0% found this document useful (0 votes)
308 views85 pages

Digital Entreprenuership 85

Uploaded by

Albadar Poultry
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
308 views85 pages

Digital Entreprenuership 85

Uploaded by

Albadar Poultry
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 85

Isma’il Aliyu Ubale

A REVOLUTIONARY BOOK
For
Digital Entrepreneurship
(Hausa Edition)

Na

Isma’il Aliyu Ubale


NCE, DCS, CCS, B.A (In View)

ALBADAR GLOBAL AGENCY LTD


[email protected]

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page i


Isma’il Aliyu Ubale

An buga shi a Nigeria, 2022


An fara bugawa a Shekarar 2022, July.

©Haƙƙin Mallaka (M):


Ba’a yarda a juya wannan littafi ba, ko a Sarrafa shi, ko a sake
buga shi, ba tare da izinin Mawallafin sa ko mamallakin sa ba.
Albadar Global Agency Ltd. July, 2022
[email protected]

©Haƙƙin Mallakar Matanin Rubutun (M):


Isma’il Aliyu Ubale
[email protected], 08038485677, 08086251045

Kamfanin da ya buga:
Juhaifah Ventures F.C.E Kano
08086889983, 07037131142
[email protected]

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page ii


Isma’il Aliyu Ubale

SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafin ga marigayi Yakubu
Muhammad Fannami, wani dalibin Makarantar Darus-salam
Science and Islamic College, Maiduguri, wanda ya sadaukar da
rayuwar sa domin ceto masallata daga harin kunar bakin wake na
bomb a jihar Borno a lokacin da ya hango wata mace ta dirfafi
masallacin da ake tsaka da sallah, yayi kukan Kura ya rungumeta
domin hana ta isa zuwa ga masallacin wanda hakan tasa yayi
sanadiyar rasa ransa tare da ‘yar kunar bakin waken , wannan abu
ya faru ne a ranar 25 ga watan Janairun Sheakarar 2017. Da kuma,
Marigayi Umar Adamu dan ‘yar uwa tad a ya rasa ransa
sanadiyar harin ‘yan ta’addan Boko Haram da ya rutsa dashi a
wajen sana’ar shi a garin Gaidam dake Jihar Yobe Nigeria a cikin
watan Ramadan na Shekarar 2021.

Allah Ubangiji ya jaddada musu Rahma, ya yafe musu kura-kuran


su, idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da imani, Amin.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page iii


Isma’il Aliyu Ubale

GODIYA
Dukkan godiya da yabo su tabbata ga Allah Madaukakin Sarki,
masani, gwanin hikima da ya bani iko da sani da hikimar rubuta
wannan littafi, tarin salatai masu yawa su tabbata ga Shugaban mu
fiyayyen halitta cikamakin Annabawa Annabi Muhammad tsira da
Amincin Allah su tabbata a gare shi.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page iv


Isma’il Aliyu Ubale

ABUBAWAN DAKE CIKI

SADAUKARWA .......................................................................... iii


GODIYA ....................................................................................... iv
ABUBAWAN DAKE CIKI .......................................................... v
GABATARWA ............................................................................. 1
CHAPTER ONE (Babi Na ɗaya) ................................................ 3
Dalilan zama ɗan kasuwa na dijital (Digital Entrepreneur) ........ 3
Muhimman abubuwa dangane da kasuwancin Dijital ................ 4
Yadda ake fara Kasuwancin Dijital ............................................ 7
CHAPTER TWO (Babi Na Biyu) ............................................. 11
Social Media Marketing ............................................................ 11
Online Advertising and Strategies ............................................ 17
Hanyoyin Bai Ɗaya Na Inganta Kasuwancin ku: ..................... 21
CHAPTER THREE (Babi Na Uku) .......................................... 26
Consultancy Services and Strategies ........................................ 26
Digital Real Estate Agent.......................................................... 33
Yadda za kuyi hulɗa da abokan ku domin Su taimaka muku ... 35
Hotel Booking ........................................................................... 36
Tsarin “Sale your knowledge online” ....................................... 38
Referral Agent ........................................................................... 40

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page v


Isma’il Aliyu Ubale

Domestic Logistics .................................................................... 42


Jumia Business .......................................................................... 44
Marketing Translation Service .................................................. 47
CHAPTER FOUR (Babi Na Hudu) .......................................... 50
Zero Capital Business Startup ...................................................... 50
Inter-Middle Business: .............................................................. 51
Local importing ......................................................................... 52
Survival Business ...................................................................... 52
Yadda zaku tseratar da kasuwancin ku ..................................... 55
Entrepreneurship Improvisation and Developreneur ................ 57
Summary of Company Registration in Nigeria ........................ 62
CHAPTER FIVE (Babi Na Biyar) ............................................ 66
Wall Advertisement .................................................................. 66
MANAZARTA ............................................................................ 76

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page vi


Isma’il Aliyu Ubale

GABATARWA
Me ake nufi da digital Entreprenuership?
Kasuwancin Digital kalma ce dake bayyana yadda kasuwancin ya
canza, yayin da al’umma ke ci gaba da canzawa ta hanyar fasahar
dijital. Kasuwancin dijital yana canza harkar kasuwanci ta hanyar
rage shinge ga sababbin masana’antu da kuma samar da sababbin
wuraren samun dama. Don haka kasuwancin dijital yana nufin:
“ƙirƙirar kasuwanci akan yanar gizo, siyar da kayayyaki na Dijital
da wanda ba Dijital ba” A wata fahimtar kuma yana nufin: “gudanar
da ayyuka online ba tare da buƙatar zuwa ga abokan hulɗa ba”

Misalai kaɗan na kasuwancin dijital sune: koyarwar online,


kasuwancin e-commerce, blogs, tashoshin YouTube, da hanyoyin
fasaha gaba ɗaya. Babbar fa’idar wannan tsarin kasuwanci shine
cewa ba ku buƙatar saka kuɗi da yawa don farawa, idan aka
kwatanta da kasuwar zahiri. Bugu da ƙari, wannan tsari yana baiwa
‘yan kasuwa damar yin aiki daga ko ina kuma a duk lokacin da suke
so, suna da yalwar lokaci a cikin ayyukan su na yau da kullum.

A yanzu lokaci ne da duk wani matashi zai tsunduma kansa


a harkar kasuwancin zamani na dijital wanda a yanzu bincike ya
nuna cewar wata babbar dama ce ga kowanne ɗan Adam, a yayin
da ake bamu ƙididdigar harkokin shafukan yanar gizo (Internet) ko
yaushe muna samun sahihan bayanai dake nuna yawaitar miliyoyin
mutane a Nigeria dake tururuwar Shiga shafukan yanar gizo yayin
da kuma a ɗayan ɓangaren Kasuwar dijital ke cigaba da mamaye
duniya baki ɗaya. Tunanin yin aiki daga ko ina a faɗin duniya da
samun ƙarin kuɗi masu yawa yayin da kuke ko ina, ko kuke kan
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 1
Isma’il Aliyu Ubale

tafiya ko wataƙila cikin barcin ku, ko yaushe yana da jan hankali


sosai, ko ba haka ba!
Don haka koma yaya ne, kafin ku kai ga nasara a wannan
fannin kuna buƙatar ɗaukar lokaci mai yawa don yin nazarin
bayanan kasuwanci na dijital da ƙirƙirar kyakkyawan tsari. Kamar
yadda muka sani yadda tsarin kasuwancin Dijital yake shine samar
da kayayyakin Dijital (Digital Products) Kamar irin su: Software,
Application, E-book, PDF1 da kuma samar da Kasuwar aikace-
aikacen Dijital (Digital Services) kamar irin su: Freelancing ko Gig
based work2 Online Tutoring, Online Teaching, Online Coding
Jobs, affiliate marketing, Content Creator, Blogging, YouTuber,
Online author/Translator, Voice Over Artist, Online Photography,
Digital Graphics Design, Sell designer merchandise, Social media
influencer, Domain or website seller, online website tester da
sauran su.
Kasuwancin Dijital ba shida iyaka a yanzu kuma kowa yana
da zaɓin fara wanda yake so ko kuma ƙirƙirar wani, bayan misalai
da muka kawo anan gaba a cikin littafin za muzo da bayanan wasu
dalla-dalla da yadda za kuyi da kuma wasu shafukan yanar gizo da
zaku iya shiga domin farawa da kuma samun cikakkun bayanai na
misalan da muka bayar. Mun shirya cikakken bayani mataki-mataki
daidai gwargwado don taimaka muku wajen ƙirƙirar kasuwancin
yanar gizo ɗinku da sarrafa shi da kyau ta yadda zai kawo sakamako
mai kyau.

1
Portable Document Format
2
zaku iya neman littafin ɗan uwa Salisu Abdurrazak mai suna Freelancing Kashi na
ɗaya)
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 2
Isma’il Aliyu Ubale

CHAPTER ONE (Babi Na ɗaya)


Dalilan zama ɗan kasuwa na dijital (Digital Entrepreneur)

Zan so ku karanta ƙididdigar yadda kasuwa da hada-hadar online


take kasancewa a duniya musamman a Amurka wanda kamfanin
binciken Statista3 ya bayyana a shafukan sa a shekarar 2021 "Kusan
mutane biliyan 4.66 sun kasance masu amfani da yanar gizo har
zuwa watan Oktoba na 2020, wanda ya ƙunshi kashi 59 na
al’ummar duniya" - Statista (2021) "Masu amfani da yanar gizo sun
kashe dala biliyan 861.12 a online tare da dillalan Amurka a cikin
shekarar 2020, wanda ya ƙaru da kashi 44.0 cikin ɗari a shekara" -
Kasuwancin Dijital4 360 (2021) "kashi 65 na masu amfani da yanar
gizo suna cinikayya a ciki" -Statista (2020). Wannan ƙididdiga ce
da kamfanin binciken Statista ya fitar a shekarar 2021. Bugu da ƙari
idan kuka yi bincike na Google kamar: kasuwancin dijital, kasuwar
dijital, ko tallace-tallace na online za ku ga cewa za’a nuna irin
waɗannan labaran da yawa suna tabbatar da abinda muke faɗa a nan
cewa kasuwancin yanar gizo yana da fa’ida a yanzu kuma babu
wani zaɓi daya wuce cewar duk wanda suke ƙasa da shekaru 40 su
tsunduma cikin sa ko kuma su samu barazanar rasa ayyuka da
kasuwancin su nan da shekaru masu zuwa kamar yadda bincike da
yawa suka tabbatar da hakan.

Amma ta yaya zaku iya shiga wannan kasuwa lafiya kuma kuci
Nasara ku fito lafiya? Abu mafi muhimmanci shine kada kuyi
sakaci da bincike da kuma shiga manyan shafukan kasuwanni na
3
Wani kamfanin bincike ne dake kasar Jamus
4
Digita Entrepreneurship and Innovation in Central America
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 3
Isma’il Aliyu Ubale

duniya da babu zamba a cikin su, zamu kawo wasu daga ciki anan
gaba. Kuna iya fara kasuwancin ku na dijital yayin da kuke ci gaba
da karatu, ko kuma tare da sana’ar ku ta yanzu.

Kayayyakin dijital da tallace-tallace sun samu karbuwa sosai a


wurin jama’a da hakan yake nuna cewar nan gaba kaso mafi yawa
na kasuwanci zai koma Digital la’akari da ƙididdigar Statista da
muka bayar a baya. Abubuwan da suka faru na baya-bayannan na
annobar Corona sun haifar da haɓɓaka kasuwancin online waɗanda
sababbin ƴan kasuwa na dijital ke jagoranta a duniya da Afrika da
Nigeria.

Muhimman abubuwa dangane da kasuwancin Dijital

Yayin da COVID-19 ta haifar da koma bayan tattalin arziki, yawan


rashin aikin yi, da kuma yunƙurin farfaɗo wa da samar da canji na
dijital don kasuwanci ya tsira “COVID-Preneurs5” sun ci gaba da
haɓɓaka wannan kasuwancin na dijital, Kamar yadda wata cibiyar
duniya dake lura da alƙaluman tattalin arziƙin duniya ta “Peterson
Institute for International Economics” (PIIE) ta bayyana adadin
sababbin aikace-aikacen kasuwanci da cinikayya ta yanar gizo a
Amurka ya ƙaru da kashi 23 cikin ɗari daga watan Junairu na 2020
zuwa Satumba na shekarar, idan aka kwatanta da shekarar 2019.

Ofishin kididdiga na Amurka6 ya ba da rahoton cewa akwai


sababbin aikace-aikacen kasuwanci da jimillar su ya kai 1,559,950

5
Wasu gungun 'yan kasuwa dake fafutukar farfado da tattalin arziki bayan afkuwar
annobar Corona
6
American Statistical Association
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 4
Isma’il Aliyu Ubale

da aka gabatar daga watan Yuli zuwa watan Satumba na Shekarar


2020 kadai, idan aka kwatanta da sababbin aikace-aikacen 859,345
da aka gabatar a daidai wannan lokacin a cikin 2019, wannan
ƙaruwar kashi 82% a cikin shekarar 2020 shine mafi girman
haɓakar kasuwancin a duniya kamar yadda kamfanin bincike na
statista ya bayyana.

Shin kun taɓa tunanin mai yasa kasuwancin dijital ke


ƙaruwa? Sha’awar kasuwancin dijital ta cigaba da kasancewa mai
ƙarfi har zuwa ƙarshen 2021 a wani binciken statista inda kuma yace
abun ƙaruwa yake cikin watanni 12 da suka gabata, Google Trends
ya samu babban cigaba a cikin bincike.

Anan ga wasu mahimman dalilai da hanyar kasuwanci ta dijital


take haɓɓaka:
a. Qarin damar yin kasuwanci ga kowa da suka haɗar da
ma’aikata da kuma masu gudanar da kasuwanci na zahiri
dake zaune a wasu kasuwanni, a yanzu kasuwar ku tana inda
kuke, haka gudanar da mafi yawancin ayyukan ku suna inda
kuke. Masu sha’awar kasuwancin dijital, akwai ƙarin damar
fara kasuwanci fiye da kowane lokaci a baya wannan ya haɗa
da samun sauƙi zuwa fasaha mara tsada, kamar amfani da
kwamfutar tafi-da-gidanka (Android)
b. Sauƙaƙe hanyoyin kasuwanci da kuma iya aiwatarwa ga
dukkan masu sha’awa da sauƙin kashe kuɗi domin farawa.
c. Samun sauƙin rayuwa da lokacin kula da iyalai da kuma yin
walwala Sosai a ko yaushe da rage cinkoso a kasuwannin
zahiri da manyan titunan biranen duniya, yin kasuwanci a

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 5


Isma’il Aliyu Ubale

gida ko kuma a duk inda kuka samu kanku a yanzu ba ku


buƙatar zuwa kasuwa ko wurin aiki idan aikin ku digital ne
ko kasuwancin ku dangane da binciken da aka yi na Cibiyar
Morning Consult ta Amurka kashi 81% na ma’aikata a
Amurka sun ce suna jin daɗin yin aiki daga gida, kashi 74%
na ma’aikatan sun ce yafi muhimmanci da fa’ida, kuma fiye
da kaso 3 cikin 4 sun gwammace neman ayyukan da ke ba
da zaɓin aiki daga gida. Dangane da wani bincike da Sashin
bincike na Statista ya gudanar a watan Fabrairun 2021, 46%
na waɗanda suka bada bayanai sun ce suna shafe awanni
biyar zuwa shida a kowace rana akan yanar gizo da wayoyin
hannu, wannan yana nufin cewa kasuwancin dijital yana ci
gaba da haɓbaka a ko yaushe a duniya.

A taƙaice dai, abokan ciniki suna da sauƙin isa gare su domin fara
tattaunawar ƙulla cinikayya a kasuwancin dijital, fiye da kowanne
lokaci, musamman ga ƙwararrun ƴan kasuwa na dijital waɗanda za
su iya amfani da kafofin watsa labarai da dandamalin kasuwancin
dijital daban-daban a duniya. Tallace-tallace na kasuwancin yana ci
gaba da karuwa, yana haifar da ƙarin ‘yan kasuwa don sayar da
kayan su da ayyukan su a online daga watan Afrilu zuwa watan
Yuni na 2021 kadai, tallace-tallacen e-commerce gaba ɗaya a
Amurka ya kai dalar Amurka biliyan 222.5, wanda ya kasance ya
ƙaru da kashi 3.3% ɗaya bisa ukun farko na 2021. Bugu da ƙari,
mutane da yawa waɗanda suka samu damar yin aiki daga gida a
karon farko cikin sauri sun gane cewa hanyar aiki ce da suka fi so
suyi a rayuwar su.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 6


Isma’il Aliyu Ubale

Yadda ake fara Kasuwancin Dijital

Ba ku buƙatar wani lokaci mai tsawo domin farawa amma kuna


buƙatar yin shiri na gaske, kuma tunanin ku da fikira zasu taimaka
muku matuƙa wajen farawa. Abu mafi buƙatuwa shine wayar
Android ko kwamfiyuta, da kuma ingantantacciyar hanyar sadarwa
da lokaci wadatacce kamar yadda masana suke ta maimaitawa.
Koda yake a rukunin gaba zamu kawo muku wasu sana’o’in da
yadda za kuyi su amma dai a harkar kasuwancin Dijital babu wani
bayani abun dogaro na ko yaushe domin kuwa kullum sababbin
damarmaki fitowa suke yi ta hanyar juyin juya halin duniya na
tattalin arziƙi da kuma yadda masana da ‘yan kasuwa suka dukufa
wajen bincike, wani ƙwaƙƙwaran misali shine yadda a gida
Najeriya yanzu ake samun wasu dandamalai (Platforms) dake
kwatanta irin ayyukan manyan shafuka ko kasuwannin duniya na
Dijital irinsu Amazon.

