8 Tunaninka Kamanninka

Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 317

Tunaninka Kamanninka

SADAUKARWA
Na miqa wannan littafi
Gaisuwa ga ‘ya’yana:

Ruqayya da Uthman,
Rabi’ah da Amina,
Kauthar da Muhammad

***************
Ina addu’a cewar su,
tareda dukkanin sauran yara,
Za su karanta wannan littafi
su kuma yi amfani da shi
wajen kyautata tunaninsu,
domin halayensu
su haifar masu da
kyakkyawar halayya
a xaukacin rayuwarsu.

AMEEN

Ina yi wa mahaifana, Alhaji Usman da Hajiya Rakiya add’aur:


Allah Ya jiqansu Ya gafarta masu. Ameen.
Dukkaninmu mun amfanu da dagewarsu
wajen yi mana tarbiya domim xa’armu ta dace
da kyakkyawar koyarwar addininmu, Islam.

Allah Ya yi irin wannan jin qai da gafara


ga dukkanin iyaye waxanda suka dage
wajen tabbatarda ‘ya’yansu kasancewa
mutane masu ilmi da hali nagari daidai iyawarsu.
Ameen.
3i
Tunaninka Kamanninka

TUNANINKA
KAMANNINKA

Alhaji Bashir Othman Tofa

4ii
Tunaninka Kamanninka

Haqqin Mallaka (M) 1997:


Bashir Othman Tofa
Maxaba’a:
Alphabet Publishing Limited
Ruqayya House
1 Maiduguri Road, P.O. Box 760
Kano State — Nigeria

Littafi na Farko: 1993


Littafi na Biyu: 1995 & 1997
Littafi na Qarshe bugun farko: 1999
Sake bugun Littafin: 2005

Registered ISBN: 978-33390-0-1

Kamfanin Alphabet
bai yarda a buga ko a juyi wani fanni
daga wannan littafi ba tareda izni ba.
Za a iya bayar da izni nan da nan idan aka nema,
daga adireshi na sama.
———————————————

Mai shirya littafin da bugun Komfuta:


(planning and typesetting by:)
Alhaji Bashir Othman Tofa
(Duk Hotuna daga MS Publisher suke.
Ina godiya ga kamfanin Microsoft na Amerika)

5iii
Tunaninka Kamanninka

ABINDA KE CIKI

Babi TA’ALIKI: 8

0 GODIYA DA BAYANAI 12

1 GABATARWA 15

2 TUNANI DA HALI 31

3 WAHALA DA WADATA. 63

4 HALI DA HALAYYA. 80

5 TUNANI DA LAFIYA 88

6 TUNANI DA MANUFA 96

7 WAHALA DA MASIFU 109

8 TUNANI DA INGANCI 147

9 TUNANI DA NAZARI 221

X RAYUWA ABAR MISALI 250

Y TUNANI DA HIKIMA 291

6
iv
Tunaninka Kamanninka

A wannan littafi, fatahar da ke nuni ga namiji,


ita ce kuma take wakiltar kisirar da ke nuni ga mace.

Misali:

Tunaninka = Tunaninki
Kamanninka = Kamanninki
Kanka = Kanki

7v
Tunaninka Kamanninka

TA’ALIKI
Da sunan Allah Mai cikakken iko,
Mahaliccin Komai, Mai yin abindaYa so.

“TUNANINKA KAMANNINKA” yunquri ne mai


kyau, wajen kyautata xabi’un al’umma tareda
xorasu bisa tafarkin da zai ba su xaukaka a duniya
da lahira. Marubucin ya nutsu wajen fahimtar halin
xan-Adam da kuma irin cutar da ke damun
zuciyarsa, sannan kuma ya bayar da maganin
cututtukan. Haqiqa, a ganina ya gano maganin.
Duk wanda ya sha maganin da Alhaji Bashir
Othman Tofa ya ba wa zuciya a wannan littafi, to
ya waraka. Sha yanzu magani yanzu!

Marubucin, wanda gogagge ne a fannin rayuwa, ya


fito da salon rubutun da babu shi a harshen Hausa.
Rubutu a janibin falsafa tsohon al’amari ne a
tarihin duniya. Amma a harshenmu, yanzu muka
ce: “Assalamu Alaikum“.

Allah (swt) Ya qara tabbatar da abinda nake ta


tsokaci da shi kullum, cewa: baiwa ta Allah (swt)
ce. Yana bayar da ita inda Yake so. Don haka ko
yaushe sai mu duba mu gani da idon basira cewa ta
8
Ta’aliki
wacce hanya za mu iya amfani da baiwar da Allah
(swt) Ya ba wa kowannenmu domin qara
kusantarSa (Allah swt), da ci gabanmu baki xaya,
ba tareda mun raina mafitar basirar ba.

Wannan littafi mai albarka, bai sauka daga qa’idar


shari’a ko ta xabi’ar rayuwa ba. Zai yi fa’ida ga duk
jinsi na al’umma, musammam manyan gobe.

Ina mai jan hankalin jama’a da su karanci wannan


littafi tareda aiki da shi domin samun al’umma
tagari.

Allah (swt) Ya albarkaci marubucin da masu karatu


baki xaya.

Wama taufiq illa billah!

Alhaji (Dr.) Yusuff Maitama Sule


Xan Masanin Kano

20th June, 1997

Mai girma, Dan-Masanin Kano, ya yi wannan Ta’aliqi ne tun a littafin farko.


Ina matuqar godiya da addu’ar dukkannin alhairi a gare shi. Amin.

9
Tunaninka Kamanninka
MUHIMMAN TUBALAN
GINA RAYUWA

Wani Malami ne ya ke yiwa xalibansa misali. Sai ya xauko


tukunyar gilashi ya ajiye a kan tebur, sannan ya xauko duwatsu
kamar curin fura ya ringa sa su cikin tukunyar har sai da ta cika da
su yadda ba wani dutse irinsu da zai shiga. Da ya gama, sai ya tam-
bayi xaliban, “Tukunyar ta cika?” Suka ce, “I, ta cika.” Malami ya
ce, “Kun yi kuskure. Ba ta cika ba. Bari kuma ku gani.”
Ya sunkuya ya xauko kwandon tsakuwa ya ringa zuba su a
cikin tukunyar, har sai da ya cike guraben da ke tsakanin duwatsun.
Sannan ya kalle su ya sake tambayarsu, “Yanzu fa?” Sai xalibai
suka yi shiru. Can, sai wani ya ce, “Wataqila.” Malami ya yi mur-
mushi ya kaxa kansa.
Ya sake sunkuyawa, ya xauko kwanon rairayi, ya yi ta zuba
shi cikin tukunya, har sai da ya cike duk xan gurbin da ya saura tsa-
kanin tsakuwoyin. Sannan ya tambayesu. Suka ce, Basu sani ba.
Sai kuma ya xauko kwanon ruwa, ya yi ta zuba shi cikin tu-
kunya, har sai da ta cika maqil, bayan rairayi ya tsotsi abinda zai
iya. Sannan da kansa ya ce wa xaliban, “To yanzu watakila ta cika.
Kun fahimci darasin wannan misali?”
Wani haziqin xalibi ya ce, “Duk qaracin lokacinka, in ka yi
qoqari zaka yi yin wasu abubuwan dabam.”
Malam ya ce, “A a. Darasin shi ne, idan ba ka fara shigar da
muhimman tubalan rayuwarka da farko ba, to ba zaka iya shigar da
su gaba xaya nan gaba ba. Lallai ka yi tunaninsu, ka sansu, sannan
ka jera su daidai muhimmancinsu; manyan da farko sannan
qananan, ka kuma tunkaresu cikin hanzari da lura. Komai daidai
muhimancinsa. Da da rairayin na fara da tsakuwar ba ta shiga ba, da
kuma ko dutse xaya ba zan iya sa wa ba. Amma yanzu ga shi komai
ya shiga ya sami mazauninsa.

Waxannene naka muhimman tubalan rayuwar?


Ka sansu ka kuma tsara su daidai da muhimancinsu?
Ya za ka tsara waxannan? Addininka, Ilminka, Iyalinka, Sana’arka,
Mutumcinka, Tausayawarka da Jin-daxinka da …….?

10
Tunaninka Kamanninka

“Bismillahir Rahmanir Raheem”


*********************************************

“Duk abu Mai-kyau da ya riskeka


(Ya kai mutum)
Daga Allah yake;
Amma duk abu Mara-kyau
da ya riskeka
Daga gareka (zuciyarka) yake.
Kuma Mun aikoka Manzo
(Ya Muhammad!)
Domin ka faxakarda Dan-Adam;
Kuma Allah isasshe ne a shaidawa”
Sadaqal-Lahul Azeem
*******************************
Surat: Al-Nisa’ (4)
Aya ta 79

11
Tunaninka Kamanninka

Godiya
da Bayanai
‘Don a fahimta

Dukkannin godiya da yabo sun tabbata a gareShi,


Allah (swt), wanda a cikin yardarSa da alfarmarSa
na rubuta wannan littafi mai muhimmancin gaske.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga ManzonSa,
shugabanmu, Muhammad (saw), wanda koyi da
shi ya cancanci rayuwa mai fa’ida a duniya da
kuma lahira. Allah Ya sa mu gane, ameen.

Ina matuqar farin-cikin kammala wannan littafi,


wanda mutane da yawa suka karanci na farkonsa,
suka kuma yi ta qara min qarfin gwuiwar ci-gaba
da rubuta shi har zuwa wannan bugun. Ina godiya
ga dukkanin jama’a da abokai da kuma iyalina.

Da, na yi tunanin na kawo hujjoji daga cikin Al-


Qur’ani Mai Tsarki da kuma wasu littattafai da na
12
Godiya da Bayani
karanta, a kan wasu bayanai da na yi, domin na
nuna yawancinsu ba ra’ayoyina ne kaxai ba. A a.
Kusan komai na rubuta yana da hujja mai qarfi
daga cikin littattafai masu ma’ana. Amma da na
fara wannan hidima, sai na tarar a kowanne shafi
akwai hujjoji masu yawa da za a iya kawowa daga
Al-Qur’ani da littattafan Ilmi. Idan na ce sai na
rubuta waxannan, to yawansu ba shakka zai qara
qibar littafin yadda zai shige ma’ana. A hakan ma,
tuni ya shige abinda na qiyasta masa tun farko.

Saboda haka, abinda nake so in ja hankali a kai shi


ne, idan da hali a gaba, insha’Allahu, zan kawo
waxannan hujjoji a wani littafin dabam, wanda za a
iya riqeshi shi kaxai sai lokacin da ake son yin
amfani da shi wajen gano hujjar wata magana.

Haka kuma, akwai littattafai masu yawan gaske


waxanda qwararru suka rubuta su cikin hikamar
falsafar rayuwa. Abinda yake da wahala gameda
ruwaito waxannan a matsayin hujja shi ne, da kyar
za ka sami wata magana guda wadda za ka
dangantata da mutum xaya, ko kuma littafi xaya
tak. Don hakane ma na rubuta Baba na 11 (‘Y’),
wanda ya tsamo maganganun hikima har 104 da
waxanda suka yi su, don su zama jagorar tunani.
Wasu a cikinsu, ni na rubuta su.

13
Tunaninka Kamanninka

14
Gabatarwa

“Gabatarwa”

G
“Komai ka shuka......”

odiya ta tabbata ga Allah (swt),


Mahaliccin Sammai da Qassai da duk abubuwan
dake tsakaninsu. Shi ne Maxaukaki Mai Iko da
komai a kan komai. Shi ne Allah (swt) Wanda Ya
halicci Xan-Adam Ya kuma ba shi ikon zavi a kan
dukkanin Tunaninsa da Ayyukansa. Idan ka qulla
Alhairi ka ga Alhairi. Idan ka qulla Sharri ka ga
Sharri. Wannan ita ce shiriya da gargaxi ga masu
tunani da son gyarawa.

Wannan littafi ya biyo bayan littafi na farko ne, da


na biyu, saboda na fahimci yadda jama’a da yawa
suka karvesu. “Tunaninka Kamaninka”, a yadda na
kammala shi yanzu da kuma yadda zan yi ta gyara

15
Tunaninka Kamanninka
shi a kan cancanta nan gaba, ba shakka littafi ne
wanda yake qunshe da sigogin Rayuwa fanni-
fanni. Littafin farko taqaitacce ne qwarai da gaske
wajen duba wannan al’amari, kodayake ya nutsa
sosai wajen kafa harshashin littattafai na gaba, a
bayanan dangantakar Tunani da Hali da kuma
Halayyar Xan-Adam.

Wannan littafi na uku kuma na qarshe, ba shakka,


yana bukatar a karance shi a hankali tareda
zurfaffan nazari. Komai aka yi matuqar Tunani
kuma cikin haquri a kansa, ba shakka za a sami
biyan bukata a sannu. Daga Babi na 2 zuwa na 6,
babu wasu muhimman bambancin ma’ana masu
yawa da yadda suke a Littafi na farko, illa qarin
bayanai don inganta ma’anar. Amma Babi na 7 da
na 8 sun kawo sababbin (ko kuma na ce, sun sake
gabatarda) hanyoyin duba halayyar rayuwar
mutum a zahiri. Babuna na 9 da na 10 (x) kuwa,
manyan darusa ne idan aka yi qwararren tunani a
kansu. Shi kuma Babi na 11 (y), hikimomin
magana ne masu zurfi don sosa qwaqwalwa. A
wannan littafi akwai bayanai da yawa waxanda za
a iya jinginasu hujjarsu da Alqur’ani Mai girma da
ingantattun Hadisai, amma ban alamtasu ba. Toh, a
nan ma, ba za su alamtu cikin hanzari ba, kamar
yadda na yi bayani a can shafin baya. Amma na

16
Gabatarwa
san da sun karanci irin waxannan bayanai, masu
ilmi take za su dangantasu da hujjijinsu na qwarai.

Toh, bari dai na koma baya na tunaso mana da


Gabatarwar Littafi na Farko. A can ne na rubuta
cewar, rayuwa takan kasance kusan a kowanne
lokaci tamkar yadda tunanin mutum yake. “Kamar
Kumbo kamar kayanta”. Tuni mun gamsu da sanin
cewar Allah (swt) Shi ya ke tsara komai, Ya kuma
tafiyarda komai. Amma kuma mun san cewar Ya ba
wa Xan-Adam ’yanci da damar kimtsa rayuwarsa,
ko kuma watsata da kansa. Ko a addinance mun san
babbar matattakalar shiriya ita ce: “alhairi ne yake
haifar da alhairi”; haka kuma, “sharri ne yake haifar
da sharri”. Sannan kuma, akan ce, ‘Allah Ya ce,
“Tashi Na Taimakeka”, domin a nuna da ma can an
san Xan-Adam shi ne riqe da linzamin makomarsa,
sai dai wanda hanlakinsa ya gushe. Watau, kai ne
mai fafutuka; kuma kai ne jagorar kanka. Sai ka
yunqura a wajen waxannan tukuna, sannan za ka
sami taimako, ko da kuwa a gun Allah (swt) ne.

Idan xalibi bai yi karatu ba, ba zai ci jarrabawa ba;


idan mara lafiya bai sha magani ba, ba zai warke
yadda yake so ba; idan ba a shuka ba, ba za a girba
ba; idan ba ka tafi ba, ba za ka je ba; idan ka sa
hannunka a wuta, ka qone; idan ka dartsawa kanka

17
Tunaninka Kamanninka
wuqa, ka yanke. Idan ka yi tunanin banza, ka
aikata banza, ka kuma sami sakamakon banza.

Saboda haka, Xan-Adam yana da zavi; kuma iko a


kan zavin, baiwa ce daga Allah (swt), domin
waxannan su ne bambancinsa da dabba. Ita dai
dabba ba ta da zavi yadda muka san shi, illa ta “ji”
a jikinta, kuma ta aikata abinda jikin nata ya
umarta, ko ya bukata. Idan tana jin qishirwa, kuma
ta ga ruwa, sai ta sha. Idan ba ta gan shi ba ta nuna
alamu waxanda jikin yake roqon qwaqwalwarta
don ta nuna. Idan ta ji zafi, ko ta ji tsoro, ta arce.
Iyakacin irin nata hankalin da zavin kenan.

Son zuciya, qera qarya, ha’inci, gulma, zamba,


baqin-ciki, hassada da munafurci, duk mun san
suna daga vangaren Baqar Aniya ta xan-Adam.
Amma kuma xan-Adam, zai iya zavar ya zama
mai gaskiya, riqon amana, tausayawa, taimakawa,
mutumci, kawaici, xa’a, son-jamaa, qoqari da
tsoron Allah. Duk waxannan da sauransu suna
daga vangaren Farar Aniya ta xan-Adam. Da
baqaqen aniyar da fararen aniyar duka abubuwan
zavi ne ga xan-Adam. Ba ruwan Allah a cikinsu,
in dai hankalinka cur yana jikinka. In Hairi, hairi
za ka gani; In Sharri, sharri za ka gani. Watau, duk
abinda ka shuka shi za ka girba. Ya rage naka.

18
Gabatarwa
Amma akwai halaye da mutum yake shiga cikin
wata matsala, ko al’umma ta shiga cikin wata
masifa; dukkaninsu suna zargin wani ne ya jawo
masu waxannan ba su ba. Akwai kuma wasu
halayen da mutane suke ciki na matsuwa, amma
sun saduda, ko ‘wai’ sun karvi qaddara cewar haka
suke ba yadda za su yi. Waxannan halaye suna
bukatar nazari cikakke, amma daidai hankali a
wannan littafi.

Da farko lallai ne na ja hankulanmu cewar ba


manufar wannan littafi ce ta qyami marasa galihu
waxanda suke cikin matuqar tsanancin rayuwa
saboda yadda al’amura suka xauro ba. Babbar
manufar ita ce ta taimaka mana duka wajen
farkawa, domin mu sake bincika kanmu ta yadda
za mu iya nema, kuma mu sami “wadatar zuci” da
“gamsuwar” da suka dace da mu.

La’akari cewar wasu wahalun, qalubalanta ne na


rayuwa, yakan tsikari mutum ya tashi tsaye wajen
gyara matsayinsa ta hanyar tunkarar wahalunsa.
Watau, ita kanta rayuwa ba za ta yi ma’ana ba, in
komai da kowa daidai suke tafiya. Idan da haka
rayuwa take da tuni an gaji da ita, domin ba ta ba
da damar a sarrafa tunani don tunkararta gaba da
gaba ba. Da tuni ta watse ita kanta.

19
Tunaninka Kamanninka
Haqiqa, Allah (swt) Bai halicci kowa da kowa
daidai ba sabo hikimarSa. Idan muka yi tunani za
mu ga ma’anar wannan hikima taSa; kuma akwai
gurare a wannan littafi da suka tavo wannan fanni.
A qasashe dabam dabam, Ya ajiye al’umma
dabam dabam cikin halaye iri iri na jin daxi da na
wahala. Amma idan muka lura, akan sami masu
arziki sosai a guraren da talauci ya yi kanta; a
kuma sami matalauta a guraren da kuxi da arziki
suka yi yalwa.

Wannan hikima ce wadda yakamata ta nunawa xan


-Adam cewar yana da damar da zai wataya a
tsakanin waxannan halaye biyu. Idan tunaninsa da
burinsa kimtsattsu ne a kan abinda yake nema, to
akwai damar samun biyan bukata. Idan kishiyar
haka ne mashimfixar tunaninsa, to sam sam, ba
inda za shi. Masu la’akari tuni sun san haka.

Allah (swt) Bai ware wata al’umma, ko qabila, ko


wasu mutane dabam a wata zuri’a ko a wani gida,
Ya ce su kaxai za su arzurta ko su talauta ba.
Amma Ya nuna matattakalun hawa ga arziki, da
wadatar zuci; Ya kuma nuna na gangarowa daga
garesu. Mun ga xan sarki talaka; xan mai kuxi
matsiyaci. Mun ga xan malami ya zama jahili;
amma kuma xan jahili ya zama malami; kamar

20
Gabatarwa
yadda xan talaka ya zama shugaban Qasa. Muna da
labaran inda rimi ya juye da mujiya: mai gaisarwa
ya zama mai karvarta; mai doki ya koma kuturi;
sarki ya zama talaka; direba ya zama uban-gidan
mai gidansa. Mun ga mutanen da suka fito daga
qungurman qauyuka, suka zama manyan masu
kuxi ko shugabanni a manyan birane; mun ga
kuma kishiyar haka. Ga xan makaho da idannunsa;
xan kuturu da yatsunsa. Amma kuma ga xan sarki
yana roqo, ko xan alkali ya yo sata. Ga dai misalai
nan birjik. Ba shakka wasunmu sun san Allah (swt)
Ya ce, ‘Shi ne yake fidda mai rai daga matattace;
mattace kuma daga mai rai; sannan ya arzurta
wanda Yake so ba tareda awo ba’.

Darussa irin waxannan sune manufar wannan


littafi. Watau, kada don kai talaka ne, ko wani mara
galihun rayuwa, ka yarda ka watsarda rayuwarka
cikin nadama. Daga matacciyar halayya, Allah Zai
iya rayar maka da ingantattar halayya, muddin dai
ka yi abubuwan da ake bukata don cimma wannan
sabuwar rayuwar. A Gyara tunani don inganta
matsayi; a nemi sana’a don inganta rayuwa; a xau
xabi’u masu kyau don neman nasara. Waxannan
sune yakamata su zama xabi’arka domin ka zamto
mutum mai manufa, mai kuma fafutuka a kan
manufar taka, ko menene matsayinka. Kai ne kafi

21
Tunaninka Kamanninka
kowa sanin kanka da abinda zai gamsarda kai. Wa
ya san inda rabo yake? Haka, kada don kana zaton
kana da komai, shikenan sai ka watsar da tunani
mai kyau, ka qi adana zuciyarka, ka qi shirya
rayuwarka. Wa ya san inda hasara take?

Idan muka yi tunani, yawancinmu mun san: da


rabo (ko nasara) da rashi (ko hasara), ba shakka,
suna ga masu nemansu ta hanyar tunaninsu, wanda
zai gina halinsu ya haifarda halayyarsu. Ba abinda
ya fi damun mutanenmu irin kasalar zuci, rashin
tavusawa, wasu lokatai don son banza, wasu kuma
don rashin sanin ya za a yi. Wani, haka kawai, sai
ya watsar da darajar da Allah (swt) Ya yi masa,
qememe ya qi gudanarda rayuwarsa kamar
mutum. Haka kawai, sai mutum ya sadudarda
kansa, qememe ya qi neman sana’ar yi don ya
inganta mutumcinsa.

Dá samari abokai masu qarfin jikinsu za su haxa


kansu su yi tunanin sana’ar da za su fara, ko da ta
dako ce (maimakon su zama ‘yan banga, ko ‘yan
daba, ko ‘yan qwaya), dá wataran sai sun sayi ‘a-
kori kura’, Dá wataran sai mu gansu da manyan
motocin sufuri. Amma, Ina!, Yawancinmu ba mu
da wannan zuciyar. Dá masu sana’a iri guda, za su
daure su haxa kawunansu da jarinsu don inganta

22
Gabatarwa
wannan sana’ar, dá lallai wataran sun gina manyan
masana’antu. Amma Ina! Hassada da zamba ba za
su qyale yawancinmu yin haka ba. Dá samarinmu
da yayyensu za su koyi sana’un yau da kullum, dá
sun yi mamakin yadda za su gamsu da kansu. Dá
za mu maida hankulanmu wajen gaskiya a
harkokinmu, da kishin kanmu, dá ba haka ba.

Qasashen da suka ci gaba; da al’ummun da suka ci


gaba, ba haka siddan suka ci gaban ba. Tunanin
manufa da fafutuka a kanta, cikin la’akari da
muhimmancin xa’a da aikata gaskiya da kare
mutumcin mutum; tausayin na baya da taimakonsa;
ba gaba ko gasa da shi ba; girmama na gaba da
koyi da shi in ya cancanta; yabon mai gaskiya da
halaye nagari, ba girmama varayinsu ba; su ne suka
haifar masu da ci gabansu. Ci gaba kuwa, magana
ce ta tunani ba ta tsabar kuxi da manyan gine-gine
ko motoci ba. Magana ce ta shugabanci nagari, ba
satar kuxin jama’a ba. Magana ce ta qyamar
marasa kunya, ba yabonsu ba. Mu ma akwai
waxanda suka zama masu kuxi sosai a al’umarmu;
akwai masu ilmi iri-iri a cikinmu. Amma, ‘ci-gaba’
wani abune dabam wanda yake shafar al’umma
gaba xayanta, ba ‘yan tsiraru ba. A haqiqa, na san
ba inda za mu a matsayin al’umma mai ci-gaba, sai
mun gyara halayenmu. Sai mun tashi mun yi da

23
Tunaninka Kamanninka
gaske. Sai jama’a sun san mutumcin kansu, sun
san haqqunansu, kuma sun shiryu su bi waxannan
haqquna, su kuma ba wa al’umma nata haqqin. A
taqaice, sai sun dawo da Allah (swt) a tunaninsu
da ayyukansu.

Ta hanyar gyara tunani da gaskiya ce kaxai za mu iya


sa kanmu a al-qiblar ci-gaba. Ta hanyar qwaqqwarar
manufa ce kaxai za mu iya kama hanya. Ta hanyar
fafutuka ce kaxai za mu iya danganawa.

Wannan littafi ya kutsa cikin dangantakar


“Tunani” da wasu al’amura na rayuwa, da bayanai
waxanda za su iya taimakawa masu buxaxxar
zuciya. Amma akwai bayanai waxanda wasu
mutane za su iya damuwa a kansu, wataqila
saboda yadda na faxesu. Ina tabbatarwa masu
karatu cewar ban rubuta wata kalma da mummunar
niyya ba. Mummunar niyya ko kaxan ba za ta dace
da manufar wannan littafi ba. Ba shakka, akwai
hanyoyi da yawa na bayanin abu guda, amma
kowa da irin basirarsa da azancinsa. Ni ajizi ne, sai
a gafarceni a gurare irin waxannan.

Masu karatun wannan littafi, musammam ma in


sun iso Babi na 7, suna bukatar su yi cikakken
tunani. A cikin waxannan fannoni na yi magana a
kan sharrin da mutum yake jawowa kansa wajen
24
Gabatarwa
xorawa Allah (swt) laifin masifu ko wahalun da
suke samun Xan-Adam a wannan rayuwa. Wasu da
farko za su ga tamkar na kama tafarkin wata
gurvatacciyar magana ce. Wasu kuma su ce ai na
saki hanya ma gaba xayanta, saboda yadda na
hango abubuwa da yadda na fassarawa kaina su. Ba
shakka, ra’ayoyina a kan wannan matsala za su iya
xaure kai, in ba a yi zurfaffan tunani da haquri ba.
Fitarda ma’ana gameda yadda Allah (swt) Yake
sha’aninSa ba qaramin aikin kasada bane ga
mutum. Amma kada wannan gaba-gaxi nawa ya
rufe idanuwanmu da zuciyoyinmu daga ainihin
gaskiyar abubuwan da za su iya gyara tunaninmu
su inganta rayuwarmu. A yawancin lokatai,
Hausawa sukan yi mana matashiya cewar:
‘Gaskiya xaci gareta’, kuma ba shakka hakane.
Muhimmin abune mu kasance masu kyakkyawan
tunani gameda Allah (swt) a kowanne hali da muka
sami kanmu a ciki.

Idan mutum ya bar zuciyarsa a buxe, ya kuma


zama mai shirin yin tunani fisabilillahi a kan
abinda ya ‘ji’ ko ya ‘gani’, to ba shakka wannan
mutum shi ne maciyin ribar al’amura. Amma
mutumin da nan-da-nan ya xau matsayi ba tareda
zurfin tunani da auna matsaloli ba, shi ne mai
hasarar al’amura. Don haka nakan ce: “saurin zargi

25
Tunaninka Kamanninka
yanayi ne na baqin tunani”. Ba manufata ba ce na
kange kaina daga waxanda za su iya yin kuskure a
wannan sashin ilmi. Idan akwai kura-kurai
waxanda aka lura da su, ni zan fi kowa farin ciki
idan aka sanarda ni domin na gyarasu. Fatana,
xinbun mutane waxanda ilminsu da azancinsu ya
niqe nawa ya shanye, za su karanta wannan littafi.
Ina neman alfalmar irin waxannan shugabanni da
su yi haquri da ni, su kuma shiriyarda ni nan da
nan. Wannan ita ce tasu gudun mowar, wadda za ta
amfane ni da kuma jama’a masu yawan gaske.

Roqona shi ne, kada a yi saurin hukumta ni ba


tareda duba al’amarin gaba xayansa ba. In haka ta
faru, ni ban ci riba ba, sauran jama’a kuma ba su ci
ba. Kamar dai kai ne za a gurfanar a gaban alqali,
amma sai ka ji alqalin mutum ne mai gaggawar
yanke hukumci a kan abinda ya ji daga gefe xaya
na qarar. Ba shakka, hankalinka ba zai kwanta da
shi ba, domin ka san zai iya yanke hukumci cikin
zalunci. Ko da a alaqar mutum da mutum, ko
mutum da hukuma, saurin yanke hukumci a kan
jita-jita, ko zato, ba tareda cikakken bincike ba,
yakan watsa dangantaka, ko ma ya haifarda
zalunci. Haka za mu gani idan muka nazarci
halayen wasu, ko da a matsala ce ta rayuwarsu.
Kuma dai an ce, “Mahaqurci Mawadaci”.

26
Gabatarwa
A Babi na 8, na yi qoqarin bayar da shawarwari a
kan hikimar kimtsa rayuwa domin a sami nasara
wajen ingantata. Yawancin abubuwan da na yi ta
rubutawa sun cancanci a yi qoqari matuqa a
mayarda su xabi’u na yau da kullum, kuma saboda
Allah. Ba shakka, na san ba daxin furtawa kaxai
garesu ba, hakama gaskiyarsu take kasancewa a
rayuwar wanda suka zama jagorarsa.

Waxansu abubuwa suna da wuyar misaltuwa,


musammam ma ga mutanen da suke ganin sun
gwada sun gwada amma har yanzu ba su ga nasara
a rayuwarsu yadda suke so ba. Nasara, ba shakka,
tana da ma’aunai iri iri ga mutane dabam dabam.
Akwai masu son kimtsa rayuwarsu da yin gaskiya,
aunata da nunata da sanin yakamata, ba don su sami
kuxi ko muqami ba. A’a, sai dai don sun yarda yin
hakan shi ne daidai a gunsu da kuma Mahaliccinsu.
Daga irin wannan kimtsi na rayuwa, irin waxannan
mutunen kirki suke samun yalwar gamsuwarsu.
Amma, akwai kuma masu son watsa rayuwarsu
daga kishiyoyin haka, saboda baqin tunaninsu, da
kuma zaton cewar babu wani abu a rayuwa wanda
yake da muhimmanci; ko kuma dai haka suke son
yi saboda rashin nasarorinsu a wasu lokatai na
rayuwarsu. Ba mai hasara irin wanda ya xau kuxi
su ne kaxai ma’aunin nasara.

27
Tunaninka Kamanninka
Duniyar kowa dabam take. Wasu su fassarata
daidai, wasu kuma su kuskure a fassararsu, su rayu
su mutu cikin hasara. Amma lallai wanda bai
xauketa da muhimmanci ba, ya tuna cewar, ko ya
mutu, sunansa yana nan; watakila kuma ‘ya’yansa
da jikokinsa suna nan. Ko ba ka bar qwandala ba
saboda talauci, to ka yi qoqarin barin milyoyi na
mutunci da kyakkyawan suna. Yin haka ma, ya fi
barin milyoyin kuxin da basu amfaneka ba, balle
su amfani wani. Ko kuma kuxin da za su jawowa
na baya rigima da tozartawa, kamar yadda aka fi
samu a wannan zamani namu. Ko kuma kuxin da
suka jawo vatawa tsakanin mai su da Allah (swt);
kuma daga qarshe su zama sanadin qarkewarsa a
Jahannama. Wannan ya yi hasara duniya da lahira.
Amma mutum ya rayu cikin gamsuwa, ya fi komai
daxi. Sai dai, da gamsuwar da rashinta yawanci
tasawira ce ta tunanin da mutum ya saqawa
zuciyarsa. Da arziki da kuxi; da gamsuwa da jin
daxi, duk ma’aunansu dabam suke ga kowa.

Wasu suna sha’awar matsayin wasu, amma ba su


san jidalin wannan matsayin ba. Wasu na qyamar
halayyar wasu, amma ba su san jin daxin wannan
halayyar ba. Yawanci, abinda kake gani, ko zato,
ba haka suke a ainihinsu ba. Amma kuma wannan
magana ce muhimmiya a Babi na 9.

28
Gabatarwa
Komai na duniya mai sauqi ne, sai in ka maida shi
mai wahala. Amma duk yadda ka xauketa haka za
ka tararda ita. Wasu al’amuran rayuwa a fayyace
suke, ba a voye ba. Wasu kuma a voye suke ba a
fayyace ba. Mu ne dai a irin tunaninmu, muke ta
shagalarda zuciyarmu ta shiga yin fankama a
badalar waxannan, ko ma a cikin duhu. Amma
kuma an ce: “Wanda bai ji bari ba, ya ji woho”. Ko
kuma, “Kukan Kurciya ma jawabi ne, sai mai
hankali ke ganewa”.

Xaukacin wannan littafi a kan “Ilmin Tunani” ko


kuma a janibin “Falsafar Tunani” na rubuta shi.
Watau, falsafa ne a kan yadda tsarin rayuwa ya
jingina da tunanin mutum, ko al’umma, da
ayyukansu da sakamakonsu. Akwai Kurciyoyi da
yawa a cikinsa suna ta kuka. Allah (swt) Ya sa mu
gane, mu kuma yi aiki da abubuwan da muka
fahimta. Idan mutum xaya ya amfanu daga wannan
littafi, ni na ci riba mai yawan gaske. Idan mutane
goma suka qaru da shi, to ba shakka, aikina ya
cimma babbar nasara.

Alhamdu Lillahi Rabbil Alameen. Ina matuqar


godiya da addu’a ga duk waxanda suka sami damar
karanta wannan littafi. Ballantana kuma a ce sun
fara aiki da wasu darusansa. Ace…!

29
Tunaninka Kamanninka

30
Tunani da Hali

“Tunani
da Hali”
Gaskiyar maganar ita ce:
“Mu ne jagorar Rayuwarmu”

T unanin da mutum ya zava, ya kuma aikata


shi da sanin cewar, ‘zuciya ita ce masaqar labulen
hali na baxini, kuma mahaifar rayuwa ta zahiri’, shi
ne kaxai zai shiriyarda mutum izuwa matsayi
ma’inganci, ko kuma ya jefa shi izuwa matsayi
maraunanci. Wanda ya san matsayin tunani haka,
ya kuma yi aiki da hakan, to zai iya canja
matsayinsa ba tareda wahala ba. Saqar da ya yi a
zuciyarsa cikin jahilci a da, yanzu zai iya nutsuwa

31
Tunaninka Kamanninka
ya warwareta ko ya qarfafata daidai da sakamakon
da ta haifar a halayyarsa. Sanin cewar tunaninka
shi ne yake gina halayenka, ba qaramin ilmi bane.
Amma kuma babban ilmi sai mai babban tunani.

Abubuwan da suke tsakanin Ilmi da Jahilci suna da


yawan gaske, amma dukkanninsu sun yi tarayya ne
a cikin xawainiyar bincike da tunani a kansa
fisabilillahi. Ta waxannan sabon ilmi da tunani ne
kaxai, mutum zai iya canja matsayinsa daga
quntata izuwa matsayi na yalwata. Qin yin haka
kuma ya haddasa lalacewa daga yalwata izuwa
quntata; ko kuma daskarewa a quntatar.

Hausawa sukan ce,’ Hali zanen Dutse’, to amma fa


ga rago, wanda bai ilmanta da cewar shi da kansa
zai iya canjawa ba. Halin mutum yakan zama
zanen dutse, qi kankaruwa, muddin bai shirya ya
kankare shi ba. Babu wani abu a tunanin mutum
wanda mutum da kansa ba zai iya canjawa ba. Idan
kai mutumin banza ne, za ka iya sake tunani ka
gyara halayenka na banza. Idan kai mutumin kirki
ne, za ka iya sake tunani ka vata ko ka inganta
halayenka na kirki. Idan kai malalaci ne, za ka iya
canjawa ka zama mai qwazo. “Hali zanen dutse”,
yabo ne, ko kuma la’anta ce, ga masu hali in sun
aikata abubuwanda aka sansu da su.

32
Tunani da Hali
Idan Jarumi ya yi jarumta; idan Mai kyauta ya yi
kyauta; idan Xan-giya ya yi maye; idan Maroqi ya
yi roqo; idan Macuci ya yi cuta; idan Marowaci ya
yi rowa, ko kuma Sarki ya yi alfarma, to duk
waxannan halaye haka ake zatonsu daga masu su,
saboda sanin tarihin halayensu.

Amma, ba abinda zai hana mutum shan giya; ko


maroqi roqo, ko mara-kunya batsa, irin canjawar
tunaninsu daga qoqarinsu na fahimtar cewar su ne
suke riqe da ragamar rayuwarsu; kuma za su iya
yiwa kansu sabuwar jagora a tafarki wanda zai iya
canja Halinsu da Halayyarsu. Abubuwanda suka
taru suka shawarta masu, ko kuma suka tilasta
masu yin sabon tunani, wata magana ce dabam. Za
mu iya yin misali da la’antar jama’a, shugabanci na
-gari, dokokin Qasa, faxan iyaye, shawarar abokan
kirki, ko tsangwamarsu, ko ma masifar duniya ita
kanta, duk a matsayin dalilai masu qarfi.

Mun san cewar ba daidai bane mu fassara mutum


ta hanyar silin tunani guda xaya tak, ko kuma daga
wani abu mai kyau ko mai muni guda xaya da
muka ga, ko muka ji, ya yi ba. Misali: Don mun ji
wane ya yi ashar, bai kamata mu yanke hukumci
cewar shi asharari ne nan-da-nan ba. Don kawai
mun ji wasu na rigima, bai kamata mu ce su kashe

33
Tunaninka Kamanninka
kansu, don su ‘yan rigima ne ba. Haka, don kawai
mun ga mutum ya miqa sadaqa, bai kamata mu
yanke cewar ga mai tausayi ko tsoron Allah can
ba. Ainihin kamannin mutum alama ce ta kulliyar
tunaninsa, kamar yadda tsiro yake kulliyar irin da
aka shuka. Don hakane ayyukan mutum na zahiri
suka zama irin halayen da ya shuka cikin
tunaninsa. Munafuki kuwa, ranarsa takan vaci.

Ba shakka, a wannan lokacin da muka ji wane ya


zabga ashar, ya kasance mai furta ashsha. Haka a
wannan lokacin da muka ga wane ya miqa sadaqa,
ya kasance mutumin kirki. Amma ga manazarcin
xabi’u don auna halayen jama’a, dalilan ashar xin
da kuma na ita sadakar, abubuwa ne da suke
bukatar cikakken bincike, musammam ma idan
mutanen da suka aikata waxannan abubuwa ba a
sansu da waxannan halayen ba. Amma idan da ma
mun san su da waxannan aqidoji, to sai mu ce,
‘Hali zanen dutse’; mu la’anci mai ashar, mu yabi
mai sadakar.

Xa’a, nagarta, kishin addini da na jama’a, ba


abubuwa ne da suke samuwa haka kawai ba.
Waxannan kyawawan halaye girbi ne na daxaxxar
fafutukar tunani a kan hanya mai tsari da gaskiya.
Haka rashin mutumci da rashin kunya da sharri da

34
Tunani da Hali
hassada, tsiranni ne na munanan tunani cikin
rayuwa mara fa’ida, mara tushe.

Rayuwar mafi yawancinmu, ba shakka, ta kan ginu


ne a kan harshashin da iyayenmu, yayyenmu,
abokanmu ko al’ummarmu da shugabanninmu suka
gina mana. Amma a qarshe, mutum shi da kansa
yake gina kansa, ko kuma ya rusa kansa da kansa,
muddin mai hankali ne shi. A cikin kwanyar tunani
yake shirya kayan yaqin da zai cuci kansa ya
turnuqawa rayuwarsa masifa; ko kuma ya amfani
kansa ta wajen samarwa kansa Aljarnar jin daxi,
farin-ciki da kwanciyar rai, ta hanyar canja, ko
mulmula tunaninsa a kan tafarkin alhairi. Idan ya
zavi nagari, ya kuma aikata shi daidai da kuma
hikima, sai ya cimma Farin Buri. Idan ya yi zavi na
banza ya kuma aikata shi to, sai ya cimma Baqin
Buri, har sai ya zama tamkar dabba.

A tsakanin waxannan zavi biyu ne mutum yake


samun kansa; ya ceci kansa, ko ya cuci kansa,
domin shi ne kuma mai iko da zavin. A taqaice dai,
mutum yana da ximbun iko a kan mulmula hali da
makomar rayuwarsa, watau halayyarsa. Xauki
abinda Allah (swt) da ManzonSa suka ce gameda
Zuciya. Idan ta gyaru komai ya gyaru; idan ta vaci
komai ya vaci. Mutum, shi yake da iko a kan qulle-

35
Tunaninka Kamanninka
qullen zuciyarsa da abinda za ta raya masa, ko ta
nemi sa shi ya aikata. Idan ya ga dama ya bi son
zuciyarsa; in ya ga dama ya bi son hankalinsa,
watau, kyakkyawan tunaninsa. Haka waxannan
zavi suke a kowanne juyi na rayuwa. Mun kuma
san baqar makomar masu bin son zuciyarsu.

Tunda kuwa mutum yana da wannan iko, sannan


ga ilmi da hikima da Allah Ya ba shi, ko Ya bayar
a inda zai iya tambaya, toh kuwa ashe ba shakka,
mutum shi yake riqe da maqullin kowacce qofa ta
kowanne hali. Haka kuma yana da ikon da zai fara
qoqarin canja kansa da abinda yake so, har sai ya
cimma nasara. Da zarar mutum ya fara tunanin
halin rayuwarsa, kuma ya laluba dalilin samuwarsa
sosai, to kuwa zai iya gyara turbar tunaninsa cikin
kimtsuwa da hikima ta yadda zai ci moriyarta cikin
ni’ima. Wannan shi ne mutum mai la’akari wanda
a kodayaushe yake fafufukar gyara kansa ta hanyar
gyara tunaninsa. Tunanin “Ba yadda zan yi” ya fi
kowanne irin tunani baqanta, domin ta hanyarsa
mutum yake sa kansa cikin qangin da ba ficewa.
Kullum, ka cewa kanka ‘Da yadda zan yi’, shi ne
kaxai tunani da zai iya fidda kai daga quncin da ka
sami kanka ciki. Da wannan farin tunani za ka
wasa qwaqwalwarka ka fiddo da dabaru iri iri na
ceton kanka da kanka.

