa kafin yayi bacci.
Saida Suhailat Ta kwashe one week sannan tadawo daga tafiyan da tayi ashe ba ta ma cikin
garin tana Kaduna gurin bukin kanwar abokiyarta.baisanta dawo ba sai da ta kwana daya a ciki
gidan sannan ya ganta,bai mata maganar fitar da tayi ba bcox dama ta saba itama bata masa
ba.lokacin week end ne bai fita company ba yafito main pallon ne yaganta zaune bisa kujera "Hi
babe ykk"
kamar bazai amsa mata ba,saida ya gama shan kamshinsa sannan ya d'aga mata kao alamar
amsawa ,bata damu ba becox tasan bai cika son yawan magana ba tace "sorry two day's na barka
k'ai d'aya amma yanxu na d'awo i hope everything normall"baima nuna mata yaji abunda tace ba
balle tayi tunanin yayi reponding nata ko da yake hankalinta na kan waya dama batayi expecting
amsa daga gare sa ba,cigaba da chat da friends d'in tayi inda suke fasa mata kai a group d'insu na
*CLASEES* *LADIES* domin ta hadu sosai a pics din bukin da aka turo mata,wani munafukin
murmushi yayi cikin ransa yana maimaita kalamanta"wai na barka kai d'ai,to miye amfaninki ko
da kina cikin gidan,ni banga banbanci tsakanin zamanki da yawo da kika tafi b..'tina ninsa ne ya
katse alokacin da ta wanke wata mata da mari ji kake tass wacce a kallah a haife zata haifeta da
sauri ya mike ganin ta na kokarin kara mata wani ya rike hannunta cikin dacin rai waigowa tayi
tace"babe pl..................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
_Ina yiwa daukacin_ *_WASU_* *_MATAN COMMENT GROUP__* _barka da zuwa sannan
ina mika_ _sakon ban hakuri ga_ *_WASU MATAN FAN'S 1,2&3 I_* *_LOVE YOU OVER_*
*Page* 31~~32
" Pls babe wait " ta juyo gurin wannan matar tana cewa cikin harshen turanci hadi da hausa "
ke wace irin mahaukaciya ce,baki da hankali ne da ba kya kallon ga ban ki,taya wasa mun tea a
jiki? "
hausan da tasa shiyasa matar nan ta fahimci kadan daga abun da take nufi tace" hajiya dan Allah
kiyi hakuri bada gangan bane,Allah ban gani ba "
" ke wace irin dabbace da b......"cikin tsawa ya kira subanta " Suhailat "batasan lokacin da sauran
maganar ya koma,ba ita kawsi ba hatta wannan matar saida ta razana amma cikin dakewa Suhailat
tace " yadai babe lfy "
cikin harshen nasara yadda matar baza ta fahimci mike going on ba yace
" lfy kike tambayana alhali kinsan mikaka aikata,miyasa baki da hankaline Suhailat taya zaki d'aga
hannu ki mari wannan matar da ta haifeki sannan kuma ki bita da bakaken maganganu da baidace
b........." tarar numfashinsa tayi tace cikin yaren da ya mata ta mayar masa"babe nice banda
hankalin kan nadau hukunci good nagode,sannan kace ta haifan point of correction kamata ta haifa
ba niba ka gane kar ka sake hada momyna da wannan trash d'in ok,look at me fa babe duk jikina
ya baci da tea d'in da ta zuba mun sannan kace bazana dauki action ba! it's not possible Allah "
" ok kinsan Allah idan kika kuskura naji kin aikata mata wani abun da baidace *WLH×3* kinji na
rantse har sau ukku,wlh bazaki kara kawomun housemade a gidana ba then ke zaki cigaba da yin
ayukkan bcox banga amfanin ki a gidan ba "
ida nunta ta rumtse domin tabbas kalamansa sun doketa a baxata" babe nice akan wannan abun da
nayiwa wannan trash din kake cewa ba kaga amfani na a gidan nan ba? "
"to miye amfanin naki Suhailat"cikin sanyi mryarsa da baza ka d'auka fada ne yakeyi ya fadi
wannan maganar.
Shiru Suhailat ta matsa bata ce komi ba yaci gaba da cewa "baki damu dani ba
cina,shana,lafiyata duk basa gabanki ako da yaushe kina bisa hanyaa baki abuja,baki kano,,kaduna
da sauran garuruwa duk domin bukii ko kina ma gari alway's kin fita baki iya zama a cikin gidan
ki,bakya tambayana idan zaki fita sai dai na taras baki nan,kin manta ina da hakki a kanki to miye
amfanin naki *SUHAILAT?*"
" babe ni kake gayawa wadannan kalaman kan wannan trash din,laifi fa tamun na mata hukunci
dadai da ita "
" ba daya muke ba that is why,dallah ma ni kabar hada ni da ita domin wallahi bazata sabu ba dole
tabar mun gidana a yau dinnan not tomorrow "
" what am i told you?ban fada miki bana bukatar y'ar aiki a gidana ba?miyasa baki bi umur
ninaba?da kika tasgi kawota kinyi shawara da ni ne?nasan amsar *NO* ce to ki buda kunnuwanki
kijini da kyau tunda har ki ka tsallake umurni na kika zo da ita,ba inda zata je sai in ita ce ta
bukaci hakan " yafada tare da hayewa uptchairs sannan ya waiayo yace" idan kika kukura kika
kaucewa maganata wannan time d'in ni da ke na " yafada yana ciza lips d'in sa tare da ida hayewa
uptchairs d'in"
Wani kololon bakin ciki ne ya to karewa *SUHAILAT* wuya "yau ita babe yake gaywa magana
tabbas tasan ta d'an kure hakurinsa ne,amma ai ita bata ga wani abun bacin rai ba kan wannan aun
da tayi,dage shoulder dinta tayi tateda tabe lis dinta ta juyo gurin wannan matar da jikinta yayi
sanyi sosai tun dazu da taji suna musayar kalmomi cikin harshen nasara duk da yadda Haidar ke
magana cikin sanyi amma tasan kanta ne ake maganar musamman lokacin da Suhailat ta nuna ta "
get out my frnd tun ban saba miki ba "taada tare da nuna mata hanya.
Wucewa tayi batare da ta fahimci abun da Suhailat tafada ba.Part d'in yan aiki da Suhailat ta
nuna matajiya da suka dawo ta nufa .
Suhailat kuwa tayi part d'in ta domin itafa maganganun babe basu daga mata hankali ba kawai
ta kyale matar nan ne saboda rantsuwar da yayi amma ita baza tayi aikin gida ba wallahi tunda
bashi aka kawota ba inji ta (😳🤣😂)amma dole ta karo wata y'ar aiki tunda ya hana ta korar
wannan m.................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 33~~34
Dole ta karo wata y'ar aiki tunda ya hana ta korar wannan matar.
Tana shiga d'an madaidaicin bedroom da Suhailat ta bata,zaunawa tayi bisa katifa tana cewa "
ohni hasiya duniya ina zaki damu?ina zaman zamana gdan mutunci ta d'aukoni amma gashi kwana
na daya na fara fuskantar wulakanci harda mari abunda ko uwa ta har ta koma ga Allah na manta
rabon da ta yi mun wannan marin " tafada tana rike hab'a " anya bazan gudu ba dan da'alama
matar nan ba mutunci gare taba ko wancan gidan da ta d'aukoni in tazo sai tai ta nuna isa tana
wulakanta irina y'an aiki bata d'au ki talaka a bakin komi ba"cikin zuciyarta take wannan zancen
batare da tasan ya fito fili ba .Allah ka sawwaka mana katausayawa talaka(nace ameeen)
Bangaren Haidar kuwa yana shiga cikin room d'insa aka kira wayarsa *UMEEY LUV* shine
sunan da ya bayyana akan screen d'in wayar,accepting calling d'in yayi tare da k'ara wayar a kunne
" Assalamu Alaikum ya Umeey"
shiru yayi sannan yace "afuwan umeey ayyukane sukamin yawa wallahi shiyasa ban shigo Abuja
ba kamar yadda na fad'a miki"shirun ya sake yi yana saurarenta sannan yace " yace inshaallah
cikin weak d'innanzan shigo domin akwai wani course da nake son na tafi nayi a india "jim kadan
yace "ok badamuwa sai na shigo,bye "yaman nawa wayar kiss .
Bayan ya ajiya wayar ne bisa d'an madaidaicin glass dake gabansa,ya zauna saman royal kujera
1siter tare da kunna tv yana kallon news.
Abangaren Abban Khaleel kuwa biyar da rabi daidai ya kulle shagonsa,bayan ya fito daga
kasuwar direct islamiyya ya nufa,yau ranar hardace don haka harda ya dibawa yan class d'insa
bayan sun kammala akayi addu'ar tashi sannan ya wuce gidansa.
Kamar kullum yadda gidansa yake haka ya tarar dashi,bata gajiya da ayyukan gidan shiyasa ko
da yaushe kaunarta ke kara ratsa zuciyarsa da gangar jikinsa ,komi baci da ransa yayi idan yashigo
cikin gidansa sai yaji ya wanke musammanidan yayi tozali da kyakkawar matarsa wannan ita ce
ake kira *_MAR'ATUSSALIHA_*.
Sallama yayi ta'amsa tana cikin kwalliyarta mai daukar hankali,riga da siket ne take sanye
dasu na atamfa yayin da d'unkin yayi mata cip a jikinta gwanin shawa tokarewa yayi a bakin kofar
yana kallonta itama shi d'in take kallo rungumar davyaran sukamasa yasa yadawo cikin haiyacinsa
suna cewa oyoyo Abba sannu da zuwa rungumarsu yayi yana amsa musu tare da tambayarsu
suma suna lafiya,kusa dashi tazo ta zauna itama tana masa sannu da zuwa amsawa yayi d'auke da
murmushi a fuskarsa yayin ta cewa yaran oya ku tashi kubari Abba yaje yawatsa ruwa "tou
umma"sukace yayin da suka daga daga cinyar Abban khaleel ta kardun da ya shigo dasu a
hannunsa ta dauka da'alama daga islamiyya ya biyo dasu dakin sa ta kai masa yayin da tafito cikin
tsakar gidan ta hada masa ruwan wanka ya shiga yayi yayin da a zuciyarsa yake cewa" miya kai
haka dadi a duniya!samun mace ta gari shine ginshikin farin ciki a rayuwa shiyasa Annabi
Muhammad Sallallahu alaihi wassalam yake cewa, ,فنكح المراءة الءربع لمالها
فعلك بذات الدين تركت يداك,ولدينها,ولحسبها,ولجمالها.
Manzon (S.A.W)ya bada zabi ku aure mace don abubuwa guda hudu.
1-Domin dukiyarta
2-Domin kyawunta
3-Domin nasabarta
4-Domin Addininta
Amma sai yace wacce tafi alkhairi itace ku aureta dan addininta domin shi yake dawwama kuma
shine dawwamamme.
Bayan yafito daga wanka tana tamaka masa yana saka tufafi ya dube ta yace "madallah da samun
mace ta gari mai Addini,ako da yaushe ina kara godewa Allah da ya mallaka min ke a matsayin
matata"murmushi ne ya subuce mata ta rungumeshi tana cewa "madalla da samun miji kuma
malamina "bayan ya kamma shirin suka fito falo suna cin abincin dare,sannan suka dan taba hira
saida yaran suka yi bacci ta kaisu makwancin su tare da sauya musu kaya zuwa na bacci ta musu
Addu'a tasha fa musu sannan suma suka nufi ma kwancinsu.(Asuba ta gari )
Aka ce dare mahutar bawa amma abangaren Dr.Aysha ba haka bane zaune take takasa bacci da ta
rufe idanunta Dr.Haidar take gani ji take kamar ace yana kusa da ita da ta nuna masa kalar
soyayyar da take masa zuciyarta na kunci ne idan ta tuna ko wani ma'aurata a wannan lokacin
suna tare da junansu,rumtse idanunta tayi tanaji kamar an watsa mata tafasasshin ruwan zafi idan
tayi wanan tunanin.juyi kawai take yi bisa makeken gadonta daga kai tayi ta kalli agogon dake
manne bisa bangon dakin na zinari karfe 1:30Pm na dare jingina jikinta tayi da gadon yayin da ta
lalibo wayarta iphone 11pro ta danna tsakiya haske ya kawo photonsa ta zurawa ido wanda yake a
walpeper wayarta yana sanye da suit black yayi masifar kyau kayan sun kara haskaka hasken
fatarsa suman kansa sai sheki take yana d'aura agogo a hanunsa da'alama unexpected pics akayi
masa galeery dinta sunansa ne a password dinta Aliyuheartbeat💓 bayan ta cire password d'in ta
cigaba da kallon pics dinsa kala kala dake cikin wayarta kama daga na kananan
kaya,suit,shadda,boyel,da kayansu na likitoci bata ankara ba sai da taji agogo ya buga karfe uku
saura na dare ajiyar zuciya ta sauke yayin da zuciyarta ta kasa hakuri saida ta lalibo number sa ta
d'an na masa k.......................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 35~~36
Ta lalibo numbersa ta d'an na masa kira....har ta katse har ta katse bai daga ba ......
wani takaici ne ya ziyarci zuciyarta mara iyaka, ita daya kamar zararra take cewa " dama nasan
cewa yana chan tare da tsinanniyar matarsa (ma'ana Suhailat🤣) .
Wasu hawaye ne suka wanke mata fuska yayin da d'ayar zuciyarta ke sanar da ita cewa "a'a Aysha
shi d'aya yake kwance kin manta wace ce Suhailat?Kin manta halayen ta."
Wani sanyayyen murmushi ta saki tana cewa " na rantse da ubangijin daya busa mini rayuwa sai
na ruguza miki farincikin ki Suhailat saina aure Aliyu domin na fiki da cewa dashi,sonsa da
kaunarsa acikin jinina yake na fiki bukatarsa a rayuwa,saina mallake sa ko ta wani hali ne"
sake kiransa tayi a karo na biyu..
A bangaren Haidar kuwa,baccinsa yake sha mai dadi cike da mafalkai masu tsayawa arai da
zuciya,wayarsa yaji tana ringing bai samu damar dagawa ba har ta yanke,bayan wasu yan mint aka
sake kiransa cikin yanayin baccin da bai gama sakin saba ya daga wayar aransa yana mamakin
wazai kirashi a wannan lokacin kuma wannan number famlinsa ne kawai ke da ita.
Wani sihirtaccen murmushi ne ya kwace mata a yayin da taga an amsa kiranta harda wani shauki
ta tsinci kanta aciki a yayin da ta diba lokaci ukku da rabi saura minti biyar na dare,wannan shike
nuna cewarr ba ya tare da waccan abar.
Cikin yaudararrar murya mai murya mai kashe jiki tare da sanya kasala tace "Assalamu Alaika ya
habiby"
Bayan ya daga wayar ne ya d'aura a kunnensa ba tare da ya binciki number ba,muryar da tayi
amfani da ita wurin yi masa sallama ta daki dodon kunnensa,hakika muryar ta ratsa gangar jikinsa
yayin da tayi nasarar kara kashe masa jiki dalilin mafarkin da yayi,wannan abun yasa takara tasiri
akansa amma bai nuna hakan ba illa mikewa zaune da yayi cikin mamaki,aransa yake cewa"a ina
tasamu number na ?ubanwa ne yabata ita ?".
wani irin b'aci ransa ya kara yi a yayin da yatuna mafarkin da yake ta katsesa.Duk d ya gane
muryar domin ba boyayya ce a garesa ba duk da yakasance ako da yaushe da wani kalan salo da
take zuwar masa dashi ta hanyar lanqwashe murya da kararrayata cikin kissa,shiru ya mata baice
komi ba amma ya amsa sallamar a zuciyarsa(🤣sabon salo).
Jin tayi sallama amma bai amsa ba yasa itama tayi shiru duk da tana fatan taji muryarsa ko
kad'anne domin tasamu damar yin bacci cikin salama.Tsawon wani lokaci bai ce mata komi ba, ya
sa tasake magana zuciyarta achinkushe tana mamakin miye dalili,muryarta tana ta tsiri akan kowa
amma banda haidar d'inta "hello heartbeat kana jina ?" ta fada cikin yaudarar murya.
shirun da yaji tayi yasashi jan tsaki cikin ransa yana cewa *_CHINGOM_* kawai,yayin yayi jifa
da wayar chan karshen bed d'insa ba tare ya katse kiran ba.chan side guda na bed d'in ya koma ya
kwanta yana ja mata Allah ya isa na tadaa shi daga baccinsa da tayi,ayayin da chan take masa
magana shiru ba amsa.
"Hello dear kana jina?plss say something dan Allah",shiru bai amsa mata ba.
"my haidar wlh ina azabtuwa da rashin jin muryar yarka! dan Allah kamun magana ko naji sanyi
araina".har dai yanzun baice komi ba atunaninta,kallon wayar tayi amma ba'a katse kiran ba
wannan shike nuna yana jinta,cikin narke murya ta kara cewa" pls and pls haidar kamun magana
ko nasamu yin bacci cikin salama wlh zuciyana zafi take na rashin jin ganin ka, kunnuwana na
mararin jin sautinka suke,idanuna ciwo suke na rashin tozali da kai,hancina kewar kamshinka
yake yayin da gangar jikina take jin kamar ace kana kusa da ita.
Duk wannan zubar da takeyi har yanzu bataji yace mata kanzil ba (ko numfashinsa ba taji ba
amma hankalinta bai kai ga hakan ba ta lula duniyar masoya🤣).
My dear Haidar Dan Allah kace wani abu mana,dagaske nakeyi *ina sonka* na mallaka ma
zuciyata da gangar jikina, plss ko na minti biyu kace min biyu ne kace mun wani abu wlh ina
kishin muryarka.
Yanzu kam shirun nasa ya kular da zuciyarta a yayin da kuma ta kasa jin haushinsa, sai tunaninta
da karkata kan cewa Suhailat ce ta daga kiran ba Haidar ba,cikin bakin cikin tuanin da yazo cikin
ranta ta cillar da wayar itama ba tare da ta yanke kiran ba tafada jicce tana zubar da hawayen kishi
(tofah wata sabuwa inji y'an chacha)tana k'ara daukar alwashi a kan Suhailat tare da tsanarta dake
kara lunkuwa cikin zuciyarta,take sosai tanaji ajikinta zata iya rasa rayuwarta idan bata samu
Haidar ba dimin shine muradin zuciyarta da rayuwarta,adadin kwallar dak fita tu daga zuciyarta
izuwa idaniyar ta wadanda ke zubar da anbaliyar hawaye suke adadin kiyayya da tsanar Suhailat
da kuma soyayyar Haidar dake lunkuwa adukkan zuciyarta da rassanta.
Haidar kuwa ya katsa komawa baccinsa juyi kawai yake yi bisa makeken gadonsa da ya gaji da
juyin ne ya mike ya shiga bathroom ya watsa ruwa,bayan ya fito ya saka white jallabiya ya nufi
wani corridor mai kyau design dinta kamar masallaci ga qur'an nan masu yawa d littafai nan kala
kala na musulunci agefe,bisa shinfidadd'iyar dardumar dake gurin ya hau ya kabbarta sallar
nafila,sai da aka kira subhi ya sallace ta sannan bacci ya dauke sa yana karatun Al-qur'ani mai
girma.
*Zeesardaunerh ce*
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 37~~38
Bangaren Suhailat Kuwa ta raya daren ne tana charting sai da bacci b'arawo ya saceta gabanin
subahin,dama ita bata bacci a dare saida safe domin dare lokacin charting ne na MANYAN
MATA.
Safe kuwa lokacin baccin tane sannan rana lokacin yawo da d'aukar wanka.Ita rayuwarta
a tsare take,komi ta gama tsarashi ta yadda zata gudanar dashi (lol Suhailat Sarkin tsari🤣).
Kiran sallar subahin ake tayi ako ina,muminai na kwarai suna hanzari domin su gaida
Ubangijin su ya yin da baccin WASU MATAN yake k'ara dadi suna ji kamar kada a tada su,to
hakanne ya kasance a wurin SUHAILAT,DR.AYSHA,MARYAMA Da kuma d'ai-d'ai kun mutane.
Bangaren MARYAMA Kuwa baccin ta take sha cikin kwanciyar hankali ya yin da take
mafarkin Kabeer ya k'ara dawowa hannunta sai yadda tayi da shi.
Kwankwasa kofar d'akinta Kabeer Ya yi amma shiru Suhailat Bata farka ba,dama ya san halinta na
rashin yin salla a kan lokaci.
Bayan ya dawo daga masallaci misalin bakwai saura(domin sai da rana ta fito sannan ya dago
daga masallacin),wanka yayi ya shirya,dama duk lahadi yana hutawa ne sai ya barwa abokinsa
kemis(chemist)d'in ya kular masa da shi.
Yunwa ce ke kwakular y'an hanjin sa dan haka ya shiga motar sa kirar civic ya nufi Runjin Sambo
gurin mahaifansa.
Cikin lilwantaccen harabar gidan yayi pakin(parking),cikin gidan ya shiga da sallama,ba kowa a
tsakar gidan,part d'in mahaifiyarsa ya nufa.Kutsa kansa ya yi cikin palon tare da sallama ,zaune ya
riske ahalinsa suna karin kumallo(breakfast)Alhaji Sa'id Wato mahaifinsa sai Hajiya Aisha
mahaifiyarsa wato (Ummu)tare da k'annensa Batul Da Fatima.Da gudu su Batul Su ka zo inda
yayan su suna oyoyo kamar yara kanana.Rumngumesu ya yi yana amsa ina kwana da suke yi
masa .
Dining area ya nufa yana gaida mahaifansa,
"Abba Ina kwana "
"lfy lau Muhammad Kabeer Kana lafiya"
"lafiya lau nake Abba Dafatan na sameku lafiya"
"muma lafiya muke "
Ummu ya gaida itama ta amsa cikin farin ciki ganin yaronta ya fara dawo wa cikin hayyacinsa.
Sarving d'insa Batul Ta fara ya yin da Fatima Ke had'a masa tea,Abba ne ya dubesa yana cewa
"dafatan dai lafiya ko?naga kayi sammako sosai gashi yau lahadi ne ,
"lafiya lau Abba"
"tou mashaallah ya iyalin taka "
"qalau take tana gaida ku"
"muna amsawa"
Abba ya fada,ummu kuwa shiru tayi domin ta san wacece Maryama.Karin kumallon(breakfast)ya
zauna ya narki abunsa sai da kowa ya rigasa kammalawa,Bayan ya gama ya dawo palo suka
cigaba da fira da y'an uwansa ya yin da farin ciki ya cika zuciyoyin wannan ahali.Bayan sun ci
abincin rana(lunch)aka dora daga inda aka tsaya.
Kachokan wannan yinin ranar a gidansu ya yi shi doimin bayan ma yayi sallar azzahar zama
yayi shida su Batul suna ta shirme tare da kalle-kalle a Youtube da IG,da la'asar kuwa sai da ummu
ta kora su Batul suka d'aura mata girki shikuma ya fita gun abokanansa.Bayan anyi magrib ya
dawo sukaci abincin dare(dinner)a tare da ahalinsa,shine bai bar gidan ba sai da ummu ta kora sa
misalin karfe goma na dare sannan yabar gidan cike da kewar y'an uwansa.
MARYAMA Kuwa misalin bakwai da rabi na safe kiran wayarta ya tada ta daga baccin da ta
koma bayan Kabeer Ya tashe ta,kafin ta samu damar d'aukar wayar kiran ya katse,mika tayi
sannan ta duba agogon wayarta zaro idanu tayi da taga lokaci da sauri ta fad'a makewayi(toilet)ta
d'auro alwala sannan ta kabbarta sallar subahin(innalillahi wa inna ilaihi raji'un).
Bayan ta idar da sallar ne cikin ta ya fara kiran chiroma da hanzari ta d'auki kudi cikin jakarta ta
bugawa makociyarsu waya domin ta turo mata Almajirinta sai tace mata
"bayanan amma bari ta turo mata saleem" d'anta .Bayan yaron ya iso ya gaida ita ta amsa sannan
ta mika masa kud'in tana cewa,
"Saleem kasan madam Turai Restaurant?"
"eh Anty "
"ok chan zaka je ka siyomin soyayyar indomie da kwai sai shayi kar a sa sugar da yawa"
"tou"yace yana fita da hanzarinsa .
Wanka tayi ta saka riga doguwa,bata jima da zama ba ya dawo ya mika mata aiken,amsa tayi tace,
"yawwa Saleem d'an Albarka"ta mika masa naira hamsin yace,
"na gode" ya wuce gidansu yana murna.
Bayan cikin ta ya cika ta dawo normall sannan ta dauki wayarta,miss call uku ta gani na
mahaifiyarta.kiran number tayi ringin biyu aka d'auka,
"ummana ta kaina dafatan dai lafiya naga kiranki har uku a wayana ina bacci"
"Bacci kuma shalele?karfe bakwai da rabi fa"
"eh wallahi umma yanzun na farka banjima da yin sallah ba"
"ok ya batun aikin malam kin kammala?"
"a'a umma "
"me yasa to?kefa kika d'agan hankali sai da na k'arbo miki maganin nan amma aikatawa ya ga
gareki"
"to ni umma fa na fada miki bansan ya zan sa masa maganin nan a abinci ba!nifa ban ma san a ina
yake cin abincin sa ba"
Bangaren umma idanu ta zaro waje tace "ah lallai shalele ai ga irin ta nan da kina yi masa girki ai
baza kisha wahalar sa masa maganin ba amma kin k'i jin maganata,ke ba kiyi ba kuma baki bari na
kawo miki y'ar aiki tayi ba saboda bakin kishin ki na tsiya"
zumburo baki Maryama Tayi tace" kinsan halina ko a gida idan ina karatun novels bana iya aikata
komi , yanzu haka ni mafa abincin nake tsaya a waje inaci"
"Hmmmm ya miki kyau,ke kyautawa kanki, yanzu duk abunda na koyar dake a gida kenan ta
bayan kunnenki yabi,karatun novel d'in banza dan ni banga amfanin da ya ke miki ba,maimakon
ace kin k'ara gogewa ta bangaren kula da mijin ki tunda kece ke son sa amma a'a,kece ko da
yaushe aje gun malam amma idan an karbo kuma aiki da maganin ya miki wuya,haba shalele
kima kanki fad'a mana"
Cikin d'an bata rai alamun fad'an mamanta bai mata dad'i ba tace, "tou yanzu ummama ya kike son
na yi?"
"shalele kin san komi,ya dace ki d'in ga hadawa da y'ar kissar nan ta mata domin ba ko da yaushe
magani ke aiki ba,kuma idan kika hada biyu zaki fi samun yadda kike so"
"umma sanin kanki ne bana son na tambayi abu ace a'a bazan yi ba duk da ina son Kabeer ba shi
ke nuna zan iya bin umurnin sa ba kinga kuwa idan nace kissa zan sa a al'amurana dole sai nabi
umurninsa ni kuwa hakan ne bana so gwara yazan kar tasan kar,naifison idan na basa umurni jiki
na rawa ya aikata kamar da"
"tou naji,amma dai yanzun dole ki san yadda za'a yi, matukar kina son burinki ya cika to dole
cikin biyu ki zab'i daya"
"ok mine ne zan zab'i dayan"
"hanyar da za'a sa maganin mana"
Murmushi Maryama tayi tace,
"shiyasa nake k'ara sonki ummana gashi harkin nemo hanya biyu sai wadda na zab'a "
itama umma murmushi tayi kamar tana gaban maryama tace,
"to ai ke shalele bani da tabbacin hanyoyin suyi miki "
"fada naji innata in sunyi kuma nasan ko ma ba suyi ba zaki nemowa shalelenki wasu"
"hmmmmmmmmmmm gaski bana ganin akwai wasu bancin wand'annan shalele"
"umhmmm"
"mafitar ko nace hanyoyin su ne...............................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*_Don Allah ina mai neman_* *_Alfarma ga duk wanda ya_* *_karanta wannan page din da_ ya
taimaka ya ma Abbana Addu'a Allah ya bashi lafiya*🙏🙏 🙏
*Page* 39~~40
"Mafitar ko nace hanyoyin sune......... *na daya* dole ki sauya ki rika yi masa girki a ko da
yaushe sannan duk abunda ki kasan mace na yi wa mijinta ta bangaren ladabi da biyayya ki dinga
yi masa,ki kwantar da hankalinki ki rika bin umurninsa,ki kuma daure duk fada ko wani abu da zai
miki ta hakan ne zai tabbatar cewa kin sauya.Ta nan ne zaki yi amfani da damarki wurin ganin
cewa yaci maganin sannan na wankan ma kin sa masa yayi amfani dashi, kinga kuwa bukata ta
biya domin shi zai d'auka kin sauya ne saboda shariyar da yake miki amma ke a gunki ba hakan
bane,ki sauya ne na wani lokaci saboda cimma burinki".
"umma......"
Da hanzari tace ,
"dakata shalele!ki bari na ida bayanin mana".
Tana gama fadar haka ta katse kiran ya yinda ta bar Maryama cikin kogin tunani domin ta rasa
madafa(kishi zata aje ta bari akawo mata y'ar aiki ko kiwa zata cire ta ma mijin ta girki).
Haka MARYAMA Ta yini ciki tunani da neman zab'i acikin biyun,lokacin da taga kanta zai yi
ciwo sanadiyyar zafin da ya d'auk a sai ta watsar da komi da d'auko wayar ta ta cigaba da karatun
littafin ta,bayan ta turawa ummanta text na alala take so tayi ta bada akawo mata.
Yinin yau jin kanta take cikin feeling mara iyaka tun tana d'aurewa saboda alwashin da tayi na
baza taje gun kabeer ba sai mallakesa .Tofa abun na yau na neman fin karfin ta,ta rasa ya
zatayi,karatun novels d'in ma ya isheta ta ajiye wayar.
Bayan tayi sallar magrib ta shirya kanta cikin doguwar rigar bacci mai kyau ta zauna falo tana
jiran dawowarsa domin yau kam baza tayi jurewa ba.ta na nan zaune akayi isha'i taje tayi tana
Allah Allah Kabeer Ya dawo amma Kabeer Shiru kamar an aiki bawa garin su gashi abun nata sai
tsamari yake.
Takwass ta wuce Tara ma haka amma ba'alamar Kabeer,iya shaka ta shaka domin tasan baza ya
wuce yana gun mahaifansa ba,tsanin kanta ne Kabeer a ko ina yake da anyi sallar isha'i ya dawo
gida,idan ko hakanne dole tayi zab'i acikin biyun da ummanta tace.
Abu kamar wasa karfe goma na batun wucewa bai shigo ba,cikin ta ne yayi wani jafurin mirdawa
saida ta duke kafin ya lafa.Abu ya zame mata gom da ashirin ga yanayin da take ciki sannan ga
ciwon ciki ya sako ta gaba.
Tana nan zaune tana jiransa cikin ta yayi mirdawar da saida ta kwasa a guje tayi
makewayi(toilet )da ke cikin dakin ta.ciwon cikin nata bai rasa nasaba da Alalar da tace wa
ummanta ayi mata,ita taci a matsayin abincin rana sannan ta kara cinyewa da maraice.
Shigarta cikin dakin ba da jimawa ba kabeer ya shigo cikin gidan,ta falon yabi yayi dakinsa
ganin bai ganta a falo baya dauka tayi bacci .Dakinsa ya shiga tare da rufe kofar.
Tufafin jikinsa ya cire ya watsa ruwa sannan ya saka tufafin bacci(sleeping dress )ya yi
kwanciyarsa a gado .
Duk inda ranta yake ya yii matukar b'aci ya yin da sai tsinewa iyayen Kabeer Take kamar sune
silar shigarta halin da take ciki(hattara y'an uwa iyayen miji suma fa iyayenki ne domin sune suka
haifa maki shi,duk rashin kunyar da ki kama uwar mijinki mamanki ce ki ka yi wa domin hausawa
nace wa "kowa ya raina iyayen wani......."Mu samman ma uwar miji sai kiji ana ce ma ta
ulcer,hypertension da dai sauransu abunda kuwa idan da mahaifiyar kice baza kice mata haka ba
kuma kar ki manta duk abunda ki ka yiwa uwar wasu sai anyi wa taki kuma kema zaki haifa kuma
zaki kasance a wannan matsayin na *UWAR MIJI.* Duk da nasan cewa wata uwar mijin sai a
slow amma hakuri zakiyi domin da mahaifiyar ki ce haka hakurin zakiyi domi baza ki chanza wata
ba.)
Abu fa ya ta'azzara yayin da MARYAMA sai murkususu take a ranta tana cewa "ashe haka Kabeer
ya ke ji?kalolin tawye hakki da take masa lokacin da baya cikin hayyacinsa ta shiga tuna wa wani
lokaci da kyar yake iya bacci.
Karfe d'aya na dare duk kuzarinta ya kare sai juye-juye tanajin kamar ta mutu.Yadda taga rana
haka ta ga dare yau,duk ta fita hayyacinta dare d'aya sai kusan karfe hudu baccin wahala ya tafi da
ita(Allah bi da lafiya Maryama🤣)
*Bari mu waiwayi bangaren Aliya;* Yanzu na samu rangwammen d'an takurar da inna Saude keyi
mini sanadiyyar rashin lafiyar da take fama da ita domin mura ta mata mugun kamu sosai cikin ma
tana shan magani,Karatu kuwa Alhmdllh komi yana tafiya dadai da yardar Allah gashi yanzu abu
ya kara zo mana da sauki,Allah ya albarkaci y'ar buga-bugar da Bappana Keyi har ya hadasa da
Abokinsa wanda sukayi makaranta a tare kusan shekara Ashirin da d'ori sai gashi Allah ya sake
had'a su shine Bappa yazo dashi gida.
Bayan sun gaisa cike da farincikin haduwarsu tare da labarin bayan rabuwa har yake tambayar
Bappa" wace sana'a yake? "
"Hmm muktar abun ba'a cewa komi domin Abubuwa sai dai Allah ya sawwaka,a yanzu d'ai ba
wata sana'a da nakeyi "
"Ameen"
"mashaallah,amma zaka barta ta ci gaba da karatu ko?"ya fada yana fatan hakan.
"inshaaallah domin shine burin mamanta kafin ta rasu,nima kuma inshaallah zan cika wannan
burin nata" yafada cikin alhinin tuna babban rashin da yayi.
"ameeen"
Salmat itama ta shigo dauke da lemon gora da Aliya tasata siyowa bakon, bayan ta kaimasa ya
rinka janta da hira abunka da suda mai shegen surutu sai ta biye tana ta bashi labari sai da Aliya ta
kira ta sannan ta fita .
Bayan fitar ta Bappa yake gaya masa "wannan Salmat kenan itace auta kanwar Aliya suka dai
Allah ya bani"
Anan Bappa shima yake tmbayar Abba muktar ina diyan su,
"suna chan Abuja bada su na zoba"
"ina gaidasu"
"zasuji inshallah"
Ya jima sosai a gidan kafin yayi sallama da su Aliya Da inna Saude wacce tunda ya shigo gidan
suka gaisa sai washe baki take tana mamakin wai wannan Alhajin aminin mijin ta ne itafa abun ya
yi mata dad'i sosai .
Bayan ya yi musu sallama ya bawa inna Saude Dubu ashirin,Aleeya Da Salmat Dubu goma ko
wannen su dubu biyar-biyar suka dinga godiya da addu'a musamman inna Saude.
Ai ko yana fita inna Saude Ta buga tsalle tana cewa................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 41~~42
Murmushi ne ya subucemini ina kallon innata da k'anwata da farin ciki mara iya ka ya wanzu a
fuskokin su.
Ihun murnar da Salmat keyi shi ya tabbatar wa inna Saude dake tunanin mafarki take ba hakan
bane gaskiya ne,kasa naga inna Saude tayi tare da yin sujjadar shukur tana cewa,
"Allah na gode maka,wai ni Saudatu nice keda kudi kimanin dubu daya-daya har dubu ashirin kai
Allah na gode maka"
bayyana farin cikin inna saude ma b'ata lokacine domin fa ta fara ganin alamun cewa burinta na
zama *HAJIYA SAUDE* zai tabbata ga alamu nan ta fara gani (sannunki dai amaryar Bappa
hajiya saude🤣).