Naci karo da shafukan Facebook da WhatsApp da dama a


wani bincike da nayi musamman a jihar Kano, Katsina da Bauchi
inda matasa kan buɗe shafin su, su kuma gayyato ‘yan kasuwa
domin yin rajista da shafin ta hanyar tantancewa da samar da tabbaci
akan kasuwancin su, inda kuma daga ƙarshe masu gudanar da
shafukan kan baiwa ‘yan kasuwar da suka yi rajista damar tallata
kasuwancin su a wannan shafin, hakan yana nufin cewa duk wanda
ya siya kaya a wannan shafin, masu gudanar da shafin sun ɗauki
nauyi da ɗawaniyar tabbatar da cewa kayan ya isa ga wanda suka
siya, baya ga haka kuma suna sanya ido akai wanda masu gudanar
da shafukan sukan karɓi kuɗin rajista a matsayin kuɗin gudanarwa

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 7


Isma’il Aliyu Ubale

ga kowanne ɗan kasuwa da yake buƙatar rajista, abun sha’awar


shine ma yasa nace suna kwaikwayon manyan shafuka na duniya
shine yadda masu gudanar da shafukan kan yi ƙoƙari wajen tara
mutane a shafukan nasu. Don haka, babu wani abun ƙayyadewa ga
masu buƙatar farawa a kowane lokaci da kuma yanayi, ƙofar a buɗe
take kuma tana da faɗin gaske.

A taƙaice, abun nufi shine baya ga manyan misalai da muka bayar


da kuma wasu shafukan da zamu kawo adireshin su, hakan yana
nufin cewa a ko yaushe zaku iya ƙirƙirar fikirar ku ta Dijital misali
kwatankwacin yadda ake mayar da komai Dijital koda kuwa a zahiri
yake. Wasu daga cikin Shafukan da zaku iya ziyarta domin bibiyar
yadda za kuci moriyar kasuwancin Dijital:
i. Domin siyar da kayayyaki Online
 amazon.com
 flipkart.com
 ebay.com

ii. Shafukan da zasu baku damar yin aiki daga gida


 crowdsource.com
 speakwrite.com

iii. Shafukan da zaku iya koyarwa Online


 http://www.skillshare.com/teach
 https://www.udemy.com/
 Tutor.com

iv. Shafukan da zaku zamo online author


 www.flipkart.com
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 8
Isma’il Aliyu Ubale

 www.infibeam.com
 www.lulu.com
 www.pothi.com/pothi

v. Shafukan da zaku siyar da zanen ku (Creatives art and


graphics)
 http://www.zazzle.com/
 http://www.cafepress.co.uk/
 https://www.threadless.com/

vi. Shafukan da zaku zama masu fassara (Online


Translation)
 translatorsbase.com

vii. Online transcription jobs


 mturk.com

viii. Shafukan da zaku siyar da muryoyin ku (Voice over


artist)
 voicebunny.com/talent
 voice123.com

ix. Shafukan da zaku siyar da hotunan da kuka ɗauka (Sell


photos online)
 istockphoto.com/sell-stock-photos.php
 creativemarket.com

x. Shafukan da zaku siyar da website ko domain ko


application

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 9


Isma’il Aliyu Ubale

 Sedo
 Flippa
 Godaddy

i. Shafukan da za kuyi waƙoƙi ku siyar


 Distrokid.com
 loudr.fm

Abun lura ga waɗannan misalan shine wani ɓangare ne da ake


maganar duniya baki ɗaya har kullum kuna da zaɓin yin kasuwanci
ko aikace-aikacen ku dasu, kamar yadda kuma kuna da damar
ƙirƙirar naku domin aiwatar dasu a misalai masu zuwa za muzo
muku da wasu abubuwa masu muhimmanci da ma’ana wanda babu
shakka zasu taimaka sosai. Kada ku manta babban abunda ake
buƙata shine tunani da Hikima da kuma fikira akan yadda zaku
Samar da Technology Entrepreneurship da kanku wato ku samar da
wata fasahar ku domin shiga filin dagar kasuwar Dijital.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 10


Isma’il Aliyu Ubale

CHAPTER TWO (Babi Na Biyu)


Social Media Marketing
Tsarin Social Media marketing wani sanannen tsari ne da mafi
yawancin masuyi basa amfani da ƙwarewar su, wani muhimmin
tsari ne na gudanar da kasuwanci kowanne irine a Social Media
wato abu na farko shine idan kana wata sana’a ka tallata kanka da
abunda kake siyarwa ko kuma irin aikin da kake yi, misali idan kana
sana’ar fenti (paint) kana iya tallan sana’ar ka, ko kuma kai
Consultant ne a ɗaya daga cikin abubuwan da mai karatu zai
tsinkaya a Consultancy Services to za kayi bayani kuma kabayyana
ƙwarewar ka, saidai anan akwai muhimman abubuwa guda biyu:

i. Dole ku lura da inda za kuyi tallan hajar ku ko abunda da


kuke tallatawa ba zaku tallata hajar ku a ko ina ba domin
hakan zai gajiyar daku, ma’ana idan kukaga kun yawaita
tallan sana’ar ku kuma ba’a siya ba to dole za kuji kun rasa
ƙwarin gwiwar yin wannan sana’ar to hakan yana nufin cewa
duk abunda kuke tallatawa ku tallata shi a muhallin sa,
ma’ana ku tallata kasuwancin ku ga al’ummar da dayawa
daga cikin su suna buƙatar irin wannan sana’ar ko wannan
kayan.

ii. Abubuwan da zaku iya tallatawa online:


Ba kowane abu bane za kuyi tallan sa online ba dalilin Shine
akwai abubuwan da idan kukayi tallan su a online saidai
iyakar mutanen unguwar ku su siya domin kuwa duk wanda
zai siya idan a nesa yake kuɗin da za’a biya kayan ya isa
wajen sa za kuga ya fi kuɗin kayan. Misali idan akayi tallan
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 11
Isma’il Aliyu Ubale

gyaɗa marau-marau wacce farashin kowanne ƙulli da wahala


ya wuce ₦100, to ko daga wata unguwar abune mai wahala
wani ya iya siya balle kuma daga wani gari saidai idan da
yawa ne za’a siya, anan babu laifi a tallata abubuwa ko
kayayyakin da suke da ƙananan kuɗi amma za ayi sharaɗin
siyan wani adadi kamar misali: ace dole Mutum ya siya
dozen ɗaya ko kuma ya siya na dubu biyu kafin a iya aika
masa zuwa wani gari hakan ma da sharaɗin idan zai biya
kuɗin kaiwa ko kuma gwargwadon yadda aka ƙulla cinikin.

Zan kawo wasu muhimman abubuwa dangane da Social Media


marketing kamar haka:

i. StoryPreneur/InfoPreneur:
Story-preneur ko kuma Info-preneur wata muhimmiyar hanya ce da
zata taimaka Ƙwarai da gaske a harkar Social Media Marketing
kamar yadda muka sani a Social Media Marketing abu na farko da
ake buƙata shine yawan Followers (Mabiya) ba followers ɗin ba ma
kaɗai koda yake wannan bayanin zaizo a "Targeting Advert"
Babban abunda muke so shine masu bibiyar mu (wato followers) su
yawaita, to kuma babu yadda za ayi ku tara Followers sai kunbi
wasu hanyoyi, ɗaya daga cikin hanyoyin shine wanda muke magana
akai yanzu wato ‘Story-preneur’ yadda tsarin yake dole ne mutum
ya zama mai labarto wasu labarai masu jan hankali kuma na
gaskiya, ko kuma labaran hikaya koda bana gaskiya bane amma
masu ma’ana da kuma ɗauke da darussan rayuwa, ko kuma Mutum
ya lizimci samar da wasu muhimman bayanai kamar na ɗaukar aiki
ko scholarship ko kuma wasu abubuwa masu matuƙar amfani ga

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 12


Isma’il Aliyu Ubale

al’umma, kai tsaye mutum zai tara Followers masu yawan gaske ta
hanyar amfani da wannan tsarin babban abun shine nuna ƙwarewa
a wajen rubutu da kuma Jajircewa akan aiki yau da kullum, zaku
tabbatar da tasirin Storypreneur ne idan kuka bibiyi shafukan wasu
‘yan jaridun da kuka sani, za kuga sun tara mabiya masu tarin yawa
a shafukan su na Social Media ba dan komai ba sai don kawai suna
bayar da labarai.

ii. ComedyPreneur:
Shima wannan tsarin kamar Storypreneur ne amma shi kuma
mutum zai zama mai gabatar da labaran barkwanci ko zanen
barkwanci ne, ko kuma ya dinga amfani da wasu hotunan ban
dariya, duka fa wannan anayi ne domin samar da Followers masu
yawa domin tafiyar da harkokin kasuwancin Social Media dinku
cikin nasara.

iii. Social Media Management/Assistant:


Tsarin Social Media management kuwa ya ƙunshi samun ƙwarewa
ne a ɓangaren sarrafa shafukan sada zumunta musamman Manya
daga cikin su da suka hadar da: Facebook, WhatsApp, Instagram,
Twitter, Tiktot da sauransu, ba kawai ƙwarewar kaɗai ba da kuma
iya sarrafa su cikin tsafta ba tare da wasu abubuwa marasa kyau ga
tarbiyya ko al’ada ba, hakan yana nufin cewa mutum zai iya zama
Social Media Assistant wato mai sarrafa shafukan wani ɗan siyasa
ko wani kamfani ta hanyar taimakawa da kuma tafiyar da shafukan
ydda ake buƙata, ba kuma anan ayyukan Social Media
management ya tsaya ba, ya haɗar da buɗe feji (Page) da dandali
(Group) wasu daga cikin shafuka kamar su Facebook da kuma

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 13


Isma’il Aliyu Ubale

yadda ake tafiyar da Fejin da samar da mabiya cikin ƙanƙanin


lokaci, da kuma yadda ake ƙirƙirar Fejin, da irin su Broadcasting
advertising na WhatsApp, waɗannan dabaru ne da kuma ƙwarewa
da zasu taimaka sosai a ɓangaren Social Media Marketing. Duka
dai ta wannan ɓangaren zaku iya samarwa kanku sana’a idan kuka
ƙware misali yadda zaku buɗewa mutane Feji da yadda zaku
taimakawa mutane su kare shafukan su na Social Media da kuma
ydda zaku dawowa da mutane shafukan nasu idan wani abu ya faru,
ko kuma yadda zaku taimakawa mutane wajen samun Facebook
verification badge da sauran su. Akwai abubuwa da yawa shiyasa
tunda farko na faɗa batun Social Media yana da faɗin gaske abun
buƙatar kawai shine ku faɗaɗa tunanin ku ta yadda za kuci gajiyar
hakan.

A taƙaice Social Media Management ko assisting wani ɓangare


ne na kasuwancin Social Media da zaku iya yin sa domin ƙarfafa
naku kasuwancin, ko kuma ku riƙi ƙwarewar ku a matsayin sana’a
yadda zaku dinga taimakawa masu gudanar da kasuwanci ta
shafukan su suna biyan ku.

iv. Targeting Advert/Target Audience:


Tsarin Targeting Advert Ko Target Audience yana taka
muhimmiyar rawa matuƙa gaya a harkar tallace-tallace koda ba’a
Social Media ba ma, balle kuma a Social Media, yadda tsarin yake
shine fayyace irin mutanen da za’a yiwa talla ko kuma yin talla a
inda ya dace, misali a lokacin da kuke tallan kayan ƙawa da ado na
mata a Social Media babu inda ya kamata ku yawaita tallan ku sai
a group da Fejin da matane tsantsa ko kuma suka fi yawa, haka

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 14


Isma’il Aliyu Ubale

kuma a lokacin da kuke tallan kayan ball (wato football dress) dole
ne ku bibiyi groups ɗin da samari ne suka fi yawa ko kuma shafukan
‘yan ƙwallon ƙafa kai tsaye, abunda ake nufi anan shine dole ne ku
duba abunda kuke tallatawa kuma ku duba irin mutanen da kuke
mu’amala dasu a shafukan ku na Social Media ana buƙatar ya zama
abunda kuke tallatawa yana da alaƙa sosai da mutanen da suke
bibiyar shafukan ku, dan haka za ku iya amfani da hikimar neman
mabiya (Followers) wanda za suyi tasiri akan sana’ar ku, misali
kamar ku ɗaura Photon ku a kan shafin ku sanye da kayan ƙwallo,
ko kuma ku dinga yin wasu abubuwan da zasu janyo hankalin irin
Mutanen da kuke so su dinga bibiyar shafukan ku kamar ace idan
kuna tallata magungunan kaji ne to dole ku lizimci masu kiwon kaji
ku tara su a shafin ku domin kuwa ko mabiyan ku Sun kai Zambar-
Dubu7 idan basu da alaƙa da abunda kuke tallatawa saidai ku
gundure su, su kuma su gajiyar daku a tallan da kuke yi. A taƙaice
dole ne ku daidai ta abubuwan da kuke tallatawa da buƙatun
mabiyan ku, ko kuma ku samar da sabbin mabiya masu buƙatuwa
zuwa ga abubuwan da kuke tallatawa ta hanyar amfani da dabarun
da kuka ambata a baya da kuma wanda zasu zo anan gaba.

v. Social Media Influencer:


Wani mutum ne da ya tara followers da yawa kuma yake tallata
hajoji na kamfanoni daban-daban da kasuwanci daban-daban wanda
hakan yake zama wata gagarumar hanyar samun kudi gare shi har
ta kai shi ga zama wakilin kamfani (Ambassador) a wata shiyya.
Don haka zaku iya zama Social Media Influencer ta hanyar tara

7
Miliyan ɗaya
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 15
Isma’il Aliyu Ubale

followers kamar yadda bayani ya gabata a baya akan yadda ake tara
followers.

Influencer shine mutumin da ake amfani da ilimin sa ko


baiwar sa kan wani ilimi ko kwarewa tare da kokarin bayyanawa
duniya hakan a cikin posting da yake yi a social media (Geyner,
2022) Don haka Influencing a Hausance, zamu iya fassara ta da
tasiri, ma’ana, ma’ana a duk yayin da Influencer yayi rubutu
wannan wallafar za tayi tasiri a wajen masu bibiyar shi (Followers).8
Saboda haka Influencers a Social Median sun kasu kasha-kashi
akwai Mega-Influencers wanda yake da followers sama da Miliyan
daya, wadannan su ake kira da Celebrities, a kwai kuma Macro-
Influencers sune masu followers dubu Arba’in zuwa Miliyan Daya,
akwai kuma rukunin Nano-Influencers sune zaku same su da
followers kasa da dubu daya, sai kuma Fake-Influencers sune
wadanda ba sune mutane na asali da suke amfani da sunan ba, satar
shi sukayi, kamar misalin Musa L. Maje dake amfani da Zahra
Mansur.

Daga cikin amfanin Social Media Influencer shine:


1. Tallace-tallace:
2. Ayyuka da NGOs
3. Bunkasa Kasuwanci

Saboda haka za’a iya kiran ka Social Media Influencer idan ya zama
kana tallata harkokin kasuwancin wasu suna biyan ka. Don haka
dole ka zama kana da ƙwarewa wajen tallata haja ko kasuwanci

8
Aliyu M. Ahmad
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 16
Isma’il Aliyu Ubale

kuma ka ƙware wajen rubuta tallace-tallace, Kuma uwa-uba ya


zama kanada followers masu tarin yawa, yanzu ina Fatan mu
fahimci me ake nufi da Social Media influencer.

Online Advertising and Strategies

Talla online wanda aka sani da tallace-tallacen yanar gizo, yana


nufin amfani da tashoshi na yanar gizo don haɓɓaka kasuwa da
kuma tallata kasuwanci domin samun sababbin abokan hulɗar
cinikayya da tallace-tallace a yanar gizo.

Kasuwancin kowanne nau’i na iya samun damar hanyoyin


da ba su da tsada don talla da haɓɓaka kasuwanci idan an kwatanta
da hanyoyin tallace-tallacen kan tituna da kwararo-kwararo a iya
cewa tallan yanar gizo wata muhimmiyar dama ce da cigaba
musamman ga ƙananan Kamfanoni da ‘yan kasuwa.

Samun sabbin abokan ciniki don kasuwanci babban ƙalubale


ne ga ɗimbin ‘yan kasuwa, abu na farko shine yadda za ayi tattalin
abokan hulɗar cinikayya na yanzu da ake dasu kafin tukunna ayi
tunanin dabarun samo sababbin kwastomomi a shafukan sada
zumunta na yanar gizo.

Domin taimakawa kasuwancin ku, haƙiƙa mun tattaro jerin mafi


kyawon shawarwari don nemo sababbin masu siye da kuma inganta
kasuwancin ku da kuma haɓɓaka kasuwancin Online ko Social
Media Marketing kamar haka:

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 17


Isma’il Aliyu Ubale

i. Ƙirƙirar bulogi (Blog):


Blog wani Shafin yanar gizo ne wanda mutum ke kirkira tare da
sarrafa shi domin shigar da bayanai ko yada wani ilimi.

A bayyane yake, hanya mafi muhimmanci da za ku iya tallata


kasuwancin ku a online ita ce gina blog ko shafi inda za ku iya
aikawa da duk saƙonnin da kuke so na tallace-tallace. Tabbas
wannan dabara ce ta dogon lokaci, kuma ba za ta biya buƙata dare
ɗaya ba, dole sai an Jajirce, amma kowane ɗan kasuwa yana buƙatar
fahimtar muhimmancin rungumar wannan hanyar talla ta online.