36
Tunani da Hali
Cin ribar rayuwa takan samu ne idan mutum ya ci
gaba da rairaye halinsa tareda sanin cewar komai
ya dogara ne a kan yadda ya gudanarda
al’amuransa. Ta irin wannan hanya, kowanne
mutum zai iya bincika kansa, ya shiga cikin
ruhinsa, ya mulmula halinsa, sannan ya shimfixa
tafarkin rayuwarsa da makomarsa. Sai da irin
wannan fafutuka tsakaninka da kanka, kuma domin
kanka, sannan za ka iya ceton kanka daga qangin
rayuwar da ba ta dace da kai ba. Hausawa, sukan
ce: “Mai nema na tareda samu”. To ka nemi kanka
ka sami kanka tukuna; sannan ka binciki abinda
kake neman. Lallai ne ka fara auna bukatunka da
matsayinka da damarka tukuna, kafin ka nema. Ta
hakane kaxai za ka san ko abin ya dace da kai ko
bai dace da kai ba. Idan ka cimma wannan matsayi,
to, sai ka qwanqwasa, ba sau xaya ba, ba sau biyu
ba. Da haquri da juriya, tareda imanin za ka samu,
za a buxe maka qofa da taimakon Allah.

A nan, yakamata ka san cewar, ba lallai ne a buxe


maka qofar da ka qwanqwasa ba, ko kuma a
vudeta gaba xaya yadda kake so ba. Amma ba
shakka, a sannu da sannu, qofa za ta buxu. Kamar
mai addu’a ne ga Allah (swt) da bukatar wani
alhairi, lallai ya san alhairin ba zai samu ba, sai ya
yi imani da mahimmancin addu’arsa da kuma

37
Tunaninka Kamanninka
fafutukarsa a kan abin. Kuma ba lallai ne ya sami
daidai, ko yadda ya nema, ko yake zaton abin ya
dace da shi ba. Amma, ko ta wane hali, cikin
haquri da ci gaba da addu’arsa da fafutukarsa,
Allah Mai amsa masa burinsa ne, kuma alhairin zai
riske shi, ko da ta hanyoyin da bai zata ba ne.
Yawancin jama’a tuni sun san haka. Amma idan
ba ka tace tunaninka ba, ba ka roqi ko nemi abinda
ya dace da kai ba, kuma ba ka yi fafutukar da ta
dace da abin ba, to ba za ka sami biyan bukata ba,
ko da kuwa ka sami abin. Kana ji kana gani abin
zai zame maka bala’i ya jawo maka masifun da ba
ka zata ba, waxanda kuma ba za ka iya jurewa ba.

A nan za mu ga ashe ma akwai dangantaka


tsakanin tunani, addu’a da fafutuka. Idan
tunaninka gurvatacce ne a kan amfanin addu’a;
watau, sam ba ka yi imani da mahimmancinta ba,
ba yadda za a yi ka yi fafutukar da ake bukata don
qofar ta buxu a gareka. Rashin tsabtar zuciyarka
da gajen imaninta da raunin haqurinta, sai su ringa
ingizaka tafarkin da babu alhairin. Samun kanka
kafin ka sami wani abu ya zama maqasudi a cikin
tsarin gyaran halayyarka. Qarkon imani ya dogara
ne a kan sanin haka.

Da tunani da halin mutum duk abu guda ne. Kamar

38
Tunani da Hali
yadda halin mutum yake fito da kansa ya nuna
kansa, toh, hakama sigar mutum take. Ma’ana ita
ce: a dangantakar Hali da Rayuwa, babu bambanci
tsakanin zahirin mutum da baxininsa. Mayanin da
mutum yake iya lulluve baxininsa da shi, shi ne na
munafunci. Amma tunda gaskiya xaya ce, asirin
munafuki yakan tonu lokaci zuwa lokaci. Ko
Hausawa ma sukan ce: ‘Munafunci Dodo ne ya kan
ci mai shi’. Wannan Magana da ma’ana take!

Harkokin kowanne mutum suna gudana ne a kan


dokokin da ya sawa kansa, waxanda ya tsara su
cikin Tunaninsa; wanda shi kuma tunanin yake
haifarwa a zahirin Halayensa da kuma kasancewar
Halayyarsa; watau, yadda yake a raye. Tunanin
mutum ashe shi ne makamashin rayuwarsa. Watau
dai, a cikin rayuwa ba abinda yake faruwa haka
siddan ba dalili. Komai sakamako ne na waxannan
saqaqqun dokokin tunani a kowanne hali da mutum
ya sa kansa, ko ya sami kansa ciki -ko na wadatar-
zuci ko na quntatar-zuci. Don hakane ya zama tilas
mutum ya kasance cikin koyon darasi daga halin da
yake ciki, ya kuma yi amfani da shi a cikin halin da
zai zo masa nan gaba don ya aza dokokin
rayuwarsa a tafarkin alhairi.

Shugabanmu, Muhammad (saw), yakan yawaita

39
Tunaninka Kamanninka
cewar, Fafutuka ita ce xabi’arsa. Wannan doka
babbar darasi ce, abar koyi ga ma’abocin nazari.
Fahimtar wannan ita za ta ba wa Xan-Adam damar
canja halayyarsa ko matsayinsa a kowanne lokaci;
ita ce kuma za ta iya daidaita rayuwarsa da
manufofinsa da bukatunsa. Amma idan mutum ya
xauka cewar komai a sassaqe yake tuntuni, ba
kuma damar canjawa, to haka wannan mutum ba
zai iya canja kansa ta kowacce hanya ba. Amma,
idan mutum ya yarda cewar shi ne mai ikon canja
abubuwan da suka shafe shi, kuma ya yarda shi ne
kaxai mai iya umartar zuciyarsa ta gyara tunaninsa
na baxini, to ba shakka, wannan mutum ya zama
jarumi a kan tafarkin inganta halayyar rayuwarsa
ta zahiri. Wannan barde yanzu ba shakka, ya zama
mai galaba kuma uban-gidan kansa. Daga wannan
lokaci mutum zai iya yunqurin fafutukarsa da
addu’o’insa don warkarda lahanin halayyarsa.

Kada mutum ya ce, ya ji Allah (swt) Yana cewa,


“Shi ne Mai arzurta wanda Yake so ba tareda awo
ba”, ya xauka wannan alama ce sakamakon
fafutuka da addu’a ba su da nasaba da qwazon
mutum a kansu. Allah (swt) ba Ya nufin haka.
Hasalima dai, Yana so ne ka tashi tsaye da
gaskiyarka da qarfinka, da addu’arka, ka yi
qoqarin kanka, ka kuma yi amfani da irin baiwar

40
Tunani da Hali
da Ya ba ka wajen gyara da inganta rayuwarka.
Yana son ka nemi duk abinda kake so daga
falalarSa domin Shi ne kaxai Mai Arzurtawa.
Amma lallai ne ka san cewar tabbatar arzikin yadda
ka nema, ko ta wata hanya dabam, wannan IkonSa
ne, ba naka ba; ba kuma na kowa bane. Shi ne Mai
ba wa duk wanda Ya so, yawan yadda Ya so, ba
tareda Ya ba wa kowa dalili ba. Da Allah (swt)
Yana ba da dalili da Ya sha tambayoyi marasa
ma’ana. Saboda haka, keve dalilin awon, nuni ne
na Hikima, ba na zalunci ba, domin Allah (swt) ba
Ya zalunci, ba Ya kuma ha’inci. Kada ka xau karin
maganar nan da ake cewa: “Zafin nema ba ya kawo
samu” tamkar hani ce gareka wajen nema yadda za
ka iya. So ake ka lura da abubuwan da suka zama
lallai ka yi su, in kana son ka samun, kuma
yakamata ka san iyaka da sauran dokokin neman.
Kada ka bar mutumcinka ko lafiyarka, ko ta wasu
su salwanta a cikin nacin neman.

A naka, lallai ne kayi qoqarin kanka kamar yadda


Allah (swt) Ya ce, kuma ka ci gaba da qoqarin har
sai ka dace; watau, har sai an buxe maka qofa.
“Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daxe ba a je ba”
inji Hausawa. Kada ka damu da daxewar in dai
kana yin abubuwan da suka dace da samun a cikin
fafurukarka tareda kiyayewar mutumcinka da

41
Tunaninka Kamanninka
lafiyarka. Kodayake sukan ce, “Zafin nema ba ya
kawo samu”, za mu iya yin wata fassarar da cewar,
wannan gyara ne kawai na magana, ko kuma
matashiya ce don ka yi la’akari da iyakacin abinda
za ka iya yi a kan bukata guda, da kuma iyakacin
abinda mutumcinka da lafiyarka za su iya jurewa.
Watau, kada ka salwantar da su a wajen neman. A
kullum, lallai mutum ya san:

A Fafutkar rayuwa da buri, ba “nasara” yadda


muke fassarata ce mafi muhimmanci ba; ita
Fafutukar ce mafi muhimmanci, musammam in an
haxa ta da cikakkiyar addu’a saboda Allah.
Fafutukar kaxai za mu iya yi. “Nasara tana daga
Allah”. Kuma, Yana yawaita bayar da ita ta
hanyoyi da dama, Ya kuma zava mana abinda ya fi
alhairi. Amma yawanci sai an lura za a gane.

Wanda bai yi fafutuka ba, kuma ya rasa, shi yake


da-nasani. Wanda ya yi fafutuka bai samu ba, shi
yake da ilmi da damar sake xaura xamara don
gaba. Waxansu, in sun kasa cimma burinsu, sai su
karaya su watsar da fafutukarsu. Wannan kuskure
ne. Babu asara ko kaxan a cikin fafutuka wadda
aka yi ta a kan abinda ya dace. Duk wanda ya bar
wa Allah (swt) amanar fafutukarsa, to ba shi da
wata damuwa, ko ya cimma nasara a yadda ya

42
Tunani da Hali
nemeta, ko bai cimmata a yadda ya nemeta ba.

Wadatar zuci takan samu ga duk wanda ya yi


fafutuka saboda Allah, ko menene sakamakon,
domin fafutukar ita ce kaxai abar da zai iya yi.
Kamar yadda na ce, Nasara tana daga Allah, kuma
duk mai la’akari da nazari, ya san an sami nasarar
ta wasu hanyoyin. A wannan matsayi, tuni mutum
ya sarrafa tunaninsa a tafarki mai kyau, ya kuma ci
xamara don gaba. Sai a jira wata damar.

Ba shakka, zuciya ita ke tanxo ababan kwaxayinta;


haka kuma ita ce mai tofarda ababan qyamarta, har
sai ta cimma matuqar bukatarta. Duk wata qwayar
tunani da aka shuka a zuci, a nan take yaxo ta yi
furanninta, har sai ta sami damar bayyana kanta.
Ashe kuwa duk tunanin kirki, to furannin kirki zai
tsirar a zuci. Haka tunanin banza furannin banza
zai tsirar a zuci. Watau, duk abinda ka shuka, ko da
a zuciyarka ne, shi za ka girba. Tuni kuma mun san
cewar, halin rayuwar da mutum ya taso cikinta, ko
ya shigeta, ko yake ciki, yana shafar irin tunaninsa,
har ma da irin halayensa da halayyarsa.

Girma cikin mutanen kirki masu mutumci, yakan


sa mutum ya koyi halayen kirki da mutumci. Zama
cikin ‘Yan Caca, yakan sa mutum ya iya ta, koma

43
Tunaninka Kamanninka
ya zama xanta. Rashin kular iyaye takan sa xa ya
zama taqadari, lalatacce. Rayuwar qunci takan iya
haifar da halin fushi ta jefa mutum cikin wasu
rigimun. Rashin makaranta shi ke kawo jahilci har
ma a tafi a bar mutum a baya. Ga misalai nan dai
da yawan gaske a kewaye da mu. Ashe, ba shakka,
halayyar muhalli da hulxa muhimmai ne wajen
gina hali da tunani. Haka, mun san ana cewa,
mutum da irin abokansa ake shaidarsa. Hausawa
da hikima suke! In ka nazarci karin maganar
qabilu da jinsina kaxai, ba shakka za ka ci riba.
Yawancin fahimtarsu ta rayuwa tana cikinsu.

Lallai mu san cewar duk abinda aka shuka a zuci,


aka kuma qyale shi ya yi furanni a zucin, to, ko
badaxe ko bajima, sai ya vullo a fili a aikace a duk
yayin da halin aikatawar ya samu. Son rai da kuma
buri, duk tunani ne a kan tafarkin aikata wani abu,
ko a kasance wani abu da zarar damar ta samu. Ka
ga ashe, yadda tunanin baxini (qulle-qullen zuci),
yake shafar halayyar zahiri; haka halayyar zahirin
itama take shafar tunanin baxinin, har sai mutum
ya aikata tunanin sannan zuciyar za ta cimma
burinta. Kamar maye ne ya sa qwalamar maitarsa a
kurwar wani. Sai ya ci zai sami hutu. Ba a sanin
maye sai ya kama mutum. Amma, tunda maye ne,
wataran zai kama da dama ta samu.

44
Tunani da Hali
Mutum ba ya ba da sadaqa, ko ya yi sata haka
siddan, ko kuma don haka aka rubuta masa. A’a
yana yin waxannan abubuwa ne domin su ya qulla
a zuciyarsa, kuma yake son aikatawa. Mutum mai
hankali da tsarkakkar zuciya ba zai aikata miyagun
ayyuka haka katsahan don zuga, nishaxi, ko don
wata wahalar duniya ta xan shigo masa ba. Da ma
can zuciyarsa tana tanxo bukatar aikata waxannan
miyagun ayyuka a asirce, har sai da dama ta samu
ya kuma aikatasu. Dama ba ta iko da mutum,
fassara shi kawai take yi. Watau, ganin galala ba za
ta sa mai gaskiya sata ba; duk wanda ya xauka ba
izni, dama can akwai saqar sata a zuciyarsa. Duk
wanda ya zageka, dama sha’awarsa kenan. Haka
duk wanda ya gaisheka cikin raha da zumunci.

A yawancin lokuta, mutum ba ya jawowa kansa


abinda ba ya so, sai dai abinda dama shi shi ne. Ba
ka jawowa kanka rigima, sai dai dama in kai dan-
rigima ne, ko kuma ita kake son yi a lokacin. Ko da
Giya tana sa rashin kunya; mai son yinta, sai ya sha
ya ce ita ce. Mutum ba zai tare a qofar gidan wasu
ba aikin yi ba, sai dama in shi malalaci ne, ko mai
son banza. Mace ba ta karuwanci, sai dama in
lalatacciya ce. Alqali ba ya zalunci, sai dama in shi
makwaxaici ne, ko maqetaci. A zukatan mutanen
banza, qulle-qullen banza. A zukatan mutanen

45
Tunaninka Kamanninka
kirki, shirye-shiryen kirki. Bukatunsu duka a zuci
suke, kuma daga nan suke wanzarda su a fili su
aikata ashsha, ko su aikata alhairi.

Ina masu cewar, ‘Matsuwa ce ta sa ni”; ko kuma,


“Komai haka Allah Ya shirya”. To hakane ta wani
fanni, amma kada su manta Allah (swt) Ya yi
alkawarin yin cikakken Hisabi a ranar gobe
qiyama. Hisabi kuwa, tunasarwa ce da gargaxi ga
xan-Adam cewar shi (xan-Adam xin) ke riqe da
makomarsa tun daga ayyukansa a wannan duniyar.
Allah (swt) Ya ba mu hankali da iko a kan
hankalin, sannan Ya taimakemu da shiriya (tamkar
shawarwari) a kan yadda za mu inganta
rayuwarmu. Ya kuma zayyana mana horo iri-iri da
lada iri-iri; Ya kuma ba mu labarin Wuta da
Aljanna. Saboda qaunarmu da kuma son mu
shiryu, sai Allah Ya kuma sauko mana da
Littattafai (kamar Al-Zabura, Al-Taurat, Al-Injil
da kuma Al-Qur’ani Mai-Tsarki a qarshe, wanda
ya qunshi duk waxancan). Tare kuma da
waxannan littafai, Ya sake aiko mana da
AnnabawanSa, domin mu koyi darusan rayuwa
ingantacciya. Ba shakka, a addinanmu muna da
duk abubuwan da suka kamata mu yi amfani dasu
don kyautata tunaninmu, tace halayenmu da kuma
inganta ilahirin halayyarmu. Waxannan lallai ne su

46
Tunani da Hali
zama shika-shikan manufar rayuwa in dai mutum
yana nemarwa kansa makoma ta alhairi a wannan
duniyar da kuma can lahirar.

Masu tunani zurfaffa sun san, da ba mu ne masu


iko da zavin tunaninmu da ayyukanmu ba, da Allah
(swt) Bai aiko mana da shiriya ba. Dá hakane, da
babu Hisabi. Dá hakane da babu horon Wuta ko
sakayyar Aljanna. Dá hakane da ba dalilin addini,
balle irin ibadunsa. Sannan kuma, dá duk
waxannan hakane, dá maiyiyuwa ne Allah (swt)
Bai halitto mu yadda muke ba, tunda Ya ce dalilin
halittar mu shi ne mu bauta maSa. Amma saboda
alkawarin Hisabi, sai Ya bamu zavin mu bi, ko mu
qi, daga qulle-qullen tunaninmu. Rayuwarmu da
makomarmu tana hannunmu. Ashe, imani shi kansa
a cikin qoqon tunaninmu muke sassaqa shi. In mun
ga dama mu yi imani; in mun ga dama mu bi son
zuciyarmu na shexanci.

Abu biyu kawai da bamu da iko a kansu a wannan


duniya tamu sune QUDRA DA IRADA. Su kuwa
waxannan ikonni, ba yadda za mu iya yin iko da
su, domin Allah (swt) Ya bar wa kanSa iko da su,
Shi kaxai. Da duniyarmu da sauran duniyoyi da
dukkan abubuwan dake tsakaninsu; kai, dukkanin
Sararin Samaniyar gaba xayansa, da dukkanin

47
Tunaninka Kamanninka
abinda ke cikinsa, da Qudra da Irada Allah (swt)
Yake sarrafa shi. Komai da komai, har da mu
kanmu, sakamakon QudrarSa da IradarSa ne.

Amma, ikonnin Allah da suke tafiyarda


rayuwarmu a cikinmu suke ba a wani guri suke ba.
Waxannan ikonni a halittarsu, mun sansu sarai,
domin su ne zuciyarmu da qwaqwalwarmu.
Zuciya ta sarrafa ranka; qwaqwalwa kuma ta
sarrafa rayuwarka. Tunaninka a tsakaninsu yake
tsira ya kuma yaxu. Allah (swt) Shi ne Yake da iko
a kan rayuwar waxannan; amma kai ne kake da iko
a kan yadda ka za ka yi amfani da su da yadda za
ka gyara lafiyarsu. Tunaninmu shi ne abincinsu.
Sannan kuma ayyukanmu sune amansu.

Mutum, kamar yadda muka sani, shi ne mai iko da


kansa. Idan ka ga dama sai ka tashi ka faxa rijiya.
Idan ka ga dama ka tashi ka yi nafila. Idan ka ga
dama sai ka tsabtace kanka; in ka ga dama ka mari
mutum, komai ta fanjama fanjim. Idan ka ga dama
ka nemi ilmi; idan ka ga dama ka yi taurin bashi ko
ma ka qi biyansa, alabarshi a la’anceka; idan ka ga
dama ka duqufa wajen rubuta littafi mai amfani.
Idan ka ga dama ka yi fafutuka; idan ka ga dama
ka watsar ka zama xan daba ko xan qwaya. Duk
ya rage naka da ganin damarka.

48
Tunani da Hali
Tunaninmu da ayyukanmu su ne sukan zama qangi
ko ‘yancin makomarmu. Su ne suke jefa mu
kurkukun talauci, ko na rashin mutumci. Su ne za
su iya jawo mana zagi ko wani bala’i dabam, idan
muka zavi tunanin sharri da aikata shi. Amma kuma
su ne mala’ikun rahamarmu masu ‘yantarda mu
izuwa daular bushasha da mutumci, idan muka zavi
tunanin alhairi da aikata shi.

Mutum ba ya samun abinda yake so, ko ya roqa


wajen Allah (swt), sai abinda ya dace ya samu. Ka
yi karatu sosai tukuna, sannan ka roqi Allah Ya sa
ka ci jarrabawa. Ka nemi maganin cutarka tukuna,
sannan ka roqi Allah Ya kawo sauqi da waraka. Ka
fara ciniki kafin ka nemi riba. Ka yave gidanka
kafin damina ta zo, domin yin haka ne kaxai zai
kare gininka. Ka qulle kantinka da kyau, sannan ka
roqi Allah Ya tsare maka shi. Watau, lallai ka fara
yin abinda yakamata ka yi tukuna. Da bukatun
mutum da addu’oinsa duka suna karvuwa ne idan
sun dace da tunaninsa da ayyukansa. Kada ka yi
qaranci a cikin abinda yakamata ka yi, sannan ka ce
za ka yi kukan Allah (swt) Bai taimakeka ba. Allah
(swt) da kimiyya Yake aiki, kuma tuni ya tsara
yadda komai zai tafi. Ba abinda Allah (swt) ba Zai
iya yi ba. Amma akwai abubuwan da ba Ya yi,
domin ba haka Ya tsara ba.

49
Tunaninka Kamanninka
Mai hassadar matsayin wani ba zai sami wannan
matsayin ba ko da ya roqa, domin matsayin bai
dace da tunaninsa da ayyukansa ba. Idan kuwa ya
samu, to halaka ce gareshi. Sai mutum ya zama
sarki, amma babu sigar sarkin; ko kuma ya zama
don wani tsautsayi a gaba. Sai mutum ya sami
kuxi babu arziki; ko kuxin su sa shi cikin wata
halaka da baqin ciki. Sai mutum ya sami xaukaka,
amma ya qarke a kurkuku. Sai ka ga tafkekiyar
gona babu tsiro ta zama daji. Haka za ka ga wasu
shirim ba ci ba. Ga matsayi babu mutumci; ga kuxi
babu masoya; ga sarauta babu Mulkin, ba kuma
talakawam; ga ilmi ba xalibai.

Amma mai sha’awar matsayin wani, wanda kuma


ya yi qwazo da fafutuka saboda Allah, sai ya sami
matsayin in ya dace da wannan sha’awar da
fafutukar. Irin waxannan mutane su ne suke cin
ribar abinda suka samu ko suka zama. Ta hanyarsu
kuma alhairi iri iri ya tsiro wanda zai amfani
jama’a masu yawan gaske. Ta nan kuma su sami
biyan wata bukatar daga Allah (swt), su kuma tarar
da alhairi a lahirarsu. Duk kuma daga kyaun
tunaninsu.

Mutane suna son su kyautata matsayinsu da


halayyarsu, amma ba sa son su kyautata kansu. A

50
Tunani da Hali
hali irin wannan, sukan kasance cikin qangi na
rashin ci-gaba da rashin biyan bukata. Duk
mutumin da yaqi fahimtar kansa, yaqi gyara
zuciyarsa, yaqi yin fafutuka don kansa, ba zai tava
cimma bukatar da ya shuka a zuciyarsa ba. Wannan
haka yake, ko mecece bukatar; kuma ko da ta
duniya ce, balle kuma ta lahira. Tamkar mutumin
da ya xaura niyyar tafiya ne, amma bai fito daga
gidansa ba. Ba inda za shi duk qarfin niyyarsa, don
bai yi abinda yakamata ya yi ba. Bai xauki taqar
farkon da ta zama tilas ba.

** Xauki mutum wanda ya kamu da ciwon


sukari. A shirye yake ya biya munqudan kuxi, ko
ya yi wata xawainiya don neman maganin cutar,
amma ba ya son ya daina shan zaqin. Watau, yana
son ya biya bukatar shan zaqinsa, kuma har-wa-yau
yana son lafiyarsa. Wannan mutum bai cancanta ya
zama mai lafiya ba, domin bai koyi komai daga
darasin sadaukarwa ba. Rashin azancinsa ya
dulmiyar da shi; son-kansa (ko ma mu ce, ‘qin
kansa’) ya raraki bukatarsa. Ya zama shashasha
mara la’akari.

** Xauki misali, Dan-kasuwa da ya shahara


wajen Algus da zafafa farashi; illoli biyu a kasuwa
daga macuta. Idan mutane suka komar da cinikinsu

51
Tunaninka Kamanninka
ga masu gaskiya da tausayi, sai ya yi ta fusashin
ana guje masa, ba ya duba nasa laifin; har ma ya
ringa sa qabilanci a cikin al’amarin. Wannan
mutum ya zama sakarai. Har abada ba zai yi arziki
ba, kuma ba zai inganta matsayinsa a kasuwar ba.
Shekara bayan shekara, haka zai kasance ba ci
gaba, kullum a cikin wannan rumfar, in ma ya ci
sa’a. Haka wasu suke ta qorafi ba son gyarawa.

** Xauki malalata masu son banza, waxanda


suka qi neman aikin yi ko wata sana’a, amma suna
zargin wasu na dannesu. Irin waxannan mutane ba
sa tunanin amfani da wata baiwa da Allah (swt) Ya
yi masu, balle su yi amfani da ita wajen inganta
kansu. Sun fi sha’awar su shantake a gaban wani,
ba sa kishin kansu. Irin waxannan mutane haka za
su rayu a banza, suna gani ana ta shigesu. Su yi
hasara a duniya, su kuma yita a lahira.

** Ko kuma xauki al’umar da ba a biyan


haraji; ba sa haxa kai ko jaddawa hukuma gameda
aikata gaskiya, amma suna ta zage zagen cewar an
qi gyara matsalolin rayuwarsu. Irin waxannan
mutane ba su fahimci ma’anar ‘yanci ba, ba su
kuma san cewar kwabonsu na haraji shi ne zai ba
su haqqi a cikin milyoyin Baitul-Malin ba. Wanda
bai biya haraji ba, ya rasa wannan haqqin.

52
Tunani da Hali
** Ko kuma xauki jama’ar da suke yabon
shugabannin banza; suke kai caffa ga macutansu;
suke zavar waxanda ba su dace ba, su kuma sun qi
tavusawa, amma kuma suna qorafin banzaye na
mulkarsu; ko ana fasa Baitul-Mali ana cinye
kuxaxensu. Shekara da shekaru, amma sun kasa
xaukar darasi, sai ihu a kasuwa wai an dannesu, an
hana su ci-gaba. Ba sa tsayawa su yi tunanin su ne
suka bada iznin a cuce su. Irin wannan al’umma ba
za ta ci gaba ba, sai talakawa sun san haqqinsu da
mutumcinsu. Sai sun sa masu mutumci da gaskiya
da qwarewa a gaban harkokinsu.

** Ko kuma xauki Mai-gidan da ya dakushe


rayuwar yaransa; ko yaran-gida da suke cutar mai
gidansu, amma dukkaninsu suna sha’awar inganta
matsayinsu. Idan al’amuransu suka lalace sai su
ringa zargi ba tareda nazarin nasu illolin ba. Mai
Gidan ko Mai Kantin ya qi biyan haqqinsu, su
kuma yaran suna yi masa sata. Dukkaninsu sun yi
hasara daga illar son zuciyarsu.

** Ko kuma xauki iyayen da suke jin daxin


karvar kuxi da turare wajen ‘yarsu mara aure mara
aikin yi, amma suna kukan ta lalace; wai ba yadda
za su yi da ita. Sun manta su suka zugata ta wajen
kau da fuska daga sharrukan da ta ke aikatawa.

53
Tunaninka Kamanninka
** Ko kuma xauki mai qaramin jari, da ya je
ya qaro aure, ya kuma canja mota, ko ya fente
gidansa don riba ta xan qaru. Amma kuma idan ya
kasa inganta cinikinsa, ko ya karye gaba-xaya, sai
ya ringa la’antar wasu da jawo masa hasara, ya
manta da nasa almubazzarancin.

Mutum, ba shakka, shi yake riqe da makomar


halayyarsa, domin shi kaxai zai iya gyara
rayuwarsa. Kowa ya san kansa fiye da yadda wasu
suka san shi. Wanda yake neman ci-gaba da
ingantuwa, amma kuma yana ta vata hanyarsa da
qazaman tunani da ayyuka, ba yadda za a yi ya
cimma waxannan bukatu. Bari in sake nanatawa:
‘Kowa ya san kansa fiye da yadda wasu suka san
shi’. Mutum ya iya bin diddigin tunaninsa da
ayyukansa ya ga ko sun dace da neman biyan
bukatarsa. Da kansa zai iya zama alqali a kan
dalilan nasararsa ko hasararsa.

A nan, za mu yi la’akari da cewar matsalolin da ke


shafar nasara ko hasara suna da wahalar
fayyacewa, domin ba a kodayaushe suke zama
daidai ba. A cikin halayyar rayuwa, abubuwan da
za su iya haifarwa wani farin-ciki, sai kuma su
haifarwa wani baqin-ciki. Mutum ya iya
kasancewa mai gaskiya da aiki tuquru, amma

54
Tunani da Hali
kuma ma’abocin wahala. Haka kuma, akan sami
macuci mara gaskiya, amma kuma ma’abocin
wadata. A zahirin rayuwa, ba kasafai irin
waxannan misalai suke faruwa ba tareda dalili ba,
ko ta yaya muka auna rayuwar. Kada mu xauka
cewar mai gaskiyar ya rasa wadatar ne don shi mai
gaskiya ne; ko kuma macucin ya sami wadatar ne
don ya yi cuta. Idan muka xau haka, to mun kai
tunaninmu qarshen bango, kuma tunani irin
wannan wanda bai ba da wata ‘yar kafa ta wani
dalili dabam ba, kuskure ne.

Maiyiwuwa ne, mutumin da muke ganin mai


gaskiya ne a zahiri, yana da wani aibu a baxininsa.
Haka, wanda muke gani macuci ne, maiyiwuwa ne
yana da wani abin kirki tareda shi, kuma wannan
wadata ta samu ne saboda wannan abin kirkin. Ko
ta yaya dai, Mai gaskiyar zai ci ribar gaskiyarsa a
inda ya aikatata, amma kuma zai yi hasara daga
aibun da ke zuciyarsa na sharri. Shi kuma mara
gaskiyar zai yi hasarar baqin tunaninsa a inda ya
wanzar da shi, amma kuma zai ci ribar tunaninsa na
kirki a inda ya aikata shi.

Wannan matsala, kamar yadda na ce, tana da


wahalar warwarewa, musammam ma ga mai
gaskiya da aiki tuquru wanda yake cikin wahala.

55
Tunaninka Kamanninka
Za mu tarar da wannan magana a can gaba.

‘Me yasa mutanen kirki suke shiga wahala?’ Ba


shakka, wannan tambaya ce wadda yakamata a
amsata a nutse da basira. Waxansu imaninsu yakan
bar su xungum, ko kuma ya raunana duk lokacinda
tunanin matsalolin rayuwarsu ya xan giftawa
qwaqwalwarsu. Sukan bincika yadda za su iya,
amma sukan kasa samun amsar da za ta gamsarda
su. Sun ga sun yi fafutukar, sun gwada gaskiyar,
sun yi ibadar, sun yi addu’ar, sun nuna mutumcin
da yakanar, amma ina! Maimakon abubuwa su
gyaru, sai daxa tavarvarewa suke. Amma fa duk a
ganinsu, domin watakila ba su auna wasu
abubuwan ba. Hankulansu suna wasu guri dabam.

Ba za ta yiwu a san takamaiman dalilan da suka sa


mai gaskiya ya qasqanta ba, sai an tace tunaninsa,
an tankaxe an kuma rairaye qulle-qullen zucinsa.
Sannan ne kaxai za a san ko qasqantakar tasa
sakamakon kyaun niyarsa ne, ko kuma ta
mummunar aniyarsa ce. Amma, idan shi da kansa,
ya nutsa sosai a cikin tunaninsa, kuma fi-
sabilillahi, to zai tarar da babbar dokar nan ta
Allah (swt) mai cikakken adalci, wadda ba yadda
za a yi ta yi sakamakon tunani ko aikin kirki da
sharri; ko kuma aikin sharri da sakamako mai

56
Tunani da Hali
kyau. A irin wannan matsayi, mutum, zai iya
komawa baya ya binciki jahilci da makantar
rayuwarsa, har sai ya tararda dalilan da suke kawo
masa cikas a rayuwarsa. Haqiqa, gaskiyar wasu
takan sa su cikin wahala, domin al’umarsu ta banza
ce wadda ba ta son mai gaskiya. Sai dai irin
wannan wahala, ba sharri ba ce ga mai shanta.
Babban alhairi ce a gaba, kuma a wajen Allah
(swt). Haka akwai masu jin daxin rayuwarsu domin
su marasa gaskiya ne, ko kuma ‘yan iska ne, ko
kuma marasa kunya ne. Harwayau, suna jin daxin
ne domin suna cikin al’umar banza wadda ba ta
qyamar mutane irinsu. Sai dai irin wannan jin daxi
ba alhairi ne ga mai shansa ba. Sharri ne babba a
gareshi a lokaci mai zuwa. A kowanne hali, mun
san: Allah ba azzalumin kowa bane. Za mu nanata
wanan magana a gaba.

Wanda ya quduri alheri, ya kuma aikata shi, to, zai


ga alheri. Wanda ya quduri sharri, ya kuma aikata
shi, to, lallai zai ga sharri, ko badaxe ko bajima.
Wannan doka a rayuwar xan-Adam ba yadda za a
yi ta canja, duk runtsi. Kada mu manta cewar, wasu
mutane ba kasafai suke fahimtar irin baiwar da
Allah Ya yi masu ba. Wasu kuma sukan fahimta,
amma sukan raina, saboda hankalinsu na kan wani
abu dabam da suke ganin ya fi wannan baiwar da

57
Tunaninka Kamanninka
Allah Ya yi masu. Ba wata baiwa da Allah Ya
bayar wadda ba za a iya amfani da ita a cimma
muhimmin burin rayuwa ba. Sai dai in an raina ko
ba a bincika ba.

Sai ka ga mutum yana ta addu’ar neman rufin asiri,


ashe tsabar kuxi yake so, bai fahimci ma’anar rufin
asirin ba. Wani ka ji yana neman matsayi, amma
ya san bai dace da shi ba. Harwayau, ga mai kuxi
kuma ya kasa gamsuwa don bai sami saurauta ba.
Ga xan-Kasuwa ya qwallafa ransa a kan sai ya
raunana wani. Sai ka ga manomi yana wahala da
kwangila, ko kuma talaka yana neman auren mata
ta biyu ko ta huxu, ga ‘ya’ya barkatai, yana cewa,
“bakin da Allah Ya tsaga.....”. Haka dai za ka ga
mutane iri iri suna fankama iri iri cikin bukatu
marasa ma’ana a garesu. Gaba xaya sun fita daga
tsarin rayuwar da ta dace da su, sun shiga wata can
dabam. In sun shiga wata wahala ko wata masifa,
mun san inda za su jefa qorafinsu: Sukan ce,
“Allah ne Ya jawo masu!” Wannan Jahilci!

Mutane irin waxannan ba sa cikin lissafinmu,


domin sun qaranta a wadatar zuci, sun qaranta a
tunanin abinda zai fi masu alhairi. Ba su fahimci
Allah (swt) sosai ba. Kuma, sun sha bamban da
irin waxanda muke zance a kansu.

58
Tunani da Hali
Ko da a cikin neman biyan bukatu ma, mun san
cewar, duk abinda ka shuka shi za ka girba. Ba za
ka shuka Dawa ka girbi Gero ba. Haka ba za ka
tatsi Zuma daga Saniya ba. Akwai abubuwan da za
su iya faruwa, ko za a iya yi, ko samu; akwai kuma
waxanda ba haka bane. Wasu abubuwa ba za su
canja ba, don kawai mun neme su, ko don mu ne.
Tilas mutum ya fahimci wannan doka ta rayuwa
kuma ya yi la’akari da ita. Sa’a, ita kanta, ba ta
samun wanda tunaninsa ba kimtsatstse bane. A
kodayaushe tafi son ta taimaki gwarzo wanda
tunaninsa ya yi saiti a kan fafutukarsa. Ko da za ka
ci Sa’a, to sai ka gwada nema, ko yin abin tukuna
ta hanyar tunani qwaqqwara. Duk da haka, ba za
ka ci Sa’a a kan abinda bai dace da kai ba, ko
abinda ba zai yiwu ba. Duk wanda ya ci Sa’a, to
dama can zuciyarsa da qwazonsa a shirye suke su
karveta. Ba mai iya rarrabe mutane irin Sa’a,
domin ba a cinta a banza.

A dandalin sakamakon rayuwa, dukiyar kuxi gefe


ce kawai. Wataqila duk ganin wahalolin nan namu
yakan faru ne saboda taqaita sakamakon rayuwa
cikin dukiyar kuxi kawai. Watau, ba ma duba
sauran abubuwan da Allah (swt) Ya yi mana na
sakamako da su. Misali: Kamar shugabanmu,
Muhammad (saw), za mu iya sa Wadatar Zuci, a

59
Tunaninka Kamanninka
tsarin sakamakon ayyukan kirki a rayuwarmu.
Haka, Rufin-Asiri, Mutumci a idanun Jama’a,
Yawan Tuna Allah, Soyayyar jama’a, Hikima da
zurfin Tunani, Iyali na-gari, Damina da girbi masu
kyau, Kwanciyar-rai, Kwarjini, da lafiya. da
sauran irinsu birjik. Duk waxannan sakamako ne
da Allah (swt) da Yake ba wa bayinSa a dalilai
dabam dabam. Rashinsu, ba shakka, hasara ce ga
waxanda suka rasa su a dalilai dabam dabam.

Dukkanin waxannan abubuwa, da wasu da yawa, a


tsarin “ARZIKI” suke, kuma in shi ne ma’auni, to,
wahalunmu, ko hasarunmu, kaxan ne. Wanda ya
san, ya kuma fahimci haka, to, zai ga sakamakon
ayyukansa: Na alhairi a cikin Arziki. Na sharri
kuma cikin Nadama da raina matsayi. Duk wanda
ya yi tunani mai zurfi, to kuwa zai gode Allah
(swt), domin Shi ba azzalumin kowa bane.

Za mu ga haka a Babi na 7, insha’Allah. Na


tunkari wannan al’amari gaba-gaxi a can. Amma a
karanta a hankali a nutse.

60
Tunani da Hali

61
Tunaninka Kamanninka

62
3
Wahala da Wadata

“Wahala
da Wadata
“Mahaqurci, Mawadaci”

Y in la’akari da jawaban baya, zai sauqaqa


fahimtar cewa, ita wahala kusan a kodayaushe
sakamako ce ta gurvataccen (ko karkataccen)
tunani. Watau wahala, nuni ce ga alamar mutum ya
fita daga tsari na kirki. Shan wahala, ko shiga
cikinta, alama ce ga mai hankali cewar yakamata
ya fara tunanin tsarkake kansa, ya sabunta kansa,
domin ya nemawa kansa rayuwa wadda ta dace da
tsari nagari. Watau, lallai ne ya sake sabon tunani.

Kamar dai “Ciwon Kai” ne, yadda yake nuna


alamar wani abu a jiki ya tavu. Nan da nan sai a yi
bincike a nemi magani. Ashe, “Wahala” ita ma

63
Tunaninka Kamanninka
ciwon-kai ce ta rayuwa. Wanda ya fahimci ya fara
shigarta, lallai ne ya binciketa, ya nemi dalilinta da
maganinta. Tilas ne binciken ya sanarwa kai, ko
wahalar ta gaskiya ce, ko kuwa ta son zuciya ce da
rashin gode Allah, kamar dai wahalar neman
abinda bai dace da kai ba, ko ta xaukar nauyin da
bai dace da kai ba. Xaukar wannan mataki nan da
nan shi zai sa mutum ya gyara tunaninsa domin
tunkarar gyaran halayyarsa.

Kafin mu yi nisa, yakamata mu tambayi: wai shin,


“Mecece Wahala?” A gaskiya, “wahala” tana da
wuyar fassarawa, ko mu ce ‘wahalar’ fassarawa.
Amma daga wannan batu, za mu fara fahimtar
ma’anarta. A taqaice, za mu iya cewa, ita ce:
“abinda aka kasa yi”, ko kuma, “ake yi da kyar”.
To, wasu sa iya tambayar: tilas ne sai an yi abinda
ba za a iya yi ba? A nan maganar take. Idan ya
zama tilas a yi wani abu, amma babu halin yi, to
akwai alamun za a iya shiga wahala a kan wannan
al’amarin. Wanda ya hango haka, lallai ne kuma
ya fara neman mafita, watau yadda zai yi ya
kwarawa wannan matsala ruwan sanyi tun kafin ta
zama wahalar. Yawancin wahalu, mutane suke
jawowa kansu, amma yawanci ba tareda sani ba,
saboda rashin hangen nesa. Akwai kuma mutane
da suke sa kansu cikin wahala a kan dalilan da

64
Wahala da Wadata
basu cancanci halayyarsu ba. Amma a gaskiya
akwai da yawa waxanda ake jawo masu ita, sai dai
in ka duba sosai sai ka tarar cewar sune suka qyale
ake jawo masu ita. Watau, suna gani sun qi su
kauce gabatowarta ko yin maganinta in ta ison.