Bangaren Bappa kuwa bayan fitarsu daga gidan suka k'ara yin sallama da juna Abba muktar yace,
"inshaallah duk lokacin da na shigo sokoto zan d'inka biyowa"
"Ameen" Abba yace sannan ya shiga cikin motarsa.Zagayowa gefen taga Bappa yayi sanadiyar
kiran da Abba yayi masa,duko kainai yayi Abba ya miko masa kudi kimanin dubu saba'in.
Suman tsaye Bappa yayi yana kallon kud'in da ke a hannunsa dakyar ya kakalo miyau a bakinsa
da nufin yace wani abu amma kash sai Abba ya rigasa da cewa,
"don Allah in har ka dauke ni matsayin d'an uwa ba aboki ba kar kace bazaka amsa ba"
rasa abun cewa Bappa yayi , dakyar ya bud'i ba yace,
"amma .....'
Sallama yayi amma Aliya ce kawai ta'amsa ya yin da Salmat da inna basu san ma yayi
ba,tsayawa yayi yana kalon su,fuskar su kawai ta isa bayyanar da farin cikin dake cikin
zukatansu.Dakinsa Bappa ya shiga domin yasan a wannan lokacin ko yayi musu magana ba
ganewa za suyi ba.
Wayarsa ya d'auka ya lalibo number kanwarsa dake aure a nan sokoto,ringin biyu ta daga tare da
cewa,
Bayan sun kammala waya da Dadda ya kira Anty yelwa dake aure a chan yola ya sanar da ita,tayi
murna sosai tare da yiwa Abba mukhtar Addu'a.
Inna Saude kuwa farin ciki ya hanata bi takan kud'in mu duk da cewa ta gansu ko nace addu'ar
Salmat ce ta kammata domin Allah - Allah take kar inna ta amshe kudin tasan halinta indai game
da kudi ne.
Ko abinci inna Saude kasa ci tayi sosai kan farin ciki shidai Bappa kallonta kawai yake.
Bayan an kira sallar zuhur yaje masallaci yayi,muma muka tashi domin yin sallar bayan mun
mikawa Bappa kud'in mu ya a dana mana domin inna Saude cewa tayi mu aje har zuwa gobe zata
karb'a,Salmat gudun inna ta karbe kudin taki bamu ko sisi ya sa tace min Inna tace mu kaiwa
Bappa ya adana mana.
Misalin karfe uku sallamar mama kareema ta karad'e gidan da d'an sauri na mike yayin da Salmat
ta fita da gudu na bita a baya,gun mama kareema muka nufa muka fada saman
jikinta.Rungumemu tayi muna cewa cikin harshen turanci,
"yi hakuri kanwata ta musaman nayi kewarki mana,ban lura dake bane ina chan ina daukin ganin
mamana"
Mumurshi ta saki yayin da ta saka ihu ta nufi salmat da maganar da Ramlat tayi ya ankarar da ita
domin ko.. bata lura da ita ba,ihu itama tasa tayo kanta da gudu suka rungume junansu suna farin
ciki,mama kareema tace,
"wai nikam yaushe ne zaku girma salmat,ji wannan abun da kuke kamar kananin yara"
murmushi na saki yayin da nago idanuna da niyar nace wani abu naga mutum yana kallona ,kasa
nayi da idanuna gashi ko hijab ban saye da shi,kunya duk tabi ta lullubeni domin wlh ban lura da
mutum a bayan mama ba,ko yanzu jayewar da Ramlat Tayi yasa na ganshi.sake d'ago kaina nayi
naga yana amsa gaisuwar da Salmat ke masa amma idanunsa na kaina,tsaki naja ciki-ciki domin
na sani yawan kallo shiyasa ma na rage zuwa gidansu.
Kawda kaina nayi daga gefensa sannan nace,
"ya *ANWAR* ina yini"
shiru ya yi bai amsa ba kuma b'e dena kallona ba.
Mama ta juyo ta fuskance sa tace,
"baka ji mai sunan Dadda na maka magana bane ?"
Kawda kansa yayi daga barin kallona ganin shi mama ke kallo sannan yace,
"kyaleta mama naji amma bana bukata sai yanzu ta ganni ne"
murmushi mama tayi ta dubeni tace,
"to kinji abunda yayan naki yace"
"Allah mama ban lura da shi ba"
Inna Saude kuwa tana jin sallamar mama kareema ta mike saman dardumar da take ta dauki
kud'inta sai hankad'in katuwar katifarta ta boye su tana tunanin mi ya kawo mama kareema
gidan( domin bata san an ba Bappa kudi ba),boye kudin tayi don wai kar ace ta bada wani abu
cikin su,Sam inna Saude basa shiri da mama kareema tun mamien Aliya na da rai domin a ganin
mama kareema saboda inna saude Bappa ke kin kula Anty halima(mahaifiyar Aliya).
Tana zaune bisa katifar ta wadda ta boye kud'in Salmat ta shigo tana fada mata mama kareema
tazo ,
"eh naji gani nan fitowa"tafada tare da mikawa Salmat Ta barma ta shinfida kafin ta fito.
Tabe baki inna Saude dake fitowa daga daki tayi sannan tace,.....................................✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
_plsss karku manta ku cigaba da sa mahaifina a Addu'o'inku Allah ya bashi lafiya dan darajar
Alqur'ani 🙏🙏🙏_
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab sardaunerh*
_________________
______
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa
da jama'a bisa harshen hausa_
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 43~~44
Tabe baki inna Saude da ke fitowa daga d'aki tayi sannan ta ce,
"ai kam kin b'ata innarmu domin tun shigowarmu ba mu gan ki ba sai da mu ka kai ga
cigiyarki"cewar Ramlat Tana dariya,Salmat ta chab'e zancen cikin dariya tana cewa,
"hmmm ke dai kawas bari,inna kud'i ta yi shiyasa ki ka ga ta b'ata,tana gudun ta fito daga d'aki
aljani ya santale mata kud'i"
Dariya su mama suka sa ka harda ya *ANWAR* Duk da cewa ba su fahimci zancen Salmat
Ba,amma ganin yadda inna ta ha yayyako musu da fad'a kamar taci babu ya saka su dariya.
Ni dai lokacin da na sa mu hankalinsu ya d'auku ga fad'an inna na sulale zuwa d'aki na saka
hijab d'ina blue iyakrsa guiwa sannan na dawo gunsu na zauna.
*ANWAR*
Dukda cewa idanuna na kan diramar su Ramlat Da inna amma hankalina na gunta,ina kallonta sai
da ta diba taga ba mai kallonta sannan ta shiga d'aki,bayan wasu mintukka ta fito sanye da hijab
d"inta ta zauna,dama ni tun da ta shiga d'aki nasn cewa da wuya ba shine zata saka ba domin
yadda take takura kanta kamar wadda z'a cinye d'anya.
Bayan inna ta gama fad'an nata suka gaisa da mama kareema sannan ya Anwar Da Ramlat suka
gaida ita,ta amsa gaisuwar ya Anwar Amma ta Ramlat cewa tayi ba ta so ta rike abunta,aiko mi
Salmat zatayi in ba dariya ba .
Ana cikin haka Bappana ya shigo gidan da sallamarsa muka amsa tare da gaidashi,ya samu wuri
ya zauna suka gaisa da mama kareema da su ya Anwar.
Bayan sun gaisa ne yake fad'a mata dalilin kiranta inda ya shiga ba ta labarin abun alkhairin da ya
same su.
Alokacin da taji bappa na fad'in "dalilin da ya sa nace kizo......."har zuwa in da yake sanar da
ita kudin da aka ba ma su inna Saude,wani takaicine ya yi nasarar lullube inna cikin ranta take
cewa,
"yo da ma kenan shi ya kirata,hmmm to mi yake nufi da sanar da ita kudin da muka samu?yasin ni
ko kwandala ta baza ta gani ba bare na b'ata ehhhe"
tana cikin wannan tunanin ne taji Bappa na fad'in Muktar ya ba shi kud'i kimanin dubu
saba'in,cikin zaro idanu tace,
"eh"
a takaice domin shi lamarin saude kan kud'i mamaki yake bashi,tun d'a zu yana lura da ita yadda ta
b'ata ranta saboda kawai ya fad'awa k'aunarsa abun da suka samu,,amma dibe ta yanzu kamar ba
ita ba daga jin maganar kud"in da ya samu.
"yanzunnan kuma bayan na fito daga masallaci muktar ya kirani yana shaidamin cewa ya turo
yaro da sako wurina na jirasa yana hanya,bayan wasu y'an mintoci yaron ya iso,muka gaisa sannan
ya mikimin wasu takardu da makulli yace gashi cewa akayi ya bani nace masa nagode,bayan ya
tafi na duba takardun anan na ga cewa takardun shago ne a sabuwar kasuwa( Sokoto central
market)ya saya da sunana ya mallaka min,kinga ta kardun"
ya fad'a yana nuna muna takardun.
Murna kowa ya shiga taya bappa yayin da inna Saude da tayi suman tsaye jin cewa an bashi kud'i
kimanin dubu sab'ain ga kuma maganar shago bata san lokacin da tace,
Bata damu da kallon da kowa ya yi mata ba don ba taga abun kallon da ta yi ba,ya yin da ta shiga
cikin ayarin masu taya bappa murna,nan ta zage aka shiga kasafa kud'in bappa tare da lissafa
abubuwan da za'azuba a shago ya yin da farin ciki ya lullube ta ganin ba wanda yabi takan
kud'inta.
Anan su mama sukayi i'sha bayan sunci girkin da na girka ni da su Salmat Da Ramlat,ya *Anwar*
santi kawai ya ke, su Salmat na ta yi masa dariya, wai duk dad'in girkin sune ya saka shi santi,
"ina wannan girkin ya yi dadi balle har nayi santi,msstwwss kawai dan Agla tasa hannunta ne yayi
dad'i(Agla ko beauty shine sunnan da ya ke kiranta da su)
"lallai ya Anwar ka ci mu game wlh,yanzu tsabar son kai za ka ce wannan girkin bai yi dad'i
ba"cewar Salmat,
"hhhh kedai kawas kyale ya Anwar d'inan,yanzu duk abunda za ya fada cikin santi ne"
Ramlat ta fada tana dariya itama.
Ina jinsu ko kala bance musu ba sai ma mai da hankalina kan firar da mukeyi da mama nayi.
Tara saura su mama suka wuce tana jadda damana cewa tana dibin zuwan mu wani sati,idan
kuma muka kuskura ba mu je ba hmmm mu da itane.
Bappa ya bawa mama wani abu cikin kud'insa taki karba sai da ya nuna b'acin ransa sannan
takarb'a tana kara jin son d'an uwan nata aranta.
Inna Saude kuwa d'aki tayi shigewarta don wai kar su ma yi tunanin ta bada wani abu a cikin
kud'inta(😂).
Bayan mun dawo daga rakiyar su Ramlat Naje d'akin bappa na kara taya shi murna da sanya
alkhairi,nan Salmat ta iskeni muka ci gaba da fira kafin bappa ya samu muyi alwala mu kwanta.
Aysha Kuwa sanadiyyar kukan da tasha ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani,sai da takira
k'awarta Dr.Rabi'atu tazo gida ta duba ta tare da rubuta mata magani.layin y'an aiki takira ta ba da
takardar a siyo mata maganin a *A.M.A PHARMACY* .
"Soyayyar haydar"
"dama na sani,labarin gixo ba ya wuce na k'ok'i,wai miyasa baza ki hakura da shi bane k'awata"
"ko na so yin hakan zuciyata ba zata iya ba,soyayyar A.M a jinina take"
"kinsan Allah idan ba ki rage sa tunaninsa a zuciyarki ba zai iya kawo miki wata matsala,haba
Aysha,kamar ba likita kike ba ki rage plsss ko don lafiyarki"
"naji,ki bari gobe za muyi maganar a asibiti,yanzu bana son yawan magana"
"ok bye"
Bayan tafiyar Dr.Rabi Ba da jimawa ba aka kawo mata maganin tasha sannan ta samu ta kwanta
domin a kwai maganin sa bacci a ciki.
*_ALIYU_*
Sai wuraren 11 ya farka daga baccin da yayi nasarar sace shi,wanka yayi sannan ya shirya cikin
kananan kaya kyawunsa da gwarjinin sa suka kara fitowa turarensa na imperial majesty ya ma
jikinsa wanka da shi sannan ya nufo main palo.
A shirye ya iske dining table d'in abunda ya manta yaushe rabon da ya gani,zaunawa ya yi tare
da sarving d'in kansa.
Bayan ya kammala ya zauna saman kujera yana aiki acikin system nasa tare da kallon
news,misalin sha biyu karar takalminta ya k'arad'e palon tare da kamshin turarenta,bai dago ba
yaci gaba da abunda ya keyi,kusa da shi tazo ta zauna tare da sumbatarsa a kumatunsa tana cewa,
Kansa kawai ya daga mata ba tare da yace mata komi ba,mike wa tayi taje dining area ta
zauna,sarving d'in kanta tayi sannan ta fara cin abincin,sanye take cikin mini siket wanda bai kai
guiwar ta ba da riga bakin ta iya cibiyarta ba hulla a kanta tayi parking kanta wanda ba kitso sai
uban gyaran da yasha.
Bayan ta kammala cin abincin ne ta wuce part d'inta.bada jimawa ba ta fito sanye da shadda
gezner blue wacce aka yi mata dinkin buba tare da kwalliyar zare pink,ta yane kanta da mayafi
chingom ga madubi ta saka wanda ya kara k'awata fuskarta,ta sanya takalmi masu kafurin tsini su
ma chingom,iya kar haduwa Suhailat ta hadu.
Takon ta take yi cike da yanga jakarta na hannunta sai kamshi ke tashi daga jikinta,tana kawo
daidai inda haydar yake ta cire madubinta tare karasawa inda yake zaune bisa kujerar mai zaman
mutum uku,a yanzu ba aiki yake a system d'insa ba,ya jingina kansa da kujerar idanunsa a lumshe
amma ras yake kallonta ba tare da ta sani ba,sumbatar sa da tayi a kumatunsa baki daya a ko wane
gefe yasaka shi buda idanuwansa ras cikin nata,murmushi ta sakar masa sannan ta d'aga tana sa
madubinta tayi waving d'insa tana cewa ,
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
💫💫
*ARUMAI WRITERS SSOCIATION*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
*💫(..)💫*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh
_Assalamu Alaikum masoya littafin wasu matan barkan mu da dawowa hutun sallah dafatan anyi
sallah lafiya, naji korafe -korafen ku da dama game da rashin samun update bayan sallah, ina mai
baku hakuri wani uxirune ya rike ni amma inshaallah zan kokarta na dinga typing ko da sau biyu
ne a sati.Inshaallah idan komi ya dai-dai ta zan cigaba da typing kamar da.Na gode da kulawar ku
a gareni Son So Fisabillilah❤️❤️❤️_
*Page* 45~~46
Bai ce mata uffan ba sannan bai yi yunkurin dakatbar da ita ba illa sake lumshe idanunsa da ya yi
yana tunanin halayen Suhailat Da rayuwa Aurensu.
Kamar jiya haka ya yini cikin gidan yana aiki a system d'insa salla kawai ke fitar dashi,sai
misalin karfe biyar Suhailat Ta dawo gidan;lokacin da ta shigo yana dakin karatunsa.
Ana kiran sallar magrib ya sauko daga sama domin zuwa masjid,zaune ya tarar da ita sanye da
k'ana nan k'aya ta saka earphone tana shan waka tare da kallon abu a Instagram,har ya gitta ta ya
dawo.
Cikin muryarsa mai amo yace mata,
"hello"
bata lura da shi ba kawai sai jin saukar lallausan y'an yatsunsa tayi a kunnenta ya zare earphone
din.Dago idanunta tayi ta na kallansa tare da d'aga masa gira daya(ya dai)da idanunsa ya yi mata
in kiya yana duba agogonsa.
Agogon da ke sanye ga hannunta ta duba sannan ta dubesa tace ,
"ok"
tana narkar da idanuwanta cikin nasa lumshe idanuwansa yayi tare da mika mata abunda ya cire
mata yana mata gargadin kar ya dawo ya cin mata nan, sannan ya yi ficewarsa.
Turo lips d'inta tayi ,chan kasan makoshinta tace,
"tou"
domin ta fahimci sakon da idanuwansa suka isar mata ba tare da ya furta ba.
Tasan halinsa sarai shiyasa ta mike tayi sashen ta,har a ranta bata son takura amma A.M ya
kasa fuskantar hakan.
Palon ta ya hadu iya kar haduwa.Ba'a ma maganar bedroom komi ya yi,duk wanda ya shigo
sashen Suhailat Yasan cewa y'ar gata ce kuma naira ta koka a wannan wurin.Misilta muku yadda
part dinta yake b'ata lokacin,iya abunda nasani shine tabass ya hadu sosai.
Alwala tayi sannan ta shinfida carpet ta kabbarta sallah.
Sai bayan isha'i ya shigo gidan,bayan yayi shirin baccinsa coffee kawai ya hada a kitchen dake
nan part dinsa ya zauna bisa gadonsa yana kurba yana waya da Ammiensa.
Na tashi ciki farinciki a wannan ranar,hakan kuma baya rasa nasaba da abun Alkhairin da riske mu
a jiya,ko a karin kumallon mu (breakfast)na yau da banbanci domin Inna Saude Mai bakin cin
d'adi (inji Salmat)ta siyo muna abun karin kumallo mai rai da lafiya,harda kawai ta bada a tsoyo
mata.
Ga ba daya mun sha'afa da batun zuwa boko,gashi jiya ko islamiya ba muje ba.
********
Da sauki ta tashi yau domin rashin kwarin jiki ne kawai ke damunta amma ta d'aure ta shirya
domin tana muradin ganin rabin ranta.
Bayan ta kammala karin kumallonta ( breakfast)a nan sashenta ta wuce sashen momynta amma
kash ko da ta shiga bata riske ta ba.Motar ta kawai ta shiga tare da wucewa Asibiti(Hospital)
domin ta zaku tayi tozali da rabin rayuwarta HAYDAR.
********
Bata jima cikin baccin ba Kabir Ya kwan-kwasa mata kofa wanda yasa sai da tafarka gashi dama
bacci ba wani nisa yayi ba sosai.
Rasa abunda zata ce masa tayi domin imani yawa yayi mata kuma kalmomi suka mata karanci,
tsaki kawai ne ya samu muhallin fitowa daga bakin ta ba tare da ta shirya ba.
********
Jin ya kwan-kwasa mata ba amsa ya sashi kutsa kansa cikin dakin.Dai dai da shigowarshi tsakin ta
ya dira a kunnuwanshi,baisan lokacin da ya juya ba,hakan kawai yaji zafin abinda tayi masa,gashi
har yana neman rasa jam'i saboda ita aransa yake kara mamakin hallinta batasan darajar wanda ya
halicce taba balle ma shi mijinta.Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kutsa kanshi cikin
massalacin.
********
Mikewa tayi ta shiga ban d'aki(bathroom)ta watsa ruwa domin jikinta ya saki sannan tayi brush
tare da Alwala,tsaye tayi tana duban kanta acikin madubi,duk ta rame dare daya tak kamar ba
maryama ba,zuciyarta zafi take mata kuma har yanzu bata jinta dai-dai,fitowa tayi ta kabbarta
sallah yayin da yin sallar kawai take amma batasan mi take karantawa ba balle tasan raka'a nawa
tayi,zuciyarta sai tunzurata take kan kar ta ragawa kabir,a da ta dauki zabi daya cikin zabin da
mahaifiyarta ta bata amma a yanzun bata jin zata aikata daya acikin su dole kabir yasan wacece
MARYAMA In ma yasani mantawa ne yayi to ya tuna,
sai da ta gaji dan kanta ta sallame sallar zuciyarta fal tunani.
********
Gaba daya ya gama tafiya da da imaninta har hasaso kanta take tare dashi suna tafiya a jere cikin
farinciki,kallonsa take ta kasa dauke idanunta a kansa duk da kwarjininsa da ya cika mata
idanuwa.Matsayi DR.ALIYU MUHAMMAD AHMAD Daban yake a zuciyarta baza ta iya hakura
dashi ba,ga ba d'aya ta fita daga duniyar mutane ta afka duniyar SOYAYYA ba ta ankara ba sai ji
tayi ya gifta ta gefenta ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba sai zazzakar muryarsa take ji dake
amsa amo a cikin kunnuwanta yana amsa gaisuwar sauran Doctor's da ke gaba da ita kadan.
********
Office d'insa ya shiga yana k'ara hade rai,shifa duniya ya tsani mutum mai shegen kallon tsiya
amma Aysha Ta ki fahimtar hakan,shin wannan abun da take shi zai sa ya SO ta komi,
"mssstwwss"
yaja tsaki,dariya yaji an kwashe masa da ita,dago kyawawan idanuwansa yayi ya sauke su kan
Dr.Abdallah Dake cikin office d'in.
Gaba daya shi sam bai lura dashi ba har ya iso tsakiyar office din,saurin d'auke idanunsa
Dr.Abdallah Yayi domin kwarjinin da Dr.HAYDAR Ke masa amma hakan baisa ya tsagaita da
dariyar da yake ba,share shi haydar yayi yaje kan kujerar sa ya zauna ba tare da yace masa komi
ba sai da Dr.Abdallah Ya gaji don kansa yayi shiru sannan ya dubi A.M Yace..
*******
Bayan mun yiwa Baffa Allah ya tsare domin ya fita kasuwa yana son yau ya zuba abubuwan da ya
dace ya saida a shagonsa.
Misalin sha biyu na rana da wasu mituna muna zaune ni da salmat muna cin dambun shinkafa da
zogale wanda shine yau na dafa matsayin abincin rana, muka jiyo muryar Inna Saude dake chan
nesa damu tana shan sauti a redionta tana kwalawa Salmat Kira, mikewa Salmat tayi tana cewa,
"lfy lumi.... dama batun kudin ku ne da nace kibawa mai tsada(Agla)ta ajiye,karbo mini s.........
Bata ida zancen ta ba Salmat Ta waro idanunta waje tare da hadiye dambun dake cikin bakinta
batare da ta shirya ba haka ya yi sanadiyar sarke ta, ta rika tari ba kakkautawa.
Zeesardauner ce
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
💫💫
*ARUMAI WRITERS SSOCIATION*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
*💫(..)💫*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh
*Page* 47~~48
"subhanallah lafiya dai salamatu mi ya sameki"
Dakyar tarin ya tsagaita amma ta d'an ji jiki.Na taso da sauri tare da mi kawa Salmat Ruwa tasha.
Tunani kawai Salmat Keyi yadda za su kaya da Inna,tana cikin wannan tunanin ne Inna Saude
Ta nisa da niyar yin magana Salmat ta rike kanta tana layi,duk sai Inna Saude Ta rud'e domin bata
son abinda zai taba Agla Balle Salamatun Ta duk sai tabi ta rikice.Ni Aleeya Diyar Muhammadu
jikanyar Yusuf na tsaya kallon ikon Allah,idan na kalli Salmat muka hada ido sai ta kyafta min ido
tare da kashe min daya idan na kalli Inna Sai ta bani tautsayi sai tambayar Salmat Take ko bata da
lafiya ne?ita kuwa sai kara langwabewa take ala dole ga marar lafiya.
Daki Inna Ta kai Salmat tare da kwantar da ita bisa yaloluwar katifar mu tana tofa mata Addu'a
domin ce mata Salmat tayi kanta ke ciwo kuma ta lafe kamar marar lafiyar gaske.
tana kwashewa da dariya,kafin nayi magana Inna Ta nufo dakin aiko kamar walkiya na nemi
Salmat Na rasa.
A chan saman katifar mu na hangeta sai zuba nishi take a hankali,bayan Inna Ta shigo Salmat
Ta daga kai ta kalleta sannan a hankali,
"tou Innata"
Kallon Salmat Nake amma bansan lokacin da takawo kusa dani ba tana cewa a hankali don kar
Inna taji,
Komi bance mata ba na tsureta da idanu alamun tambaya,sai turo baki tayi sannan tace,
"wai fa kan batun kudin mu ne fa Adda Shine take son in bata shiyasa kika ga nayi wannan abun
fa"
kallon mamaki na ke yi mata domin ni a sanina nace ta kaiwa Inna kudin gudun jidalinta amma ita
da kanta tace mu bawa baffa ya ajiya, to mi hakan ke nufi?
"bara na koma gurina Inna ta kusan dawowa amma don Allah ki dauko min sauran danbun mu
yasin ban koshi ba Inna Ta kirani kinji Addana"
dariya maganar ta ta bani amma sai na yi murmshi na mike domin kuwa ta narki dambu d'azu
amma ta ke cewa wai bata koshi ba,ita kuma ta koma gurinta.
Ina fita Inna na shigowa ta mikawa Salmat Maganin sannan ta debo mata ruwa ta mika mata,ko
da na shigo zata shan maganin na tsaya ina kallonta ina mamakin halin Salmat,yanzu haka kawai
zata shan magani alhali lafiyarta lumi;a duniya ni da nasha magani nafison allura domin sam Allah
bai hada jinina da magani ba, amma ita shan abunta take hankali kwance.
Bayan Inna Ta fita na mika mata dambu taci iya cinta ta kora da ruwa ta kwanta.
Inna Saude Na dakinta tana jimamin rashin lafiyar y'arta ta tuno da maganar kud'in kuma suna
hannun Agla sai ta mike ta nufi d'akinsu.
******
Bayan y'an mintukka Inna Ta sake shigowa da Sallama na amsa mata,ta dube ni da niyar yimin
magana,
"umm Aleeya"
na dubeta na ce,
"na'am inna"
har zata ce wani abu charaf Salmat Da farkawarta kenan tayi y'ar k'ara da tasa hankalin Inna ya
dauku gare ta kila maganar kud'in ne Inna zatayi komi ohho.
Fasa maganar Inna Tayi tayo kan Salmat Din tana tambayar lafiya kuma.
"tou kwanta kinji da kinyi barci kin samu hutu kan naki zai daina sara miki "
"tou Innata amma kema kije ki kwanta kinsan baki ida walwalewa ba daga rashin lafiyarki kina
bukatar hutu kema"
Kiran sallar Azzahar ya tada ni,na fita nayi alwala na tada Salmat Dakyar saboda nauyin baccinta
mukayi sallah bayan mun idar ta koma baccinta ni kuwa na tsaya di ba karatuna na islamiya,sai da
uku tayi sannan nafita domin d'aura girkin dare;yau tuwo da miyar zogale Inna tace ayi.
Tuwon shinkafar na fara daurawa bayan nayi la'asar na daura miyar zogale,yau kam sai da na
samo yaro yamun chefane domin Salmat Inna tace ba zataje ba bata da lafiya nidai ban tanka mata
ba domin hakikanin gaskiyarta ne Salmat Bata da lafiya.
Lokacin zuwa Islamiya ya yi nace salmat ta shirya Inna tace atafir ba inda Salmat zataje hakan ba
ta da lafiya dakyar Salmat ta shawo kanta a y'ar da taje badon ta so ba.
********
Banyan mun fito waje muna tafiya Salmat ke fadin,
"yasin Inna ta so ta ballomin august yanxu haka bansan hukuncin da zan taras ba na rashin zuwan
mu jiya yau take son kara min wani tab"
"ai wallahi na so ta hanaki zuwa yau idan kika tafi gobe a chaskalaki tunda ni bansan lokacin da
kika koma y'ar wasan kwaikwayo ba kuma karya ba ta miki wuya"
bata rai Salmat tayi, dai-dai nan muka cinma su Amina Da bilkeesu muka ci gaba tafiya.
" chab waya isa ya chaskala Salamatun Inna Saude Da Baffa kanwa ga Dr.Aleeya ya zauna lafiya"
tafada cikin murmushi,Abokiyar shiriritarta Bilkeesu ta chabe da cewa,
"ai duk wanda ya taba Salamatun Inna Saude yasan mi ya tabowa kansa"
duk dariya muka yi yayin da muka cigaba da tafiya muna sauraren hirarsu har muka isa
makaranta.
********
"Ya dai Likita bokan turai wa ya tabo mana kai da sassafiyar nan haka ?
ya fada cikin sigar zolaya,ko kala A.M baice masa ba sai ya sake cewa,
"ko mutuniyar ka ce don naga tun d'azu take sintirin nemank..... "harara Dr.A.M ya watsa masa
amma sai ya nuna kamar bai gani ba yace ,
ya fada yana kumshe dariyar da taxo masa ganin yadda yanayin A.M ya sauya nan ta ke.
"kasan Allah idan zacenta zakayi zaka barmin office dina ka koma naka kayi shirmenka.. haba
mutum sai shegen surutun tsiya"
"sorry nawan abun bai kai haka ba daga magana haba mijin Suhailat Angon Aisha Miye na saurin
daukar zafi "
Bugu Dr.A.M Ya kaiwa Dr.Abdull Ya samu ya kauce yana dariya.Sai 2:00pm haydar ya fita daga
Asibitin,Center plus a biya yayi Take-away sannan ya wuce Company.
********
Ta jima sosai a wurin saida Dr.Rabi'atu tazo ta ja hannunta sannan ta iya dagawa da ga gurin da
take tana jiran zuwansa amma ya mata haka dakyar take tafia kafafunta sunyi mata nauyi
Zuciyarta tayi mata zafi kamar ta fashe,sai a office din Dr.Aysha suka yad'a zango.
*_Zeesardaunerh ce_*
# _comment_
# _like_
# _share_
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
*💫(..)💫*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Page* 49~~50
"Wai mike damun ki ne Aysha?haba dan Allah kina son jawo mana raini a Asibitin nan wannan
wallahi,kinga yadda sauran likitoci da nurses maza da mata ke kallonki?&
kaf cikin Asibitin nan waye baisan soyayyar da kike yiwa Dr Aliyu Muhammad Ahmad ba"
"abun da nake son ki fuskanta Aishert shine wannan abun da ki keyi fa shine news din dake
yawo a cikin Asibitinnan, samari da dama suna farin cikin hakan saboda wulakancin da kike musu
gashi kuma wanda kike yi kansa ya nuna baisan kina yi ba"
"ni fa wannan ba ya damu na Rabi'at in har A.M Zai karbi soyayyata, ki duba fa saboda shine na
dawo wannan kasar,saboda shine na dawo sokoto saboda shine na nemi aiki a wannan Asibitin
amma duk da hakan ban chanci ya soni ba ?
Tautsayin ta duk ya cika Dr.Rab'iat ta ma rasa abinda zata ce mata domin ta sanyaya mata
zuciya,ta lura cikin bacin rai take a yanxu.
Sautin ne ya fara tashi a jakar Aisha,hannu Dr.Rabi'at Tasa ta dauko wayar ta mi kawa Aysha.
Ba tare da ta duba no din ba tasa hannu ta kashe kiran(rejecting),sake kira akayi ta share wayar
har ta sinke amma duk da hakan mai kiran bai hakura ba ya sake kira.
Daukar wayar tayi a hasale domin wannan mai kiran ya takura mata budar bakin ta bayan ta
aza wayar a kunnenta sai cewa tayi,
"wai wani irin rashin hankali ne ake damun mutum da kira ko na gayama ina bukatar hakan ne
nonsense msstwwwssss"
ta yanke kiran ba tare da ta saurari ko wanene ba.
"kin gani ko wannan yana cikin abinda yasa ki ka kasa samun Hydar"
"ba maganar bacin rai bane kawai gaskiyace, ki gyara ko da Allah zai taimakeki.
" sannan ki cigaba da addu'a ki rage damuwa da tunaninsa a ranki idan ba haka ba hawan jini zai
samiki wallahi"
"naji
"a'a alamunki ne suka nuna hakan!kinga ni na tafi na duba maras lafiya sai anjima "
Dr Rabi'atu Ta fada tana ficewa daga office din ya yin da Ayshert ta zurfafa a tunanin rabin
rayuwarta.
Da kyar ta dan yi wani aiki yau a office din domin rayuwarta bata yi mata d'adi,agogon hannunta
ta kalla lokacin tashin Dr.A.M ya kusa kuma tana bukatar sanyashi a idonta kafin ya tafi domin
hakan zai saukaka mata radadin da take ji.Saura minti biyar ya wuce ta fito daga office d'inta
domin ta jira isowarshi amma kash tana bisa hanya Dr.Jameela ta tsaida ita da magana ko da ta isa
har ya wuce(amma djameela kin iya bakin ciki🤣)
Itama motarta ta shiga ta figeta da gudu domin bataga amfanin zamanta a Asibitin ba.
*********
Bayan mun taso daga islamiyya muka ci abinci Salmat Ta masa sai munje mun kwantaba yadda
banyi da ita ba amma taki,domin naso ne mujira baffa da ya fita,wani makocinmu ne ba ya da
lafiya shine suka tafi kaishi Asibiti yanzu.
Alwala nasa ta yi nima na yi tare da yiwa Inna saida safe muka shiga dakin mu itama Inna ta
shiga nata.
Bayan kamar minti ar'ba'in da kwanciyar mu Salmat Ta fasa kara wacce tasa na farka dama
bana da nauyin bacci.
Ihu kawai Salmat ke yi da gudu Inna Saude ta fito daga d'akinta ta yo namu ko da shigo ina
tambayar Salmat Lafiya amma ta ki magana sai ihu take zabgawa.
Gunta Inna ma tayi itama tana tambayarta,
ina Salmat Baki yaki yin shiru.jijjigata Inna Saude Ta rinka yi tana cewa,
zaro idanuwa nida Inna mu ka yi har muna hada baki wurin cewa,
"b'a..mi?"
"b'arawo"
Salmat Ta idar mana.
"eh Inna na ganshi da idanuna ya dauki kudinmu wandanda kikace Adda Agla ta ajiye,muna hada
ido ya ari na kare"
"kud'i fa ki ka ce Salamatu?"
"eh wallashi Inna na ganshi idanuwana muna hada ido ya sheka,Inna yi sauri mu duba shi kar ya
tsere"
Salmat ta fadi haka tana arcewa ganin kallon da Aleeya ke jifanta dashi ya yin da Inna Saude Iya
gaskiyarta ta yarda da batun autar ta.
"inna ki cewa Adda ta fito itama mu duba tare tun bai fita ba"
tafada cikin tsauri da muryar tsoro,aiko inna ta koma cikin dakin da hanzarinta harda bugewa ta
yi da kanta.
Salmat kuwa ganin Inna Ta shiga dakin su sai taci taya sai dakin Inna ya yin ta kwaso kud'i ta
watsa wasu a kasa, irin barawo ya shigo dauka abu yaga za'a kama shi ya yarda ya yi ta kansa.
A saba'in ta fito dakin Inna Sauden ya yin da ta shiga ya da duk kyallen da taci karo dashi ga
yagiyar shanya.
*******
Sannu nake wa inna amma fada ta ke min wai,
"na taho na zauna ko ajikina kamar ba barawo naji ance ba kenan ko bindiga gareshi in ya harbesu
ba ruwana ina d'aka zaune ban ma san anyi ba"
ko kala bance mata ba face hakurin da na ke bata, domin nasan duk wannan shirin na Salmat
ne,tunda ta fara maganar kud'i nasan karyace kuma na lua da rantsuwar karyar da tayi dazu wai
wallashi "hmm" sai naci kaniyar yarinyar nan take hankali.
Kaf gidan mu zagayeshi ba mu ga kowa ba ya yin da duk inda muka bi sai Salmat ta yarda duk
abunda ta gani.
Hankalin inna fa duk ya tashi da kyar muke lallashinta har ta hakura da bid'ar barawon ya yin sai
debewa barawo albarka take Salmat na kama mata.
_Manage please inshallah ranar monday zanyi mai yawa sai kun gaji da karatu_ 😊
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*⚜️©J.A.W*
*PAGE*51~~52
Muna shiga cikin dakin da kud'i muka fara cin karo dasu kan hanya aiko salmat ta wage baki tana
rafka salati da kalima inn ta dauko daga farko kafin ta ida ta dauko,
"da d'a shikenan Inna,ashe kema ranar zakka tayi? tunda har barawo ya shigo dakin ki,yanzufa
shikenan ya kumushe miki kudin da duk ke gare ki da wadanda kike boyewa?da d'a inna kam sai
hakuri amma barawon ya gama damu.."