Gidan yanar gizon ku na iya zama kyakkyawan gidan yanar


gizo don tara sababbin masu bibiyar ku domin ji daga gare ku akan
wata baiwar ku, ko kuma kasuwancin ku, sannan kuna buƙatar
tabbatar da cewa rukunin yanar gizon yana nuna muhimman sassa
na rayuwar ɗan Adam masu banƙaye, misali ku dinga zuwa da
sababbin labarai masu jan hankali ko kuma koyar da wasu darussa.

ii. Yi amfani da tallace-tallacen Facebook:


Tallace-tallacen Facebook sun kasu da yawa, ga wasu daga ciki:

a. Facebook Ads: koda yake wannan tsarin yana buƙatar wasu


kuɗaɗe ‘yan kaɗan domin biyan facebook ta hanyar
Promoting duk wani Posting da kuka yi na tallace-tallace a
Dandali (Group) ko Feji (Pages) amma babu tantamar cewar
wannan muhimmiyar hanya ce da take baku zaɓin zaɓar irin
na’u’ikan mutanen da tallar ku za tafi zuwa gare su ta hanyar
jinsi da kuma shekaru, misali idan sana’ar ku ta shafi mata
ne kaɗai zaku iya zaɓar cewar Facebook ya aiko tallan
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 18
Isma’il Aliyu Ubale

kasuwancin ku zuwa ga mata ne kaɗai bugu da ƙari zaku iya


zaɓar shekaru Misali idan ‘yan mata kuke so tallan
kasuwancin ku ya riska kuna iya sanya daga shekara 18 zuwa
30, haka ma idan maza kuke buƙatar a aikawa da tallan ku.

b. Facebook Marketplace: Kasuwar Facebook yanki ne na


talla a Social Media wanda ya himmatu wajen taimaka wa
ɗaiɗaikun mutane da kasuwanci su siyar da abubuwa a cikin
kasuwar shine faɗaɗa Facebook zuwa kasuwanni don yin
gogayya da ayyukan kasuwanci kamar eBay da Craigslist.
Ga dukkan masu harkar kasuwanci a Social Media yana da
kyau matuƙa Su san Facebook marketplace ba kawai Su san
tsarin ba a’a kuyi bincike tare da ƙwarewa sosai, a cikin sa
za muyi tsokaci ne kaɗan.

Menene Kasuwar Facebook?


Facebook marketplace wuri ne mai dacewa ga mutane don
siya da siyar da abubuwa. Mutane na iya samun abin da suke
suke nema ta hanyar nema (searching) a Facebook
marketplace nau’i nau’i daban-daban na kayayyakin da
farashi da kuma wurin da mai kayan yake

iii. Facebook Pages da Groups: wani rukuni ne daga cikin


lunguna da rukunnan facebook wanda da yawa kun san
cewar zaku iya buɗe feji (page) ko kuma dandali (Group)
domin kasuwancin ku ko kuma tallace-tallace daban-
daban amma babbar matsalar da wannan rukunin yake
fuskanta shine rashinjajircewa daga farkon farawa zuwa

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 19


Isma’il Aliyu Ubale

lokacin cin nasara, babu shakka a lokacin da kuka buɗe


Sabon group ko feji kuna buƙatar rainon sa ta hanyar
yaɗa shi da kuma yawan sanya abubuwa akai-akai da
kuma neman taimakon abokan ku su taya ku yaɗawa.

iv. Ƙirƙiri darussan bidiyo: Bidiyo wata babbar hanya ce


ta isar da sakon kasuwancin ka don tallata shi ta yadda
zai isa duk wuraren da suka kamata. Yayin da zaku iya
samun ɗan tsaiko a farko don tara masu sauraron ku, idan
kun mayar da hankali kan ƙirƙirar koyarwar bidiyo masu
amfani a ƙarshe, zaku isa ga adadi mai yawa na mutane,
bugu da ƙari, dole ne ku mai da hankali kan ƙara ƙoƙari
ba tare da damuwa don samar da riba a lokaci guda ba.

v. Haɓɓaka dangantaka da abokan cinikin ku ta hanyar


tallan E-mail:
Tallace-tallacen E-mail wani abu ne da ya kamata
kowane mai kasuwanci ya tsunduma cikin sa, don yin
nasara tare da tallan E-mail, kuna buƙatar adireshin E-
mail abokan cinikayya ko mu’amala domin tura musu
wasu muhimman littafai ko Ebook yayin da lokaci zuwa
lokaci zaku rika tuntuɓar su ta E-mail ɗin tare da aike
musu tallace-tallacen ku

vi. Haɗin gwiwa:


Haɗin gwiwa tare da shahararrun masu rubuce-rubuce a
yanar Gizo ta kowanne ɓangare yin haɗin gwiwa dasu zai
taimaka wajen sanya tallace-tallacen ku a shafukan su da

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 20


Isma’il Aliyu Ubale

kuma wuraren da suke rubuce-rubuce inda suka zama


fitattu.

Hanyoyin Bai Ɗaya Na Inganta Kasuwancin ku:

Waɗanda hanyoyin sunyi tarayyar dabarun tallata kasuwancin ku ta


ɓangaren yanar gizo da kuma zahiri:

i. Halartar wuraren baje-kolin sana’a da aiki (Services)


Ana shirya bukukuwa da yawa a kowace shekara na baje-kolin
sana’a ko ƙwarewar wasu muhimman ayyuka waɗanda zaku samu
damar shiga ciki, domin baje taku hajar, kada ku ɗauki wannan da
wasa domin kuwa kuma zaku iya shirya naku baje-kolin a online
wato a shafukan sada zumunta irin WhatsApp da facebook da kuma
Manhajar Zoom ko kuma a zahiri da sauran su.

Ku lura waɗanne baje-kolin ne suka fi ban sha’awa ga


abokan cinikin ku kuma ku samu damar shigar su ko kuma shirya
naku na ƙashin kai.

A cikin bikin baje-kolin yana da muhimmanci a yi aiki don ƙirƙirar


sababbin abokan hulɗa duka biyun ta hanyar yin magana da baƙi da
nuna ƙwazo ta hanyar sauƙaƙe wa baƙi yin tambayoyi akan
kasuwancin ku.

ii. Yi amfani da abokan ciniki na yanzu:9


Idan kuna da kyakkyawar alaƙa tare da abokan cinikin ku na yanzu
ko yaushe kuna iya tafiya tare da su idan suna da buƙatar hakan

9
Current Customer
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 21
Isma’il Aliyu Ubale

domin kasancewar su abokan hulɗar ku zaku iya halartar tarukan su


na bukukuwa ko shiga jerin masu taya su alhinin wani abu na
rayuwar su daya faru, hakanan rangwamen kuɗi ga masu siye na
yau-da-kullum saboda suna kawo muku sababbin abokan cinikayya

iii. Neman Sa’anni domin haɗin gwiwa:


Idan kuna sana’ar ku kuma kuna buƙatar a tallata muku a wasu
shafukan yanar gizo kuma baku da kuɗin da zaku iya biya,
sakamakon kasuwancin ku sabo ne a yanzu kuna neman hanyoyin
haɓɓakawa domin tsayuwa da ƙafafunku to kamar haka ne zaku
samu shafukan jaridu ƙanana masu tasowa wanda zaku iya tuntuɓar
juna kuma ku ƙulla yarjejeniyar yin aiki tare ba tare da kuɗi ba a
karon farko. Yadda tsarin yake shine zaku amince suyi muku tallan
kasuwancin ku da sharaɗin cewar zasu zama wakilai ta hanyar da
zasu iya sanin cewar kun samu Abokin ciniki ta hanyar tallan su
daga nan kuma zaku biya su akan duk mutum ɗaya da tallan su ya
samar wanda kukayi hulɗar kasuwancin dashi zaku iya ƙulla
yarjejeniyar raba riba ko kuma wani kaso mai tsoka ga masu tallan
domin cigaba da wanzuwar hulɗar ku.

iv. Ɗaukar nauyin gasar nuna fasaha ko ƙwarewar


rubutu a yanar gizo ko a zahiri:
Zaku buƙaci sanya wasu sharuɗan dake nufin tallan kasuwancin ku
a online domin shirya wata gasa ko tallafawa ga masu shiryawa.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 22


Isma’il Aliyu Ubale

v. Koyi da kishiyoyin ku:


Babu wani abu daidai ba tare da ɗaukar misalai daga abokan sana’a
irin taku ba, nazarin masu sana’a irin taku da irin salon da suke bi
zai iya ƙarfafa ku don gano sababbin abokan ciniki.

Wata hanyar koyo daga abokan sana’ar ita ce ganin yadda suke yi
sannan kuma a yi akasin haka, wato kuyi ƙoƙarin finsu da fara’a ko
bayar da wurin zama ko ɗaukar waya a kowane lokaci wannan
hikima ce ta daban, sannan kuna iya gwada aika saƙon kai tsaye ga
kwastomomi maimakon idan duk abokan sana’ar ku suna amfani da
tallan dijital na bai ɗaya ne.

vi. Haɓaka saƙon tallace-tallace ku da salo


mabambanta:
Dole ko yaushe a dinga yin sababbin kalmomin tallata kasuwancin
da kuma salo iri-iri wanda ya haɗar da dogaye da gajerun hanyoyi
hikimar hakan itace misali: a tallan da zaku buga na facebook kuna
buƙatar yin dogon rubutu domin wasu suna buƙatar cikakken bayani
yayin da wasu kuma suna buƙatar gajeren rubutu yayin da basa
saurarar duk wani rubutu mai tsayi.

Yi tunanin dalilin da yasa suke siya daga gare ku da wacce


matsala kuka warware musu misali a lokacin da suke buƙatar
siyayya ko aikin da kuke yi zaku iya fahimtar dalilin zuwan su ko
tuntuɓar ku, wajibi ne a maida hankali akai domin ɗorewar
kasuwancin ku tare dasu.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 23


Isma’il Aliyu Ubale

vii. Kulawa da Kwastoma:


Kyakkyawar kulawa ga masu tambayar farashin kayayyakin ku ko
ayyukan da kuke yi yana da kyau ku basu amsa mai gamsarwa cikin
girmamawa harma kuyi musu barkwanci kaɗan, aminci yana
yaɗuwa cikin sauri kuma yana iya taimaka muku da yawa a cikin
neman sababbin abokan ciniki.

Irin wannan kulawar abokin ciniki yana bada shaida mai


kyau wacce ke yaduwa cikin sauri.

viii. Ƙirƙirar sababbin abubuwa ko ayyuka:


Kada ku zauna baku sabunta kanku a ayyukan ku ko kayayyakin da
kuke siyarwa, yana da kyau ku dinga sabunta ayyukan ku ta hanyar
cigaba da samun horo na musamman a wasu shafukan da kuma
samar da sabbin abubuwan siyarwa idan kun lura da kyau za kuga
a lokacin da kuke saida Na’urar tafida gidan ka (Computer) wani ko
tallan ya riske shi amma bashi da buƙatar ku amma da zaran kun
fara saida wayar salula mai yiwuwa ne a yanzu kun tallata abunda
yake buƙata.

ix. Amsa Kiran da Saƙonni:


Amsa kira akan lokaci babu zaɓi tare da saurin amsa saƙonnin da
aka aike muku kai tsaye ta inbox.

x. Shiga ƙungiyoyi:
Shiga ƙungiyoyi daban-daban da kuke ganin akwai na’u’in mutanen
da suka dace ku tallatawa aikin ku ko kayayyakin da kuke siyarwa.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 24


Isma’il Aliyu Ubale

xi. Tafiya kasuwa don gano sabbin abokan ciniki ta


hanyar zuwa kantunan wasu:
Ta hanyar zuwa babban kanti da tattaunawa da mutanen da ke cikin
shagon kai a matsayinka na ɗan kasuwa za ka iya samun sababbin
kwastomomi cikin sauƙi musamman idan kun ƙware wajen bayyana
sana’ar ku.

xii. Aiki tare da sauran ‘Yan kasuwa:


A wasu lokutan kuna iya tuntuɓar juna kuji cewar ko ana tambayar
ka irin nau’in sana’ar ku ga wasu ‘yan kasuwa? Kuna iya
taimakawa juna wajen kowanne rukuni ya tallata sana’ar rukunin da
ba nashi ba misali: a lokacin da mai yin fenti a gida yana iya tallar
wani mai saida labule (curtains) ko sanyawa a gidaje. Haɗin gwiwa
tare da ‘yan kasuwa na kusa da ku yana taimakawa a gano
kasuwancin ku misali: a lokacin da aka nemi mai irin sana’ar ku a
wajen wanda aka yarda dashi idan ya kawo ku kuma ku zama
amintattu.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 25


Isma’il Aliyu Ubale

CHAPTER THREE (Babi Na Uku)


Consultancy Services and Strategies

Consultancy Services wani nau’in kasuwanci ne me gwaɓi domin


kuwa babu shakka ana samun maƙudan kuɗaɗe a cikin sa.

Don haka Consultancy Services yana nufin: "Shawarwarin ilimi da


wani abu na musamman da ake son aiwatarwa da kuma taimakawa
wajen aiwatarwar"

Yadda tsarin yake Shine da farko zaka zama mutum mai


ƙwarewa da sanin bayanai da tsari akan gudanar da wasu
muhimman abubuwa da mutane zasu buƙata domin rayuwar su ta
yau da kullum, duk da yadda suke son wannan abun basu san ma ta
yadda zasu fara ba ko kuma sun sani amma ba zasu iya ba, ko kuma
suna gujewa yin kuskure a cikin wannan abun to wannan dalilin
zaisa suna buƙatar shawarwari daga ƙwararrun masana a wannan
ɓangare ko kuma suna buƙatar taimakon masana domin cimma
burin su cikin sauƙin gaske, a nan zan bada misalai da yawa dalla-
dalla:

1. Project Consultancy Services:


Mun sani cewar da yawan ɗalibai idan sun zo yin Project na
kammala makarantar su yana matuƙar basu wahala tun daga wajen
samar da Topic da Literature Review da dukkan wasu abubuwan da
ake buƙata anan abune mai sauƙin gaske a matsayin ka na wanda ka
ƙware a Project ka buɗe Project Consultancy Services ba wai ka
dinga yiwa mutane project ba a’a ka dinga ɗaura su a hanya da kuma

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 26


Isma’il Aliyu Ubale

basu dukkan taimako domin suyi project ɗin da kan su kama da daga
Topics, Literature Review da kuma abubuwan buƙata kamar littafan
da zasu taimaka da sauran su, idan ma ta tabbata ba zasu iya ba zaku
iya taimaka musu duka su kuma su biya ku, baya ga haka zaku iya
buɗe assignment Consultancy Services yadda zaku taimakawa
ɗalibai wajen yin assignment da kuma taimaka musu wajen yin
bincike (research)

2. Letter Writing Consultancy Services:


Wannan ma wani babban rukuni ne da idan kuka ƙware akan shi
zaku iya taimakawa abokan hulɗar ku wajen rubuta kowace irin
letter (wasiƙa) ta neman aiki ko ta neman biyan diyya na wani abu
da ya faru ko kuma ta neman taimako ko kuma ta neman
amincewarwani babban mutum ya zamo uba a wata ƙungiya,
sannan da kuma irin na’u’in wasiƙa da ake aikawa masarauta dan
gayyatar zuwa taro ko sauƙa ko bikin yaye Ɗalibai ko kuma irin
wasiƙar da ake aikawa Jami’an tsaro ko kuma irin wasiƙar da ake
aikawa wata hukuma domin yin wani koke (complaint) akan wata
matsala ko kuma wasiƙar bada uzurin rashin halartar taro ko ƙin
zuwa wajen aiki ko nema tallafin zuwa ƙasar waje neman lafiya da
sauran su, ko kuma wasiƙar neman sasantawa tsakanin wasu kai
harma da wasiƙar soyayya ko bikon mata ko kuma wasiƙar karɓar
aiki (Acceptance Letter) ko rubuta wani agreement (Yarjejeniya)
tsakanin Company da Company ko ɗan kasuwa da ɗan kasuwa ko
abokin hulɗa da abokin hulɗa da sauran su waɗannan duka dama
wasu idan za kuyi bincike akan su cikin kwanaki kaɗan zaku tattara
dukkan bayanai kuma ku iya fara gwada kanku sannan ku nunawa

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 27


Isma’il Aliyu Ubale

al’umma kwarewar ku kuma ku tallata kanku akan wannan harkar


kasuwanci ta Consultancy.

3. Curriculum Vitae Consultancy Services:


Curriculum ko kuma kace CV Yana buƙatar ƙwarewa wajen
tsarawa da kuma zamanantarwa da kuma sanin irin yadda ya kamata
a tsara shi ta hanyar lura da inda ya kamata akai shi koda yake da
farko zan fara yin bayanin menene Curriculum Vitae ko CV.
Ataƙaice CV shine "Ƙunshin bayanan kai-da-kai wanda ya ƙunshi
ƙwarewar mutum a wasu ɓangarori da kuma bayyana bayanan
karatun sa da inda yayi aiki da kuma cikakken bayanan ƙashin kai
(Personal details) da kuma bayanan inda mutum yake zaune
(Address) da kuma bayanan wasu fitattun manyan mutane aƙalla
guda biyu da zasu iya tsayawa mutum a matsayin Guarantor ko
wakili, galibi ana ɓukatar CV ne a kamfanoni ko ma’aikatar da za’a
bawa mutum aiki inda karon farko ake buƙatar cewa duk mai neman
aikin ya aika da CV ɗinsa tabbas babu kokonton cewar mutane da
yawa suna rasa samun aiki ne Saboda kuskuren da suke yi lokacin
rubuta CV ɗinsu, don haka wata babbar hanya ce da zaku iya neman
ƙwarewa akan ta kuma ku jarraba kanku kafin ku tallatawa al’umma
cewar kunayi kuma kuna da ƙwarewa akai.