Kada a xauka a nan cewar, wahala nuni ce ta cewar


wanda ya shigeta mutumin banza ne. Ko kaxan ba
haka ce manufa ba. Fita daga tsarin kirki, yanayi ne
na tunani wanda ba zai taimakawa mai yinsa
samun masalahar rayuwa ba. Rashin wannan
masalaha shi ne sanadiyar tavarvarewar al’amura,
watau, tushen samuwar wahalar; kamar yadda
rashin tsarkin zucin ya zama ummul-aba’isin
raunannan tunanin. Wanda ba shi da kuxi, ko
matalauci, ko faqiri, ba ya cikin wahala har sai
zuciyarsa ta fara saqa masa wasu bukatu da ba su
dace da matsayinsa ba. A wannan hali ne ake shiga
cikin quntatar zucin dake haifarda wahalar. Haka,
‘sai na yi abinda wane ya yi’, ita ma mataki ce ta
shiga cikin wahala, musammam ma in gasar ba ta
alhairi ba ce. Mutumin da ya raina matsayi, ko
hanyar da Allah (swt) Ya zavar masa, ya maida
hankalinsa kan wani matsayin, ko wata hanyar da
ba ta dace da shi ba, to sai ya shiga wahala, ko
badaxe ko bajima. Haka mutumin da ya xora, ko
ya tsara rayuwarsa a kan qarya, to wataran sai

65
Tunaninka Kamanninka
Gaskiya ta yi halinta. Daga rannan kuma an shiga
wahala da jin kunya.

Matalaucin, ko faqirin da ya yi tsab da tunaninsa,


ya kuma shirya canja halayyarsa ta wajen wani
yunquri ko wata fafutuka ta alhairi, to a hankali
Allah (swt) Zai taimaka masa da hikimar da za ta
fitarda shi daga qangin talaucin ko faqircin.
Babban wahalalle, shi ne mai neman abinda bai
dace da shi ba; shi ne kuma mai nema don fariya
ko don rashin gode Allah, ko don gasa. Shi ne
kuma, mai son aikata abubuwan da suka fi
qarfinsa, ko waxanda ba su dace da shi ba. Wasu
na sane suke jawo wan kansu wahala, saboda
ragwanci ko saboda wawanci, ko don son su
burge. Masoyanka ba sa bukatar burgarka;
maqiyanka kuma ba za su burgu da burgar taka ba.
Saboda haka menene kenan amfaninta?

Idan ka haxa ma’anonin waxannan batu, za ka


tarar cewar, a fannin farko, ita kanta wahalar da
ake zaton ana ciki, saqa ce ta zuciyar da ba ta
wadata daga sauran baiwoyi da mutum yake da su
ba. Ko kuma, a sauqaqe, zuciyar da ba ta binciki
sauran kyautuka da Allah (swt) Ya yi waxanda za
su iya cike gurbin wahalar da ake zaton ana ciki
ba. A fanni na biyu, son zuciya da rashin gode

66
Wahala da Wadata
Allah, da son iya yi, su kansu wahalu ne
matsananta wadanda suke haifarda wasu wahalun
dabam. Wanda ya xaukarwa kansa abinda ya fi
qarfinsa, ba shakka shi ya gayyaci wahala.

Mun san wahala a gun wani, ba wahala ce a gun


wani dabam ba, domin ba matsayinsu da
halayyarsu xaya ba. Amma a yawancin lokaci,
wahalar wasu ta haifu ne daga kwaxayi, ko kishi
ko qyashi, ko gasa, ko kuma hassada. Wani in ba
shi da kuxi, sai zuciyarsa ta raya masa yana cikin
wahala, duk da sauran abubuwan da ya mallaka.
Wani kuma ga kuxin, amma hankalinsa na kan
wani abu dabam da ya rasa. Wani yana da bukata,
amma baya son ya sarrafa baiwar da Allah (swt)
Ya yi masa wajen neman abin biyan wannan
bukatar. Wani wahalarsa matarsa; wani ‘ya’yansa;
wani dukiyarsa; wani kwaxayinsa; wani rashin
gaskiyarsa da rashin mutumcinsa; wani ra’ayinsa;
wani maqiyansa; wani kuma lalacinsa ko rashin
dauriyarsa. Duk waxannan da sauransu da yawa
suna da magani, in an yi tunani mai tsarki a tsanake
a kansu, an kuma aikata abubuwan da suka dace.

Zurfaffan tunani mai kyau shi ne zai taimaki


mutum wajen fexe wahalar da gurvataccen tunanin
ya haifar; ya wanke gubar wahalun har sai an

67
Tunaninka Kamanninka
cimma wadatar zuci ta wajen tunowa da ni’imomin
da Allah (swt) Ya bayar tuni, amma wadanda
baqin tunanin ya rufe. Irin wannan tunani yana
daga cikin muhimman hanyoyin da mutum zai iya
gina zaman lafiya da kansa, ya kuma godewa
Allah (swt), ko mecece halayyarsa a idanun
mutane. Idan ka daka ta mutane, ko ka ce rashin
wani abu da ka rasa illa ce, to ba shakka, ka shigar
da kanka cikin wahala. Sarrafa abinda kake da shi
wajen sauwaqe wahalarka. Girman kai ba naka ba.

Duk tsanancin halayyarka, akwai wanda ya fi ka.


Duk jin daxin rayuwarka, akwai wanda ya fi ka.
Mawahalci shi ne mai duban na sama da hassada,
ko duban na qasa da fariya. Ma’abocin wadata shi
ne wanda ya dubi na sama da farin tunani da
addu’ar shi ma Allah Ya taimaki fafutukarsa ta kai
shi fiye da haka. Sannan ya dubi na kasa da godiya
da ni’imomin da Allah Ya yi masa, ya kuma
tausaya ya taimaka. Amma duk wanda tunaninsa a
kan abinda ya rasa ne; da wanda ya kasa daidaita
bukatunsa da halayyarsa, to ya shiga wahala.

“Wadatar zuci”, ba dukiyar kuxi ba; ba yawan


‘ya’ya ba; ba mulki ba; ba gida mai tsada ba, ba
kyakkyawar mace ko miji mai kuxi ba; ita ce
babbar ma’aunin tunani wanda ya kasance

68
Wahala da Wadata
kyakkyawa, kuma ita ce alamar rayuwa mai
albarka da arziki. Haka kuma, “Wahalar-zuci”, ba
rashin kuxi ba; ba rashin ‘ya’ya ba, ba rashin
sauran adajen duniya ba, ita ce ma’aunin tunani
mummuna, da rayuwa mai qunci. Kowa ya yi
tunani a nutse cikin gaskiya da kishin-kai, to kuwa
lallai a sannu zai sami amsarsa.

Ma’ana a nan ita ce: Mai-Kuxi ya iya zama


tsinanne; Talaka kuma mai-albarka, kamar yadda
aka fi samu. Amma, Kuxi da Albarka, ba yadda za
a yi su haxu a kan mutum guda, sai in kyakkyawan
tunaninsa ya haifar da kyakkyawan amfani da
kuxin. Wannan mutum shi ake kira Mai-Arziki.
Mutumin da Allah (swt) Ya rufawa asiri, ya lulluve
shi da mutunci da yawan tuna Allah, ba shakka,
yana cikin masu arziki na qwarai, ko da ba shi da
jarin qwandala. Jarinsa shi ne wadatar zucinsa da
zaman lafiyarsa, a lungunsu ko a qauyensu cikin
mutuncinsa da masoyansa. Kuma da ya yi magana
a saurare shi.

Talauci da Wahala, ba za su haxu a kan mutum


guda ba, sai a kan wanda ya qi tsarkake tunaninsa,
ya qi kuma yin kyakkyawan amfani da duk irin
baiwar da Allah (swt) Ya yi masa; ya qi daidaita
rayuwarsa da halayyarsa. Mutum irin wannan shi

69
Tunaninka Kamanninka
ake kira, Matsiyaci, komai kuxinsa, ko sarautarsa,
ko ilminsa. Haka Mai-kuxin da shi kaxai kuxin ke
amfana, ba shakka, yana cikin tsarin matsiyata
marasa albarka. Kuxin ne za su kai shi su baro.
Ranar da ya rasa su ya shiga uku. Ba mai yi masa
jaje, balle taya shi addu’a.

Kamar yadda kuxi da arziki suka bambanta, haka


Tsiya da Talauci. Idan muka yi nazari sosai, sai mu
ga dukkaninsu yanayin zuciya ne ga mai su. Yadda
ake samun matsiyacin Mai-kuxi, haka kuma ake
samun Talaka Mai-arziki. Bambancin kowanne a
yanayin zuci yake; kuma shi suke fassarawa a
zahirin Halinsu da kuma Halayyarsu. Zuciyar Mai
arziki fara ce cike da alhairi da bushahar wadatar
zuci. Amma zuciyar Matsiyaci, baqa ce, cike da
muni da quntatar zuci. Duk wanda ya bincika
yanayin zuciyarsa, to kuwa zai iya sanin ko shi
Mai arziki ne (komai rashin kuxinsa), ko kuma shi
Matsiyaci ne (komai kuxinsa). Duk abinda ka tarar
shi ne haqiqanin gaskiyar kamanninka. Sai dai ka
hilaci kanka, amma ka san hilatar kanka kake yi. A
nan kuma ka sake zama shashasha, domin ba za ka
canja ba. Ka cuci kanka da kanka.

Lallai mu lura cewar: ba wanda Allah (swt) Ya


halitta Matsiyaci. Haka ba wanda Ya halitta Mai-

70
Wahala da Wadata
kuxi. Da kuxi da tsiya duk masifun duniya ne, ba su
da nasaba ko kaxan da jin daxi, halin kirki, arziki
ko imani. Siffar zuciya da tunanin mutum na ainihi
a suturce su ke cikin ni’imar wadata, kwanciyar
hankali da cikakken imani. Akwai wanda zai iya
sarrafa talaucinsa wajen kyautata rayuwarsa. Akwai
kuma wanda zai iya sarrafa kuxinsa wajen watsa
rayuwarsa. Mai kuxin da ya sarrafa kuxinsa wajen
kyautata rayuwarsa da ta wasu shi ne Mai-Arziki,
kamar dai Talakan da ya sarrafa rayuwarsa wajen
kyautata rayuwar wasu har da tasa. Dukkaninsu
mutane ne masu farin tunani. Daga qoqarinsu na
farantawa jama’a, wasu mutanen kirki suke samun
nasu farin cikin da wadatar zucin.

Dokokin halittar mutum a tsarin biyayya ga duk


umarnin Allah (swt) suke. Mun san wannan shi ne:
Deen-al-Fitra, watau: ‘hukumcin asali’, wanda a
tsarinsa, duk gavovi da jikin kowacce halitta
umarnin Allah (swt) kawai suke bi. Watau, ba
halittar da take da ikon ainihi a kan kanta. Idan
idonka ya mutu, ba za ka iya ce masa ya buxe ba.
Idan Rai ta zo fita, ba za ka hanata ba. Idan qafarka
ta gurgunce, ba za ka ce mata miqe ba. Idan gashin
kanka ya fara zagwanyewa, ba za ka ce masa daina
ba. Idan tsufa ya doso, ba za ka ce masa dakata ba.
Duk umarnin Allah (swt) suke bi ba naka ba.

71
Tunaninka Kamanninka
Zuciyarka kaxai kake da ikon sarrafawa, kamar
yadda na ce a can baya: ita ma a tunani kaxai,
amma ba a rayuwarta ba. Akwai darasi babba a
nan ga masu tunani da zurfin nazari.

Watau, ashe duk jikinka musulmi ne, kodayake ka


iya zama kafiri ta wajen tunaninka. Kafirci kuwa
salo-salo ne. Ka iya kafircewa kanka ta wajen cire
suturar da aka haifeka da ita, idan ka zavi yin
mummunan tunani da aikata shi. Ko ka rufawa
kanka asirin da aka halicceka da shi ta wajen
kyakkyawan tunani da adance shi, yadda za ka ci
gaba da kasancewa yadda kake tun asali.

Xan-Adam ba zai iya fita daga wahala ta hanyar


tsiwa da zamba ba, balle kuma ta cuta ko sata ko
hassada. Amma idan ya yi qoqari ya shiga neman
rufin asirin kansa, to, ba shakka, zai iya sabunta
kansa ya koma cikin halittarsa ta ainihi.

Daga lokacin da ya fara tsarkake zuciyarsa, sai ka


ga ya fara daina zargar wasu da cewar sune suka
jawo masa wahalarsa. Sai ka ga ya fara jingine
nadamarsa da sadudarsa cikin halayyar wahalar da
tunaninsa ya nannaxa masa. In kuma macucin
wasu ne, sai ya fahimci zalunci ba maslaharsa ba
ne. Ko menene munin halayensa; ko mecece

72
Wahala da Wadata
masifar halayyarsa, mutum zai iya sake tunani ya
canja su. Wanda ya yi wannan, nan take zai farka
ya fara gina kansa izuwa mutum mai imani, adali
mai mutumci kuma qwaqqwara a tunaninsa da
halayensa. Nan take zai fara amfani da Halayyarsa
wajen bincikar kansa da ci-gaba da gyara kansa.
Nan take zai zama mutumin kansa, mai qoqarin
inganta kansa. Mai farin tunani gameda rayuwarsa
da halayyarsa. Ba abinda ba zai iya ba na alhairi, in
ya sa kansa wajen yinsu; kuma cikin lokaci ya ga
sakamakon alhairin.

Doka, ba ruxami ba, ita take tafiyar da komai a


Sararin da Allah (swt) Ya halitta. Haka Adalci, ba
Zalunci ba, shi ne ruhin rayuwa. Aikata daidai, ba
Mugunta da Ha’inci ba, shi ne yake haifarda
dangantaka ta-gari, ya kuma samar da mutum a
cikin al’umma tabbatacciya. Ashe kuwa tilas ne
mutum ya gyara kansa in har yana son ya haxe da
tsarkakakken sararin da Allah (swt) Ya halitta,
domin wannan shi ne mataki na farko a cimma
inganta. Tareda Allah ba Wahala, ba Talauci, balle
Tsiya. Ba Ha’inci, ba Mugunta, balle Zalunci.
Yawancin wahalu sharrukan qullin zuci ne. Zuciya
mai tsarki ba ta jinsu balle ganinsu.

Saboda haka, wanda tunaninsa ya kauce kyawawan

73
Tunaninka Kamanninka
alamun Allah (swt) shi ne ya fita daga tsarin
rayuwa mai wadata, ya shiga rayuwa mai wahala.
Amma duk wanda ya gyara kansa ta hanyar
kyautata tunaninsa gameda kansa, da jama’a, da
sauran abubuwa, to zai ga cewar su ma jama’ar da
sauran abubuwan sun gyara tunaninsu da
al’amuransu gameda shi. An ce; “Alhairi danqo
ne, ba ya faxuwa qasa banza”. To, ka yi wa kanka
alhairi, ka fita daga tunanin nadama don ka rasa
wani abu; ka tashi tsaye wajen gyara al’amarinka
kafin wahala ta ci qarfin tunaninka, ko kafin
tunaninka ya dulmiye cikin wahala. Wannan ita ce
gaskiya wadda ta kan gagari musu, ga mai nazari
da tunani, wanda kuma ya san muhimmancin
kansa yake kishin kansa.

Muhimmin darasi a nan shi ne, mu san yadda za


mu fassara wahala da yadda ta shafemu. Idan ka
gina wadatar zuci ta hanyar tunaninka, to ko kai
Gyartai ne, rayuwarka mai ni’ima ce. Sai ka ga
kana alfahari da sana’arka, kana yin abubuwan da
za su ingantata, har sai ka kai matsayin da wasu za
su yi mamaki. In kai direban wani ne, wataran kai
ma sai an tuqa ka. In kai Lebura ne, wataran sai ka
xau wasu wannan aikin, ko da a matsayin Helman
ne. In kai mawaqin qauye ne, wata ran sai an sayi
fayafayenka a birni. In kai yaron makanike ne, ko

74
Wahala da Wadata
na mai-kanti, wataran sai ka yi shagon kanka. In
kai talaka ne a lungu, to nemi wata sana’a da za ka
iya yi, ko mai qanqantarta ka kuma himmatu a
kanta, ko da ta faskare ce, ko sayar da ciyawa.
Wataran sai ka yi mamaki, muddin dai ba ka
wulakantata, ka watsar da ita ba. Duk mai sana’a
komai qasqantarta, ya fi mara sana’a komai faxin
ransa. Amma in ka shagala cikin nadama, to ka
shigarda kanka cikin wahala mara magani. Muddin
dai ka daure ka canja tunaninka cikin nagarta, ka
kuma fassara rayuwarka da jin daxinka yadda suka
dace da kai, ka kuma godewa Allah (swt) sauran
baiwoyin da Ya yi maka, ka kuma yi yunqurin
amfani da su, to, ko badaxe ko bajima, duniya za ta
tallafa maka da yardar Mai Iko da ita. Kada ka
fidda ran fita daga halayyar qunci izuwa ta wadata,
musammam ma a zuciyarka. Lallai ka tashi tsaye
kan sana’arka, ka kuma dogara da Allah wajen
nasararka. Mara sana'a shi ya yi hasara.

Amma duk wanda ya xau al’adar auna rayuwarsa


da ta wasu, ya shiga qangin wahala. Wanda ya
tsaida matsayinsa a gefen na wasu, ba don ya koya
ko ya inganta kansa ba, ya shiga dabaibayin
rayuwa. Wanda ya rena kansa da qwazonsa da
mutumcinsa da isarsa, don ba shi da abin duniya, to
ya fijircewa hanyar arzurta matsayinsa. Wanda ya

75
Tunaninka Kamanninka
bar kansa cikin tunanin wahala ya shigarda kansa
kurkukun rayuwa. Wanda yaqi nema, ko koyon
sana’ar yi, shi ya cuci kansa, kuma shi ne
wahallale, wulaqantacce. Wanda ya ce bara ko
roqo sune sana’arsa, to haka zai kasance a
wulaqance. Kaicon wanda kuma ya ce savon Allah
ne sana’arsa ko sana’arta. Ba hasarrare irin
wannan. Mai qwazon fafutuka da imani da rashin
girman kai, shi ke cin riba. Shi ke iya maganin
wahala. Kuma, gwada ka gani.

Da dukiya da muqami, ba sune kaxai ma’aunan


xan-Adam ba, sai dai a al’ummar banza. Halin
mutum da xawainiyarsa a kan al’amuran jama’a a
qauyensu ko a lungunsu, da qoqarin inganta kansa,
sune manyan ma’aunai a al’umma ta-gari. Duk
al’umar da ba ta sha’awar mai gaskiya, don ba shi
da abin bayarwa; ba ta qaunar mai aiki tuquru don
canja matsayinsa; ba ta son taimakon mai qoqari,
sai malalci; ba ta tafawa gwani sai masu ganganci
da rayuwarsu, ko ma macutansu; ba ta sha’awar
masu mutumci sai marasa kunya; ba ta tausayin
abin tausayi sai qyashin masu qoqari; to wannan
al’umma ta shiga uku ta lalace. Kaiconta! Ba ta da
shugabanni na-gari. A irin wannan al’umma ba
wanda ya isa ya faxa a ji shi, ballantana a bi
umarninsa. A irin wannan al’umma talauci yake

76
Wahala da Wadata
kanta, ka ga kowa da komai sai lalacewa suke yi.

A al’uma ta-gari, wadda ta san abinda take yi, da


abinda ya dameta, ba a ganin mutum da kandiri,
nan da nan a ce Liman ne. Ba a ganin Liman nan
da nan a ce na Allah ne. Ba a ganin mai kuxi a ce
mai arziki ne. Ba a ganin mutum nan da nan a bi
shi. Ba a ganin talaka a qyame shi. Ba a ganin
marar lafiya a guje shi. Haka ba a ganin sarki nan
take a faxi a gaishe shi. Dukkaninsu, sai an auna
halayensu da daviunsu tukuna, an kuma fahimci
abinda ya dace a yi masu. Ba duk mai rawani yake
sarki ba. Ba kuma duk mai-sarauta yake mulki ba.
Ba duk talaka ne matsiyaci ba. Ba kuma duk mai
riqe da carbi ne na Allah, ko yake wuridi ba. A
wannan tsari kuma, ba duk abinda mutum ya ce
wahala ne, ya ke kasancewa wahalarba. Ko
gajiyayye, in ya yi tsaf, zai iya sarrafa gajiyawar,
ba ta hanyar bara ba, ya inganta rayuwarsa, ya
kuma samarwa kansa wani jin daxi da alfahari
daidai shi. Bincika a hankali ka kuma yi nazari,
saboda Allah.

Masu zaton suna cikin wahala, lallai ne su san


cewar ba duk wahala ce take kanta har abada ba,
sai in ba a tunkareta da tunani nagartacce da kuma
jarumta da dauriya da fafutuka da sadaukarwa ba.

77
Tunaninka Kamanninka

78
Wahala da Wadata

79
Tunaninka Kamanninka

Hali
da Halayya
“Hali nagari Halayyar ni’ima

M utane sukan zaci za su iya voye


tunaninsu, amma a zahiri ba za su iya ba, domin
waxannan TUNANI su ke jirkita su zama HALI;
kuma halin, shi yake haifarda HALAYYAR mutum.

Misali: Susutaccen tunani, shi ke jirkitar da Halin


mutum ya zama sususu har sai Halayyarsa ta zama
tamkar ta dabba. A wannan halayya, haka sauran
jama’a za su xau mutum tamkar dabbar har sai ya
canja halinsa ta hanyar canja tunaninsa.

80
Hali da Halayya
Mutumin da bai tace tunaninsa kafin ya ambaci
ra’ayinsa ba, yakan iya faxar shirme, kuma jama’a
su xauke shi mashirmaci, har sai ya gyara
maganarsa ta hanyar tace tunaninsa. Halayyar da ya
sa kansa ciki sai ta ba shi sigar wawa, ko gavo, ko
ma marar hankali ga waxanda basu san shi ba, har
sai ya gyara maganarsa ta hanyar gyara tunaninsa.
Amma ga waxanda suka san shi, sai mamaki ya
kama su tareda tunanin, ‘Me ya sami wane ne?’

** Haka tunanin Tsoro, ko na Shakku, ko na


Fargaba, suke sa mutum ya zama matsoraci, ko
mara tsaida shawara, ko mara qarfin hali. Su kuma
ke sa a gama da shi, ko a raina shi, ko a yi watsi da
shi. Duk waxannan suke sa mutum ya yi biris da
abubuwan da za su iya maishe shi cikakken
mutum, su saka shi cikin halayyar lalacewa da
dogaro a kan wasu. Duk Azzalumi Matsoraci ne.

** Tunanin Lalaci, shi ke sa mutum ya zama


malalaci, wanda ke jefa shi cikin halayyar qazamta,
rashin aiki, bara, riqo, har ma da rashin gaskiya,
koma sata. Malalaci ba ya newarsa kansa alhairin
rayuwa. Sai ka ga mutum yana ta lalacewa.

** Tunanin Qiyayya da na la’antar wasu, suke sa


mutum ya zama mai halin qeta, yawan zagi da

81
Tunaninka Kamanninka
yawan faxa. Waxannan illoli su kuma ke jefa shi
cikin halayyar watsewa da rashin masoya.

** Tunanin Son-kai, shi ke sa halin mutum ya


zama mai-qwaxayi, marowaci, mara tausayi ko na
mahandami. Wannan hali shi ke jefa mutum cikin
halayyar rashin mutumci.

** Tunanin Hassada, shi ke sa mutum cikin halin


baqin ciki, annamimanci, qulle-qullen sharri, fushi
da jafa’i. Wannan hali shi ke jefa mutum cikin
halayyar tsiya, talauci da rashin madafa ko
makoma. A kullum a cikin baqin-ciki da damuwa
yake, saboda hassadarsa ta rufe hukuncin Allah.

** Amma, mutumin da tunaninsa na alheri ne, toh,


ba shakka shi ne mai kyakkyawan hali, wanda zai
haskaka halayyarsa. Wannan halayya mai haske da
ni’ima, ita ce za ta maishe shi mutum mai qwazo,
hikima, dauriya da son jama’a; kyauta, kwanciyar
rai da wadatar-zuci -har ma da tsoron Allah.
Wannan mutum shi ne mai kulliyar arziki, mai
cikakken rufin asirin duniya da na lahira.

** Mutumin da ba ruwansa da neman hana-wani,


ba haxama, ba nufaqa, ba yawan qarya ko yawan
rantsuwa, ba ganin qyashi, ba sharri balle qulli a

82
Hali da Halayya
zuciyarsa. Wannan mutum shi ne mai cikakken
imani; shi ne wanda ya yi daidai ya kuma dace da
Sararin da Allah (swt) Ya halitta cikin tsarki da
ni’ima. Tunani irin wannan shi ne ke sa halin
nagarta, wadda yake mai da mutum mai qwazo da
kwanciyar hankali a xaukacin rayuwarsa.
Albarkarsa kuma ta bi har zuri’arsa. Irin wannan
mutum, ba shakka shi ne abin sha’awa da koyi.

** Tunanin Jarunta kuma, shi ke haifarda qarfin


hali, ya sa halayyar mutum ta zama ta fafutuka da
dogaro da kansa, tareda jin wata iska mai huro
‘yanci. Wannan mutum shi ne kaxai zai iya yin
gwagwarmaya da fafutukar da za su kawo xinbun
alhairi tareda shi. Mutane jarumai suke iya
shugabanci da mulki cikin adalci domin tuni sun
kau da mutanen banza daga gefensu, waxanda za
su ingiza su hanyar zalunci da kama-karya don su
kare matsayinsu ta wajen lahanta jama’a. Adalci ba
shi ga rago ko matsoraci.

** Tunanin Jin-qarfin Jiki, shi ne ke kawo halin


tsabta da son aiki; waxanda su kuma suke sa
mutum ya zama lafiyayye, sannan kuma halayyarsa
ta zama ta alfahari da gamsuwa da kai.

** Tunanin Kirkin-zuci yake haifarda halin kirki,

83
Tunaninka Kamanninka
da mutuntaka da haquri. Mutum mai tunani irin
wannan, shi yake cikin halayyar soyayya da zaman
lafiya. Shi ne wanda zai tsinci dukkanin alhairansa
a duniya da kuma lahira.

**Tunanin aikata Gaskiya, shi ke sa mutum ya


zama mai gaskiya da riqon amana, waxanda ke
haifarda halayyar kwarjini, farin-jini da kuma
shugabanci, ko da a cikin abokai ne. Mutane irin
waxannan sune abin dogoro, abin bi. Idan suka yi
magana ko suka faxi ra’ayi, lallai ne sauran jama’a
su saurara, don sun san ba wasa ko annamimanci a
cikin maganarsu. Ku dubi dai Muhammad (saw),
da sauran annabawa a misali. Da maqaryata ne da
ba a bi su ba. Da ba inda Islam za shi.

** Tunanin Sanin Yakamata, shi ne yake sa


mutum ya zama kimtsattse mai xa’a, waxanda su
kuma suke haifarda halayyar zaman lafiya da
zumunci da kowa, tallafar juna da gina iyali ko
al’umma a kan tafarki mai kyau. Mai irin wannan
tunani shi ne maciyin nasara a kowanne hali.

Duk irin tunanin da mutum ya maqalewa, mai


kyau ko mai muni, ba zai kasa haifarda
sakamakonsa a cikin Hali da Halayyar mutumin
ba. Halayen mutane da yawa, su ne jumullar
halayen al’umma; kuma yadda sakamakon halin
84
Hali da Halayya
mutum zai tadda shi, haka sakamakon halin
al’umma zai tararda ita.

Idan kowa ya gyara Gidansa, to Unguwa ta gyaru.


Idan Unguwanni suka gyaru, to Gari ya gyaru. Idan
Garuruwa suka gyaru, to Qasa ta gyaru. Wannan
abu haka yake a kan kowacce matsala. Daga
ingancin Mai-gida da ‘ya’yansa, sai Qasa gaba
xaya ta inganta. Idan daga cikin kowanne gida, ko
a cikin kowanne iyali aka sami Mai-Arziki guda
xaya, to Qasa ta arzurta.

Don haka, kada mutum ya ga kamar halinsa shi


kaxai yake shafa. Kada mutum ya yi zaton shi
kaxai ba zai iya yin komai ba. Haka, kada al’umma
ta xauka cewar talauci da quntata, ko arziki da
yalwa, na wasu qalilan ne a cikinta ba nata ne gaba
xaya ba. Kada ‘yan unguwa su xauka cewar abinda
ya shafi maqwabci bai shafesu ba. A qididdigar
halayyar jama’a, ko Hausawa ma suka ce: “wake
xaya vata gari”. Ashe kishiyar haka ma gaskiya ce.
Mai kyau xaya sai ya haskaka munana da yawa.
Duk halayen mutum sa iya shafar wasu.

Kodayake mutum ba zai iya zavar halayyarsa


tawwali ba, amma zai iya zavar irin tunaninsa
tawwali, har sai halayyarsa ta wanzu daga halin da

85
Tunaninka Kamanninka
wannan tunanin ya haifar. Wato daga TUNANI akan
je ga HALI; daga Hali kuma ake qaddama cikin
HALAYYA. Haka za ka taho zuwa ga Halayyarka;
kuma ta wannan hanya, za ka koma izuwa
tunaninka.

Mutum ya daina qazamin tunaninsa, na-da-nan ya


ga duniya ta qarbe shi cikin gaggawa da hannayen
taimako. Mutum ya daina hassada, yanzu ya ga
arziki ya doso shi. Mutum ya daina tunanin cuta da
lalaci in yana son jikinsa da lafiya. Mutum ya buxe
zuciyarsa ga tunanin alheri, in yana son ya kori
sharri, xaixaicewa da kunya. Mutum ya zama
jarumi, yanzu ya ga an ba shi hanya. Mutum ya
zama mai tsabta, yanzu ya ga soyayya. Duk abinda
ka zava, shi za ka tarar; komai ya rage naka.

Duniya ita ce filin rawarka. Idan ka zavi kixanka


daidai, sai rawarka ta qayatar: ka ji daxi, a kuma yi
maka tafi.

86
Hali da Halayya

87
5
Tunaninka Kamanninka

Tunani da Lafiya
“Jiki baran Zuciya”

B a shakka, duk wanda ya san, ya kuma


yarda cewar, “Jiki baran Zuciya ne”, to kuwa, zai
iya danganta tunaninsa da lafiyarsa, kamar yadda
yake danganta tunaninsa da Halayyarsa. Idan
mutum ya yi tunanin kirki, sai jikinsa ya bazu da
qyallin yarunta da lafiya. Idan mutun ya qulla
tunanin sharri, sai jikinsa ya yanqwane cikin cuta
da ruvunta. Kamar yadda tsiya takan zama
halayyar mutum mai tunanin hassada, haka lafiya
da cuta duk halayya ne dake da tushensu daga
tunani da halayen mutum.

88
Tunani da Lafiya
Tsoron mutuwa da yawan tarradinta, sukan gayyoto
saurin tsufa, ko su qarasa marar lafiya nan da nan,
kamar yadda qarfin zuci yake riqe samartaka, ya
kuma warkarda marar lafiya cikin gaggawa. Wani,
sai mu ji an ce, ‘Ayya! ai ya karaya’; wani kuma
mu ji an ce: ‘Kai! wane da karfin hali yake; har
yanzu yana nan’. Mutanen da suka fi tsoron cuta,
sun fi saurin kamuwa da ita domin tunanin tsoronta
tuni ya tsiraice jikin ya kuma buxe qofofin da cutar
za ta shige shi. Masu aiki da marasa lafiya a asibiti,
da masu jiyyar marasa lafiya, misali, ba su kamuwa
da cutar majiyatan, in ba ta ganganci ko haxari ba,
domin ba sa tsoronta, kuma ba ta cikin tunaninsu.
Tunaninsu na alhairi da tausayi da son taimakawa,
sune suke kare su daga xaukar cutar.

Yayin da mutum yake yin mummunan tunani,


jikinsa yakan canja, jininsa kuma ya gurvata,
saboda irin umarnin da suke samu daga zuciyarsa
mummuna ne. Amma idan umarnin zuci ga jiki mai
kyau ne, to, haka ba shakka, jikin da kuma jinin
zasu kasance. Zuciyar da ta zama juji, haka jiki zai
ruve. Zuciyar da ta zama lambu, haka jikin zai yi
ni’ima. Watau, tunani shi ne famfon rayuwa:

Kwanto Ruwa garai-garai ka ga lafiya.


Kwanto kwatami ka ga cuta.

89
Tunaninka Kamanninka
Canjin abinci ba zai canja lafiya ba, in har tunani
bai canja ba. Sai mutum ya yi tunanin lafiyar
tukuna, sannan zai iya cin abincin da zai dace da
jikinsa. Tunanin tsabta shi ke sa a yi wanka a gyara
jiki. Waliyin da ba ya wanka, ba waliyi bane,
qazami ne kawai. An ce: Tsabta, na daga bin
Allah. Matsabtaci tuni ya sha maganin yawancin
cutaka. Babban darasinmu har zuwa nan shi ne:
Idan kana son gyara lafiyarka, toh, kare zuciyarka.
Idan kana son ka sabunta jikinka, toh, adance
zuciyarka ta hanyar tunani tsabtatacce, wanda ba
zai muzguna maka ko wasu ba. Ba sharri ga lafiya
irin baqaqen tunani.

Tunanin hassada, ganin-qyashi, rashin mutunci da


fushi, sukan kwavewa jiki lafiyarsa da martabarsa,
a wannan lokacin da bayansa. Turvunanniyar
fuska ba haka kawai ake ganinta ba; tana zuwa ne
daga turvunanniyar zuciya. Hausawa ma sukan ce,
“Labarin zuciya a tambayi fuska”.

Haka kuma, mutumin da yake a turvune a zuci


yake da saurin tsufa; amma mutumin da yake a
haskake a zuci yake riqe samartakarsa har zuwa
lokaci mai tsawo. Sai ka ga yaro ya tsufa nan-da-
nan, amma ka ga mai shekaru da yawa da fuskar
samari. Haka tunanin tsufa, ko yalwata al’adun

90
Tunani da Lafiya
tsofaffi, ko son girma, ko yawan karvarsa; yawan
taqama da sa Alkyabba, sukan fyade saurayi, nan
da nan ka ga ya tsofe. Dubi samari da suke karvar
sarauta ka gani. Kamar dai yadda yawan sunkoyo,
ko tafiya a sunkuye suke sa doro, ko da a kafaxar
yaro ce. Waxansu daga al’adunsu suke kamuwa da
cuta, ko kamanninsu su canja. Idan mutum bai
damu kansa ba, ba zai ajiye mummunan tunani a
zuciyarsa ba. Mutumin da bai xauki buri
matsananci ba, ba zai ga tsananta ba. Irin
waxannan mutane suke cin ribar rayuwarsu, su
kuma kiwaci lafiyarsu da jikinsu ta hanyar
kyawawan tunaninsu. Duk inda ka gansu sai ka yi
sha’awarsu saboda haibarsu, wadda ta tsiro tun
daga zuciyarsu har zuwa fuskarsu.

Yadda Iska da hasken Rana ba za su shigo xakin da


aka qulle tagogi da qofofinsa ba, haka farin-ciki da
kwanciyar hankali ba za su shiga zuciyar da aka
rufe ba. Rufaffar zuciya kuwa, ba ta jin shawara, ba
ta kuma karvar alhairi. Yadda ta zama mara lafiya
cike da mummunan tunani da kaba’i, haka Halayya
ke qara mata rashin lafiya, har sai tunanin ya canja
izuwa mai haske sannan za ta sami wasila.

A fuskokin tsofaffi mun ga gurayen fata da suka


samu don yawan murmushi; mun ga kuma

91
Tunaninka Kamanninka
waxanda suka samu don yawan turvune fuskar. Ga
mutanen da suka yi rayuwar alheri, ta mutunci da
wadatar zuci, tsufa girbi ne, ko kuma sakamako ne
na alherin da suka shuka cike gamsuwa da
kyakkyawan zato. Su ne masu godiyar Allah (swt),
tamkar Rana ta taso Gabas ta faxi Yamma don
cika umarni.

Amma ga waxanda suka yi rayuwar banza, tsufa


horo ne na sharrin da suka aikata cike da nadama
da tararradi, tamkar varawon da aka kama. Wanda
ya tsufa cikin mutumci, zai mutu cikin haiba da
lafiyar zuci, ko da tsufan ya tava lafiyar jikinsa a
idanuwanmu. Wanda ya tsufa cikin nadama, zai
mutu cikinta, ko da jikinsa garau yake a
idanuwanmu. Wanda ya cimma lafiyar zuci da
kwanciyar hankali, shi ya cimma lafiyar jiki da
rayuwa abar misali. Kamanninka na qarshe sune
kamanninka har abada a idanuwan mutane.

Ba likita irin tunani, don shi ne zai wanke duk


wata cuta ta jiki. Ba wani abu mai kwantar da
hankali da ya fi kyaun hali wanda zai iya watsarda
duhun takaici da baqin-ciki. Rayuwa cikin
qazamin tunanin hassada, mugunta da qazafi,
rayuwa ce wadda ta fi kurkuku quntata. Amma
fatan alhairi ga kowa, yawan murmushi tun daga

92
Tunani da Lafiya
zuci, taimakon maqwabci da zuciya xaya, zatawa
kowa alhairi saboda Allah, suna daga imani, kuma
sune matattakalun shiga Aljanna tun daga duniya.
A Aljanna kuwa, ba a cuta, ba a kuma rayuwar
nadama. Mara lafiya, amma mai halayen kirki, ya fi
saurin warkewa, domin zatonsa a kansa mai kyau
ne. Wannan shi zai qarfafa jikin ya karvi maganin.

Idan ka ga mutum yana yawan fushi babu dalili, ko


ka ga mutum yana saurin tsufa babu dalili; to
binciki hassadarsa ko burinsa, ko al’adunsa. Da
yawan fushi da saurin tsufa cutuka ne na zuci,
kuma azabarsu tafi ta ciwon qaba. Gushewar imani
tana ga mai ciwon zuci; irinsu ne ke kashe kansu da
sun kai maqura; ko ciwon zuciyar ya kashesu.

Zuciyar da ba imani a cikinta, ita ce zuciyar


nadama, tarradi da fargaba, wadda da take angaza
jiki ga lalacewa cikin cutar da ba a san kanta ba; ta
kuma angazasu ga xaukar rayukansu. Ashe tunda
kyaun zuciya shi ne yake haifar da farin tunani, shi
kuma ya haifar da lafiyar jiki, ba wahalar danganta
imani da wadatar zuci da kuma lafiya. Mai imani
shi ke da madogara a kodayaushe.

Bala’i da hassadar mahassada; jidali da qiyayyar


maqiya; takaici cikin sharrin masharrata, duk haxe-

93
Tunaninka Kamanninka
haxe ne da za su iya quntata zuciyar mai fama da
su, su aza masa cutanni. Imani da kyaun zuciya ne
kaxai za su iya kawo masa caffa ya sami lafiya da
kwanciyar hankali. Mai imani, shi ne wanda ya
dogara da Allah (swt), yake kuma neman tsari
daga gareShi kaxai. Mai neman tsari fi-sabilillah
zai samu domin zuciyarsa a tsabtace take. Ba ya
sharri, ba ya mai da martani ga mai sharri. Allah
(swt) Ne madogarar Mai imani. Haqiqa, duk Mai
imani ya sami madogara tabbatacciya.

Mahassadan da maqiyan da masharratan sune za


su gaji bala’in da jidalin da kuma takaicin da suka
shuka, ko suna so ko ba sa so. Shaixan da baqaqen
tunani sune abokan hidimarsu, kuma a cikin zurfin
nadama da galabaita za su dawwama. Wannan
halayya kuma ta haifar masu da ciwon zuci. Shi
kuma ya halakasu. Takaici a kan takaici! Wannan
ko shakku babu.

Mai imani shi ya ci ribar lafiya domin ma’aunin


tunaninsa ingantacce ne. Mara imani shi ya yi
hasarar lafiya, domin kuwa mun san ma’aunin
tunaninsa gurvatacce ne.

94
Tunani da Lafiya

95
Tunaninka Kamanninka

Tunani
da Manufa
“Juji Rami ne kawai

z
har sai an zuba masa shara”.
“Gona daji ce kawai
har sai an dasa mata shuka”.

uciyar xan-Adam tamkar Miya ce


wadda za a iya yi mata shirin musammam don ta
yi garxi; ko kuma a barta ta yi tsami, amma dai za
a sami miya ta kowanne hali. Yadda mai dafa
miyar za ta gyara miyarta, ta sa kayan qanshi da
sauransu, ta kuma dafata a tsabtace don ta yi garxi
da kyaun gani a ido, haka mutum yakamata ya yi
wajen kyautata miyar zuciyarsa.
96
Tunani da Manufa
Yadda Manomi zai gyara gonarsa, ya kauda qayoyi
da ciyayin banza, ya kuma zuba mata taki mai kyau
don ta tsiradda ni’imominta, haka mutum yakamata
ya kyautata gonar zuciyarsa, ya kauda tunanin
banza don ya ci amfanin rayuwarsa. Ta yin hakane
kaxai mutum zai iya sanin shi ne mai ikon gyara da
adana zuciyarsa, watau tunaninsa, duk sa’inda yake
so; shi ne kuma mai gudanar da rayuwarsa yadda ta
dace da shi a kowanne hali. Ba wanda zai iya shiga
ya yi wa mutum wannan gyara, sai shi kansa. Wa
ya fi shi qaunar kansa? Wa ya fika qaunar kanka?

Kamar yadda Mai miya ta gyara miyarta, ko Mai


gonar ya gyara gonarsa don cimma biyan
bukatunsu (garxin miya da albarkar gona), haka ya
zama wajibi kowanne tunani ya maqalu da hujja ko
bukata, in dai ana son samun sakamako mai ma’ana
da martaba. Tunani ba tabbatacciyar manufa
tamkar yawon mahaukaci ne, sai inda iskoki suka
kai shi. Haka, tunani ba sanannar manufa, tamkar
shiga kwale-kwale ne ba sandar tuqi, sai inda igiyar
ruwa ta fizgeka. Tunanin da ba shi da manufa,
daidai yake da aikin da ba shi da sakamako.
Tunanin da ba shi da ma’ana, hanyar su xaya da
hauka. Haka manufar da ba ta da ma’ana daidai
take da jifan shaho. Haka, manufar da ba ta
ma’aunin iyaka da lokaci, shirme ce kawai.

97
Tunaninka Kamanninka
Duk waxanda ba su da manufa mai ma’ana a
rayuwarsu, su ne cikin haxari, tsoro, ciwon zuciya
da rashin madafa, ko ma makoma. Waxannan
lahanoni alamu ne na kasalar zuciya, waxanda
sukan jefa mutum ga qarkon banza, rayuwar baqin
-ciki, da-nasani, takaici da wulaqanci.