" amma da saura inna tunda gashi ke ya ragamiki wasu a kasa mukuma da bayaso ga badaya ya
kundume su"
Durkusawa muka nayi ina bata baki ganin gabadaya takai matakin da ko magana ta kasa yi ,domin
wannan abun yasata cikin wani yanayi,hakuri na dinga bata ina mata kalamai masu sanyi har
muka samu ta d'an dawo daidai.
Ita Salmat Dariya abun ya bata domin ganin yadda innarta tayi zaman y'an bori sai baki agla ke
bata.
Ta buda baki da niyar magana domin ta kara zautar da inna na katse cikin kakkausar murya ina
cewa,
"kinsan Allah wallahi kina cewa tak wurin nan sai na baki mamaki"
gum tayi da bakinta amma dariya sai son kubce mata take yi,harara na ballamata tayi saurin
hadiye dariyar.
munkai tsawon minti goma kafin inna ta dafa gina ta mike tana tattara kud'in ta ba tare da tace
mana kanzil ba,sai da ta hada kudinta wadanda ke a yashe kasa da wadanda ke hankadin katifa da
barawo (salamutu bata tab'a😂)kuma ta bincika ba'a dauki komi na taba sannan ta sauke
nauyayyar ajiyar zuciya tana cewa,
"wai Alhamdulilah,Allah na gode ma ka rudar da wannan dan iskan barawo ya kasa daukar kudina
"
"ai kuma inna kin yi b'anna,keda ke godewa Allah kuma kina zagin bawanai ? Addu'a ya dace kiyi
masa domin nuna godiyarki ga Allah kinga ko makaranta ana gayamana cewa zagin musulmi
fasikanci ne ...."
"eh"
"to ke ina naki ?"
"gasu"
"to don haka kibar zaginsa kar ya zamana yana da aljannu ya biyo dare ya sace kudin ki ba
ruwana, nidai nawa dana Adda ya dauka mun yafe masa domin guziri ne ya yi mana a Aljanna, ba
abunda zance face Allah ya yiwa wannan barawon Albarka"
"Nikam bazance Allah ya yi masa Albarka ba amma ko don kudina da bai dauki ko nera ba nace
Allah ya shiryar dashi "
"in banda wani abu da nayiwa barawon nan Allah ya isa wlh amma dai na yafe"
"saninsa kinka yi da zaki ce ya gode,banason har kar shashanci fa karkisa nace ban yafe ba"
"a'a miya yi zafi shi ba wuta ba,kwantar da hankalinki hajiya saude matar baffa inshallah an bar
wannan batu"
tun fara maganar su bance kala ba sai da na sun gama nace Salmat ta taso muje mu kwanta amma
sai ta kalleni ta sheke da dariya tana cewa,
"wa?Ni?rufan asiri nikam yau dakin inna zan kwana haka kawai naje dakin mu ki chaskalani
hhhhh haryanzu da wayona yaseen"
dariya zancenta ya bani har dai ciki sigar da tayi magana amma sai na kara hade rai domin taban
haushi da daren nan wallahi.
muryar inna naji tana cewa,
tafada tana lullube kafafunta da abun rufa.Ba yadda inna batayi da ita ba ta bini mukwana amma
sai cewa tayi kanku akeji domin kadar fillow ta diba ta toshe kunnuwanta da su ta juya mana baya
ala dole bacci take.
Saida safe na yiwa inna sannan na sake Alwala na shige dakin mu bayan nayi azkhar na kwanta.
********
Bangaren Aliyu kuwa sai da ya kammala cike-ciken da zai yi a companyn sannan ya koma gida.
********
Da safe ya fito cikin shirin tafiya yana sanye da boyel yard ruwan kwai wnda ya yi mugun yi
masa kyau hular kansa,takalmi da agogonsa ko su kansu kawai abun kallone.Breakfast ya zauna
ya na yi bai jima da zama ba suhailat ta fito daga part d'inta sanye take da wata tsadaddiyar atamfa
da ake ya yi a yanzu mai zaiba anyi mata dinkin wata arniyar riga doguwa duk anci mutuncin
atamfar amma kuma dinkin ya yi kyau sosai tana rataye da jakar hannu.gefen sa taje tare da basa
morning kiss a kome gefe na kumatunsa tana cewa,
Bayan sun kammala karin kumallon (breakfast) yasa tayi masa kiran inna Hasiya,
"wace ce haka?"
"dara daran idanuwansa y dago ya sauke mata su yana mata kallon kin rena ni"
"nifa babe bana son irin wannan kallon tambayar ka fa nayi amma kabi duk ka tsareni da
wad'annan idanu naka"
"opps ka ga na ma mant da ita wallahi,da yake ban cika zama gidan ba kuma bantaba haduwa da
ita ba always tana cikin (room)d'akinta.
"ta ya zaki tuna da ita,ko da yaushe kina out baki zama gida"
ya fada yana tab'e lips d'insa
Tana isa d'akin ta tura kofar, zaune ta riske ta tana jan wani jan wani abu da batasan sunanshi ba
(tasbaha)ta tunani.
biyo bayanta Inna Hasiya Tayi ba tare da ta fahimci wa take nufi ba.
Bayan sun fita waje inna Hasiya ta durkusa ta gaida Aliyu ya amsa yana tambayarta ya aiki,kud'i
ya mika mata sannan ya yi mata bayanin cewa tafiya zaiyi wacce zaya jima sosai godiya ta dinga
yi tana msa addu'a da fatan alkhari sai da yace ta bari hakanan.
D'akinta ta koma ra harhada ko matsanta ta fito ko da tazo yana sallamar ma'aikata maza sai da
ya sallame kowa suna ta masa addu'a sannan duk muka fita shi kuma ya shiga mota shida Suhailat
Suka wuce mun daga masu hannu mai gadi kawai aka bari shida y'ay'ansa masu kula da
compound da shufke shufke.
A airport driver ya sauke su sannan ya juya,basu jima ba aka fara kiran passenger's suka shiga
sai birnin tarayya wato ABUJA.
*_A SAUKA LAFIYA MIJIN SUHAILAT_*
( _amma akwai kura ka yi tafiya batare da sanin Ayshert ba_)
********
Bari mu waiwayi Maryama
Yadda tace haka take aiwatarwa domin sabon shafin rashin mutunci ta bud'e a gidan Kabir na
lura da ita amma sai ya ba banza ajiyar ta iskanci kala-kala take masa duk ya share ta wani lokaci
bar mata gidan yake ya tafi gidansu su sha fira da kannensa da mahaifiyarsa cikin farin ciki kala
Dije wato gwaggon su kabeer tana kai munafunci wurin Maryama har aka kai ga Maryama taci
matamutunci tsaf sannan ta kama bakinta tayi shiru duk da bata sob ganin farincikin mutanen
gidan.
*WANE NE KABEER.........*
*Zeesardaunerh ce*
( ~Y'ar karamar su babbar~ ~su~👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
Page 53~~54
WANE NE KABEER.............
Alhaji Sa'id Ibrahim Shine mahaifinsa sai Hajiya Aisha Mahaifiyarsa hausa fulani ne su,
wurno local goverment channe kauyensu;achan Alhaji Said ya yi primary da secondry d'insa
bayan result dinsa ya fito kuma ya yi kyau sosai sai kanen mahaifinsa Abba Lurwanu dake aiki
anan birni yasa ma masa Admission a *Sokoto State University* inda ya karanci pharmacy. Ya
nada abukkai da dama wad'anda suke karatu a tare wata rana suka tafi gidan abokinsa Bashar
shida sauran abokanan su achan ne yaga kanwarsa Aisha.
Tun ranar da ya dora idanunsa kan Aisha yaji yana sonta so mai zafi gashi ya rasa hanyar da zai
sake zuwa gidan,ana cikin haka bashar ya yi rashin lafiya har ta kai saida aka kwantar dashi
Asibiti.Ciwo ba d'adi domin Said baiji d'adin rashin lafiyar abokinsa ba amma kuma sai wannan
rashin lafiyar tazama alkhairi ta wannan hanyar yasamu ya kulla soyayya da Aisha,kullum yana
Asibiti da sunan jinya yana soye wa da sahibarsa.
maganar soyayyar su tayi nisa har manya suka shigo ciki ya yin da Abba Lurwanu ya wakilci
mahaifin Said wato Alhaji Ibrahim inda aka tsaida magana kan cewa in ta kammala jarabawar
SSCE sai ayi auren.
Cikin ikon Allah takammala jarabawa lafiya akasha buki inda aka kai amaryar anan shiyar da
kanen mahaifinsa ya tsaya masa gida a Runjin sambo.
Kabeer shine d'ansu na farko sai Fatima da Batul twins tun daga haka Allah bai kara basu
haihuwa ba yanzu haka Batul da Fatima suna rubuta WAEC da NECO ne ya yinda kabeer ya yi
karatun Pharmacy kamar mahaifinsa inda ya cigaba da kula masa da chemist dinsa kuma yana
karatun computer.
Kabeer yana soyayya da wata yarinya a nan shiyarsu mai suna Asma'u suna matukar son
junansu sosai har iyayen Kabeer sun san da maganar itama Asma'u gidansu sun san da maganar
ana batun kai sadaki gidan su Asma'u rana tsaka kabeer ya haukace musu cikin gida shi baya sonta
akwai wacce yake so tun iyayen sa na daukar abun wasa har suka sawa sarautar Allah ido domin
har gida kabeer yaje ya yiwa Asma'u cin mutunci kuma yace mata baya sonta ya tsaneta a take a
wurin Asma'u ta sume amma ko ajikinsa.An kai ruwa rana kan wannan batun domin mahaifansa
sun dau zafi kan abunda ya yiwa yarinyar mutane kafin aka zauna tsakanin iyayensa da na Asma'u
da shi da kuma Asma'u ya kara tabbatar musu baya sonta kuma ko andaura sai ya saketa domin
iyayensa cewa sukayi aure ba fashi.
cikin kuka Asma'u ke tambayarsa mi tayi masa ya yi mata haka mi yasa ya yaudari zuciyarta
sai da ta ba kowa tausayi amma shi ko ajikinshi,taci gaba da tambayarshi wacce yake so mi ta fita
dashi ?yace bata fiki da komi ba kinma santa bakowa bace face kawarki *Maryama* cikin razana
da kaduwa tace,
"maryam.."
bata ida ba a wurin ta suma saida aka yayyafa mata ruwa ta farfado maganganu take tayi tanal
cewa mahaifin Kabeer Abba na hakura da shi in nice baya so amma don Allah ku ceci rayuwarsa
kar ku aura masa maryama Wallahi ba yarinyar kwarai bace zata raba ku da danku ko a yanzu na
san ba cikin hankalinsa yake ba da bazai min haka ba Abba duk tabi ta rikice dakyar mamanta taja
ta yi daki da ita domin itama da ganinta kasan ba a hayyacinta take ba tana cewa,
"haba dama biri ya yi kama da mutum ni tunda naga Maryama ta like min mama nace miki ba
alkharine tazo dashi ba ki kace na kyaleta kila ta chanza kinga abun tayi min ko mama"
"kingani ko mama Kabeer ba'a hayyacinsa yake ba akwai abunda tayi masa nasan kabeer bazaimin
haka ba yana sona sosai don Allah mama ku karya Asirin da ta masa kinji mamana"
sai da aka bata maganin kwana sannan bacci ya dauketa tana yi tana kiran kabeer acikin
mafarkinta.
Bayan su Asma'u sun fita Abban Asma'u ya ba baban Kabeer hakuri amma tunda kabeer yace ba
yason Asma'u don haka bazai bada diyarsa ga wanda baya sonta ba don Allah su yi hakuri su
barshi ya aure wacce ya ke so.
Haka iyayen Kabeer suka koma batare da jindain hana su auren Asma'u da akayi ba musamman
Ummu Aisha mahaifiyar Kabeer domin ko wace mace tana burin samun suruka kamar Asma'u.
Kalaman Asma'u na nan cikin kan Ummu ya yin da Abba ya dauke su shirme kuma ya yi bincike
kan Maryama mahaifinta ba ya da matsala sai dai mahaifiyarta ce mai matsala sannan ko yarinyar
ance bata da mutunci shiyasa ya watsar da zancen Kabeer na son aurenta ya yin da Umma ke yiwa
d'anta addu'a amma kamar ta azzara abun ake domin ko wace safiya son Maryama kara hauhawa
yake a zuciyarsa ya yin da ko da yaushe yana gidansu Maryama.
Abunda Allah ya kaddara ba fashi domin dakyar akai auren Kabeer da Maryama ba tare da
danginsa na so ba sai don babu yadda zasu yi Alokacin.
Bayan aure suka dawo tunanin ya akayi suka yarda da wannan auren bayan sun san halin
yarinyar dana mahaifiyarta amma ba amsa domin sun kasa tunawa.
Abu ya zame musu goma da ashirin domin maryama ta mallake musu d'a ya yin da ya manta da
Ahalinsa ba ya zuwa inda suke kuma ko sy Batul suka je chan sai Maryama tayi musu wulakanci
yana gani bazai tanka ba in suka maida martani idan ta zagesu yakmasu ya jibga son ranshi
shiyasa suka daina zuwa gidansa.Haihuwar maryama daya inda ta samu d'a namiji suka samai
suna Maleek yana chan gun mahaifiyar Maryama ita ke kula da shi baisan kakarsa ta uba ba
domin bata bari akaishi chan.
Abu guda ke gama Kabeer da maryama shine kazamta kwata-kwata ba tada tsafta bata iya gyara
dakinta bare ta gyara masa nasa gashi bata sallah sai ta ga dama ga shegen karatun littafan hausa
ya yin da in ta rika waya dakyar take dagawa ko da yaushe abu dayane karatun littafi bata
gajiya.Alokacin da taga ta mallaki Kabeer ko gardama ba ya iya yi mata duk abunda tace shikenan
sai ta sakankance da banka masa Asirin da take.
Addu'a bata faduwa kasa banza ko sau daya Ummu bata taba gajiya da yiwa d'anta Addu'a ba
haka ma Abba domin y yardashima cewa Kabeer ba'a hayyacinsa yake ba,Batul,fatima da kuma
Asma'u wacce har yanzu bata yi aure ba karaunta ta cigaba da yi suma ko da yaushe suna yi masa
Addu'a domin duk da Kabeer bai auri Asma'u ba hakan bai hanata yin zumunci da su Umma ba
hakama Mahaifiyarta da Ummu sun zama ka'waye.
Wata rana Asma'u tazo ziyara nan inda Ummu sai ga Kabeer ya shigo lokacin dai anfara samun
sauki yakan zo wani lokacin batare da sanin Maryama ba domin ba ya son bacin ranta suka gamu
da Asma'u a dakin Ummu ta gaidashi ya amsa har yana tambayar wacece ita.Abun ya basu
mamaki sosai sun dauka raina musu hankali yake sai daga baya suka fahimci cewa gabadaya ya
manta da Asma'u,ya manta ya taba yin soyayya da ita bazai iya tuna ta ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har izuwa yanzun da yadawo cikin hayyacinsa kaso sittin cikin
dari.
Inna Dije takasance kanwa ga Alhji Sa'id.
Abba Lurwanu shine mahaifinta itace yarsa ta farko mijinta ya rasu bata da d'a ko guda,
gabadaya mahaifiyarsu bata koya musu son dangin mahaifinsu ba bata kaunar Sa'id tun yana
gidansu mahaifiyarsu tace musu gani take cinye musu dukiyar mahaifi zai yi, amma yanzu da taga
Allah ya masa bud'i tazo gidan ta tare tunda bata da aure shikuma Alhji Said bazai iya korarta ba
domin mahaifinta ya gama masa komai a rayuwa.
Da taimakonta Maryama ke aikata wasu abubuwa na asirce Kabeer.
*WACE CE MARYAMA........*
*Zeesardaunerh ce*
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh
*Page* 55~~56
*WACE CE MARYAMA*...........
Maryama ta kasance y'a ta farko ga Alhji Umar Abba da hajiya Hawwa'u.Alhji Umar Abba ya yi
tashen kud'i a shekarun da suka gabata amma ko yanzu Alhmdllh za'ace.
Hajiya Hawwa itace uwar gidansa kuma amaryarsa domin ta kasa ta tsare ba wacce ta isa ta shigo
gidanta a matsayin matar Alhji Umar.
Duk halin hajiya Hawwa Maryama ta kwashe har ta zarta domin ita hajiya Hawwa tana saka
kissa a lamarinta saɓanin Maryama da komi nata direct ne,
Shiyasa Hajiya Hawwa ko a dangin mijinta bata samun matsala,tana sa Alhji Umar ya bada
kuɗaɗe da sunan danginsa zata bawa amma sai ta raba su biyu ta rike rabi ta basu rabi su kuma
suyi ta farin ciki suna samata albarka.
Aganinsu Alhaji Umar ya yi dacen mata ta gari wacce bata damu da da dukiyarsa ba mai sonsa
don Allah ga kyauta.
Ko bukata wani keda ita a familyn Alhji Umar ita ke masa hanya,duk tabi ta saye zuciyar su.
Idan lalura ta tashi familynsa zata yi abubuwa dadama ya yinda a zahiri zata nuna da kuɗin ta tayi
komi amma a baɗini shi ya bada kuɗin tabasu.
Cikin matacce Allah ke fitar da rayayye hakanne ya kasance ga Nafeesat domin sam bata yo halin
uwarta da yayarta ba.Mafi yawan lokaci tafi zama inda kakarsu Balqeesu mahaifiyar Alhji Umar
Abba,hakan ya saka dangin mahaifinta kaunarta sosai saboda kyawawan halayenta ba kamar
Maryama ba.
Asma'u da Maryama ƙawaye a makaranta amma sukan samu saɓani saboda banbancin halayya,
musamman Maryama da tarbiyyar kwarai bata isheta ba ko a makaranta bata da aiki sai soyayya
da malamai kala-kala.
Ko sun samu saɓani da exam ta matso Maryam zata fara neman shiri domin Asma'u na cikin
hazikan dalibai na wannan lokacin.
Tun lokacin da Maryama ta ɗaura idanun ta akan Kabeer taji zuciyarta ta halba sai da ta dafe saitin
zuciyarta,a lokacin suna tare da Ummanta sun biyo layin.
Taji a duniya ba wanda take so kamar sa.!domin son sa ya yi mata mugun kamu.
Ta rasa ya zatayi gashi sunyi kusan wata takwas basa magana da Asma'u ga exam ta yo kusa ga
kuma soyayyar saurayin da batama san sunansa ba.
Shiyasa Maryama ta shirya taje gidansu Asma'u ta nemi sulhu dakyar ta sauko sai da momyn
Asma'u ta tasa baki sannan, amma sam zuciyarta bata yarda da kalaman Maryama ba duk da cewa
tasan lokacin exam ya yi kusa.
Ko a makaranta Maryama bata da aiki sai yiwa Asma'u firar Kabeer tana cewa tayi dacen saurayi
amma Asma'u bata kawo komi a ranta ba.
Duk yadda Maryama zatayi taga tasamu shiga wurin Kabeer tayi amma babu nasara.
Bata kara fita hayyacin ta ba sai da Asma'u ta fada mata cewa za'a yanka mata sadaqi, suma ne
kawai bata yi ba a wannan lokacin.
*_"Wlh Ummah kin ji na rantse muddin kika bari na rasa Kabeer nima zaku rasani har abadan
abada, domin zan kashe kaina"_*
Ba shirin Hajiya Hawwa ta kira kawarta Binta suka garzaya wurin boka,suka sa ya yi musu aikin
da Kabeer yaji lokaci guda a duniya ba wacce yake so sai Maryama.
Itace ta saka shi yana yiwa Asma'u wulakanci yana jaddada mata cewa baya sonta baya ƙaunarta
har hakan ya saka aka yi zama tsakanin mahaifan Kabeer dana Asma'u.
Wannan zaman da akayi ya saka mahaifan Kabeer fushi dashi sosai har ya so ya tada hankalinsa
kan fushinsu amma sai Maryama ta ɗinga kwantar masa da hankali ta cewa zasu sauko ne ai,ya
yin da take banka masa magungunan asiri cikin abincin da take kawo masa in yazo fira.
A lokacin da Asma'u ke jinyar zuciyarta alokacin kuma Maryama ke shan soyayyar ta.
*************
Lokaci yaja yini ya tafi ya koma kwanaki,kwanaki sun koma satuttuka, satuttuka sun koma
watanni, watanni na kokarin zama shekara amma iyayen Kabeer sunki yarda da aurensu shiyasa
suma tasa Ummanta ta kai su wurin boka akayi aikin akansu kuma tasa akayi aikin da Kabeer ya
manta da wata Asma'u a wannan duniyar.
Aure ya ɗauru da taimakon dije wacce Maryama ta bata kuɗi ta saka ma mahaifan Kabeer magani
a abincin su suka ci.
Amma maganin bai jima ba ya warware aka barsu ta tunanin ya hakan ya faru.Ba haka Maryama
ta so ba amma tun da ta samu muradin ranta sai ta share su.
*Rayuwar auren Kabeer da Maryama* ba a cewa komi domin Maryama ta zamo miji shi kuma
Kabeer mata,sai yadda tayi dashi, ga Maryama da shegen son jiki da ƙazamta.Aikin gida Kabeer
keyi ta rabashi da danginsa har Allah ya azurtata da ɗansu Maleek.
Ko Maleek bata bari yasan dangin Mahaifinsa ba a cewar ta baya da bukatar hakan kuma idan su
Batul da Fatima suka so gidan ta dinga yi musu abubuwa kala_kala idan suka rama tasa Kabeer ya
korasu wani lokacin har da duka.
************
A lokacin da Maryama ta sakankance cewa ta mallake Kabeer sai yadda tayi dashi,alokacin kuma
addu'ar iyaye da y'an uwa Allah ya amsa domin Addu'ar iyaye bata faduwa kasa sai gashi Kabeer
ya dawo hayyacin sa;asirin Maryama ya fara warware wa.
Hakan ya ba Maryama mamaki da tsoro har sai da ta sake sa mahaifiyarta ta koma wurin boka ta
karbo mata magani.
Amma a yanzu ta kudurta a ranta cewa ba zaɓi daya da zata ɗauka cikin zaɓin da mahaifiyarta ta
bata domin sai ta gasawa Kabeer aya a hannu.
Dole ta nunawa Kabeer ai nahin halinta dole ne yasan *WACCE MARYAMA*,ta shirya rashin
mutunci kala_kala da zata yi masa domin rashin lafiyar da tayi akansa baza ta tafi a banza ba( 🤔😱
hajiyar Maryama mrs Kabeer Allah taimaka 🤣😂)
*_CIGABAN LABARIN_*
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
*💫(..)💫*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh
*Page* 57~~58
*_CIGABAN LABARIN_*
Da safe muna karin kumallo inna na bawa baffa labarin barawon da ya shigo jiya,baffa sauraronta
kawai yake baice mata komi ba yana shan kununsa.
"ai ke ma naga ba kuɗin ki bane!kuma naga waɗanda aka ɗauke wa sunce sun yafe,to miye na tada
maganar"
Kyafci inna tayi ta tashi daga gurin da take tayi gun pampo, domin sharewar da BAFFA ya yi mata
ya bata haushi sosai.
Sallama muka yiwa Baffa ya amsa tare da yi muna addu'a,karawa gaba nayi nabar Salmat tana
fadawa Baffa wata magana bansan mi take cewa ba ta jima kafin tazo inda nake tana cewa
mutafi,harara na galla mata cikin liqab dina Ina cewa,
"dá kuma zaki ganni anan yanzu,tunda azawa ne kika yi sauke tun bai tafasa ba"
"lallai yarinyar nan kin rainani, sai na saita ki zakiyi hankali,ni da ke ne"
Na fada ina kwafa, murmushi Salamat tayi tana tafiya tana cewa,
"Dalili"
na tambaye ta
"A'a"
"tambayar ki na yi ne?"
"ba ke kika tambaye ni ba amma yadace ki sani shiyasa,bawai da gangan na hanawa inna kuɗin ba
a'a kawai ina so ne kiyi amfani dasu wurin yin JAMB ɗinkin kin ga lokaci ya yi kusa.kuma idan
baki da JAMB ko nursing baza'a ɗauke ki ba, sai inbari inna ta cinye kuɗin ga banza ga kuɗin mun
samu abunda muka jima muna rokon Allah ya kawo muna kuɗin kafin wannan lokacin na JAMB
ya yi kisamu ki zana,ga waec na matsowa kuma sai an bincike ku bada kuɗi shiyasa kawai nayi
wannan karamin acting domin nasan hakan kawai zai sa inna tabar maganar kuɗin.
"ameeen"
Salmat ta fad'a tana wucewa zuwa ajinsu,yau sun makara shiyasa ma basu taras da su Amina da
bilkisu ba sun wuce tun ɗazu.
***********
"Whattt?"
"tsaya ma wai,ni fa ban fuskanta ba Dr.Abdull what are trying to said(mi ka ke ko karin cewa ne)"
"kinsan Allah kin bani dariya wlh, domin yanzu haka da wuya A.M ya kasance a Abuja kinga yau
juma'a yana yiwa ya kasance ya jima da wuce India kuma dawowarsa ba nan kusa ba"
Tsayawa kallonsa tayi tamkar Tv ta rasa abunda zata furta,gabadaya tarasa kalmomi a
bakinta,juwa kawai tayi ta wuce cikin motar ta ta kifa kanta a stiyarin motar ta lula duniyar
tunani;tun ranar talata take faman nemanrA.M har a yau jum'at.
A koda yaushe zata zo ta tsaya lokacin shigowar sa asibiti amma baza ta ganshi ba hakama
lokacin tashinsa kuma ta yi ta kiran wayarsa amma baya ɗagawa duk abubuwa sunbi sun jagule
mata takasa hakuri saida ta tuntubi Dr.Abdull ashe wai ma A.M baya kasar bama garin ba bai
sanar mata ba ita ya bari da wahalar zuciya da nemansa.
Ajiyar zuciyata ta sauke a ranta tana tambayar _SHIN MINE NE MATSAYINA AGUNSA_ ?
_MIYA ƊAUKE NI NE ?MIYASA YAKE AZABTAR DA ZUCIYATA DA RUHINA_ !
_Ina bukatar waɗannan amsoshin daga bakin ka,zan jira ka har ka dawo kuma bazan daina sonka
ba domin sonka numfashi na ne kuma jininane ko mutuwa sai dai ta ɗaukeni da soyayyar ka_.
_zanyi jinyar zuciyata har ka dawo Aliyu domin wannan karon bazan bika ba amma zan jira ka!
zan jira ka._
Jan motar ta tayi ta wuce gida ranta na kuna zuciyarta na begen sahibinta.
Ko a yau kacha-kacha sukayi da Maryama, ya taka mata burki na kwarai ya fada mata
magangannun da suka soya mata rai da zuciya domin ya lura iskancinta kara yawa yake amma zai
yi maganin tane yana ganin shawarar abokanin sa zai ɗauka kila tayi hankali.
Wani lokacin yana mamakin wai ma ya akayi ya aureta?ina ya ja jibowa kansa mugun iri irin
wannan ?
Sam Maryama bata da tarbiya kuma ita da kunya da sunyi hannun riga sam Maryama bata dace da
macen auran shi ba,ya hakan ta kasance? amma ba mai bashi amsa...✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 59~~60
Cikin bacin ran da Maryama ta dasa masa ya nufi hanyar gidan su dake Runjin Sambo saman
mashin ɗinsa.
Yana chan yana tuna ni ba tare da ya lura ba kuma baisan ya akayi ba ji kawai ya yi mashin
ɗinsa ya ɗan bugi mutum sai karar matashiyar budurwar da yaji ta kwalla kara tana kiran Adda...!
Yau Assabar mun tashi da murnar zuwa gidan mama Kareema da zamu yi,shiri muke cikin farin
ciki da annashuwa ya yin da inna Saude sai cin magani take tace baza muje ba Baffa ya ce zuwa
ba fashi,
"Haba malam taya zakace sutafi bayan nace a'a to aikin gidan waye zai yi ne"inji inna Saude cikin
bacin rai
"dama hala wa ke aikin gidan lokacin da basunan?ko kuwa sune matar gidan"
"ko daya,amma ƴaƴana ne kuma idan ban koya musu ba ai ni za'a zaga idan sukayi aure"
"Naji duk zancenki amma zuwan su ba fashi tunda ita kanta Kareemar ta bukaci hakan.watan su
nawa rabon su da chan da har zaki ce baza suje ba ko kuwa don ke bakya zuwa shine zaki hana
musu zuwa? ki hana musu zumunci da y'an uwana"
"Ameeeeeeeeeen malam,waye ne bai bukatar shirin Allah aikowa komi hankalinsa yana bukatar
wannan ehhe,sannan kuma inada tambaya shin wai hala so kake hayaki ya kashe min glas din ido
ne kaje ka auro wata?
in ba haka ba haka ba taya zaka tashi kara turamun yara wani wuri wai suyi kwana biyu"
tafada ciki. Masifa da jidalin da ke cinta kuma ga haushin mama Kareema na kuɗin da ya bata
amma ita da ke matarsa bai bata komi ba,kuɗin su _AGLA_ da ta kwallafa rai ɗan iskan barawo
ya santale ya tsere.
Ko cikan ki Baffa bai ce mata ba illa fita batunta da ya yi ya zauna bisa tabarmar da na shinfida
masa ya kara sautin redion inna Saude wanda take saurara yana sauraren *_Sakkwatawa
kwallahiya daga Vision FM radio_* ya lura fitarnar ta ta ce ta motsa da sassafen nan.
"Ni fa na lura tunda bawan Allah nan ya baka kuɗi ka chanzamin kana wani shareni don kaji taro
da sisi na shiga aljihunka to bara kaji wlh,duk wacce ta shigo gidan nan sai tafita da kafafunta
domin wannan gidan na Saude ne ba yadda ka iya dani ehhe yadda na hakura na zauna dakai
lokacin da babu kaina hakannne yanzu zakayi hakuri ka zauna dani ba yadda ka iya wlh"
Ta wuce ta bubbuttai,
"ni Saude naci dubu sai ceto ba yadda mutum ya iya dani sai hakuri "
Abun ma dariya ya koma ba Baffa amma ys gimtse ya yin da inna Saude zuba kawai take kamar
y'a'an ƙanya,Salmat kam sai da ta dara sosai,taso ta tankawa inna Saude amma tana gudun ta kara
harzukata taci gidansu amma da farko har gabanta ya fadi da inna taso ta hana da ga baya kuma
abun na mahaifiyarta ya koma bata dariya.
Nidai aikina kawai na cigaba da yi ina da sabo munsaba da halin inna duk da ta rage kwanakin
nan,naji daɗi da zamu yi kwana biyu wurin mama amma ina rokon Allah ya sa yah _Anwar_ ba
yanan har mu dawo.
Duk abinda zamuyi mun kammala ko da sha biyu tayi mun gama shiryawa muka yiwa inna sai an
jima ciki_ciki ta amsa dama Baffa ya bamu kuɗin adai_adaita na saka liqab dina muka dau hanya
sai *_RUNJIN SAMBO_*
Mai adai_adaitan baishiga da mu cikin kwanar gidan mama Kareema ba yace gaskiya shi anan
bakin hanya zai sauke mu,har Salmat taso ta tsaya jayayya da shi na hanata domin da'alama
mutumin ba yada kirki irin samarin nan ne na zamani.
Haushin hanata chachar bakin da nayi da mai napep din yasa tayi tafiyarta bata jirani ba.
Bayan na sallami mai napep na biyo bayanta ina mata magana amma taki saurarena kawai jinayi
mashin ya bugeni da kafa tare da karar Salmat tana cewa,
"Adda.........✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 61~~62
Maganar ta ce ta datse a lokacin da tayi arba da goshina yana zubda jini ta cikin liqab ai da sauri
ta daga liqab ɗin tana cewa,
Lokacin da Kabeer ya faka machine ɗinsa ya matso kusa dasu domin ya bada hakuri a dai_dai
lokacin kuma Salmat ke dagewa Aliya liqab dinta ta hanata amma Salmat taki bari tana cewa,
"jini ne fa ke juba a goshinki Adda amma kice baza'a cire wannan abun ba"
"Fatabarakallahu ahsanul haliki" shine abunda Kabeer ya furta a lokacin da yayi tozali da
kyakkyawar fuskar Agla,bai dawo daga duniyar kallon fuskanta ba yaji sautin muryar ta mai
taushi tana cewa,
"bafa wani ciwo naji ba Salmat,kawai kaina ne ya dan bugu da wannan dutsen"
Tafada a lokacin da ta saki liqab dinta ta dage goshin da hannu daya ya yin da take nunawa
yarinyar da ke tare da ita dutsin.
"juriyar tsiyane ke gareki wlh Adda,da nice yasen sai an kwasheni da mota wurin nan domin bazan
tashi ba ehhe,ko da yake mai machine ne ya bugeki ɗan air kawai kilama ya tserewarsa kar a sashi
biyan kudin magani dana diyyar jininki da ya zuba"
Inji Salmat tana jan tsaki
Tsaye ya yi yana kallon Salmat dake zuba ko uffan bai ce mata ba.
Hakama Aliya da ta mike ta ganshi kusa da su ya zuba mata idanu suna hada ido ya yi sauri ya
juya yana kallon Salmat.
Juyowar da Salmat za tayi tayi ido hudu da Kabeer sai tayi shiru.
Hakuri ya basu yana cewa ba da gangan bane don Allah su yi hakuri,cikin sanyayyar muryarta
tace,
"shikenan ba komi"
"Salmattt.."
"wace Salmat!garama ki yi shiru da bakinki Adda domin ni bazan hakura ba,abu sai kace yar
sadaqa !
ya buge ki har jini ya fita sannan daga ya bada hakuri kice kin hakura ba batun ya kai ki chemist a
dubaki a baki magani? a'a sai wani cewa yi hakuri"
Tafada tana kwaikwayon muryartai
"cikin ma ba'ace ya biya diyya ba,kilama diseases sun shiga"
Ji ya yi yarinyar ta kara burgeshi har cikin ransa komi nata ya yi masa gata bata da hayaniya,
surutun da Salmat ke yi ya tsayar da tunaninsa ya koma saurarenta domin shi abun ma dariya ya
bashi sai yaji duk bacin ran da maryama tasa masa yana gushewa ,kuma shi bai ga laifin yarinyar
ba domin gaskiya take faɗa.
"ok Kanwar mu kar kisamu damuwa wannan shine abunda kike bukata ko?
"eh"
"ba chemist ba Asibiti ma zankaiku adubata domin bazan so wani abu ya samu Addarmu ba"
"ohho"
Waigowa Kabeer da Salmat su kayi da niyar yiwa Aliya magana amma wayam ba Aliya Kabeer ya
dubi Salmat yace,
"ai duk laifin ki ne kika tsaya surutu gashi kin sa ta tafi ko sunanta ban sani ba"
"tou naji,mu tafi na sauke ki kinga sai na kai Addan naki chemist din"
"Allah?"
"ba wani daɗin baki,nidai muje ka saukeni yadda kace,ko man machine ɗin ka na kona na rage
haushin mai napep din da ya ki shiga da mu ciki har kayi sillar buge Addata"
"da naga wannan mai napep din da sai nayi masa kyauta saboda yayi silar haduwata da
kyakkyawan fure"
"mi kace?"
"cewa nayi da naga wannan mai napep din da na mazga masa mari domin bai kamata ya sauke
kyakkyawan yara bisa hanya kuma gefen titi ba"
yafada yana murmushi
ko kala bata ce masa ba illa nuna masa kwanar da zaya shi da tayi"
Duk yadda da Kabeer ya so yaja Salmat surutu tunda ya lura yarinyar parrot ce amma taki ta tanka
masa.
A bangaren Salmat kuwa tunani take yadda za su kwashe da Adda ita da mama Kareema idan taji
abunda ya sai da ta.
Dai_dai gidan da Salmat ta nuna masa ya faka har ta wuce ba godiya ya tsaidata,
"in badamuwa cewa nayi kimin magana da mai gidan don Allah"
har Salmat ta so taki amma da tayi wani gajeren tunani sai tace,
"ok badamuwa"
**********
Tunda naga ba saurarata Salmat za tayi ba na kama gaba,na lura ko wanda ya tsaya saurarenta
shima ba ya da aikin yi ne.Duk da inajin ciwo a kafana amma na ɗaure har na isa gidan mama
Kareema.