4. Educational Consultancy Services:


Wannan ma wani babban rukuni ne a Consultancy shine samar da
wata cibiyar binciken ilimi da kuma taimakawa ɗalibai da iyayen
ɗalibai akan abunda ya shafi harkokin karatun da kuma jarabawoyi
daban-daban yadda ake yinsu, lokacin da ake rijistar su da kuma
abubuwan da ake buƙatar ɗalibi yayi da dukkanin Sauran bayanai

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 28


Isma’il Aliyu Ubale

haka ma ɓangaren Admission hanyoyin da ake bi da sauran su, sai


kuma ɓangaren online Universities irin National Open University
da kuma manyan Jami’o’in mu da suke da ɓangaren Distance
Learning wato karatu daga gida (Online) wanda kuma ba kowane
ma yasan suna yi ba kamar jami’ar Maiduguri da Ahmadu Bello
University dama wasu duk suna yin Online Program ɗinsu bayan
National Open University ɗin, a taƙaice dai wannan ma babban fage
ne da zaku iya ɗaukar shi a matsayin ɓangaren sana’a na
Consultancy wanda Shima ɓangaren yana da faɗin gaske ya haɗa
da batun karatu a ƙasashen ƙetare (Abroad) da kuma batun
scholarship cikakke (fully funded) da kuma wanda ba cikakke ba
(Partial scholarship) da kuma batun manyan Makarantun mu na
gida masu zaman kansu da sauran su, abunda ake buƙata domin fara
wannan sana’ar bai wuce wayar Android ba da kuma cikakken
lokacin yin bincike da kuma adana binciken, bugu da Ƙari wannan
ɓangaren ya ƙunshi dukkanin harkokin makarantu na gwamnati
(Public) da kuma masu zaman kansu (Private schools) sannan kuma
manyan makarantu da ƙanana.

5. Company Consultancy Services:


Wannan kuwa ya ƙunshi harkar gina kamfani da yiwa kamfani
rajista sanin nau’o’in kamfani, gami da alfanu da kuma dokokin yin
rajistar bugu da ƙari da kuma sanin filla-fillar bayani sala-sala akan
rajista daban-daban wacce ta shafi yiwa kamfanoni da wasu
rukunoni kamar a karon farko rajistar CAC ta rarrabu zuwa Limited
by Shares company da kuma Unlimited by shares, Sannan kuma
akwai Unlimited akwai Kuma Limited by Guarantee babu Shakkar
cewa duk mai ɓukatar yin rajistar kamfani yana buƙatar
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 29
Isma’il Aliyu Ubale

Consultancy domin sanin yadda tsarukan suke, baya ga haka akwai


wasu kamfanoni na musamman kamar yadda ake kafawa ko buɗe
kamfanin Travel (Wato Travel and Tours) da yadda ake kafa
kamfanin Logistics, da kuma yadda ake kafa kamfanin Production
da yadda ake rajistar zuba hannun jari a kamfanoni da sauran su
duka waɗannan abubuwa ne masu muhimmanci da idan kuka yi
bincike kuma kuka fahimta babbar hanyar samun kuɗaɗe ce,
waxannan ayyukan suna daga cikin aikin kamfanin ALBADAR
GLOBAL AGENCY LTD wanda ya ɗauki nauyin wallafa wannan
littafin.

6. Governance Consultancy Services:


Idan fa ana maganar Consultancy a wannan Zamanin to babu iyaka
domin kowanne rukunin rayuwar ɗan Adam yana buƙatar
Consultation, a Nigeria muna da hukumomi daban-daban wanda
ƙididdigar su tana da yawan gaske kuma kowacce hukuma da nata
amfanin yayin da da yawan al’umma wasu abubuwa kan bijiro
musu har su buƙaci wani ɓangare daga cikin aikin wata hukuma
amma abu na farko fa shine sai su rasa ta ina zasu fara misali a
lokacin da tafiya ta kama wasu sukan buƙaci Travel Document
(Wato International Passport) abunda kawai zasu iya tunawa shine
a immigration office ake yin International Passport amma bayan
haka ba suda wata masaniyar yadda abubuwan suke wakana a
wannan hukumar kuma zasu buƙaci hakan wannan fa ɗaya daga
cikin ayyukan immigration kenan amma ayyukan su sunfi gaban
haka irin wannan Services ɗin ne ake kiran su da "immigration
assistance" wato yadda za’a taimaka wajen yin hulɗa da hukumar
abu na farko da za’a fara muku shine cikakken bayanan abubuwan
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 30
Isma’il Aliyu Ubale

da kuke so da kuma hanya mafi sauƙi da za kubi bisa dokokin


hukumar dana ƙasa domin mallakar abunda kuke buƙata a wannan
hukumar, baya ga hukumar immigration akwai hukumomi da
yawan gaske wanda sai kun tashi wani abu da ya shafe su ma
tukunna zaku iya sani kamar hukumar Nigerian Export Promotion
Council (NEPC) hukumar da take kula da harkokin Safara da
fataucin kayayyakin gida zuwa waje da kuma kayayyakin waje
zuwa gida abu na farko da zamu iya tunawa akan shigowa ko fita
da kaya Shine hukumar kwastom wacce ita aikin ta shine hana
shigowa da kayan Laifi wanda doka ta hana ko hana fita da kayan
da doka ta hana sai kuma karɓar harajin kowanne kaya da zai fita
ko kuma ya shigo amma ita hukumar NEPC tana taimakawa
kamfanoni ne wajen harkokin su na shigo da kaya ko fita da kaya
domin akwai matakin da har rancen kuɗi za’a iya bayarwa a
hukumar ko kuma wani taimako na musamman, sai hukumar
National Association of Nigeria Travel Agencies (NANTA) wato
hukumar da take yiwa kamfanonin Travel Agencies rajista a
matakin ƙasa, kada mu tsunduma bayani akan hukumomi ba akan
su muke magana ba muna magana ne akan yadda zamu iya yin
sana’ar mu ta hanyar yin Consultancy akan wata hukuma guda ɗaya
ko kuma wasu hukumomi yadda zamu taimakawa al’umma da
bayanai da kuma yadda zasu cika sharuɗɗa domin wata buƙatar su
a wata hukuma, kamar yadda na faɗa akwai hukumomi a Nigeria
sama da 200 kuma kowacce hukumar idan kukaje kukaga yadda
suke aiki za kuyi tsammanin kamar su kaɗai ne hukumar da take
aiki a Nigeria hakan yana nufin kowacce da nata aikin daban kuma
ana bukatar sa Misali: kamar hukumar da take samar da Lasisin

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 31


Isma’il Aliyu Ubale

tuƙin mota wato driving license da irin su hukumar NDIC kar dai
muyi ta zayyano hukumomin gwara mu bari anan gaba wataƙila
zamu iya yin littafi na musamman akan hukumomin Nigeria da
kuma amfanin su abun lura anan shine kowanne zai iya ƙirƙirar tasa
sana’ar ta Consultancy Services ta hanyar yin nazari da bincike.

Mun bayar da manyan Misalai guda shida (6) akan


Consultancy Services zamu ɗanyi tsokaci kaɗan akai: Ba wai harkar
Consultancy Services ta tsaya bane kaɗai a iyakar abubuwan da
muka lissafa ko kuma bayar da misalai ba, a’a wani fage ne mai
faɗin gaske da akan ɗauki kowanne ɓangare kuma amayar dashi
sana’a ko harkar Banki da buɗe account tana buƙatar Consultancy
Services domin kuwa kawai dai kun jima kuna jin ana cewa Current
Account da kuma Savings account amma fa da yawan ku baku san
bambanci ko kuma amfanin su ba, to kuma ba waɗannan bane kaɗai
tsare-tsaren da bankunan suke dashi akwai nau’o’in asusun
(Account) Banki da yawa wanda ba kusan su ba kuma bakusan yaya
tsarin su yake ba, kuma na tabbatar da yawa al’umma da zasu san
tsarukan zasu buƙata, to dan haka intaƙaice muku kowanne bangare
walau hukuma ko kamfanoni masu zaman kansu ko makarantu ko
wasu abubuwan na daban zaku iya kafa cibiyar wayar da kai da
taimakon al’umma akai da kuma basu shawarwari da yi musu
cikakken bayani ko kuma ta hanyar haka zaku samu maƙudan
kuɗaɗe domin al’umma suna buƙatar shawarwari da taimako akan
kusan kowanne al’amari na rayuwar su.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 32


Isma’il Aliyu Ubale

Yadda zaku kafa Consultancy Services ɗin ku


Abu na farko yin cikakken bincike akan dukkan ɓangaren da kuke
buƙatar zama Consultant kuma ku bada himma ku gwada kan ku,
bugu da ƙari ku nemi tsari da dokokin hukuma idan hukuma ce ko
tsari da dokokin makaranta da hanyoyin samun Admission da kuma
abubuwan da ake buƙata (requirements documents) da sauran su.

Abu na biyu bayan kun tattaro bayanai shine ku fitar da


adadin kuɗin da za’a iya kashewa da duk wani chaji da akeyi a
hukuma ko makaranta daga nan kuma sai ku sanya abunda zaku
chaji kowanne abokin hulɗa mai sauƙi (Services fee) Kuɗin ɗauke
ɗawainiyar Zirga-zirga da gudanar da ayyuka ga wanda aka yiwa
aikin tare da bashi shawarwari.

Digital Real Estate Agent

A zahiri, zamu iya cewa dillalan Gidaje da Filaye da gonaki, a wani


bincike akan wannan harkar ya nuna cewar kaso mafi yawa na masu
yin wannan kasuwancin ko sana’a basa tallata harkokin nasu a
shafukan sada zumunta, ko shafukan yanar gizo kuma wata babbar
damar ma itace da yawa masu harkokin Gidaje, shaguna, ofisoshi
da Filaye da Gonaki kowanne ya ta’allaƙa ne da al’ummar garun su,
wato yanayin hulɗar sa ne da al’ummar garin su kaɗai, yanzu misali
idan ina garin Zamfara kuma ina buƙatar gida a Kaduna to dole sai
nazo Kaduna kafin na iya samun wanda zai nema mun gidan haya
ko kuma na siyarwa wannan wata muhimmiyar dama ce ga mai son
fara irin wannan sana’ar ta yadda zai yi hulɗar sa da mutanen
garuruwa daban-daban, kamar yadda muka sani ne a yanzu komai
ana buƙatar zamanantar dashi da kuma sanya shi a shafukan yanar
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 33
Isma’il Aliyu Ubale

gizo yanzu abun tambayar ko kun sani wani takamaiman shafin


yanar gizo daya ƙware kuma yake ayyukan Samar da gidajen
siyarwa ko na haya ko kuma ofisoshin da manyan shaguna amsar
wannan tambaya kai tsaye zaku iya cewa babu koda zaku faɗa sai
kunyi dogon nazari, a taƙaice ni zan iya cewa a shekaru kusan Uku
(3) baya na taɓa bibiyar wani shafin yanar gizo da ake hulɗar gidaje
sunan shafin Kasuwar Bello koda yake shima bai ɗore ba daga
bisani.

Yanda za’a fara Sana’ar Real Estate Agent:

Abu na farko Shine za muyi nazarin wanna rukuni ko ɓangare zamu


Shiga a dama damu domin kuwa harkar gidaje tana da faɗe.

Abu na biyu Shine mu nemi ƙulla alaƙa da wanda suke


harkar a unguwanni da garuruwa kuma mu ƙulla alaƙa dasu mai
kyau domin lokaci-lokaci, zamu dinga tuntuɓa suna sanar damu ga
wasu gidajen siyarwa ko kuma na bada haya, ko manya da ƙananan
ofisoshi ko wasu wuraren kasuwanci, haka ma a lokacin da abokan
hulɗar mu suka bamu cigiyar cewar suna buƙatar gidan haya kona
siyarwa, ko kuma gidajen gona ko kamfanoni ko kuma waya Hawus
(Wire House) da sauran su zamu kasance ko yaushe muna ɗaura
tallace-tallacen akan shafukan mu da kuma yin cikakken bayani
akai, misali: wannan ofishin ciki da falo ne da kuma Makewayi
(Toilet) kuma yana da girman murabba’i kaza ko Mita, sannan ku
bayyana bayanin kan hanya ko titin da wannan Plaza ko rukunin
shagunan suke, a taƙaice yanzu kun bayar da dukkan bayanai da ake

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 34


Isma’il Aliyu Ubale

buƙatar Sani game da abunda kuke tallatawa na Ofisoshi na haya


kona siyarwa ko kuma gidaje da shaguna.

Abu na Uku Shine samun hotunan waɗannan gidajen ko


shagunan inda za’a tallata su tare da taƙaitaccen bayani akan su,
sannan a lokacin tallan zaku bayar da lambar wayar ku domin
tuntuɓa da kuma adireshin da za’a iya samun ku, ko na shagon wani
abokin ku ne ko kuma gida ko wurin da kuke zama ko kuma
makarantar ku.

Amma wacce za tafi dacewa da Social Media itace harkar


Office. Office a Manya da ƙananan Plaza a garuruwa daban-daban
musamman ga matashi, misalin hakan shine duk inda idon ka ya
ƙyalla kaga wata sabuwar Plaza da aka gina zaka iya bincikawa
kasan tsare-tsaren ta da kuma kuɗin da ake biya duk shekara yayin
da zaka iya tallatawa masu buƙatar irin wannan tsarin abu na farko
da zaka fara yi Shine nemo masu buƙatar ofishi irin wannan kuma
a kwatankwacin wannan wajen, sau da yawa a garuruwa da yawa
wasu ‘yan kasuwa suna fatan kafa reshen su kuma suna shan wahala
wajen neman shago ko Office a inda Suke so, kamar misalin garin
Zaria ace ana neman Office na haya a kasuwar PZ kunga abune mai
wahala ga wanda ba ɗan Zaria ba, amma kasancewar ka Agent na
Samar da haya ko siyarwa zaka iya taimakawa kuma ka samu
kuɗaɗe masu yawan gaske.

Yadda za kuyi hulɗa da abokan ku domin Su taimaka muku

Babu shakka cewa abu ne mai sauƙi idan za muyi wannan harkar a
iyakar garin mu ko kuma inda muke rayuwa amma abu me wahalar
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 35
Isma’il Aliyu Ubale

shine yadda zamu iya samarwa da abokan hulɗar mu Office ki shago


a garuruwan da bama cikin su, abu na farko shine zaku nemi
taimakon abokan ku dake sauran garuruwa kuma zaku dinga yawan
tambayar su lokaci zuwa lokaci kan cewar a wasu manyan wurare
da ake dasu kuma inda ake bada hayar su, su dinga baku labari
al’amarin zai yi sauƙi Sosai anan gaba idan ya zama cewa kun ƙulla
hulɗa da manyan Agents na Sauran garuruwa da yaw kenan hakan
yana nufin cewa zaku iya zama Multi-Agent wato ma’ana kuna
zaune a gari ɗaya amma kuna iya ƙulla hulɗa a garuruwa da yawa.

Wannan fa ba kawai kuna farawa bane zaku samu nasara a’a


abunda ake buƙata shine ku yarda cewa zaku zama Agent na Gidaje,
shaguna, da ofisoshi, kuma ku yarda cewa a karon farko akwai
ƙalubale da zaku fuskanta a matsayin ku na sabbin farawa.

Amma dai har kullum ku saka a ranku cewar za kuyi harkar


ne a shafukan Social Media ta hanyar amfani da sadarwar yanar
gizo, akwai bayani na musamman akan yadda zaku tara abokan
hulɗar ku a shafukan sada zumunta.

Hotel Booking

Wata tsohuwar sana’a ce a ƙasashen ƙetare inda yawancin Agents


na Kamfanoni musamman Travel Companies Suke yin wannan
sana’ar, yadda tsarin yake Shine a lokacin da kuke buƙatar zuwa
wata ƙasar domin wani uzurin ko kasuwanci ko kuma neman lafiya
ko yawon buɗe ido, to lalle kuna buƙatar masauƙin da zaku sauƙa
kuma tunda baku da wani a garin dole hotel zaku sauƙa to sai ku
ziyarci ɗaya daga cikin wanda Suke wannan aikin domin suyi maku
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 36
Isma’il Aliyu Ubale

booking ɗin ɗakin da zaku Kwana, da kuma samar maku motar taxi
wacce za tazo ta tarbe ku a airport domin kai ku wannan masaukin
naku wanda tuntuni an faɗa maku lambar ɗakin kuma an baku
lambar sirri da zaku nuna a baku mabuɗin ɗakin (Keys)

Abu na farko da mai karatu zai fara tambaya Shine: ta ina


za’a samu kuɗi a wannan harkar? Eh yadda zaku samu kuɗi shine
ku naku aikin Services ne na farko kunyi masa booking ɗin hotel
baya nan.

Na biyu kuma zaku turo a ɗauke shi zuwa ɗakin sa a hotel


ɗin to misali idan hotel ɗin kuɗin kamasho dubu goma ne, sai kuma
kuɗin Taxi dubu ɗaya to a nan ku zaka kasha ₦11,000 kenan to zaku
iya Chajar abokin hulɗar ku ₦13,000 zuwa ₦15,000 ko wani abu
da yayi kama da haka.