Maci ribar rayuwa, shi ne wanda ya qudiri wata


manufa daidai shi, ya kuma yunqura wajen
fafutukar cimmata, sane da mahimmancinta da
ma’anarta a gareshi. Lallai duk mai manufa, ya
kimtsa mata gurbi cikin tunaninsa, ko da ta burin
tsabtace zuciya ne, ko kuma ta neman wani ado na
rayuwa. Ko ta mecece, lallai ya yi saitin qarfin
tunaninsa a kan cimmata, kada ya bar nutsuwar
tunaninsa ya bauxe cikin kokwanto, wasi-wasi,
shakkun-kai da sauran irin waxannan raunanan
tunani. Tsananta tunani a kan cimma buri shi ne
shishshiken fafutuka. Ko da ba a sami biyan
bukata bayan gwaji biyu ko uku ba, to ribar da aka
samu ta fafufutukar -ilmi da sanin jama’a da kuma
dakewar zucin- su ma nasarori ne; kuma su ne
ababan alfahari, makaman tunkarar gaba da qarfin-
zuci don samun cikakkiyar nasara. Kamar yadda
ake cewa: ‘Alheri danqo ne, ba ya faxuwa qasa
banza’, to haka ita ma fafutuka wadda qarfin
tunani da qwazo ya gabatar, ba ta kasancewa a

98
Tunani da Manufa
banza. Duk sa’inda ka sake shiryawa sai ka xauka.

Mutanen da ba za su iya jure tararradin tunkarar


muhimmiyar manufa ba, to yakamata su maishe da
tunaninsu wajen alfahari da gaskiyarsu, iya aiki da
riqon amanarsu, ko menene qasqancin matsayin
rayuwarsu. Duk wanda ya qudiri buri mai ma’ana
saboda Allah, ya kuma yi fafutukarsa saboda Allah
(watau, da zuciya xaya mai qarfi), toh ba shi da
hasara ko kaxan. An ce, “wani hanin baiwa ne”, toh
ba shakka a sannu mai fafutuka irin wannan zai
fahimci dalilin rashin nasararsa a yadda ya zaceta,
ya kuma gamsu; sannan a sannu zai ga sabuwar
nasararsa a yadda ta kamace shi ta hanyoyi dabam
dabam, ya kuma gamsu; in dai shi mai nazari ne.

Lallai mu fara sani da yardar cewa, ba dukkaninmu


ne za mu iya zama Gwamnoni ko Ministoci, ko
Sarakuna ko Masu-kuxi ko Shaihunnan Malamai,
ko auren waxanda muka fi so ba. Amma
dukkaninmu ma iya kwatanta alfaharinmu a cikin
‘yan abubuwan da za mu iya zama, ko samu. A
yawancin lokatai, za mu iya tararda gamsuwar
rayuwa ta aikata abubuwan da suka kamata, tamkar
mun taka tsanin burinmu. Ta irin wannan tunani ne
kaxai, da rashin raina-kai, wasunmu za su iya
tattara hankulansu, su kuma gyara tunaninsu don

99
Tunaninka Kamanninka
fuskantar gaba, sannu da sannu, da kuma qwazo da
alfahari fiye da da. Ma’ana, kada mutum ya sake
ya bar tunaninsa cikin matsayin qasqanci da rashin
qaqa-na-ka-yi. Ko da zuciyar da ta fi kowacce
rauni, muddin dai ta fahimci cewar, qarfin zuci zai
iya ginuwa a hankali, kuma ta yunqura wajen yin
haka, cikin juriya da haquri, toh, a hankali-a-
hankali ba shakka, Allah Zai tallafa har sai ta sami
qarfinta, ta kuma cimma burinta daidai ita.

Kamar dai mai karaya ne da aka xora. A sannu-da-


sannu zai fara yunqurawa, yana tattakawa har sai
ya miqe da qwazonsa. Haka kuma zai ci gaba da
xingisawa, yana tattakewa har sai qafar ta samu
sosai. In ya yar da sandarsa ya kwanta, sai qafar ta
ruve. Haka burin da aka watsar yake watsewa. An
ce: “Da rashin-gwaji (ko tayi) a kan bar araha.”
Kuma, masu hikimar magana sun ce “Kashi 80 na
nasara zuwa gurin ne kawai”. Gwada ka gani.

Duk wanda ya watsar da rashin alqibla, lalaci da


ragwanci; ya fara yin tunani da manufa mai tsabta,
toh ya shiga sahun jaruman da suka san cewar,
Wata gazawar a yau, matattakala ce ta cimma buri
a gaba. Ashe kuwa wani hanin mabuxar ilmi ce a
gareka, domin ka yi la’akari da kura-kuren da suka
kawo maka cikas, ka sake xamara don gaba;

100
Tunani da Manufa
muddin dai ka yi tunani kuma ka amince
manufarka ta alheri ce, kuma daidai kai. Komai ya
faru a qarshen fafutukarka, ka tuna cewar:

Nasara tana ga mutanen da suka sarrafa halayyarsu


don ta amfanesu; suke yin qwararan tunani don
tsarinsu; suke gwaji ba tsoro; kuma suke tunkarar
manufofinsu cikin hikima da kyakkyawan zato.

Daga lokacin da mutum ya qudiri manufarsa, to sai


ya tsara tunaninsa a miqe don cimmata, ba duban
dama balle hagu, sai dai don kawai ya kauda
qayoyin hanya. Lallai mutum ya girgije shakku da
tsoro domin sune suke gurvata turbar nasara, suke
jawo hasara. Qwazon aikata abu, fure ne na sanin
za a iya aikatawa. Shakku da tsoro da jin rashin-isa
su ne maqiyan wannan ilmi. Duk wanda bai yaqe
su ba, toh kuwa za su gama da shi a kowanne
mataki. Amma wanda ya gama da su, ya gama da
gazawa, yá kuma doshi fuskar nasara.

Tunanin da ya abokanci manufa ba tareda tsoro ba,


ya zama barden buri. Haka, duk wanda ya san
wannan, toh a shirye yake ya inganta matsayinsa,
domin yá mallaki qwaqwalwarsa, yá kuma laqanci
tasawirar da za ta kai shi ga rayuwa mai kyau da
ma’ana.

101
Tunaninka Kamanninka
Ashe za mu iya cewar kusan, ko ma duk, abinda
mutum ya iya samu a rayuwarsa, sakamako ne na
irin bukatunsa da tunaninsa a kansu, wanda Allah
(swt) Ya duba Ya bayar da abin ta hanyar auna
buri, fafutuka da amsa addu’a. Haka yawancin
hasara, ko rashin nasara, suna daga nauyin da
mutum ya tilasta xaukarwa kansa, illa kaxai
waxanda aka san qaddara ne. Qarfin halin mutum
da lalacinsa; tsarkinsa da gurvatarsa, duk nasa ne,
ba na wani ba, kuma shi ke jawowa kansa su da
kansa, kuma shi ne kaxai zai iya canjasu ba wani
ba. In abubuwa suka yi tsamari, Halayyarsa tasa
ce, ba ta wani ba. Haka nadarmarsa tasa ce ba ta
wani ba; haka bushasharsa. Yadda yake tunani,
haka yake; yadda kuma ya ci-gaba da tunani, haka
zai kasance. Wasu na kusa da shi, sai su xanxana
zaqin nasararsa, ko su xanxana xacin hasararsa.

Mai qarfin hali ba zai iya taimakon rago,


razananne ba, sai ragon ya zama a shirye ya karvi
taimakon. Kuma duk da haka, shi ne (ragon) kaxai
zai iya maishe da kansa mai qarfin hali ta hanyar
qoqarin kansa da tsirarwa kansa irin qarfin halin
da ya yi sha’awa na wasu. Wanda yake zaton bai
isa ya samu ba; ko bai isa ya zama ba, toh, ya dubi
waxansu ya auna yaya aka yi su suka isa? Ya aka
yi suka samu? Ya aka yi suka zama? Menene

102
Tunani da Manufa
bambancinsa da su? Da irin wannan ma’auni ne
kaxai mutum zai iya auna kansa sosai don ya
tabbatarwa kansa wanene shi, mai kuma zai iya yi
ko samu ko zama? Da ya samo amsoshinsa daidai,
toh daga nan komai zai zama a fayyace a gareshi.

Daga nan zai san cewar shi ne kaxai zai iya canja
al’amarinsa, ya kuma ciyarda kansa gaba daidai
gwargwadon qarfinsa da kuma damar da yake da
ita. Amma ‘Dama’ aba ce wadda sai an nemeta ko
an qirqirota. Idan ba ka je gurin da ake yin abu ba,
ba za ka sami damar yinsa ba. Idan ba ka je gurin
da ake bayarwa ba, ba za ka karva ba. Wanda ya
zauna bai tashi ba, ba inda zashi. Wanda bai nema
ba, ba zai samu ba. Akwai azancin Larabawa da ke
cewa, “Mai nema yana tareda samu”. Ashe dama
tuni mun san sai ka nema zaka samu.

Wasu sukan ce: ‘Jamaa sukan sha wahala ne domin


wani na wahalarda su’. Ko kuma:‘Mutane bayi ne
domin wani ya bautarda su’. Saboda haka: ‘a tsani
mai wahalarda sun; a tsani mai bautarda sun’.
Amma kuma, za mu iya duba waxannan ta xaya
gefen: “Wani na wahalarda jama’a don sun yarda
su wahalallu ne’. Ko kuma: “Wani na bautarda
jama’a don sun yarda su bayi ne’. Saboda haka: ‘a
tsani wahalallun; a tsani bayin”.

103
Tunaninka Kamanninka
Hikimar wannan batu ita ce ta nuna yadda wasu
suka zubarda damarsu da ‘yancinsu, yadda ba za
su iya inganta matsayinsu ba. Hasarar, ba shakka,
tasu ce su ma, ba kaxai ta wanda suke zaton ya
dannesu ya hanasu sakat ba ce. Ba wanda Allah
(swt) Ya halitta banza, sai dai mutum ya maishe da
kansa banza. Duk rashin kuxinka ko galihunka, za
ka iya gina mutumcinka ta yin fafutuka daidai kai,
ka kuma ci nasara daidai kai. A qalla ka kasance
cikin masu neman na kansu, komai qanqantarsa.
Ta haka sai mutumcinka ya tsira, kai ma ka zama
cikin masu alfahari wadanda suka yi qwazon cetar
kansu da kansu. Gaba kuma ta fi baya yawa.

Ko da a gasar ciniki ko matsayi, ko zave; wanda


ya bari aka cuce shi da gangan yana gani bai yi
wani abu a kai ba, to ba shakka ya cuci kansa.
Haka a gasar rayuwa gaba xayanta. Wanda ya
zauna ya ce, “haka Allah Ya yi shi”, ya gama qulle
kansa daga qudirin manufa da fafutukar da za su
‘yantarda shi daga qangin rayuwarsa. Wannan
mutum ya yi hasara mai yawan gaske.

Da macucin da ya yi cuta don ba yadda za a yi da


shi. Da wanda aka cuta yana gani bai tavuka don
kare kansa ko hana ta nan gaba ba, dukkaninsu
kansu suke cuta. Da masu mulkin zalunci, sata,

104
Tunani da Manufa
dankwafe jama’a da rashin kunya; da kuma jama’ar
da suka sadudar da kansu ga waxannan azzalumai,
alhali suna da yadda za su yi, dukanninsu hasararru
ne; sai mu tsane su. Dukkaninsu junansu suke cuta;
sai mu tsane su. Tunani mai zurfi zai nuna mana
wofancin wanda ake cuta, da kuma izgilancin mai
cutarwar; sakacin wanda ake cuta, da kuma rashin
mutumcin mai cutar. Dukkaninsu suna bukatar
canja matsayinsu da tunaninsu ta yadda za su
amfani halayyarsu. Wanda ya kau da lalaci, da
tsoro da kwaxayi, ya fita daga matsayin mai
cutuwa. Haka wanda ya kau da son-rai, kwaxayi da
rashin kirki, ya fita daga sahun macuta.

Mutum ba zai iya inganta kansa ba, sai ya tashi ya


yi fafutuka ya inganta tunaninsa. Zai iya ci gaba da
kasancewa cikin talauci da muzanci idan ya qi
inganta tunaninsa, kuma ya qi xaukar damarsa. Sai
dai kuma shi Inganci, ba ya samuwa ba tareda an
sadaukar ba. Mutumin da ya nemi inganta kansa,
amma ba ya son ya sadaukar da wasu abubuwa,
nasara za ta kasance mai nisa daga gareshi. Wanda
ya kasa hana kansa don ribar gaba, ba zai iya
gudanarda abubuwan da yakamata ya yi waxanda
za su kai shi ga ingancin ba.

Dokokin halitta, ba sa taimakon mai son-kai, ko

105
Tunaninka Kamanninka
mara-gaskiya, ko kuma mamugunci; kodayake
wasu loton sai ka ga kamar ba haka bane saboda
tsarin abubuwan da ba sa canjawa. Amma, ba
shakka, masu gaskiya, riqon amana, alhairi da
qwazo, har abada ba sa tavewa. Riqe addini da son
Allah (swt), su ne maqasudin rayuwar alhairi da
buri nagari. Duk wanda ya rayu cikin yanayin zuci
mai kyau, ya kuma mai da hankalinsa ga
abubuwan kirki, toh kuwa zai iya cimma inganci
mayalwaci. Ranarsa ta yi qoli; watansa ya
haskaka; hankalinsa ya kwanta; imaninsa ya
qarfafa; matsayinsa ya girmama da albarka.

Samun biyan bukata kowacce iri ce, sakamako ne


na fafutuka, wadda ita kuma huda ce ta tunani. Ta
hanyar iya sarrafar da kai, qwazo, gaskiya da
kuma kyakkyawan nufi da manufa, mutum yake
inganta kansa. Haka, ta hanyar shashanci, lalaci,
kwaxayi, rashin gaskiya, da sauran gurvatattun
tunani, matsayin mutum yake qaskanta.

Duk wanda yake son cimma kaxan, toh, ya


sadaukar da kaxan. Wanda yake son cimma da
yawa, toh, ya sadaukar da yawa. Wanda yake son
ya riqe mutumcinsa da girmansa, toh, ya adanasu;
ya kuma ba wa wasu nasu. Kada ka dankwafar da
kanka, domin duniya ba azzalumar kowa ba ce.

106
Tunani da Manufa

Tsara manufarka daidai kai,


Yi saitin tunaninka da fafutukarka a kanta,
Gwada ka gani.
Ba ka san inda rabo yake ba.
Sake Gwadawa ka gani.
Ba ka san inda rabo yake ba!

107
Tunaninka Kamanninka

108
Wahalu da Masifu

Wahalu

s
da Masifu
“Allah ba azzalumin kowa bane”

au da yawa, masu ilmin Falsafa sukan


faxa mana cewar: ‘Wahalunmu ba wahalu bane a
haqiqa. Tunaninmu ne yake hidimar saqa su a
zuciyoyinmu, har sai wahalun sun sami gurbi a
cikin halayyar rayuwarmu’. Daga nan kuma sai mu
shiga nadamar rayuwa har wasu su kai maqurar da
ba dawowa. Watau, wahala, saqa ce ta zuci.

Kodayake mun xan tavo shigen wannan magana a


gurare a baya, amma mun san, ba shakka, magana
ce mai nauyin gaske da kuma wuyar fahimta. Ya za

109
Tunaninka Kamanninka
a yi a fassarawa matalauci ko kuma mai fama da
cuta ma’anar halayyarsu ta yadda ba za su ga
wahalunsu ba, ba kuma za su yi zargi a kansu ba?

Wannan magana yanzu ta sa ya zama tilas mu qara


zurfafa tunani, mu yi bincike mai zurfi a kan: ‘Wai
shin, mecece masifa da wahalarta? ‘Me’ (ko ‘wa’)
ke jawo ta? Ya za mu yi da ita?’ Haka kuma, shin
za mu iya binciken, ‘Me ya sa take samun wasu ta
bar wasu?’ Akwai waxanda kawai su ‘yan-gatan
duniya ne komai nasu lafiya lau; amma kuma wasu
wahalallunta, abubuwansu a watse? Ya tsarin
halittun wahala da bala’i suke? Wai ma shin, me
zai hana kowa da kowa su zama daidai, ba wanda
ya fi wani. Shin, Allah (swt) ne Yake aiko da
masifun da za su shigarda mutum ko jama’a cikin
wahalu -daga gare Shi kai tsaye zuwa ga waxanda
suka sama- ko kuwa? Duk waxannan tambayoyi
daidai ne a yi su domin a fahimci wasu abubuwa
iya gwargwado da hankali.

Duk da waxannan tambayoyi masu nauyi, mun san


cewar a duniyar zahiri yawancin abubuwa dama
can masu xaure kai ne, duk da ximbun imaninmu.
Amma, idan lallai muna son mu qarfafa imaninmu
ga Allah, kuma saboda Allah, to kuwa lallai ne mu
yi waxannan tambayoyi, mu kuma kori tsoron

110
Wahalu da Masifu
amsasu, cikin la’akari da cewar, ‘Allah ba
azzalumin kowa bane’, kodayake ba shakka, Shi ne
Mai Iko a kan komai da kowa xin.

Mun san, a tsarin dangantakar mutum da mutum,


wasu munanan abubuwa ba takaicin waxanda suka
sama kaxai bane. Misali: idan jarin babban xan-
Kasuwa ya karye, yawancin ‘yan-kasuwansa sukan
shiga matsala wadda za ta iya haifarda wahala, in
ba a tunkari al’amarin da hikima da gaggawa ba.
Shi kam tuni ya shiga. Haka mutuwar mai-gida.
Haka mun san wasu masifun sukan wanzarda
kokwanto ga zuciyoyin jama’a gameda adalcin
duniya, musammam ma idan suka sami mutanen
kirki, ko yara, ko waxanda a tunaninmu bai kamata
su samesu ba. Misalin ka ga mutumin kirki, watau
mutum mai amana, bin Allah, tausayi, qoqari da
qwazo, kyauta da sauqin-kai, haka kawai (ko a iya
saninmu, haka kawai) wani bala’i ya aukar masa,
nan take ya zama abin tausayi. Irin wannan takan
sa wasu su tambayi kansu: ‘ko zama mutumin kirki
yana da fa’ida in har har abu kaza zai iya samun
irin su wane Allah Na gani Bai kare masa ba?’.

‘Saboda me munanan abubuwa za su sami mutanen


kirki, ko waxanda ba su ci ba, ba su sha ba?’
Wannan tambaya ba ta gushewa a tareda mu

111
Tunaninka Kamanninka
kullum muka dubi abinda muke kira, ‘zaluncin’
duniya. Wasu sukan yi zaton cewar wasu ne suke
jawowa wasu bala’i, kamar yadda xa ke jawowa
ubansa zagi, ko yadda ganganci ke jawo haxari. A
wasu halayen, wannan haka yake, amma kuma
mun san, da so samu ne, watau dá duniya ba ta da
aibu a idanunmu, dá a zahirin lamari, bai kyautu
wani ya wahala ko ya shiga masifa don matsala ko
laifin wani ko gangancin wasu ba. Dá abubuwa, ko
ita kanta halitta, ba yadda muka sansu suke ba, dá
“wanda bai ji bari ba ne kaxai zai ji woho”, don
shi ne ya jawowa kansa. Dá kowa shi kaxai zai sha
wahala da masifar da shi kansa ya jawowa kansa.
Toh amma, a yawancin lokatai ba haka bane.

Toh, ya kenan za mu fassara duniya idan masifar


rayuwa ta sami mutumin kirki, ko al’ummar kirki?
Ko kuma, rahamar rayuwa ta lullube mutumin
banza, ko al’ummar banza? Don me idanun
mutumin kirki suka mace? Ya aka yi mota ta faxi
da liman? Ya xan sarki ya shiga layin matalauta?
Ya xan mai kuxi ya zama matsiyaci? Ya aka yi
wane mai kuxi, wane kuma mara su? Don me
wasu suka ci riba, amma wasu suka faxi, alhali
hajjarsu iri xaya a kasuwa xaya? Me ya sa cuta ta
kama wane, amma ta bar wane, alhali shigen
rayuwarsu xaya ne? Me ya sa mara imani ya yi

112
Wahalu da Masifu
galaba a kan mai imani? Me ya sa aka ci zalin su
wane ana gani ba a yi komai ba? Me ya sa aka
kama wani, amma aka saki wani? Ko kuma…,

Me ya sa muka ga Gobara ta qone gidan mutumin


kirki, ta halaka iyalinsa da dukiyarsa? Ya aka yi
mutumin banza ya arzurta da dukiya da lafiya,
komai nasa yake tafiya daidai? Ko kuwa mutumin
kirki shi ne wanda duniya ta zava ta yi masa
sakayyar alhairi ba tareda la’akari da ayyukansa da
xabi’unsa na banza ba; mutumin banza kuma
wanda ta wulakanta, ba tareda la’akari da
ayyukansa da xabi’unsa na kirki ba? Me ya sa
wasu abubuwa suke faruwa haka tamkar babu
adalci a rayuwa? Ko kuwa mu ne dai ba mu
fahimci halitta da rayuwa yadda Allah (swt) Ya
tsarosu ba, muke fassara abubuwa yadda son
ranmu ya raya mana; ko yadda mu ke zato?

Akwai mutanen da in masifa ko wahala ta bayyana


a garesu suke xauka cewar Allah (swt) ne Yake
horonsu da azaba saboda wasu kura-kure nasu.
Wannan matsala takan raunana imaninsu; kuma
takan sa su kalli Allah ta hanyoyin da ba su dace da
siffarSa ba, musammam idan suka lura Bai hori
wasu a kan waxannan dalilan ba sai su. Shin kuwa
yakamata mu bar tunaninmu da hikimomimmu a

113
Tunaninka Kamanninka
kan wannan kakkaifan siraxi mai ximbun haxari?

Wasu kuma, saboda halayyarsu ta miskinanci ko


gajiyawa, ko wata cuta, ko hasara, sukan tuhumi
imanin zuciyoyinsu, sannan su shigarda kansu
cikin takaici da zargi iri iri gameda wannan
halayya tasu. Sakamakon duk wannan ita ce
babbar nadamar rayuwa, wadda ita kuma a nata
juyin take haddasa irin nata wahalun. A haka, sai a
watsarda rayuwar xungum a shiga bara, ko sata, ko
dai wasu xabi’u waxanda ba zasu amfanawa kowa
ba, sai ma qara illoli ga al’umma gaba xayanta.

Da tsiya da talauci; da kuturta da makanta; ciwon


qaba da na sukari; haxari da mutuwar masoyi; duk
ababan qorafi ne ga masu fama da su. Wasu kuma
anazarce-nazarcensu na yadda abubuwa suke
wakana a wannan duniya tamu, sukan tambayi: Me
ya sa na yi hasara, amma su wane suka ci riba? Me
ya sa ba a amsa addu’ata ba, amma ga wasu
shagalallu can komai nasu daidai? Ga azzalumi,
macuci, varawo, marar kunya marar mutumci yana
ta bushasha da annashawa don jin daxin rayuwarsa
cikin wadata; amma ga mai adalci, mai gaskiya,
riqon amana da mutumci yana ta fankama cikin
rayuwar talauci, ko cuta. Ko rashin gaskiya da
rashin-kunya su ne a’ala, yin su hasara?

114
Wahalu da Masifu
Wasu masu imani sun yarda cewar wahalunsu da
hasarunsu jarrabawa ce daga Allah (swt), kuma
sakamakonsu yana gaba, watakila a lahira. Marasa
imani kuma sun xauka cewar dukiyarsu da jin
daxinsu alama ce babu Allah; in kuma akwai Shi,
toh, Bai damu da hanyar da ka zava a wajen
yalwata rayuwarka ba, komai muninta.

Amma masu la’akari sun san a qarshe, komai yana


da dalilinsa, a sarari ko a voye. Kuma, Allah (swt)
ba Ya xorawa Rai abinda ba za ta iya xauka ba.
Haka kuma ba Ya azawa mutum masifa don ba Ya
sonsa, ko don haka Yake sha’awa. Sha’awar
zalunci ba taSa ba ce, domin Shi Mai qaunar
dukkanin halittunSa ne. Haqiqa, babu zalunci a
cikin al’amuran Allah (swt). Masu ilmi da nazari
sun san Allah (swt) da Kimiyya Yake aiki, kuma
komai naSa a tsare yake, kuma a aune da lissafi.
Ilminsu da nazarinsu sun nuna masu abubuwa da
yawa, waxanda yawancinmu ba mu sani ba. Sun
san qalubalantar duniya tana daga cikin sirrin
rayuwa; kuma ita ce gishirinta. Amma sanin Allah
(swt) da yadda Yake ayyukansa, ilmi ne mai
wahalar fahimta ta wani gefen, mai kuma sauqin
gaske ta xaya gefen. Shiga cikin wannan ilmi sai an
daure an faxaxa zuciya da haquri. Allah (swt) Ya
yi mana jagora. Ameen. Bari na fara da wannan:

115
Tunaninka Kamanninka
Sigar sharri da alhairi tamkar shukar irannin
Ciyawa ce da ta Mangwaro. Sai ciyawar ta tsiro
nan da nan ta bar mangwaron. Amma bayan xan
lokaci, sai kuma ciyawar ta mace ta bar
mangwaron. Haka misalin mutanen banza da
mutanen kirki suke. Banzar ita ce ciyawar mara
dogon rai; kirkin kuma shi ne bishiyar magwaron
mai tsawon rayuwa har da furanni da ‘ya’ya. Haka
kuma dangantakar take tsakanin Qarya da
Gaskiya; tsakanin Zalunci da Adalci; tsakanin
Kafirci da Imani. Duk mai hankali da basira ya san
cewar akwai dalilai masu qarfin ma’ana na yadda
Allah (swt) Ya tsara komai.

Bayanan masifu da auna wahalun rayuwa a sikelin


azanci abune mai wuya, amma kuma tilas a yi, in
har muna son bin diddigin dalilan da suka sa
rayuwa take kasancewa haka ga mutane dabam
dabam. Tambayar da za mu yi a yadda muka taho
da zancenmu ita ce: Menene bayanin dalilan da
suka sa rayuwar jama’a take bambamta, wasu tasu
da muni, wasu kuma da kyau?

Bari mu yi nazari a kan waxannan bayanai uku,


mu ga ko za su iya gamsarda mu; watakila
xayansu, ko dukkanninsu, su ne dalilan da suka sa
muka zama dabam. Kafin na fara, Ina roqon a

116
Wahalu da Masifu
karanta a hankali a haqurce cikin tunani. Kada a yi
saurin rufewa qwaqwalwa hikimar rairayenta: An
ce: “Mahakurci, Mawadaci”. Saboda haka, sai a bi
ni a hankali; kada a yi saurin husata da irin wannan
azanci na masana abin, wanda zan yi amfani da shi
don nazari da neman dalilan da suka dace da
tambayoyinmu:

1.
TSARIN RAYUWAR
‘YAN-ADAM TAMKAR SAQAR FAIFAI CE:

Da ka dubi faifai, ko tabarma ko darduma, za


ka ga daga “cikin” faifan ga saqa nan kyakkyawa
gwanin sha’awa; kowanne zare, kowanne launi, ya
shiga xayan daidai, kuma gaba xayansu sun
haifarda tsarin saqa da launuka masu kyau da
qayatarwa ba kuskure. Amma juya “bayan” faifan
ka ga hargitsi da rashin tsari. Zararruka a tsinke, ko
a yanke, ko a qulle; wasu gajeru, wasu dogaye
cikin hargitsi ba tsari balle qayatarwa. Duk wannan
(watau, da “ciki” da “bayan” faifan), ba don wani
zare yafi wani ba, a a, sai dai don haka saqar ta
haifar. To haka, idan muka dubi rayuwa da azanci
irin wannan, sai mu ce haka bambamcin ‘yan-
Adam yake a yadda Allah (swt) Ya saqa faifan
rayuwa. Wasu baqaqe, wasu jajaye, wasu kuma

117
Tunaninka Kamanninka
farare, wasu ruwan makuba. Wasu dogaye, wasu
gajeru. Wasu gasu a miqe, wasu a lanqwashe.
Wasu a qulle, wasu a murxe; ga wasu can kuma a
sassauce, amma wasu tamau. Wasu sun yi hagu,
wasu kuma dama. Gasu nan dai, ba mai son amfani
da bayan faifan saboda rashin daidaituwarsa.

Toh amma, da hankalinmu, ma iya cewa haka


Allah (swt) Ya tsara rayuwar duniya: ciki da tsari,
baya ruxami? Idan “bayan” duniya ce, masu imani
sa iya yin godiya cewa duk da halayyarsu ta yalwa
ko quntata, sun kasance daga tsari na saqar Allah,
wadda sakamakonsu ita ce “cikin” faifan, watau
Lahira, inda kowa ma zai ji daxi. To amma kuma,
ina adalci a wannan tsari tunda duk zararrukan sun
sami ni’ima iri xaya a sakamakonsu, ba tareda
la’akari da matsayinsu a bayan faifan ba? Watau,
ibadunsu da ayyukansu masu kyau basu amfanesu
ba kenan? Wasu kuma sun sami kyakkyawan
sakamako a vagas kenan? A wannan tsari ba
adalci, musammam ma ga waxanda suka wahala a
duniya komai imaninsu da kyaun halinsu.

Ko a kimiyyance mun san akwai dalilan da suke


sawa a haifi wasu da lafiya wasu kuma a naqashe;
wasu kyawawa, wasu munana. A cikin rayuwar
duniya kuma akwai abubuwan da suke jawo

118
Wahalu da Masifu
masifu da wahalunsu ta hanyoyin da muka tauna da
waxanda za mu duba a gaba. A lahira kuma, mun
san akwai Hisabi da Sakamako, kuma, ma’aunan
Allah (swt) suna da yawa. Shi ya fi sanin ilahirin
dalilan halayyarka, amma kai ma ka san wasu.
Haqiqa, Allah Bai yi tsari irin saqar faifai ba. A
naSa tsarin, babu kuskure ko misqala-zarratin.
Saboda haka, wannan ba amsa ba ce.

2.
A CIKIN TSARIN ALLAH (swt)
DUK HALITTA DA KISHIYARTA:

Wannan haka yake ba shakka, kuma haka ma Allah


Ya ce; domin ga Dama da Hagu, ga Kyau da Muni,
Mace da Namiji, Dare da Rana, Sama da Qasa, Fari
da Baqi, Gaskiya da Qarya, Arziki da Talauci,
Hankali da Hauka, Kyauta da Rowa, Adalci da
Zalunci, Lafiya da Cuta, Tausayi da Mugunta, Ilmi
da Jahilci, Imani da Kafirci, Zaqi da Xaci, Haske
da Duhu, Sanyi da Zafi, I da A’a, Gaba da Baya,
Sama da Qasa, Rani da Damina, Dogo da Gajere,
Rayuwa da Mutuwa. A lahira ga Aljanna ga Wuta.

Ga dai misalai nan birjik; idan ba xaya toh, ba


xayan. Idan ba Dare toh ba Rana. Idan ba Yau, toh
ba Gobe. Idan ba Arziki, yá za a san Talauci? Ko

119
Tunaninka Kamanninka
idan ba Adali, yá za a san Azzalumi? Idan ba
marowaci, yá za a san mai kyauta? Ko kuma, idan
ba Rayuwa yá za a Mutu? Allah (swt) da hikima
Yake! Komai da kishiyarsa, kuma duk saboda
komai ya daidaita.

To amma, saboda me wasu suka zama daga tsarin


munanan halittun, wasu kuma daga kyawawan
halittun. Ya aka yi Almu ya zama mutumin banza,
amma Alu mutumin kirki? Me yasa Ishola talauci,
amma Sikitu arziki? Don me Ngozi ta kamu ta
cuta, amma Jamila lafiyarta lau?

Duk waxannan tambayoyin suna da amshoshinsu.


A hankali, za mu fahimci yadda tsarin Allah (swt)
da ‘yancin mutum suka zama tushen hallayarsa.

3.
MASIFUN RAYUWA
DARUSSA NE GA MASU SHANSU:

Cuta, Talauci, Hasara, Kurkuku da ire-irensu, duk


darussa ne ko kuma horo ne daga Allah (swt)
domin masu shansu su tsarkaku su gyara
halayensu. Kamar dai yadda uba ke horon xansa,
ba don yana qinsa ba, sai dai don yana son xan ya
gyara halayensa. Ba shakka mun san duk

120
Wahalu da Masifu
waxannan baqaqen alamu ne masu nunin lallai a yi
sabon tunani mai kyau a tsarkake hali domin
halayya ta gyaru. Amma, in Allah (swt) ne Ya aiko
darussa don horo, don me sai wane suka samu ba
wane ba, alhali wannan ya fi wancan qazamta da
halayen banza? Mecece makomar imaninka kenan,
idan a zatonka ba ka dace da wannan darasin da
horo ba, amma ga shi an aiko maka da shi?

Toh, Ya kenan? A ina za mu tsaya a wannan siraxi


mai wuyar tsallakewa? Shin, maqalawa Allah (swt)
ilahirin jidalanmu shi ne hankali, ko kuwa zai fi
mana alhairi mu tsame Allah (swt) daga cikin
samuwar masifu da bala’an da suke samunmu;
amma kuma mu amince cewar Yana nan shirye Ya
taimaka mana jure masu da ficewa daga garesu, in
mun shige su? Toh, in ba Allah ne Yake aiko su ba,
‘wa ye’, ko kuma, ‘menene’ yake turo mana, ko sa
mu, cikin wannan quntatattar halayya? Ko kuwa,
akwai masifu da za mu iya dangana su ga Allah,
mu ce, ‘Haka Allah Ya yi’; wasu mu dangana su ga
kanmu, mu ce, ‘mu muka jawowa kanmu’; wasu
kuma mu dangana su ga wasu abubuwa dabam, mu
ce, ‘abu kaza ne ya jawo su’?

Duk waxancan Misalai guda uku, sun maqalu ne a


kan cewar Allah (swt) ne Yake aiko mana da

121
Tunaninka Kamanninka
yawancin masifu, ba mu ke jawowa kanmu ba; ba
kuma wani abu dabam ke jawo su ba. Saboda
haka, ko mu yi fushi da kanmu don mun san mun
dace Allah (swt) Ya aiko mana da su; ko kuma mu
yi takaicin cewar Allah (swt) Ya ware mu Ya aiko
mana da masifu ba tareda mun dace da su ba.
Masu cewar, Allah Ya aiko mana ne don darasi a
garemu, suna faxar haka ne don imaninsu ya tilasta
masu kare Adalcin Allah (swt). Sun sha’afa da
cewar ‘Allah ba azzalumi bane’, kuma ba Ya
bukatar kariyarsu. Ba abinda yake faruwa haka
siddan ba dalili. Idan ba a ga dalili ba, to ba a
bincika sosai ba.

Maqalawa Allah (swt) dalilan masifunmu da


wahalolinmu, ba su ne maslaha a garemu ba. Duk
da imaninmu na cewar, “Allah ke iko da komai”,
zai fi mana alhairi idan muke nemi dalilan da suka
dace da afkuwar masifun, muka kuma yi qoqarin
kauda su, ko gyarasu, a tsarin rayuwarmu. Idan
muka ci gaba da xorawa Allah ba tareda nazari ba,
to kuwa, kafin mu je ko’ina, imaninmu zai raunana
ko ma ya salwanta, kuma ba haxari irin wannan.
Amma kuma, xauke Allah (swt) xungum daga
cikin waxannan al’amura, har-wa-yau, ya fi komai
ganganci. Tsakanin waxannan gefuna biyu, lallai
mu nemi azancin da zai kawo maslahar wannan

122
Wahalu da Masifu
matsala, don mu fita daga wannan tarko na imani.

Bari mu sake tambaya: Akwai dalilan da suke sa


masifu faruwa, ko kuwa haka katsahan suke isowa
ba tareda hannun Mai-ikon ba? Wannan ita ce
magana abar dubawa. Amma, kafin ita, zai yi
amfani mu duba wasu misalai tukuna, domin
maiyiwuwa ne, idan muka nutsu sosai, za mu fara
ganin masalaharmu a wannan sabon azancin.

** Mai Gida ne ya kunna aci-balbal, ko kandir


ya xora kan taga ko ya ajiye a cikin alkuki, inda ya
saba xorawa, ba tareda ganganci ba. Can, ba zato
ba tsammani, sai iska ta huro ta tunkuxe kandir xin
a kan kujera ko wani abu mai saurin kama Wuta.
Kafin ka ce wannan, Gobara ta mamaye gidan;
rayuka da dukiya sun salwanta.

** Xalibi ne ya qi karatu da nazari yadda


yakamata, kuma ga Jarrabawa a gabansa.
Maimakon haka, sai ya yi ta addu’ar Allah Ya sa
ya ci jarrabawarsa. Ya yi ta addu’a har ranar da aka
kawo sakamakonta. Da ya buxa anbulan, sai ya ga
ya yi muguwar faxuwa!

** Mai cikakken imani ne a kan cewar Allah


Shi ke bayar da lafiya ga marar ita. Wataran, sai ya

123
Tunaninka Kamanninka
kamu da Cuta. Ciwo ya yi tsanani, amma ya qi
neman magani, yana ta addu’a da fatan zai warke.
Amma Ina! Kafin wani lokaci sai Cuta ta bazu a
jikin; Rai kuma ya yi halinsa.

** Mutum ne mai qwazo, wanda ya tashi


haiqan wajen neman wata daraja, ko dukiya, ko
wani ado na rayuwa. Mutumin ya yi duk abinda
yakamata a kan hanyoyi karvabvu domin ya sami
biyan bukatarsa, amma har yau ba ta samu ba.

** Mutane ne da yawa suka taru a wani


muhalli don neman wata alfarma a gurin
shugabansu. Alfarmar guda xaya ce tak, kuma duk
sun dace da ita. Da fitowar shugaban, sai kawai ya
zavi mutum xaya ba tareda la’akari da wani abu da
aka sani ba, ya ba shi alfarmar, ya sallami sauran
ba tareda bayani ba.

** Saurayi ne, sabon aure, mai qoqari da


kyakkyawan fata a gaba, wanda yake riqe da
nauyin duk iyalinsa. Yana cikin tuqin motarsa a
hankali da nutsuwa, sai katsahan tayarsa ta fashe,
ya kuma rasa ransa, ko gavovinsa, a wannan
haxari mummuna.

** Mai-Kuxi ne, duk yadda za a misalta mai

124
Wahalu da Masifu
kuxi a garinsu. Ana nan, ana nan, sai kawai duk
kuxin suka qare; kadarori kuma suka vace; yanzu
ga shi ya zama matalauci abin tausayi.

** Budurwa ce mai hankali da iyaye na-gari ta


shiga auratayya da wani saurayi mai sigar
mutumci. Wata rana sai ya wulakantata ya saketa;
ga ‘ya’ya, ba kuma tareda wani laifi da aka sani ta
yi masa ba.

** Mahajjata ne suna dawowa gida daga Hajji,


sai jirginsu ya kama wuta a sama, ya faxo. A
wannan mugun haxarin, dukkaninsu suka rasa
rayukansu.

** Al’ummar wani qauye ce wadda ta dogara


nomarta ga wani qaton kogi da ya ratsa garin. Wata
damina da kogin ya kawo, sai qarfin igiyarsa ya
karya madatsarsa, ambaliya ta shafe qauyen, wasu
suka rasa rayukansu da dukiyarsu.

Duk waxannan misalai ababan tunani ne don


warware matsalar dake cikin tambayoyinmu, kuma
ba su dace a maqalawa Allah (swt) dalilan
faruwarsu ba, in har aka yi tunani mai zurfi. Idan
har yanzu ba ka yarda cewar bala’ai da masifu za
su iya faruwa da kansu ba, toh ‘wa’ za ka xorawa

125
Tunaninka Kamanninka
laifin ambaliyar Ruwa da ta halaka ximbun
jama’a? Waye da laifi idan mahaukaci ya xauko
bindiga ya harbe jama’a a titi? Waye ya jawo
faxuwar Jirgin Saman da duk na ciki suka rasa
rayukansu? Wa ya haddasa girgizar qasar da ta
haxiye Gari guda da yawancin jama’arsa? Wa ya
fasa Dutse da aman wutarsa ya mamaye komai?

Shin, za mu iya cewa duk waxannan masifun


Allah (swt) ne Ya haddasasu don kawai
sha’awarSa? Ina yaron da ya yi haxari da mota ya
mutu? Ina wanda ‘yan fashi suka tare suka kashe?
Ina wanda Cuta ta kama ta halakar? Ina yarinyar
da mijinta ya saketa? Ina wanda ya nemi dukiya ya
rasa? Ina tajirin da ya karye? Duk wa ya jawo
masu waxannan masifu? Lallai ne mu qididdige
masifu da bala’ai da kuma wahalolin da suke
samunmu, mu bambance, “wa?” ko, “me?” yake
haddasa irin waxannan; Haka, “wa”? ko “me?”
yake haddasa irin waxancan. Kuma waxanne ne
suke faruwa don kansu, ko don wasu dalilan.

* DOKOKIN HALITTA da Allah (swt) Ya samar, su


ne suke tafiyarda komai, kuma ba sa canjawa a
tsarinsu na asali. Watau Allah (swt) Ya riga Ya
kammala tsarinSa, Ya kuma shiriyarda komai-da-
komai yadda za su tafi da yadda za su cuxanya da

126
Wahalu da Masifu
yadda za su kasance. Kuma, kodayake Ya ba wa
kanSa Iko a kan komai, amma kuma ba Ya canja
wasu abubuwa, kuma ba Ya hana wasu faruwa,
kuma ba Ya sa wasu su faru, muddin dai tuni suna
cikin injin Dokokin HalittarSa. Waxannan dokoki,
mataimaka ne a garemu, ko a jikinmu suke, ko
kuma a kewaye da mu suke. Amma kuma za su iya
lahantamu idan muka sava tsarinsu.

Misali: Mun san amfanin Dare da Rana. Don


hakama sai mu yi barci da daddare, mu yi
xawainiyar rayuwa da Rana, kamar yadda Allah Ya
tsara mana. Mun san jikinmu yakan iya kare kansa
daga cutanni. Don haka ma idan muka sha magani
sai mu tayar da makaman da za su yaqi cutar. Mun
san yadda komai ka jefa sama, toh, qasa zai faxo.
Don hakama muke tsaye daram, mu da gidajenmu,
mu kuma yi yawo a kan doron duniya ba tareda
mun faxi ko muna lilo a Sama ba. Mun san
amfanin Ruwa. Don hakama mun san rayuwa gaba-
xayanta ta dogara ne a kansa. Mun san
muhimmancin duk waxannan da sauransu.

Amma kuma, mun san cewar idan ka qurawa Rana


ido, ta iya makantaka. Idan ka sha ruwa ba qa’ida,
ya iya qulle cikinka. Idan abu ya faxo kanka, ko ka
faxo daga cikinsa, ya iya halakaka. Idan ka dogara

127
Tunaninka Kamanninka
kan jikinka kaxai ba magani, ko ka qi kula da shi,
ka iya kamuwa da wata cuta wadda za ta iya zama
ajalinka. Mun san amfanin wasu abinci a tareda
mu, amma idan ka qi gyarasu guba ne. Mun san
amfanin Wuta, amma ta iya qonaka. Mun san
amfanin iska, amma ta iya hureka, ko ta rushe
gidanka. Duk waxannan ba ka da iko da su, ko
yadda suke aikinsu. A rayuwarka, tilas ka san
yadda za ka yi mu’amulla da su, ba sune za su san
yadda za su yi mu’amulla da kai ba, ko waye kai.