Haka mama Kareema itama ta fito ta tarbeni cikin farin ciki da kauna ya yin da suke tambayata ina
Salmat ko ba tare muka zo ba na ce,
mama Kareema ce ta lura da yadda nake taka kafana da zamu shiga parlo aiko arikice tayo kaina
tana cewa....✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing*💋
I just published "page 63&64" of my story "WASU MATAN".
https://www.wattpad.com/1110858972?
utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=
create_on_publish&wp_uname=zeesardaunerh&wp_originator=n1VImgkWaHrZ5gfQJiFz7bOHk
Yxi3XpTcnG2105RdPy29csbLIlYssD274yZF0xkvwO74TT3i7gY6W7siWx9ZQhpNZ8X6%2Bw
NaqzUMqjOwSeTvRZ%2BwnjVnlPCnjhKYZBa
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
_Page_ 63~~64
"ba komi bane mama,mashin ne kawai ya dan bugeni da kafa amma ba wani ciwo naji ba"
"haba mamana buguwar machine zaki ce wa kawai,baki san hakan yana iya janyo wani matsala
ba,kalli goshinki fa ya fashe wai ya ma haka ta kasance?saman titi ki ka haw ko kuma matukin
mashine din ne bayada hankali...
"ko daya mama abunda Allah ya kaddara ne shiyasa ya afku amma kuskure ne kuma ma ya bani
hakuri"
"wa?
Labari na bata daga A har Z saidai ban fada mata cewa Salmat ta tsaya sa'insa da shi ba domin
bazatayi mata da wasa ba.
"Assalamu Alaikum.....
taji ba'a amsa ba koma an amsa ita dai bataji ba,sake mai-maita sallamar tayi amma nan ma shiru
ko oyoyo bataga an fito anyi mata ba.Cikin ranta take cewa,
Cikin Parlon ta kusa kai tare da sabuwar sallama,zaune ta tadda su mama Kareema na yiwa Adda
Agla dressing na jimuwarta,mazewa Salmat tayi tare da bata rai tana cewa,
" _sai yau na kara tabbatar da wani abu amma bakomi rayuwa ce, idan baku sona bazan rasa masu
sona ba sai in koma gidanmu,yaseen kuma baza a kara gani na ba_ "
sai da ta bawa su mama dariya,da gudu Ramlat ta fada jikinta ta rungume ta cikin dariya tana
fadin,
"yi hakuri kawas muna sonki, wa ya isa yace baya son Salamatun inna saude"
"ni dai kyaleni ba ruwana dake wlh,nasan yah *Anwar* baya nan shiyasa da tun farkon sallamata
zai zo yanamin oyoyo"
Tafada cikin son ba Ramlat haushi aiko tayi nasara domin sakin baki Ramlat tayi tana kallonta
kamin tayi murmushi tace,
"Ayya gashi kuma kinyi rashin sa'a saurayin naki baya ma garin sai ki koma gida in ya dawo kema
sai kya dawo"
"ýar air kawai shi yaya Anwar din ne saurayina dan kin rainashi"
Da gudu Salmat tabi bayan Ramlat suna kama zagaye dakin sai da suka gaji suka zube saman
Kujerun dakin suna haki.
"a'a"
"sorry gwaggo"
Tashi tayi ta dauki hijab din Ramlat dake kusa da ita ta saka sannan tafito sakar gidan ta sake
komawa daki da sallama suka amsa ta duka kusa da mama Kareema tana cewa,
Da kallo kawai mutanen dakin suka bita Kafin mama Kareema ta amsa,
"ina amsawa"
miya sai dake saman hanya baki iso tare da ýar uwarki ba?
"ba wani kin manta renin hankali ne kawai mama,wai ace tundazu mutum yana garka tsaye
fissabilillahi"
"rufe min baki duk bake bace ki ka batamun lokaci na biye miki ai da ban manta "
Cewar Salmat
"Mumhhh don Allah,wai ni na bata miki lokaci ko Kunyar fada baki ji ba, dani dake wa ya fara
makawa wani pillo"
"Hmm ba wani nan in kina karbar laifinki ki karba yafi miki yarinya"
"ko dai blue zaki ce bai dameni ba kuma sai nagaya masa"
tafada tana fita daga dakin
Kuryar ďaki mama Kareema ta Shiga domin Saka hijab dinta ni kuma na tashi na shiga ďakin
Ramlat na kwanta domin bacci nake ji.....🖊🖊🖊
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 65~~66
Ko da Ramlat ta fita Kabeer yana zaune saman mashine dinsa duk alamun gajiya sun bayyana
gareshi kai da gani kasan ya Jima anan ga rana ta fito duk sai yabawa Ramlat tausayi gaishesa tayi
ya amsa sannan tace ance ya shigo ciki.
tare suka shiga gidan da Ramlat tana bashi labarin cewa Salmat bata fadi cewa yana waje ba ta
tsaya iya yi da kaudi.
Abun dariya ya bashi domin saida ya murmursa acikin ransa yake cewa,
"duk wanda aka bawa Salmat da Ramlat ko da na kwana biyu ne sai sun sakashi cikin nishadi da
dariya "
Ko da suka shiga Palon mama Kareema bata fito ba Salmat kawai ce a Palon cikin jan magana
Ramlat ta takalo Salmat aikuwa suka kama gardama da rikici ana cikin haka mama Kareema ta
shigo tsit sukayi kamar basu ne ke rashin ji ba domin sun san halinta duk iskacin su basu yi mata
gaban baki.
Gaisawa mama Kareema da kabeer su kayi sannan ya bada hakuri Kan abunda ya faru bada
gannan bane kaddarace mama tace,
"Ameen"
Duk yadda ya so ya ga Agla babu hali domin bata fito ba haka ya tafi cikin farin cikin haduwa da
ita,yanaji aransa ya samu wani abu da ya rasa duk da ya manta ko minene amma zuciyarsa na
sanar dashi cewa ya rasa muhimmin abu a rayuwarsa.
Ko a gida ma da yaje ba labarin da yake musu sai na Aliya da su batul suka tambaisa minene
sunanta sai yayi shiru suka dinga masa dariya
a ransu kuwa suna fatan Allah yasa yarinyar nan da tatafi da zuciyar yayan nasu ya kasance ta
kwaraice ba Kamar maryama ba.
Duk da ba haka su ka so ba,son so ace yazamana yayan nasu su kulla Alaka da Adda Asmeey
(Asma'u tsohuwar budurwar kabeer)ganin yadda suke mutunci da junansu duk da kabeer har
yanzu bai tuna komi game da ita ba kawai yana mutunci da ita ganin yadda mutanen gidan nasu
keji da ita amma sun san cewa har yanzu akwai soyayyar yayansu a cikin zuciyar Adda Asmeey.
Suna masa fatan samun wannan yarinya duk da basu yi tozali da ita ba kuma basu san wacece
ita ba amma yadda yake ta basu labarinta ko gajiya baya yi yasa sukaji suma ta kwanta musu arai
kuma suna son mummy'n Maleek(maryama)ta gane kurenta domin yaseen yah kabeer yana yin
aure sai ta raina kanta sai ta gane ba dangin miji ba abun wulakantawa bane kuma addu'a makamin
Mumuni ce bata bar komi ba(🙄).
************
Har na manta da batun ciwon da naji a kafana domin ban dauke shi serious ba duk da cewa kafan
na dan yi mun ciwo,mun yini cikin farinciki da walwala a gidan,sosai na godewa Allah da yah
Anwar ba ya nan ya yi tafiya.
Bangaren Salmat da Ramlat kuwa shirme kala_kala suka yi Kamar su yallallaba,ďan waken
fulawa,dan ta malili da dai sauransu(d.d.s)kuma mama Kareema bata hana su ba,idan suka gama
wannan shirmen sai suyi wani,sosai suka ji haushin rashin yah Anwar abokin shiritarsu da yana
nan da abun sai yafi dad'i da armashi.
Duk da da girkin dare su sukayi jellop din macaroni da nikaken Kofi Salmat uwayen kwadai ta
bude ciki ta kwashi girkin tana santi Kamar basu ne suka yisa ba,Ramlat ba biye mata tayi suka
narki abinci iya son ransu.
Dakin mama Kareema na shige na kwanta domin banajin dad'in kafana zafin ciwon kamar ana
increasing dinsa,hakan na daure na kwanta batare da na bari mama ko Salmat da Ramlat sun san
abunda na keji ba.
Su Salmat suna palo suna kallon kwana casa'in bayan angama shirin mama ta korasu suyi bacci.Da
farko dakin Ramlat suka so su kwanta amma mama Kareema tace dole su kwanta a dakinta domin
Agla da bada lafiya ita kuma a dakin Abban Ramlat zata kwana.Bayan ta Saka su karatun
suratul_Mulk da yaseen tare da Azkar din kwanciya.
Abu kamar wasa jimuwar Aleeya sai ziza take mata tana kara daurewa dakyar bacci ya Dauketa
sai chan sakar dare ciwon ya dawo sabo takasa bacci gashi ko maganin da mama ta bata bata sha
ba yassuwa tayi.
Cikin bacci su Ramlat suka dinga jin nishin Agla ko da suka bincika Kafarta ta fara kumbura abun
ka da farar fata,ba yadda ba suyi ba amma ta hana su sanar da su mama;kwanan da ba su koma ba
kenan har subahin idanunsu biyu.
************
A bangaren kabeer kuwa ya so ya koma da daddare ya bincike lafiyarta amma hakan baisamu ba
sakamakon aikensa da Abbansa ya yi shine bai dawo ba sai 11,badon ya so ba ya hakura da safe
sai yaje.
hakan ya kwanta cike da tuna tunanin Aliya da fatan ta kasance masa mahadin rayuwa.Ana kiran
subahin ya farka ya yin da mafarkin da ya yi ya shiga dawo masa wai shida Aliya suna musayan
kalamai na soyayya cike da so da Kaunar juna.
Mikewa ya yi ya nufi bayi(bathroom)tare da yin alwalla ya yi nafila raka'a biyu kafin a tada
sallar subahin yana rokon Allah ya tabbatar masa da wannan mafarkin ya zama gaskiya.
Shiryawa ya yi ya nufi chemist dinsa duk da cewa Agla na makale a zuciyarsa amma yasan cewa
ko ya tafu yanzun ya yi musu sammako sosai shiyasa ya bari misalin 12pm yaje.
*Maryama*
Ganin yadda yau ya ke cikin farinciki alhali ita ya b'ata mata rai jiya ya barta da haushin abunda
ya yi mata a duk lokacin da ta tuna maganganun da ya gaya mata sai ranta ya kara baci don haka
itama tayi niyyar bata masa farincikin da ta ganshi a ciki.
Kamar yasan abunda ta ke shiryawa, yana gama shirinsa ya tafi domin ce mata ya fita ko da
yazo tana bayi, ba tare da ya tsaya jiranta ba ya yi ficewarsa domin yau bai shirya chachar baki da
ita ba balle ta b'ata masa annashuwar fuskarsa da zuciyarsa.
Ko da ta fito kabeer ya dade da barin gidan aiko ta yi ta zaginsa ta uwa da ta uba sai da bakinta
yayi ciwo(🤔)
*Aliya*
dakyar nayi sallah subahin da taimakon Ramlat da Salmat ko da gari ya danyi haske mama ta
shigo dakin domin tace musu su fito su yi breakfast tana mamakin rashin fitowarsu duk a
tunaninta baccin safe suka koma da sallama ta shiga dakin suka amsa,sosai ta mama ta rikice
ganin yadda kafar Agla ta kumbura dakyar in ba kariya bace ko gusdewa Allah yasa Abban Ramlat
na nan bai fita ba shi ya dinga kwantar mata da hankali dakyar sukayi breakfast sai fada takewa su
Salmat kan rashin sanar da ita tun Jiyan da daddare.
Bayan sun Kammala kowa yaje ya watsa ruwa tare da shiryawa suka dauki hanyar wamako.
Abban Ramlat ya so a sanar da Baffa amma mama Kareema ta hana domin tasan irin son da
Baffa ke yiwa Agla idan yaji wannan abun hankalinsa zai yi mugun tashi don haka suka bari akan
cewa sai sunje sun gani duk yadda ake ciki idan abun da sauki sai a sanar dashi.
*Kabeer*
Misalin 12 na safe kabeer ya kasa hakuri ya fito daga chemist din bayan ya barwa yaronsa ya kula
masa da komi ya nufo Runjin sambo bai yi parking a ko ina ba sai a kofar gidan mama Kareema
domin bai manta gidan ba amma abun mamaki sai yaga gate din gidan sakale da mukulli har tura
gambun ya yi amma a rufe yake yajima Wurin kafin wani makocin su Abban Ramlat ya gansa
tsaye a wurin shi ne ke sanar da shi cewa sun tafi wamako wai yarinyarsa ce bata da lafiya ko wai
ta samu kariya ne ko ya ya ne shidai ya manta.
Sosai hankalin kabeer ya tashi da jin wannan batu zuciyarsa na gaya masa tauraruwarsa ce bata
da lafiya godiya ya yiwa mutumen sannan ya hau mashine din sa ya nufi gidansu domin bazai iya
komawa chemist yanzu ba gabadaya ji yake ba yada wani kuzari a jikinsa.
Ko a gida Ummu bata gane kan kabeer ba ko abinci dakyar yaci duk ya susuce yanan kwance biyu
tayi aka tada su batul daga makaranta suka dawo gida,ganin halin da yake ciki yasa su tambayar
Ummu tace itama batasan mike damunsa ba.
Wujinsa suka zo suna tambayar mi ya ke damunsa yace ba komi duk da basu yadda ba sai suka
share abun suka hau tambayarsa ya Antynsu wacce ya buge da mashine jiya Kamar dama jira yake
ya shiga basu labari yanzu haka yaje gidan ya riske sa a kulle wai sunje wamako a tare suka ce,
"Wamako?"
Yace,
"eh"
yana ma tunanin cewa itace ta jimu domin jiya ya lura da yadda take taka Kafarta illa bai maida
hankali ga hakan ba.
Addu'a suka shiga yi Allah yasa ba kariya bace suna kuma kwantar masa da hankali har ya samu
ya dan saki jikinsa suka dinga hira rabin duk ta Aliya ce suna cikin firar Asma'u ta shigo aka
cigaba da hirar da ita ba tare da ta nuna komi ba har dare tana gidan sai bayan magrib ta wuce gida
ya yin da su Batul da Fatima suka shirya domin suna son kabeer ya tafi dasu su ga wannan
yarinyar.
*Aleeya*
Tafiyar minti talatin ta kaimu wamako,a dai_dai Asibitin kashi ta wamako motarmu ta yada zango
muka shiga ciki ina taka kafar cikin dauriya ko da aka duba gusdewa ce ba kariya ba domin da
kariya ce bazan iya taka kafana ba sannan kumburin sai yafi haka.
An gyara kafar amma kam nasha hawaye su Salmat ma sunyi kuka Kamar sune akewa ana
gamawa aka bani magani nasha sai bacci.
Bansan Adadin awannin da na dauka ina baccin ba sai da na farka na ganni a gida misalin karfe
biyu dana tambayi Ramlat yaushe muka dawo tace daya saura muka iso,
"amma to waya daukoni ya saka a mota kuma waya kawoni daki ?"
"nice Adda kin sanfa nayi karfi sosai ga ki ke kuma ba wani auki "
Tafada tana yimin gwalo,fillon katifar na dauka tare da jifan ta dashi aiko ta fita da gudu tana
dariya.
Tanajin haka ta fita tana ma Salmat dariyar keta har take cewa sai ta gayawa ya Anwar cewa
rashin kunya take wa Adda Agla aiko nan rigima ta kaure tsakaninsu sai da suka gaji dan kansu
suka bari,mama kareema na jinsu ko cikanki ba tace musu ba.
Alhmdlh kafar ta dan rage haushin da tayi dazun,bayi na shiga ina dafa bangon dakin nayi wanka
tare da alwala na fito nayi Sallah ina idar wa mama Kareema ta shigo dakin da plate din abinci ta
saka ni gaba tace sai na cinye amma ko rabin abincin ban ci ba nace na koshi,ba yadda mama ba ta
yi ba kancewa na kara cin abincin amma na kafe cikina ya cika.
Magani mama ta bata domin tasha aiko ta fake idanun mama Kareema ta watsa karkashin gado
sannan na ruwa kam ba yadda ta iya haka ta shashi tana bata fuska sannan aka shafa mata wurin
jimuwar.
Haka ma bayan Isha'i muna tare da Ramlat da Salmat mama ta bani magani sai da na bari
hankalinsu ya ďauku ga wani abu sai na watsa karkashin gado ashe mama na kallona bansani
domin d'azu tayi mamakina da nasha maganin ba gardama, nan da nan alhali ta san halina yadda
na tsane magani kamar rai da mutuwa.
Ashe d'azu da na koma bacci mama ke ba su Ramlat labarin yau yarta tasha magani babu
gardama aiko Salmat tace bata yadda ba Adda Agla da ta tsane magani ace wai tashashi kai tsaye
abun abin dubawa ne.
Ko ina Salmat ta duba bataga Inda na yarda maganin ba amma an aje kan cewa zasu sakamin
Idanu anjima su gani, wurin da ta yadda na d'azu batare da angane ba nan zata sake yarwa ko a
gida hakan take yiwa inna,sunyi naam da shawarar Salmat gashi yanzu duk sun ganni...
**************
Bayan Isha'i kabeer ya shigo shida mahaifinsa bayan sun ci abincin dare suna zaune suna fira
Batul ke rokon kabeer da ya tafi dasu su ganta sun san da yadda Allah yanzun sun isa dawowa
suna son su mata ya jiki dakyar ya yarda aiko suka buga tsalle suna murna hijab dinsu suka saka
suka dawo palon Ummu ce ta dubesu tana cewa,
Kabeer da tun d'azu da suka fara zancen baice musu kala ya dago idanunsa ya sauke kan iyayensa
dake jiran amsa yace...
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing*💋
*_Wayyo hannuna_*😢😭😂
I just published "page 67&68" of my story "WASU MATAN".
https://www.wattpad.com/1120727080?
utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=
create_on_publish&wp_uname=zeesardaunerh&wp_originator=qPCD2Of0%2FdYuOE7YSZkwe
SCeLOb6MEd1SFXxUrHq3FrifTyzZUg720%2F6GbtYhdVFJYze1eCxYJ9ZGt7Gsi2DSya0D09J
CdUZ6bsLrx9e9wHYZMzbQvHr8DD2A59VwFU4
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 67~~68
"Nima Ummu bansani ba wlh sai munje zamu gani amma dazu naje basa nan sunyi wamako"
"amma Muhammad baka kyauta ba,shine ko ka fada naje na bawa iyayen nata hakuri shine ka
kama bakinka kayi shiru"cewar Alhji Sa'id
Dukar da kai kawai Kabeer ya yi yana sauraren mahaifinsa ya yin da Ummu ta cigaba,hakuri ya ba
su sannan su kayi musu Allah ya tsare Alhji Sa'id nacewa inshaallah gobe shima in yasamu time
zai je ya dubata.
Cikin kankanin lokaci su Kabeer suka isa gidan mama Kareema bayan sun biya sun siyowa Agla
kayan makulashe na marasa lafiya.
Sun samu tarba ta mutunci kwarai ya yinda Salmat da su batul suka Jone suna zuba labari duk da
cewa zasu girmi Salmat a shekaru amma kadan sai dai Salmat akwai girman jiki ga shegen iya yi.
Sun yaba da Agla kwarai ga kyau ga nutsuwa duk abunda zaya saka ta dariya Batul yin sa take
ya yinda Fatima ke daukar wa Kabeer pics din Agla cikin hasken da ya haskaka gidan na generator
da Abban Ramlat ya kunna.
Labari sosai ya barke tsakanin su Ramlat da su Fatima kamar anjima da haduwa duk da cewa ita
Ramlat ta san su Fatima domin tana ganinsu a shiyar gashi school d'insu daya amma sun tsare
mata da aji guda.
Dakyar mama Kareema ta Kora su Batul da suka shanya Kabeer waje yana jiransu,sallama su kayi
da kowa batul na cewa,
Har zasu fita waje sai ga Abban Ramlat bayan sun gaisa da Kabeer ya shigo dashi ya ga jikin Agla
ya yi mata ya jiki suka gaisa da mama Kareema ya ajewa Agla ledodin tare da kudi amma Sam
mama Kareema tace aa ba'a haka kayan ma an gode,badon ya so ba sai don baya son jayayya ya
maida kudin ya wuce yana Allah kara sauki(Anya kabeeru kodai_kodai🤣)
Ko a yanzu sai da Salmat da Kabeer suka taba drama Kafin su wuce su batul na daga musu hannu
suma hakan.
_*Aleeya*_
Fada sosai nasha wurin mama Kareema na watsar da maganin da nayi kafin ta saka min wani a
baki da hannunta na kora da ruwa kamar nayi amai amma ba hali domin ta daure fuska ba sassauci
irin no mercy dinnan,mi kuwa su Salmat zasuyi in ba dariya ba;wai yau anga uwa da d'iya a rana.
Zuwan su Batul su ke kowa ya d'an taimaka na saki jikina domin yammatan akwai ban dariya da
zasu tafi ba daďi domin Al'umma rahama ne suma suna da rawar kai irin na Salmat.idan suka
cemin antynmu kunya ma nakeji domin ba wata tserayyyar shekaru a tsakanin mu sosai illa
girman jikin da bana da sai ka dauki shekarunmu guda dasu Samlat.
Rufe idanuwa na nayi da yayyansu ya shigo domin Kafeni ya yi da idanuwansa shegen kallo ke
gareshi kamar yah Anwar.
"ai wannan abun mu aka kawo wa domin mune masu jinyar ko ba haka bane k'awas"
"to Kajin turai surutun mi ne ko ke mata akai kunki barin ta tayi bacci "
"Ayya mama yau kuma wannan sunan muka samu?mungode dama kasafin kayan dubiya ne muke
yi da aka kawo mana"cewar Salmat
"Kune ko da yaushe baku gajiya da surutu,kasafi sai kace kayan sai dawa?wai ma saya cikin ku
wacece aka kawowa kayan dubiyan?
"wlh Salmat kiji tsoron mai mana ruwan sama domin yana kallonki,yan zu bada amsar ne shine sai
kin ware kanki daban to tsaya kiji ni ba irin ki bace sannan kuma ki sake hali, ta dubi mama tana
cewa,
"to dai mama maganar gaskiya Adda Agla aka kawowa amma kinsan halinta ba ci take ba shine
muke kasafawa ni da Ramat kar ya lalace"ta karisa tana saka cinyar filamingo a bakin ta.
Girgiza kai kawai mama Kareema tayi domin iskancin su Salmat mai degree ne.Pate ta dauka ta
dibarwa Agla gasasshen nama tare da flamingon ya yin da ta dibarwa su Salmat lemo da ayaba
domin tasan idan ta barmu cinyewa zasuyi tunda kurayen gaskene ta dau Hollandia guda ta barmu
su guda suna chan wurin rikincin da ya barke tsakaninsu kan Salmat tace Ramlat ta sake hali shine
fa yazama abun gardama.
Mama na bawa Agla naman ta naci shima cikin ta matsa mata domin Agla bata son ciye-ciye da
yawa domin ko naman bata ci tsunke biyar ba sai kankana da tasha da ayaba.
Ganin rigimar tasu bata ajewa bace mama ta daka mutsu tsawa tana cewa Allah zata kora su waje
ko suje dakin Ramlat su kwana tunda hakan ake jinya sannan sukayi shiru aka koma ciye_ciye.
_*Kabeer*_
fadan da yaso ya yi musu na shanya shi da sukayi ya kau domin yaga annurin zuciyarshi.
Su Fatima sun cika shi da surutun sun dace,sai yabon ta su ke domin duk wanda ya zauna da Agla
sai ta shiga ranshi.
Haka suka ci gaba da tafiya cikin motar suna masa firar Aliya da kuma sabbin abokanai da suka
samu;da yake ba yawo suke yi ba shiyasa basa da kawaye da yawa.
Yana jin farin ciki from no where yana shigarsa shi Kansa ya tabbatar da cewa ba karamin so ya
kewa Agla ba sai dai fatan Allah yasa ta so shi ko da kwatan son da yake mata ne.
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 69~~70
Su Ummu sun yi farin cikin jin cewa ba'a samu karaya ba,Alhj Sa'id da Kansa yaje ya duba Agla
hakama Ummu taje ita da Fatima a kabar Batul da girki kamar ta yi kuka fatima sai gwalo take
mata.
Inna dije na jin abunda ke faruwa amma ko cikanku ba ta ce musu ba sai ma yawon da take a
kwanakin nan bata cika zama ma acikin gidan ba.
Bayan Ummu sun dawo daga gidan su Ramlat Fatima ke bawa Batul labarin abunda akayi bata
nan har da sakon Antynmu (Agla) da Salmat na gaisuwa da suka bada a kawo mata,nan suka hau
firar Agla wadda Ummu ce ta jawo ta tambayarsu kawai ta yi wacece antyn tasu?abunka da mai
nema cikin duhu bare an haska sai kawai suka hau firar ta domin fa tayi bala'in burgesu,Ummu na
sauraren su bata tanka ba amma ko ita yarinya ta kwanta mata a rai ta ya ba da nutsuwarta sosai
har cikin zuciyarta.
Hada kayan mu muke slowly kowa jikinsa ya yi sanyi domin duk da cewa wannan Jimawa ba ta
lafiya bace amma shakuwa ta kara Shiga tsakani kamar kar mutafi.
Amma tafiya dole domin nayi kewar Baffana sosai ga kuma WAEC da ke kusantowa.
Salmat ce ta dubi Batul dake kusa da ita tayi shiru baki ya mutu ta kyalkyale da dariya tana cewa,
"amma fa yarinyar nan Kazar kauye ce ke, dubi fa yadda kika bata fuskarki kamar wacce aka cewa
idan muntafi shike nan baza mu sake haduwa ba,ga yayanku nan basai kusa ya kai ku gidanmu mu
ba ana tare ai"
Tunda suka zo dubiya Allah ya hada jininmu shiyasa ko da yaushe in basa school ko Islamiyya
suna gidan mama Kareema hakan ya karasa shakuwarmu karfi.
Sometimes haka kawai yayansu wanda suke cewa yah KB ya ke kawo su da daddare mu zauna
muyi ta nishadi sai dare ya yi misalin 11 ko 10:30 ya dauke su su koma gida.
Bugu da kari Ramlat itama barin zuwa makaranta tayi ya yin da ta antayawa malaman karyar cewa
sun yi tafiya,shirme da shiririta kuwa karuwa ma suka yi domin Batul ba baya ba itama.
Hakan suke shiryawa suje gidan su Batul suma idan suka ishi mama Kareema da haukarsu sai ta
korasu tasamu ta yi bacci musamman da rana wannan shine yasa Shakuwar tayi karfin da akejin
ba daďi wurin rabuwa.
Ta bangarena kuwa ina cikin farincikin nazo *yah Anwar* ba ya nan sai ga wani kuma kaddara ta
hada mu ya na takuramin idan badon shi ba da kuma Baffana da nake son gani da sai na kara sati
daya dai-dai naji sauki sosai,
"Mssstwwwsss"
tsukin da ban shirya masa ba ya fito.
Duba na Ramlat tayi domin itace kawai taji tsukin su Salmat hankalinsu baya kaina tana cewa,
"bakomi Ramlat"
"Ok"
tace tana maida dubata ga Fatima da tayi murmushi tana cewa Salmat,
"hakan ma za'a yi kuwa Salamatun inna koma bai kaimu ba sai mushiga napep.."
Karfe biyu na so mu wuce amma Salmat tace sai Hudu kafin mu isa biyar ta yi domin tasan
muddin muka isa karfe uku sai inna Saude ta samu girkin dare.
Bayan munyi Sallar la'asar muka yi Sallama da juna ya yin da mama Kareema ta hada mana sha
tara na arziki,namu da na inna Saude hakama Ummun su Batul itama tabada kayan kwalliya da
turare su Batul suka kawo mana tare da Kudi aciki inji Abban Batul bansan ko nawa bane da farko
naki karba saida su Fatima suka nuna rashin jindadinsu sosai sannan na amsa nayi godiya.
Tafiya muke yi a hankali ya yin da su Salmat ke fira har muka kawo bakin titi da zamu tare napep
mun jima tsaye abu Kamar wasa amma ba emtyn napep din da ta wuce duk wadda suka tara
mutane ne a ciki har suka gaji da tsayi domin biyar har ta kusa.
Ana cikin haka sai ga motar Kabeer, tun daga nesa Fatima ta hangeshi ta yi murmushi tare da
cewa,
"shikenan ma Allah ya yanke muna wahala ga yah KB nan sai ya yi dropping dinku "
Batul ta ba Samlat hannu suka taba hannu har suna hada baki wurin cewa,
"babu"
***************
Tun daga nesa ya hangesu ya sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya domin bai saka sammanin
taraddasu ba tun dazu yake sauri ya taho amma go slow ya saida shi a kan hanya.
Tsaye muke a jera gefen titin inda nice farko then Fatima,Salmat,Batul sannan Ramlat amma duk
saida ya gota su ya iso inda na ke ya yi parking tare da zuge glass dinsa yana cewa...
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 71~~72
kallon juna naga su Salmat sunyi suna murmushi tare da yin magana kasa_kasa.
"Yawwa gsky ka kyauta,tun dazu ma muke nan bamu samu napep ba gashi dare yayi,nifa ma
kazama yaya na daga yau tunda ka ragemin hanya"
tsaye nayi tamkar wacce aka dasa ji nake kamar in tuma in shako Salmat domin yaseen iskacin ta
ya fara tukeni,kafin in ce wani abu naji tana cewa su Batul su shigo ciki dan nan ma suga gidanmu
tunda yayansu ne sai ya dawo da su.
Kamar jira suke suka antaya bayan mota harda Ramlat batare da Izinin yayan nasu ba tunda ga
uwarsa Salamatu ta basu umurni.
Nama rasa yarda zanyi ina tsaye ji nake kamar wadda aka sanyayawa kafafu Batul ta dubeni cikin
murmushi tace,
"Amma dai Adda Agla idanunki sun koma irin na inna ko?"
"eh mana idan ba haka ba ga kujera guda daya chan gaba muka bar miki zakice babu wuri sai kin
haw napep?to dai Allah da kansa ya hana almubazzaranci ehhe"
Dariya kowa yayi ni kuma naja kafafuwana nashiga gaban motar araina ina raya irin hukuncin da
zanyiwa Salmat.
Bamuyi nisa da tafiyar ba ya yi parking a wani mall *STOP AND SHOP* yace mubashi minti
biyar yanzu zai dawo.
Salmat ta dubi Fatima tace
"eh,inajinki"
"wannan wurin da yayanku ya shiga ina ne hala?naga mutane sai shiga suke,ko da yake nima
yanzu yayana ne"
"Oh wurin shopping ne inda ake siyar da kayan makulashe kala kala harda su chocolate"
"Ohho kila"
"ai ko muma yaseen sai ya yi muna kuzo mu bishi ciki kowa ya dauki abunda yake so"
"ya yi kyau boss,to idan aka samu akasi kema ya hada dake fah "
"hakanma za'ayi"
Cewar Batul
Ina kallonsu suka shiga mall din bayan kamar mintin 30 suka fito a tare suka shiga motar ya tada
muka cigaba da tafiya.
"uban wa ya baku izinin bina ciki har da damar daukar abubuwa bada izinina ba"
ta madubi na kalle fuskokinsu duk sun yi tsuru_tsuru gwanin tautsayi harda boss dinsu
*SALAMATU* gabadaya sai suka bani dariya har na dan dara a hankali.
**************
Kallonsu ya keyi idan wannan ya kalli wannan sai wannan ya kalli wanchan kamar wanda aka
tsikara sai ya kalli sashen da take ta gefen ido dai dai lokacin da take dariya,
ba karamin kyau tayi masa da tana dariyar ba har sai da ya shagala da kallonta.
"shike nan Salmat kin gama damu bansan wane hukunci yah Kabeer zai mana"
"ku kwantar da hankalinku idan ya kara tambaya muce Adda Agla ce"
"nidai ba ruwana gsky zan fada kar ki kuma samu cikin wani case kuma"cewar Batul
Karar oda da akewa Kabeer domin ya tara go slow ita ta dawo da shi hayyacinsa domin ya manta
cewa a tsakiyar titi suke,jan motarsa ya yi tare da cigaba da tafiya ba tare da ya kara tada maganar
su Salmat ba.
Da kwatancen da Salmat ke yi masa suka iso gidan ana gab da kiran magrib.
Godiya na masa ban tsaya jin komi ba na wuce cikin gidan dama duk a takure nake jin kaina
cikin motar.
Da Sallama na shiga cikin gidan wani farin ciki na ratsani hakika nayi kewar gida sosai da Baffa
na fara cin karo yana zaune bisa kujera yar tsugunno da butar alwala a hannunsa.
Cikin farin ciki ya amsa min yana tambayar lafiyar kafana da kuma su mama Kareema,
muna cikin maganar sai ga inna Saude ta fito daga cikin madafi hayaki dai ka tashi idanuwan ta
duk sun cika da ruwan hawaye,
"dalla ni sake ni kin wani zo kin kanainaye ni,ai na dauka a chan zaku tabbata baza ku dawo ba"
"ikon Allah miya yi zafi haka inna shi ba wuta daga dawowa sai fada?to Allah huci zuciyar uwar
gidan Baffa nidai a sassauta wannan jidalin tare da baki muke"
bata ida rufe baki ba saiga su Ramlat da Batul sun shigo cikin gidan bakinsu dauke da Sallama.
Har inna taso ta sharesu sai ta kara kallonsu da kyau taga ba zubin talakawa bane irinsu dagani
diyan manya ne ga hannuwansu dauke da ledodi,amsa sallamar tayi ciki ciki.
Durkusawa sukayi suka gaida Baffa ya amsa musu cikin sakin fuska sannan suka gaida inna
ta'amsa tana kakalo murmushin yake.
Tabarma ta shimfida musu suka zauna ya yinda Salmat tayi gurin Baffa ta gaishesa domin sam
bata lura da shi ba tana dokin ganin innarta amma ta bata red card, gaisawa Ramlat taka yi da
Baffa yana tambayarta su mutanen gida tace kowa lfy yake.
Ko minti uku banyi da dawowa ba saiga Baffa ya shigo yana cewa su Batul su taso su tafi yayansu
yace gida yakeson yayi magrib,tashi sukayi suka miko min leda wai inji yayansu,kin karba nayi
suka ajiye suka fita ina kiransu amma suka ki dawowa gashi kuma banason fita waje wlh.
"yaseen baza tayi ba shedan kawai ke mayar da hannun kyauta baya" tayi wucewarta tabarni
tsaye.
Achan waje kuwa bankwana su Salmat suka karayi tana jaddada musu tana dubinsu ko wane
lokaci tunda sun san gidansu,ta dubi Kabeer tace,
"in har zakimin kampen wurin Antynmu nikuma zan dinga kawo miki su har ma da chocolate zan
biyo miki dashi "
"bakada matsala inshaallah "
Kudi ya bata yace tasha minti sannan tacewa maman Agla yana gaisheta kuma inshaallah zai zo ya
kawo gaisuwa
sannan ya shige mota su Fatima na daga mata hannu..✍️✍️✍️
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
_Ina Kuke masoyan *WASU MATAN* masoyana ku fito ku nunamin kaunar ku a fili ta hanyar
siyen littafina mai suna Diyah akan Naira *#300* kachal ta hanyar turo katin MTN ta wannan
number *09066484295* ina jira sai na ji kuuu🥰🥰🥰🥰🥰_
I just published "page 73&74" of my story "WASU MATAN".
https://www.wattpad.com/1126782875?
utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=
create_on_publish&wp_uname=zeesardaunerh&wp_originator=Z%2FNUGNtiW5L
%2BtXHRzT8jJnXKRcWO
%2FS8csO5HwC6EQ8U4dvv4iZM2j1XVq3pJHYn3hnKCmGLmesV
%2Bj0n7HmVV3RpH1y3VeQfMOCvrbBBYY065aK%2FeEdkOZQfq5vo6RJKs
📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
*Page* 73~~74
Bayan mu idar da Sallar magrib da Isha'I muka dawo saman tabarma muka zauna muna jiran
dawowar Baffa ya yinda inna Saude ke cikin madafi tanashan hayaki takammala tuwo miya ce ta
rage ta kada,na tashi na kama mata domin naga itacen danyu ne amma ta bankomini harara sai da
najuya na dawo wurin da nake,Salmat ta dubeni cikin dariya tace,
"wa ya ake ki Adda,baki lura a kufule take damu ba shiyasa ta sharemu,kinci arzaki harara kawai
ki ka samu banda zagi"
"Inna"
Shiru Inna tayi ta kyaleta amma duk da hakan ba tayi shiru ba so take sai ta tsokano hajiya Saude,
"Inna!Inna!!,Innata!!!"