To nasan Masu karatu za suce ai wannan sana’ar ba zata yuwu ba


to ku biyo alƙalamin nawa domin jin ydda za kuyiirin wannan
sana’ar agida Nigeria kaɗai

Yadda za muyi sana’ar Hotel booking

Da farko zaku buƙaci zuwa manyan Hotel da Ƙanana domin ku


tattauna da masu tarbar baƙi, (Receptionist) wato mai karɓar baƙi
zaku tattauna ne akan kuɗin kowanne ɗaki a Hotel da kuma nu’in
ɗakunan yadda zaku iya yiwa abokan hulɗar ku bayanin yadda
ɗakunan suke idan da dama ma har Hotunan ɗakunan zaku iya
ɗauka amma ba dole bane, to da zaran kun tattara bayanai akan
Hotel da yawa tare da lambobin wayar Receptionist ɗin ta yadda a

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 37


Isma’il Aliyu Ubale

ko yaushe za ku iya kiran su kuji ko akwai ɗaki a yanzu dan haka,


daganan sai ku karkata akalar ku zuwa neman abokan hulɗar ku
wanda za kuyi amfani da salon tallan ku na cewar kuna da ɗakunan
kwanan baƙi na Hotel masu sauƙin gaske kuma da zaran Mutum
yana buƙata zai iya booking harma lokacin da ya shigo gari zaku
tura Taxi a ɗauko shi zuwa masaukin sa, ta haka ne zaku iya tallata
Sana’ar ku a wurare daban-daban musamman manyan tashoshin
mota da kuma filin jirgin sama (airport) da kuma Sauran wurare to
yadda za’a tsara harkar Shine za ayi amfani da masu Taxi ne a duk
lokacin da baƙo ya shigo domin su tarbe shi zuwa ɗakin da aka kama
masa wannan sana’ar zata yuwu a Jihohi irinsu: Kano, Kaduna,
Abuja, Katsina, Bauchi, Adamawa dama dukkan jihohin Nigeria
abunda kawai kuke buƙata shine neman abokan ciniki koda yaushe
tare da wayar da kan mutane akan cewar zasu iya kama ɗakunan
kwanan haya a hotel cikin sauƙi da kuma aminci, ba anan wannan
harkar ta tsaya ba, har ɗakunan taro da wuraren biki zaku neman
bayanai akan su a garuruwa daban-daban tare da ƙulla hulɗar
kasuwancin ku da shuwagabannin da suke tafiyar da waɗannan
ɗakunan taron misali a duk lokacin da za’a yi biki ko wani
gagarumin taro ana neman ɗakunan taro na musamman kuma galibi
masu neman suna nema ne daidai aljihun su babu abunda zai hanasu
tuntuɓar ku idan suna buƙatar cikakken bayani akan farashi da kuma
yadda zasu iya samun ɗakunan taro.

Tsarin “Sale your knowledge online”

Wani Salo ne na amfani da ƙwaƙwalwa da basira da Allah ya baku


domin koyarwa. Muhimmin abu ne daya zama wata babbar

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 38


Isma’il Aliyu Ubale

madogara ga matasa musamman ɗalibai. Na ambaci ɗalibai ne


domin a lokuta da yawa sune suke Shiga tsaka mai wuyar samun
sana’a domin haɗa Sana’a da karatu ba kowa ne zai iya ba, amma
wannan tsarin ba karatu ba ko kaine Alhuda-huda zaka iya yin
wannan sana’ar yadda tsarin yake Shin: duk wani Ɗan Adam da
Allah (SWT) ya halitta yayi masa wata baiwa ko a bayyane ko kuma
a ɓoye (Hiden Talent) wannan baiwar kuwa za kuga cewar wasu
dubban mutane suna buƙatar amfanuwa da ita wanda kuma a ko
yaushe a shirye Suke su koya ko su amfana da wannan ilimin dan
haka ga kowanne mai son fara sana’a ta yadda zai saida ilimin sa ko
baiwar sa a online. To Na farko ya fara gwada Ƙwarewar sa akan
fannin da yake tunanin zai iya bada gudun-mawa kuma ya samu
kuɗi wato wannan abune mai sauƙi idan muka baku misali: a
lokacin da kuke makarantar Sakandare zaku iya tuna wani subject
da kuka fi iyawa da ƙwarewa Misali: Mathematics, Chemistry ko
kuma Accounting ko Economic, ko English, to anan abune mai
sauƙi ku iya buɗe hajar ku ta cewar ku ƙwararru ne a ɓangaren
Turanci kuma zaku koyar da masu buƙatar koyo da ƙwarewa a
harkar turanci ta hanyar ajin online amma da farko kuna buƙatar
kowanne daliɓi ya biya kuɗi ₦200 da farko zaku sanya farashi mai
sauƙin gaske domin tallata kanku Sosai da kuma neman jama’a su
baku dama domin suga ƙwarewar kaku, haka ma idan Economics
kuka iya ko Biology ko Physics, to na kawo misalai ne akan
ɓangaren karatu amma fa ba a nan kaɗai tsarin Sale Your Knowledge
Online ya tsaya ba, duk wata basira da Allah yayi muku koda ba’a
makaranta ake koya ba idan dai kun lura Mutane suna buƙata zaku
iya koyarwa kuma Masu Buƙata Zasu rinƙa biyan kuɗi suna koya,

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 39


Isma’il Aliyu Ubale

misali so da yawa mata ƙwararru kan buɗe ajujuwan koyar da girki


Online ko kuma wasu sana’o’in haka ma maza kan buɗe ajujuwan
koyar da wasu muhimman abubuwa ta hanyar video ko sauti ko
kuma rubutu, kamar zane (art) da sauran su.

Referral Agent

A ko yaushe nakan tuno abubuwa da yawa idan na samu kaina zanyi


magana akan referral Agent ba dan komai ba sai yadda nake ganin
wata babbar hanyar kafa sana’a ko samun kuɗaɗen dogaro da kai,
bugu da Ƙari a yanzu Ni Agent da nake Referring a wasu kamfanoni
kuma abune mai sauƙi masu karatu kuma zaku iya zama Referral
Agent na Kamfanin ALBADAR GLOBAL AGENCY LTD.
Amma kuma da yawa matasan mu basu fahimci yadda tsarin yake
ba, kalmar referral Agent sabuwa ce a furuci amma kuma ba
Sabuwa bace a ma’ana me nake nufi da hakan ?

Abun nufi shine kalmar Referral Agent bata yawaita ba a


gare ku har saida harkar yanar gizo ta shigo cikin ku inda da yawan
shafuka kan bayar da damar zama Referral Agent nasu wato ku
zama mutum mai gayyatowa tare da tallata musu wannan shafi nasu
na yanar gizo ko kuma Application ɗinsu ko kuma wani aiki ko
ayyuka da suke yi zasu bayar da sharaɗin cewar duk mutum ɗaya
idan kun samar yayi rajista dasu zasu baku wani adadin kuɗi harma
zasu faɗa muku idan kuɗin ku sun kai wani adadi zaku iya cirewa
haka mutane da yawa sunyi wannan tsarin musamman masu yawan
ta’amuli da shafukan yanar gizo da kuma dandamalai (Platforms)
da wannan dalilin yasa nace kalmar referral sabuwa ce a furuci

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 40


Isma’il Aliyu Ubale

wato kenan bamusan da wannan furuci ba galibin mu sai bayan


yanar gizo ya yawaita, dalili na biyu da nace amma fa kalmar ba
Sabuwa bace a ma’ana dalilin shine yadda shekaru aru-aru a
kasuwannin mu na garuruwan da muke rayuwa mun san cewar
akwai wasu mutane da ba suda shaguna a kasuwa amma kuma sun
san ciki da wajen kasuwa sun kuma san duk inda ake siyar da komai
da inda za’a samu duk wani abu da ake nema a kasuwar suna
tsayawa ne a manyan hanyoyin kasuwa da Ƙofofi domin da zaran
baƙo yazo zasu tareshi domin sanin me yake buƙatar siya ko yake
nema, nan take zasu kaishi shago ko inda suka san zai samu abunda
yake nema kuma duk inda suka kaishi indai yayi siyayyar mai
shagon zai sallame su, mafi yawan kasuwanni sun ƙayyade adadin
kuɗi da suke bawa duk wani referrer daya kawo musu abokin ciniki
(customer) nasan cewar da yawa masu karatu zasu iya tunawa da
wannan sana’ar musamman a manyan kasuwanni na manyan
garuruwa kuma a kowacce kasuwa akwai sunan da ake faɗa musu
Amma dai a lokutan baya ba’a kiran su da sunan refferal Agent
koda yake har yanzu ma haka.

Yadda za kuyi sana’ar Referral Agent:

Abunda ake buƙata domin zama Digital Referral Agent shine:


wayar Android baya ga haka sai kuma haɗa hulɗa da kamfanoni ko
manyan shaguna da suke sayar da abubuwa daban-daban bayan
haka, sanin bayanai da farashin kayayyakin (items) sai kuma Samun
samfuran kayan a wayar Agent wanda dasu ne zaku tallata kuma ku
samo mai siye ku kawo da zaran kun ƙulla yarjejeniya da shago ko
Kamfani zasu bada farashin kayayyakin kuma duk wanda kuka

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 41


Isma’il Aliyu Ubale

kawo zasu baku kason da sukayi alƙawari na ciniki ba kawai ga


masu siyar da kayayyaki harkar ta tsaya ba harda masu gudanar da
ayyuka daban-daban na Services.

Misali: Zaku iya bayyana kanku cewar kuna son ƙulla alaƙar
kasuwanci da kamfanoni ko shaguna ko masu wasu ayyukan da
sharaɗin cewar duk kwastomomi da kuka kawo zasu baku kason ku,
wannan abu ne mai sauƙi dalili kuwa kowanne mai sana’a yana so
a tallata masa sana’ar sa domin samun sababbin abokan ciniki bugu
da ƙari zaku iya yin wannan sana’ar a duk inda kuke idan kun saba
da kamfanoni ko shaguna da kuke tura musu Mutane kuna gida a
kwance zaku iya sanar da kamfanin cewar kun turo wani sabon
kwastoma kuma da zaran angama zaku bada asusun bankin ku a
turo muku naku kason na cinikin.

Domestic Logistics

Abun mamaki ne a wasu lokutan idan ina ganin wasu damarmakin


ƙirƙirar sana’a amma kuma sai ayi biris dasu. Yanzu wani lokaci ne
na yawaitar aikawa da karɓar kayayyaki daga wasu garuruwan
zuwa wasu koda yaushe a cikin haka ake wasu kayayyakin sun
jiɓanci ‘yan kasuwa wasu kuwa sun jiɓanci al’ummar gari baki
ɗaya, harkar Logistics kamar yadda muka santa sana’a ce (Services)
da wani ko wasu zasu Jiɓanci ɗaukar ɗawainiyar aikewa da karɓar
saƙonnin al’umma na kayayyaki daban-daban daga wata ƙasa zuwa
wata ƙasar, misali yanzu daga nan Nigeria idan ana buƙatar aika
wasu kayayyaki to akwai Logistics Office da za aje abada kayan su
tabbatar da abunda yake ciki sannan su rubuta a littafin adana

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 42


Isma’il Aliyu Ubale

bayanan su, su karɓi kuɗin aikawa da saƙon yayin da su kuma zasu


tara kayan su aika su a Jirgin sama, ko hanyar kwantena, ko Jirgin
ƙasa gwargwadon yadda mai kaya ya buƙaci a aika kayan ko kuma
hanyar da zata yuwu, wannan wani nau’in kasuwanci ne da akeyi
wata muhimmiyar sana’a ce da aka jima ana samun alheri a cikin
ta, amma na fara bayar da Misali ne da ainihin sana’ar Logistics da
nasan masu karatu zasu fi sanin ta, amma Muna Magana ne akan
"Domestic Logistics" wato harkokin ɗawainiya da Jigilar kayan
al’umma daga wani gari zuwa gari a cikin gida Nigeria ko kuma
zuwa wasu ƙasashe da suke maƙota da Nigeria waɗanda ake iya
zuwa a Mota.

Ataƙaice Domestic Logistics ana nufin sadar da kayayyakin


al’umma daga wasu garuruwan zuwa wasu ko kuma daga wasu
unguwanni zuwa wasu.

Yadda zaku Fara

Da farko ana buƙatar kuyi binciken garuruwa da kuma inda ake


samun motocin fasinja zuwa waɗannan garuruwan, bugu da ƙari
musamman garuruwa da suke nes kai tsaye zaku iya tuntuɓar
jami’an tasha domin tattaunawa dasu akan yadda zaku ƙoƙarin
bayar da kayayyaki zuwa garuruwa da dama.

Zaku Jiɓanci ‘Yan kasuwa ne daban-daban daga wurare


daban-daban domin karɓar kayayyakin su a kowanne lokaci, kada
ku manta kuna buƙatar tantancewa na irin nau’in kayan kafin ku
aika shi sannan ku adana bayanan kayan da kuma inda za’a kai. Ba

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 43


Isma’il Aliyu Ubale

rana ɗaya bane zaku fara samun abokan hulɗar ku amma kuma rana
ɗaya ne zaku yanke shawarar fara sana’ar ku.

Jumia Business

Kamar ydda muka sani cewar harkar Entrepreneurship kullum tana


buƙatar sabon tunani da kuma zuwa da abubuwan ƙirƙira, a ko
yaushe tsarin ƙirƙira da jarrabawa da kuma aiwatar da tunanin zuci
zuwa zahiri (Realize dreams) hakane yasa tsawon lokaci na ƙirƙiro
kasuwancin dana sanyawa suna da Jumia Business.

Jumia Business wani nau’in kasuwanci ne na zamani, da


zamani ya samar dashi, kuma yake garawa koda yake na san cewar
masu karatu sun zaƙu domin suji yadda tsarin yake.

A taƙaice wani kasuwanci ne da zai baku damar siyar da


kayayyaki masu wahalar samuwa a kasuwanni, yayin da ku kuma
zaku samu samfuran kayayyakin a kasuwannin yanar gizo irin su
Jumia, Alibabexpress, Konga, Jiji, OLIST da sauran su, na sanyawa
kasuwancin sunan Jumia Business ne Saboda da JUMIA na fara
Kasuwancin.

Yadda tsarin yake kamar yadda muka sani ba wai JUMIA


kaɗai ba dukkanin wasu manyan kasuwannin duniyar gizo na
duniya cike suke da kayayyaki daban daban a kowane rukunin
ababen buƙatar ɗan Adam to da wannan salon ne za kuyi amfani da
wani salo da ake kiran sa da “Difficult Found” wato ababen da suke
da wahalar samuwa a kasuwanni.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 44


Isma’il Aliyu Ubale

Da farko kuna buƙatar sake manhajojin kasuwannin yanar


gizo da yawa a wayar ku, kuma ko yaushe zaku kasance masu Shiga
shafukan kasuwannin yanar gizo domin binciken sababbin
kayayyaki, wanda babu a kusa da inda kuke ko kuma kasuwannin
ku, a wasu lokutan ma zaku iya ganin kayayyaki sabbin kira da
samarwa a duniya, har ila yau kuma zaku iya ganin kayayyakin da
suke an daina yayin su ko kuma sun ja baya a kasuwa.

Anan idan kun lura ana buƙatar manyan abubuwa guda biyar kafin
aiwatar da kasuwancin JUMIA kamar yadda na yanka masa ragon
suna:
i. Application na kasuwannin yanar gizo
ii. Bincike akai-akai
iii. Samun kayayyaki masu wahalar samuwa
iv. Samun sababbin kayayyaki da aka ƙera basu iso gida
Najeriya ba
v. Samun kayayyaki da suka Ja baya a kasuwa

Bayan haka a ko yaushe idan kun lalubo kayayyakin dana faɗa a


sama zaku Shiga tallan su a shafukan ku na Sada zumunta bayan
kun tattaro dukkan ƙunshin bayanai na wannan kayayyakin da aka
zayyana a kasuwar da kuka samo kayan kada ku manta har mafi
yawan kwanakin da kayan zai iso gare ku zaku rubuta ku ajiye
domin a lokacin da zaku tallata kayayyakin zaku sanar da abokan
cinikin ku idan sunyi Oda lokacin da kayan zai zo gare su.

Babu zaɓi na farashi ga abunda babu shi a kasuwa a yanzu


ko kuma abunda bai ma iso Najeriya ba tukunna hakanan kuma

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 45


Isma’il Aliyu Ubale

babu zaɓin siyan wannan kayan awajen wasu shaguna ko


kasuwanni zaɓin guda ɗaya ne Shine a siya kayan a wajen ku domin
a wajen ku aka ganshi har ila yau kuma kune zaku sanyawa kayan
farashi gwargwadon yadda zaku biya kuɗin Mota zuwa karɓowa ko
kuma kaiwa abokin ciniki da kuma ydda za kuci ribar ku, a
shawarce shine ku sanya farashi mai sauƙi idan de kun samu riba ko
babu yawa.

A ƙarshen bayanin JUMIA Business zan so nayi tsokaci kaɗan:

Tsarin kasuwannin yanar gizo irin su JUMIA da sauran wanda


muka ambata da wanda bamu ambata ba, tsarin gudanar da
kasuwanci ne ta ɓangare biyu zaku iya siyayyar ku kuma ku adana
kuɗin ku sai an kawo kayan gare ku wato (pay on delivery) ko kuma
zaku iya siyayyar ku kuma ku biya kuɗin kafin akawo kayan, galibi
kasuwannin suna yin ragi (discount) na wani kaso idan zaku biya
kuɗin ne kafin a kawo kayan, a shawarce zaku iya farawa da biya
bayan ankawo kayan kafin ku samu ƙwarewa a harkar.