A wasu halayen kuma, mun san harshashi ba shi


da hankalin zavi, idan aka harbo shi, bai damu ko
waye kai ba. Idan fukafukan Jirgin Sama suka
valle, ko inji ya lalace a sama, in zai faxo ba
ruwansa da ko su waye a ciki. Idan annoba ta doso
gari, ba ta san Liman ba, balle Sarki.

A cikin Dokokin Halitta, Allah (swt) Ya tsara


komai tuni. Idan abu-kaza da abu-kaza suka
gauraya, abu-kaza ne zai faru; ko abu-kaza ne zai
samu. Wannan doka ba za ta canja ba har abada-
abadin, kuma ko waye a gurin. Dá Dokokin Halitta
sukan canja, da ba mu rayuwa ba; domin dá
wataran Ruwa ba zai kashe Wuta ba; ba kuma zai
yi maganin qishirwa ba. Dá Wuta ba za ta qona
komai ba, balle ta dafa shi. Dá Maniyin namiji bai

128
Wahalu da Masifu
maqalu da Qwan mace an sami ciki ba, balle iyali
da al’umma su ginu. Dá fatar Jikinmu ba za ta
fidda gumi ba har sai ta qone. Dá Girgije bai zamto
hadiri an yi ruwa ba, balle qasa ba ta fidda tsiro. Dá
wataran Haske ya zama Duhu. Dá ba a sami Petur
daga guvataccen Mai ba. Dá Gaskiya ta zama
Qarya. Dá Zalunci ya zama Adalci. Dá wani sai ya
qi mutuwa. Dá ba Hisabi.

Dá al’adar Allah (swt) ce Ya rinqa miqa Hannu a


kowanne lokacin da masifa za ta faru, don Ya
tsame mutanen kirki; dá mutanen kirki sun nemi
qure Allah. Dá kuma sauran jama’a sun zubda
imaninsu domin Allah Ya nuna ba ruwanSa da su,
don su ba mutanen kirki bane. Dá Allah zai jingine
Dokokin Halitta ga mutanen kirki, ko wasu, da ba
su yi rashin lafiya ba; dá sai su ringa keta titi da
gangan; dá sai su ringa dirowa daga bene,
maimakon su biyo ta matattakala; dá sai su qi gudu
in gobara ta tashi. Haka kuma dá duk makafi,
kutare, guragu da marasa lafiya; ko matalauta da
mahasaranta, an fassarasu da siffar mutanen banza.
Dá haka Allah (swt) Ya tsara rayuwa, dá ruxanin
ya faskara. Dá yanzu ba duniyar! Allah (swt) Shi
ne Mai hikima, mai iya tsarin da ya fi dacewa.

Baikamata mu ringa dangana dukkanin masifu

129
Tunaninka Kamanninka
cewar “Haka Allah Ya yi ba”. Idan marasa lafiya
suka mutu saboda rashin magani a Asibiti; idan
Shugabanni suka danne haqqin talakawa saboda
rashin imani da rashin tausayi; idan Mota ta qi
tashi saboda rashin gyara; idan Yaro ya zagi na
gaba da shi saboda rashin kunya; idan Mara kunya
ya ci zabe saboda shashancin al’umma; idan
Bango ya faxi saboda rashin yave; idan Madatsar
Ruwa ta valle saboda rashin qarfi da rashin gyara;
idan Abinci ya qare saboda rashin noma; a faxa
min: Meye na Allah (swt) a cikin waxannan? Ko
kuwa so ake a maida Fadar Allah (swt) jujin zuba
qorafi? Ko kuma muna so ne mu lave da Shi don
mu ringa voye gazawarmu? Ko kuwa har yanzu ba
mu san Shi bane; labarinSa kawai muke ji?

Ba abinda yake cutar al’umma, ya kuma dakushe


ci-gabanta, irin saurin cewa: “Haka Allah Ya yi”.
Kuma ga wasu mutane da bahagon imani. Da wani
wawa ya katse magana da wannan furuci, shikenan
magana da shige. Ba mai sake tasota, balle wani ya
ce, “Kai, wannan laifinmu ne”, balle a yi tunanin
gyaran lahanin; balle a sami ci-gaba.

Idan Girgizar Qasa ta girgizo; Ambaliyar Ruwa ta


kwararo; Guguwa ta nannaxo; Gobarar Daji ta
danno; Dutse mai harshen Wuta ya fashe, tavon

130
Wahalu da Masifu
wutarsa ya malalo; toh, dokokin halitta ne suke
sha’aninsu, domin wasu abubuwa sun gaurayu da
wasu, ko domin wani abu ya tsikaresu, a cikin tsare
-tsaren halitta na fil-azan. Duk waxannan da muke
kira, “Masifun Halitta”, sukan faru ne yawanci
saboda Qasa a doron duniyarmu, tana ci-gaba da
gyara zamanta. Ikon Allah da TausayinSa ne kaxai
za su iya kiyaye jama’a su kuma taimaka masu
wajen sake gina rayuwarsu. Sanin wannan yana da
xinbun mahimmanci ga imani.

Fari da yunwa da cutannin da suke rakosu.


Muggan yanayin sanyi da na zafi da irin illolinsu.
Aradu da kwarankwatsa da xinbun ruwan saman da
yake biyo bayansu. Guguwar iska da ta teku da
yadda suke farfasa komai a kan hanyarsu: Duk
waxannan masifun muhalli ne da tsarin yanayinsa.
Mazauna irin waxannan gurare da sauran ‘yan
Adam a doron duniya, lallai su san haka halitta take
a guraren zamansu, su kuma nemi maganin
lahaninta tunda wuri, ko su bar gurin. Caffar da
Allah (swt) Zai kawo ce kaxai za ta tserarda su ta
kuma turo mutanen kirkin da za su tallafawa
waxanda suka tsira domin su sake gina rayuwarsu.

Amma, idan ‘yan Ta’adda suka sa bom a jirgi, ko a


kantuna. Idan Varawo ya yi fashi, ya halaka

131
Tunaninka Kamanninka
Maigida ko ya kwashe dukiyarsa. Idan Maqiyi ya
farma mutum ya raunana burinsa. Idan masharraci
ya yi sharrinsa, wani ya shiga cikin wata masifa.
Idan Matsafi ya yi makarunsa, har ya lahanta
lafiyar wani abokin adawarsa: A waxannan halaye,
ba Dokokin Halitta ne suke varna ba; mutanen
banza ne ke yinta. Ikon Allah da kiyayewarSa ne
kaxai za su iya ceton jama’a da warkarda su, da
kare su daga masu sharri da varna, su kuma ba su
qarfin hali da tunani da imanin da za su iya jure
wannan rashi da hasaru da jidalan rayuwa.

Idan shugabanni suka ci amana, mutane na ganinsu


ba su yi komai a kai ba; idan saboda haka Hukuma
ta tsiyace, fatara kuma ta dannowa Qasa. Idan
Talakawa ba su san mutumcinsu ba; idan saboda
haka suke girmama waxanda ba su dace ba, suna
yabo da biyayya ga marasa kunya, suna zaven
varayunsu; idan saboda haka ba sa samun
shugabanni na-gari, al’umma kuma ta lalace. Idan
Azzalumai suka yi yawa a Qasa, har doka ta zama
makamin kama-karya; idan saboda haka, cin-
mutumcin masu mutumci ya yi yawa, wata masifar
kuma ta vullowa qasar: Ku faxa min, wa ya
haddasa duk waxannan masifu? Dokokin Halitta
ne, ko kuwa mutanen Banza, ko kuma Jama’a su
da kansu suka jawowa kansu saboda sakacinsu?

132
Wahalu da Masifu
Amma mun san cewar, Ikon Allah da RahamarSa
ga muminai, da waxanda ba su ci ba, ba su sha ba,
su ne kaxai za su iya cetar jama’a daga waxannan
miyagu, su kuma taso da maza da matan qwarai
waxanda za su yi gwagwarmaya don ceto da kafa
tushen ci-gaban al’ummar. Yawancin mutane suna
xauke da kuskurarrun “kamanni” da “alamun”
Allah (swt). Sai ka ga ana yi maSa shaidar da ta sha
bambam da yadda Shi Ya misalta kanSa. Duk
kyawawan Sunayen nan 99 na Allah (swt), ba
mummuna guda xaya. Ba inda Ya ce Shi, “Mai-
Cutarwa ne”; ko Shi, “Mai-Mugunta ne”, ko Shi
“Mai-wahalarwa ne”. Lallai ne mu fara lura!

Ko ana zaton cewar Allah Ya ajiye adakun cuta da


mugunta da masifu ne; sai Ya xau waccan ya
jefawa wannan; Ya xau wannan Ya jefawa
waccan? “Talauci! Mamaye Abubakar. Zazzabi!
Kama Balaraba. Mota! kaxe Samuwal. Hasara!
Harbi jarin Gambo. Lami! Yi vari; Audu! Saki
Jummai. Jirgi! Faxo kowa ya mutu. Maciji! Sari
Helen. Ruwan Sama! Rushen gidan Jauro. Gobara!
Cinye gidan Goje. Kuturta! Ciji Musa. Makanta”
Rufe idanun Bello”. Haba, Jama’a! Ai yakamata
mu ringa aiki da hankali da kuma ilmi. Lallai ne
jama’a su sake tunani a kan waxannan abubuwa.

133
Tunaninka Kamanninka
Idan Dokokin Halitta, ko Mutane da Shugabannin
Banza, ko kwaxayi da fadanci, ko Jama’a su
kansu, ko xaurowar al’amura, (kamar saran maciji,
tuntuve, da wani bangare na haxari), ko rashin lura
da ganganci sun haddasa wani abin takaici, to lallai
ne mu san ba Allah (swt) bane. Amma kuma
muhimmi ne mu san cewar Yana nan a shirye Ya
karemu, Ya kuma taimakemu wajen isarda sauqi
ko warwarewar duk waxannan ababan takaici da
suka same mu, in dai mun neme Shi.

Lallai mu fahimta, mu kuma amince cewar, a


wajen taimako da caffa ake samun Allah (swt), ba
wajen cutarwa ba. Idan muka hango wata masifa ta
nufo, muka nemi taimakonSa da kariyarsa, toh ba
shakka, Zai zo mana a kan waxannan taimako.
Amma fa lallai ne muma mu yi abubuwan da suka
dace mu yi, ba kawai mu saduda ba.

Idan wata masifa, ko wani abin takaici, ko wahala


ta sameka, to maza tsarkake tunaninka, ka yi
abinda yakamata; ka kuma nemi Allah (swt) da
taimakonSa. Ba shakka Zai zo maka, kuma Zai
taimaka maka ta duk inda ba ka zato; in dai
tunaninka da al’amuranka na alhairi ne. Allah
(swt) Shi ne Mataimaki. Ba abinda Allah (swt) ba
Zai iya yi ba. Ba abinda ba Shi da iko a kansa. Ba

134
Wahalu da Masifu
abinda zai faru ba tareda saninSa ba. Iznin Allah
(swt) a kan tabbatar komai tuni ya kammala, a
lokacin da Ya idar da lissafinSa, Ya kuma tabbatar
da dokokinSa. Shi Ya halicci komai da komai a
aune, Shi ne kuma Mai iko a kan komai da koman.

Don hakane ma a shikashikan imaninmu, muka


amince ba abinda zai faru ba tareda iznin Allah
(swt) ba; da mai kyau da marar kyau. “Iznin” ba
irin wanda akawu yake karva wajen manajansa
bane, ko irin wanda uba yake yi wa xansa. Iznin
Allah (swt) a cikin rayuwar halittunSa yake; ta
yadda suke aikinsu ko tunaninsu. Watau, iznin ne
injin samuwarsu da rayuwarsu da al’amuransu.
Lallai mu fahimci wannan ta yadda yakamata, mu
guji amfani da ma’anar “izni” yadda muke karvarsa
ko ba da shi ga junanmu, wajen maqalawa Allah
dukkanin jidalanmu. Ba shakka, Allah (swt) Ya ke
iko da komai, amma akwai abubuwan da Allah ba
Zai yi su ba, ko kuma ba Ya yinsu yau da kullum,
domin tsarin yadda Yake tafiyarda abubuwanSa
sun kammalasu tuni, tun kafin su farun.

Duk wanda Ya san Allah (swt) sosai, ta hanyar


alhairi kawai ya san Shi, ba ta hanyar sharri ba. A
naSa ayyukan, Shi ba Ya sharri, duk da mun san
sharrin -da masu aikata shi ko kawo shi- suna cikin

135
Tunaninka Kamanninka
tsarin izninSa. Misali: Idan mutum ya aikata sharri,
mun san a cikin “iznin” Allah ya aika wannan
sharri, domin Allah ne Ya halitto shi tareda duk
abinda ya yi amfani da shi wajen aikata sharrin. In
ta hanyar mulki ne, Allah ne Ya ba shi mulkin.
Idan ambaliyar ruwa ta rushe gidaje ko ta halakar
da mutane, to Allah ne Ya halicci ruwan da kuma
iskar da ta huro ruwan, kuma Shi ne Ya yi lissafin
cuxanyarsu. Idan Damusa ta cinye mutum, mun
san Allah ne Ya zavar mata nama a cikin abincin
da tafi so, Ya kuma ba ta qarfin da za ta iya
turmushe abincinta.

Amma kuma, mun san masharracin nan, shi ya


zavi ya aikata sharrin; wanda Damusa ta cinye, shi
ya je kusa da ita. Azzalumin nan shi ya zavi yin
zalunci daga vangaren mulkin da Allah (swt) Ya
ba shi, duk da ya san Allah (swt) Yana fushi da
azzalumai. A cikin waxanda ambaliya, ko aman
wutar dutse, ko girgizar qasa ta halaka ko ta rushe
gidajensu, ko ta lalata gonakinsu, akwai waxanda
suka jawowa kansu, domin sune suka nace da
zama da noma a gindin wannan dutse wanda sun
san zai iya fashewa. Akwai kuma wanxanda haka
al’amarin kawai ya xauro, saboda kasancewarsu a
wannan muhalli a wannan lokaci. Watau, tsautsayi
ne, ba yadda za a yi. Waxanda suka gina gidajensu

136
Wahalu da Masifu
a kwari ko a hanyar ruwa ko a kan tsohon
kududdufi, yakamata su san in ruwan ya zo ba zai
saurara masu ba. Duk irin waxannan al’amura haka
suke. Tunaninmu ne kaxai zai iya shiryarda mu
domin mu yi abubuwan da za su taimaka mana
kare waxansu bala’ai. Amma ba shakka, Allah
(swt) Mai jin addu’a ne, Mai kuma aiko da taimako
ne duk sa’inda aka nema, kafin ko bayan masifar.

Kada mutum ya nemi Allah (swt) a ayyukansa na


lalata, ko ayyukansa na sharri, ko ayyukansa na
mugunta. Allah (swt) ba Zai taimaka ba. Ya riga
Ya barwa Iblis wannan sararin da aqidar. Kada
mutum ya yi zaton akwai wasu haxe haxe da zai yi
da sunan Allah (swt), ko Ayoyin littafinSa don
lahanta wani abu, ko jawo wani bala’i ga wasu ko
ga qasa. Irin waxannan tunanin, da ayyukan da
sakamakonsu duk tsafi ne. Allah (swt) ba Ya
sharri, baYa yarda a yi sharri da sunanSa. Duk
wanda bai san haka ba, toh bai san Allah (swt) ba.
Duk wanda ya zaci cewar akwai sharri a littafin
Allah (swt), ko zai iya amfani da Allah wajen qulla
sharrinsa, to wannan mutum ya halaka, har sai ya
sake tsarkake zuciyarsa, ya tuba ya dawo kan
sabuwar hanya miqaqqiya. Kuma Allah (swt) Mai
sauraron nadamunsa da tubansa ne. Allahu Akbar!
Allah da tausayi yake!

137
Tunaninka Kamanninka
A tsarin Samaniya gaba-xayanta, Allah (swt) Ya
kafa dokokinSa na yadda komai zai tafi. Tun asali
Ya tsara kulliyar dokokin ISKA, RUWA da WUTA.
Ya riga ya lissafta komai, Ya ba da umarninSa na
Dokokin Halitta. A doron Duniya Ya ajiyewa duk
halittunSa dokokin rayuwarsu. Waxansu tilas
jikinmu ya bi su; wasu kuma ‘yancin zuciyarmu
ya sa tunaninmu ya bijire shawarwarinSa garemu
na yadda za mu yi rayuwa mai amfani.

Haka wannan umarni da biyayya suke ga duk


halittun Samaniyoyi da Qassan da Allah (swt) Ya
halitta. Ashe, babu abinda zai faru sai da yardar
Allah (swt), ba kuma wanda zai iya tsaida komai,
sai Shi, domin komai naSa ne. Don hakane muke
cewar komai umarninSa yake bi, umarni na tun fil-
azan. Deen al-Fitra. Amma mutum ya iya
bijircewa a tsarin tunaninsa da ayyukansa. Ya iya
qin gudu in Kura ta biyo shi; ya iya qin yin Salla
in lokacinta ya yi; ya iya qin shan magani in ya
kamu da cuta; ya iya gina gidansa a kan hanyar
ruwa, ko ya kafa bukkarsa a kusa da maqera; ko ya
bi qungurmin daji cikin dare shi kaxai; Ko ya sa
kansa cikin yanayin da zai kamu da wata muguwar
cuta. Haka mutum ya iya cutar maqwabcinsa, ko
ya yi fashi a daji ko a ofis. Duk zavi na gare shi,
domin kuwa Allah Ya ba ba shi ikon yin zavin.

138
Wahalu da Masifu
Da bijircewar zuciya da kafircinta suna da
muhimmin bambanci. Akwai bijircewar zuciya ta
qi bin umarnin Allah (swt) na yadda ka zavi ka
bauta maSa, ko yadda kake fahimtarSa, ko kuma
yadda za ka tafiyarda rayuwarka. Akwai kuma
kafircewar zuciya, watau rufewarta xungum, daga
imani da samuwar Allah (swt) Shi kaxai yadda
Yake. Bayanin wannan kafirci ya fita daga manufar
wannan littafi, sai dai kawai mu ce zuciyar ce kaxai
take cikin wannan kafirci, ita ce kuma take dasa
hali da halayyar karfircin.

Akwai misalai na bijircewar zuciya daga bin


tafarkin rayuwa mafi maslaha; watau bijircewarta
daga yin amfani da shawarwarin da za su haifarda
rayuwa ta-gari, da kuma bijircewarta daga son
biyan bukatar jiki. Idan jiki ya bukata, amma tunani
ya qi yarda a biyawa jikin bukatarsa, to sai
halayyar jiki ta tavu. Misali: idan ka ji yunwa ko
barci (bukatar jiki), amma ka qi cin abinci ko
barcin da gangan (bijirewar tunani), to sai halayyar
ciwon-Kai ta wanzu; wadda ita kuma alama ce
wani gu (ko wasu gurare) a jiki sun sami naqasa,
kuma yakamata a duba. Idan ka qi, har kuma
wannan ta jawo wata masifar dabam, toh ka ga kai
ka jawowa kanka wannan illa ta jiki daga
mummunan tunaninka. Haka, idan ka kamu da

139
Tunaninka Kamanninka
wata cuta saboda ka shiga halin da za ka kamu da
ita, sai ka qi shan magani, to in halaka ta riski inda
cutar take, maiyiwuwa ne kaima ka halakan. Ka
ga, mummunan tunaninka ya jawo ka rasa
rayuwarka xungum. Wannan tsari da Allah (swt)
Ya mallaka mana iko a kan tunaninmu ba qaramar
rahama ce tareda mu ba. Amma idan muka bijirce,
to mun san sakamakon a taredamu. A taqaice: Ita
kanta shiriyar addini don amfaninmu ce kaxai, ba
don amfanin Allah (swt) ba. Ya haqiqa!

Za mu iya bijircewa bukatar jikinmu ta hanyar


munanan tunani, nan-da-nan halayyarmu ta zama
ta cuta, wadda za ta iya jawo babbar naqasa ko ma
ta kawo halaka. Haka kuma, za mu iya bijircewa
bukatun rayuwarmu ta hanyar munanan tunani,
nan-da-nan Halinmu da Halayyarmu su raunana,
waxanda kuma za su iya kawo nadama a cikin
rayuwar gaba xayanta.

Farin Tunani a kullum, a kan kowacce matsala, shi


ne yake kusanta mutum da Allah (swt), a kuma
sami taimako da tallafarSa a kodayaushe. Wannan
shi ne tsarin addini da dalilinsa, domin mu ci ribar
rayuwarmu. Amma kuma, Baqin Tunani shi yake
sa mutum ya bijircewa shawarwarin Allah (swt),
ya qazamta zuciyarsa da tunanin Allah ne Yake

140
Wahalu da Masifu
barin wulakanci da wahaloli suna shafar
rayuwarmu. Mai wannan tunani, ba zai iya
komawa ga Allah (swt), ya kuma yi abubuwan da
suka kamata wajen sabuntawa da inganta
rayuwarsa ba. Tilas ya canja tunaninsa tukuna,
sannan ya sami maslahar wahalolinsa tareda
taimakon Allah (swt). Idan ka xafawa Allah (swt)
laifin wahalunka, yaushe kuma za ka je gareShi
neman taimako, tunda ka ce Shi ya jawo maka?

Lallai ne daga yanzu mu san kanmu, mu kuma san


dalilan da suke sa mu cikin wahalu, ko suke kawo
bala’i da masifu a qasa da kawunanmu. Idan na
Dokikin Halitta ne, to mu yi nazari, mu ga ya za
mu iya fisshe da kanmu daga garesu tun kafin su
zo, ko in sun zon. Idan na Miyagun mutane ne a
cikinmu, mu san ya za mu yi da waxannan mutane.
Idan namu ne na kanmu, mu san ya za mu canja
kanmu, mu kyautata, mu inganta rayuwarmu. Idan
masu faruwa ne don haka al’amari ke xaurowa, mu
san ya za mu kiyayesu, ko mu magantasu, ko mu
jure masu, in sun farun.

Abune muhimmi ga mutum ya zama mai qarfin


zuciya daga qarfin tunani. Kada wanda ya yi
fafutuka sau xaya ko sau biyu ya barta domin bai
sami nasara a gwajin farko ko na biyun ba. Kada

141
Tunaninka Kamanninka
mutum ya fidda rai xungum daga samun nasara
daidai shi a rayuwarsa. Kada matar da aka saki ta
kama hanyar lalacewa, ko ta fidda rai daga
sabuwar rayuwa, ko samun miji wanda ya fi
wancan alhairi a gareta. A tsarin Allah, watakila
sabuwar rayuwa ce a gabanta mai albarka da
gamsuwa. Kada Mai arzikin da talauci ya riske shi,
ya zubda rayuwarsa cikin jujin nadama da fitar
imani. Ya tambayi kansa: ‘Da, ya aka yi na samu?’
Sannan ya sake maida himma da gyaran tunaninsa
da halayensa da kurakurensa. Da wannan sabon
tunani da aqida Allah Zai kimsa masa wadatar-
zuci, Ya kuma isar masa da sababbin bukatunsa.
Kada mutum ya rufe imaninsa ga Allah. Canjin
alhairi yakan biyo bayan takaici, in an barwa
Allah. Don hakama ake cewa, “Wani hanin ga
Allah baiwa ne”, kuma akwai misali da yawa.

Kada mutanen da ba su sami alfarman nan daga


shugabansu, su xauka nan gaba ba za su samu ba,
har su kama hanyar watsewa, ko vatawa wanda ya
samu, ko zagin shugaban. Lallai ne su sake maida
al’amuransu wajen Allah su kuma yi aiki tuquru.
Qofofin Allah suna da yawan gaske. Kada iyalin
saurayin da ya rasu a haxari, ko shi, in ya tsira da
ransa ba da wasu gavovinsa ba, su xauka shikenan
ba wani sauran haske a rayuwa sai duhu. A cikin

142
Wahalu da Masifu
wannan canjin halayya, Allah Ya san yadda zai yi
da su ya cike masu gurbin hasarunsu, muddin dai
tunaninsu da qwazonsu ba su raunana ba. Kada
‘yan’uwan Mahajjatan nan su xauka cewar Allah
(swt) Bai damu da ibadar ‘yan’uwansu ba, kuma
bai damu da su ba. Sakamakon ayyukansu na
alhairi, da ibadarsu, ba za su tave ba. Allah ne Ya fi
sanin hanyoyin alhairi da zai sakawa mamatan da
kuma waxanda suka yi rashin.

Amma lallai ne xalibin nan ya san ba zai tava cin


jarrabawa ba, sai ya yi karatu a nutse. Allah (swt)
ba Zai canja sakamakon jarrawabarsa ba; ba zai
kankare ‘Faduwa’ Ya rubuta masa ‘Ci’ ba. Haka,
duk mai Cuta ya san magani ne kawai mai warkar
da ita, kuma don haka Allah (swt) Ya ba mu
maganin komai, har ma a cikin wasu ayoyinSa, Ya
kuma ilmantarda mu a kansu. Ka sha maganin
tukuna, sannan ka yi addu’ar domin Allah (swt) Ya
tallafa maganin ya warkar, ko da maganin ya
naqasa a dacewarsa da cutarka. Idan ba ka da halin
sayen maganin kuma, sai ka yi addu’a Allah Ya
aiko maka da yadda za ka yi ka sami maganin da
ya dace da cutarka. Kada ka manta cewar wasu
ayoyin Al-Qur’ani mai girma, muhimman magani
ne, musammam in ba halin neman irin maganin da
aka sani. Ba ta’inda Allah (swt) ba Ya tallafawa,

143
Tunaninka Kamanninka
indai an name Shi da farin tunani na farar zuciya.
Mai nema daidai, akodayaushe, yana tareda samu.

Amma, wanda ya tunkari abinda ya fi qarfinsa, ko ya


qi kaucewa abinda zai illace shi da gangan, komai ya
faru gareshi shi ya jawowa kansa. Duk abinda ya
faru ga mutum, ko ga al’uma, ya zama tilas a yi
tunani mai zurfi tukuna, a binciki dalilai sosai,
sannan a nemi maganin abin, in ana da shi, ko a
qirqiri dabarar tunkararsa, idan ba shi da magani.
Mutum da al’ummar da suka xau wannan Hali a
xabi’arsu, to ba shakka su ne masu iya kange
masifun da suka doso su, ko suka same su. Su ne
kuma masu iya tunkarar su idan ba za su kangu ba.
Allah (swt) Zai taimaka a wannan gwagwarmaya ta
masu amfani da imaninsu da hankalinsu da
qoqarinsu. Amma waxanda suka saduda, suke
maqalawa Allah (swt) laifin jidalan su, ba inda za su
a filin dagar maganin masifunsu, balle kuma na
warakarsu da ci-gabansu.

Ba jarin da ya fi muhimmanci ga xan-Adam irin ya


fahimci Allah (swt) daidai gwargwadon yadda zai
iya, domin ya san yadda Yake gudanarda ayyukanSa
da HikimoninSa. Ta hakane kaxai, mutum zai san
nasa ayyukan da abinda tilas ne ya kiyaye, muddin
yana son zaman lafiya da gamsuwa a rayuwarsa.
Allah (swt) da Ya haliccemu, Ya fi qarfin ya
zaluncemu. Su wa ye mu? Yaushe kuma muka isa?
144
Wahalu da Masifu

145
Tunaninka Kamanninka

146
Tunani da Inganci

Tunani
da Inganci

A
“Araha ba ta ado”

rayuwar mutum, akwai wata aba guda


wadda take da muhimmancin gaske wajen auna
matsayinsa. Wannan aba kuwa ita ce, Nasara.
Akwai waxanda suka ci “nasara” a rayuwarsu;
akwai kuma wadanda suka yi “hasara” a
rayuwarsu. Da ‘nasara’ da ‘hasara’ a yawancin
lokuta, tunanin inganta kai, ko rashinsa, suke
haifarda su. Wannan shi ne harsashin maganar.

Haqiqa, ba mutumin da ba ya son nasara a cikin


duk abinda ya sa, ko ta sa, a gaba, sai dai wawa. A
kodayaushe mukan ce, “Nasara tana daga Allah”,

147
Tunaninka Kamanninka
kuma wannan magana gaskiya ce. Saboda haka,
lokaci ya yi da yakamata mu bincika ma’anarta a
nutse. Mun san cewar, qwazo da fafutukar mutum
wajen neman nasara sukan taimaka qwarai da
gaske wajen samun nata. Don hakama muke cewa,
“Allah (swt) Ya ce, ‘Tashi In taimakeka’”. Watau,
kada wanda bai tavusa ba ya sa rai a cikin
samunta, ko ya yi qorafin bai sameta ba. Ashe,
Allah Ya ce: Tashi In taimakeka, gargaxi ne, ko
kuma qarfafa gwiwa ce, ga masu nema domin su
tashi tsaye su yi fafutukar da ta dace da burinsu da
manufarsu. Ita kanta “Sa’a” takan zo ne ga
zuciyar da ta kimtsu ta karveta.

Akwai abubuwa na Halaye waxanda in mutum ya


yunqura ya gina su cikin tunaninsa, toh, ba shakka,
zai iya inganta rayuwarsa da Halayyarsa ta hanyar
inganta Halayensa, kuma ya ji daxin gudanarda
kansa da al’amuransa a kowanne hali. Mutane da
yawa sukan yi hasara a rayuwarsu, ba don komai
ba, sai dai don kawai sun yi sakacin gyara, ko nuna
wasu halaye waxanda za su iya kusantarda su ga
mutane, su kuma qara masu kwarjini, mutumci, da
sauran alamun mutum masu angazo nasara a cikin
hulxa, kowacce iri ce.

Gyara Hali ta wajen gyara Tunani, zai iya fassara


mutum a surar da za ta amfane shi, ta kuma ba shi
148
Tunani da Inganci
damar aikata wasu abubuwa da za su qara masa
sa’a wajen cimma wasu buri, waxanda in ba tareda
waxannan halayen ba, da wuya a sami sa’ar, balle
kuma nasarar. Ita dai Nasara, tana da
muhimmancin gaske, domin takan hure baqin-ciki
da tunanin banza; ta hana zaman banza; ta kuma
kore damuwa. Duk waxannan dangi ne na Farin
Tunani, mai yalwata Farin-ciki da lafiya da basira
da alfahari-da-kai, da kuma cancanta. Ba shakka,
nazarin wannan Babi da shawarwarinsa zai yi
fa’ida ga waxanda suke son nasara a tareda su.

Akwai dokokoin rayuwa kamar 19, ko ma fin haka,


waxanda mutane masu son inganta kansu za su iya
la’akari da amfani da su, har sai sun zama
xabi’unsu. Na tabbata masu yalwata tunani da
nazarin rayuwa za su iya qara wasu dokokin a kan
waxannan da na zana. A nan ga xabi’un da zan fara
maganarsu a cikin sauqaqaqqen bayanansu, don a
fara amfani da su.

1
KYAKYKYAWAR LAFIYA

Kamar yadda muka gani can baya, a Babi na 5,


Tunani mai-kyau yana da babbar nasaba da lafiya
mai-kyau. Ita kanta lafiyar jiki mai-kyau,

149
Tunaninka Kamanninka
sakamako ce ta kyakkyawan tunani gameda
lafiyar. Idan mutum ya ringa tunanin rashin lafiya,
misali ‘ciwon Kai’, sai ya ringa jin kamar ya kama
shi. Tunanin bawali, yakan matsa jin bawalin; haka
tunanin hasara yake kawo fargaba; tunanin tsoro
kuma ya haifar da ragonci.

Tunanin fargaba da tsoro sukan qara saurin famfon


zuciya har gudun jini a jijiyoyi ya qaru. Da
wannan ta faru, sai jinin ya fara xumi, abu wanda
ke haifar da ‘hauhawar jini’ -cuta wadda za ta iya
halakarda mutum nan da nan. Ashe yaqin fargaba
ba zai yi nasara ba, sai an yaqi tunanin hasara
kowacce iri ce. Yawan tunanin hasara, yana daga
qarancin imani, har da na gamsuwa, gaskiya da
wadatar-zuci. Amma, mutumin da ya yalwata
zuciyarsa da Tunani mai kyau, shi ne zai iya
samun kwanciyar hankali.

Idan mutum ya yalwanta tunanin lafiya, ya kuma


ringa faxawa kansa labaranta tun daga zuciyarsa
cewar, “Ni, ba ni da wata matsananciyar Cuta”, ko,
“Ni, Jiki na lafiyayye ne akasarinsa”, ko, “da
yardar Allah ba zan bar wannan cuta ta gama da ni
ba”, to kuwa, ya tabbata, ba shakka, saqon da jikin
zai ji kenan; kuma umarnin da zuciya za ta ba shi
kenan domin ya baza makamansa na yaqin duk

150
Tunani da Inganci
wata ‘yar qwarya-qwaryar cuta. Abin fa kamar
imani ne; wanda ya yi imani da magani, toh sai
farin zatonsa na alhairi, watau, farin tunaninsa, ya
umarci jiki ya karvi maganin da zuciya guda. Haka
ma addu’a take. Wanda kuwa ya yi shakkun
magani ko addu’a, ko ya ringa zatawa kansa cuta,
to ba zai warku daga maganin cikin sauri ba, domin
tunaninsa bai karvi maganin ba, ko kuma bai
amince da addu’ar ba. Cimma waraka da samun
biyan bukatar lafiya cikin hanzari za su yi wuya ga
mai qorafi ko zafafa cuta.

Hausawa sukan ce: “Riga Kafi Ya fi Magani”.


Wannan ba qaramar shiriya ba ce ga mai tunani.
Amma, Riga-Kafi, ba shi ne kaxai ka sha magani
kafin cutar ba; a a, ka kori ma duk wani abu wanda
zai iya lahanta lafiyarka daga tsarin al’adunka.
Shaye shayenka da ciye ciyenka; barcinka da
makwancinka da mahutarka da wajen sana‘arka;
har ma da jima’inka, lallai ne su kasance masu
la’akari da lafiya. Ko juji ka ringa zubawa tarkace,
to ya qara wari. Kada ka lahantar da jikinka da
gangan, domin ba za a musanya maka shi ba.

Lallai ka kyautata jikinka. Shan Giya, Shan Taba,


Shaqar Iskar banza da shan Yaji ba qa’ida
ganganci ne. Haka cin abincin da ba qa’ida, yadda

151
Tunaninka Kamanninka
cikinka zai cika tam, ko numfashi ba ka iya yi sai
da kyar. Wannan takan matsawa huhu da zuciya
wajen aikinsu, ta kuma haddasa wata cutar in ba a
yi hankali ba. Lallai mu xauki shawarar Annabi
Muhammad (saw) wadda ta ce: “Raba cikinka gida
uku: Sulusi, ”Abinci”; Sulusi, “Ruwa”: Sulusi,
“Iska”. Haka ya ba mu shawara, cikin Kimiyya ta
hikimar kiwon lafiya. Kullum ka zama mai tunawa
da wannan batu: ‘Ci Mai-lafiya, ka yi Lafiya. Ci
Cuta ka Cutu’. Lafiyarka dukiyarka. Lafiya uwar
jiki. Kai zaka kula da lafiyarka ba wani ba.

Isashshen Barci, Motsa Jiki a-kai a-kai, abubuwa


ne masu muhimmanci sosai, kuma lallai ne a
maida hankali a kansu. Wasu na wasa da lafiyarsu
ta wajen matsantawa jikinsu da neman qure shi.
Ko inji yakan bukaci hutu da binciken lafiya loto-
loto. In ka qi kula da shi ya buga. To haka jikin
mutum, ba shi da bambamci da injin Mota, domin
an qerata ne daga tasawira da bukatun xan-Adam.
Duk abinda ka gani a halittar mutum, to Mota na
da shigensa. Haka yadda mota za ta buga daga
gurvataccen petur, mutum ma zai buga daga
gurbataccen abinci ko abin sha. Zuciyarka,
Kaburetanta. Jininka, Petur xinta. Jijiyoyinka,
Wayoyin injinta. Tumbinka shi ne Tankinta.
Rihinka kuma Hayaqinta. Yadda ka ke son ruwa,

152
Tunani da Inganci
haka take so. Yadda take son sabis, haka ka ke
bukata. Ka kula da ita, amma ka qi kula da kanka?
Ko Babur gareka, shi ma haka yake. In ba ka da su
kuma, ya fi zama wajibi ka kula da kanka da
lafiyarka, domin kai ne abin hawanka.

Zuciya Jagorar Lafiya; Lafiya Uwar Jiki; Jiki


Magayi. Duk waxannan batun Hikima mataimaka
ne a gareka wajen tunaninka gameda lafiyarka.
Tunda kyakkyawar zuciya takan yalwata lafiya,
ashe kuwa yakamata ka nutsu ka kuma tabbata
cewar kana jin daxin ayyukanka, ko cinikinka, da
hidimominka ga al’umma, iyalanka da abokanka;
ka kuma san kuxi ba su ne kaxai tushen farin-ciki
ba. A gaskiya ma, yawancin lokatai su ne tushen
baqin-ciki, musamman idan ba a aikin alhairi da su.
Lallai ne ka sami abokai na kirki masu qaunarka
saboda Allah, ko da basu kaika a matsayi ba. Ka
shiga ayyukan taimakon jama’a da taimakon kai-da
-kai da na addini, don ka farantawa kanka, ka
tabbatar cewar rayuwarka ta zama cikakkiya mai
lafiya da amfani gareka da al’umma duka.

Wanda ya mayarda lafiyarsa abokiyar rayuwarsa,


shi zai rayu cikin halayyar da zai iya neman nasara
a al’amuransa. Wanda kuma ya yi banza da
lafiyarsa, shi ne ya yi hasara. Duk wanda za ka yi

153
Tunaninka Kamanninka
hulxa da shi, amma ya lura ba ka da cikakkiyar
lafiya, to ko bai qyameka ba, to kuwa lallai zai ja
da baya a wannan hulxar. Ba mai son ya xau
kasadar ciniki ko kasuwanci da marar cikakkiyar
lafiya. Haka ba wanda yake son ya xanka amanar
al’amuransa ga wanda lafiya ta guje shi. Duk
sa’inda aka lura ba ka da lafiya, to ba shakka za a
fara nesa da nemanka a kan al’amuran mutane,
balle kuma na shugabancinsu a kowacce harka. Ko
rumfa gareka a kasuwa, ba ka da jarin da ya fi
lafiyarka, domin in ba ita ka karye. Daga nan
nasara ta vace. Duk wanda ya sake da lafiyarsa, ba
shakka, ya sake da rayuwarsa. Don haka lallai ne
mu himmatu ga lafiyarmu fiye da komai.

2.
KALAMI MAI KYAU:

Iya Magana da amfani da kalmomi masu ma’ana


da qayatarwa sukan cicciva alfarmar mutum su kai
shi sama. Haka Murya wadda ta dace da al’amarin
da ake magana a kansa; kuma cikin murya
miqaqqiya mai fidda zance taryan-taryan, ba
yawan gyaran murya, ko kaki, ko shaqar hanci,
kilisar haqora, gyatsa, balle tofarda miyau. Ko ba
komai duk waxannan xabi’u ne munana, waxanda
ba su dace a yawaita yinsu cikin jama’a ba.

154
Tunani da Inganci
Mutumin da ya san zai yi magana cikin jama’a, to
lallai a kodayaushe ya zama cikin tunanin irin
maganganunsa. Lallai ne ya yi la’akari da ma’ana
da kuma tsayawa a kan abinda ake zance. Wajibi
ne ka auna matsayin mutanen da ka ke magana da
su da gurin da ka ke magana da su; sannan ka ba su
girman da ya dace da su ta hanyar yin maganar da
ta dace da su.

Idan ka cika mutane da surutu, ko dogon bayani


tamkar mai magana da kidahumai, ko ka ringa
magana ba ci-gaba; watau, ka yi gaba, ka dawo
baya, ko kana ta susar wuya ko hammata; ko kana
ta kalle kalle, ko kana kallon qasa ko sama, to kafin
xan lokaci mutane za su qagu, wataqila ma su yi
fushi da kai. Kodayaushe ka xauka cewar mutanen
da ka ke magana da su sun san abinda suke yi, ko
da yara ne; ala-barshi, ka ba su damar tambayoyi a
qarshen jawabinka. Wannan shi zai fassaraka a
garesu ta hanyar reni ko girmamawa.

Yin magana cikin hikima da murya mai dacewa,


kuma fitatta, a hankali, takan qara martaba da
karvuwar mutum da maganarsa cikin sauqi da
lumana. Wani, da iya tsara maganarsa, daxin
muryarsa da azancinsa, ya ke kafa manufofi da
aqidunsa. Komai gaskiyar magana da

155
Tunaninka Kamanninka
muhimmancinta, in ba a yi ta cikin lafazin da ya
dace ba, sai ta yi xacin da ba mai xanxanata.

3.
TSABTA:

Shiriyarmu a Hausa da addini a kan wannan ita ce:


“Tsabta tana daga bin Allah”. Watau, Ibada ce.
Sanya tufafi masu tsabta da haske, sukan fiddo da
mutum cikin surarsa ta mai tsabtataccen tunani.
Gujewa launuka rambatsau kamar mahaukaci,
yakan fiddo da mutum a surarsa ta mai
kimtsatstsen tunani. Iya ado na azanci, ba na fariya
ba, yakan fiddo da mutum a surarsa ta mai xa’a da
daidaituwa a tunaninsa. Tsabta da nunata a
kowanne hali, manyan darajoji ne ga mai ita.
Tsabta alama ce ta farin-ciki da godiya. Qazamta
kuma alama ce ta baqin ciki da rashin godiya.

Da qazami da mai rambatsa launuka, da mai jibgo


ado wai sai ya fi kowa, duk mutane ne masu
quntatattun zucuyoyi da tunani. Idan ka danqa
shugabanci ko wani al’amari a hannunsu, to yadda
suke sa kaya, haka za su tafida shugabancin ko
al’amarin. Kuma, tuna wasu da ka sani ka gani.