"dan Ubanki lafiya kike yimini kiran maharauta kamar wacce ta yi wa Ubanki sata"
"Lah lah lah mi ya yi zafi haka hajiya inna?kawai naga rashin da cewar ace ga mai girki a cikin
madafi ni da bani na girka ba na tashi zuwa diba,ba ki ga Adda Agla idan ta girka abinci zubawa
kowa take takaimasa"
"ki jira Ubanki ya dawo ya zuba miki shine Sa'an yina ba ke ba"
Wucewa inna tayi ta cigaba da harkokinta ya yin Aliya ta tashi ta zuba musu abincin,
"Ayya ashe kullum nama ki ke ci inna gashi har kiba ma kinyi shiyasa kike cin magani baki so
muka dawo b...."
Maganar ta ce ta katse ganin Baffa ya shigo cikin gidan da Sallama a bakinsa,sannu da zuwa
sukayi masa hakama inna amma ciki ciki ta yi,
ruwan randa masu sanyi Aliya ta dibar masa sannan ta zuba masa abincin.
Salmat takai lomar farko a bakin ta bayan haɗiya ta dubi inna Saude tace,
"Inna"
"Lafiya"
Cewar inna
"lafiya lau,dama wai cewa zanyi miyar nan daddawa da gishiri ya yi masa yawa kuma cin gishiri
ba kyau musamman ma ga wanda ya tsufa"
takalmi inna ta ra rimo da niyar ta jefawa Salmat aiko kamar walkiya Salmat ta ari na kare sai
dakinsu tana dariya,aiko inna ta dinga fada kamar taci babu dama hake ta ke da su ko ni kaina
saida na dara haka inna tai ta fada har saida ta gaji tayi shiru.
Fitowa daga dakin Salmat tayi taje gurin randa ta debo ruwan sanyi da kofi ta ajiye gaban
inna,ba tare da musu ba inna ta dauka tasha domin tana bukata.
"ko kefah innata yanzu da kikayi fada ba kinji sanyi cikin ranki ba?amma ace mutum ya dinga cin
magani yana ta bakin rai "
Shiru inna tayi taji ance tsaraba,wanke hannu Baffa da ya kammala cin abincinsa ya yi Aliya ta
kwashe kwanukan dama ita tun Inna na fadanta ta kammala cin abincin domin ba wani yunwa
take ji ba.
Hira suka dingayi su da Baffa Salmat na ta bashi labari musamman ma sabbin hawayenta.
Shiru shiru inna na ta jiran tsarabar amma taji tsit,har sai da tagaji tacewa Salmat,
"wai ina tsarabar ne ko sai abu ya lalace zaki fitar ki bawa mutane ne?"
"Bafa abunci bane inna kawai turare ne maman su Batul ta bada ankawo miki,"
tafada tana jawo Daya daga cikin jakar da suka zo da ita kayan kwalliya ta fara cirewa ta aje
gefe sannan ta fiddo turarukan,turaren ďaki
ne da na tufafi,saida Salmat ta hesa taji wadanda suka fi kamshi ta daukarwa kansu sannan taba
inna saura duk abunda take inna na kallonta aiko tace batasan zance ba haka sukayi tayi da inna
karshe dai Salmat tace a chakudesu wuri guda sai kowa ya dauka,aka ko chakude tacewa inna ta
fara dauka,inna ta rasa wanne zata dauka domin bata rike kalolin na dazu da Salmat ta dauka ba
sai tace a'a Salmat dai ta fara dauka,murmushi Salmat tayi aranta take cewa,
Sai ta sa hannu ta dauki wadanda tabawa inna dazu charab inna Saude ta amshesu tana cewa,
"wannan ne daman nake so,kuma wlh ko da wasa kika yi gigin chanza mini su ni dake ne"
Duk da dariyar da keson kufce mata sai ta gimtse ta turo baki tana cewa,
Shiru Salmat ba tare da tace komi ba daman zuciyar ta ta raya mata hakan tasan halin innarta
kwarai shiyasa tayi hakan gashi cikin sauki ta kare da matsalarta.
Kayan da mama Kareema ta basu Salmat ta fiddo ba tare da ta fiddo kudin da Abban Kabeer ya
basu ba,su kubewa da daddawa,citta da sauransu shine mama Kareema tace a bawa inna,karba
inna tayi ba yabo ba fallasa duk da cewa taji dadin kayan amma bata nuna ba.
Robar dambun inna takai hannu zata dauka Salmat ta dauke tace,
" inna bari mu sammiki wannan kayan mune fah ba naki ba"
Cewar Salmat tana zuba dambun naman cikin plate,inna na kara tazali dashi yawonta ya
tsinke,Salmat ta dube Agla tare da cewa,
" kyaleta Aleeya,ni wlh renin da Salamatu ta yi mini bansan iyaka tai ba kina gani da na dauki
robar dambun karbewa ta yi sannan ta dawo tana ce miki wai kizo ki raba,dad'a bansan mi take
nufi ba iya rabon ne ban yi ba kome"
Ni dai ko kala bance ba domin nasan da na karbi robar da fadan kaina zai fada ba Salmat ba.
Duk fadan inna baisa Salmat ta bawa inna rabon danbun naman ba domin acewarta *_wa zai bawa
kura hida ai wannan sai DAN KASADA_* (my new novel)d'ibarwa Baffa Salmat tayi da nufin ta
mika masa ko da ta duba ashe baya nan tun dazu da tafara buda tsaraba akace ana sallamamasa ya
fita waje,debarwa inna Saude tayi tabarwa kansu saura,sai da inna ta cinye take cewa bata gode ba
Salmat tace "ai dama bake ta bawa ba inna"
"kowa dai tabawa dai ba ruwana ni dai nace baa gode ba"
Haka fa inna ta saka su gaba har madarar sai da aka dibar mata ko wacce,saida Salmat ta bari
hankalinta ya dauku ta dauke Ledar da Kabeer ya bata tabawa Agla takai cikin d'aki sannan ta
dawo ta dauko kayan chocolate da Kabeer ya siya musu a STOP and SHOP tafara sha inna na ta
ya ta nidai danbum naman kawai naci amma duk da hakan sai Salmat ta dibarmun chocolate din ta
ta ajiyemin,ganin inna zata shanye mata kaya yasa ta diba ta ajiye da sunan na Baffa ne.
Bayan Baffa yadawo takai masa kayansa amma kamar yadda ta zata bai karbi chocolate din ba
dariya ya mata yace ai wannan kayan yara ne,kudin da Abban su Batul ya bada ta dauko ta bashi
tare da wanda Kabeer ya bata tagayamasa cewa babban wanda ya kide Agla ne yabada akawo
musu da farko Adda taki karba amma da suka nuna rashin jin dadinsu mama Kareema tace su
amsa bata nuna mai cewa Kabeer ya bata kudi ba domin fada dai zata sha.
Dubu goma ne Abban su Batul ya bada Kabeer ya bata dubu biyar sunkama shabiyar,dubu
goma Baffa ya dauka yace su bawa innarsu biyu sauran su rike su tsiye abunda suke so saida safe
Salmat ta yiwa Baffa sannan ta wuce dakinsu ta riske Aliya da tun dazu tayi shigewarta.
Dubu Ukku Salmat ta mika mata tace Baffa ne yace ta sayi *_past Q wato past questions
paper_* sosai Agla taji dadin hakan sannan Salmat ta mikawa Aliya Naira dubu tace ita dari biyar
Aliya dari biyar Baffa yace su saye abunda suke so cikin kudin da suka samu ne,ita kuma inna ita
adda Naira dubu sai da safe ta kai mata.
Addu'ar bacci suka yi suka kwanta Aliya na cikin farin cikin kudin da Baffa ya bata na past Q.
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
*comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing*💋
*I _just published "page 75&76" of my story "WASU MATAN".
https://www.wattpad.com/1136765448?
utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=
create_on_publish&wp_uname=zeesardaunerh&wp_originator=Sy0TBAaSNfjugkbkTrG0lgUuPz
dwkL2AvU1uxm3Y43n%2FaJ008b%2FyMvwjiG3UBwsXV7778Gz58rBK9rq0YnI
%2FIha1woweFpk9l%2Foxy%2F3GZ78Ql%2FSBhK6%2FzW%2BaVEfdcb5M_*
*WASU MATAN*
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W*
_*DIYAH*_
_Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account
number 2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp
number 09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan
number 09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295_
©️♤♡ *_Zeesardaunerh_*
*Page* 75~~76
Da safe bayan sun kammala shirin zuwa makaranta suka dibi kunu da niyar su karya dashi kafin
su tafi,kurbawa Salmat tayi taji kunu salaf ba sugar ta dubi inna Saude da ke fitowa daga dakinta
tace,
"amma ai dazu da nafito daga wanka naga lokacin da Baffa ya miko miki kudin sugar kafin ya
fita"
"to karyar da na saba yi miki ce ya bani hana wa ne nayi kada Allah yasa kisha"
tafada tana shiga kitchen din ta debo nata itama tazo inda su Agla ke zaune ta ajiye kunun ta shiga
daki da niyar ta dauko sauran sikarin da ta rage jiya.
Ajiye kunun Salmat itama ta mike ta shiga dakinsu,naira dubun da ta ajiye tabawa inna Saude ta
dauko ta yi waje,Aliya na tambayar ta ina ta yi amma bata tsaya bata amsa ba ta fita.
Wurin mai siyar da kosai ta nufa ta siyo na Naira dari biyu sannan ta wuce shagon malan Abu ta
siyo sikarin dari madara pick sachet ukku ta dawo gida.
ko da tadawo inna Saude nata banbamin fadan ta ajiye sikari bata gani ba.
"kisha abinki hakan mana inna,kila kusu ne ya santale miki sikarin mukam dai baza musha abu
salaf ba"
ta karisa tare da fiddo sikarin ta zubawa kanta da Agla,sannan ta fito da madarar ta bawa Agla
sachet daya ita ta zuba dayan ta ajiye daya.
Spoon ta dauko guda biyu itada Aliya sannan ta buda ledar kosai ta ajiye tsakiyar su tana cewa,
"Adda Agla muyi sauri mu karya lokaci na tafiya kar muyi latti"
Da "to" Aleeya ta amsa mata ya yin da inna ta kame kamar status ta kallon bakin Salmat da ke
shan dadi.
Duk kallon nan da takewa Salmat tana lure da ita,Aliya bata wani sha sosai ba ta mike kosan ne
kawai taci da d'an yawa sai a sannan ta lura da inna wacce ta tokare bakin kofa tana kallon su.
Ta so ta tambayi Salmat ina kayan inna amma tana gudun aras ta fado kanta gashi dama a gidan
inna bata bari suna zance da turanci cewa take zaginta ne sukeyi.
Rasa ya zata yiwa Salmat maganar tayi kawai sai ta shige dakin su ta saka safarta da hijabinta ta
dauko jikarta ta fito.
lokacin da suka hada ido da Agla ta dauka ta yiwa Salmat maganar bata b'ata nata kayan ba amma
sai taga tayi shiru daga karshe ta shige dakinsu.
Tsuki tayi har saida Salmat ta dubeta amma kuma batace mata komai ba taci gaba da karinta.
Kasa daurewa inna tayi saida ta maganta ai ko suka hau yinta da Salmat dakyar Salmat tabawa
inna madarar guda ta dibar mata sikari wai tasan halin inna da shan zaki kar ta shanyeshi gobe tace
kuma bazata basu na kari ba,kosan ma inna ta barwa sauran kadan ne bai kai na dari ba nan da nan
inna ta washe baki tana zubawa Salmat albarka itada Aleeya.
Har zasu fita Salmat ta mikawa inna sauran changin dari biyar da wani abu tace,
"Inna ga wannan ki rike ki kara cikin kudin chefanen da Baffa ya baki ki yi mana girki mai d'adi"
Saida kudin suka shiga hannun inna sannan ta daure fuska take tambaryar Salmat ina ta samu
kudin,
"Ayya inna kinason ki samu latti wlh,wannan kudin da kika gani mama Kareema ce ta bamu dari
biyar maman wanda ya kide Adda ta bamu dari biyar,sune na baki gabadaya ko Baffa ban baiwa
ba,shikenan abun da kike bukatar ji"
"a'a fa inna,fadin gaskiya yafi mugunyar sallah kedai kawai kice tunda kudin suka shiga hannun ki
hankalinki ya kwanta"
"aa wlh ina ni ina zama mamarki inna,rufamin asiri barni da sunana Salamatu kar Hafsu(cewa da
Hafsat uwar inna Saude) tajiki ki kunno min wata wutar"
"Salamatu.."
"Ni kinga tafiya ta kije kar kosanki ya huce inma godiya zakiyi Adda Agla zakiyiwa domin itace
tace na baki kudin amma a karan kaina ...kin dai sani basai na ce komi ba"
"yawwa innata ashe kin haddace wadannan kalmomin gaskiya ina bala'in matukar sonki cikin
parcent dari ina miki 1%"
takarisa maganar tana shekawa da gudu tasan halin inna sarai yanzunnan zata iya jifarta da duk
abunda ta samu domin tasan abinda ake nufi 1%.
Wurin kunun ta ta nufa aranta tana cewa ko ba komi zuwanku gidan Kareema ya yi d'an amfani
gashi jiya naci kayan dad'I yau kuma ga kudi.
Bangaren Salmat kuwa saida ta hada da d'an gudu sannan ta cimma Aleeya domin tayi mata nisa
ashe duk surutun da take Agla ta tafiyarta ta barta.
"wash Allah na, Adda kinsa nayi gudu duk na gaji miyasa baki jirani ba"
"na dauka baki gama dramar taki ba shiyasa na tafiya ta har ki kammala ki chimmin'
Juyowa kadan Aleeya tayi ta kalleta sannan taci gaba da tafiyarta ahankali tana cewa,
"Allah kuwa , ai dagan_dagan nayi amfani da kudinta nasan halinta sarai yaseen da tasan kudinta
nayi wannan facikar na shigesu "
***************
Duk hakurin da *Dr Aysha* taso tayi amma takasa wadannan satittukan jin su take kamar cikin
kurku_ku take tadauka zata iya hakuri da juriyar jiran dawowar *Dr A.M* amma ina sam abun ba
haka bane,ashe da duk abunda takeji wasa ne tunda har tanajin muryarsa,kamshinsa sannan uwa
uba daddadar muryarsa.
Har wata rama tayi ta rashin ganinsa gashi kuma ko labarinsa bata samu domin tun lokacin da
Dr.Abdul ya gayamata yayi tafiya bata sake tambayarsa labari Haidar ba amma yau ta shirya yarda
makaman yakin da ko sanin tana yi baayi ba ta shirya tambayar Dr. Abdullah labarin sanyin
idanunta.
**************
"eh mana Inna,in ba mugunta ba taya zai kama jibgata sai kace baiwarsa,nafa yi masa bayanin
dalilin da yasa mukadau kwanaki da yawa bamuje makaranta ba amma saboda tsabagen son rai ko
nace mugunta shine yasa akamin bulala goma don kawai ba ya sona"
"Amma ko malamin nan bai kyauta,kiyi hakuri duk rashin jin maganarku ne yaja muku,ita Aleeyar
nawa ya sa akayi mata"
"wa! rufe bakinki,hmmm waya isa ya buge Adda a makarantar nan *malam Ishak da malam
Ayub* suna makarantar kedai inna bari,ko laifi Adda tayi basu bari a bugeta ballema da wuya kiga
tayi laifi bare kuma wannan da yakasance ciwo"
Kasa da murya Salmat tayi yadda Agla dake d'aki baza taji taba tace,
"wai fa a haukarsu wai sonta su ke,hhhhhhhh wlh abun za dariya shifa *mlm Ayub* harda d'an
tunbinsa,yayi diya ma da Adda? duk wannan abun da suke wacce suke yi kanta bata ma san sunayi
ba yaseen"
"Allah ya kyauta amma kam wannan malamin ya iya cin zalin yanason yayarki amma yana cin
zalinki"
"kedai Inna kyaleshi,ada naso na bawa malam Ishak ita domin yana dan d'an kyawunsa kuma
muna mutunci amma yaseen sai dai ya mutu tunda ya bugeni Allah bashi ba Adda."
"da harda cewa Salmat don Allah ki samo min soyayyar Addar ki wlh ina sonta kamar rayuwarta
Allahne ya jarabceni da sonta ba yin kaina ba"ta karisa tana kwaikwayon muryarsa sannan ta
cigaba da cewa,
"a'a,amma ai nasan Baffa bazai yi mata Auren dole ba kuma kema kanki nasan kinason mijin Adda
ya kaiki makkah, don haka na samo ma *_Addana mijin da zata Auraaa............_*
*Zeesardaunerh ce*
# _comment_
# _like_
# _share_
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
DIYAH
{ Short story }
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number
2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number
09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number
09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Thanks for the prayers Fan's Allah ya saka muku da mafificin Alkhairinsa Thanks alot
Page77~~78
"hmmm Salamatu Allah ya shirye ki maimakon kiyi hankali naga birkicewa kawai kike"
"Allah bawasa ba inna na samo wa Adda miji wanda ke sonta kamar ransa"
"wanene shi"
" kar ki samu damuwa yace zai zo ya gaisheki ai,sunansa Muhammad Kabeer kyakkyawane kamar
Adda,
amma Addana tafishi kyau"
"Allah ya kawo shi lafiya,hhhh dama nasan ba fadar gaskiya zaki yi ba domin a duniya bantaba jin
kince ga wanda yafi addar ki kyau ba"
"Allah ba hakan bane inna,ko ke kanki kinsan Adda Agla kyakkyawa ce ajin karshe,ko ya mamien
Adda ta kasance?nasan tanada kyau sosai amma da wuya tafi Adda ko inna?"
Shiru inna tayi tana tuna fuskar Halimatu,yanayinta da kuma sanyinta,tabbas Halimatu kyakkyawa
ce itama domin a hasashenta kamar tafi Aleeya kyau sai dai Agla ta nuna mata farin fata
sosai,wani kishine ya taso mata da tuna irin son da Baffa ke yiwa Sadiya yanzu nan take fuskarta
ta chanza.
Da "to" Salmat ta amsa tana tunanin ko miye ya batawa inna rai kuma?amma ba mai bata
amsa,mikewa tayi ta shiga dakinsu ta chanza tufafi tare da yin alwala tayi sallar azhar,taso su ci
abinci amma ganin Aleeya bacci ya seceta a wurin da tayi sallah yasata itama kwantawa domin
batason ta tasheta.
Sai karfe hudu suka farka,bayan sunyi sallar la'asar Agla tayi mitar miyasa Salmat bata tasheta
ba,gashi hudu tayi tasan kuma karfe shida islamiyya zasu na gashi ko girkin dare bata aza ba"
"lokaci fa ya riga ya wuce Adda,kwana ne mun riga mun sha shi kinga sanadin baccin da kikayi
nima na samu na runtsa,kuma dama rayuwa saida hutu "
"kinga ma Adda Allah ya hutar sheki abincin safe dana dare inna tayi "
Murmushi Agla tayi tabbas taji dadin hakan domin ko a yanzu tunanin yadda zata daura girkin
take batare da sunyi lattin islamiyya ba.
Abincin suka ci Salmat na santin inna yau tayi abin kwarai ta yi girki mai dadi,
"yaseeen inna bata kaiki iya girki ba,nifa har yanzu banci girkin da yafi naki dadi ba Allah "
"hmmm Salmat kin fara ko?ai me na riga nasan baki fadin gaskiya,ko da yaushe hakan kike fada"
"Dagaske fa Adda gaskiya na fada sirrin daga hannunki ne da kike girka abincin dashi bawai
abincin ba "
Wanke hannunta tayi ta hau kakkamcin gidan kuma har ta kammala tayi wanka ta shirya Salmat
ma hakan amma inna tana daki bata fito ba.Jakar littafansu Aleeya ta dauka suka shiga dakin inna
sukayi mata Sallama,murya a cinkushe ta musu Allah ya tsare suka wuce kowa na tunanin mike
damun inna Saude.
Gidansu Amina da Bilkisu suka biya,bayan sun gaisa da mahaifiyar su Amina suka wuce dakinsu
bilkisun,koda suka shiga suna shiri.
Kafin Amina tayi wani yunkuri Agla ta sakar mata dundu a baya saida ta duka.
Dariya maganar ta bawa Agla wanda yasaka saida ta dara wushiryarta ta fito gwanin burgewa
"ni ba wata mugunta da na miki, nasan yanzu kin farka kin gane cewa ba mafarki ki ke ba "
"amma dai lamarin nan akwai ganin laifi aciki,nidai naga bamu mu kar zomon ba kuma ko rataya
ba a bamu ba"
Sai bayan sun fito daga gidan su Amina Salmat ta tuna da chocolates din Agla cewa tayi suje
kawai zata chinmusu.
Basu dade da shiga makarantar ba ta itama Salmat ta isa ko da tazo suna tambayar ta jikin ta.
Ledar chocolates din ta ajiye saman desk din dake gaban Aleeya kafin tayi magana
Aisha,Amina,sun bude ledar domin ganin abinda ke ciki.
Maryam(Ummi)tace,
"Rahama kalli wannan mai shape din heart gsky ni yafimin kyau"
"kefa Allah duka chocolates dinnan manya ne,nama waye hala?"Aisha ta fada tana duban Ummi
Kallon Agla Salmat tayi taga itama ita take kallo kamar sauran domin ita kanta bata san da zaman
chocolates din ba
"na kune ku duka domin saurayin kawarku yace akawo mata "
Atare Rahma da Aisha sukace,
Zeesardaunerh
# _comment_
# _like_
# _share_
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
DIYAH
{ Short story }
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number
2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number
09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number
09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 79~~80
Dukansu idanu suka zubawa Salmat har Aleeyar domin ita ma abun yazo mata a shock kamar
sauran abokananta.
"nidai nayi ajinmu har malam ma ya shiga,duk tambayar da Kuke bukatar amsarta zaku iya
tambayar Adda,amasa daya ce zan baku wato sunansa"
Cikin zakuwa tare da mamaki suke tambayar sunan,saida ta bari ta kai bakin kofar fita ta daga
murya yadda zasu jita tace,
Amina tace,
"kedai kyaleta Amina ta kyauta,da yanzu Salmat bata sanar muna ba shikenan sai munji za a yanka
engagement"cewar Aisha
"ni fah duk bama wannan ba abun mamaki ya bani wai Agla ta fara soyayya ikon Allah shiyasa
naga kin chanza"Maryam ta karisa cikin dariya.
Dariya suka saka harda tafawa sannan Rahama tace cikin zakuwa,
""y'ar uwa bamu musha labari,wanene ya yi nasarar tafiya da zuciyar mai tsada"
Maryam taci gaba da cewa,
"yaushe kuka hadu har kika kware masa domin nasan duk namijin da ya ganki sai ya kware miki
amma banyi zaton zaki fara soyayya soon ba"
Wata dariyar aka saki domin yanayin yadda Maryam tayi maganar dole yasaka ka dariya
"kyaleta Aisha kinsan halinta yar air ce sai ta karemana jan aji"cewar Amina
Shiru Agla tayi ta zuba musu ido tana saurarensu domin ita fa takasa tuna waye MUHAMMAD
KABEER din da Salmat ta fadi,ko ita kanta batasan wayeshi wannan da yabada sakon akawo ba.
Suna chan wurin surutu Malam Nura ya shigo ajin amma basu lura ba ko ita kanta Aleeya ta lula
duniyar tunani,tsit ajin yayi kowa ya zubawa group d'insu ido da yake kasa_kasa suke magana ba
a jin abinda suke cewa.
Azahiri kallon su yake amma a bad'ini Aleeya yake kallo wacce idanunta ke kan allon sai ka dauka
malamin take kallo amma tunani ne take,
Ahankali Maryam da ta lura da shiru da ajin yayi ta kai dubanta gaban allo taga Malam Nura yana
kallon su kuma dukkan attentions din yan class na kansu ya sakata tura hannunta baya ta tabo
Amina,lura da abinda Maryam ke nufi itama Amina ta tabo Aisha,Aisha ta tabo Agla wacce sai
lokacin ta fahimci Malami ya shigo domin duk zancen da suke bajinsu take ba hannu Amina tasa
ta tabo rahama amma ina Rahama labari ya yi dadi bata fahimta ba gashi malam ya kusa kawo wa
inda suke, kara tabota Maryam tayi har sai da ta dago wanda ya bawa sautin muryarta damar
fitowa tana cewa..
""aiko yau ba wani jan aji da za'a yimana sai an bamu labarin soyayyar nan domin nasan zai bada
citta sos....."
Maganarta ce ta makale a lokacin da tayi ido hudu da malam Nura,dubanta ta ya yi dakyau yana
cewa cigaba da maganar ki miyasa kikayi shiru?
raurau Rahma tayi da idanunta domin tasan yau shikenan fa ita tata ta kare in har yaji abunda ta
furta,yadda tayi da idanunta ne yasaka Agla murmusawa har saida washiyarta ta bayan wanda
hakan ba kadan ba yayi tasari a zuciyar malam Nuran har saida yasake kallon ta ya yin da su Aisha
keta kumshe dariyar dake son fito musu a hankali Amina tace,
"shine dai_dai da parrot din da bayajin kwab'a yanzu Allah kadai yasan hukuncin da zata karba"
Dariya sukayi yadda malam nura bazai ji su ba,wannan maganar takara saka idanun rahama yin
ruwa domin kowa yasan halin malamin nan baya wasa,
dan gyaran murya ya yi sannan yace,
bata idar da maganar ba aji akasa dariya,ko ba komi Rahama akwai tsoro bare yanzu da tayi
katobara
"Ok zan hakura amma dole ki zabi daya cikin zabi biyu"
batare da taji zabin ba tace ta amince a tunaninta zayace ta karanta darasi daya cikin wadanda ya
yi musu kowa yama ta tambaya cikin fiqhu ta bashi amsa.
wani munafukin murmushi ya saki da yaji zancenta ya yinda su Agla suka san ta kare ma Rahama
yau domin fa wannan murmushin akwai muguntar da ya shirya mata,jayewa ya yi ya nufi gaban
allo.
"don Allah kubar tayar min da hankali nasan bazai wuce ya tambayeni cikin karatu ba"
Kafin Rahama tace wani abu malam nura ya kira sunan ta tare da cewa ta fito gaban allo, fitowa
tayi ta tsaya ya dubeta yace,
"na daya ki maimata zancen da kika kasa karasawa na biyu ki fadi abunda kuke tattataunawa akai"
"a'a"
kallon su Amina tayi sannan ta kalle sauran yan ajin taga kowa ita yake kallo ai sai tarasa mi zata
cewa gashi ko giyar wake tasha bazata furta ainahin zancen da suke ba.
Amina tace,
"wayyo Allah yanzu ya Rahma zatayi,gaskiya malam nura ya cika ta kura ai da wannan zancen
gara ya yi mata bulala ko ya hade mu duka ya bamu punishment"
"wallahi kuwa Amina,ni yan zu na rasa wane irin amsa zata bashi bare na mata inkiya gashi
idanun kowa na class din suna kanta"
"ya kamata wata cikin ku ta dauke hankalin malam nura daga kan Rahama akwai abinda zan gaya
mata"cewar Amina
wata yarinya mai suna habiba wacce ke kusa da sit dinsu Agla kuma taji abunda Rahma tace ta
daga hannunta alamar tanason yin magana malam nura ya bata dama,
"inshaallah bazai ma saurareta ba kinsan ta cika kaudi da yawa kedai bari na ida kawai"
cikin yanga Habiba ta fara magana wanda yasaka sai da ya dubeta ta wannan hanyar Amina tayi
amfani ta jefawa Rahama takarda mai rubutu da sauri Rahama ta dauka ta rike da hannu amma
badamar karantawa .
Kamar yadda Amina tace sai gashi ya yarfa Habiba daman yarinyar bata masa gashi ita kuma tana
mugun sonsa,duk yadda taso ta bashi bayani amma ya hanata saboda haushin yadda take
kararraya.
"wannan shine karatun mu na yau, malama Rahama bissmillah kina b'ata mana lokaci"
"ok kisan yadda zakiyi kisata dariya har attention dinshi ya dawo kanta hakan shi zai bawa Rahma
damar karanta abinda ke ciki "
"Hakane kuwa kanki naja Maryam,amma kinsan hukuncin wanda yayi masa dariya a aji ko? "
"bulala kawai ce ko ya sa mutum aiki kuma duk wannan mai sauki ne in har hankalinsa ya karkata
ai shikenan "
Amina ce ta juya ta dube Agla tare da yi mata magana amma yarinyar nan taki yin dariya sai dai
murmushi,mitsinanta Aisha tace tayi koda yar kara ce tayi hakan ma zai yi,hannu takai zata
mitsineta dai dai nan malam nura ya sakar wa Rahama tsawa har sai da ta durkusa Agla dake
kallon Rahama cikin tautsayi batasan lokacin da dariyar ta kubce mata ba gashi kuma ajin yayi
shiru sana din tsawar da malam nura ya yi sai kowa ya juyo ya zuba mata ido hakan yabawa
Rahama damar karanta abinda Amina ta rubuta.
Kallon Agla malam nura yayi wacce tayi tsit kamar ruwa ya cita domin ko ita a bazata dariyar ta
fito hakan ba dabi'arta bace ta duke kai kasa yayin da ya zubamata idanu kamar kar ta dena dariyar
domin ba karamin kyau tayi masa ba .
Shiru yan ajin sukayi suna jiran jin abinda malam nura zaice sanin kansu ne duk wanda ya kama
yana yin dariya a lokacin da yake cikin aji musamman ba in akayi shiru to kashinsa ya bushe,
dauke idonsa daga kan Aleeya ya yi sannan yace A.....
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
DIYAH
{ Short story }
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number
2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number
09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number
09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 81~~82
Dauke idanunsa daga kan Aleeya ya yi sannan yace "Amm Rahama je ki zauna" cike da mamaki
Rahama da kowa da ke ajin ya kallesa harda Aleeya(Agla) wadda ke jiran sakamakon hukuncin
dariyarta.
Kallon da tayi masa shine abunda ya idar da warware duk wani notin kansa da gangar jikinsa.Ba
karamin illa dariyar ta tayi wa zuciyarsa da kwakwalwarsa ba wanda shine dalilin yanke hukuncin
da yayi ba tare da yasan ta ya hakan ya faru ba.
Da sauri Rahama ta dawo wurin ta yayin ajin yayi tsit kamar ruwa yaci shi,duba agogon hannunsa
yayi yaga saura time kalilan period dinsa ta kare batare da bata lokaci ba ya fita daga ajin.
Domin kuwa muddin ya tsaya a ajin za'a samu power gaba daya ji yake kwakwalwarsa ta
daina aiki ba abinda yake gani face fuskar Agla da dariyarta sai kuma kallon da tayi masa wanda
ya riskesa a bazata.
Kamar jira ake ya fita ajin ya hautsine da surutu ko wane group anyi gungu ana tattaunawa kowa
na cike da mamakin malam Nura .
******************
A bangaren Maryama kuwa
Har yanzu babu wani sauyi ta lura yanzu kamar akwai abunda ya dauke hankalinsa kwana biyu
yazama busy baya ma biye mata suna fada gashi ita kuma har yanzu bata dauki zabi ko daya ba
cikin zabin da mahaifiyar ta tabata,amma zata kawo karshen abun.
*************
DR AYSHERT
Office din Dr Abdullah ta wuce kai tsaye...batare da tayi Sallama ko knocking ba ta murda handle
din kofar ta shiga.
Zaune yake saman kujera ya na duba wasu file yaji an bude gambu,dago kansa yayi ya kalle Dr
Ayshert dake shigowa;matashiyar likita mai ji da kudi ga kwalisa amma duk ta rame ta dan fita
hayyacinta wanda ba kowa ne zai fuskanci hakan ba sai wanda yama ta kyakkyawan sani.
Kallon sa tayi yayin da ya dauke kai daga kallonta domin yasan halinta ba mutunci ne da ita
ba,cikin isa da gadara take magana kamar ba ta so " Hydar yana ina"
wani kallon bangane ba ya watsamata da yake ko ba komi ya tashi tare da Aleeyu kuma ya koyi
wasu daga cikin halayesa yace mata "ban fahimceki ba "
Cikin son gasa mata magana yace "oh na dauka kuna waya dashi ai"
Batace masa komi ba amma maganar ta dake zuciyar ta,yaci gaba da cewa...
"ko da yake no problem ba sai na miki dogon zance ba Aleeyu ya wuce India gurin wani course da
zaiyi kuma I think zaiyi shekara daya ko biyu"
# _comment_
# _like_
# _share_
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
DIYAH
{ Short story }
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number
2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number
09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number
09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 83~~84
"Whattt? tsaya ma wai,ni fa ban fuskanta ba Dr.Abdull what are you trying to said(mi ka ke ko
karin cewa ne)"
"kinsan Allah kin bani dariya wlh, domin yanzu haka da wuya A.M ya kasance a Abuja kinga yau
juma'a yana yiwa ya kasance ya jima da wuce India kuma dawowarsa ba nan kusa ba"
Tsayawa kallonsa tayi tamkar Tv ta rasa abunda zata furta,gabadaya tarasa kalmomi a bakinta.
A duk tunaninta Aliyu yana tsakanin Abuja da Kano amma taya hakan ta kasance,duk wata kasa
da zaije tana sani kuma some times har ta rigashi isa da sunan itama taje yin wani course a chan.
Tabbas tana bukatar sanin duk wani bayani da ya shafi tafiyarsa domin dole nema tabi
bayansa,bazata iya jure rashin ganinsa a kusa da ita ko da kuwa na sati ne bare kuma shekara,bata
san lokacin da ta furta cewa "this is impossible!"tare da bugun teburin dake gabanta har sai da file
din dake gaban Dr Abdallah suka watse.
Dagowa ya yi yana kallon ta ba tare da ta kalleshi ba ta juya tare da ficewa daga cikin office din
tana jawo handle din kofar da karfi ya rufe, yayin da kwakwalwarta ta hasko mata wani tunani
wadda ya idar da chakuda lissafin ta; yanzu idan ya kasance tare waccan tsinanniyar matar shi ya
tafi fa,wani kololon bakin ciki ne ya tokare makogaronta yayin taji yajin kishi a cikin idanuwanta.
juwa kawai tayi ta wuce cikin motar ta ta kifa kanta a stiyarin motar ta lula duniyar tunani;tun
ranar talata take faman neman A.M har a yau jum'at.
Numfashi mai zafi ta sauke yayin da ta tuna tattaunawarta da Dr Abdallah bayan tafiyar Aleeyu da
kwanaki gashi yanzu zancen satittuka ake, tabbas ta gaji zuciyar ta ta galabaita da rashinsa kusa da
ita tana bukatar son tabi bayan sa kuma tana tuna Alkawarin da tayi a wannan lokacin da tari
tambayoyin da zuciyarta ke bukatar amsarsu;
Zaune take zaman Royal chairs din dake kawataccen parlon ta,tana sanye da duguwar riga mara
nauyi wacce ta lafe a jikinta ta bayyanar da tsarin halittarta,tarasa wane hukuncin zata yanke.
Saida ta kwashe kusan awa daya kafin ta yanke hukunci, da yake bata da zuciya ta yanke
shawara binsa ko da zata zauna nesa dashi batare da yasan taje ba ko ganinsa zai rage mata
wannan zafin zuciyar da take fama dashi.