Galibin waɗannan kasuwannin ana samun duka irin


kayayyakin da muka ambata a sama na cewar kayan da babu su a
kasuwa ko sababbin kayayyaki da aka ƙera hakan yana faruwa ne
sakamakon kasuwannin suna ƙoƙarin inganta kasuwancin su dan
haka kowanne irin kaya suna ƙoƙarin ɗaurawa akan lokaci kuma
suna da hulɗa da kamfanonin kayayyakin da wasu lokutan ma suna
sawa a sarrafa musu kayayyakin saboda abokan cinikayyar su.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 46


Isma’il Aliyu Ubale

Yadda nayi Kasuwancin Jumia Shekaru Huɗu baya

Naso na gutsira muku labari kaɗan akan lokacin da nayi gwajin


wannan kasuwancin sama da shekaru huɗu da suka wuce a lokacin
ina harkar siyar da Memory Card na Waya, kwatsam sai masu siyar
da Memory suka yi yawa a kasuwannin da nake saidawa dan haka
yanzu akwai gasar kasuwanci (business competition) kai tsaye sai
na nufi kasuwar yanar gizo ta JUMIA inda naci karo da wasu
nau’ikan Memory Card (Red Color, Green Color, da Blue Color)
da ba kasafai ake ganin su ba bayan dana karanta allon bayanan
(description of the goods) kayayyakin na gamsu cewar suna da
inganci nan take na sanya oda (Order) aka bani kwanaki biyar kacal
kafin kayan su iso gare ni, nima nayi amfani da Order ne wacce sai
an kawo kayan zan biya (pay on delivery) nan take na ba zama
tallata waɗannan sababbin Memory Card inda ake ta taruruwar
siyen su, tun lokacin na gamsu da kasuwancin JUMIA.

Marketing Translation Service

Wannan kasuwancin yana nufin kuyi amfani da ƙwaƙwalwar ku


zuwa ga fassara wani ilimi na musamman daga wani harshe zuwa
wani. Ba ku Jiran kowa domin fara wannan kasuwancin abunda
kuke jira Shine ƙwarewar ku da kuma sanin makamar aiki (Actional
Orientation)

MARKETING TRANSLATION SERVICE wani muhimmin aiki ne


da yake taka rawar gani a zamanin yanzu, a ko yaushe kuna buƙatar
Samun ƙwarewa ne wajen fassara da kuma fitar da ma’ana ta asali
da kuma fassara mai ‘Yanci.
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 47
Isma’il Aliyu Ubale

A yanzu da duniya ta dunƙule waje ɗaya sakamakon yanar


gizo akwai shafuka na musamman da suke biyan kuɗaɗen fassara
harsuna musamman a wasu ilimummuka masu muhimmanci, koda
yake ba a wannan ɓangaren nake so nayi magana ba kai tsaye.

Yadda tsarin yake

Zaku nemi wasu litattafai na kimiyya ko wadanda suka ƙunshi wasu


muhimman ilimomi, da yawa al’umma basa fahimtar wannan
harshen da aka rubuta ko kuma fahimtar tana musu wahala, bugu da
ƙari ko wasu lakcoci da aka buga da wani harshe ko kuma wasu
ɓangarorin ilimi da ake da buƙatar sanin su, misali: ilimin yaren
Computer (Programming Language) da ilimin zaurance (coding) na
gina shafukan yanar gizo yana da wuya a same su wadatattu a
harshen Hausa ko kuma a wasu harsunan daba turanci ba, har ila
yau akwai ilimummuka masu ban sha’awa irin su kimiyyar sararin
samaniya da duwatsu da wanzuwar ababen kimiyya da kuma wasu
labarai masu ban dariya ko nishaɗi ko isar da wasu saƙonni ko koyar
da wasu abubuwa kamar sarrafawa da ƙirƙirar abubuwa ko
gyarawa, waɗannan duka fannon ilimi ne da zaku iya sanya kanku
a ciki domin yin bincike da nazari da kuma fassarawa zuwa harshen
da za’a buƙace shi, ba kawai ilimin fassara kaɗai kuke buƙata ba
kuna buƙatar ƙwarewa wajen haɗawa da tsara littafin Dijital na
Ebook ko PDF domin tsarawa tare da fara rabawa masu buƙata
kyauta a karon farko, yayin da zaku buƙaci cewar idan suna buƙatar
wasu sababbin abubuwan daban-daban a harshen Hausa ko wasu
harsunan kuna da su amma akan farashin kuɗi (zaku faɗi kuɗin
dazaku siyar)

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 48


Isma’il Aliyu Ubale

Julius Kume wani baturen Amurka a wata muƙala (article)


daya gabatar mai taken “fassara sana’a” kamar yadda na fassara
taken da harshen Hausa, yabayyana cewar: "koda yake ana buƙatar
izinin mai littafi kafin a fassara Littafin sa duka amma anan muna
Magana ne akan yadda za’a tsakuro wani ilimi a mayar dashi zuwa
duk harshen da ake buƙata a duniya" inji Mr. Kume ya bayyana
hakan ne a Wani taro da akayi na inganta sana’o’i a ƙasar Ghana a
2009. Anan zamu fahimci cewar abubuwan buƙata kafin yin
wannan sana’ar:
i. Ƙwarewa a harsuna biyu ko sama da haka
ii. Ƙwarewa a fassara
iii. Bincike a wani fannin ilimi mai amfani
iv. Samo fannin ilimi da zai janyo hankalin masu karatu
v. Ƙoƙarin tallata fasahar ku

Cikin ƙanƙanin lokaci da waɗannan dabarun zaku samarwa kan ku


sana’a da kuma aikin yi domin kuwa matuƙar kun ƙware a fassara
za’a iya buƙatar kuyi aiki da wata cibiyar ko ma’aikata.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 49


Isma’il Aliyu Ubale

CHAPTER FOUR (Babi Na Hudu)


Zero Capital Business Startup
Ko yaushe maganar mu itace rashin Jari (Capital) ne ya hana mu
kasuwanci ko fara sana’a babbar matsalar mu itace koda mun samu
jari sai mu raina da sunan cewar muna buƙatar dubban ɗaruruwa ne
tukuna kafin mufara kasuwanci bayan kuwa ba haka abun yake ba,
abu na farko ma da muke buƙata shine ilimin yin kasuwancin ba
kuɗi ba a karon farko, babban misalin da zamu fahimta shine mai
kuɗin da ya siya tsohuwar Mota ta dubu ɗari Uku domin ya koyi
motar kafin ya siya ta Miliyan goma, anan zaku fahimci cewar duk
da yana da kuɗi bai fara siyan Mota mai tsada ba duk kuwa da itace
burin sa, sai ya fara siyan Mota mai arha domin yanzu yana buƙatar
koyo ne da ƙwarewa tukunna, amma idan ya siya Mota mai tsada a
karon farko ba tare da ya iya tuƙi ba to kafin ya koyi tuƙin motar
kuma ta gama lalacewa kamar hakane fa idan kuka fara kasuwanci
da jari mai yawa ba tare da kun iya kasuwancin ba, anan ana buƙatar
kufara kasuwancin ba tare da ko sisi ba hakan yana yuwuwa ko
kuma ku fara da wani kuɗi ɗan kaɗan da bai taka kara ya karya ba.

Duk Nazari da karance-karance na ya tafi ne akan yadda za’a


iya kasuwanci ba tare da jari (Capital) ba, saboda Shine matsalar
matasa a yanzu, nasan ta yiwu da yawa suce ba zai yiwu ba, amma
fa ni ba karanta yadda akeyi kawai nayi ba na jarraba kuma na
tabbatar da hakan mai yiwuwa ne tsawon lokaci dana ɗauka ina
gwadawa. Abubuwa biyu ne masana suke yawan ambatawa a
matsayin "Zero Capital Business Startup" wannan tsarin ba’a fiye
magana akan sa ba kamar yadda Xio Lìm ya bayyana a China, amma

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 50


Isma’il Aliyu Ubale

tsarin wani muhimmin tsarin kasuwanci ne da ake amfani da


abubuwa guda biyu kacal a matsayin Capital:
1. Tunani
2. Lafiya

Ma’ana Jarin Sana’a wanda ba tsabar kuɗi ba, kamar yadda a wasu
lokutan muma hausawa muna da wani karin magana "Lafiya Jarin
Talaka" to haka masana sun ambata waɗannan abubuwa kamar
haka:
1. Cikakken Tunani (Complete Thinking)
2. Health (Cikakkiyar Lafiya)

A tsarin Zero Capital Business Startup waɗannan abubuwa biyun


kawai ake buƙata domin fara kasuwanci. Har kullum faɗaɗa tunani
da kuma Jarrabawa sune jigon cin duk wata nasara zamu bada wasu
misalai kaɗan yayin da zasu buɗe tunanin masu karatu suma domin
shigowa da nasu dabarun domin fara sana’a koda babu ko sisin
kobo.

Inter-Middle Business:

Inter-Middle Busines wani tsarin kasuwanci ne na haɗa mai saye da


mai sayarwa suyi cinikayya a ƙarshe kai kuma ka samu wani abu a
wannan cinikin da aka Ƙulla ko kuma wata yarjejeniyar aiki Misali:
idan kaje tasha zaka hau Mota da wuya kaga direba amma za kaga
mai karɓar kuɗin Mota wanda kuma shima direban bega wanda
suka biya kuɗin Motar tafiya ba saidai ace masa mota ta cika, shi
wannan mutumin da yake karɓar kuɗin Mota yana zuwa tasha ne

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 51


Isma’il Aliyu Ubale

babu ko sisi kuma bashi da mota amma kuma zai yi Sana’ar sa,
wannan misali ɗaya kenan a wannan ɓangaren.

Local importing

Local importing wani tsarin kasuwanci ne da ake yin sa musamman


a karkara (Ƙauyuka) ko kuma mazauna birnin da suke kusa da
karkara wato shi yadda yake: akwai abubuwan mu Local wanda
idan anje Jeji zaka iya ɗibar su a kyauta amma kuma idan anzo gari
siyan sa akeyi wannan kuwa ya haɗa da duk nau’ikan ganyayyaki
ko itatuwa ko kuma wasu nau’ikan albarkatu da arziƙin da Allah
SWT ya yiwa Daji/Jeji, Misali a Jihar Katsina suna da wani abu da
ake ɗebowa kyauta a Daji mai Suna "Tattaluɓe" wannan abun galibi
yara da mata suna siyan sa idan an kawo shi cikin gari, kuma shine
idan ya bushe yake zama goruba, kamar a wasu yankunan
Maiduguri kuma a wasu yankunan ana Samun Kifi a dazukansu,
haka a Jihar Kebbi ana Samun ‘Ya’yan kaɗanya, wasu garuruwan
kuma ana samun Bado a Rafuka/Koguna, ba waɗannan kaɗai ba
duk wani abu da za’a iya samowa daga Daji a ɗauko shi a kyauta
kuma a shigo dashi cikin gari a siyar to Shine abunda ake kira
"Local Importing" ko kuma wani mai sauƙin farashi sosai wanda
kusan za ace kyauta aka baku, a ko yaushe tunanin ku a kowanne
lamari yana da muhimmanci Sosai.

Survival Business

A taƙaice ana nufin cewar a wanzar da kasuwanci ba tare da ya


durƙushe ba, da kuma ririta jari (Capital) ba tare da ya karye ba.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 52


Isma’il Aliyu Ubale

Survival Business na ɗaya daga cikin manufar kasuwanci, yana


nufin kiyaye kasuwanci na wani lokaci, musamman lokacin da wani
yanayi na rikici ya zo ko rugujewar tattalin arziƙi ko kuma annoba
(kamar Corona) ko karyewar farashi ko wani iftila’I, don haka zamu
kasa Survival Business kashi Uku:

1. Tsiratar da Sabon kasuwanci da Jarin Kasuwancin daga


rushewa:
Tsiran Kasuwancin da aka kafa sabo ko kuma wanda aka jima anayi
amma yanzu an shigo wani mummunan yanayin tattalin arziƙi, ko
rashin ciniki ko kuma sauyawar farashi daga tsada zuwa arha yayin
da kuke da kaya a ƙasa, kowa wani juyin juya halin iftila’i daya afku
akan kasuwancin ku, ta yanda a lokacin abunda kuke buƙata shine
tsira da kasuwancin ku wannan kenan a rukunin farko

2. Tsiratar da Rayuwar masugudanar da kasuwancin:


Tseratar da kasuwanci daga rushewa sakamakon zuwan zamani ko
kuma sakamakon buɗe wani katafaren kasuwanci irin naku wanda
aka zamanantar Misali: kamar a lokacin da kuke saida magani
(Chemist) a wani ɗan mitsitsin shago a dai dai lokacin kuma azo
abuɗe wani katafaren Pharmacy Store na zamani wanda zai yi
gogayya ko gasar kasuwanci daku ta yanda har farashin ma zai iya
daidai tawa da naku ko kuma ya fiku sauƙi ko kuma a lokacin da
kuke da shagon aski wani yazo kusa daku ya buɗe wani katafaren
shagon aski mai kayan zamani har da na’urar sanyaya wuri (Air
conditioner) wato hakan yana barazanar rushewar kasuwancin ku
kenan to anan ne ake buƙatar kuyi wani yunƙuri da duk mai yiwuwa
domin tseratar da naku kasuwancin gwargwadon iko, ko kuma

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 53


Isma’il Aliyu Ubale

kunayin wata sana’ar da yanzu buƙatar ta tayi ƙaranci, misali zamu


iya kwatantawa da kuma sana’ar rini (dying) waton irin yadda ake
rina shaddodi a bugasu su dinga Ƙyalli yanzu zamu iya cewa sana’ar
tana fama da mashasharar rushewa sakamakon ƙarancin masu
buƙatar ta, ko kuma idan kuna sana’ar dukanci (rufa laya) ko
kyartanci/kyartai (sana’ar sarrafa ƙwarya da gyaran ta) a yanzu za’a
iya cewar sana’o’in suna buƙatar tsira

3. Tsiratar da tsohon kasuwanci a lokacin da barazanar


zamani take ƙoƙarin gusar dashi:
Tsira da mutunci da lafiyar masu tafiyar kasuwanci, hakan yana
nufin cewa wajibi ne da farko idan an kafa kasuwancin a lura da
cewar shin kasuwancin a karon farko zai iya samarwa masu tafiyar
dashi rayuwa? Abunda ake nufi da rayuwa Shine: shin a farkon kafa
kasuwancin zai iya ɗaukar ɗawainiyar ci da sha da kuma lafiya na
masu tafiyar dashi abun nufi anan dole ne a samu mafita idan amsar
itace a’a wannan kasuwancin a farko ba zai iya riƙe ku ba, ma’ana
a yanzu kuna buƙatar wata hanyar da zaku tsira da rayuwar ku
domin kasuwancin ku ya tsira, misali; a karon farko kun fara sana’a
da jari (Capital) na ₦10,000 amma kuma wannan sana’ar bata iya
Samar muku da kuɗin abincin da za kuci a wuni, wataƙila kuna cin
abincin ₦500 a wuni ɗaya idan an haɗa harda kuɗin siyen ruwan
leda (Pure water) da kuɗin Mota zuwa inda ake kasuwancin ta yuwu
a kowanne yini kuna kashe ₦1,000 (Dubu ɗaya) to nawa kuke samu
a wannan kasuwancin naku, a kullum in mukace zaku samu ₦800 a
kullum, kuma kuna kashe ₦1,000 domin cin abinci da kuɗin motar
ku, to yanzu anan kasuwancin ku ba zai tsira ba, kuma ba zaku tsira
ba sannan kuma Jarin ku ba zai tsira ba ina fatan yanzu bayanin ya
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 54
Isma’il Aliyu Ubale

fito a bayyane Sosai. Mafi yawancin mutane suna kukan cewar Jarin
su ya karye a mafi yawan lokuta ba tare da lura da ko me ya karya
Jarin ba, wajibine ku kula da duk inda kuɗaɗen kasuwancin ku suke
da kuma ƙididdigar yadda suke shigowa, lissafawa tare da tsara
komai zai baku damar Sanin ina kuɗaɗen ku suke zurarewa har ku
iya toshe hanyar.

Yadda zaku tseratar da kasuwancin ku

A yayin da da kuka lura abunda kuke kashewa yafi abunda kuke


samu a sana’ar ku to tabbas kuna buƙatar yin Survival Marketing
process wato ku samar da wata hanya da zata iya taimaka muku
wajen tsira da rayuwar ku, Misali kuna yin wannan kasuwancin
naku da niyar kuna fatan nan gaba zai ci gaba ya bunƙasa harma ya
riƙe ku, ya kuma samar muku ababen More rayuwa ko kuma ya
zama babban Kamfani wannan manufar itace kaɗai zata sa kuyi
kasuwancin da a karon farko baya iya biya muku buƙatun rayuwar
ku, wato kuna mafarkin wata rana ya girma kuma wannan itace
hanyar da akabi kowanne kasuwanci har ya girma, to abun lura anan
tunda kasuwancin ba zai riƙe ku a yanzu ba dole kuna buƙatar wata
sana’ar a gefe guda wacce itama zaku kirata da Survival Business
wato itace sana’ar da kuka riƙa domin ta tallafa muku ku tsira da
rayuwar ku, da sana’ar ku da kuma Jarin ku.