** Qazami, shi ne wanda bai damu da kansa

156
Tunani da Inganci
ba, balle ya damu da wani. Bai damu da lafiyarsa
ba, balle ya damu da ta wani. Ba abinda ya dame
shi, ba kuma abinda za ka faxa ya yi tunani mai-
kyau mai-tsabta a kai, domin qazami ne.
Bambancin Jikinsa da muhallinsa da na dabba
kaxan ne, in ma akwai.

** Mai rambatsau, ya iya zama mai tsabta,


amma ta hanyar wanki kawai. Ba shi da azancin
tsari da dacewa. Idan ka bar zurfafan shirye-shirye
a hannunsa, to, sai ya hautsunasu, domin bai san
abubuwan da suka dace da juna ba.

** Mai Cin ado don ya fi kowa, mutum ne mai


son nuna isa. Idan ka ba shi dama, sai ya cinkishe
kowa do son nuna ba wanda ya fi shi. Yawancin
irin waxannan mutane akan same su da girman kai,
amma ba kasafai suka sani ba. Duk waxannan
mutane marasa tsabta ba su karvuwa ga jama’a, da
zarar an gane halayensu. Hasara ce babba, mutum
ya kasance qazami a waxannan fannoni.

Mai tsabta shi ne wanda mutane ke sha’awa, domin


bayan kullum ga shi tsaf-tsaf da shi, sai kuma ka ga
ya iya ado mai ma’ana da ban sha’awa, ko da
kayansa masu sauqi da araha ne. Ko da da yadin
alawaiyo ko akoko ne, wasu sun san yadda za su

157
Tunaninka Kamanninka
tsara shi su adance kansu, su kuma fi mai adon
siliki, amma ranbatsau bakinsa da hammatarsa na
wari. Irin wannan tsabta ko qazamta ta jiki da
tufafi, har a zuci take, domin fassara ce ta irin
tunanin mai ita. Watau, matsabtata mutane ne
masu tsari, qawata kaxan da hikimar shirye-shirye.
Su ne ababan zavi, su ne kuma masu saurin samun
karvuwa da nasara a cikin mutane. Qazamai kuwa
sune kishiyar waxannan. Ko a tsarin gemunsu,
zaka gane su, domin kamar na bunsuru yake.

A kimtse, a adane, za ka sami muhallin mai-tsabta,


ko kantinsa, ko ofishinsa, ko motarsa, ko
takalminsa, ko haqoransa da faratansa da gashin
kansa da gemunsa. Ko da ba ka san muhimmancin
tsabta ba, in ka je gun mai ita, to za ka yi sha’awar
komawa. Idan kai qazami ne, ka je tsabtataccen
guri, to nan take za ka ji a jikinka cewar ka
qasqanta. Nan take za ka ji a jikinka cewar ba
gurinka bane, ko da kuwa muhallin abokanka ne.
Tsabtar jiki da muhalli da tufafi, suke sa mutum ya
zama mai tsabtar kalami da xabi’u, ba tareda
gangancin zuci ba. Irin waxannan mutane, su ake
sha’awa; su ne masu alfarma; sune suka dace da
soyayya ko ma shugabancin jama’a. Su kowa yake
son ya kusanta, a kowacce irin hulxa da suka sa
kansu ciki. Su ne ma’abota nasara tsabtatacciya.

158
Tunani da Inganci
4.
NUTSUWA DA DAGEWA

“Alamun cimma nasara suna daga zurfin nutsuwa”.


Idan Nutsuwa ta haxu da dagewa, sukan zama
matattakalun nasara a cikin al’amuran xan-Adam,
na sana’a da siyasa da mulki da soyayya da
kasuwanci da gina iyali da yawancin sauran
manufofi na rayuwa. Kada a yi shakkun haka.
Amma nutsuwa da dagewa ba sa samuwa idan
mutum ya yarda wasu abubuwa na damuwa suka
tsinka tunaninsa. Haka, tunanin wahalu a xarikar
fafutuka, ko tunanin gazawa a gwajin farko, duka
sukan gurgunta dagewar zuciya su jawo hasarar
manufa. Da-na-sani da tausayin-kai, su ma illoli ne
masu lahanta tunanin samun nasara, kamar dai
yadda zaman banza yake dakushe qwaqwalwa.
Abune muhimmi mutum ya tashi ya ringa yin wani
abu, a kodayaushe, ko da tunanin abinda zaka yi
gobe ne, ko abinda za ka yi a wannan makon, ko a
wani lokaci mai zuwa.

Dabara ce babba, mutum ya shirya tunaninsa dalla-


dalla, a rubuce in da hali. Tsara buri a tunance, da
dabarun cimmasu a rubuce, sukan kawo gamsuwa
da sakamakon alhairi mai ban mamaki ga wanda ya
yi haka. A yayin da ka ke tunani kana rubutawa, a

159
Tunaninka Kamanninka
wannan lokacin sababbin tunani da suka fi na da za
su ringa zuwan maka. Kuma gwada ka gani!
Kowanne mutum zai iya cimma bukatunsa daidai
qarfin zuciyarsa, xokinsa, maida hankalinsa,
lissafin lokaci da hangen-nesansa.

Kada ka ringa cewa kanka, “Ba zan iya ba”, ko


“Na kasa nutsuwa”. Waxannan baqaqen tunani
sune za su hanaka ci gaba, su raunana maka
zuciyarka, su jawo maka hasarar manufofinka. A
cikin niyyarka ta fafutuka, guji cewar, “Abu kaza
sai su wane:, ko, “Wane Ni”. Duk abinda ka sa
kanka, bayan ka yi tunaninsa sosai, ka kuma tsara
dabarunka yadda za ka iya, to fita ka yi shi sosai,
da kyau ba sassautawa. “Duniyar-nana, ba ta Rago
bace”, in ji Mamman Shata.

Kai dai ka tabbata a zuciyarka cewar abinda za ka


nema, ko za ka yi, ya dace da kai. Hausawa a
hikimarsu, sukan tuna mana cewar, “Da rashin tayi
a kan bar araha”. Gwada ka ga ni. Jarumin da ya
nutsu a kan fafutukarsa, yana tareda nasara. In
tunanin shirya wani alhairi don jama’a ya zo maka,
maza tashi ka shige kan gaba wajen shirya abin.
Ba da daxewa ba, za ka ji wasu na cewa, “wallahi
ni ma na yi wannan tunanin.” Watau, suna nuna
maka cewar, ina ma su ne.

160
Tunani da Inganci
5.
MARTABA LOKACI

Duk mai cikakken hankali, to kuwa yakamata ya


kasance mai martaba lokaci, domin babu abu mai
muhimmanci irinsa. Duk abinda ka sani, a qayyade
yake a lokaci, musammam ma rayuwa ita kanta.
Haka idan lokacin abu ya shige, ba mai iya juyo shi
ya tabbata yadda yake a lokacinsa. Ba mara kishi
da rashin sanin yakamata irin wanda ya san lokacin
abu, amma ya qi, ko ya kasa kiyaye shi. Xauki
lokacin Salla a misali, ka yi tunanin me ya sa Allah
(swt) Ya tsayar mata da lokatai tabbatattu? Mecece
kuma sigarka, idan ka makara ga Sallar ba tareda
qwaqqwaran dalili ba? Daga nan ma za ka san
muhimmancin lokaci, yadda Allah Ya koya mana.

A tsarin cimma bukatunka, da hulxoxinka da


jama’a, ka xebarwa komai lokacinsa, sai in ya
zama dole ka qara, ko ka rage, domin dai ka san
cewar, wata damar ba za ta sake dawowa ba. Kada
ka ringa shirya rayuwa a hargitse ba lokaci, domin
duk abinda ba lokaci a cikin tsarinsa, to shirme ne,
fankama ce. Duk abinda yakamata ka yi yau, to
kada ka bari sai gobe. Aikin da za ka yi da karfe
huxu, to ka yi shi da karfe huxun. Mutumin da bai
san muhimmancin lokaci ba, shi da dabba

161
Tunaninka Kamanninka
bambamcinsu kaxan ne. Ni, a guna ma gara ita.

Alamar mai iya riqe nauyi


da sauke haqqi da cika alqawari,
tana daga mai iya riqe lokaci.

Duk mai vata lokaci da yawan makara, to haka


duniyar za ta tafi ta bar shi, kuma mutumcinsa ya
zube, mutanen kirki su watsarda shi a kan bai san
alkawari ba, domin kuwa bai san muhimmancin
lokaci ba. Lokaci shi ne ma’aunin rayuwa. Wanda
ya vata shi ya vata rayuwa, ko tasa, ko ta wasu.
Idan ka yarda aka vata maka shi da gangan, ka
cuci kanka. Idan ka vatawa wasu shi da gangan, ka
cuce su. Shugaban da ya makara, ba shakka bai san
haqqin jama’arsa ba, domin ya renasu. Wannan
shugaba ya naqasa. Ko harkar kasuwanci, ko ta
wani abu muhimmi, zaka shiga da wani, ya zo a
makare ba dalili qwaqqwara, to, in ka kauce masa
ka kaucewa hasara da nadama a gaba. Haka,
xalibin da ya makara a makaranta, bai kama
hanyar gina rayuwarsa ba, balle kuma wanda ya qi
zuwa sam sam.

Rashin sanin muhimmancin lokaci yana cikin


dalilan rashin ci-gaban wasunmu, har da Qasarmu.
Ma’ana watau, rashin sanin muhimmancin lokaci
shi ne ginshiqi a cikin rashin cin nasarorin
162
Tunani da Inganci
rayuwarmu da ta al’ummarmu a wasu fannonin. Ga
wasu bicanni, makara har ta zama ado. Alla-wadai da
wannan mummunar xabi’a. Bin lokaci, kamar tsabta,
yana daga ibada. To haka lokaci yake. Wanda ya san
lokaci, shi ne nutsatstse wanda zai iya tsara
rayuwarsa, ya kuma cimma burinsa a lokatan da suka
dace. Shi ne wanda ya cancanci riqe amana da
shugabanci, don ya san hakkin jama’a; kuma zai yi
masu ayyukansu a lokutan da suka dace dasu. Wanda
bai san muhimmancin lokaci ba, shugabancinsa ko
wakilcinsa ko hulxa da shi, kowacce iri ce, duk
hasara ne. Manzon Allah ya ce, “Ba na murna da mai
vata lokaci”. (Buhari, Muslimu da Abu Dawud)

6.
TUNAWAR KWAKWALWA

Iya tuna abubuwa yakan qara samuwar nasara;


yakan ciyarda komai gaba; yakan bunqasa ilmi,
farin-jini da kuma bajinta a wajen magana. Sannan
kuma yakan qarfafa yadda aka amince da mutum.
Amma, mantuwa da sakaci, sharruka ne masu
samarda duk kishiyoyin waxancan kyawawan
sigogi; su jawo jin-kunya, nadama da hasara, har a
ringa cewa mutum sususu ne, ko ba shi da tabbas.
Irin waxannan la’anta, ba shakka, sukan dakushe
siga da nasara.
163
Tunaninka Kamanninka
Duk abinda mutum ya ji, ko ya gani, a cikin
qwaqwalwarsa ake ajiyesu nan take. Shiga cikin
kwanyar, da buxe shafin abin, shi ake kira,
“Tunawa”. Ka shiga, ka kasa buxe shafin, shi ake
kira, “Mantuwa”. Waxannan abubuwa suna da
tsironsu ne a zuci, watau a tunanin mutum.

Ka daina faxawa kanka cewar, “Ai ni mutum ne


Mai-Mantuwa”; ko yawan cewa, “wallahi na
manta”. Mai irin wannan hali yana fallasa kansa ne
ta waxannan batu. Yawan faxar, ko tunanin
wannan takan sa kwanyar mutum ta dakushe, ta
qara lalacewa wajen buxo shafin abubuwan da ake
son tunanwa. A kullum ka shiga gado don barci,
ko ka tashi da safe, zai taimaka maka idan ka ringa
tunanin cewar kwanyarka ta fi xazu, ko ta fi jiya
iya tuno da abubuwa. A halaye irin waxannan, ka
rinqa qoqarin tuno da duk abinda ka yi, ko ka ji, a
yau ko jiya. Lallai ne ka fara gaskanta kanka da
qwaqwalwarka. Kada ka ce komai sai ka rubuta
sannan za ka tuna.

Idan ka yi niyyar yin wani abu, maza ayyana


kanka kana yi. Wannan dabara za ta iya sa abin ya
fi zaunuwa a kwanyarka ka kuma tuna abindazarar
lokacin yinsa ya zo. Idan kana son ka tashi da
karfe biyar na asuba, faxawa kanka, cewar, “Zan

164
Tunani da Inganci
tashi karfe biyar”, kamar sau uku kafin ka kwanta,
kuma ka ayyana kanka kana tashin. To ba shakka, a
sannu-da-sannu, za ka iya saitin kwanyarka ta kaxa
maka qararrawa da qarfe biyar. Za ka yi mamakin
koyawa kanka tunawa da abubuwa ta wajen
ayyanasu. Idan ka saba da yin ibada a kan lokaci,
alal misali, da lokacin ya yi, za ka ji kwanyarka
tana kaxa maka qararrawar lokacin ibadar.
Waxanda suka tsaida Sallah a kan lokaci, ko wata
xabi’a a lokaci tsayaiye, sun san haka.

Idan kana da wata lacca da za ka ba yar, to ka


gwadata kai kaxai a xaki, tamkar jama’ar na
gabanka. Haka kuma, ka yi tambayoyin da ka ke
zaton za a tambayeka -komai xacinsu- kuma ka ba
yar da amsoshinsu da misalai da qididdiga da
isharorin da suka dace. Za ka yi mamakin yadda
yin haka zai taimaka maka wajen qayatarda mutane
a lokacin da ka ke yin maganar a gabansu.

A qarshe, kada ka ringa cewa, “Zan yi qoqari in


tuna” ko, “Ina fatan zan tuna”. Ka ce kawai: “Zan
Tuna”. Ta wannan qwaqqwaran tunani cike da
niyya tabbatacciya ne kaxai za ka iya sarrafa
qwaqwalwarka yadda kake so. Tamkar mai son
hadda ne. Tuna tasawirar shafin da salon rubutun,
makamai ne a filin hadda. Idan aka sanka da riqe

165
Tunaninka Kamanninka
abubuwa, watau rashin mantuwa, take za a yarda
da al’amuranka, a kuma ba ka dama wadda ta
dace. Idan an san ba za ka manta ba, to kuwa ba
za a yi maka wasa ba, ba kuma za a gujeka ba.

Amma idan aka sanka da mantuwa, to ka gama


yawo. Ba wanda zai xora rayuwarsa da sauran
al’amuransa a hannunka, don mantawa za ka yi.

7.
SANIN ABINDA
DUNIYA KE CIKI

Sigar mutum da karvuwarsa ga jama’a, ko kuma


nasa iya zaman da jama’a, suna da dangantaka da
irin abubuwan da ya sani da kuma waxanda ya
shiga cikinsu a wasu gurare dabam, ba qauyensu,
ko unguwarsu, ko garinsu kaxai ba.

Mukan haxu da mutane da yawa, waxanda


kidahumancinsu da jahilcinsu a kan yadda sauran
qasarsu ko duniya take ciki, sukan vata
al’amuransu, su maishesu baya a ma’auninmu.
Rashin sanin abinda duniya take ciki, yakan
dakushe ilmi, ya qulle maka damar fahimtar wasu
abubuwa da za su iya taimakonka da sana’arka.
Idan ka tafi haka sai ka yi ta fankama cikin

166
Tunani da Inganci
jahilcin rayuwa da abubuwan da suke da
muhimmanci a gareka. Ko kai Malami ne, ko xan-
Kasuwa ne; ko kai Mai-Mulki ne, ko Ma’aikaci ne;
zurfin fahimtar yadda duniya take ciki abune
muhimmi qwarai da gaske. Misali:

** Malami wanda yake qoqarin bayanin wata Aya,


ko wani Tarihi a kan mulukiyar Rum, amma fa bai
ma san inda Rum xin take a tasawiyar duniya ba,
bai kuma san abinda take ciki a da ko yanzu ba. Ba
shakka, bayaninsa ba zai qayatar ba, domin shi
kansa bai san abinda yake zance a kai ba. Amma
Malamin da ya san wani abu dangane da inda take
da abinda ya faru ko yake kuma faruwa cikinta a
tarihi da kuma a yau, zai iya yin bayani yadda
masu sauraronsa za su qayatu, har ma ya iya
kwatanta lokatan Ayar da lokatan wannan zamani,
ya fidda tafsiri tabbatacce. Rum ta Turai kenan.

To xauki Ayoyin Kimiyya, ko na Mulki, ko wata


matsala dabam. Kamar dai Malamin da yake son
bayanin wata Aya, ko muhawara a kan, “Nunqayar
Duniyoyi a Sararin Samaniya”, amma ko kaxan bai
karanci, ko saurari wani abu daga fannonin wannan
Ilmi ba. To ba yadda za a yi ya yi bayani a kan
abinda bai sani ba. Wasu suna son su nuna Sani,
amma ko abinda ke faruwa a garinsu ba su sani ba.

167
Tunaninka Kamanninka
Daga son burga, sai su zama masu kuskure da jin
kunya a maganarsu; ko ma su qara vatarda wasu.

** Xan-Kasuwar da ya san Japan, ko China da


tarihinsu da al’adunsu, da yadda abubuwa suke
tafiya a can a yau, ba shakka, zai iya harkar
kasuwanci da su, su kuma qayatu wajen ilminsa na
al’amuran rayuwa irin tasu. Ko a Hausa, mukan
ce: “Wanda ya sanka, shi ya damu da kai.” Haka,
shi zai ci ribar hulxa da kai.

** Mai-Mulkin da ya tunkari al’amuran wata


Qasa wadda bai san abinda take ciki ba, ba yadda
za a yi ya sami cikakkiyar nasara cikin hulxarsa da
wannan qasar. Ko da a hira ne, sarki ya nuna ya
san wani abu daga al’amuran qasar da tarihinnta,
kuma ya san abinda ake magana a kai, ya san
abinda ke faruwa a wasu gurare, ba shakka,
wannan sarki mai iya qayatar da abokan
maganarsa ne, balle a ce baqinsa ne daga can.
Wannan ilmi nasa, ba qaramar kadara ba ce tareda
shi da qasarsa, a guraren da suka dace.

Wanda ya san abinda duniya take ciki, ya kuma


nemi ilmin abubuwa dabam-dabam, zai tarar cewar
duk waxannan abubuwa ashe makamai ne da zai
iya amfani da su ya fidda kansa daga qangin

168
Tunani da Inganci
kaxaita da jin kunya. Sanin qasashen Bosnia da
Chechnya; Kosovo da Albania da Macedonia;
Afghanistan da Pakistan da Iraq da Palaxinu;
tarihinsu da abubuwan da ke faruwa yanzu da
dalilansu. Sanin tarihin qasashen Gabas-ta-tsakiya
da qasashen kewayenka da al’amuransu; kai hatta
fahimtar sauran qabilu da al’adunsu a qasarku, duk
ilmi ne mai xinbun yawa mai kuma amfani. Ita
kanta hirar duniya da abinda take ciki abar
qayatarwa ce, abar wasa qwaqwalwa ce tsakanin
abokai; abar hana zaman banza ce. Ba hasara da
takaici irin abokanka suna hirar da ba ka fahimta
ba, alhali kuwa kana da damar kai ma ka sani,
amma ba ka kula ba. Haka ba hasarar rayuwa irin
ta mutumin da yake da damar kewaya garuruwa, ko
ma qasashen duniya, amma bai je ba, yana kuma
da hali. Yawon duniya da manufa, ba qaramin ilmi
ba ne. Lallai mutane masu hali su tashi su je.

Sanin abinda duniya take ciki, da kewayata -in


akwai hali- sukan buxe sababbin qofofin alhairi iri-
iri; sukan kuma ba da wadatar-zucin cewar an
karanta, ko an ji, ko an je wasu daga cikin guraren
da Allah (swt) Ya samar a doron wannan duniya
tamu. Ganin yadda ‘yan-Adam suka bambanta;
launi-launi; harsuna iri iri; mutane kima-kima;
al’adu da addinai birjik, ba qaramar riba ba ce a

169
Tunaninka Kamanninka
rayuwar mutum. Wanda ya yi xamara da ilmin
sanin abinda duniya ke ciki, ya yi damara mai
qarfi, kuma nasarar rayuwa ba za ta butulce shi ba,
domin ya kiwata tunaninsa da ilmi mai amfanin
gaske wanda zai amfane shi ta kowanne juyi.
“Yawon duniya mafarki ne, a tafi a dawo”, in ji
Mamman Shata.

8.
FADAR GASKIYA BA TSORO:

Allah (swt) Shi ne, Gaskiya. Haka muhimancinta


yake. Gaskiya xaya take a kodayaushe, kuma
wanda yake faxinta saboda Allah a guraren da
suka dace, to, kada ya ji tsoron komai. Tunda ita
Gaskiya xaya ce, to kuwa ashe duk sa’inda ka
maimaitata, ba za ta canja ba. Amma qarya fa?
Duk lokacin da ka maimaitata sai ta canja, kuma
sai an fahimci karkacewar maganar da ka ke yi, ko
badaxe-ko-bajima. Marigayi, Sa’adu Zungur, yana
waqe yana cewa: “In za ka faxi, faxi gaskiya;
komai taka ja maka ka biya”. Hikimar wannan
baiti ya bayyana komai.

“Idan ka faxi Gaskiya yau,


ba ka da abinda za ka tuna gobe.”

170
Tunani da Inganci
Kullum ita kaxai ce a muhallinta, ba wani abu sai
ita. Duk lalacewar jama’a, suna darajta Gaskiya,
faxarta da aikatata. Haka kuma sukan qyami
maqaryaci, duk lalacewarsu. Da zarar mutane sun
fahimci halayenka, to haka za su xauke ka tareda
aqidunka. Kodayake maqaryaci ya fi saurin
burgewa da karvuwa, amma kuma saboda “Qarya
fure take yi, ba ta ‘ya’ya...”, burgar wannan
maqaryacin ba za ta yi qarko ba. Mai son kafa
gaskiya a al’umma, da kuma yawan faxarta duk
inda ta dace a faxeta, yakan yi wahalar karvuwa,
saboda marasa sonta a cikin al’umma yawanci su
ne masu gudanar da al’amuran al’ummar. Amma,
da zarar an fahimce shi sosai, to kuma yawancin
jama’a gunsa za su koma, ko da ba da gangar
jikinsu ba, to da ruhinsu da kuma girmamawarsu.

Mun dai gamsu da sanin cewar, shugabanmu,


Annabi Muhammad (saw), da Gaskiya ya kafa
sunansa, da kuma ita ya kafa addinin Allah (swt).
Da an tava shaidarsa da qarya, ko da guda xaya ce,
da addinin bai karvu ba, balle ya qure tsawon
lokaci. Da sai kafiran su ce, “Haba! Wa zai saurarai
maqaryaci!” Wannan ma Aya ce wadda ta cancanci
a yi nazarinta da tunani mai zurfi.

Mai faxar gaskiya, ya kuma aikatata, ba zai yi

171
Tunaninka Kamanninka
hasara ba, domin yawancin hasara takan haifu ne
daga tsari na qarya, ko na cuta. A al’umma wadda
ta xau gaskiya tamkar dukiyarta, ba a sata balle
fashi da makami. Shugabanni da suka sa gaskiya a
gabansu, to ita ce za ta zama makarin dukkannin
sharrin ‘yan-adawarsu, ko da bayan mulkinsu.
Gaskiya tana da ‘yaya da yawa kuma duk na
alhairi. Adalci, misali, xa yake gareta, domin in ba
ita ba shi. Haka alhairi shi kansa. Ba yadda za a yi
mai kwatanta Gaskiya ya tave, komai talaucinsa
domin ita take gamsar da Ruhi ta huro iska mai
ni’ima mai kuma bunqasa wadatar zuci. “Gaskiya
Ta fi Kwabo”, inji masu iya magana, domin ita,
kishiyar kuxi, ba ta qarewa, ba ta jawo masifu da
rigimu. Hasalima, ita ce maganinsu duka. Ba
abinda ya fi ta haske. Duk kuxin maqaryaci, talaka
mai Gaskiya ya fi shi. Ba zuciyar da za ta shiga
duhu in ta yi riga da ita. Da zarar an fahimci kai
mai ita ne, to nasara tuni ta zama taka, domin kai
ne abokin hulxa.

9.
TUNANIN FAFUTUKA
DA GYARA SANA’A

Farin tunani shi ne wanda yake wanke zuciyar


mutum daga duk wasu abubuwa munana, ya kuma

172
Tunani da Inganci
cetarda ita daga halin gazawa. Ba illa ga mutum
irin yin tunanin gazawa, ko kuma ya ringa yin
zaton wata illa tareda shi, ba tareda cikakken nazari
ba. Sai ka ji mai niyyar tafiya yana cewa, “Abinda
ma Jirgin latti zai yi”; ko, “Qarshenta ma a yi
Ruwa”, ko, “Watakila ma tafiyar banza zan yi”.
Wani lokaci sai ka ji xan-Kasuwa yana cewa: “In
an kawo kayan ma faxuwa za a yi”. Ko ka ji Mai-
neman aiki yana cewa: “Da kyar zan sami aikin
nan”, ko, “Wannan aikin ya fi qarfina, ba zan iya
ba”. Ko ka ji mai sana’a yana cewa, “wallahi na
tsani wannan sana’ar”, ko ma ya ringa jin kunya
ana danganta shi da ita. Dukkaninsu kaiconsu!

Yawancin waxanda ba sa zaton nasara tun kafin su


tavuka, to ba sa samunta ko sun tavukan. Irin
waxannan mutane ne baqin tunaninsu yake sa wa
su yi ta kura-kurai saboda raunin zuci, har sai
hasarar ta wanzu, kamar dai yadda suka ayyanata
tun farko. Da ma ita suke zato, to kuwa ita za su
tarar. Ko da nasara ta samesu a wannan xawainiya
ta su, ba za ta yi qarko ba, domin ba za su riqe
martabar da hanneye bi-biyu ba. A dangantakar
Tunani da Halayya, idan ka nemi lalura sai ta zo
maka; idan ka ayyana zazzabi sai ka ji shi; idan ka
tsoraci mutum sai ya azabtaka; idan ka nemi barci
sai ya kamaka; idan gabanka ya faxi an gama da

173
Tunaninka Kamanninka
kai. Kada ka yarda tunanin gazawa ya sami gurbin
da zai zauna ya yi saqarsa a zuciyarka. Ko menene
qasqancin sana’arka a idanun wasu, lallai ne ka
xauketa da qarfi da muhimmanci domin ita ce
sana’arka. Idan ka girmamata, ita ma wataran za ta
girmamaka. Idan kuwa ba ka sonta, ko ba ka jin
xaxinta, to canjata maza. Lallai ne ka zamto mai
jin xaxin abinda ka sa a gaba da sana’arka.

Maiyiwuwa ne ka daxe kana ta tunanin cewar


rayuwa ba ta kyauta maka ba. To tashi ka tunkare
ta; xauki makomarka a hannunka. Idan duniya ta
tunkuxaka, kai ma tunkuxota, har sai ta ba ka guri.
Jin cewar wani ya fi ka a abinda ka iya, shi ke sa
wa ya bar ka a baya. Tunanin damuwa da ‘ya zan
yi?‘ hasaru ne manya; kada ka yarda su ci
agararka, su yanke hanzarinka ta wajen dakusarda
zuciyarka da cin qarfin fafutukarka.

Lallai ne duk mai son tunkarar wahalun


al’amuransa, da niyyar samun nasara, ya auna su
sosai, ya kuma yi tunani mai zurfi a kansu, sannan
ya tsara dabarun kuvuce masu ta hanyoyin da za su
inganta sigarsa da mutumcinsa, sannan ya tunkare
su gaba-gaxi. Kada mutum ya yarda shi banza ne,
don an faxa masa, ko an nuna masa haka. Kada ka
sake cewa “Ba yadda zan yi”, muddin a zuciyarka

174
Tunani da Inganci
ka san ba haka bane. Takaicin da ba zai gyaru ba,
kamar rasuwar masoyi, ko wata kevavvar hasara,
ko cutar ajali; sune ake yin haquri a dangana, don
imani ya qarfafa, zuciya kuma ta quduri niyar ci-
gaba da rayuwa tareda taimakon Allah. Lallai ka
zama gwarzo a filin dagarka.

Al’ada ce mai-kyau, mutum ya yi nazari a kan


waxanda yake ganin sun yi nasara cikin rayuwarsu,
in dai ta dace da burinsa da kuma tsarinsa. Ka
fahimci ya suka yi? Me suke da shi wanda ba ka da
shi? Dama can suna da abin, ko kuwa ya aka yi
suka samu? Kai kuma ya za ka yi? Kwaikwayon
wanda ya ci nasara ba aibi bane; yi masa hassada
ne aibi. Mai hassada kuwa a cikin hasara yake kane
-kane a kodayaushe. Idan kana neman shawara,
jeka ga wanda ya sami nasara a fannin burinka.
Nemi direba ya koya maka tuqi.

Da ka fara fafutuka da addu’ar Allah (swt) Ya


tallafa maka, kuma ka daure ba ka karaya ba, kuma
ka sa nasara da qwazo a zuciyarka, to kuwa nasarar
tana tareda kai. An ce: “Mai nema yana tareda
samu”, amma, “in Jarumi ne”. A rayuwa, mutane
suna ganin abubuwa iri-iri; wasu su gamsarda su,
wasu kuma su nadamarda su. Amma yawancin
fassarar nasara ana yinta ne da son kai ba tareda

175
Tunaninka Kamanninka
zurfin tunani a kanta ba.

Wasu sukan kafa ma’aunin nasara yadda suke


sonta ba tareda la’akari da abinda yake maiyiwuwa
bane a halin da ake ciki. Sai su kikkivo buri ba
azanci ba awo, in sun kasa samun nasara su fara
qorafi. Dá sun yi tunani dá sun fahimci laifukansu;
dá kuma sun binciki burinsu da niyyar gyara shi.
Lallai ne masu tunanin laifukansu ne suka jawo
wahalunsu ko hasararsu, su tsarkakar da zuciyarsu,
su daure su nemi gafara daga waxanda suka yi wa
laifin, ba tareda noqiya ba. Tunanin laifi,
musammam ma wanda ka aikatawa wani ba ka
nemi gafara ba, yakan hanaka sakat, ya sa ka ringa
gudun mutane, ka kuma kasa neman shawara da
taimako a kan harkokinka. Managarci ne yake
neman gafara ba alkaba’ibi ba. Idan ka nemi gafara
daga mutum, ko bai yi maka ba, ka ci riba, tunda
ka yi abinda yakamata, kuma hankalinka ya
kwanta. Allah (swt) kuma Shi ne Alqali tabbatacce
a muhimmiyar Rana.

Kada mutum ya ringa cewar, “Mu dama Matalauta


ne”, ko, “Iyayena talakawa ne, ta ina zan arzurta?”
Wai Shin, ba ka ji Allah (swt) Ya na cewa: “Shi ne
Mai fidda mai-Rai daga Matacce” ba? ‘Ya’yan
Matalauta nawa ne suka kuxance a gabanka?

176
Tunani da Inganci
‘Ya’yan Jahilai nawa ne suka zama shaihunnai a
idanunka? ‘Ya’yan Talakawa nawa ne suka zama
Sarakuna, Ministoci har da Shugabannin-Qasa a
zamaninka? Duk waxannan masu “Rai” ne daga
“Matattu”, amma ba haka siddan ba. Kai ma tashi
tsaye ka ga ikon Allah (swt). Ba abinda ba za ka
iya zama ba, in dai abin ya dace da kai, kuma ka
neme shi ta hanyoyin da suka dace.

Lallai duk mai son nasara a rayuwarsa, to ya


gujewa macewa daga rayuwar tasa, ta hanyar tashi
tsaye da yin gini a kan alhairi da baiwowin da
Allah (swt) Ya samar tareda shi. Ba wanda Allah
(swt) Ya halitta, ba tareda Ya ba shi makami da
damar inganta kansa ba. Idan ka qi fahimtar
makaminka (watau, wata baiwa da Allah Ya yi
maka), ko ka fahimceta amma ka qi amfani da ita,
to, kuwa ko badaxe-ko-bajima, sai ka shiga
wahala, in dama ba a cikinta kake tuni ba. Kaicon
wanda ya san zai iya yin wani abu na halal domin
ya ci da kansa gaba, amma ya qi yi don jin kunya,
lalaci ko wani dalili mara qarfi dabam. Kai za ka
wahala, kuma kai ne za ka zargi kanka da aibinka.

Ka sarrafa baiwar da Allah (swt) Ya yi maka wajen


inganta kanka, ka kuma taimakawa wasu duk
sa’inda dama ta samu. Da mulki, da dukiya, da

177
Tunaninka Kamanninka
qwaqwalwa mai kaifi, da iya waqa, da iya
magana, da qarfin jiki (qarfin tuwo), iya noma, iya
qirqiro labarai, gudu, iya bal, iya talla; ban dariya;
iya saqa ko jima ko qira ko xinki; iya girki; kai, ko
mecece baiwar da Allah (swt) Ya yi maka, idan ba
ka yi amfani da ita ka inganta rayuwarka ba, to, ka
yi babbar hasara.

Wani daga dako yake arziki har ya sai manyan


motocin sufuri, don ya fahimci cewar Allah (swt)
Ya yi masa baiwa daga qarfin jikinsa. Sai ka ga
Gyartai ya fara sayar da qwarya, domin bai raina
iya xinketa ba. Wataran sai kantin kwanuka. Sai ka
ga Tela ya kafa masana’antar xinki, don bai raina
sana’arsa ba. Da wasu Mawaqanmu ba zunxe suke
yi ba, da yanzu suna cikin manyan masu kuxinmu.
Da wasu masu iya Girki a cikinmu ba daudu suke
ba, da yanzu sune masu gudanarda manyan gidajen
abincinmu. Da masu iya Magana a cikinmu ba
roqo ko sharri suke ba, da yanzu sune sha’awar
kunnuwanmu. Da wasu masu kuxi a cikinmu ba
almubazzaranci suke ba, da yanzu ba wanda yafi
su. Da Masaqanmu da Maqeranmu da
Majemanmu ba su rena sana’unsu ba, da yanzu
kayansu muke sawa. Da kowa ya xau sana’arsa da
mutumci, kuma kowa ya girmama sana’ar wani, da
yanzu ba haka ba.

178
Tunani da Inganci
Baqaqen tunani da ke sa a raina sana’a ko a
watsarda ita jin cewa ita wulakantacciya ce, suke sa
mu koma baya, masu sana’ar su lalace, al’umma ta
lalace. A hankali, har sai waxannan sana’un su
vace mana, ko wasu can su xauke su, su adana su
su kuma ci ribarsu muna zaune muna kallo. Sai ka
ji wani wawa wanda ya qi neman aikin yi, amma
yana kyamar sana’ar wani. Sai ka ji ya ce, ‘ai wane
mahauci ne’ ko, ‘ai gyartai ne’. Ya manta in ba su
yawancinmu ba za mu ci nama ba, ba kuma za mu
iya sayen sabuwar qwarya duk sa’inda tamu ta
fashe ba. Irin wannan hassada da rashin hankali, ba
qananan illoli suke yi mana a cikin wannan
al’umma tamu ba.

Amma kyautata sana’u da alfahari da su; tareda


binciken baiwoyin da Allah (swt) Ya yi wa mutum
da kuma amfani da su cikin hikima da alfahari da
hazaqa, su ne dangin fararen tunani masu kawo
maslaha da arziki a cikin al’umma. Dagewa da
sarrafa rayuwa da duk baiwar da Allah (swt) Ya
bayar ta hanyar kirki sune a’ala, kuma sune shukar
da za ta tsirar da furannin nasara ga wanda ya gane.
Duk wanda ya girmama sana’rsa da ta wasu, ya
kuma yi fafutuka a kanta, to a hankali zai ga
sakamakonsa na alhairi da gamsuwa da kai.
Wannan shi ne mai nasara.

179
Tunaninka Kamanninka
10.
KORAR HASSADA A TUNANI

Son-kai da ganin-qyashi mugayen abubuwa ne,


kuma sukan dakusarda arziki, ta wajen haifarda
hassada. Jin ba wanda ya dace sai kai; ko jin
nasarar wasu hasararka ce, ko hasarar wasu ita ce
ribarka ko nasararka, ba munin da ya fi su. Mai
irin waxannan tunani shi ne mai hassada, wanda in
dama ta samu sai ka ji ta a bakinsa da ayyukansa.
Irin wannan mahassadi shi ne la’ananne wanda zai
tararda nadama a rayuwarsa ko badaxe ko bajima.

Idan kai mai wannan hali ne, to wanke kanka nan


da nan, ka fara xaura niyyar taimakon wani, ko
yaya, ka ringa tunanwa kanka cewar hassada
muguwar xabi’a ce. Da ka ji ka fara tunaninta a
kan wani ko wasu, maza ka tsaida wannan tunanin,
ka tuba ka bar wa Allah (swt) al’amuranSa. Aikin
alhairi daidai qarfinka ba qaramar nasara ba ce a
tareda kai, domin zai sa ka ji a ranka kai mutumin
kirki ne, ka kuma ji cewar kana kusa da Allah
(swt). Aikin sharri kuwa, shi zai sa ka ji lallai kai
mutumin banza ne, wanda ya yi nesa da Allah
(swt). Ba mai azabta kansa irin wanda ya san shi
mutumin banza ne, ba sai an faxa masa ba.
Wannan ya yi matuqar hasara. Duk mahassadi

180
Tunani da Inganci
yana cikinsu, kuma ya sani. Kullum ransa a vace.

Wanda ya yi tsaf cikin tunani, fi-sabilillah, kuma


zuciyarsa ta tabbatar masa, tana shaida masa cewar:
“Kai mutumin kirki ne”, to wannan mutum ya
cimma falalar rayuwa da wadatar zuci. Amma
wanda ya bincika kansa ya tarar da kishiyar haka,
tilas ya farka ya canja salon rayuwarsa. Irin
wannan auna kai, ba qaramar riba take kawo ba.
Lallai fa ka tuna: Ba wanda ya sanka fiye da kai;
kuma ba ka da abokin shawara fiye da kai. Ya rage
naka ka farka, ko ka ci gaba da barci a gwalalon
nadamar rayuwa da qaskancin matsayi ta hanyar
hassada. In wani abune ya xaure maka kai, nemi
shawarar wanda ka san masoyi ne, kuma ya san
abin. Tashi ka taimaki kanka tun kana da lokaci.

Farin Tunani da aikata alhairinsa, sukan taimaki


zuciya, su qara mata qwazo da zaton nasara a
dukkannin fafutukar da za ta yi. Baqin Tunani
kuwa da aikata sharrinsa su ke lahanta zuciya, su
hanata zaton nasara, su kuma sa ta cikin fushi da
nasarar wani. Lallai mutum ya faxawa kansa
Gaskiya, ya bar tunanin hassada ya nemi nasa
arzikin. Lallai ne mutum ya roqi Allah (swt) Ya
taimaka masa kamar wane, ko ma fiye da wane,
idan shi mai sha’awar wanen ne. A cikin duk

181
Tunaninka Kamanninka
lokutan da mutum yake yin hassada, ba shakka a
irin waxannan lokatan, yana cikin masifu huxu ko
ma fiye da haka, waxanda ya sa kansa ciki:

i: Yana cikin tuhumar Allah (swt) a kan


abinda Ya hukumtawa wani. ‘Don me Allah Ya ba
shi?’ Tuhumar Allah, raina Allah ce, kuma ba
qaramin vata bane. Wa’iyaz Billah! Allah Ya tsare
mu da wannan babban kafirci, amin.

ii: Yana cikin mugun baqin ciki da azabta


kansa, domin ransa a vace yake cikin fushi da
nasarar wani. Wannan ba qaranar cuta bace, wadda
za ta iya haifarda ciwon zuciya da halaka.

iii: Yana cikin hasara, domin hassadar tasa ba


za ta canja komai ga wanda yake wa hassadar ba.
Wannan ba qaramin vata lokaci bane.

iv: Yana cikin maqurar takaici, domin a


daidai wannan lokacin, wanda ake yi wa hassadar
bai san ma ana yi masa ba; yana can cikin
bushashar nasararsa da arzikinsa. Kuma Allah
(swt) Ya kan dubi wannan hassadar ya qara
nasarar da arzikin, ala-barshi mai hassadar ya
mutu. Da ma an ce, “Hassada ga mai rabo taki”.
Hassada, ba shakka, ba qaramar hasara ba ce.

182
Tunani da Inganci
Idan abu ya fi qarfinka, kuma ka gwada ka gwada
amma babu alamar cimma maslaha ko nasara, to
sake mai da al’amuranka wajen Allah (swt), ba
tareda hassada ga waxanda suka sami nasasar ba.
Amma lallai ka ci gaba da son jama’a, sha’awar
masu nasarar, ka kuma kare mutumcinka, imaninka
da ibadunka. Lallai ne ka daure ka ci gaba da
fafutukarka, ko da ka canja bukatunka ne. Ka
tabbata kana cikin yanayin zuci mai-kyau da kuma
yawaita zaton alhairi, domin “wani hanin baiwa
ce”, in ka yi tunani a gaba.

Kada ka yarda ka raunana wajen zaton canji na


alhairi daga Allah (swt), ta hanyoyin da bá ka zato,
amma waxanda su ne mafi alhairi a gareka. Allah
(swt) Ya karanci zuciyarka, Ya riga Ya zavar maka
rayuwa mafi dacewa a gareka, in dai ka amince ka
bar al’amuranka a hannunSa. A Halayya irin
wannan, ka roqi halayyar Annabi (saw), domin sai
Allah (swt) Ya fara yi maka kyauta da Wadatar
Zuci ta zama Ganimarka”. Nan da nan sai ka ga ka
fara tunawa da sauran baiwoyin da Allah (swt) Ya
yi maka, waxanda za ka iya sarrafasu yadda suka
dace domin ka cimma sabon burinka. Maiyiwuwa
ne a nan arzikinka da bushashar rayuwarka suke.
Kai ne ba ka bincika ba; ko kuma sai yanzu Allah
(swt) Ya buxa maka saninsu, domin sai yanzu

183
Tunaninka Kamanninka
lokacinsu ya iso. Allah (swt) baYa barin mai
bukatar alhairi a cikin nadama. Amma mahassadi
kullum a cikinta zai kasance. Kowa ya san kansa,
kuma kowa ya san abinda nake magana a kai. Da
jama’a sun fahimci ba ka da hassada ko ganin
qyashi, toh ka tabbata ka ci babbar nasara. Kai ne
nasu a kowanne lokaci, ko ba ka san hakan ba.