SUHAILAT
Jirgin su na sauka a Abuja gidan su ta wuce daman tayi waya da mamynta an turo mata driver ba
batun taje ta gaida Ummyn A.M ko kala haidar baice mata dama ta saba irin wannan ba farau ba
ya saba da ganin hakan ya motarsa ya shige shima batare da b'ata lokaci ba yayi gidan Ummieyn
sa.
Kwanan sa biyu da zuwa jirgin sa ya lula samaniya sai kasar masu jajayen kunnuwa.
Duniya tayi wa SUHAILAT dadi duk da cewa mamynta na yi mata fadan yawo amma abu ga
sagartattun yara sai a slow tun tashin ta dadynta ba ya kwabarta abunda take so shi take.
Yawon buki kam ba magana shigar kasaita, ado da kwalliya sai daukan hotuna da vedios ana
posting tiktok ba abunda ya ragu.
Bayan 2weeks suka fara shirye_shiryen bukin daya daga cikin yan groups dinsu na Manyan Mata
duk ta zama busy ko damuwa ba tayi na rashin waya da basa yi da A.M.
Tun daya ya tafi so daya suka yi waya bayan isar sa ya kirata lokacin tana tare da kawayenta
but tana dauka ta gaya masa tana busy zata kirashi idan ta gama abunda take,har yanzu bai sake
kiran ta ba itama bata damu da ta kirashi ba(Allah ya shirya).
AGLA
Ga surutun yan class da gulmarsu ga surutun yan group dinsu kanta duk ya yi mata ba dadi
domin batason hayaniya dagyar taga antashi daga makarantar suka dawo gida,ko a saman hanya
Amina firar abun da ya faru islamiyya take ko kala Aleeya(Agla)bata ce mata ba yayin da Salmat
ke dari_dari sanadin abunda ta aikata.
Duk tunanin da zatayi ta kasa tuna waye MUHAMMAD KABEER tana lure da duk wani motsi na
Salmat ko kala bata ce mata ba ta kyaleta ko abinci bata ci ba sanadin ciwon da kanta ke mata ta
sha maganin ciwon kai ta kwanta ko firar da suka sabayi da bappa yau basuyi ba.
Inna Saude na lura da ita ko kala bata ce mata ba domin ko ita yau bata jin dadi Salmat ta sosa
mata inda ke yi mata kai_kayi ko kadan batason tunawa da HALIMATU a Rayuwar ta.
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
DIYAH
{ Short story }
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number
2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number
09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number
09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 85~~86
Kwana daya kwana biyu amma Aliya bata cewa Salmat komi ba ko maganar bata tadda ba tun
Salmat na jiran sammani na fadan da zata sha har ta fidda rai ta sake jikinta ko a islamiyya tun
lokacin da su Maryam suka tada maganar suka ga iya gaskiyar tace batasan wani abu game da
Kabeer ba suka bar tada maganar,idan har wani abu suke son ji gurin Salmat suke zuwa ta fada
musu duk yadda akayi tun farkon haduwar Aliya da K.B.
A gurin Malam Nura kuwa a koda yaushe idan ya shigo class idonsa na kanta har tsarguwa take
duk da cewa yana dan basarwa amma saida yan class din suka saka masa ido cikin ma suna
shakkarsa fiye da sauran malaman islamiyyar.
Idan taji bata jin dadi a rayuwarta sai ta dauko Al-qur'ani ta ringa karantawa sai taji sanyi a
ranta,wani lokaci sai taji kewar Ummynta ta kamata (wato mahaifiyar ta) duk da cewa tun tashin
ta bata taba ganin ta ba sai dai a labari ko shi wani lokaci a gun mama Kareema.
Alokacin da take yarinya a tunanin ta tadauka cewa Inna Saude ce mahaifiyar ta sai daga baya ta
fuskanci bahakan bane, wata rana bata mantawa alokacin bakinta shekara tara Inna Laure kawar
Inna Saude ta aiketa da kud'i wani dan iska ya kwace shine fa tahau fada tana mata cin mutunci
har da zagin Ummynta.
A wannan rana ne tasan sunan mahaifiyarta,tasha kuka tana tambayar Bappa ina Ummynta take
tanason ta ganta Alokacin yake bata hakuri tare da sanar da ita cewa Ummynta bata raye ta rasu
kuma danginsa sune dangin Ummynta.
Bakaramin sab'ani Inna Saude suka samu da Bappa ba a lokacin wanda shine karin tsanar da Inna
Saude tayi mata ita da Ummynta.
Tabbas tana ciki kewar mahaifiyar ta sosai kuma har yanzu zancen Ummynta bai kara hadata da
Bappa ba.
INNA SAUDE
Ta gaji da cin magani ta sake fuskarta ya yin da suka cigaba da gudanar da rayuwarsu kamar
yadda suka saba,wani lokaci Agla taji sanyi a gunta wani lokaci tasha fada da hantara musamman
ma yanzu da kishin ya dan motsa mata ga aikin gida da take jibga ba abun da ya ragu.
Bayan sati daya da dawowar su sai ga Kabeer yazo gidan gaida inna harma ya yi mata Alkhairi
wanda yasakata a cikin farin ciki (kunsan halin Inna Saude da son banza😅)
A lokacin Kabeer bai samu haduwa da Baffa ba da Agla sun dai sha fira da Salmat wacce duk
rabin fira akan Agla ne har ya koma tana daki bata fito ba.
Sai a sannan tama tuna shima sunansa Kabeer ko shine Salmat ke nufi oho bata da mai b'ata
amsa sai kawai ta share ta cigaba da linke tufafinsu da ta wanke.
BAPPA
Mashaallah cigaba yana ta samuwa Allah ya sakawa shago Albarka kasuwanci yana dan bunkasa
dai_dai gwargwado yana iya kokarin sa domin tara kudin da zai biyawa Agla kudin WAEC gashi
ta zo kusa ana bukatar kudin registration.
Duk da cewa Makarantar gwamnati ce amma wai governor kudin NECO kawai ya biya duk
wanda ya zana WAEC to bazai yi NECO ba idan kuma kanason zana biyu sai dai mahaifanka su
biya ma dayan.
KABEER
Duk zuwan da Kabeer yake yi baya haduwa da Agla; sau daya ne ya taba haduwa da ita lokacin da
ya kai su Batul gidan su suka wuni, Inna tasakata yi musu rakiya.
Tabbas shi yasan Son Agla bashi yasakawa kansa ba Allah ne ya jarabcesa dashi kuma yana
fatan ta zama mallakinsa.
Bayan wani lokaci KABEER yaje ya samu mahaifinsa kan cewa yana son yaje gidansu Aleeya ya
nema masa Izinin Mahaifin Agla yana son fara zuwa zance gurin ta.
(Maryama kina ina 😅😂)
DR AYSHERT
Duk wani bincike wanda zatayi game da wurin da Haidar ya sauka ta kammala shi har ma tayi
booking flight jirgin ta zai daga gobe da safe inshaallah,duk wani shirinata ta kammala har
takardar neman izzini ta tura a hospital, yanzu haka waya take mom d'inta tana gayamata cewa
gobe jirginta zai tashi zata wuce India, cikin d'an nuna damuwa mom d'in tata take tambayar ta
"Dafatan kina lafiya Baby ko likata zaki je gani?"
"No mom kinsan yanayin aiki stresses yamun yawa kawai zance na huta ne na d'an wasu watanni"
Daga chan cikin wayar mom d'inta tace "eh hakan nada kyau baby but wata nawa zakiyi a chan"
"Nima I don't know just kawai ki sanar wa dad domin bazan samu damar kiran nasa ba kuma idan
na shigo Kano bazan shigo gida ba"
"Ok no problem nima cikin satin nan zan wuce Germany, safe journey"
"Ok bye mom luv u much"
Karfe goma na safe jirginta ya d'aga a SULTAN ABUBAKAR III INTERNATIONAL AIRPORT
{ SAI KANO TA DABO TUMBIN GIWA}
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
DIYAH
{ Short story }
Wannan littafi na kuďi akan farashi Naira #300 kachal.zaku biya kudin ta wannan account number
2136300504 Sanusi A nura U B A,sai kiyi screen Short ki turo ta wannan WhatsApp number
09066484295 ko kuma 08104093636.Za ku iya turo katin MTN na dari uku ta wannan number
09066484295 domin karin bayani sai ku tuntubeni ta wannan number 09066484295
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 87~~88
2hours 50m+ jirginta yayi landing garin Kano,Bayan wani lokaci jirgi ya dauke su sai NEW
DELHI.
Sun kwashe kimanin awa goma shadaya jirgin su na yawo A sararin samaniya kafin ya sauka a
INDIRA GANDHI INTERNATIONAL AIRPORT.
Wata kawar ta yar kasar India mai suna Shyla yar addinin Hindu ce ta zo ta dauke ta, gaisawa suka
yi da yaren Hindu,Direct Wani kawataccen hotel suka wuce mai suna RED FOX HOTEL;wani
kawataccen room suka shiga bayan sun karbi card na bude d'akin Already Shyla tayi mata
booking,komi da ke cikin room din tsaf_tsaf yake ba wani tarkace.
Bathroom tawuce kai tsaye domin ta watsa ruwa yayin da Shyla ta ke saka mata kayan ta a
closate ,bayan wani lokaci ta fito daga bathroom lotion ta shafa tare da parfum dinta mai
sanyayyen kamshi.
Shigar kananan kaya tayi wadanda suka kama jikinta yayin da tad'an tsakuri abincin da aka
kawo daga hotel din,da yake ta saba da cin abincin kasar bai wani bata problem ba.
Cikin yaren India suke magana yayin Dr Ayshert ke cewa shyla su wuce University din da take
karatu a chan ta matsu da taga Hasken Ruhinta,nan shyla ke sanar da ita cewa da wuya su riskeshi
a chan yanzu badan ta so ba ta hakura.
************
Bada b'ata lokaci ba Allhaji Sa'id ya riske Abban Ramlat game da zancen da Muhammad Kabeer
yazo dashi ya na neman ya yi masa rakiya a gun Mahaifin Aliya.
Abban Ramlat bai yi rejecting din bukatar Mahaifin Kabeer ba suka saka date din da zasuje.
Su ukku su ka je da Abban Kabeer da wani abokinsa sai Abban Ramlat sun tattauna sosai akan
maganar auren Aleeya da Kabeer ke so amma sai dai Bappa bai amince ba ya gaya musu cewa shi
bazai yiwa y'ar sa auren dole ba amma muddin tana son Kabeer d'in shi baya da matsala.
A takaice dai an bawa Kabeer damar zuwa zance gurin Aleeya idan har Allah ya kaddara ya yi
mata falillahilhamdu idan kuma akasin hakan ne suyi hakuri.
Haka Mahaifin Kabeer da Amininsa suka koma gida suna yaba karamci da mutuntawar da akayi
musu a gidan su Aleeya ya yin da suka bar Abban Ramlat a chan.
Bayan tafiyar su,su Bappa suka cigaba da tattaunawa shida Abban Ramlat inda yake nuna masa
cewa bawai ba ya son yiwa Agla aure bane amma yana son ta samu illimi sosai yana son cika
burin Ummynta akanta,shi kansa yasani cewa aure shine hutu ga Agla saboda aikin gida da take ya
mata yawa yana son ta samu hutu itama ta huta a rayuwarta .
Sannan matsala ta biyun shine Kabeer yana da mata, da so samu nai ne ya kasance mijin Agla
itace ta farko a gunsa kuma itace ta Karshe, duk da cewa yasan halin WASU MAZAN basa iya
zama da mace daya a rayuwarsu ko da kuwa sun maka alkawarin hakan amma shi yasan cewa duk
na mijin da ya aure mamana (Aleeya) bazai samu wurin korafi ba,ko kuwa yaji son sake auren
wata mata ba .
Yasan yadda zama da kishiya yake,yasan yadda HALIMATUS_SADIYA ta rayu a gidansa, baya
son wahalar da Ummynta tasha itama tasha irinta duk da cewa shi da Ummynta auren had'i ne.
Kwantar masa da hankali Abban Ramlat ya yi tare da bashi baki har hankalinsa ya d'an kwanta
sannan ya nuna masa cewa iyayen Kabeer mutane ne masu dattako da illimin addini kuma Kabeer
yaro ne mai hankali da natsuwa tabbas yana ji aransa muddin Aleeya ta auresa baza tayi dana sani
ba zai riketa da amana,sannan a duniya ba abunda yafi dadi ga yaran zamanin irin ka aura masu
wanda suke so in har ya kasance mutumin kirki.
Idan Allah ya kaddara cewa shi mijin tane sai kaga Allah ya dasa soyayya a tsakaninsu kuma
karatu ba yada matsala ko da auren zata iya cigaba da karatunta har takai matsayin da kake bukata
inshaallah.Ba abunda yafi Alkhairi a yanzu Mallam Yusuf (sorry nayi kuskure sunan mahaifin
Aliya shine Malam Yusuf but a page 39 na Abba Mukhtar ya kira sa da suna muhammad )face mu
rika saka su a cikin Addu'a Allah ya zab'ar mana abunda yafi zama Alkhairi A rayuwar su duka.
Sai Bayan karfe 5:30 sannan Abban Ramlat ya fito daga cikin dakin Bappa wanda Aliya ta share
tayi ma tsaf ta shimfida masu tabarma ta saka masa turare sai kamshi ke tashi a gidan duka ko ina
tsaf zaka ganshi.
Bayan Abban Ramlat ya yiwa Inna Saude sallama tare da aje mata dan wani hasafi sannan ya
wuce domin yasan halinta tsaf ba wuya take yi mata taci masa mutunci ba domin ba yau farau ba
gashi taga baki harda motoci,bakin garka Bappa ya raka Abban Ramlat ya shiga motarsa ya wuce
gida.
A cikin gidan kuwa INNA SAUDE ta kasa ta tsare tana jiran dawowar Bappa taji yadda akayi
kuma daga ina wadannan Bakin suke daga ganin su kasan mashaallah akwai abun hannu, ta na nan
tana jiran Bappa su Salmat suka yi mata sai anjima suka fita, anan waje suka tara da Bappa ya
saka musu Albarka suka kama hanyar Islamiyya .
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar
korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani
dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya
tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips
Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
Page 89~~90
INNA SAUDE
Shiru Inna Saude tayi tana sauraren bayanin Bappa game da Abunda wad'annan mutanen suka zo
dashi,bawai bata fatan Aleeya ta samu miji mai wadata bane amma taso ace Salamatun ta ce
wadannan Alhazawan suka zo neman auren ta.
Duk da cewa tasan muddin Aleeya tayi aure gidan masu kud'i zata wala fiye da sammani domin
Salamatu halinta ta dauko da shegen wayon tsiya amma zata so ta rayu cikin wad'ata.
Amma kuma miye abun damuwarta a ciki badai zata samu kud'i ba falillahilhamdu.
Dan tab'ata Bappa yayi ganin ta lula duniyar tunani yana cewa "
Acikin ransa kuwa yana fatan kar yan bakin cikin nata su motsa tace bata yarda da wannan abun
ba, ba tare da ya tabbatar da cewa mamansa na son yaron ba ko a'a.
Badole na shiga tunani ba, kana neman yi mana asara,arziki na kusanto mu kana nisantamu dashi.
Taya zakace sai ta kammala karatunta? amfanin uwar me karatun nata ke yi mana, kuma ai takai
munzalin aure idan bata yi auren ba mi kake so tayi, kana wata maganar soyayya,ita wannan
yarinyar ta ina tasan wata soyayya wacce a ko da yaushe cikin hijabi da likabi take.
Shin tsaya ma wai kama taba ganin ta ta tsaya da wani saurayin ko ka taba jin labarin hakan?
Ko dai Uwarta batayi auren soyayya ballantana ita, ni dai in har bata sonsa kawai a hada aurensa
da Salamatu yafi gwara nayi mata auren da wuri da na bari ta aure samarin anguwar nan da basa
da sana'ar yi, ko ni da nayi auren soyayya uwar me soyayyar ta tsinanamin.
Ita kuma sai kayi ta barinta cikin gida har tazama uwar mata ba mashinshini.
Shiru Bappa yayi yana sauraren zubar da Inna Saude ke yi shi baiga abun fada da habaici a ciki ba
duk da ta wani bangaren ta fadi gaskiya amma shi ya kudurta aransa muddin Agla bata son Kabeer
bazai yiwa y'ar tasa Auren Dole ba ko da kuwa zata yi shekara nawa ba aure.
Yayin da inna Saude tasa a ranta cewa muddin tana numfashi da yardar Ubangiji sai anyi wannan
auren domin baza ta ga arziki kuma taga tsiya ba,gashi duk yazo yana mata Alkhairi, ina ga ta
zama surukarsa.
Domin dai duk yadda za'ayi dole adai kirata da sunan Uwar Aleeya .
Wani munafukin murmushi tayi na ganin ta zama hajiya Saude gata zaune a cikin mota ana tukata
sai kawai ta kyalkyale da dariya.
Kallon ta kawai Bappa yayi ya kawda kansa yayin da yake mata Addu'ar Allah ya shiryeta ya rage
matason kud'i acikin zuciyar ta ya saka mata wadatar zuci.
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar
korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani
dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya
tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips
Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 91~~92
INDIA,NEW DELHI
Duk wani bincike da ya shafi DR A.M A ga me da wuraren da yake zuwa time din da yake fita etc
Dr Ayshert Mas'ud mai nera ta gabatar tare da taimakon kawarta Shyla Kumar.
Ako ina yake tana da kusa da shi except makaranta da kuma gidansa,da ace da hali ko gidan
nasa da tashiga but security na chan ba dai suke da na nan ba,gidansa nada matakan tsaron da ba
yadda za'ayi ta shiga ciki but duk hakan ba laifi tunda zata iya ganinsa daga nesa har ta shaki
kamshin sa.
***********
KABEER
kamar yadda abokanan sa suka bashi shawara ya dage da Addu'a da kuma sadaka yayin da yake
saka malamai suna yi masa Addu'a da kuma saukar Al-qur'ani.
MARYAMA
Ba yadda ta iya dole ta dauki shawarar mahaifiyar ta ta lura duk wani jidali,fitina da kuma haukar
da zata yiwa Kabeer baya kulata gashi ya maida gidansu gurin zuwa ko da yaushe yana chan wani
lokacin ma idan ya fita tun safe sai dare yake dawowa amma ta shirya tsaf domin maida
KABEER a tafin hannun ta kamar yadda yake ada sai abunda tace yake yi.
Don haka yau yana fita tasaka Ummanta ta turo mata kanwarta Nafeesat tayi mata gyaran gida
tare da girki.
Ba karamar wuya Nafeesat taci ba domin gidan yayi kahurar daud'ar tsiya wacce ba tada misali
musamman dakin Anty Gimbiya(Maryama) domin shi na Kabeer yana gyaransa lokaci zuwa
lokaci.
Kitchen ba magana wasu kwanukan ma har sunyi tsutsa wasu kuma sun bushe cikin ran Nafeesat
take cewa "wlh Anty Gimbiya ba karamar kazama bace yaseen yah K.B yana da hakuri"
Haka Nafeesat ta kwashe lokaci tana gyaran gidan sai biyu ta kammala sai kuma ta dawo d'aura
girki,tuwo da miyar ganye ta girka gidan sai kamshi yake tashi.
Misalin 6:30 ta kammala ta zuba a warmers tajera kan madai_daicin dinning table na su. turaren
wuta tafara yiwa gidan da dakunan Maryama ta amashe tana cewa "
Nace" toh Anty Gimbiya" tare da wucewa kitchen a raina nasan ba aikin Allah da Annabi bane tayi
mun.
Bayan tafiyar Nafeesat Maryama ta warware kullin da ke zanenta ta fito da kullin turarukan da
Ummanta ta amso mata da gurin boka Dajjal ta zuba turare har kusan kala ukku acikin kaskon
turaren tayi dakin Kabeer duka ta turareshi har toilet dinsa sannan ta fito pallon ta turareshi shima
tare da sakar gidan.
Tana cikin turaren Nafeesat ta fito daga kitchen, cikin toshe hancin ta da mayafin kanta take
cewa "
Haba haba Anty gimbiya Fissabilillah wannan wane irin banzan turare ne haka don Allah,abu ba
dad'in kamshi idan kasha keshi sai kanka ya tsara.
"bansani ba don Ubanki kinsan dai banason shishigi a lamurana Nafeesat don haka ki kama kanki"
"Allah baki hankuri Anty Gimbiya, daga tambaya sai zagi Allah huci zuciyar ki amma gaskiya na
fada kuma yanzun barmiki gidanki duk abunda zakiyi kiyi"
Gyara jikinta tayi ta dauki jakarta tare da kulolin da tasaka abincin a ciki ta sallama da Maryam ta
wuce.
Duk cikin littafan da take karantawa tafi son wannan book din domin yana bada wuta sosai.
Sai misalin takwas da rabi ta tashi ta shiga wanka tayo Alwala ta fara salla, magrib tayi sannan
Isha'I domin lokacin da akayi magrib tana karanta littafi ne baza ta iya ajewa ba(Allah ya shirya)
Bayan ta kammala Sallar wacce ko minti biyar ba tayi tana yinta ba ta shire hijab ta wuce gaban
mirror gaba daya ta game jikin ta da turen gurin boka dajjal sannan tayi na tsugunno sannan ta
saka wata arniyar sleeping dress ta dawo parlour ta hakimce tana taunar cingom tana danna
waya.Mantawa tayi bata saka magani a cikin abincinsa ba ta yi sauri taje ta bar_bada sannan ta
dawo ta zauna.
Ko minti talatin da zama ba tayi ba tayi kukan motarsa ya dawo gyara zaman rigar ta tayi tana dan
janye ta kasa yadda za su d'an fito su dauki hankalinsa.
Da bismillah ya shigo gidan tare da Addu'ar shiga gida wani irin kamshi wanda bazai iya tantace
tsakanin kamshi ko wari ya bugi hancinsa sai da kansa ya tsara cikin sauri ya lalibo Addu'a ya
rinkayi yana ida shiga harabar gidan.
Mamaki ! al-ajabi duk sun cika zuciyar Muhammad Kabeer addu'ar ma ta subuce a bakinsa sai
a zuci yake yi wai yau gidan sa ne ko kuwa ya yi b'atan hanya mai kammala tunanin ba yaji
Maryama a jikinsa ya yin da baisan time din da ta iso ba kawai ji yayi tayi hugging dinsa tana
cewa.... "welcome home my Habiby"
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar
korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani
dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya
tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips
Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 93~~94
Suman tsaye yayi yana kallonta ba tare da ya mayar mata da martanin runguma ba.Ita kuma bata
damu ba domin tasan dole ne ya shiga shock amma sai ta fuske kamar batasan yanayin da ya shiga
ba.
Kiss ta sakar masa a kumatu da kuma lips dinsa tare da jan hannunsa tana cewa..
Direct taja sa izuwa dakinsa, suka shiga ta zaunar dashi kan gadon tana cire masa talkami da
safa,da kyar ta bari yashiga toilet domin wasa ruwa ji take wani abu na fisgarta tabbas tayi missing
dinsa ba kadan ba.
Hannunsa ta kamo tana cewa "ur dinner is ready yayana"ta idar da kalmar cikin salo mai jan
hankali.
Bin bayanta yayi zuwa madai-daicin dining dinsu,sarving dinsa ta fara yi a plate dama ta saka nata
tun dazu kafin tasa magani ciki.
Ita da shi duk wani iri suke ji har ta manta rabon da ta girka masa abinci yaci duk da wannan ba ita
ta girka ba amma ko girkin ta mance rabon da a yishi gidan sai dai na siye.
Tun bayan aurensu da wattani ta daina girki ganin cewa ta mallakesa yadda takeso sai abinda
tace,shi kansa baya son yaga tana aiki,wanke-wanke da shara duk shi yake yi.
Ba irin tunanin da baiyi ba a cikin ransa wani sashe na zuciyarsa na ce masa Maryama ta shiryu ya
yinda wani sashen ya ki yarda haka kawai maryama bazata sauya lokaci guda ba tabbass akwai
dalili! taya zai san wannan dalilin yana bukatar sanin miye ya sauya Gimbiyarsa! anya wannan
sauyin na Allah da annabi ne ko kuma zancen da abokaninsa ke fada gaskiya ne? kai ina!! duk
rashin hankali na Maryama bazata aikata shirka ba.
Bismillah yayi sannan ya fara cin abincin tabbas wannan kamshin yana takurasa amma ya kasa
gaya mata hakan.
Haka suka raya wannan daren cikin soyayya da farin ciki mussamman Maryama ko shi kansa ba
dutse bane yayi missing din matarsa.
ALEEYA
Girki Agla ke kokarin daurawa inna Saude ta hana ta tana cewa ta barshi kawai itace zata girka
tawuce taje tayi wanka bata musa ba ta wuce dabi'arta ce bata jayayya da wad'anda suka girmeta
musamman ma wacce ta kewa kallon uwa wato Inna Saude duk da cewa Al'amurran da suka faru a
yau sun matukar daure mata kai but ba tanka ba kuma bata tambaya ba domin bata kokkofi game
da harkokin mutane iya nata idanu ne kawai.
Wanka tayi da wani sabulu mai kamshi da Inna Saude ta bata wanda tunda take bata taba wanka
da irin sa ba in ba gidan mama kareema taje ba sai dai goga_goga wani lokacin ma sai dai omo, ko
da ta fito inna Saude ta bincika komatsan tufafinta ta samo mata wata riga da zane da kallabi
wad'anda basu sha jiki ba na sallar bara ta fito mata da mayafi cikin kayan Salamatu duk tasan abu
ne mai wuya.
Vasilin ta shafa sannan ta saka tufafin duk da cewa tanason kamshi sosai fiye da sammani amma
bata saka turaren ba zuciyarta na ayyana mata cewa akwai inda Inna ke son aikanta shiyasa ta
sakata yin wannan shirin haka.
Tana zaune cikin dakin nasu Inna Saude ta shigo kallo daya ta mata taga ba laifi tayi kyau sosai
duk da kuwa fuskarta bata ga powder ba, sai vasilin din da ta murzawa pink lips d'inta kad'an,
"wuce mu tafi"
cewar Inna Saude tana juyawa domin fita daga dakin.
Dauko daya daga cikin hijab dinta tayi ta saka wanda ya d'an zarta guiwarta,hakika taga mayafin
da Inna Saude ta ijiye mata amma bazata iya fita dashi ba .
Bayan Inna Saude ta bi bayan ta saka talkaminta flat wad'anda Inna Saude tabata mamaki na sake
cikata.
Tabbas yau Innarmu(sunnan da suke kiranta da shi) na cikin farin ciki wanda batasan dalilinsa ba.
Gidan Inna Laure aminiyar Inna Saude ta ga sun nufa zuciyarta ta d'an buga domin tasan cewa
matar bata kaunarta ko miskala zarratin wani lokacin ma suna d'an samun sabani ita da Inna saude
saboda ita.
Inna Laure ta kasance mai bakar zuciya ga bakin kishi ya yin da Inna Saude ta kasance bakin kishi
kawai gareta sai kuma son kud'i wanda halinsu ne dukansu da'ace Agla hannun Inna laure take
azabar da zataci sai tafi uban ta Inna Saude.
Da mota a kusa da gidan amma Agla bata lura ba tana chan wurin tunanin yaushe rabonta ta taka
ko da kofar wannan gidan.
Da sallama suka shiga cikin gidan dakin Inna Laure suka nufa yayin da Aleeya ta yi tsaye a waje,
gaisawa suka yi Inna na fadamata cewa..
"ga Aleeyar nan ki kirawo Fa'iza ta tafi da ita kinsan ba sanin kan gidan naku tayi ba ni kuma bai
kamata na tafi zogo-zogo dani ba"
dariya mai kama da yake Inna laure tayi duk da cewa ranta ba dad'i tana kwala kiran sunan Fa'iza
Da d'an gudu Fa'iza tazo wacce sa'ar Salamatu ce ta shiga dakin,bana jin abun da suke cewa sai ga
yarinyar ta fito tare da Inna Saude.
"nasan halin ki baki kaucewa maganata da kuma ta Bappanki don haka kar ki kuskura naji kin yi
wani abu wanda ba dai-dai ba ki je ciki zaki hadu da wanda zaki aura"
Shiru Aleeya tayi tana sauraren Inna a ziciyarta kuma tana mamakin wadannan zantukan da kuma
wani zancen wanda kunnuwanta keji kamar almara.
Bin Fa'iza take harzuwa wani dakin wanda da'alama dakin Hindatu ne domin ya banbanta da duka
dakunan gidan har tv plasma da kuma fridge akwai ciki,kallo daya ta yiwa dakin ta fuskanci
hakan.
Da sallama suka shiga cikin dakin ya yin da sallamarta tayi ta cikin nusuwa kuma sautinta bai fita
sosai ba,wani kamshin turare ya bugi hancinta mai dad'in kamshi har a zuciyarta turaren ya yi
mata sosai, a tunaninta turaren da Hindatu ke amfani dashi (Hindatu ta kasance yaya a gurin
Fa'iza,itace diyar Inna Laure ta fari )
Zaunawa tayi bisa kujerun dake cikin dakin madai-daita ya yin da kanta yake kasa,ita fa bata lura
da waye a cikin dakin ba a tunaninta babu kowa,idan kuma hakane me yasa Inna Saude ta turo ta
nan da kuma waye zata hadu?
Ahankali ta dago manyan idanunta masu dauke da zara-zaran eyelashes ta kalli kujerar dake
gabanta caraf idanuwanta suka sauka cikin na.........
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar
korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani
dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya
tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips
Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 95~~96
A hankali ta dago manyan idanunta masu dauke da zara-zaran eyelashes ta kalli kujerar dake
gabanta,caraf idanuwanta suka sauka cikin na yayan su Batul sai kuma wani mutum a tare
dashi,gaida su tayi a hankali tare da dukar da idanuwanta kasa a ranta tana cewa ko shine?
KABEER
Wani sanyi yaji a cikin ransa a lokacin da ya yi tozali da sahibarsa ga kuma sanyayyiyar muryarta
ta rasa kunnuwansa a lokacin da tayi sallama,wani irin kyau take kara masa a dak lokacin da ya yi
tozali da fuskarta.
Kallonta yake har tazo ta zauna batare da ta lura da shi ba,wani irin yanayi ya shiga a lokacin da
dara - daran idanuwanta masu haske kamar madara suka shiga cikin nashi.
Shiru dakin ya dauka na d'an wani lokaci kafin abokin Kabeer ya fara magana.
************
MARYAMA
Tsafi aka ce gaskiyar mai shi tabbas hakane domin kuwa duniya tayi mata dadi ba kad'an ba duk
abunda tace Kabeer nayi mata ba jayayya sannan baya iya mata korafi ko kadan.
ita kuma ta rage kazanta ganin cewa har da itace karin abunda ke kara sasu samun sabani ita
da shi,bazata iya aikin ba kuma bata bukatar y'ar aiki saboda tana da tsanin kishin bala'i mara
iyaka.
Almajiri tasa Ummanta ta nemo mata, shi yake mata shara da kuma wanke-wanke.Girki kuma
wani lokacin Nafeesat ke zuwa tayi wani time kuwa ya siyo musu na waje,tsawon sati guda kenan
ba ta da matsala duk tana son tabbatar da cewa yana zuwa gidansu ko aa amma ba wata hanya
domin sun samu sab'ani da Inna dije wacce ke kawo mata rahoto.
A ganin ta yawan zuwa gidan su da yake yi shike saka aikin da take yake warwarewa
************
Inna Saude ce zaune tana duba kayan da Kabeer ya kawo da yazo zance farin ciki take ji ba iyaka
ga kuma kudi kimanin dubu ashirin na zuwa jin kira ga kuma turaruka da kuma kayan chocolate ta
rasa ya zata yi don farin ciki a yayin da Inna Laure ke zaune kusa da ita kamar ta hadiye zuciya
wani irin bakin ciki take ji idan ta kalli kayan wai kuma na waccan tsinanniyar yarinyar ce ina ma
ace na y'ar ta Hindatu ne ko kuma Salamatu amma wannan shegen yaro bai ga wacce zai cewa
yana so ba sai waccan yarinya mai kama da mayu ga kyau kamar tsason larabawa.
Ba yadda bata yi ba da Inna Saude amma Inna Saude taki y'ar da maganar ta tun lokacin da Inna
Saude ta sameta da zancen cewa wanda ke son mai tsada zaya zo jin kira kuma a gidanta za'ayi ta
hau tambaya ta dauka daya daga cikin matasan da ke anguwar ne ko kuma tsofaffi masu mataye a
cike ta hudu da ita masu rufin asiri amma kuma sai taji sabanin haka harma da motarsa,nan fa ta
hau baki amma Inna Saude ta nuna mata cewa fa ita bata da matsala da mijin da Agla zata aura
domin ita ma cigaban ta ne idan ta auri na kwarai ehhe(mai kudi shine mutumin kirki ko da ba
yada halin kwarai na kwaran shine banza musamman idan ba yada kudi)
Bata kara rikicewa ba sai da tayi tozali da shi d'an shawalwalin saurayi dagani ya surka da
hillani ga kuma kayan da ya kawo sai da kishi ya motsa mata wai wadannan abubuwan duka na
Saude ne a yanzun ma bare yarinyar ta zama matarsa ta lura yaron hannun sa a sake yake.ko yarta
da ke yawon ta zubar bai wuce ta samu dubu ukku ko biyar ba amma tashi guda ya bada
wadannan kud'aden,kai ina hakan bazai faru ba domin bazan taba bari ayi wannan auren ba
muddin bada Hindatu za'ayi shi ba sai na bi duk wata hanya na lalata wannan abun wallahi ba za'a
yi wannan auren ba.
Salmat da tadawo daga gidan kakarta Hafsu(mahaifiyar Inna Saude) tayi matukar farinciki sosai
ita har gani take yayan su Batul ya zama yayan ta itama tunda shi zai aure Addanta.
Inna Laure tayi zaman jiran Inna Saude ta bata na ta kayan amma shiru kuma ta ki tashi ta tafi duk
da cewa tana kishin mai kayan amma hausawa suka ce RABA MUGU DA MAKAMI IBADA NE
don haka takasa ta tsare tana jira ya yin da Inna Saude duk ta lura da take taken ta tashare ta, ai
itama tana da budurwa kuma tana samun abubuwa da yawa har tv ta siye amma ko kwandala
Laure bata taba bata ba da sunan abunda da mai son Hindu ya kawo ba don haka ta tattare takai
daki tace sai Bappa yazo ya gani ba yadda Inna Laure ta iya dole ta koma gidanta tare da daukar
Alwashi kala-kala.
Bayan Isha'I Bappa ya dawo harda tarba ya samu gurin Inna Saude yau ita ce da kanta ta kawo
masa abinci sabanin Aleeya da ke kawo masa kullum harda ruwan pure water guda masu
sanyi,abincin kuma harda naman dari biyar ta saka kuma da kud'inta,Bappa bai ce mata komi ba
amma yasan da walakin goro a miya matar dan sanda ta haifi barawo.
Salmat ce ta hau zolaryar Inna tana cewa "ah lallai yau Innarmu soyayyar ta motsa" ta na dariya
duk da Bappa sai da ya murmusa ya yin da Inna ta jefawa Salmat abun hitara cikin sa'a ta kauce
tare da mata dakuwa tana cewa "wlh Salamatu kin maidani taubashiyar ki sai na sabama miki zaki
yi hankali"
Hita batun ta Inna Saude ta yi yayin da tace su basu wuri zatayi magana da Bappansu,dakinsu su
shiga ita kuma ta kwaso kayan ta gwadawa Bappa ya yi fada sosai na karbar kayan da akayi
wannan ai riyace kuma shi bai tabbatar da cewa Agla na son nashi ba ko aa, ganin Malam na son
mata bakin ciki itama tahau nata baki dole ya yi shiru ya saka mata ido domin masifar Saude ba
yadda ya iya da ita, ce mata yayi ta rabashi idan bahaka ba wallahi sai an maida kayan nan gobe
goben nan ,ganin ya rantse ya saka Inna Saude shiru badon ta so ba ga magana cikin bakinta ba
halin furtawa domin ita kam bata hada dangantaka da hasara ba wannan bakin ciki da Malam ke
son yi mata da me yayi kama, ita kam bazata ga samu taga rashi ba a lokaci guda kamar mai bakin
uwa.