Yadda za kuyi
Zaku duba wata sana’ar da take da ƙayyadadden lokaci misali a
siyar da Dabino a watan Ramadan ko siyar Fulas ɗin shayi (Vaccum
Flask) ko siyar da kayan marmari, ko kuma siyar da wuƙaƙe da

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 55


Isma’il Aliyu Ubale

kasko a lokacin ƙaratowar sallar layya, ko kuma siyar wani nau’in


kayan marmari a lokacin wahalar sa, kamar misalign masu siyar da
Rake (sugarcane) ko mangoro koma duk wani nau’in kayan
marmari da lokacin yayi ƙaranci wannan wani salo ne na siyar da
abunda babu shi da yawa a kasuwa kuma babu shakka za kuyi ciniki
da kuma samun riba, wato idan kun lura za kuga cewar duk wata
sana’a mai lokaci tana da riba Sosai kuma tana da ciniki to
amatsayin ku na masu neman tsira da sana’ar ku zaku iya rungumar
wannan kasuwancin na ɗan lokaci, ko kuma kuyi amfani da ƙarfin
ku wajen yin wani aikin ƙarfi lokaci-lokaci domin ku dinga samun
abunda zaku dinga tafiyar da rayuwar ku kafin sana’ar ku ta farko
ta girma.

A Yayin da kuka lura sana’ar ku zamani yana neman gusar


da ita ko kuma wani katafaren shagon da yake kusa aku yana neman
shafe labarin naku shagon to anan kuna buƙatar improvisation da
innovation wato ku inganta kasuwancin ku da kuma ƙirƙirar wasu
sabbin sana’o’i da zasu dace da irin wanda kuke yi da a yanzu kuke
buƙatar farfaɗo da sana’ar ku, tare da tseratar da ita da hura mata rai
kada ta mutu, kuna buƙatar abubuwa guda Uku:
1. Nazari
2. Neman shawara
3. Neman Ƙarin Jari

Bayan kunyi nazari kuma kunyi shawara a yanzu kuma buƙatar ku


samu ƙarin Jari domin inganta kasuwancin ko kuma ƙirƙirar wani a
haɗashi da wanda akeyi ɗin. Abune mai matuƙar muhimmanci riƙe
sana’a tun tana ƙarama har ta zama babba.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 56


Isma’il Aliyu Ubale

Entrepreneurship Improvisation and Developreneur

Entrepreneurship improvisation wani muhimmin batu ne dake nuna


yadda, za’a inganta kasuwanci daga ƙarami zuwa babba da kuma
inganta kasuwancin a lokacin da ake da ƙaramin Jari (Capital) ko
kuma a rashin wasu muhimman abubuwa na gudanar da
kasuwancin.

Manufar inganta harkokin kasuwanci za’a iya bayyana shi a


zaman wani yunƙuri ‘yan kasuwa na fara kasuwanci gwargwadon
yadda za’a iya tare da samar da mafita cikin sauri, kamar yadda ake
amfani da kalmar "bricolage" mafi yawan lokuta a cikin zane-zane
(art) da take nufin yin amfani da abunda ake dashi.

Ingantawa ko inganta kasuwanci na iya haɓɓaka warware


matsala, ƙirƙira, da fikira, kuma yana zama abun buƙata ga ƙananan
‘yan kasuwa da yawa musamman masu burin fara kasuwancin
Dijital, ko da yake haɓakawar na buƙatar haɓaka matakai da
ƙwarewa da horo musamman. Don haka zamu kasa
entrepreneurship improvisation gwargwadon fahimtar mu zuwa
kashi biyu:

Inganta kasuwancin da ake dashi


Matakin farko shine muke buƙatar cikakken bayani domin har ya
kaimu zuwa ga yadda zamu inganta kasuwanci zuwa kasuwancin
Dijital. Kowanne ɗan kasuwa da yake yin kowanne irin kasuwanci
a ko yaushe babu wani takamaiman lokaci yana buƙatar inganta
harkokin kasuwancin sa, abun nufi anan yanzu idan an tambaye ku
yaushe ne zaku iya tuna cewar kun inganta Kasuwancin ku ? ba
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 57
Isma’il Aliyu Ubale

lallai ne amsar tambayar ta zama satin daya wuce ba ko wata, hakan


yana nufin cewa baku inganta kasuwancin ba tsawon lokaci domin
ya tafi daidai da zamani, ko kun san cewar rashin inganta
kasuwancin ku ne yake sawa a barku a baya, ban sani ba ko kun
fahimta ga wani misali: mafi yawan masu sana’ar yankan farce
(Nail Cutting) a arewacin Najeriya za kuga ko yaushe yawo suke yi
har yanzu basu inganta kasuwancin su ta hanyar buɗe shago kamar
yadda masu aski suke yi ba, kuma babbar asarar da suke yi wasu
wanda ba masu sana’ar ba suna buɗe shagunan kuma su ɗauko masu
sana’ar suyi aiki a ƙarƙashin su sakamakon rashin improvisation
kamar yadda kuke ganin ana buɗe shagunan gyaran ƙafa na zamani
wanda ciki har da yankan farce.

Kamar mayar da sana’ar zahiri kasuwancin Dijital yana ɗaya


daga cikin improvisation wato a baya bakwa tallata Kasuwancin ku
a online amma yanzu kun fara, ko a abaya baku da website amma
yanzu kuna da shi, Misalin wani mai tuƙa Keke Napep (Adaidaita
sahu) a Kano daya inganta tuƙin sana’ar sa zuwa digital inda yake
tallata kasuwancin sa a yanar gizo kuma mutane da yawa kan
tuntuɓar sa domin yazo ya kaisu wurare ko kuma ya ɗauko musu
wasu kayayyaki ba ƙaramar dama ya samu ba kuma yake amfani da
ita kai tsaye a shafin Facebook zaku iya ziyartar shafin sa ta hanyar
binciko sunan sa kamar yadda yake amfani dashi "Matukin babur
ɗin adaidaita sahu" wato zai birge ku idan kunga yadda yake
gudanar da kasuwancin sa ko yaushe a cikin Improvisation.

Wani misali da zai ƙara fitowa fili shine ku lura da masu


sana’ar gasa nama kamar kaza ko tsire ko balangu, za kuga wasu

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 58


Isma’il Aliyu Ubale

koda yaushe wajen kasuwancin su yana cike da jama’a anata


cinikayya yayin da kuma za kuga wasu sam-sam ko yaushe wajen
babu kowa sai ɗai-ɗaikun mutane amma duk da rashin mutane ba
tare da sai mai siyan yabi dogon layi ba tanan zai wuce zuwa ga
wurin da ake dogon layi wannan kuwa ya faru ne sakamakon
inganta kasuwancin da rashin ingantawa, wani mutum dana siya
kaza awajen sa babu ko yaji aciki baya ga rashin daɗin gashin sa
kuma, ga rashin iya kula da Kwastomomi domin kuwa hatta ledar
daya saka kazar dana siya bai kamata yayi haka ba.

Ataƙaice ko yaushe kada ku zargi kowa akan sana’ar ku, ku


zargi kanku da rashin ingantawa shiyasa baku cigaba ba, yana da
kyau duk abunda za kuyi ya zama kun nemi ilimin sa da ƙwarewa a
cikin sa ta yadda zaku inganta shi ya zama sai sam-barka, koda
kuwa a yanzu kasuwancin ku yana biya muku buƙatun ku shin
bakwa tunanin cigaba da bunƙasa wa har kuma kukai inda wasu
suka kai!

Inganta Kasuwancin da za’a fara


Inganta kasuwancin da za’a fara kuwa misalin sa dalla-dalla
shine: yadda malamin makaranta zai karantar da wani abu da yake
buƙatar nunawa ɗalibai zahirin abun ba hoto ba, kuma abun yana da
tsada ko wahalar samuwa to kamar misali Malami yana ƙoƙarin
nunawa ɗalibai yadda wata dabba take kamar maciji to anan zai iya
zuwa da macijin roba a madadin na gaske, to haka abun yake ga
kafa kasuwanci ko yaushe mutane kanyi ƙorafin rashin Jari
(Capital) ko kuma rashin kayan aiki wadatattu ko kuma wani abu
na daban. A ko yaushe abunda ake buƙata a wannan ɓangaren na

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 59


Isma’il Aliyu Ubale

improvisation shine zurfafa tunani tare da ƙarfin gwiwa dajin cewa


zaku iya, ta haka ne kawai za’a samu mafita mai ɗorewa, kamar
yadda kuka sani duniya cike take da abubuwa da yawa ta yadda
wasu suke maye gurbin wasu idan kun lura za kuga cewar gida
sunan sa gida amma gidaje suna da bambanci a tsakanin su yayin
da gidan da akayi da laka10 a ƙauye sunan sa gida haka gidajen dake
birane ƙerarru sunan su gida kuma duka manufa ɗaya ake tunkara
dasu, haka abun yake ga gudanar da kasuwanci a ko yaushe za kuyi
ƙoƙarin yin kasuwancin ku ta hanyar ingantawa gwargwadon
abunda kuke dashi a lokacin.

Improvisation a wannan bangaren yana bayuwa zuwa ga


abunda ake kira "Developreneur" wato maida wani abu da ba sana’a
ba zuwa ga sana’a.

Developrenuer
Developreneur tsarin da yake tasiri a tafiyar Digital
Entrepreneurship, koda yake Tiara Mandera wani fitaccen
Entrepreneur ɗan Ƙasar India yace: Kalmar bata yawaita ba a baki
ko kuma a rubuce amma kalmar ta daɗe tana aiki a aikace, abunda
ake nufi da kalmar Developreneur Shine: "Zamanan tar da wasu
abubuwan su koma Sana’a wanda ta yuwu a baya ba’a ɗauke su
sana’a ba" ko kuma inganta wani abu daga ƙaramar sana’a zuwa
babba, ko kuma maida wani abu da yake normal ne a cikin al’umma
ya koma sana’a. Mutane da yawa kan samun kansu a cikin wata
sana’a da a farkon farawa suna yi ne domin nishaɗi ko wasannin

10
turbaya
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 60
Isma’il Aliyu Ubale

gida, da yawa masu sana’ar dambe ko kokuwa wasannin al’ada ne


kan kaisu zuwa ga mayar da dambe ko kokuwa sana’ar su.

Babban Misali shine wasan barkwanci, a shekarun baya kalmar


Comedy bata shahara ba amma ai a cikin al’ummar mu, munsan
wasu da muke yiwa laƙabi da masu barkwanci ko ban dariya amma
da tafiya tayi tafiya sai barkwanci ya zama Comedy wanda ake yi a
Samu wasu ‘yan Kuɗi Ƙalilan kuma a burge Mutane amma da tafiya
ta ƙara tafiya yanzu Comedy ya zama wata babbar Sana’a ko kuma
katafariyar hanyar Samun kuɗi a duniya baki ɗaya kamar a Nigeria
muna da wasu fitattun Mutanen da suka yi suna a Comedy kuma
suka zama Hamshaƙan masu Kuɗi daga cikin su akwai marigayi
Rabilu Musa Ibro (Allah ya jiƘan sa) daga Kudancin Nigeria kuma
akwai irin Su: Ojo/Mama Ojo (Mai yin shigar Mata) da kuma Mark
Angel da irin su Emmanuella da sauran su, a ƙasashen Ƙetare kuwa
akwai fitattun masu barkwanci (Comedy) irin Jack na ƙasar
kwaddebuwa11 da sauran su. To a taƙaice wannan shine bayanin
wani ɓangare na Developreneur.

Ga wani misali a lokacin yarinta mukan yi wasanni da sunan


Nishaɗi amma daga ƙarshe wasu wasannin zasu iya komawa
Sana’ar mu ta dogaro dakai hakan yana nufin a tsarin
Developreneur komai na iya komawa Sana’a banda wasu tsirarun
abubuwa kamar addini da sauran su kamar yadda Huaxink wani
fitaccen Entrepreneur ɗan ƙasar China ya faɗa. Don haka muma a

11
Côte d'ivoire
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 61
Isma’il Aliyu Ubale

lamurran mu na yau da kullum zamu iya yin amfani da wannan


salon domin mayar da wani abu Sana’a.

A taƙaice wannan bayanin yayi nazari akan yadda ƴan


kasuwa ke amfani da haɓɓakawa domin dacewa da yanayin sauyin
yanayi da zamani ta hanyar lura da kasuwanci ko sana’a, ingantawa
tana faruwa ne lokacin da ya zama akwai buƙatar yin hakan zuwa
ga cimma wani buri. Don haka, ana bada shawarar cewa a samar da
wani ma’auni na ɗabi’a don taimakawa ‘yan kasuwa da masu
bincike wajen tantance abubuwan da suka dace don aikin
ingantawa, gina sabuwar ka’ida da haɓaka tsarin horo na aiki.

Summary of Company Registration in Nigeria

Kafa kamfani a Nigeria wata muhimmiyar dama ce ga matasa


domin su shigo suma a dama dasu, kamfani ba kamar yadda mafi
yawan lokuta ake tunani bane, a ko yaushe matasa kan tsorata da
zaran sunji maganar kafa kamfani, sakamakon yadda suke da
ɗaukar abun da girma, eh ƙwarai harkar kamfani abune mai girma
amma ba kamar yadda mafi yawan Mutane suke tunanin cewa su ba
zasu iya ba, a lokuta da yawa daga anyi maganar kamfani mutane
kan tuna cewa wani katafaren gini da abubuwa wannan kuwa baya
rasa nasaba da yadda muke ganin wasu manyan masana’antu da ake
kira da kamfani.

Da farko abun lura shine wanne irin kamfani za ayi? A


shawarce shine matasa zasu iya farawa da Micro Business, wanda
yana ɗaya daga cikin kasuwanci ƙarami wanda ba za’a ɗauki
Mutum fiye da goma ba a cikin shi ko ƙasa da haka. Mafi yawancin
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 62
Isma’il Aliyu Ubale

waɗanda suke waɗannan kasuwanci suna dogara da kansu


Sakamakon ribar da suke samu mai riɓanya. Abubuwan da ake
buƙata don fara Micro Scale Business sune:
1. Jarin da ba zai gaza ₦50, 000 zuwa ₦100,000 ba.
2. Samun ma’aikatan da ba su gaza goma ba ko ƙasa da haka

Mafi yawancin Micro Business suna buƙatar rajistar CAC12, da


tsarin kasuwanci (Business Plan) domin haɓɓaka kasuwancin su.

Kalubalen da Ma su Micro Scale Business Ke Fuskanta


1. Rashin Samar da abunda zai ƙayatar da Kwastomomi
2. Rashin Samar da tsayayyen tsari
3. Rashin Samar da Shafin Kasuwanci na yanar gizo
4. Rashin Mayar da hankali wajen tallatawa a Social Media
5. Tara wa mutum daya ayyuka da yawa

Don haka, abun bukata don warware wannan ƙalubale shine:


ƙirƙirar sababbin dabaru da tallata Kamfani a duk Social Media,
Samarda ingantattun Injinan aiki da Softwares masu tsari da nagarta
gwargwadon yadda za’a iya.

Saboda haka abu na farko mafi muhimmanci shine yin rajista da


hukumar CAC, hukuma ce dake yiwa kamfanoni ƙanana da manya
rajista wanda akwai rabe-raben rajistar wato business name da
Company Registration.

12
Coorperate affairs commission
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 63
Isma’il Aliyu Ubale

Bambancin Business Name da Company Name


Dukan su rajista ce da ake yi da gwamnatin Nigeria domin
kasuwancin ku ya samu Legal baking13 saidai Mutane da dama
sukan kasa gane bambancin dake tsakanin su.

Shi Business Name rajista ce da zaka yiwa kasuwancin ka


wanda zai zama yana da Legal baking, sannan kuma babu wani
wanda zai yi amfani da irin wannan sunan, sannan kuma idan wani
rigima ya haɗa ku da Customers dinku har ta kai ga za aje matakin
Shari’a, to ba Business ɗinku bane za’a kai ƙara, ku za’a kai ƙara In
Person14 yayin da Shi kuma Company idan wani abu ya faru
tsakanin ku da kwastomomin ku to ba ku za’a kai ƙara ba, kamfanin
ne za’a kai ƙara, saboda ya zama artificial person15 amma shi
business name ba artificial person bane.

Amma shi kuma Business Name idan ka ƙulla Kwantaragi da wani


Kamfani ko ɗaiɗaikun mutane sai kasuwancin naka ya karye ya
zama ba kuɗin, kuma babu kayan to dole saika biya mutane kuɗin
su.

Wanne yafi dacewa kuyi?


Ya danganta da yanayin kasuwancin naku da kuma girman shi da
kuma ma Capital ɗinku, Misali: Mu ɗauka kasuwancin ku ya kai na
miliyoyin nairori, to wanda ya dace kuyi Shine “Company
Registration, Wato Limited Liability Company”

13
Wato goyon bayan doka
14
A ƙashin kan ku
15
Mutum-mutumi
A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 64
Isma’il Aliyu Ubale

Idan kuma matakin farko ne na farawa da kuɗaɗe ‘yan kaɗan to sai


ku fara a matsayin Micro business yayin da za kuyi rajistar Business
Name ba kamfani ba.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 65


Isma’il Aliyu Ubale

CHAPTER FIVE (Babi Na Biyar)


Wall Advertisement

1. RAHINAT SCHOOL OF LAW (E-Learning)

Dangane da Makarantar:
Wannan Makarantar tana bawa dalibai horo na musamman akan
abunda ya shafi dokokin kasa da dokokin musulunci da kuma sanin
‘yancin kai ta bangaren abubuwan da suka wajaba ga mutum a
matsayin shi na Dan Kasa ya aikata su, da kuma wadanda suke
haramun ne ya aikata su. Kazalika, Makarantar zata taimaka ma
dalibai da suke da Sha’awar Karatun Law, hakan ne ma yasa
makarantar take koyar da darussan tad a harshen Hausa ta yadda
kowa zai fahimta cikin sauki.