11.
YAKANA DA KULA DA HAKQI

Waxannan manyan halaye na-gari ba su da


bambanci da junansu sosai, kuma rashin xaya daga
cikinsu ba qaramar hasara ce ga Halayyar mutum
ba. Rashin Yakana, shi yake kawo taka haqqin
wasu; ka ga mutum yana ta wahalarda mutane,
yana wulaqantasu, ko yana matsanta masu, ko
kuma yana quresu. Mutumin da ba shi da Yakana,
shi ne ya yi hasarar muhimmiyar madafar rayuwa
mai qarko, komai qudinsa ko mulkinsa. Mutumin
da xabi’arsa ita ce ya keta haddin wasu, to kuwa
zai tadda baqin-ciki, ko ba-daxe ko ba-jima.
Rashin Yakana da rashin Sanin Yakamata uwarsu
xaya ubansu xaya. Sukan kashe aure; sukan kori
‘yan’uwa har ma da abokan arziki; sukan jawo
hasarar sana’a da baqin jini irin wanda ba a saba
yinsa ba.

184
Tunani da Inganci
Mafi yawancin mutane ba sa son a wulakantasu ko
a qaskantarda su a nuna masu ba su isa ba.
Waxannan munanan xabi’u kuwa su ne halayen
mutane mara Yakana. Waxanda aka wulakanta xin
tilas ne su yi fushi, in dai suna da mutumci, kuma
qiyayya ta iya shiga tsakani in ba a yi hankali ba.
Jama’a sun qi jinin a taka haqqinsu, a hana su
damarsu da ‘yancinsu; a hana su sakewa da
walawa. Waxannan kuwa xabi’un mara Yakana ne.
Hankali ne a tsammaci mutane za su fusata idan
aka takurasu, ko ma su kai duka idan tura ta kai
bango. Yawancin mutane ba sa son mai girman-
kai, mai burga da son nuna isa. Waxannan kuwa su
mara Yakana ya gawurta a kai. Tilas a tsammaci
mutane za su tunzura idan aka yi masu girman-kai,
kuma su mai da martani irin nasu duk lokacinda
dama ta samu. In sun yi haka, wa zai zarge su?

Yakamata mutumin da yake neman gyara


rayuwarsa da arzurtata ya san Yakana, ya kuma
nunata a halayensa da xabi’unsa. Kada ka ce sai ka
qure wani, ka nuna masa bai isa ba, sannan zai san
ka isa. Kada ka ce ba wanda ya isa ya yi magana in
kana zaune. Kada ka qi sauraron mai ba ka haquri,
sai in ba yadda za ka yi. Kada ka fizge abu daga
hannun wani don kana zaton bai isa ya riqe abin
ba; karvi a hankali cikin xa’a. Kada ka shiga xakin

185
Tunaninka Kamanninka
mutum gaba-gaxi ba izninsa, don shi yaronka ne,
ko xanka ne. Kada ka tofarda miyau a gaban mai-
qurji. Kada ka yi latti don ka isa, ko don mutanen
ba su isa a idanunka ba. Kada ka baxawa jama’a
qura don kana cikin mota, shige a hankali. Kada ka
zagi mutum don ka san ba zai iya ramawa a fili ba.
Kada ka qwacewa yara alawarsu ko ka zaluncesu
don ba su da qarfin ramawa. Kada ka kushe aikin
wani don son muzanta shi. Kada ka washi abin
yabo. Kada ka ci fuskar wani, ko ka sa a yi masa
dariya don kana zaton bai isa ba. Kada ka cinkishi
mutane da surutanka, don kana zaton ba yadda za
su yi. Kada ka wulakanta iyayenka da iyalanka, ko
ka hana su daga arzikin da ka ke da shi; ku ci tare
shi ne qarkon arzikin. Kada ka zagi na gaba, ko
yawan kushe masa, don kawai ba ka sonsa, ko ba
ya gurin. Jeka ba shi shawara in za ka iya, ko da ta
hanyar wani ne. Kada ka wulakanta masu nema a
gurinka ko marasa galihu don kana zaton ka fi su.
Ba su taimako, ko ka ba su haquri da murya mai
taushi. Kada ka zalunci wani ko wasu don kana
zaton ba yadda za su yi da kai. Kada ka qi cika
alkawuranka don kana zaton ba yadda za a yi da
kai. Lallai ne ka kiyayi kanka.

Duk abinda ka san kai ba ka son a yi maka, to,


kada ka yi wa wani. A wannan duniya, matsayinka

186
Tunani da Inganci
zai iya canjawa nan-da-nan daga matsayin mutum
gingirim mai tsoratarwa zuwa na abin tausayi. In
mulki ne, akwai ranar qarewarsa. In kuxi ne, akwai
inda ba su isa ba. In kyau ne, akwai wanda ya fi ka.
In Ilmi, kai koma bayan wasu ne. Ko menene ka ke
da shi, mutumci ya fi shi, kuma wasu da yawa sun
fi ka abin. Maza zubar da girman kanka, yadda za
ka dace da jama’a ka sami walawar rayuwarka. Ba
sai ka nuna ka isa sannan za a san ka isa ba. Wanda
bai isa bane yake son sai ya nuna. Mutane sun san
sirri da matsayin kowa. Mai Yakana ya san haka.

Mutum mai Yakana shi ne ya san dabarar rayuwa


mai falala, kuma Yakanarsa takan sanyayarda
zuciyarsa ta kuma jawo masa alhairi daga duk inda
ba ya zato. Yabon abin yabo; godewa abin godiya;
girmama masu mutumci; tausayin mawahalta;
ladabta na gaba; yalwata murmushi da miqa
hannun gaisuwa da na kyauta; halarta a kan lokaci;
cika alkawari; bin qa’ida da dokoki; gyara kuskure;
ba wa wasu dama, qauracewa guraren da ba su
dace da kai ba -duk halaye ne nagari. Mutanenda
aka yi masu Yakana da xa’a, sukan ji daxi, su
kuma saka da yabo ko ma da wani alherin dabam.
Wanda ya yi Yakanar shi ne ya ci riba mai yawa,
mutumcinsa da kimarsa su xaukaka a idanun
jama’ar. Shi ne irin mutumin da jama’a za su iya

187
Tunaninka Kamanninka
sawa a gaba a kan al’amuransu duk sa’inda dama
ta samu. Saboda haka, Yakanarsa, ta kafa masa
tushen nasara cikin nasa bukatun, ko a yanzu ko a
gaba. Hausawa sun ce: “Alhairi danqo ne, ba ya
faxuwa qasa banza”. Wannan magana cike da
hikima take, kuma lallai mutum ya lura da ita.

Mara Yakana, shi zai ga wulakancin jama’a duk


sa’inda dama ta samu garesu. Ba shakka a
kodayaushe jama’a suna cikin lura da halayen
mutane dabam dabam. Saboda haka, rashin
Yakana ashe tushe ne na hasara a cikin bukatun
mutum, ko a yanzu ko a gaba.

12.
GYARA MATSAYI:

Gyara Matsayi da hanyar “Bi” a rayuwar mutum


su ne qwararan ginshiqan ni’imar rayuwa
waxanda a nasu juyin suke kafa ginshiqan shiriya
da Jin-daxi. Mutanen da ba su da tafarkin “Bi” a
rayuwa, sukan shagalce cikin rashin makoma,
jidali da mummunan matsayi. “Manufarka ita ce
Madafarka” ta rayuwa, domin sai kana da manufa
za ka san inda ka dosa; watau, ina ne al-qiblarka,
wadda kuma ita ce za ta kai ka ga tsara hanyar
cimma manufar.

188
Tunani da Inganci
Mutane masu manufa su ne suke iya gyara
matsayinsu su kai kansu da kuma al’umma inda
suke so. Da babu irin waxannan mutane, da har
yanzu xan-Adam bai qirqiri tufafi ba, balle
muhalli; da har yanzu bai iya xinka takalmi ba,
balle qirar basukur, ko mota, balle kuma jirgi.
Dukkanin ababan ci-gaba masu taimakawa da
sauqaqawa da daxaxa rayuwarmu, sakamakon
himmar mutane ne masu son gyara matsayinsu.
Irinsu ne suke shiga xawainiya iri-iri ta bincike
domin su gano duk yadda za su yi domin su
kyautata rayuwarsu da kuma ta al’ummarsu. A
sakamakon wannan xawainiya tasu, kowa zai
amfana ya ci riba.

Yawancin ilminmu da fahimtarmu da dabarunmu;


ci gabanmu da jin daxinmu, duk daga sakamakon
xawainiyar irin waxannan mutane ne. Telan da ya
fito da sabon salon xinki, yana cikinsu. Likitan da
ya binciko hanyar sabon magani, yana cikinsu.
Samarin da suka gyara hanya don su qawata
unguwarsu, suna cikinsu. Mai hikimar da ya
qirqiro wata na’ura, yana cikinsu. Mai basirar da
ya rubuta abinda zai amfani wasu, yana cikinsu. Ko
da kanka kaxai ka samowa hanya ma fi maslaha
wadda za ta kyautata rayuwarka, kana cikinsu,
domin wataran wani zai yi koyi da kai.

189
Tunaninka Kamanninka
Lallai mutum ya bincika kansa, kuma ya yi
qoqarin inganta kansa don ya zama cikakke mai
tsarin rayuwa da qoqarin ciyarda kansa da wasu
gaba. Wasu a rayuwarsu, sukan saduda su qi
himmata, don a zatonsu tavukawar ba za ta canja
komai ba. Irin wannan salon rayuwa ba shi da
amfani, domin shi ke dakushe al’umma har talauci
da rashin makoma su ci qarfinta.

Amma, a al’ummar da jama’a suka yunqura wajen


yin abubuwanda za su xaukaka matsayinsu, tareda
kishin junansu, to ba shakka, su ne waxanda falala
da kwanciyar hankali za su lulluvesu. Al’ummar
da akodayaushe tunanin yadda za su ciyarda kansu
gaba suke yi, don matsayinsu ya inganta,
rayuwarsu ta zama mai amfani, falala da ban
sha’awa, ita ce al’umma ta-gari, wadda ta san
ciwon kanta. Haka mutum mai wannan hali don
kansa, shi ya kama hanyar nasara a rayuwarsa.

Manufa takan faxaxa ta zama buri ga waxanda


suka taceta, suka xau wani muhimmin abu da za su
yi fafutuka a kansa a rayuwarsu, ko a yanzu ko a
wani lokaci na gaba da ya fi dacewa. Shi kuwa
buri madaidaici, wanda aka qudire shi saboda
Allah, watau da kyakkyawar zuciya, inji ne na
rayuwa, sai ka hau ka yi ta sukuwarka a kansa; in

190
Tunani da Inganci
ba ka dangana yau ba, gobe tana nan. Lallai ne irin
wannan aqida ta rayu a zukatan masu burin
kyautata rayuwarsu da ta wasu. Amma kuma buri
na rashin kima, wanda ya ginu saboda hassada, ko
nufaqa, ko zaqalewa da gasar banza, qaya ne a
tafarkin rayuwa, domin ya iya zama sharri ya kawo
cikas a rayuwa a gaba. Irin waxannan mutane ne
suke yanqwanewa su lalace. Nan da nan su tsofe.

Idan ka gyara tunaninka, to sai ka xau damarar


gyara rayuwarka. A kodayaushe ka nemi mafi kyau
a komai, ko da don ka kalla ne, domin kallon abu
mai-kyau ko ayyana shi a zuci, yakan haskaka
Zuciya ya kuma sanyayata cikin tuananin alhairi.

Ringa duba Sararin Samaniya cikin sha’awar


tsarinta da zurga-zurgar taurarinta da qyallinsu da
nisansu. Yi al’ajabinsu da tunani a kansu da yabon
hikimar Wanda Ya haliccesu. Ringa sansana turare
mai-kamshi, kuma ka ringa shafa shi. Ringa kallon
furanni da launukansu masu ban sha’awa, ka kuma
samarda su a muhallinka. Ringa sha’awar jama’a
lokacin da suke cikin bushasha ta buki ko ta wani
alhairi da ya samu. Ringa kallo kana nazarin ‘yan
yara in suna wasa ko suna hira cikin irin nasu
azancin. Ringa kallon dabbobi da tsuntsaye a
muhallansu na ainihi suna harbin iska. Ringa kallo

191
Tunaninka Kamanninka
da sha’awar mutane masu tsabtar kaya da ado mai
tsari a jikinsu, ka kuma lura da yadda suke alfahari
da kansu. Ringa hirar nishaxi da mutane da abokai
masu iyata domin yalwata murmushi ko dariya
matsakaiciya. Ringa hira da ‘ya’yanka da matarka,
domin ku fahimci juna ku qara kusantar juna.
Ringa nazarin mutane masu manufa a rayuwarsu,
waxanda saboda qoqarin inganta kansu, al’uma
gaba xaya ta ingantu.

Duk waxannan xabi’un inganta kai ne ta wajen


kwantarda zuciya da ciyarda ita ga abubuwan
alhairi. Zuciyar da ta ci ta sha alhairi, su za ta
haifar. Wanda hankalinsa yake kwance shi ya ci
riba, kuma shi ne mai iya nazarin al’amuransa.

Saboda haka, lallai ka daure ka kauda idanuwanka


da tunaninka daga munanan abubuwa ko na sharri,
ko na lalaci, don ta hakane kaxai za ka iya keve
zuciyarka daga sharrin da lalacin. A taqaice dai,
lallai mutum mai son gyara matsayin rayuwarsa
cikin nasara, ya gyara zuciyarsa, ya kuma yi
yunquri, ya dage sosai wajen cimma manufarsa da
burinsa ta hanyoyin da suka dace da abinda yake
nemarwa kansa ko jama’arsa. A sannu-da-sannu,
zai ga sakamkon fafutukarsa. Hausawa ma, sukan
ce: “Mahakurci Mawadaci”.

192
Tunani da Inganci
12.
NUTSUWA DA HANKALI

Waxannan muhimman sigogi ne, musammam ma


idan aka yi wa mutum shaida da su.“Kai! Ai Hajiya
Amina mace ce mai nutsuwa da sanin yakamata.
Ko kuma,.“Musa? Ai yaro ne mai hankali”. ko
kuma, “Ganiyu da nutsuwa yake”. Ba shakka,
waxannan ababan alfahari ne ga duk wanda ya
mallakesu, domin sukan qara masa mutumci su
kuma kare shi, sannan su hanzarta nasara a cikin
al’amuransa. Duk nutsattse ya san abinda yake yi.

A wasu lokatai, sai ka ga shekaru ko muqami ko


cuxanya da jama’a ba su qari waxannan sigogi ba.
Sai ka ga Yaro mai hankali; Babba gavo. Shugaba
mara kirki; talaka mai tausayi da son taimakawa.
Xalibi mai nutsuwa; Malami watsatstse. Namiji
rago; Mace jaruma. Da Kimtsuwa da Nutsuwa da
Shiriyar hankali, sukan samu ne ta hanyar
kyakkyawan raino daga iyaye, ‘yan-uwa, malamai
da abokai nagari. Haka lalacewa, takan zo ne
saboda sakacin reno daga waxannan mutane.
Tsoron Allah da bin umarninSa, sukan sa mutum
ya zama mai xa’a da hankali, waxanda su kuma
suke taimakawa wajen kafa ginshikin Nutsuwa da
Sanin Yakamata. Kishiyoyin waxannan, suke sa

193
Tunaninka Kamanninka
mutum ya zama mara haquri, mara tsinkaye.
Ga misalai:

** Gurvataccen Ra’ayi: yakan wanzu a


yawancin lokatai saboda gajeren haqurin sauraron
cikakken bayani. Nan da nan sai ka ga mutum ya
xau ra’ayi ba tareda jin ilahirin maganar ba.
Wannan Hali na gajen-haquri yakan sa mutum ya
taka haqqin wani, ko mai-Shari’a ya yi zalunci, ko
Shugaba ya xau matakin da ba zai haifarda alhairi
ba. Maqiya da mahassada, mutane ne masu baza
munanan labarai gameda wanda ba sa so. Idan mai
gajeren haqurin bincike ya ji, sai shi kuma ya
karva ya aikata nasa sharrin ko ya baza shi. Ta
haka, sai sharri ya bazu a qasa, qiyayya kuma ta
sami makwanci. Amma, masu nutsuwa da haqurin
binciken al’amura, suke da makaman fyaxe sharri
da masharrata. “Mai haquri shi kan dafa dutse ya
sha romo.” Akwai hikima a wannan magana.

** Jahilci: Kowa yana da Jahilcin wasu


abubuwa, amma mutum mai nutsuwa ne kaxai ya
san haka, da kuma inda nasa jahilcin yake. Mara
nutsuwa yakan jahilci abubuwa da dama, amma,
kaico! Bai san haka ba. Kamar dai Ilmi ne; sai ka
ga wasu suna ta qoqarin sai sun burge mutane da
son nuna sun san komai, har su je suna bayarda

194
Tunani da Inganci
amsoshin da za su vadda mutane, su kuma jefasu
cikin halaka. Amma idan mai Nutsuwa ya ji
tambaya, ko wani abu da bai sani ba, nan-da-nan
zai san aikin dake gabansa shi ne ya nemo amsar
abin don inganta nasa ilmin shi ma, maimakon ya
ba da amsar da ba daidai bace, nan gaba a ji kunya.
Gudu daga Jahilci yanayi ne a zuciyar mai-
Hankali, mai-Nutsuwa, wanda ya san abinda
yakamata. A kullum nutsatstsen mutum ya kan
nesarda tunaninsa daga ra’ayin riqau, son-iya-yi,
son nuna sani, da hanzarin xaukar matsayi ba
tareda cikakken sanin bayanin matsalar ba, ko
saurin bayarda amsa ba tareda sanin haqiqaninta
ba. Irin waxannan mutane masu shisshigi su ne
suke dulmiyar da al’umma, musammam a inda
jahilci ya yi yawa, su jawo ruxani da muguwar
hasara ga jama’a, musammam waxanda su ka
dogara da su.

Mecece alamar MALAMI na qwarai?


Mecece alamar SHUGABA na qwarai?

Malami na qwarai shi ne wanda aka yi masa


tambaya, amma da ya nutsu cikin tunanin bai san
amsar ba, sai ya shaidawa mai tambayar da cewar,
“Ban san amsar tambayarka ba. Amma,
insha’Allahu, yau zan bincika littattafai, idan ka zo

195
Tunaninka Kamanninka
gobe zan yi maka bayani yadda zan iya”. Wannan
Malami ya san Allah (swt) ne kaxai Yake da
cikakken Ilmin komai. Duk Malamin da ya cika-
baki ya san komai, kuma yake ta qoqarin amsa
kowacce tambaya, to guje masa. Ba masani bane,
mai shisshige ne kawai. Masu sauraronsa da aiki
da maganarsa sai sun yi da-na-sani wataran.

Shugaba na qwarai shi ne wanda ya yi kuskure a


wata matsala ta shugabanci. Da aka sanarda shi
kuskuren, sai ya nutsu, bai ximauta da fushi ba don
ya san idan bai gyara ba, jama’arsa ne za su cutu.
Saboda haka, ya karvi kuskurensa ba tareda
girman kai ba, ya nemi gafarar jama’arsa, ya kuma
gyara kuskuren da sabon tsari wanda ya dace.
Wannan shugaba ya san Allah (swt) ne kaxai,
saboda kulliyar IlminSa, ba ya kuskure a kan
kowanne al’amari a cikin mulkinSa. Duk shugaban
da ya san yana cikin kuskure, amma ya qi gyarawa
don girman-kai ko son-kai ko mugunta, to ba
shugaba bane, mazaluncin jama’arsa ne kawai.
Nutsuwa da sanin haqqin jama’a su ne suke sa a
gane shugabanni da mutane na qwarai.

** Camfi: Mutum nutsatstse ba ruwansa da


Camfi, don ya san Camfi ya kan keta imani, ya
jefa mai shi vatan da ba dawowa. Haka kuma mai

196
Tunani da Inganci
nutsuwa ya san, lallai idan ya daka ta Camfi da
wasu al’adun banza, zai dakusarda rayuwarsa ne
kawai, wataqila ma har da ta wasu. Duk mai
hankali ya san yarda da Canfi, balle bin tafarkinsa,
yana daga baqaqen tunani. Duk kuma wanda ya
dauwama cikinsa, to kuwa wata rana zai iya yin
maraba da tsafi. Abin takaici shi ne akwai masu
camfin da suke zaton suna amfani da Sunaye ko
Ayoyin Allah (swt) don cimma manufofi da sauran
baqaqen ayyuka, amma ba su fahimci cewar su
matsafa bane. Akwai kuma masu aikata miyagun
zunubai cikin camfa cewar alhairi zai zo masu na
kuxi ko na wani muqami ta hanyar waxannan
zunuban, amma ba su san su gafalallu bane. Sun
raina Allah (swt) da gargaxinSa. Ba shakka, sun
kasance masu matuqar izgilanci ga Mahaliccinsu;
kuma mun san makomarsu. Wa-iyaz billah!!!
Haqiqa wasu suna cikin wannan kafirci.

Ba irin halakar da Camfi ba ya kawowa ga mai


yinsa da mai yarda da shi. Nutsuwar tunani ne
kawai ke qarfafa imani yadda zuciya da tunaninta
za su yaqi shaixanci, su kafa iyaka mai qarfi daga
sharri, su kuma iya aikata abubuwan da suka dace
don samun nasara a xawainiyar da ke gabansu.
Camfi shi ne kishiyar Imani, kuma ba abinda zai
haifar sai sharri. Idan kana da bukata wajen Allah

197
Tunaninka Kamanninka
to nemeta wajen Allah. Idan kana da ita a wajen
wani, to nemeta wajen wanin, sannan ka roqi
Allah Ya taimaka maka. Haqiqa mutane masu
Nutsuwa da Hankali su ne abokan sirri, su ne
abokan harka. Su ne masu nasara a aljihunsu.

13.
HAQURI, JURIYA
DA LA’AKARI DA WASU

Mutane marasa Haquri da Juriya su ne wahalallu a


zuciyarsu, kuma ba a kowanne hali za su yi
rayuwa mai kyau da amfani ba. Irin waxannan
mutane, ba su iya zama da jama’a ba tareda rai
yana vaci ba. Sannan yawancinsu, masu voye wata
gazawa ce a tareda su. Wannan gazawar, ita ce
take qona masu zuciya, suna tozarta kansu daga
yanayin fuskarsu da kalamansu waxanda suka
bayyana daga abinda zuciyarsu da tunaninsu suke
dafawa. Amma Mahaqurta, su ne masu zuciya a
sanyaye cikin ni’imar gamsuwa da kansu,
waxanda za su iya rayuwa a ko’ina, kuma a
kowanne hali ba tareda hassada ko qin jinin
halayyar rayuwar wasu ba. Hausawa sun yi hikima
da suke yi masu take suna cewa: “Mahakurci
Mawadaci”. Ba makawa hakane ta duk inda ka
auna. Mahaqurci ne kaxai zai iya kare imaninsa

198
Tunani da Inganci
daga jinkirin amsar addu’o’insa, a nasa ganin; ya
kuma sa ran Allah Zai amsa a kan lokacin abin.

Haka, masu Juriyar jama’a, ba ruwansu da launin


fatarka, ko qabilarka, ko addininka, ko matsayinka
a wajen hidimarsu ta kyautatawa jama’a saboda
Allah (swt). Masu waxannan halaye na-gari, sun
san akwai hanyoyi da yawa na kallon abubuwa da
yawa, kuma ba ruwansu da tunanin haxama,
ballantana na qyashin wani ya samu. Waxannan
mutane su ne salihai ababan misali da koyi.

Adalcin rayuwa a gunsu shi ne kawai su rayu ba


matsi ko matsantawa wani. Aqidarsu ita ce, “In
Alhairi ne, mu Ci tare”; In kuma sharri ne, ka Ci
kai kaxai”. Sun san cewar akwai qazamtu a rayuwa
waxanda illolinsu sa iya lahanta jama’a. Sun san
akwai mutanen banza waxanda suke yawan
gurvata gaskiya, sannan su sa qafa su shure abin
tausayi. Amma nutsuwarsu da haqurinsu da
juriyarsu sun haxu sun karesu daga son yin
mugunta, ganin-qyashi, girman-kai da
annamimanci, ko da za a kwaxaita masu wata
bushasha in sun aikata hakan. Waxannan mutane
su ne masu nasara a cikin rayuwarsu, duniya da
lahira. A cikinsu ake samun masu:-

199
Tunaninka Kamanninka
** La’akari da wasu; waxanda suka san cewar
akwai wasu ba su kaxai ba, kuma sun san cewar
Son-kai shi ke cizge jijiyar ci-gaba da zaman-
lafiya a cikin al’umma. Masu La’akari da wasu
sukan yalwata tambayar kansu:

“Menene amfanin Dukiyata ko Arzikina, idan


ban bautawa Allah (swt) da su ba? Hankali ne na
qi taimakon maqwabcina, amma na je na ba da
gudun-mowar fariya da qarya a daji? Shin,
yakamata na ba da lokacina da qarfin jikina ga
wani aiki na alhairi don qaruwar jama’a, tunda ba
ni da kuxin bayarwa, ko kuwa yawon banza da
zaman banza sune suka fi min alhairi? Mecece
dangantakata da sauran jama’a?: Shin damuwarsu
damuwata ce; kuma jin-daxinsu nawa ne? Ko
kuwa, son-kai da annamimanci da mugunta su ne
tafarki na?

A tsarin mutum da halittarsa, akwai kogon tunani


iri biyu kamar yadda muka sani: Kogon Farin
Tunani da na Baqin Tunani. Watau, a bayyane,
akwai siffar “Annabci” da ta “Ibilisci” ga kowanne
mutum, kuma zavi na gareka. Ko ka zavi vangaren
Annabci ka yi fafutuka don Jama’a ba don kanka
kaxai ba; ko kuma ka zavi ka yi son-kai ba tareda
la’akari da halayyar jama’a ba. Wanda ya ce: “Ni,

200
Tunani da Inganci
ba abinda ba ni da shi, don haka ba ruwana da
kowa”, to ya zavi vangaren ibilisci. Amma, wanda
ya ce: “Allah Bai ba ni ba, sai don Yana son in
aikata alhairi; na yi amfani da wani bangare na
baiwar da Ya yi min ta wajen fafutukar jama’a”, to,
ba shakka wannan mutum ya zavi vangaren
Annabci. Allah (swt) Yana tareda irin waxannan
mutane waxanda suka bi tafarkin annabawa, domin
su ne suka zavi hanyoyi madaidaita, waxanda za su
kaisu ga nasara mai amfani. Haka Zai ta qara masu
wannan baiwa ninkin baninki, duk sa’inda suka
aikata alheri da ita. Amma waxanda suka zavi
tafarkin Iblis, to su ne masu hasara masu fama da
lahanin zuci.

14.
ZURFAFA TUNANI

Tun daga wayewar gari har zuwa lokacin barci da


daddare, xan-Adam cikin tunani yake a kowacce
daqiqa ta rayuwarsa, ko yana sane, ko ba ya sane.
Bambancin mutane shi ne na zurfafa tunanin don
ganin damarsu. Lokacinda wata muhimmiyar
matsala ta ratsa kwanya, wasu sukan keveta su yi
tunani na musammam a kanta; wasu kuma ba sa yi,
sai abinda kwanyar ta ba su don kanta. Wasu sukan
yi tunani yadda yakamata, su kuma cimma amsoshi

201
Tunaninka Kamanninka
na gaskiya waxanda za su taimakesu wajen
fuskantar al’amuransu; wasu kuma ba sa yin tunani
yadda yakamata, sai su cimma amsoshi na banza
waxanda za su iya tavarvara matsalarsu.
Bambancin yawancimu a zurfin tunaninmu da aiki
da shi yake.

Tundayake, tunanin mutum shi ne yake gabatarda


mutum, ashe ya zama tilas mutum ya nutsu sosai
ya yi ta yin tunani mai zurfi a kan matsaloli masu
muhimmanci tareda shi. Bambancin mutum da
dabba, shi ne tunani. Bambancin mutum da
mutum, shi ne tunani mai zurfi. Wanda ba ya
yinsa, ko kuma ba ya yinsa a nutse, haqiqa, Nasara
zata yi nisa daga gareshi.

A al’umma irin tamu, ci-gaban jama’a ya dakushe


sosai ne saboda jama’a sun xauki tunani mai zurfi
abune mai wahala, ko kuma abune wanda ba shi da
muhimmanci, ko kuma abune sai ‘wasu’ ba ‘ni’
ba. Tunani shi ne maganin tavewa, kuma ko
al’amura ba su gyaru ga mai zurfin tunani ba, to
kuwa zai iya tsinkayar wahalolin da ke gabansa, ya
yi shirin tunkararsu kafin su zo, ko kafin lokaci ya
qure masa. An ce, Riga kafi ya fi magani.”

Amma, kaico! Wasu mutane sukan guji yin zurfin

202
Tunani da Inganci
tunani, wasu, don tsoron abinda zuciyarsu za ta
fassara masu; wasu kuma don tsananin sakacinsu.
Amma kuma, kowa ya san cewar matsoraci shi ne
wanda zai kasance cikin qangin rayuwa, ya yi kane
-kane cikin fargaba mai tsawaita wahala, har sai
abinda yake gudun ya cimmasa. Idan kana son ka
kasance “Mai-Tunani” toh, ka fara tunanin, kuma
tunani mai-zurfi cikin gaskiya ba tareda tsoron
abinda tunanin zai fassara maka ba. Idan Kai da
kanka, kai-kaxai, ka qi faxawa kanka gaskiya, to
waye zai faxa maka? A lokaci irin wannan, kana
da maqiyi fiye da kai kanka? Ka tuna fa: Ka fi
kowa sanin kanka, kuma ba ka da aboki irinka.
Asirinka naka ne. In kana zaton akwai mai sonka
fiye da kai, to kana cikin babban kuskure da
qarancin hankali. Wanda bai san ciwon kansa ba,
shi ke cikin hasara da nadama.

Mutum zai iya fara tunani a kan matsaloli ko


abubuwa dabam-dabam, ba lallai sai waxanda suka
shafe shi tawwali ba. Ko a hira, ko a karatun jarida,
ko wani Littafi (kamar wannan), ko a muhawara,
ko radiyo, ko laccar malami ko ta wani xan siyasa,
ko daga yadda shugabanni suke gudanarda wata
matsala da masalaharta. Ga dai dama nan birjik a
kewaye da kai waxanda zaka iya yin tunani a
kansu. A kullum tambayoyin su ne:

203
Tunaninka Kamanninka
Ta Farko: “Me ake nufi?” (tunaninka);
Ta Biyu: “Gaskiya ne, ko kuwa?” (bincikenka);
Ta Uku: “Ya za a yi?” (amsoshinka).

Ya zama tilas ka yawaita waxannan gameda kai


kanka, da kuma abubuwan da suke kewaye da kai.

Dukkannin waxannan suna da irin nasu amshoshin


dabam-dabam, kuma ya rage sabon tunani mai
zurfi ya auna komai a kan sikelin azanci da adalci,
ya zavi wadda ta dace a halayyar ake ciki.
Kowanne al’amari, ko wacce magana, ko wanne
aiki, yana da manufarsa da sakamakonsa a kan
waxanda ya shafa. Idan tunaninka ya nuna maka
cewar abu ya shafeka, kai kanka, ko iyalinka, ko
ma Garinku da Qasarku, to, ba shakka akwai
bukatar a yi sabon tunani da nazari a kansa. Idan
ka yi biris da waxannan al’amura, to wataran za a
ba ka mamaki ma’illaci a gareka, watakila ma da
iyalinka da kuma jama’arka, daidai matsayin
rayuwarka. A inda ka san wayonka da hikimarka
sun gaza ga samun amsar da ta dace, sai ka yi
tambaya a gurinda ka tabbata za a ba ka amsa
saboda Allah, ko da kuwa gurin xanka ne ko
matarka, ko wani yardajjenka.

Babu abu mai daxi da wanke zuciya irin tunani na

204
Tunani da Inganci
gaskiya, tsakani da Allah. Farin Tunani, wanda ya
fi sukari zaqi; kuma ya fi tuwo qosarwa. Ga araha,
ga sakamakon alhairi. Mai tunani mai zurfi, shi ne
mai nasara mai faxi.

15.
CIKA ALQAWARI

Ba sharri mai illata mutum da dangantakarsa da


wasu irin rashin cika Alqawari. Ba qazamin
mutum, mara sanin yakamata, mara mutumci, mara
tausayi, mara madafa a tareda shi, irin mutumin da
zai xau alqawari da sanin ba zai cika shi ba. Da
mutanen kirki sun fahimci wannan illa a tareda
mutum, to ba yadda za a yi su miqa kayansu a
gunsa, don ba zai iya xauka ba, balle ya sauke. Ba
mai hasara irin mara cika alqawari, kowanne iri ne
alkawarin, balle na lokaci ko taimakon wani.

Da mara cika Alkawari ya ga an rubuta, “Alqawari


Kaya ne”, sai ya karanta a hagunce yadda abin ya
dace da mummunan halinsa: “Alqawari qaya ne”.
Irin waxannan mutane sam ba su san mutumcin
kansu ba balle na matsayinsu ko muqaminsu, in
suna da shi. Har ga Allah (swt) su mutane ne
waxanda ba su san yakamata ba. A idanuwan
jama’a su mutanen banza ne, komai muqaminsu da

205
Tunaninka Kamanninka
kuxinsu; kuma maqaryata ne, komai ilminsu;
kuma mamugunta ne komai darajar da ake ba su;
kuma macuta ne idan suka sami damar cutar. Me
ake yi da mara cika alkawari. Amma, kash! Wasu
da yawa sun xau wannan xabi’a. Can dai!

Idan ba za ka taimaki mutum ba, to kada ka qara


masa wahala. “Jeka ka dawo” mugunta ce, in an
san ba abinda za a yi in an dawon. Wanda ba shi
da niyyar cika alkawari, to kada ya xauke shi,
komai runtsi, sai dai in halaka ya gani. Amma,
mutumin da zai zubda ta idonsa, ya dubi jama’a ya
xau alqawari, ya kuma qi cikawa da gangan,
wannan mutum bai san mutumcin kansa ba, bai
kuma damu da komai ba. Hasalima, mayaudari ne.

Tunanin irin waxannan mutane, ba shakka baqi ne


qirin, kuma ba yadda za a yi su ci nasarar
rayuwarsu sai ta zamba da qarya da hilata da
yaudara da zubda mutumcin da ba su da shi.

Amma mutum mai cika Alqawari, shi ne cikakken


mutum har ga Allah (swt), domin wannan mutum
ya san haqqi, ya san yakamata, ya san martabar
waxanda ya yi wa alqawarin da abinda ya yi
alqawarin a kai. Mutane sun san shi, kuma sun san
mutumin kirki ne shi, wanda zai iya riqe amana da

206
Tunani da Inganci
shugabanci. Wanda ya san nauyin alqawari, yake
kuma cika shi, toh ya yi galaba a kan mummunan
tunani, ya ci nasara tuni a rayuwarsa. Wanda zai
iya cikawa wasu alqawari, ba shakka, zai iya
cikawa kansa alqawarin tunaninsa da niyarsa ta
fafutuka a kan duk irin burin da ya sa a gabansa.
Daga wannan qarfin zuciyar alqawarin, zai iya
samun sabon qarfin tafiyarda al’amuransa, har ma
da na wasu; ya kuma yi wa kansa jagora zuwa ga
nasara a dukkanin abubuwan da ya sa kansa yi.
Idan ya xau alqawari sai ya cika shi, sannan zai san
ya sauke nauyin da ya xauka. Sannan kuma
hankalinsa zai kwanta. Wannan shi ne mutum!

Ba yadda za a sami rago a cikin masu cika


alqawari; kuma rago ba zai iya kasancewa a
cikinsu ba. Xaukar nauyi da sauke shi, ba shakka,
aiki ne na jarumai, waxanda zuciyarsu ta xau
manufarsu da qarfi, tunaninsu kuma ya duqufa
wajen qara himma a kan turbar cimma wannan
manufa, har sai an kai gaci. Nasarar rayuwa, ba
shakka, ta tabbata a gareshi, duk wanda ya xau
xabi’ar cika alqawari a lokacin cika shi.

Cika alqawari yana daga bin Allah (swt), kuma ba


qaramar ibada bane. Mai cika alqawari, shi yake
iya tsaida ibada, fisabilillah, ba don ganin ido ba;

207
Tunaninka Kamanninka
ba kuma don kawai haka ake zato daga gareshi ba.
A gareshi, cika alqawari ruwa ne da yake gudu a
cikin jininsa. Duk mai son mutumcinsa ya tsira,
nasara ta tabbata a rayuwarsa, to lallai ya wanke
zuciyarsa, ya kuma qarfafa tunaninsa a kan hanyar
cika Alqawari.
16.
MASLAHA DA GAFARTAWA

Riqe mutum a zuci da qin gafartawa wanda ya


aikata maka laifi, sun fi laifin da aka aikata azaba.
Wannan abu haka yake domin sai ka tarar ka fi
tunanin qullatar mutumin fiye da yadda ka ke
tunanin laifin da ya aikata. Maganin wannan baqin
cikin shi ne kaxai mutum ya sabunta tunaninsa ya
xau xamarar gafartawa da neman maslaha. Mafi
muni kuma shi ne tunanin ‘maida martani’, watau
ka qudiri niyyar sai ka rama.

Ramuwar Gayya tana ga Allah (swt) domin Shi


yakamata ka miqawa kukanka gameda haqqinka
da aka taka da gangan domin a quntata maka, ko
tozartaka, ko a ci maka mutunci. Idan ka shige
gaba ka ce kai ne mai ramawa, to wataran sai ka yi
da-nasani. Amma idan ka haqura ka barwa Allah
(swt) sakayyarka, to ba shakka kai ne mai nasara
ko badaxe ko bajima.

208
Tunani da Inganci
Ga bayani mai sauqi:

Idan wani ya cuceka, sai ka ce sai ka rama irin


wannan cutar, toh take a nan ka aikata miyagun
abubuwa biyu: Da farko dai ka cire Allah a cikin
al’amarinka, sannan kuma kai ma ka zama macuci.
Idan ka cire Allah a cikin al’amarinka, ka ce kai ne
za ka karewa kanka, toh idan wanda ya cucen naka
ya fi ka qarfi ko iko ko galihu, toh nan take zai
sake cutarda kai. Dalilin kuwa mai sauqin fahimta
ne: domin babu adalci a cikin tsarin; domin an cire
Allah (swt) daga cikinsa. Toh, amma, idan ka
barwa Allah (swt) sakayyarka fa? Waye ya fi Allah
qarfi ko iko ko galihu? Ai ka ga a wannan hali,
lallai za ka sami cikakkiyar sakayyarka ta hanyoyi
uku. Da farkon fari, sai Allah (swt) Ya mayar maka
da duk abinda ka rasa daga waccan cutar ta
hanyoyi iri iri; sannan kuma in ka zuba ido, a
hankali za ka ga yadda wanda ya cucen naka zai
zama. Ta ukun kuma, ká adana lokacinka wajen
yin wasu abubuwan dabam na alhairi.

Mutum mai iya gafartawa shi ne kuma mai iya


neman gafara da maslaha a tsakaninsa da duk
wanda ko waxanda wani abu na rashin jin daxi ya
wakana a tsakaninsu. Lallai ne mutum ya kimtsa
tunaninsa a kodayaushe wajen yin la’akari da

209
Tunaninka Kamanninka
rashin kyautatawarsa ga mutane ko menene
qaskancin rayuwarsu a idanunsa. Kada mutum ya
manta cewar a gurin Allah (swt) kowa muhimmi
ne, musammam kuma masu taqwa. Ko almajiri ka
zaga cikin fushi don ya nace yi maka bara, toh ba
shi haquri, ko ka dawo ka ba shi sadaka da niyyar
ita ce haqurin da ka ba shi. Ya zama tilas ga
mumini ya san cewar Allah (swt) a tsarin
adalcinSa ba Ya yafe laifin da aka aikatawa wani.
Sai ka yi ta ibadarka kana ta samun ladanka, amma
duk ka zagwanye shi da haqqin jama’a a kanka.

Duk mai la’akari ya san wannan; ya san kuma


babbar xabi’arsa ta farko ita ce ‘kiyayewa’. Ta
biyu kuma ‘neman gafara’ da ‘maslaha’ idan ya yi
kuskure ga waxanda ya yi wa kuskuren. Ba
qaramin jarumi ne shi ba, wanda ya duqufar da
kansa ya nemi gafarar waxanda ya aibanta. Haka
kuma, ba qaramin mai dabara ne shi ba.

Duk wanda ka yi wa laifi, ko wanne iri ne, ka


kuma zama jarumin da zai je ya nemi gafara ya
kuma sulhunta, to ba shakka ka sami zaman lafiya
da kanka, ko da ba a gafarta maka xin ba. Allah
(swt) Yana sane da kai da niyyarka, kuma Ya san
abinda Zai yi a kan wannan al’amari naka. Ba
mutumin banza a idanun Allah (swt) irin wanda

210
Tunani da Inganci
aka nemi ya gafarta ya qi, ko kuma ya kasance mai
saurin maida martani don ramar-gayya. Irin
waxannan mutane in ka lura za ka ga ba su da
madafa a rayuwarsu, domin ba za su sami gafarar
Allah (swt) ba; domin ba su yi koyi da Shi ba; ba su
kuma yi koyi da ManzonSa ba. Ka gafartwa wanda
ya yi maka laifi, alabarshi ka nisance shi, in har ka
tabbata yin haka shi ne mafi alhairi a gareka.

Kai dai adana zuciyarka, ka tserarda ita daga sharri


ko qulla shi; ka nesantar da ita daga rashin haquri
ko ramuwar gayya. Lallai ka zama mai neman
maslaha a rayuwarka. Kada ka yarda ka riqe
mutune a zuciyarka, ballantana ka kafa wasu a
muqamin maqiyanka. Duk masu qiyayyar da
sharrin da hassadar da muguntar da sauran irin
waxannan baqaqen tunani, haqiqa, su ne cikin
azaba da nadama a rayuwarsu. In kana cikinsu ka
san haka. In ba ka cikinsu, ba ka san haka ba.
Wannan ita ce babbar shaida, wadda kowa zai iya
bincika zuciyarsa don ya fahimta ya kuma gyara
tunaninsa a kansa da kan wasu.