Gunguni ta dingayi a hankali ba halin magana,umurtarta yayi kan cewa ta kai kayan daki sai
gobe zai san yadda za'ayi dasu,cikin zaro ido take cewa "to ai nayi shiru banyi magana ba"
Hita batun ta ya yi sai da ta gaji ta kwashe kayan tayi hanyar dakin ta dasu yace mata idan ta kai ta
kira masa mamansa(Aleeya)
ALEEYA
Bayan Innarmu ta sanarmun Bappa na kirana na saka hijab din Salmat na tafi,a dakinsa na riske sa
yana zaune bisa tabarma sake gai da shi nayi ya amsa sannan ya hau yi mini tambayoyi game da
wadanda suka zo a d'azu shin ya yi min ko baimin ba shiru nayi bance komi ba domin ni bansan
amsar da zan bawa Bappana ba sake mai-maita tambayar yayi na daure na bude baki na cikin jin
nauyi na ce "Bappa ni ba ni da zabi a rayuwata da ya wuce zab'in ka,duk abun da ka zabamin a
rayuwata bazai kasance cutarwa a gareni ba idan har ya yi maka nima haka farincikin ka shine
farinciki na"
Murmushi Bappa ya yi domin har cikin ransa yaji d'adin bayanin ta sosai tabbas yana mugun son
yarsa domin shima zabin ta shine zabinsa damuwarta itace damuwarsa,farincikin ta shine nashi
farinciki, dubanta ya yi yana cewa "na yarda da abunda kika fada mamana amma ni bazan tauyeki
a rayuwar ki ba tabbas ni bana da matsala ko cewa kika yi bai yi miki ba domin ni bazan miki
auren dole ba nafison ki auri wanda kike so yake sonki wannan abun shine farinciki na, ki nutsu ki
yi tunani kiyi shawara da zuciyar ki idan har bai miki ba kada kiji kunyar sanar dani kinji mamana
domin duk shawarar da kika yanke itace nima hukunci na"
Shiru nayi ina sauraren mahaifina kaunarsa na da d'uwa a cikin zuciyata tabbas ba namijin da zan
so sama da Bappa na a duniya .
Cigaba Bappa ya yi da cewa "ki sani wannan hukuncin na ki babban hukunci ne wanda shine zai
hukuncin da zaki yankewa rayuwarki da ta y'ay'anki,ki sani zab'ar mijin aure wahala ne da shi
domin idan har kayi kuskure wurin zabar nagari to wannan kuskuren bazai tab'a gogewa ba a
rayuwaka da kuma ta y'ay'anka,rashin sa'ar abokin zama babbar illace a Rayuwa wacce bata da
magani, ki maida lamuranki ga Ubangiji ki mallaka masa zabi Inshaallah baza ki taba dana sani ba
a rayuwarki tashi ki tafi Allah ya yi miki Albarka"
"Ameen Bappa nagode sosai Allah ya saka maka da mafificin Alkhairinsa "
Dakin mu na shige ya yin da maganganun Bappa ke ta mun yawo a kwanyata ban ma lura da Inna
Saude ba wacce ke lab'e tanajin tattaunawar mu da Bappa.
INNA SAUDE
Duk da cewa ya ban haushi na cewa na ajiye kayan ba tare da nasan dalili ba amma kiran mai
tsada da ya saka nayi masa yafi komi daga mun hankali tsoro na daya kar tace yaron kirkin nan bai
mata ba wai Almajiri da zab'ar abincin da zaici ta zajamin asara shiya na labe ina sauraren hirarsu.
Bakaramin bugawa zuciyata tayi ba jin tambayar da Malam yayi mata shirunta kuma ya hargisa
min tunani kamar nayi wuff na afka cikin dakin amma ba halin hakan,wata nauyayyiyar ajiyar
zuciya na sauke jin amsar da tabashi karon farko da naji dadin soyayyar da ke tsakanin su domin
tayi min rana sai da naje na sha ruwa kan bushewar da makwagarona yayi sannan na dawo naji
shirmen da malam ke gayamata Allah na tuba shirme mana wace soyayya ce ba mu yi ta ba ni da
malam karshe mi ta jazamin face talauci duk da har yanzu ina son abina amma ko ba soyayya ana
rayuwa atare musamman idan kanada abin hannunka balle ma wannan yarinyar da bata damu da
soyayya ko kud'i ba.
Ko minti biyar Aleeya bata yi da zama ba Inna Saude itama tazo ta fara zubar ta,cikin tausasawa
take mata bayani wanda ya kara sanyayar da jikin Agla ta nuna mata cewa a matsayin uwa ne take
mata wannan bayanin.
Karo na farko da Inna tace mata haka a rayuwa har wani sanyi taji a zuciyarta wai Inna ce yau ta
kira kanta da sunan mahaifiyar ta farincikin hakan ya kasa boyuwa a fuskarta, lura da hakan Inna
ta ci gaba da nuna mata kirkin Kabeer da kuma nuna mata cewa Ahalinsa mutanen kirki ne zasu
karbeta tamkar su suka haifeta kannensa kuwa zasu riketa tamkar yayar su,ta kara nuna mata cewa
ko Bappa ya na son wannan abun amma bai nuna bane don kawai yana son jin ta bakinta, "don
haka idan har kin daukeni a matsayin mahaifiyar ki a duk shekarunan ina neman alfarma
guda,idan Bappanki ya kara tambayar ki kice masa kin amince wannan shi zai tabbatar min kin
daukeni a matsayin uwa ba matsayin kishiyar uwa ba kuma uwa bazata taba zabarwa d'anta abun
da zai cutar dashi ba Allah yayi maki albarka "
Kamar ta Allah Inna Saude ta tashi ta fita tanaji a ranta cewa MAI TSADA bazata taba bata kunya
ba,cikin dad'in rai ta kwanta ba tare da wata damuwa ba sabanin Agla da ta kwana cikin tunani
tare da neman zabin Ubangiji.
Tabbas wannan ranar zata kasance cikin ranakun da bazata tab'a mantawa ba a rayuwarta Inna
Saude ta kira kanta matsayin mahaifiyar ta na biyu kuma ta saka mata albarka abunda bata taba ji
ba abakin Innarmu ba tun tana yarinya har girman ta tabbas zata cikawa Inna Saude muradinta in
har hakan na cikin kaddarar ta.
Yayin da Inna Saude tayi kwanan farinciki sai safiyar yau ta kasance mata akasin haka,Aleeya da
tayi kwana jiya cikin neman mafita sai safiyar yau ta kasance mata kamar mayafin yaye
damuwarta farinciki ya wanzu a fuskarta ita da Salmat sab'anin Inna Saude da Fuskarta tayi kicin-
kicin Saka makon bakuwar da tayi musu zuwan bazata bakowa bace face Da.....
Zeesardaunerh ce
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar
korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani
dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya
tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips
Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
Duk abinda kake da bukata zaka iya nemana ta👉07037112549
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 95~~96
Ba kowa bace face Dadda mahaifiyar Malam Yusuf wato Bappa tsohuwa mai ran karfe,da gudu
Salmat taje ta rungumota tana mata oyoyo ya yin da Agla ta rike hannunta suna gaisawa da ita
cikin farinciki da kaunar juna.
Murmushin yake wanda yafi kuka ciwo Inna Saude ta aro ta yab'awa fuskarta itama ta shiga
jerin masu yiwa Dadda barka da zuwa tare da murnar ganinta.
Idanuwa kai Dadda ta zuba mata domin sarai ba halin Saude wanda bata sani ba.
Sosai Bappa ya yi farincikin ganin mahaifiyar sa ba kad'an ba duk da cewa daman yasan da zuwan
na ta,raba dare suka yi suna hirar yaushe gamo dukansu banda Inna Saude ta sharbi baccin ta son
ranta Bayan ta boye dubu biyar da kuma turare guda daga cikin kayan da Kabeer ya kawo na jin
kira domin baza a kasa dai_dai da kowa a bata ba,dame zata tashi kenan?gara walla tayi wa kanta
kaso kafun a kaiwa waccan tsohuwar cewa ga Dadda.
Tun da safe sai ga mama Kareema tazo ita da Ramlat,yah Anwar baya nan shiyasa basu zo tare da
shi ba gidan ya kara cika kowa cikin farin ciki sabanin Inna Saude da ke jibgar aiki, ta saba duk
wata wahala Agla keyi ita kuma tasha bacci son ranta amma yau komi ita keyi Dadda ta rike mai
sunanta ko ina suna tare ba batun wani aiki, da Aleeya ta tashi zata kirata tace ta dawo ta zauna ba
ta gaji da ganin ta ba tayi kewarta sosai.
Har vedio call sukayi da Mama yelwa babbar yayarsu(wato diyar Dadda ta fari ) dake yola a
wayan mama Kareema,taji kamar tayi tsuntsuwa tazo,Anwar ma haka sunyi vedio call da Dadda
har tsokanar ta ya dingayi haka ake yi, ayi doguwar tafiya baza a sanarwa miji ba gaskiya da sake
kar fa tasa yace ya fasa,ya dage sai janta fira yake alhalin zuciyarsa da ruhinsa suna kan Agla
wacce ke zaune a gefen Dadda batare da ta sanya hijab ba.
A ko da yaushe ako wane lokaci ko kuma yanayi muddin yayi tozali da fuskarta sai yaga tamkar
ana zuba mata madarar kyau ne wanda ke karuwa ko wani second,ba karamin farinciki yayi ba na
tozali da kyakkyawar fuskarta,tabbas hakurin sa ya kai intiha da yadawo zai sanar da Bappa cewa
yana mahaukacin sonta mara iyaka a taimaka a yi masu aure(🤣😂 an maka kutse yah Anwar,Agla
ta mai rabo ce Allura a ruwa)
Sai dare su mama Kareema, suka wuce Bayan sun tattauna da Bappa ga me da Kabeer kuma kudin
an yake shawarar ayi wa Agla amfani da su sai a cika sauran wurin jarabawar da zata yi ta WAEC
DA NECO ga kuma JAMB mama Kareema ta nuna masa cewa wannan abun ba riya bace ya zama
kamar al'ada bada kudin jin kira.
Ko da Bappa ya duba kayan da akace Inna Saude ta kawo yasan cewa tabbas ta tab'asu ba hakan
suke ba amma bai nuna musu hakan ba yasan halin mama Kareema ko kad'an basa shakar inuwa
daya da ita,kuma ba sa wani dogon shiri da Dadda kai kaf danginsa ba sa wani yin Saude ko kadan
illa shi da ya nace kan cewa yana son a barsa kuma sai ya Aureta.
Rashin son tada hasuma kar Inna Saude tace ba a yi mata adalci ba ya saka mama Kareema zage
nera dubu cikin jakarta ta hada da turare sai kuma chocolate da sunan a bawa Inna Saude amma
Bappa ya hana karshe ya rantse baza a bata kudi da turare ba sai chocolate aka bata ta karba tana
gunguni(oh ni Inna Saude ikon Allah, bayan duk abubuwan da kika d'auka hakan duk bai miki
ba😂🤣🤣)
Kuma mama Kareema takara nunawa Bappa cewa a bawa Aleeya lokaci kafin ta kare zana
jarabawar ta sai a kara tambayar ta idan har tanason Kabeer ko a'a kafin sannan ta san wasu daga
cikin halayyarsa da dabi'unsa kuma ya yi na'am da wannan shawarar harma da Dadda itama tace
bazata koma ba sai takwarar ta ta kammala zana jarabawar ta.
Sai dare Abban Ramlat ya zo ya daukesu ba don Ramlat na son tafiya ba Salmat sai gwalo take
mata.
Tashin hankali wanda ba a sama sa rana Inna Saude na cikin jimamin kud'in da ba'a bata ko sule
da yanzu bata d'iba ba shikenan duk wahalar ta tatashi a banza ta tabbata mai bakin uwa, sai kuma
taji sabon labari mai kama da Almara wai Dadda sai bayan wata biyu da kwanaki zata koma gida,
birkicewa Bappa ta yi sosai sai da ya taka mata burki mai tsauri muddin baza ta iya zama da
mahaifiyar sa ba sai dai ta koma gidan su, ya tafi ya barta da jimami. Dan dole tashiga hankalinta
duk da cewa Malam ya d'an tsufa amma kuma tanason abinta ba kadan ba domin kuwa ita soyayya
bata tsufa.
Haka Inna Saude ta koma komi na gidan ita keyi sai wani lokacin idan Aleeya ta faki idon Dadda
take kama mata da wani abun, wani lokacin kuma babu hali domin Dadda a dakinsu ta sauka komi
na Aleeyar ta saka masa ido cewa take ta dage tayi karatu kada duk shekarun da ta kwashe tana
karatu su tashi a banza.
INNA SAUDE MAI BAKIN CIN DADI wani gefe zuwan Dadda yayi mata rana domin kuwa
harda su taliya da macaroni na leda da masu kudi ke ci ba irin wadanda ake kullawa hamsin dari a
shaguna ba Abban Ramlat ya kawo a ringa dafawa surukarsa harda indomie da shinkafar
gwamnati, duk bayan kwana biyu idan ya kawo mama Kareema gidan idan yazo daukarta sai ya
siyo musu kaza ko kuma gasasshen nama .
Hakan ba karamin dad'i ya yiwa Inna Saude ba a ranta take tuna cewa itama wani lokacin haka
za a yi mata a gidan Aleeya da Kabiru kafin Salamatun ta takai munzalin aure.
Yawan zuwan Kabeer gidan ya saka suka saba da Dadda domin ta lura cewa yana da halin kwarai
kuma mutumen kirki ne ba karamin dace takwarar ta tayi ba na samun miji kamarsa.
A nan gurin ta ga kokarin Inna Saude da tunana goyon bayan ta akan wannan lamari batare da
nuna hassada ko kyashi ba.
Mama Kareema tasan cewa d'anta Anwar ya nason Agla amma bai bayyana ba, da so samunta ne
ace Aleeya ta zamo surukarta,da tayi dace sosai amma farin cikin Agla ya fi mata komai muddin
Aleeya na son Kabeer to ba makawa sai anyi auren shi kuma Anwar ya bawa zuciyar sa hakuri
domin duk abunda zai kuntata Agla basa kaunarsa,shi ya yi wa kansa da yayi ZURFIN CIKI da ya
bayyana kowa yasan da zancen da Abban sa bazai zo nemawa wani auren yarinyar da dansa ke
mugun so ba.
Duk weekend Batul da su Ramlat sukan zo gurin Dadda, sun dauketa kamar kakarsu haka itama
hankalinsu da tarbiyar su na burgeta tabbas Aleeya tayi sa'ar kannen miji.
Cikin yardar Ubangiji Agla ta zana JAMB dinta hankali kwance kuma results ya fito a lokacin da
suke WAEC Alhmdllh results ya yi kyau sosai .
Suma Batul da Fatima kannen Kabeer sun rubuta JAMB suma results ya yi kyau ba laifi yanzu
haka WAEC DA NECO suke rubutawa.
Wani lokacin idan suka zo gidan su Agla har lesson yake musu game da past Q kafin su kai ga
paper da za suyi tun Aleeya bata sakewa har ta sake domin tana matukar son karatu.
Lura da yadda Dadda ke yabon Kabeer ta fahimci cewa itama tana ra'ayin yaron ga kuma Inna
Saude da ke yi mata hannunka mai sanda kan maganar su.
Hayakin itace kam Inna Saude ta shashi yayin da ta fahimci wahalar da Aleeya ke yi wacce itace
ke girki tun da ta fara ta sawa har a yanzu,wani lokacin ne take d'an karbawa tayi amma da
busasshen icce ba d'anyu ba.
Alhmdllh kimanin wata daya da rabi su Aleeya na rubuta paper gashi an shiga wata mai sarki
watan Ramadan,kowa ya maida hankalinsa da IBADA tare da neman yafiyar Ubangijinsa gashi
exam dinsu ta kara daukar zafi duk cewa saura kadan su kare hakan dole Inna Saude ke aikin
gidan sai Salmat dake taimaka mata wani lokacin da wanke-wanke ko shara domin itama raguwa
ce kamar Inna Saude wani lokacin ma kwancin ta take a ranta tana cewa itama Innar ta d'andana
irin wahalar da Addar ta kesha a ko ne lokacin da kuma ko wane a zumin(😂).
Bayan Azumin ta na farko a gidan Bappa ba ta ba Azumin da ya yi mata dad'i irin wannan azumin
ba,taci kayan da'di sosai sannan kuma ta jibgi aiki kamar me.A lokacin Bappa yana da rufin
asirinsa sosai barin HALIMATUS_SADIYA gidan da kuma mutuwarta komai ya fara lalacewa
kasuwancinsa da komi ma.Tun daga lokacin talauci ya aure su.
Sai sha tara ga watan Ramadan suka kammala jarabawar suka samu hutu sai jiran sakamakon
jarabawa.
Dadda ta so ta koma gida Adamawa amma Bappa ya hana shi da mama Kareema ba yadda ta iya
anan tayi sallah karama cikin farinciki tare da jikokinta harma da Anwar.
Bayan Sallah Anwar ya shigo da zancen cewa yana son Aleeya, Bappa da Dadda suka bashi hakuri
domin nema cikin nema haramun ne suka nuna masa cewa matar mutum kabarin sa idan Allah ya
kaddara cewa Agla matarsa ce to zata zama mallakinsa ya fawwalawa Allah.
Ranar ba karamin zazzabi ya rufe shi ba ya yin da sai da aka kwantar dashi asibiti,duk wata
hanya da Aleeya zata san dalilin kwancin yah Anwar asibiti Inna Saude ta toshe ta domin har
abada bazata taba hwatan zama surukar mama Kareema ba Allah na tuba.
Ko ga sallar nan abubuwa iri-iri kabeer ya kawo mata batare da sanin Bappa ba tace zata bawa
Aleeya amma wasu ta bata wasu ta boye, shigar bukinta mai tsada za tayi dasu ta fito Hajiya
Saude.
Ko kad'an bata nuna musu cewa ga wanda ya kawo kayan ba,ta nuna musu cewa ita tayi mata su
ita da Salamatu.
Tun lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata abinda Anwar ke sanarwa Bappa da Dadda hankalinta
ya tashi duk da cewa Dadda na ra'ayin Kabeer amma kuma Anwar jikanta ne tasan cewa bazata
cutar da Aleeya ba,dole sai anjira anji zabin Aleeya. A yanzun tanason Kabeer ko a'a wannan
amsar ake jira kuma lokacin ba yarda wannan amsar ya yi don haka muddin aka samu matsala
Aleeya tace a'a shikenan fa duk fatan ta da burikanta ba rayuwa duk sun ruguje.
Shiyasa tasan duk yadda tayi ta boye wa Aleeya dalilin ciwonsa duk da bakowa ne ya sani ba,
Abun da kawai yaran suka sani shine ciwon son watace wacce basu san sunan ta ba yake
damunsa,ya yin da suke masa Addu'ar ta zama mallakinsa in har ita rabonsa ce.
Ko a hanya Anwar ya hadu da Kabeer ba ya amsa gaisuwarsa mugun kishinsa yake na tashin sense
duk da cewa preetynsa bata furta cewa tanason Kabeer ba kuma baya fatan hakan har abada.
Result din Agla ya fito ko wa yayi farinciki daga A sai B Credit ma guda daya ke gare ta WAEC
dinta tayi kyau NECO ce bata fito ba har yanzun .
Anyi walimar su Agla ta kammala makaranta cikin farin ciki,harda mahaifan Kabeer suka zo
Ummu da kuma Abba sai su Batul, Inna dije da tadawo daga tafiyar da tayi tace ba inda zata je.
Anyi komi lafiya Agla ta samu kyautar abubuwa daga masoyanta har da su Malam Ishak da
malam Ayub na makarantar su ta boko masu haukar sonta (inji Salamatun Inna tace har tumbi gare
su😂)sai kuma malam Nura wanda ya samu halarta,Amina da Maryam ne suka gayyace shi (duka
set guda ne ita da Aleeya in baku manta ba)Aisha da Rahama school dinsu daban.
Kallon kallo aka shiga yi a lokacin da suka hadu da juna kowa yazo zai mikawa Agla tashi
kyautar; Kabeer,Anwar sai kuma Malam Nura .
Daga karshe wucewarta ta yi da sunan an kirata domin ita bata fuskanci miye ma'anar wannan
kallon ba,sai su Rahama da Aisha sai kuma su Batul ne suka amsar mata kyautar domin su
Maryam da Amina kowa yana tare da jama'ar shi.
Ansha hutun gajiya ya yin da bayan kwana biyu da Walimar aka titse Aleeya da tambayar zata iya
auren Kabeer ko a'a?
Cikin yakini na cewa bazata batawa ko rai ba ta amsa "eh" domin tabarwa Allah zabi,ko a
sallolin ta a Ramadan tayi ta Addu'a Allah ya zaba mata abunda yafi zama Alkhairi a rayuwarta
batare da tasan cewa dan uwanta Anwar ya na son ta ba.
Ta amsa ne bawai don tanason Kabeer din ba kawai domin farin cikin ahalinta da kuma alhalin
Kabeer din. Ita bata san soyayya ba,bata san ya take ba kuma batasan yadda ake jin taba kawai
tasan cewa akwai d'an sabo da kuma yar sakewa wacce ta shiga tsakanin ta da Kabeer a wata ukun
nan .
A ranta tana jin zata iya zama dashi ba tare da kundura ba bata sonsa amma ba shike nufin cewa
tana kinsa ba.
Ba karamin farin ciki Inna Saude ta yi ba na cika mata burinta da Aleeya tayi tabbas ta tabbatar da
cewa Aleeya ta cika diy'a.
A bangaren su Bappa kuwa suma sunji dadin haka domin farincikin Agla shine farincikin su
gaba daya.
Kabeer kuwa baki har kunne ya rasa inda zai saka kansa sa bagen farincikin da yake ciki su Batul
harda karamin party sai da suka shirya.
Duk wannan abun da suke Inna dije na jinsu ta share ba fatan Alkhairi kuma ba mugun fata sai
bakar hassadar Ummu dake cinta sai kace kishiyarta, ji take ina ma ace basu samu sabani da
Maryama ba da yanzu ta feso mata wannan mummunan labarin nan tasan yadda za tayi itada
mahaifiyar ta a hana wannan auren amma ina! ko ita tana da zuciya a girji bazata iya jurar
Maryama ta dinga sakar mata maganar da taga dama.ko ita kanta zata iya zuwa gurin malamai a
hana wannan auren.(to fah 🤔)
kwanan bakin ciki sosai Anwar yayi har sai da takai an kara mai ruwa leda biyu duk ya rame sosai
sai ya baka tautsayi har rubutun dangana mama Kareema tasaka ake yi masa yana sha,ba karamin
saka ransa yayi ga Agla ba,zuciyar sa duk mallakinta ce.
Hankalin Inna Laure ya tashi ainun harma da Hindatun yar tata da taga kayan da aka kawo wa
Aleeya,gashi sai kashe kudi Inna Laure ke yi a gurin malamai sun tabbatar mata baza ayi auren ba
amma a banza gashi abubuwa sai kankama suke ba asirin dake kama Aleeya.
Sai kuma ta koma binciken Ahalin Kabeer idan akwai wanda baison auren su taru su ruguza shi,
cikin ikon Allah ta gane cewa Kabeer yana da mata Maryama amma Inna Saude bata sanar da ita
ba (to fah Inna Laure zata ballo mana August 888😜)
Dadda ta komawarta Adamawa domin fara shirin bukin jikarta wacce ta fi so a rayuwarta, ta jima
sosai tana jiran wannan lokacin tana kuma fatan Allah ya barta da ranta har ta ga auren Aleeyar
ta.
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
WASU MATAN
@2021
~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
🔔📚
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?
story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W
Assalamu Alaikum sunana Ummu Maleek
munada maganin Ni’ima macce duk rashin ni’imarta Insha allahu rabbi zataji ni’ima tamkar
korama ±💃💃💃💃
Muna da maganin infection ko wanne iri duk nacin infection Insha allahu rabbi kikayi amfani
dashi zai rabu dake
munadasu Tsumin kala kala Munada gumbar nonon rakumin munadata dabino
Akwai mallakar miji masu zamu🔥🔥wanda inki kayi amfani dashi mijinki ko dutsene shi saiya
tanka
Munada Emergency thghting duk yadda kika kai da budewa zaki hade tsaf Insha allah’ akwai hips
Elargenment akwai breast Elargenment
Munada kayayyakin mata kala da iri masu zafi🔥🔥tamkar boom😻😻sha yanzu magani yanzu
©️♤♡ Zeesardaunerh
Page 99~~100
Ana wata ga wata hausawa suka ce tashin hankali ba'a saka masa rana, hakanne ne kuwa ya
kasance a gurin Maryama domin kasa gasgata Inna Laure ta yi tana cewa ai wannan shirme ne ita
bazata taba yarda ba,duk da cewa zuciyar ta a saba'in take bugawa a lokacin.
Kai ina wannan abun karyane ta ya ma hakan zata kasance gareta,duk wata kofa sai da tasan ta
toshe ta bata bar wata kafa ba,to a ina Kabeer ya hadu da wata har ake batun aure kuma taya yaya
hakan takasance?
Korar Inna Laure tayi yayinda ta zurfafa a tunani, ko kadan bata taba lura da cewa Kabeer na boye
mata wani abu ba, a ina ma yasamu kwarin guiwar yin wannan tunanin batare da sanin ta ba? shi
da ko gardama da jayayya bai iyayi da ita,itace ke juyasa duk yadda take so acikin gidan wannan
abun bazai ta ba faruwa ba.
A haka ta kwana cikin zullumi da tunani batare da ta nunawa Kabeer komi ba zuciyar ta sai zafi
take, wutar bala'in kishi na kara ta'azzara cikin zuciyar ta,da ace za'a aunata a wannan lokacin da
tabbas za'a tarar da cewa jinin ta ya yi mugun hawa sosai .
Abunda Maryama bata sani ba shine duk tasirin asirinta a gida yake ko kuma idan tana tare dashi
amma da ya fita waje ba wani sihiri da yake tasiri a kansa face tana tare dashi ko a wajen.
Da niyar da safe taje gidan su wannan tsohuwar matar domin tana bukatar sanin gaskiya idan ba
haka ba zuciyar ta bugawa zatayi.
Allah Allah kawai take Kabeer ya fita gidan itama ta fita domin ba taga zama ba.
Bayan fitar Kabeer da kimanin mintuna goma sai ga Inna Laure a gidan duk wata shaida da zata
tabbatar wa da Maryama gaskiyar ta sai da ta nemo ta saka a cikin wayar Hindatu domin wannan
karon tare da ita suka zo .
Kamar zararra haka Maryama ta koma idanuwanta sunyi jawur sab'agen kishi ya yin da zuciyar ta
ta cigaba da bugawa da sauri_sauri ganin cewa fa tana iya zube musu anan ya saka Inna Laure jan
y'ar ta suka yi gaba yanzu ko ba komi tasan ta hadawa Kabeer boom wanda zai tashi da shi karshe
ma ya yi sanadiyar wargajewar auren kuma hakan take so.
Tun farko sai da tayi bincike sosai game da wacece Maryama kafin ta tunkareta tasan akwai
kura,idan ma batasa aka kashe Aleeyar kowa ya huta ba.
Dakyar Maryama ta saka hijab ta kulle gidan ta dau hanya tafiya take kamar wacce akace uwarta
ta mutu kafi babur ta tara sai anguwar su ya sauke ta.
Ko kad'an hawaye sun ki diga a kan fuskarta balle nauyin kirjinta ya ragu, tabbas ta san cewa a
wannan yanayin da take ciki zuciyar ta gab take da bugawa.
Tana shiga Palon ta tarar da Ummanta zaune saman kujera taci ado sai kamshi take tana latsa waya
ya yin da Nafeesat ke kallo a tv, ba wanda ya lura da shigowarta face jin kar zubewarta bisa
kujerar da Umman ta ta ke zaune a kai,a d'an razane dukkansu suka juwo kanta, ganin halin da
take ciki ya kara saka su rikicewa, hajiya hawwa duk ta daburce ta rasa wane taimako zata iya
bawa shalelenta.
Ruwa masu sanyi Nafeesat ta zuba a cup tayi Addu'a ta bawa Maryama tasha cikin ikon Ubangiji
sai nauyin kirjinta ya d'an ragu aiko sai hawaye sharr kamar karamar yarinya.
Tambayoyi Ummanta ta hau yi mata "Kabeer ne ya samu hadari?" ta girgiza kai "to sakin ki ya
yi?" shima ta girgiza kai "wai to mutuwa ya yi ne"shima ta girgiza kai tana cigaba da kuka,fada
hajiya hawwa ta hau yi mata tana tambayar ta miya faru ko so take sai zuciyar ta buga da wannan
shirun na ta ? sai sannan tace cikin shesheka "ai Umma da mutuwa ne yayi dama yafi mini bisa
abunda ya aikata min
wani kukan taji ya kara zuwa ya yin da bakin cikin ranta yake daduwa, ji take kamar ta gunce
harshen ta,cikin dacin rai da zuciya mara iyaka tace "Umma Kabeer yaci amanata ya yaudara
ne,Umma aure zai kara harma an saka rana"ta fashe da wani marayan kuka.
Wani ja baya Umman ta yi domin maganar ta shigeta ba kad'an ba amma sai ta dage ta hau yiwa
Maryama fada da kuma lallashi tare da alkawarin cewa wannan auren baza ayi shi ba in har tana
raye.
Dakyar ta samu ta lallaba Maryama ta koma gidan ta tare da tabbatar mata cewa wannan auren
sunansa babu ta kara daurata kan wasu hanyoyi na halaka ta kuma gargadeta da cewa kar ta
kuskura ta bari Kabeer yasan cewa tasan abun da yake kokarin aikatawa na cin amanarta domin
muddin yasan ta sani to aikin bazai tafi yadda suke bukata ba.Yadda yaci amanarta itama tayi
masa ta wannan sigar.
Ba hakan Maryama taso ba domin a yadda takeji ko kashe Kabeer tana iya yi idan ta ganshi kusa
da ita.
sai misalin shidda Maryama ta koma gidan yayin da take ganin komi na gidan ya koma mata baki
sai ajiyar zuciya take kamar kwad'o .
Bayan fitar Maryama gidan zage_zage hajiya hawwa ta hau yi tana durawa ahalin Kabeer
ashariya,wannan abun ma tatsuniya yake,y'artata yakeson yayi wa KISHIYA,shalelen tata?
Waya ta dauka ta kira babbar aminiyarta ta sanar mata wannan mummunan labari itama ashariya
ta zubo kamar dangin maguzawa nan suka hau shirye-shiryen zuwa gurin boka domin basu ga
zama ba wannan abun kunya da ke neman ya same su, wannan labarin idan sauran kawayensu da
sukaji sai a musu dariya makiya kuma sun samu abunda suke so wai d'iyar hajiya Hawwa da
Kishiya. Babu bokayen da bata sani ba a nan Arewa harma Kudu balle kuma Niger.
Ita ke zage damtse tayi iyayin ta ganin ba'a yiwa diyan wasu KISHIYA ba balle kuma
y'arta,yadda ta sane kalmar KISHIYA ko mutuwarta bata tsana hakan ba.
Da daddare lokacin da Kabeer ya dawo duk ya sukukuce ganin halin da gimbiyarsa Maryama ke
ciki ya ringa tambayarta mi yake damunta .
Baisan mike damunsa ba ko kadan baya samun nutsuwa in yana cikin gidan muddin Maryama
bata cikin farinciki ko ta kasance cikin bacin rai.
Lallab'ata ya ke yi domin yaji miyasa ka fuskarta ba wal-wala ya yin da takejin kamar ta caka
masa wuka tsab'agen bakin kishin da ke cinta.
Wayen cewa tayi ta nuna masa kanta ke ciwo shiyasa kuma ba karya ta ke ba kanta kamar ya fashe
kan ciwon da yake mata,magani ya b'ata tasha ya kaita daki ta kwanta dakyar baccin wahala ya
dauketa.
Yawan kiran da Ummanta keyi mata tana bata baki ya saka tad'an saki jikinta ga kuma
alkawarukkan da mahaifiyar ta keyi mata wacce a yanzu hakan suna chan gurin bokansu.
Asiri iri-iri ba wanda ba'a yi ba bangaren Inna dije,Inna Laure da kuma mai gayya mai aiki Hajiya
hawwa mahaifiyar Maryama akalla ba'a kasara ba sunfi zuwa gurin bokaye²⁰ ashirin ga kuma
malaman tsibbu masu fakewa da Al_qur'ani mai sarki suna aikata shirka babu irin sihirin da basu
yi ba amma ko kad'an babu wanda ke kama Agla,anyi ta yunkurin haukata ta ko kuma yi mata
kurciya amma ina basa iyawa da tsarin da ke jikinta wanda tun tana cikin ciki mahaifin Bappa ya
ke bawa Ummieynta tana sha kuma da aka haifeta ya kuma yi mata wani wanda ba wani asiri ko
tsafi wanda yake iya tunkarota balle ma har ya kusanto ta.
Sun kashe kud'ade ba adadi amma ko wane boka da malami abu guda suke sanar musu shine
baza'ayi wannan auren ba wasu kuma suna gayawa musu gaskiyar cewa tabbas za'a daura auren
amma kuma da wannan yarinyar ba gashi kuma sai kankama abubuwan buki keyi har lehe ankai
kuma har yanzu wannan zance Kabeer bai gayawa Maryama.
Ba irin asiri da Kabeer bai ci ya sha ba har wanka ma haka ga kuma turaren da kullum sai ya
shaqa amma duk da hakan ba suga alamun za'a fasa wannan auren ba .
Bakin ciki gurin Maryama kamar me ,A LOKACIN DA BUKI YA RAGE SAURA WATA DAYA
wani mummunan zazzabi ya rufeta wanda sai da ta kwanta asibiti ya yin da Ummanta ta shura
kafa sai India wurin wani mashahurin boka da ta samu labarinsa achan wanda zuwan ta guda gurin
sa.Duk wani aiki wanda ya ba manya malamanta wahala da kuma bokayenta tasan shi bazai bashi
wahala ba,dakyar ta samu ganawa dashi saboda tsabagen mutane da ke akwai a wurinsa harda
manyan mutane masu kud'i wadanda tasan su anan Nigeria da kuma manyan yan siyasa duk ta
gansu achan,tun bata fadamasa dalilin zuwan ta ya sani domin yayi bincike dakin tsafinsa.Wasu
abubuwa ya bata masu kama da gari da kuma wasu ruwa acikin kwalba sai kuma laya ya fadamata
yadda za'ayi sannan ya fada mata cewa dole ne Maryama ta bayar da jinjirin da ke cikin ta idan
bahaka ba makawa sai anyi wannan auren, sannan kuma daga yau karta kuskura ta koma yin salla
sai bayan wata daya kuma duk ta amince da wadannan shardodin nasa.(Allah ya shirya)
Duk wadannan surutun da suke wani ke fassara mata idan bokan yayi magana domin bata jin
yaren Hindu shima bai san da wani yare hausa ba.
Sosai hankalin Maryama ya kara tashi alokacin da likita ta sanar da ita cewa tana d'auke da juna
biyu wata ukku.Ita wai mi ke dawainiya da rayuwarta ne, tana cikin yarintar ta bata tsufa ba amma
masalsalu sunzo sun sakata gaba Innalillahi wa innaillaihi ra'jiun.
Malek ma rainonsa ya zame mata jidali ba kadan ba,mijin ta na neman kawo mata Kishiya
sannan kuma yanzu ace ga ciki ya akeson tayi ne da rayuwarta?
Bazata iya renon wannan cikin ba bare ma haihuwarsa dole ne ta zubda wannan cikin domin bata
shirya sake haihuwa yanzu ba.
Tayi farin cikin dawowar Umman ta daga India wanda dama ita ce take jira ta dawo da tuni ta
zubda cikin dake jikinta,hamdala hajiya hawwa tayi na ganin cewa Maryama bata aikata wannan
gangancin ba dama tana tunani game da jinjirin da boka yace domin ita tasan cewa Maryama bata
da juna biyu kuma ta kasance tana yawan yin planning don haka bata tunanin ciki gareta yanzu.