Makarantar tana koyar da Kwasa-kwasai 12, dan haka idan


mutum ya kammala karatun za’a bashi takardar Shaidar
kammalawa ta “Pofessional Certificate in Law”

Sannan kuma tana da bangaren Advanced Class, inda shi kuma take
koyar da Kwasa-kwasai guda 10, amma sai wanda yayi Professional
Certificate ne yake da damar Shiga Advanced Class din ko kuma
wanda yayi wata makarantar law.

Ga Jerin Kwasa-kwasan da Makarantar take koyarwa a bangaren


Professional Certificate:

i. Introduction to Law
ii. Nigerian Legal System

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 66


Isma’il Aliyu Ubale

iii. Constitutional Law


iv. Criminal Law
v. Law of Tort
vi. Introduction to Islamic Law
vii. Legal Writing
viii. Islamic Law of Crime
ix. Islamic Law of Tort
x. Laws of the Federation
xi. Legal Maxims
xii. Legal English

A bangaren Advanced Class kuma zamu koyar da wadannan


Kwasa-kwasan:
i. Law of Contract
ii. Company Law
iii. Banking Law
iv. Law of Insurance
v. Commercial Law
vi. Islamic Law of Transaction
vii. Islamic Family Law
viii. International Law
ix. Land Law
x. Labour Law

Domin Shiga wannan Makarantar zaku iya tuntubar wadannan


lambobin: 08025498888, 08038463491 ko kuma Email Address:
[email protected] ko kuma ku ziyarce ta a shafin tan a yanar gizo
www.rahinatschooloflaw.com.ng

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 67


Isma’il Aliyu Ubale

2. ARABIC GRAMMAR AND CULTURE SCHOOL (E-


Learning)

Dangane da makarantar

Makaranta ce da take koyar da harshen larabci da bangarorin sa


wanda suka hada da: grammar (Nahawu) Adabi (Arabic Literature)
da kuma Balaga (Rhetoric). Makarantar tana da ajujuwa kamar
haka: Basic Class ga dalibai masu son koyon rubutu da karatun
larabci da kuma Advanced Class ga daliban da suke neman
kwarewa da sanin ka’idar larabci, Sannan Student Class ga daliban
da suka iya tuiranci suke son koyon larabci.

Abubuwan da Makarantar take yi:

Abubuwan da take yi sun hada da: Arabic TypeSetting, Arabic


Letter, Arabic Project and assignment, Arabic Editing da Content
Writing, Arabic Books Publishing.

Domin Shiga Makarantar sai ku tuntubi wadannan lambobin:


07039875423, 08087584902.

3. BADAR ENTREPRENUERSHIP SCHOOL (E-


Learning)

Dangane da Makarantar:
Makaranta ce da take koyar da dabarun kasuwancin zamani da
kuma bayar da horo na musamman da kirkira da rainon sababbin
kasuwanci da sana’o’i. makarantar tana da ajujuwa kamar haka:

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 68


Isma’il Aliyu Ubale

Basic Class, ga dalibai masu koyon kasuwancin zamanin daga tushe


da kuma Advanced Class ga dalibai masu son cigaba da samun horo
akan kasuwancin zamani na Digital.

Kazalika, Makarantar tana taimakawa kamfanoni da matsakaitan


kasuwanci wajen yin rajistar da ta dace da kasuwancin su da kuma
tallata hajojin su.

Domin Shiga makarantar sai ku tuntube su ta wadannan hanyoyin:


Lambar waya: 08088119753,
Email: [email protected]

4. FLOWDIARY ACADEMY (E-Learning)

Dangane da Makarantar:
Makaranta ce dake koyar da muhimman darussan computer da na
yanar gizo wanda suka haɗar da: Android Development, Software
Development (Desktop), Crypto currency, Web design, Cyber
security, Graphic design, Data science, SQL, Java Script,
Networking, PHP, WordPress da sauran su. Makarantar tana
ƙarƙashin babban kamfanin Alphamega Limited.

Domin shiga Makarantar sai ku tuntuɓi wadannan lambobin kamar


haka: 08162374764

Ko ku ziyarce su a Shafin sun a yanar gizo:


https://flowdiary.com.ng/enrol.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 69


Isma’il Aliyu Ubale

5. ACL COMPUTER ACADEMY (E-LEARNING)

Dangane da Makarantar:
Makaranta ce dake koyar da darussan computer da harshen Hausa,
kuma take bayar da horo na musamman akan Ethical hacking da
Cyber security da kuma graphic design. Bugu da ƙari makarantar
tana siyar da sababbin computer masu inganci a cikin farashi mai
sauƙi, domin tuntuɓa 08137350232

6. ALBADAR GLOBAL AGENCY LTD

Dangane da Kamfanin:
Kamfani ne da ya ƙware wajen gudanar da ayyuka kamar haka:
Tikitin Jirgi a gida da waje (International and domestic Flight)
Dubai Visa, Egypt Visa domin Ɗalibai, India Visa domin zuwa
asibitoci da kuma uwa uba Visa zuwa Saudiyya domin yin Umara
ko kasuwanci ko kuma Hajji. Bugu da ƙari kamfanin yana samar da
Admission ga ɗalibai a ƙasashen ƙetare (Abroad Universities) Baya
ga haka kamfanin yana taimakawa wajen shigowa da kayayyaki
Najeriya ko fita dasu. Sannan Kamfanin yana taimakawa ƙananan
Kamfanoni da ‘yan kasuwa domin cimma burin su na kafa
kasuwancin su ko ingantawa

Domin tuntuɓa sai ku nemi daya daga wadannan lambobin:


08086251045, 08134692043, ko kuma ta adireshin Email:
[email protected]

7. STACKPLAZA

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 70


Isma’il Aliyu Ubale

Dangane da Kamfanin:
Kamfanin Stackplaza shi kaɗai ne irin sa a arewacin Najeriya
Wanda matashi kuma bahaushe ya kafa. Stackplaza Babbar
kasuwar yanar gizo ce kamar JUMIA Inda kowanne mai buƙata zai
iya buɗe katafaren shago domin siyar da kayayyakin sa, yayin da
Kuma mai siye zai iya samun kowanne irin kayayyaki yake buƙata
a mashahuriyar kasuwar. Kai tsaye zaku iya garzayawa babban
shafin su a: www.stackplaza.com Ko ku tuntuɓi wannan lambar
domin ƙarin bayani 08162374764

TALLAN LITTATTAFAI:

1. ƊAN SANDA ABOKIN KOWA


Wannan littafi mai Suna “Ɗan Sanda abokin kowa” na
rubuta shi ne duba da cewa Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda sune suka
fi kowanne Jami’in tsaro kusanci da al’umma, kasancewar sune
dokar ƙasa ta wajabta masu kare rayuka da dukiyoyin al’ummar
ƙasa, to sai naga cewa ya kamata ace akwai wani littafi na
musamman a cikin harshen Hausa wanda zai yi bayanin hakkoki da
hurumin da Jami’an ‘Yan sandan suke dashi a lokacin gudanar da
ayyukan su na tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wannan littafi zai warware matsaloli da dama da suke


faruwa tsakanin Jami’an ‘yan sanda da kuma ɗaiɗaikun mutane a
lokacin da jami’an ‘Yan sandan suke gudanar da ayyukan su na
tsaron Rayuka da dukiyoyin al’umma. Littafin yana da matuƙar
amfani ga duk wani ɗan Nigeria musamman ma wanda yake iya
magana da harshen Hausa. Sannan littafin yana da matuƙar amfani

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 71


Isma’il Aliyu Ubale

ga su Jami’an tsaron na ‘Yan Sanda wajen sanin hurumin su da


sanin abubuwan da zasu iya yi wajen gudanar da aikin su a
matsayin su na ‘Yan Sanda
Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah
Mallakar: Na’Allah & Rahinat Foundation

2. CIKAKKIYAR KARIYA
Littafi ne da yayi magana akan ɓangaren bayar da kariyar Hacking
ga wayoyi da compute, bugu da ƙari da kuma yadda Mutum zai kare
kansa faɗawa komar ‘yan damfara

Marubuci: Salisu Abdurrazak Sahil


Shugaban Arewa Computer Library

3. ENGLISH LITERATURE DA HAUSA


Littafi ne da yayi bayani akan adabin turanci da Hausa wanda ya
tattaro muhimman abubuwan da suka shafi Adabin turanci kuma
yayi bayani da yaren Hausa
Marubuci: Muhammad Nura Sallau ‘Yar Hanji
Mallakar: Arewa Students’ Orientation Forum

4. CHEMISTRY DA HAUSA
Littafi ne da aka fassara darasin Chemistry a matakin Sakandare
zuwa yaren Hausa
Marubuci: Kabir Abdullahi Ƙanƙara
Mallakar: Arewa Students’ Orientation Forum

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 72


Isma’il Aliyu Ubale

5. PHYSICS DA HAUSA
Littafi ne da aka fassara darasin Physics a matakin Sakandare
zuwa yaren Hausa
Marubuta:
Isah Hamza Excellency
Abba Haladu Umar
Mallakar: Arewa Students’ Orientation Forum

6. BIOLOGY DA HAUSA
Littafi ne da aka fassara darasin Biology a matakin Sakandare
zuwa yaren Hausa
Marubuci: Muhammad Salisu Kamfani
Mallakar: Arewa Students’ Orientation Forum

7. BEGINNERS GUIDE FOR GRAPHIC DESIGN


Littafi ne da ya ƙunshi bayar da horo akan Graphic Design da kuma
dabarun sanin makamar aiki. Abubuwan dake cikin sa:
 Ma’anar Graphic Design
 Rabe-Raben Graphic Design
 Inda ake Samun Kayan aikin Graphic Design
 Background
 Images & Icons
 Yadda ake Samun Font
 Inda ake Samun Texture
 Wacce Kala Ce ta dace da aikin Ka
 Wanne Font ne Ya dace da aikin Ka
 Application & Softwares Na Graphic Design

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 73


Isma’il Aliyu Ubale

Marubuci: Khalil Shu’ibu Garunbabba

8. FREELANCING KASHI NA ƊAYA


Littafi ne da akayi shi musamman akan fara kasuwancin
Freelancing ga masu sha’awa, kuma littafin ya ƙunshi kasuwanni
goma na Freelancing da za’a iya farawa a ko yaushe.
Marubuci: Salisu Abdurrazak Sahil
Shugaban Kungiya Arewa Computer Library

9. TSARABAR RAMADAN MUHIMMAN


APPLICATION DA WEBSITE GUDA 40
Littafi ne da ya ƙunshi wasu muhimman website da application
guda 40 da kuma yadda za’a amfana dasu.
Marubuta: Salisu Abdurrazak Sahil da Isma’il Aliyu Ubale

10. Magani Daga Tsirrai


Littafin ya ƙunshi ɓangaren harkar noma da ganyayyaki da kuma
yadda za’a amfana dasu ta hanyar amfanin yau da kullum.
Abubuwan da Su ke ciki:
 Phytochemicals Basis of Medicinal and Aromatic Plants.
 Alkaloids
 Glycoside
 Polyphenols
 Terpenes
 Essential Oils
 Crude Drugs
 Methods for the Preparation of Herbal Medicine

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 74


Isma’il Aliyu Ubale

o Decoction
o Powdering
o Extraction
 Plants of Medicinal importance
 Lemon Grass
 Mango
 Ginger
 Acacia Nilotica
 Adansonia Digitata
 Manazarta (Reference)
 Sadaukarwa

Marubuci: Salisu A. Farouk

11. RESEARCH GUIDE FOR ENTERING TERTIARY


INSTITUTIONS
Wannan Littafin ya ƙunshi hanyoyin da ake bi wajen neman
Admission zuwa manyan Makarantu
Marubuci: Muhammad Suleiman Kutama
Domin samun ɗaya Daga cikin wadannan littattafai sai a tuntuɓi
wannan lambar 08086251045

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 75


Isma’il Aliyu Ubale

MANAZARTA
Von Briel, F., Davidsson, P., and Recker, J. 2018. “Digital
Technologies as External Enablers of New Venture Creation
in the IT Hardware Sector,” Entrepreneurship Theory and
Practice (42:1), pp. 47–69.

Von Briel, F., Recker, J., and Davidsson, P. 2018. “Not All Digital
Venture Ideas Are Created Equal: Implications for Venture
Creation Processes,” Journal of Strategic Information
Systems (27:4), pp. 278–295.

Browder, R. E., Aldrich, H. E., and Bradley, S. W. 2019. “The


Emergence of the Maker Movement: Implications for
Entrepreneurship Research," Journal of Business Venturing.
(https://doi.org/10.1016/j.jbusvent.2019.01.005).

CB Insights. 2019. “The Global Unicorn Club,” CB Insights.


(https://www.cbinsights.com/researchunicorn-companies,
accessed December 6, 2019).

Ceccagnoli, M., Forman, C., Huang, P., and Wu, D. J. 2012.


“Cocreation of Value in a Platform Ecosystem: The Case of
Enterprise Software,” MIS Quarterly (36:1), pp. 263–290.

Davidsson, P., Recker, J., and von Briel, F. 2018. “External


Enablement of New Venture Creation: A Framework,”
Academy of Management Perspectives.
(https://doi.org/10.5465/amp.2017.0163).

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 76


Isma’il Aliyu Ubale

Dimov, D. 2016. “Toward a Design Science of Entrepreneurship,”


in Advances in Entrepreneurship, Firm Emergence and
Growth (Vol. 18), A. C. Corbett and J. A. Katz (eds.).

Du, W. D., Pan, S. L., Zhou, N., and Ouyang, T. 2018. “From a
Marketplace of Electronics to a Digital Entrepreneurial
Ecosystem (DEE): The Emergence of a Meta-Organization
in Zhongguancun, China,” Information Systems Journal
(28:6), pp. 1158–1175.

Dy, A. M., Marlow, S., and Martin, L. 2017. “A Web of Opportunity


or the Same Old Story? Women Digital Entrepreneurs and
Intersectionality Theory,” Human Relations (70:3), pp. 286–
311.

Fang, Y., Henfridsson, O., and Jarvenpaa, S. L. 2018. “Editorial on


Generating Business and Social Value from Digital
Entrepreneurship and Innovation,” Journal of Strategic
Information Systems (27:4), pp. 275–277.

Faulkner, P., and Runde, J. 2011. “The Social, the Material, and
the Ontology of Non-Material Technological Objects,” in
27th European Group for Organizational Studies
Colloquium, Gothenburg, Sweden.

Faulkner, P., and Runde, J. 2019. “Theorizing the Digital Object,”


MIS Quarterly. (https://doi.org/10.17863/CAM.37903).

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 77


Isma’il Aliyu Ubale

Del Giudice, M., and Straub, D. 2011. “IT and Entrepreneurism:


An on-Again, off-Again Love Affair or a Marriage?,” MIS
Quarterly (35:4), iii–vii.

Goh, K. T., and Pentland, B. 2019. “From Actions to Paths to


Patterning: Toward a Dynamic Theory of Patterning in
Routines,” Academy of Management Journal.
(https://doi.org/10.5465/amj.2018.0042).

Grégoire, D. A., and Shepherd, D. A. 2012. “Technology-Market


Combinations and the Identification of Entrepreneurial
Opportunities: An Investigation of the Opportunity-
Individual Nexus,” Academy of Management Journal (55:4),
pp. 753–785.

Hitt, M. a., Beamish, P. W., Jackson, S. E., and Mathieu, J. E. 2007.


“Building Theoretical and Empirical Bridges across Levels:
Multilevel Research in Management,” Academy of
Management Journal (50:6), pp. 1385–1399.

Huang, J., Henfridsson, O., Liu, M. J., and Newell, S. 2017.


“Growing on Steroids: Rapidly Scaling the User Base of
Digital Ventures through Digital Innovation,” MIS
Quarterly (41:1), pp. 301–314.

Ingram Bogusz, C., Teigland, R., and Vaast, E. 2018. “Designed


Entrepreneurial Legitimacy: The Case of a Swedish
Crowdfunding Platform,” European Journal of Information
Systems (28:3), pp. 318–335.

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 78


Isma’il Aliyu Ubale

Jarvenpaa, S. L., and Standaert, W. 2018. “Digital Probes as


Opening Possibilities of Generativity,” Journal of the
Association for Information Systems (19:10), pp. 982–1000.

Kallinikos, J., Aaltonen, A., and Marton, A. 2013. “The Ambivalent


Ontology of Digital Artifacts,” MIS Quarterly (37:2), pp.
357–370.

Karhu, K., Gustafsson, R., and Lyytinen, K. 2018. “Exploiting and


Defending Open Digital Platforms with Boundary
Resources: Android’s Five Platform Forks,” Information
Systems Research (29:2), pp. 479–497.

Kuhn, K. M., and Galloway, T. L. 2015. “With a Little Help from


My Competitors: Peer Networking among Artisan
Entrepreneurs,” Entrepreneurship Theory and Practice
(39:3), pp. 571–600.

Kyriakou, H., Nickerson, J. W., and Sabnis, G. 2017. “Knowledge


Reuse for Customization: Metamodels in an Open Design
Community for 3D Printing,” MIS Quarterly (41:1), pp.
315–332.

Lyytinen, K., Yoo, Y., and Boland, R. J. 2016. “Digital Product


Innovation within Four Classes of Innovation Networks,”
Information Systems Journal (26:1), pp. 47–75.

Professor Byers, Tom, 2008, Stanford University, "Top ten elements


of technology entrepreneurship"

A Revolutionary Book for Digital Entreprenuership Page 79

You might also like