Duk yanda boka Shankar yace ayi duk saida ta tsare Maryama ta aikata a gidan nata bayan an
Sallamota daga asibiti yayin da layar suka sakata acikin pillon da Kabeer ke kwanciya ko yaushe,
cikin jikinta kuma aljanu sun sace sun kaiwa boka.
Farin ciki gun Maryama ba iyaka domin tabbas ta yarda da aikin wannan bokan kuma tanaji a
ranta cewa tafi karfin kishiya ba wata la'ananniyar da zata shigo mata gida.Hankali kwance ta
cigaba da gabatar da komi nata,maganar auren ma itace ta yiwa Kabeer maganar ta sigar turke
mutum gaba daya rikecewa yayi ya rasa amsar bata,kawai ta sakar masa kukan kissa tare da tashi
ta shigewarta d'aki harda saka key.
Hankalin Kabeer duk ya bi ya tashi yana tuna lokacin da Maryama tayi kwanciya asibiti
kwanciyar da baisan dalilinta ba, idan har lissafin ya bashi dadai kenan wannan labarin ta samu ya
sakata a wannan halin,bubbuga kofar ya yi tayi amma Maryama taki budewa,a ciki kuwa dariyarta
tasha kafin tayi kwanciyarta tabar shi da zullumi.
Ba abunda ke kara batawa Maryama rai bayan cin amanarta da Kabeer ya yi mata irin in ta tuno
yarinyar da Kabeer ya dauko yar karamin gida kuma wai ita zai hada kishi da ita,ita Maryama.
Hakika tasan Aleeya ta fita da komi na diri da kuma kyau domin yadda taga yarinyar a waya a fili
ma tafi kyau fiye da hakan,yadda taji labarin yarinyar tasan bazata iya kishi da ita ba ko kadan
domin itace zata juyata amma kuma hausawa na cewa dan hakin da ka raina shike tsole maka ido
kuma ta lura da take-taken tsohuwar gidan(wato Inna Saude)kuma ko ita tana da nata labarin
tabbas itama ba karama a bace kuma zata san hanyoyin da zata bi ta fitar da ita daga gidan kamar
yadda ta fitar da tata kishiyar,ko kadan matar bata da tsoro ga makiyi, don haka maganin bari kar a
soma bazata yarda ma wata akirata da sunan MATAR KABEER bayan ita ba.
KABEER
Tabbas yasan halin Maryama da shegen bakin kishi yana gudun taje ta yiwa kanta illa,har safe
Maryama bata bude kofar dama ba sallah take ba kuma ta samu daurin gindi wurin
boka(Wal'iyazubillah)
Yau Kabeer kasa hita yayi gashi abokanan sa nata kiransa game da shirye_shiryen buki lokaci ya
na ta kurewa amma bazai iya fita ya barta cikin wannan halin da baisan abinda zata iya aikatawa
ba.
Kiran mahaifiyar Maryama yayi tazo hankali tashe tana mamakin kiran gaggawan da surukinta
ya yi mata,da kyar Kabeer ya yi mata bayani cikin kunya da ganin kamar bai kyauta ba, wanda
yau ne karon farko da yaji hakan. Itama ci masa mutunci tayi iya iyawarta sai hakuri yake
bata,dakyar Maryama ta bude kofa jin muryar mahaifiyarta bayan tasakawa idanunta wani abu
suyi ja kace dagaske kukan tayi ko kallon Kabeer bata yi ba, hankuri mahaifiyar ta ta rinka bata
kamar tagari, ya yin da Kabeer yake zaune ya kasa cewa komi ganin Maryama ta sauko ya saka
Kabeer ya fita ya basu wuri ita da mahaifiyar ta.
Dariya suka dinga yi harda tafawa Maryama harda cewa "Allah Umma kin iya acting sai kace yar
Wasan hausa"
Murmushi Ummanta tayi tana cewa "kyale dan banza dama inajiran wannan damar domin na
zazzage abunda ke cikina na ci masa mutunci, amma ke ya akayi shalele kika kwana ba kici abinci
kuma hakama da safe kuma wai kukan gaskiya kikayi naga idanuwanki sun yi ja"
"Haba umma kyace bakisan ni ba ai duka sai da na shirya sannan nayi hakan" shiga d'akinta tayi
sai gata ta fito dauke da plates din taci abunci kafin ta kwanta da kuma cups din da tasha tea da
safe.
Abunda ta sakawa idanunta sukayi ja ta nunawa Ummanta sosai hajiya hawwa ta yaba da
kokarinta kafin suka cigaba da tattaunawa game da wasu al'amari wad'anda su kadai sukasan
abunsu .
Hajiya hawwa ta kara jaddada mata cewa ta saka masa ido duk abunda ake ciki ta sanar da ita.
Dakyar Kabeer ya shawo kan Maryama kafin ta sauko bayan ta kammala garashi babu daukar
lokaci ya kawo mata kayan fadar kishiya(ko nace kayan kashin laifi) dama tun da ya hada lehen
Aleeya itama yayi mata nata ya rasa yadda zaya kai mata sune,kuma ta yaya.
Ba laifi kayan sun yi kuma duk manya ne akwati ukku golden wasu daga cikin kayan iri daya ne
da na Agla colour ne ya ban-banta taji dadin kayan kuma taji kunci a ranta domin ko sunan kishiya
bata so balle ma wani abun da ya dangance ta amma hakan ta jure ya yin da Kabeer ya sakar mata
bakin aljihu tana kwasar kudi da sunan cewa itama zata yi wani event.
FAMILYN KABEER
Duk rashin mutunci da Maryama taje ta shuka a gidan su Aleeya Ummu taji domin lokacin da take
rashin kunyar ta su Batul suna gidan ta fada Inna Saude ta mayar mata amma Inna Saude ta ja
musu kunne kar su sanarwa kowa su kyaleta hawkar kishi ke damunta.
Ko da Ummu ta tambayi Muhammad wato Kabeer kan cewa ya sanar da matarsa cewa zaya kara
aure,ya kara tabbatar mata cewa bata san da zancen ba kuma lafiya suke zaune da ita.
Addu'a Ummu ta cigaba da yiwa d'anta tana sawa ana masa saukar Al-qur'ani da kuma sadaqa
tasan cewa akwai wani mugun nufi a ran matar d'an nata kuma baza ta barshi a banza ba akwai
abunda suke shiryawa.
Mashaallah ankai lehen Aleeya akwatuna shida sai kuma bakko daya mai shake da kaya,dangi na
kusa da wasu na nesa sun zo kamar buki, aka kai kayan sai yabon yarinyar da Kabeer zai aura
suke suna ya ba halinta ba irin matarsa ta farko wacce bata san darajar mutane ba yayin da wasu
sai bayan auren nema suka samu labari kuma suka je gidan ta musu rashin da'a shiyasa ko da
akace ta haihu kalilan ne suka zo ko jaririn dakyar aka bari suka dauka har wa yau baza su iya
cewa ga kamannun d'an Kabeer ba, kuma wasun su ko sunansa baza su iya kawowa ba.
Maryama akwati ukku aka yi mata aka barsu nan wajen Ummu domin Kabeer yace ba yanzu zai
kai mata ba sai ana saura sati daya buki,ita kuma ta zuba masa ido bata ce masa komi ba ya yin da
d'anta ke kara bata tautsayi na rashin sa'ar matar da bai yi ba.
Ana saura wata daya bukin ko nace kwana ashirin da dori yazo ya kwashi akwatunan cikin
farinciki, a taikaice yayiwa Ummu bayani ba tare da ya fada mata cin mutuncin da mahaifiyar
Maryama tayi masa da ita kanta Maryama, da Addu'a ta bishi tana rokon Allah ya kareshi daga
sharrin wannan makirar Macen.
*************
ASMA'U
Taci kuka sosai jin cewa Kabeer dinta zai kara aure wanda har yau har gobe wutar sonsa na
ruruwa a jinin jikinta,zuciyar ta na bugawa da tunaninsa, ya yin da numfashin ta ke fita da
sunansa.
Tayi kuka mara iyaka har kwanciya sai da tayi ya yinda tayi masa fatan Alkhairi da Addu'ar Allah
ya sa ayi lafiya akare lafiya .
Ta daure sosai duk da cewa tana azabtuwa ya yin da ta shiga ayarin yan kai lehe.
Tabbas ta yaba da zabinsa kuma Aleeyar ta shiga ranta ba kad'an ba ganin irin son da abin
kaunarta ke yi mata,ta sake sosai cikin su Aleeya ana shirin buki duk da cewa ba wani event da
za'ayi domin Amaryar tace bata son bidi'a amma duk da hakan saida suka shirya wani event guda
na kawayen Amarya.
Tayi kewa sosai na tafiyar Dadda ba kad'an kafin ta sake ga kuma fargaba duk da cewa wani
lokacin mantawa take da batun wani auren da zatayi yayin da Kabeer baya gajiya da zuwa,wani
lokacin kuma sai ya kwashe Sati biyu bai zo ba ko ma ya zo bawata firar kirki suke ba duk da
cewa yana iya kokarin sa gurin jan ta hira.
Rayuwarsu Suke gudanarwa kamar yadda suka saba a gidan amma ana samun sauyin wasu
abubuwa, aka ce lokaci baya jira haka suka kwashe wata ukku da kwanaki .
Wata rana suna cikin gida zaune da yake tunda ta kammala makaranta ba inda take zuwa tana
cikin daki zaune ita da su Batul da suka kawo mata ziyara,Salmat tayi makaranta Inna Saude kuma
tana cikin dakinta.yanzun ba laifi ta sake da su Batul sosai ba kad'an ba suna cikin daki suna hira
suka ji kamar hayaniya na tashi waje,fita sukayi dukkan su wajen,cikin waro idanuwa da tsabagen
mamaki Fatima da Batul suka hada baki suna cewa "Anty Maryama " kallon yadda take zuba
rashin kunya da rashin mutuncin nata nayi nasha jinin jikina a raina ina tunanin ko ita din
danginsu ce,to mine ne ya kawota ko auren ne bata son ayi?ba mai bata amsa chan naji Batul tana
cewa matar yaya K.B ce, gabana ya fad'i na rinka ambaton sunayen Ubangiji.
Cikin d'aki Batul da Fatima suka koma ya yin suke jin kunyar abunda matar yayan nasu ke
aikatawa a ko da yaushe a kowane lokaci suna dana sanin kasancewarta matar yayansu kuma har
abada baza su daina ba, ina ma ace yayansu bai aure ta ba! inama ace adda Asmeey ce matarsa!
Ina ma ace da Agla ya fara haduwa ta kasance mallakinsa! wani lokacin suna jin cewa ina ma
inama ace ko kadan yayansu bai hadu da Adda Asmeey bare har ya hadu da Maryama a sanadinta,
amma kash kaddara ta riga fata domin bawa ba shi ke yankewa kansa kaddararsa ba everything
yana rubuce tun kafin zuwansa duniya Addu'a itace magani itace mai chanza mummunan kaddara
izuwa kyakkyawa.
Ita sam rayuwarta ta manta da zance cewa yana da mata kuma ko da tuna miye nata aciki amma
tabbas tasan cewa bazata ji dadin zama da wannan matar ba.
Maryama ta cigaba da cewa "ai kema da kika riske uwarta da ta rigaki zuwa sai da kikasan yadda
kika yi kika korata waje kika zauna ke ka dai,to bare ni da iskoni za tayi ina mai tabbatar miki
cewa muddin kika kuskura harma ta shiga gidan nawa ki tanadi likkafanin daukar gawarta domin
sai ta mutu fiye da daya"
Cikin bacin rai Inna Saude take mayar mata tare da karyata zancenta "ahir dinki yarinya ba abunda
kika isa kiyiwa mai tsada domin tasha tabara tasha yaseen ba mutum ba sai Allah,ke in banda kike
ballagaza wacce bata iya rike miji ba ahto ballagaza idan ba haka ba kuma idan har kin cika mace
mizai saka mijin ki kara aure abu haka dake sai kace muciya da zane kamar wacce ta rako mata
duniya,ki tsaya kiji ki kuma saurara da kyau idan har baki yi hattara ba wannan yarinyar tashiga
gidan tana nuna Aleeya wacce sai sannan Maryama takare mata kallo wlh sai mijinki ya koraki
gida domin ba wani amfani da zaki sake yi mai "
"Ni kuma ina d'aukar miki alkawarin cewa muddin wannan yarinyar taki ta shiga gidana sai ta
gwammace rayuwa da mutuwa sai na kaskantar da rayuwarta na wulakantata wannan kenan idan
harma tashigan balle ma ko kofar gidan bata isa ta taka ba da sunan MATAR KABEER domin
wannan auren sunansa babu,ni Maryama Diya ga Hawwa'u na daukar miki alkawarin cewa in har
ina numfashi a doron kasa ba uban limamin da ya isa ya daura wannan auren kuma mu zuba mu
gani"ta karisa tana fita daga gidan batare da ta saurari amsar da Inna Saude ke mayar mata ba.
Tabbas nashiga tashin hankali mara iyaka wanda ko kadan bazaka ganshi a fuskata ba kalamanta
sun tsaya cikin kwanyata kamar rubutun da akayi akan dutse wanda baya goguwa har abada .
Bakaramin tashin hankali Inna Saude ta shiga bawai na kalaman Maryama ba da tad'auka hauka
da kuma kishi a'a wannan abun da tayi gaban su Batul shine ya tada hankalinta tana tsoron su
Batul su sanarwa iyayen su tabbas tasan yadda mutanen nan suke da dattako ba za su yarda a cutar
da rayuwar Aleeya ba saboda d'ansu karshe kuma za'a iya fasa wannan auren haka kuma idan har
Bappa yaji to wannan auren sunansa babu domin bazai bari y'arsa tayi rayuwar wulakanci ba ita
kuma tasan idan aka fasa wannan auren mutuwa ne kawai baza tayi ba.
Kalaman Maryama sun daki zuciyar su Fatima ba kad'an ba kuma sun basu tsoro amma haka inna
ta rokesu kan cewa karsu sanarwa kowa ko da kuwa Salamatun, ta kara cewa su hita batun wannan
matar yayan nasu haukar kishine kawai ke cinta .
Lokaci yaja sosai yayin da babu ranar da kalaman matar nan basa maimaita kansu a kwakwalwar
Aleeya ya yin da ta kara dagewa da rokon Ubangiji,wasu abubuwa Inna Saude ke bata tanaci
wad'anda bata san na minene ba kuma bata saba da jayayya ba dole ko ba d'adi hakan take
daurewa taci.
Ana jibi za'a kawo lehe mama yelwa tazo ita da daya daga cikin y'ayanta mai suna Murjanatu
wacce sa'ar Aleeya yace ko nace ta girmeta amma kad'an .
Farin ciki gurin ahalin gidan ba'a misiltawa ranar da ta iso mama Kareema ta zo gidan domin
tayi kewar yay'ar tata sosai ba kad'an ba ko su Aleeya sun jima rabonsu da ita idan ba ta waya ba
da suke magana da ita wani lokaci.
Shirye-shiryen tarbar masu kawo lehe ita ta d'auki nauyi kuma Inna Saude bata da halin jayayya
domin mama yelwa ba irin mama Kareema ma bace tafi mama Kareema tsauri da tsare gida ita
takasance yayar Bappa ce ko kadan bata daukar reni gata yar boko ce ta iya abubuwa kala-kala na
zamani (Cewar Inna Saude 😂)
Duk shirin da akeyi a gidan mama Kareema akayi shi domin chan yafi dad'in aiki kuma tare da
Inna Saude akaje ba yadda ta iya,ita har ta manta shekara nawa rabonta da gidan baza ma ta iya
kawo ba.
Sosai zuwan Murja ya yiwa Agla dad'i aka ce jini ya wuce wasa nan da nan suka saba da juna.
Duk da cewa gidan mama Kareema akayi aikin amma nan gidan Bappa za'a kawo lehen.
Salmat da Ramlat sai Bilkisu kanwar Amina da kuma Fa'iza diyar Inna Laure suna chan gidan
mama Kareema suna taya su aiki, ya yin da kawayen Aleeya;Amina,Ummi(Maryam),Rahama sai
kuma Aisha suke nan gidan su Agla suna gyaran gidan tare da Murja da yake sai karfe hudu masu
kawo lehen za su iso.
Tsaf-tsaf suka gyara gidan suka saka turare sannan suka wuce gidan su Amina a chan suka zauna
da yake baya da nisa da gidan su Aleeyar suna ta labarai irin nasu na yammata harda labarin
malam Nura wanda ya daina zuwa Islamiyya saboda tabbatarwa da yayi ya rasa Agla kace
dominta ne yake zuwa makarantar.
Karfe hudu shiyar ta dauki bakuncin motoci har mota biyar wurin kawo lehen Agla.
Tarba ta mutunci suka samu wacce su kayi farinciki da ita tare da ya ba zabin d'an su da ya dauko
a ahalin mutumci.
Basu kara yabawa da zabin sa ba sai da suka yi tozali da Agla tamkar balarabiya tana sanye da
wata Abaya mai mugun kyau wacce mama yelwa tazo da ita domin ita, ta aza mayafin bisa kanta
ga gashin kanta da yasha gyara gurin Murja ya kwata yayi kyau kamar ba nata ba, duk da cewa
tana kula dashi sosai.
Duk sai taji kanta a takure na rashin hijab din da babu a jikinta, idanuwa sai yawo suke a kanta
gashi ita ko kadan batason yawan kallo.
Anan su Batul suka zauna basu bi sauran mutanen ba su da wata mata wacce ta girmesu mai suna
Asma'u,akwai ta da son mutane nan da nan suka saba da Murja da kuma su Amina.
Tabbas Agla ta chan-chanci sunan ta mai tsada abunka da Area ta tallakawa ko nace masu rufin
asiri zuwa kawai ana ganin kayan,masu farin ciki na yi masu hassada irin Inna Laure nayi ita dai
inna Saude ta kasa ta tsare gurin kayan kar a samu masu bakin hali mara dangana su yi musu
sata(ah to 🤣)
Sai bayan da kura ta lafa anka daina zuwa ganin lehen mama yelwa tasa aka kwashe su kayan
duka aka kai chan gidan mama Kareema domin yafi tsaro ba kuma yadda Inna Saude ta iya dole
tayi shiru sai kananan zantukan da take,dubu dari na dinki suma duk a hannunta aka barsu bayan
an fitar da kayan da za'a dinka domin wasu daga ciki duk an d'inkasu a chan.
Daren da mama yelwa zata koma tasaka Agla ta hada kayan ta, dama chan sunyi magana da Bappa
kan cewa zata wuce da Aleeya achan wurin ta kafin buki kuma ya amince mata duk da cewa baya
son Aleeya tana yin nisa dashi.
Da farinciki sosai Inna Saude ta tashi saboda sanin cewa yau mama yelwa zata tafi amma
farincikin nata ya koma bacin rai ganin da Aleeya zata ta fi.Ita fa bata fuskanta ba miye dangin
mijin nata ke nufi da itane ta fuskanci sun suke su nuna sunfi iko da Agla fiye da ita alhalin ita ce
ta rike har ta girma.
Ba yadda ta iya tanaji tana gani suka tafi Salmat harda yan kwallarta ganin cewa Addarta zata tafi
wani gun da ban batare da ita ba.
Tun tashinta da girmanta ko ina atare suke zuwa kuma suke kwana dole zatayi kewar yar uwarta
ba kad'an.
Bappa da su Mama Kareema suka yi musu rakiya har tasha da zasu tafi harda kwalla suka cika
idanunta tabbas zata yi kewar Bappa ba kad'an ba shi da y'ar kanwarta Salmat.
Yanayin yadda ta yiwa fuskarta ne kamar wata baby doll wacce keson yin kuka ya kara yi mata
kyau ba kadan ba,tun daga nesa yah Anwar ke kallon ta duk yadda yaso hana idanuwansa amma
ya kasa,ya jima sosai bai ganta ba a idanuwansa amma ako da yaushe fuskarta na cikin allon
zuciyar sa.
Suna tsaye motar ta tashi sai garin yola,ji yake kamar yaje chan ya sace ta su gudu a daura musu
aure.
Gida ya koma shiru-shiru babu Aleeya duk da da Inna Saude sai da gidan ya yi mata ba dadi da ba
Aleeya a ciki,ta saba da ko wane lokaci muddin Aleeya na gidan zatace Agla daukomin kaza,yi
kaza wani time har da fadan rashin dalili take mata.Tabbas hausawa sunyi gaskiya da sukace "KO
KARE MA YANA DA RANA BALLE MUTUM DAN ADAM MAI TUNANI"
GARIN YOLA
sosai Aleeya taji dadin zama gurin mama yelwa duk da cewa kewar su Bappa na damunta,gyara
kala-kala mama yelwa ke mata ya yin da kyawunta sai kara fita ya ke yi sai abubuwa da ake bata
tana ci da kuma nasha wai maganin sanyi ko mine haka oho.
Turaruka iri-iri Anty Amrah matar yaya Umar (baban d'an mama yelwa) ta kawo mata na wanka
da kuma na jiki,matar tana son mutane ta dauki Aleeya kamar kanwarta wasu abubuwa idan tana
koyawa Agla har kunya take ji kamar ta nutse,kari harda labarin da taji ga Murja cewa wanda zai
aure Aleeya yana da mata shiyasa itama ta zage damtse tana kara gyarata ciki da waje domin
yarinyar ta shiga ranta ba kadan ba.
Ga turaren da mama yelwa ke yi mata ko ina na jikinta kamshi yake kamar me, ga kuma dilka da
halawa.
Rayuwar gidan mama yelwa rayuwa ce mai ban sha'awa duk da cewa ta manyanta amma jikinta
na fulani baya nuna shekarunta.Mijinta Al'ameen dan kasuwa ne kasuwanci yake yi amma yanxu
ya barwa babban dansa wato yaya Umar.
Y'ayan mama yelwa biyar amma biyu sun ratsu wato hasana da husaini yannen Murja, yaya
Umar shine Babba sai su Anty Hasana wadanda suna da shekara tara Allah ya karbi abunsa sai
kuma Murja da kuma auta sadiq mai shekara sha hudu.
Yaran yaya Umar biyu da Jauhar da kuma jafar yan biyu ne masu kyau abunsu akalla zasu kai
shekara biyar,yaran akwai shiga rai ga Agla da son yara,wannan shine abunda yakara saka anty
Amrah kaunarta ganin irin kaunar da take yiwa yaranta.
Ana saura sati uku buki suka dawo Adamawa gurin Dadda itama tayi nata gyaran,mutanen da ke
makawaftaka da Dadda sunyi ta mamakin girman Aleeya da kuma kamannunta da mahaifiyar ta
kamar an tsaga kara,su a wajensu ba'a dadewa da yarinya ta tasa suke mata aure abunka da
mutanen Ruga.
Buki ya rage saura sati biyu ya yin da suka dawo Sokoto ita da Dadda da mama yelwa sai Murja
da sadiq.Anty Amrah sai ana saura sati daya buki zata zo inji yaya Umar.
Inna Saude sakin baki tayi ganin irin kyawun da mai tsada takara yi wanda ba'a magana hakama
Salmat harda tambaya tana cewa "anya Addana ba sauyaki akayi ba" sai tabawa su mama dariya
Dadda na cewa "kibari idan zakiyi aure sai a kai ki a sauyakin"
Bappa sosai yaji d'adin ganin mai sunan Dadda cikin kwanciyar hankali ga kuma kyau da ta kara
hakan sai ya tuna masa da Ummynta.
Shirye-shiryen buki ya kankama ta kowane bangare ya yin da baki sauka kawai suke,su Anty
Amrah har su iso.
Su Amina sunyi ta yiwa Agla gunguni da tace baza'ayi event ko daya ba sai walima amma duk da
hakan sai da suka gudanar da ranar kawaye tare da taimakon Anty Amrah da Murja sai kuma
Asmeey (Asma'u).
A gidan Mama Kareema aka gudanar kuma event din yayi kyau ba kadan ba harda mai decoration
su Batul suka dauko domin su buki na su ne,gasu gefen amarya ga su kuma kannen ango.
Event din da aka shirya karami sai gashi ya koma Babba harda anko su Amina suka yi batare da
sanin Aleeya ba,sai da event din yayi nisa sai ga ango da abokansa sunci wankan shadda da babbar
riga kalar ankon yan mata yayin da shaddar ango ta kasance kalar kayan amarya sai kuma Batul da
Fatima kalar nasu tufafin daban yayin da Salmat da Ramlat suma nasu daban harda mai hoto aka
dauka.
Bakaramin baci ran Aleeya yayi ba da ya kasance bata da mayafin kirki a jiki domin da tace zata
saka hijab karar ta suka kai gurin Inna Saude kuma sukace mata mata ne kawai amma gashi kuma
harda maza.
Sam ko kad'an su Amina basu san da zuwan abokan ango ba ko su kansu,kuma sun san ran Agla
ya b'aci ba kad'an ba sanin kansu ne idan ranta ya baci bata magana sai dai tayi shiru.
Kamun kafa da mama Kareema suka yi ta lallasar musu Amarya domin sun san sunyi laifi .
Ko Inna Saude ba'a barta abaya ta zage tana gyara Aleeya ita da mama Kareema kowa nayin
nashi,abubuwan har sun fara isar Aleeya ba kadan ko ina ta gifta sai kamshi ya tashi a gurin.
A ranar friends day Kabeer rikicewa ya yi ganin kyawun da Aleeya ta kara ji yake kamar ya
maidata ciki wani yanayi yake ji akanta na mussamman ga dan karamin bakinta da ya sha jambaki
wanda shine karon farko da ta saka shi a rayuwarta,ji yake kamar ya kama karamin bakinnan nata
ya shanye jambakin nan tass amma bayason yasaka mata tsoron sa sannan wannan abun bai dace
ba zata iya masa kallo na daban.(adai kara hakuri angon balarabiya😉😂)
Sunan da abokansa ke masa kenan wai Agon Balarabiya domin yaseen sun dauka Agla balarabiya
ce ko ta hada jinsi da larabawa.
Inna Laure ba'a barta abaya ba tasan halin Inna Saude rass shiyasa itama ta siye kayan mata masu
inganci da turaruka takai nata gudummuwa,kan tsabagen mugunta duk da hanata ba Aleeya kayan
mata da akayi amma sai da tayi yadda zatayi Agla tasha su,a ranta so take yar banza taci wuya
domin ta yarda da malamanta sosai tasan cewa wannan auren baza ayi shi ba.
ANWAR
Ako da yaushe yana kallon hotunanta wadanda mama Kareema ta aza a status na ta na ranar
kawaye,duk da cewa yasan zata zama mallakin wani amma sonta bazai gushe a cikin zuciyar sa
ba.yana ji a ransa cewa baza a samu wani namiji wanda zai so ta kamar yadda shi Anwar yake
sonta ba.
Anan gidan Bappa akayi wankin amarya yayin da mata suka ta fashe korai,kid'i kawai ke tashi
yayin da masu rawa ke shan rawar su hayaniyar sosai take damun Aleeya har kanta ya fara ciwo.
Batasan mike damunta ba tana yawan ji faduwar gaba ba kadan ba duk da cewa tana fargabar
auren amma ta rasa faduwar gaban ta miye ? Bawai batason auren ba amma kasalar da takeji ta
micece itasan tasan ba wanda ta ke so a rayuwarta ko wanda takejin sonsa a ranta amma miyasa
takejin cewa kamar tana shirin rabuwa da wani abun wanda ke da kusanci da zuciyar ta ?
Babu mai bata wadannan amsoshin kuma bata iya sharing felling dinta da kowa domin bata saba
da hakan ba.
Shiyasa kewar mahaifiya yayi mata yawa,Uwa ta daban ce itace zaka sanarwa damuwarka batare
da shakku ba kuma ta baka shawara ta kwarai,tayi kewar aza kanta bisa kafafuwan mahaifiyarta ta
kwanta kamar yadda taga Salmat nayi,tayi kewar abubuwa da dama wadanda basa misiltuwa.
Daren buki mata sun zage sai aiki suke ko wacce tasha lalle da kitso gwanin burgewa,duk rashin
son Agla da kitso mussamman kanan ba yadda ta iya haka aka yini ana mata shi gashi Allah ya yi
mata baiwar gashi ga cika ga tsawo tubarakkallah mashaallah,lalle ma ba'a magana domin
kwararriyar mai lalle Asma'u tazo da ita ta zana ma amarya da yan matanta.
Tun da safe suka yi waya da Kabeer wanda ya dame Batul sai da takaiwa Agla wayar,hakan kawai
yaji yana son jin muryarta,bayan sun gaisa tayi shiru domin batasan mi zata ce masa ba shima
shirun ya yi na jin saukar numfashinta ta cikin waya.
Kwana biyu ya rasa mike damunsa haka kawai yake jin kamar zai rasata kamar baza ayi
wannan auren da shi ba,gashi sai mugayen mafarkan da yake masu ban tsoro.
Mijin mama yelwa da kuma yaya Umar duk sun sauka tare da fridge da yaya Umar ya kawo wa
Aleeya kyautar aure sabo dal cikin kwali.
MASU IYA MAGANA SUKA CE RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA
ALKAWARIN ALLAH YANA SHIRIN CIKA YAU NE ZA'A DAURA AUREN ALEEYA
YUSUF MUHAMMAD DA KUMA KABEER SA'ID IBRAHIM
A lokacin maza ke shirye-shiryen zuwa daurin aure a lokacin WASU MATAN ke sauke tukanen da
suka daura na yan daurin aure ana sakawa cikin takeaway.
Bakin kafar gidan su Aleeya tsit domin a Babban masallacin unguwar za'a daura auren yayin da su
Aleeya da kawayenta suke zaune gidan Inna Laure kusa da gidan nasu domin gidansu a cike yake
baza suji dadin sakewa ba.
Masu zuwa daurin aure sun ci ado sosai musamman ma Bappa fuskarsa cike da farin ciki mara
iyaka.
Sanye yake da shadda ruwan habdi,daya daga cikin kayan da Abba Mukhtar ya aiko masa, tayi
masa kyau ba kadan ba.Hakuri sosai Abba Mukhtar ya bawa Bappa kancewar ba zai samu damar
zuwa ba saboda a yau jum'at zasu gudanar da babban taro tare da D'an mai ma'aikatar da yake aiki
kuma taro ne da yazama dole ya halarta amma inshaallah zai zo shida iyalansa ko da bayan buki
ne tare da aikowa Agla kyautar fridge LG da kuma babban gas cooker sai dinkunan da ya yiwa
abokin nasa.
Anshirya amarya cikin leshi mai kyau baki daya daga cikin kayan lehen ta,tayi azababben kyau
mara mitsali sai kyallin amarci fuskarta keyi.
Inna Saude itama taci ado tafito sak uwar amarya kai kace wata hajiya ce,suma su mama Kareema
da mama yelwa da sauran mutanen da ke gidan kowa ya ci ado ana jiran dawowar y'an Dauren
aure.
Haka rayuwar duniya take kana taka Allah na nashi shiyasa ake son ko wane bawa yabarwa Allah
zabi domin komi na duniya mukaddari ne daga Allah,ba wanda ya isa ya kaucewa kaddarar sa ako
ina yake a kuma ko wane irin yanayi.
Mutanen da suka je daurin auren cikin farin ciki sai gasu sun dawo cikin damuwa mara
iyaka,faduwa Bappa ya tashi yi a lokacin da Kabeer yace ya fasa auren Aleeya a tsakiyar lokacin
da ake kokarin daura auren kuma ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunsa muddin akayi
gangancin daura wannan auren to su sani a take anan gurin zai mata saki uku.
Kwakwalwar Bappa ce ta dena aiki yayin da wani abu ya gifta a idonsa sai da ya abanci
"Innalillahi wa innaillaihi ra'jiun" taresa Baba Al'ameen ya yi mijin mama yelwa ganin cewa zai
iya faduwa a wannan wurin kuma kamai zai iya faruwa dashi.
Masallacin daurin auren ya koma wurin cece kuce kowa yana fadin Abarkacin ba kinsa yayin da
Ango Kabeer ya zube a gurin bayan mahaifinsa Alhji Sa'id ya wanke sa da mari hagu da dama
kuma ya rantse sai an daura wannan auren ba fashi shi ko Kabeer ya dage muddin aka daura
auresa da Aleeya sai ya saketa saki uku, duk mai hankalin da ya kalli Kabeer a wannan lokacin
yasan cewa baya cikin hayyacinsa ko kuma yana da mutanen boye, karshe ma zubewa ya yi anan
wurin daurin auren sai da abokanan sa suka kwashesa izuwa
gidan mahaifansa.
Alhaji Sa'id kasa dagawa yayi daga gurin da yake kunyar abunda Kabeer ya aikata wa yar mutane
duk ta da baibayeshi da badon kar ya yiwa Kabeer baki ba ya ida lalacewa da ba wanda ya isa ya
hanashi tsinewa Muhammad Kabeer a yau dinnan.
Alokacin da labarin ya isa gidan su Kabeer ga kuma ango an kwaso Ummu sai da takai zaune
daga tsayen da take yayin da ta cigaba da kiran sunayen Ubangiji zuciyar ta tayi mata nauyi kamar
ta fashe.
Wannan abun da mai yayi kama,ya Allah ka basu ikon cinye wannan mummunan Kaddara da ta
same su.
A cikin dakin ta aka ajiye Kabeer yayin da aka kira makwafcin su likita domin ya dubashi.
Yanayin y'an Dauren aure ya saka su mama Kareema da Inna Saude shan jinin jikin su ya yin da
gaban Inna Saude ya fadi yafi a kirga jininta ya hau fiye da misali jiranta take a sanar da ita
abunda ke faruwa kar zuciyarta ta buga. A lokacin da kunnuwanta suka jiye mata cewa AN FASA
AUREN ALEEYA batare da ta ida jin abunda ya faru a gurin daurin auren ba gani kawai akayi ta
zube kasa yayin da gidan ya kara hargitsewa da haniya,anyi iya kokari amma bata farfado ba kuma
bata numfashi,tashin hankali iya tashin hankali sun shigeshi Salmat da Ramlat sai kuka suke ya
yin da aka saka Inna Saude cikin mota sai asibit....
Zeesardaunerh ce
# comment
# like
# share
Sanarwa
Assalamu Alaikum
Barkanmu da wannan lokacin ya Kuke ya gida dafatan kowa yana cikin koshin lafiya{ameen}🙏
Ina mika sakon godiyata ga daukacin masoyana masu min fatan Alkhairi a duk inda suke,
nagode sosai da addu'o'inku gareni tare da fatan Alkhairi.
Ina godiya mara misali game da kaunar da kuke nunamin ga littafi na mai suna WASU
MATAN ina alfahari daku.Son SO FISSABILILLAH ♥️♥️♥️
Ina mai sanar muku cewa anan ne na kawo karshen littafina na WASU MATAN BOOK 1 zaku jini
d'auke da cigabanshi wato BOOK 2 inshaallah.Ku biyoni domin jin amsar wadannan tambayoyin
Duk amsar wad'annan tambayoyin zaku jisu ne a cikin littafin WASU MATAN BOOK 2.
Ku biyoni domin jin cigaban wannan labarin Nice taku har kullum🥰
©️♤♡ Zeesardaunerh
Sanarwa 2
Assalamu Alaikum
Ina yiwa kowa barka da Sallah Allah maimaita mana ameen😍 (ina jiran nawa soyen😉)
Kamar yadda na fada muku a posting dina na daya gabata cewar na kammala littafina na WASU
MATAN BOOK1 to Inshallah WASU MATAN BOOK 2 zai fara zuwar muku ne a ranar Laraba
wato 20th july 2022 Inshallah.
Inason amfani da wannan damar domin sanar da ku cewa nayi missing SIMS dina wato layukana
da nake chart daku a yanzu haka duk wanda ya turamin sako a wannan number 09066484295 ko
kuma 08104093636 ba zai ga nayi responding ba a sakamakon sace mun waya da layuka da akayi.
Ga sabuwar number na ga dukkan wanda ke bukatar magana dani 09132441081
©♤♡ Zeesardaunerh