17.
RIQE SIRRI

Riqe sirri alama ce ga mai iya yinsa cewar yana da

211
Tunaninka Kamanninka
adanannar zuciya, wadda ta kimtsu, ta nutsu, ta san
abubuwan da za ta haxiye da waxanda za ta tofar.
Zuciyar da ba ta san waxannan ba, almubazzara
ce; wataran sai ta rasa komai na kanta. Mai irin
wannan zuciya yana cikin haxari.

Da muke cewa, ‘Wanda ya rufa asirin wani, Allah


zai rufa nasa’, ai matashiya muke yiwa kanmu ga
muhimancin sirri, musammam ma idan aka ba ka
amanarsa, ko kuma ya kasance dole ka adana shi
don kada kai, ko wani ya lahantu. Kishiyar waccan
magana ita ce, duk wanda ya tona asirin wani,
Allah Zai tona nasa’. Daga wannan magana za mu
iya fahimtar cewar ashe idan ka tona wani asiri a
kan rashin cancanta har ta kai aka shiga cikin wata
wahala saboda hakan, ashe kai ma wataran kana
tafe zuwa ga wannan wahalar ko ma wadda ta fita.
Haka, kuma ana cewa, “In za ka haqa rami, haqa
shi gajere”, saboda ko wataran za ka faxa cikinsa.

Mutane biyu su ne aka fi sani da tonon asiri: Da


Wawa da Mamugunci. Wancan don bai san abinda
yake yi ba; wannan kuma don sharri. Amma kuma
lallai ne mutum ya san da wa yakamata ya yi
magana; wa yakamata ya bar wa sirrinsa; a ina
yakamata ka yi, ko ka ce, abu-kaza? Wanda bai
adana sirinsa ba, to shi ya jawowa kansa. Ashe

212
Tunani da Inganci
maganar sirri, magane ce mai gefe biyu. Gefen da
ya fi muhimmanci shi ne gefen mai sirrin; sannan
gefen wanda ya san wannan sirrin ta wata hanya.
Shi kansa sirrin kuma iri biyu ne: Da sirri mai kyau
da mai muni. Sannan kuma akwai sirri wanda sai
an faxa za a gane shi, akwai kuma wanda sai an
aikata wani abu za a iya gane shi. Mu qara tunani a
kan wannan.

Idan ka ji wani yana qulle-qullen cutar wani, ko


aikata wani sharri dabam wanda zai illata wani ko
ya kawo wata rigima ga wasu ko ga Qasa, lallai ka
auna da kyau ka san abinda za ka yi gameda
wannan sirri. Idan abinda za ka iya hanawa ne, toh
maza hana. Idan wanda za ka iya tonawa ne don
al’umma ta sami maslaha, toh maza tona. Amma
idan mutum yana da sirrinsa na kansa, ko da wani
abin kunya yake aikawa tsakaninsa da Allah, toh
rufa masa asiri, ko ka ba shi shawarar ya daina, in
za ka iya. Baza shi a kasuwa cewar shi ne mai
aikata kaza da kaza a voye ba shi ne maslaha ba,
sai dai in ka ga yana neman jan mutane a Sallah, ko
neman wani shugabanci wanda bai dace da masu
irin waxannan aqidu ba. Idan azzalumai suna
neman wanda suke son zalunta, shi kuma ya vuya a
wani gu, toh kada ka nuna makwancinsa. Duk
wanda ya san ka san asirinsa, ya kuma roqe ka don

213
Tunaninka Kamanninka
ka rufa masa asirin, to yi qoqari ka rufa masa.

Yawancin abubuwa da shirye-shirye muhimmai a


cikin sirri ake tsarasu. Wanda ya fallasa su ya
doshi hanyar tarwatsa su. Inda babu sirri a kan
abubuwan da suka cancanta a asircesu, toh babu
nasara cikakkiya a tareda su. Haka kuma duk inda
surutu ya yi yawa, toh ba shakka sirri zai yi kaxan.
Guji hirar sirrinka da mai surutu da kuma wanda
ya faxa maka sirrin wani. Guji fallasa asirinka ga
waxanda ba ka amince da su ba, ko mecece
bukatarka. In a gun Allah (swt) ka ke nema to tuni
ya san sirrinka, ba sai ka tonawa wani ba.

Yawancin masu tona asiri mahassada ne, kuma ba


za su iya riqe amana ba. Lallai ne mu yi la’akari da
wannan, mu kuma san su waye abokan hira; su
waye abokan yawo; su waye abokan kasuwanci ko
wata mu’amala; su waye kuma abokan sirri.
Wanda ya iya rarrabe mutane haka, shi ne zai ci
ribar rayuwarsa asirinsa a rufe.

Duk wanda ya ji sirri, toh ba shakka babban aiki ya


same shi. Lallai ne wannan mutum ya zauna ya yi
tunani a kimtse domin ya san wanne irin sirri ne
wannan, kuma ya zai yi da shi? Da ya tsaida
shawara, toh lallai ne ya yi tunanin ita shawarar, ya

214
Tunani da Inganci
sake tankaxeta da rairayeta har sai ya tabbatar ita ce
wadda ta dace, sannan ya yi maza ya aikatata.

Da mai tona asirin da bai kamata a tona ba, da


mahassadi da munafuki, duk launinsu xaya. Mutane
ne waxanda nufaqarsu ta cinye zuciyarsu.

18.
TALLAFAR IYALI

Tsarin rayuwar al’umma gaba xayanta ya ginu ne a


kan iyali, kuma tallafar iyali aikin karva-karva ne.
Watau, wannan ya karva ya ba wa wancan daga
zuri’a zuwa zuri’a. A inda duk zaren tallafar ya
tsinke, to zuri’a xinkakka ta yage.

Ya zama wajibi jama’a su fahimci muhimmancin


wannan gini na iyali da zuri’a, su kuma san menene
matsayinsu a wannan bango, watau wanne tubali ne
su. Idan mutum ya san shi ne tubalin ginshiqin
bangon, to lallai kuma ya san cewar idan ya goce
bango ya tsage, ko ma ya ruguje. A tarayyar iyali,
lallai duk dangi su san cewar ‘tsintsiya xaya ba ta
shara’, domin ta sanin hakane kaxai za su iya
tallafar junansu, su kare iyalinsu da zuri’arsu daga
watsewa. Lallai ne kowa ya taimakawa ginshiqin

215
Tunaninka Kamanninka
bangon nan ta yadda kowa zai iya, kuma lallai ne
su yi shirin ‘in ba wane akwai wane’, domin rufin
asirinsu yanzu da kuma gaba. Idan suka qi
taimakawa juna, ko suka yi sakacin fahimtar
magaji, toh kuwa su san cewar daga lokacin da
ginshiqin ya kasa, toh daga wannan rana wahalu za
su fara sallama, sai dai kuma wani taimako na
Allah (swt) a dalilin da Shi Ya fi kowa sani.

Mutane da yawa ba sa sa muhimmancin iyalinsu a


cikin tunaninsu na yau da kullum. Su kan manta
cewar iyali, musammam ma na kurkusa, watau, na
aure da ‘ya’ya da iyaye da yayye da qanne, su ne
babban nauyin da yake kawunansu. Sai sun sauke
waxannan haqquna tukuna, sannan za su iya
xaukar sauran ’yan’uwa, sannan kuma wani a
waje. Amma sai ka ga wasu, sai wajen ta qoshi
tukuna, sannan za su kawo sixi gida. Sai ka ga
wasu sun yi watsi da matansu, ko ‘ya’yansu ko ma
iyayensu, suna ta hululu da waxanda ba su kamata
ba. Sai ka ga wasu sun ginawa maroqi ko karuwa
gida, ko sun sai masu motoci, amma ga iyayensu
da matansu da ’yan’uwansu duk cikin wahala. Sai
ka ga wasu tunaninsu tamkar na dabba.

A tsarin rayuwa, tallafar iyali tana da muqami mai


girman gaske. Lallai ne a yi tunani mai haske a kan

216
Tunani da Inganci
wannan. A cikin iyali kimtsattse, ba a jin labarin
jahilci ko fatara ko rashin aikin yi, domin jama’ar
wannan iyali sun ba wa zuri’arsu muhimmanci, sun
haxa kansu ga taimakon juna daidai yadda za su
iya, kuma kowa daidai qarfinsa. Fafutukarsu a
kodayaushe ita ce su san yadda suka rufawa kansu
asiri, suka xauki xabi’u da al’adu waxanda za su
tabbatar masu da mutumcinsu. A irin wannan iyali
ake samun na-gaba wanda idan ya faxa za a saurare
shi, ba don shi ne mai-kuxi ko wanda ya fi kowa
ilmi ba. A a, sai dai don shi ne babba, ko kuma
wanda ya fi dacewa a cikinsu. A cikin iyali irin
wannan kowa ya san matsayinsa da duk
abubuwanda ake bukata daga gareshi. A cikin iyali
irin wannan rufin asirinsu gaba xaya da kuma
ingantar kowannensu su ne babbar manufa.

Duk wanda ya salwantar da iyali, ya salwantar da


babban haqqi. Duk wanda ya tallafi iyali daidai
qarfinsa, to ya tallafi babban haqqi yadda Allah
(swt) Yake so. Irin waxannan mutane masu son
iyali, masu kula da zuri’arsu yadda za su iya, ba za
su tave ba har abada abadun, domin Allah (swt)
Yana tareda su a kodayaushe. Jama’a ma sukan yi
sha’awar masu zumunci da tallafar iyalansu.

Kuskure ne qasaitacce, mutum ya ringa tunanin

217
Tunaninka Kamanninka
hasara wajen taimakon iyali, domin jarin da yake
cikinsa ya fi na kowacce irin sadaqa. Sannan ga
shi ta nan ake samun xaukaka, zuri’a ta ginu, gari
ya ginu, qasa kuma ta ginu, kowa ya ci riba.

19.
IMANI DA ALLAH (swt)

Masu imani da Allah ne kaxai za su ci riba biyu:


Ta duniya da ta lahira. Tuni dai mun gamsu da
cewar nasarar da za a samu a duniya a cikin tunani
ake shirya samunta. Tundayake kuma daga duniyar
ake shirya lahirar, ashe wancan tunanin nasarar na
farko shi ne maqasudin komai.

Imani da Allah (swt) abubuwa uku muhimmai ya


qunsa. Na farko ka yi imanin cewar Shi kaxai ne,
kuma babu wani abin bautawa sai Shi kaxain. Na
biyu, ka yi imani da duk abinda a haqiqa Shi ne ya
faxesu da waxanda suka kawo saqon. Na uku
kuma, ka aikata duk umarninSa, ka kuma bar duk
abubuwan da Ya hana. A cikin waxannan ukun za
mu ga cewar komai ya shigo. Shiriyarmu da
shari’armu, duk sun shiga mazauninsu. Amma, sai
tunani ya kimtsu ya karvesu sannan za su sami
gurbi a cikin zukatanmu; sannan ne kuma za mu
iya zama kimtsatstsu mutanen kirki waxanda suka

218
Tunani da Inganci
san yakamata, suke kuma da tsari na alhairi.
Tushen komai, musammamma ‘nasara’ daga imani
da Allah (swt) yake. Wanda ba shi da wannan
imani a zuciyarsa, ba shakka, ya yi babbar hasarar
rayuwarsa ta duniya; tuni kuma ya rasa damar
kimtsa ta lahira. Mai imani ne kaxai ya san haqqin
wasu, ya kuma san dukkanin nauyin da yake kansa
ko menene matsayinsa, jin daxinsa da wahalarsa.
Shi ne ya san muhimmin aikinsa a wannan duniyar
bai shige gina lahirar ba.

Mai imani da Allah (swt) ne kaxai yake iya


daurewa fitinu da masifu in sun zo; ya sarrafa
kuxinsa da talaucinsa cikin arziki. Irin wannan
mutum shi ne mai fahimtar duniya a matsayinta na
‘tasha’ ce mai qarancin lokacin jira, domin ya san
shi matafiyi ne daga wani gu wanda bai sani ba
zuwa wani gu dawwamamme, wanda ya sani.

Mai imani ne kaxai ya ke la’akari da duk


waxancan shawarwari goma sha takwas na baya,
ya ke kuma iya sarrafa tunaninsa saboda Allah.

219
Tunaninka Kamanninka

220
Tunani da Nazari

Tunani
da Nazari
“Kukan Kurciya ma
Jawabi ne ….”

“Duk wanda ya fahimci bambancin da yake


tsakanin kwano da abinda yake cikinsa,

W
toh ya sami isasshen ilmi”

annan Magana ta sama lallai abar bin-


cike ce, domin tana qunshe da bayanai masu zurfi.
Maganar, ita kanta, ta fidda zato ce, ko kuma tana
fahimtarda mu ne yadda a al’ada aka fahimci wasu
abubuwa, aka kuma riqe ra’ayi a kansu ba tareda
zurfin nazarin da zai tabbatarda hakan ba. Tankaxe
abubuwa da rairayesu, suke sa a fahimcesu a kuma
san yadda za a yi da su. Ba kowaxanne kwanuka ne

221
Tunaninka Kamanninka
suka dace da xaukar abinci ba; wasu na ado ne;
wasu kuma na zuba furanni ne; harwayau, wasu na
xaukar shara ne. Don haka bai kamata a ba wa
kwano fassara xaya ba don shi kwano ne, ba tareda
an nazarce shi ba. Ashe, ‘Kwano’ a nan yana nufin
abubuwa da yawa.

Daga tunani irin wannan za mu ga: ba kowanne


mai kuxi yake da arziki ba; ba kuma kowanne ma-
lami yake da ilmi ba. Ba kowanne Kare ke cizo ba,
ba kuma kowacce dabba ce kidahuma ba. Ba
kowanne sarki ke mulki ba. Ba kowanne wuridi
yake ibada ba. Kamar yadda ba kowacce dariya
take bayyana jin daxi da bushaha ba. Wata dariyar
ta qeta ce, kamar yadda wani kukan yake na jin
daxi. Wani a wuridinsa sharri yake neman qul-
lawa, wani kuma kuxinsa yake qirgawa da ‘ya’yan
carbin. Wani Karen haushi kawai ya iya, wani
kuma na wasan yara ne. Sai an nazarci kowanne
abu tukuna, sannan za a san haqiqaninsa. Sannan
za a san ko menene shi.

A nazarin halayen mutane, shin, za mu iya cewa


kowa yadda ake zatonsa, ko yadda ake zaton an
san shi, haka lallai yake? Shin ma wai, za mu iya
zuba al’umma a kwano xaya mu ce duk haka suke
don kawai ana yi masu take haka? Ko kuwa za mu

222
Tunani da Nazari
iya cewa nama daxi gare shi a bakin kowa? Ko duk
sarki mai alfarma ne, duk talaka kuma quntatacce?
Ba shakka, zai zama wawanci mu zuba mutane ko
wasu abubuwa a kwano xaya, mu ce duk daidai
suke, domin duk a cikin kwano xaya suke. Shin zai
zama hankali mu ce halayen duk ‘yan-tagwaye
xaya ne ta ko’ina muka aunasu, ko da kamaninsu
iri xaya ne ta kowanne gefe muka duba su? Me-
nene bambancin mahaukaci da mai rawa ba kixa?
Menene bambancin siliki da alawaiyo?

Yadda kwanuka suka bambanta, haka mutane suka


bambanta. Kai, ko a dabbobin ma, akwai masu
hankali irin nasu, ba dukkaninsu ne kidahumai ba.
Iya bambance abubuwa, tankaxesu da rairayesu, ba
qaramin ilmi bane. Amma wannan aiki ne na masu
haqurin nazari waxanda suka san muhimmancin
bambance abubuwa. Ko a fahimtar halayen mu-
tane, sai ka ga abinda ya dace da wani bai dace da
wani ba. Abinda wani ya xauka da muhimmanci,
sai wani kuma ya banzartarda shi. Haka, in ba ka
lura ba, sai ka xauki mutum mai kirki ka sa shi a
matsayin da za ka ga rashin kirkinsa; ko ka ga mu-
tum fes fes da shi, amma ba ya wanka, watau a
fuska kawai tsabtarsa take. Da ya tuve, sai ka ga
dauxa ko ma kirci a qirjinsa. Kamar dai ka ga mi-
ciji ne, nan da nan ka shara da gudu ba ka san wan-

223
Tunaninka Kamanninka
nan micijin baya sara ba. Ko kuma ka fahimci
murmushin wani tamkar alama ce ta kirki, nan
kuwa gani ya yi za ka faxa rami. Ba shakka akwai
fuskoki masu murmushi a fili, amma turvunannu a
zuci. Wasu a hannun gaisuwarsu kunama suka
voye. Wasu a hirarsu ta yabo, munafurci suka
qulla. Abubuwa ba kodayaushe suke yadda ake
ganinsu ba. Sai a duba a hankali.

Wani ba za ka san iya aikinsa ba, sai ka ba shi


damar yin aikin. Ba za ka san qwazo da hikimar
matarka ko xanka ba, sai ka amince masu da wata
hidima daidai su. Idan ka bar matarka a qulle, ko
‘yarka a dankwafe, to har abada ba za ka iya
saninsu a ainihin yadda suke ba. Haka ba za ka
san yadda zamanin gaba zai yi watsi da su ba,
domin watakila ba ka nan. Wasu matan, mata ne
kawai a siffance, amma zuciyarsu da qwazonsu
sun fi na maza. Wasu mazan kuma mata ne ta
kowanne gefe ka dubasu, illa a kayan sawarsu.
Toh amma, ta yaya za ka san haka, idan ba ka yi
nazarin kowa ka ba shi damar da yakamata a san
ko waye shi ko ita ba?

Dáma ba qaramin ‘yanci take haifarwa ba. Kuma


sai da ‘yanci za a san qokarin mai shi. Kamar dai
Uba ne, ko Shugaba, wanda ya takura xansa ko

224
Tunani da Nazari
jama’arsa domin su yi biyayya a gareshi. Toh, zai
sami biyayyar, amma fa ba ta soayya ba, sai dai ta
tsoro. Daga ranar da tsoron ya fice, Uban ko
Shugaban, sun shiga uku; sai juyin juya hali. Ko da
ga Allah (swt) ne, ba tsoronSa Yake so ka ji don
Zai iya azabtaka ba. Haka, ba biyayyarka Yake so
don Zai iya ni’imtaka ba. Allah (swt) Ya fi so ka so
shi da soyayya ta gaskiya, ko a ina Zai sa ka.

Don haka, tsoro kaxai ba shi ne siffar mumini ba.


Soyayya ga Allah ita ce siffar. Idan ka tsorace Shi
don Yana da Wuta, toh a gaskiya Wutar ka ke tsoro
ba Shi ba. Idan ka bi Shi domin Yana da Aljanna,
toh a gaskiya Aljannar ka fi so fiye da Shi. Da Bai
yi maka zancen Aljannar ko Wutar ba fa? Lallai a
yi tunani mai zurfi a kan wannan domin a iya bam-
bancewa. Wanda yake sonka da gaskiya, ba zai
keta haddinka ba; ba zai vata maka da gangan ba,
ba zai ci maka amanarka ba, ba zai yi abubuwan da
ba ka so ba. Amma mai tsoronka, yana gudun aza-
barka ne kawai. Shugaban da ake tsoro sai a bi shi
sau da qafa, da ya kau sai zagi, domin dama can ba
sonsa ake yi ba. Shi kuma bai iya bambancewa ba.
Wasu abubuwa fa ba yadda suke ake ganinsu ba.
Ladabtarwa ta hanyar tsoratarwa ba ta qarko,
amma ta hanyar soyayya sai ta kafa tushe mai
qarfi, furanninta su yaxu nan da nan. Lallai a bam-

225
Tunaninka Kamanninka
bance biyayya don tsoro da biyayya don soyayya,
sannan a duba hanyoyin da za a gina abinda zai yi
qarko. “Tsoron Allah”, na soyayya da biyayya ne.

Malamanmu masu bulala a hannunsu, cin zalin


yara kawai suke yi, domin idan da za a auna na-
sarorinsu na ladabtarwa a ma’unin kimiyya, ba
abinda za a samu na gamsarwa. Irinsu ke sa yara
su zama taqadarai ko ma daqiqai. Yara suna son a
nuna masu soyayya, a kuma faxakarda su amfanin
ilminsu domin su maida hankali cikin sanin abinda
ya dace da su. Ta haka za su zama masu biyayya
da qoqari a duk inda suke, domin sun san su za su
fi kowa cin amfanin biyayyarsu da ilminsu.
Haqiqa, ladabtarwa in ta zama tilas, sai a yi ta.
Wanda aka ladabtar xin kuma ya fahimci dalilinta
da dacewarta domin ya guji maimaita rashin ladab-
insa, ko halayensa na banza.

Iya bambance abubuwa da aza komai a mazaunin


da ya dace da shi ba qaramar hikima bace. Ko da
kai ne da kanka, ka iya auna kanka daidai, ka
nazarci kanka daidai, ka fahimci kanka daidai, to
ba qaramar ribar rayuwa za ka samu ba, don ka san
yawancin abubuwan da suka dace da kai. In kai
mai nauyi ne, ba za ka shiga layin masu tsalle ba,
balle ka ji kunya. Amma, idan aka ce ‘danne min

226
Tunani da Nazari
nan’, ka san da kai ake, kuma in ka danne xin ba za
a xaga ba. Wannan magana muhimmiya ce ko da a
wajen auna matsayinka, damarka da mutumta-
karka. Haka, ta hanyar nazarinka, al’umma ita
kanta za ta iya aunaka.

Misali: Idan a sikelin cikar mutum, watau, Ingancin


mutum, akwai abubuwan dubawa waxanda
kowanne yana da nasa awon. Idan a ce maqurar
inganta ita ce a inda aka sami awon waxannan
abubuwa sun cika 100 bisa 100, to ashe lallai ne a
binciki kowanne daga cikin waxannan abubuwa
domin a ga awo nawa suka bayar a cikin xarin.
Idan a misali, a awon Inganci, aka ce:

‘Gaskiya’ tana da awo 20 cikin 100; ‘Ilmi’ da am-


fani da shi’ yana da awo 15; ‘Yakana’ tana da awo
15; ‘Kyauta’ tana da awo 10; ‘Tausayi’ yana da
awo 10; ‘Biyayya’ tana da awo 10; ‘Son jama’a da
murmushi’ suna da awo 10; ‘Iya aiki’ yana da awo
5, duk sauran suna da awo 5; to ai ka ga za a iya
cewa jimlar ingancin wane ya kai awo 40 ko 60
cikin 100, ko dai yadda aka fahimce shi aka kuma
auna shi da qiyasin hikima da adalci. Shi kansa zai
iya yi wa kansa wannan awon fiye da kowa, ya
kuma gyara ingancinsa yadda ya dace, in dai shi
mai qaunar kansa da gyara ne.

227
Tunaninka Kamanninka
Amma fa duk waxannan, mutum ya iya sirkawa
yadda ya ga dama a guraren da ya ga dama, kuma
a fahimce shi a hakan in ba a yi nazari mai zurfi
ba. Wani ya surka daidai, wani kuma ya surka a
kuskure. Waxanda suka surka da hikima, kuma
saboda Allah domin su inganta kansu, sai su sami
yabo ta kowanne gefe aka duba, kuma asirin halay-
ensu ba zai tonu ba domin babu wani kuskure.

Amma waxanda suka qi duba kowanne ma’auni


yadda ya dace domin su inganta kansu, sai ka ji
ana cewa, ‘kai wane da gaskiya yake, sai dai rowar
tsiya’. Ko kuma a ce, ‘akwai iya aiki, sai dai rashin
tausayawa’. Wasu ma ka ji an ce, ‘me za a yi da
wane? Wannan kirkin da murmishin duk na banza
ne, in ka ba shi amana, sai a lahira’. Wani a ungu-
warsu, sai ya kasance mai inganci da yawa a gun
‘yan-unguwar, amma da ya bar gurin, sai ya xau
xabi’arsa ta ainihi. Idan ‘yan unguwar suka gan shi
a wannan gurin, sai ka ji suna cewa, ‘anya kuwa
wane ne?’ Ko, ‘ashe haka wane yake?’ Ashe dai
yadda suke zaton sun san shi ba haka yake ba,
domin ba su yi nazarinsa da zurfi ba.

A duk waxancan awon, babu hidimomin addini da


ibada a cikinsu, domin muna zancen fahimtar mu-
tum ga mutum ne kawai. Idan muka kawo addini

228
Tunani da Nazari
da ibada, to wa zai iya voyewa Allah (swt) ainihin
kammaninsa? Ko kuma wa ya san abinda mutum
yake yi a bayan qasa? Duk ibadarka, Allah (swt)
Ya san ko waye kai. Sai dai ka burge mutane wax-
anda ba su san sirrinka ba. Idan mutane suka ce za
su yi awo ne da ibadarka, to sai su bi ka duk inda
ka ga damar kai su don yawan ibadarka; ko su
kauce maka duk ta inda ka ja su, don qarancin
ibadarka. Amma ba a nan take ba. Wa ya san
abinda ka ke yi a asirce saboda Allah? Wa kuma ya
san abinda ka ke yi a asirce saboda Iblis? Haqiqa,
wanda aka sani da ibada, akwai alamun mutumin
kirki ne shi ko ita. Amma a nan awon ya tsaya.

Mutane za su fi fahimtar mutum idan suka auna


xabi’un da suka san shi da su tun farko, suka ajiye
addininsa da yawan wuridansa sai daga qarshe.
Daga awon ingancin xabi’unsa kaxai ma, sai su
fara samun shaida ko addinin nasa na gaskiya ne ko
kuwa na bilhu ne. Idan suka xau yawan ibada da
farko, to za su yi mugun kuskure, domin sai su fara
amincewa ingantacce ne tun ma kafin su auna in-
gantar tasa. Ta haka sai su xora mutum a matsayin
da bai dace da shi ba, domin ba su san shi ba.
Abinda suke zato ba haka yake ba. Kamar dai a
kama liman ne da kwartanci, ko sarki da kwalabe.
Ko ba a kama su ba, idan waxannan halayensu ne,

229
Tunaninka Kamanninka
toh ba su cancanci limancin da sarautar ba. Amma
tunda ba lallai ne duk mutane su san waxannan
xabi’u nasu ba, sai su yi ta binsu cikin rashin sani.
Wasu limaman ba su dace da ko sharar masallaci
ba; wasu sarakunan kuma ba su dace da zama
dogarai ba; wasu shugabannin ko kaxan ba su dace
da muqamansu ba. Amma kaico! Haka yawanci
ake tafiya da ka, saboda rashin sani ko qin binci-
kawa, ko tsoro, ko kwaxayi, ko wani abu dabam.

Akwai waxanda in sun zo auna inganci, sai su ba


wa dukiya ko kuxi muhimmanci a awonsu, su ce
dukiya ko kuxin suna da awo 20 ko ma 30, ko dai
yadda kuxi suke da muhimmanci a cikin al’um-
marsu. Wannan al’umma ba ta kirki bace. A
al’ummar kirki, sai an yi amfani da kuxin ko duki-
yar tukuna, sannan za a san a ina za a sa su. In ba a
yi amfani da su ta hanya mai kyau ba, to suna cikin
abubuwan da ake tsarawa a awon rashin inganci,
domin kuxi sukan iya jefa mutum cikin hanyoyi na
rashin mutumci waxanda suka dace da la’anta. Ko
Zakka aka tabbatar ka qi fitarwa da gangan, toh ka
cancanci a la’anceka. Zakka tana daga sashen
addini, amma ‘taimako’ yana sashin al’adu na-
gari, kuma mutane za su iya auna shi. Don haka,
duk abubuwan da suka shafi addini, sai a ajiye su
gefe guda da farko, domin a fahimci mutum sosai.

230
Tunani da Nazari
Haka kuma, abin a ce: A awon Munanci misali:
‘Qarya’ tana da awo 10; ‘Munafurci’ yana da awo
25; ‘Jahilci’ yana da awo 10; ‘Rashin Yakana’
yana da awo 10; ‘Rowa’ tana da awo 10; ‘Qeta’
tana da awo 10; ‘Rashin Kunya’ tana da awo 10;
‘Kin jama’a da saurin fushi’ suna da awo 5;
‘Lalaci’ yana da awo 5; duk sauran suna da awo 5.

To ka ga ashe, za a iya cewa ‘Munancin wane ya


kai awo 50 ko 60’ a yadda mutane suka fahimce
shi, suka kuma auna shi da hikima da adalci. Haka
kuma ya iya sirka waxannan ma’aunai yadda yake
so a guraren da yake so. A inda aka san shi, sai a yi
watsi da shi a siffarsa ta mutumin banza. A inda ba
a san shi ba, sai ya ci da buguzun har sai lokacin da
ya fallasa kansa, ko kuma masu haqurin nazari
suka fahimce shi. Dá ma an ce, “Munafunci dodo
ne, yakan ci mai shi”. Saboda haka, duk yadda ka
sirka waxannan, ba yadda za a yi ka fiddo da kanka
illa a mutumin banza. Ba shakka, mutum mai da-
bara, shi kansa, zai iya yiwa kansa wannan awon
fiye da kowa, ya kuma gyara ingancinsa yadda ya
dace, idan shi jarumi ne mai son ingantuwa da
kuma karvuwa a cikin jama’a.

Marasa mutumci za su iya shiga rigar mutumci nan


da nan ba tareda wahala ba, amma ta xan lokaci

231
Tunaninka Kamanninka
qanqani, don neman biyan wata bukata, ko don
wani dalili. Amma, mai mutumci ba zai iya shiga
rigar rashin mutumci ba ko menene dalilin, ko da
ta lokaci qanqani, domin ba za ta tava dacewa da
shi ba. Da ya ganta, sai ya qyameta, ko da kuwa da
mayanin siliki da zaren dinare aka xinka ta. Masu
haqurin nazari ba sa samun wahalar bambancewa
tsakanin masu inganci da marasa shi, kowacce irin
riga suka sa. Haka kuma duk yawancin abubuwan
da za su zo gabansu, nan da nan za su iyar fahimtar
yanayin abin su kuma yi magana ta hankali a
kansa. Su ne suke iya fallasar marasa mutumci ko
da sun zo a rigunan mutumci. Su ne kuma suke iya
gane mai nutumci, ko da a cikin tsumma yake.
Amma a al’umar marasa mutumci, ‘yan iska suke
tashe, kuma su ne shugabanni domin yawancin
jama’ar sun qi, ko sun kasa bambance halayensu;
sun qi sa su a cikin ajijuwan da suka dace da su.
Wannan kuwa, domin halayensu kusan xaya. Don
haka, suka kasa fahimtar bambancin wahalunsu da
irin shugabancin da suka amince da shi.

Algus da sauran ha’inci ko waxanne iri ne, har da


na halaye, suna daga cikin miyagun xabi’un da ake
illatar mutane da su. Akwai masu yin algus a ma-
ganganunsu da harkokinsu, sai ka rantse su ne dai-
dai, ka kuma halaka wajen amfani da su a gaba.

232
Tunani da Nazari
Sai ka ji wasu na wa’azi a cikin abokansu ko a
wata walima in an gayyacesu, amma duk xabi’un
kirkin da suke magana a kai, ba halayensu bane.
Sai ka ga mace mai tsarin siffa, ashe duk kayan
kanti ne. Sai ka ji an ce ‘Galadima ya zo’, ashe
galadiman ‘yan banga ne. Ko ka ga agogo kamar
mai tsada, amma na giri ne. Ga dai misalai nan bar-
katai. Wani mawaqi mai hikima, Jan-kixi, yana
cewa, “Holoqo hadirin Kaka, duba shi da kyau
duba ka gani…” Watau, ga hadiri ya kai hadiri,
amma babu ruwa a cikinsa. In aka daka ta tasa sai
dai a mutu da yunwa. Wasu kuma ka ji magana
tiryan tiryan har da rantsuwa a cikinta. Amma
kuma, ‘mafi rantsuwa mafi qarya’. Haka za ka yi ta
tararwa ga mutane masu yawan gaske, har da wasu
malamai da sarakuna da shugabanni da masu kuxi
da ‘yan kasuwa da ma’aikata da ‘yan siyasa.
Yawancin rigunan da suka sa ba su dace dasu ba.
Amma mutane sun kasa, ko sun qi, bambancewa a
tsakaninsu don a san na kirki, as san na banza.

Addini shi kansa, musammam na Islam; yadda


wasu mutane suke ta fassara shi cikin jahilci, ba
haka yake ba. Sai ka ga musulmi amma ya zubarda
halayen musuluncin; ka ga wanda ka ke maqalawa
kafirci, shi ma kuma bai xau xabi’un kafircin ba.
Idan ka nazarci mutane a cikin addinansu, sai ka

233
Tunaninka Kamanninka
rasa inda za ka wasunsu a haqiqa. In kai ne alqali,
a ina za ka ajiye wancan munafukin musulmin?
Shin furuci kaxai ya yi imani da Allah xaya ne,
kuma Muhammadu ManzonSa ne, shi ne zai kai
shi ga tsira, ko kuwa furucin haxe da ayyukansa na
tabbatarda ingancin furucin ne za su nuna shi mai
cikakken imani ne a kan hanya miqakkiya?

A musulunci, mun san ayyuka su ne suke nuna


gaskiyar furucin. Wanda ya furta, amma kuma ya
qi aikatawa ya zama munafuki. Amma, Allah (swt)
Ba ya raina aikin mumini komai qanqantarsa. Don
haka, mai raina aikin alhairi komai qanqantarsa,
bai san hasarar kyakkyawan sakamakon da yake yi
ba. Mun ji Hausawa, suna cewa, “Xan haqqin da
ka raina, shi ke tsokane maka ido”, ko menene
haqqin, ko na alhairi ne, ko kuma na sharri, domin
ma’aunan Allah (swt) suna da yawan gaske. Wasu
abubuwa ba yadda ka ke zatonsu suke ba. Ga wata
qissa mai ma’ana don misali:

An yi wani babban malami a wata Qasa a cikin


tarihi. Mutum ne mai son Allah, mai kuma hidimar
addini da kyaun xabi’u. Wata rana sai Allah (swt)
Ya turo Mala’ika (Jubril) domin ya yi masa al-
bishir da gidan Aljanna. Wannan malami ya yi
matuqar farin ciki da cikakkiyar godiya da wannan

234
Tunani da Nazari
albishir da aka kawo masa. Amma da ya nutsu, sai
ya tambayi Mala’ikan: ‘Me Allah (swt) Ya yi am-
fani da shi a cikin hidimomina na ibada da
xabi’una na kirki, Ya yi min kyauta muhimmiya?’

Da Mala’ika ya dawo, sai ya ce masa ba xaya a


cikin waxannan. ‘Dalilin kawai da ya sa Allah
(swt) Ya yi maka wannan kyauta shi ne: Akwai
wata rana kana alwala, sai Quda ya sauka a kan
hannunka ya sha daga danshin ruwan da yake han-
nunka ba ka kore shi ba. Wannan kawai ta sa Allah
(swt) Ya yi maka Rahma, Ya kuma ba ka Aljanna’.

Malam ya yi mamakin wanan abu. Tareda qaskan-


tarda kai, ya sake tambayar Mala’ika: ‘Toh sallo-
lina da sauran ibaduna, a me suka tashi?’ Da
Mala’ika ya dawo sai ya ce masa: ‘Idan aka haxa
dukkanin sallolinka da sauran ibadunka, ba za su
iya sai maka idonka xaya ba. Idan kuma ba ka da
idanun, to ba za su sai maka, ko kunnuwanka, ko
qafafunka ba; ballanta na qwaqwalwarka, ballan-
tana kuma halittarka gaba xaya da kawo ka wannan
duniyar har ka san akwai Wanda Ya halicceta’.
Malam ya xaga kansa sama ya ce, ‘Allahu Akbar!’

Allah (swt) Shi ne mai yin abinda Ya so a kan


dalilai da ma’aunan da suka dace da irin xau-

235
Tunaninka Kamanninka
kakarSa. Ashe wasu abubuwan da mutum ya raina
na alhairi ko na sharri, suna kuma da irin nasu mu-
himmanci da sakamakon a wajen Mahaliccinsa. Ba
shakka, wasu abubuwa ba yadda muka fahimcesu
suke ba. Haka kuma, ashe ‘sharri’ qanqani, ya iya
kai ka ga halaka babba. Ina masu fyadar jakuna
kamar an aiko su? Ina masu qwacewa yara
alawarsu? Ina masu korar Mage in ta roqesu?
Kada ku raina muhimmancin waxannan wajen
Mahaliccinsu. A wajen Allah (swt) babu bambanci
tsakanin zahiri da baxini. Yana sane da sirrin
kowannensu, domin dukkaninsu a tareda Shi suke,
kuma Shi ne Mai iko da su a kowanne lokaci. Mu
ne jahilai, waxanda zahirin ma ba mu fahimce shi
sosai ba, kuma har yanzu ba mu san haqiqaninsa
ba. Sai mun nutsu za mu fahimci kaxan.

Sanin haqiqa, ba shakka, sai Allah (swt) domin


Shi kaxai ne ita. Watau, Shi kaxai ne tabbatacce.
Duk wani abu ga shi nan ne dai kawai tamkar a
mafarki yake. Idan muka yi zurfin tunani da auna
abubuwa, lallai mu yi al’ajabin wannan rayuwa
tamu. Lallai mu yi tambaya: ‘anya kuwa ba a cikin
wani gagarumin mafarki muke ba, a yadda Allah
Ya tsara abubuwa? Shi kaxai ne fa tabbatacce! Me
ya bambanta zahirin farkawarmu da zahirin
mafarkinmu? Barcin kawai shi ne bambanci. A

236
Tunani da Nazari
wasu lokatan ma, sai mu yi mafarki cikin farkawar
tamu, mu ga abubuwa tamkar a mafarkin, nan
kuwa idanunmu biyu, mu rasa yadda aka yi, sai
mun yi zurfin tunani sannan za mu fara fahimta.

A garemu, zahiri dabam take da baxini, wanda ba


mu da sani ko qanqani a cikinsa. A zahirin, sai
mun duba mun nutsa sosai sannan za mu iya fahim-
tar wani abu wanda zai amfanemu. Idan ba mu yi
la’akari ba, sai mu dulmiya cikin duhu; zahirin ta
zame mana baxini. Da wannan ta faru kuwa, shi-
kenan mun shiga wahala. Kafin a fita an cutu.

Rashin bincika mutane da sauran abubuwa, suke


sa mu zavi na banza; suke sa a ci mu da buguzun;
su ke sa mu girmama raunanan shugabanni; suke sa
mu cikin vata; suke sa mu cikin qangin rayuwa iri
iri. Wasummu ba su da ma’aunin inganci, saboda
haka, sai su kai daraja ga wanda ba shi da ita, su
kuma hana mai ita.

Wasu da an ce, ‘ai wane digirinsa biyu’, shikenan


sai su maishe shi wani babba. Wasu da an ce, ‘ai
shi ne sarki’, sai su faxi gabansa irin yadda ba sa yi
a gaban Allah (swt). Wasu da an ce, ‘ga mai-kuxi
can’, shikenan sai su saduda su zama yaransa.
Wasu da an ce, ‘wane gurgu ne’, sai su xauka ba

237
Tunaninka Kamanninka
shi da wani amfani. Wasu da an ce, ‘wallahi’, sai
su yarda. Waxansu da sun ga mara galihu, sai su
tsane shi. Duk waxannan ba lallai ne a ce sun can-
canci amincewa, ko qi, haka ba. Cikin rashin sani
da rashin bincike, sai ka kuskure a wajen ajiye mu-
tane a matsayin da ya cancancesu. Irin wannan ta-
kan sa wasu su yi da-na-sani; ta kan kuma kawowa
al’umma hasarar mutane ingantattu, waxanda suka
cancanci a ba su amanar shugabanci.

An yi wani mutum baqo a wata unguwa wanda ba


ruwansa da shiga harkokin da ba nasa ba. Kullum
yana kaxaice yana sha’aninsa wanda shi kaxai ya
fi sani. Talaka ne shi qwarai, amma ba ya roqon
kowa abinci. Saboda haka sai jama’ar unguwar
suka xauka mahaukaci ne shi, ganin yadda tsarin
rayuwarsa yake. Wasu lokatan ma, yara har dariya
suke yi masa manya na gani. Wannan bawan Allah
dai bai tava qorafi ba.

Wata rana xaya daga cikin makwabtansa, ya tafi


Hajji. A yayin da yake xawafi, sai ya ga wannan
mutum shi ma yana Dawafi, amma a cikin ka-
manni da tufafi masu kyaun gaske da ban sha’awa.
Wannan abu ya ba shi mamaki qwarai da gaske.
Ya ce a zuciyarsa, ‘ko wannan mutum da muke
zaton mahaukaci ne, ko ma waliyi ne? Yaushe ya
zo Makkah? Ashe yana da halin tafiya har nan?
238
Tunani da Nazari
Da ya gama xawafinsa, sai ya tsaya daidai bayan
‘mukami Ibrahim’ yana jiran wannan mutum ya
gama nasa xawafin. Da shi ma ya gama, ya kuma
iso gurin, sai wannan makwabci ya gaishe shi, gai-
suwa ta girmamawa. Mutumin ya amsa cikin
nutsuwa da haiba a fuskarsa. Wannan makwabci ya
ce, ‘ka gafarceni Malam. Wallahi rashin sani ne ya
sa xabi’unmu gameda kai suka zama haka’. Malam
ya ce, ‘Ba komai. Amma don Allah ka rufa min
asiri, kada ka faxawa kowa a gida cewar ka ganni a
nan’. Maqwabcin ya amsa zai yi hakan; ya kuma
roqe shi ya yi masa addu’a, shi kuma ya amsa.

Da wannan alkawari suka rabu; kuma bai tava tona


asirin ba. Bayan yan shekaru da dawowarsu, sai
makwabcin ya kamu da ciwon ajali. Don haka, ya
shaidawa matarsa cewar lallai in rai ya yi halinsa,
wannan malami yake so ya yi masa Sallah. Matar
ta yi mamaki, har tana zaton ko zafin cuta ne ya sa
shi wannan bukata ta cewar mahaukaci ya yi masa
Sallah. Ya sanarda ita ba haka bane. Sannan ya ti-
lasta mata ta yi alkawri a kan hakan. Da ya rasu, sai
matar ta shaidawa duk ‘yan’uwansa wannan wasi-
yya tasa. Da ta ga sun fusata, sai ta ce masu ita kam
ta yi wa mijinta alkawarin cika wannan bukata
tasa; lallai wannan mutum ne zai Sallace shi, ko
wasu sun yarda ko ba su yarda ba.

239
Tunaninka Kamanninka
Da suka ga ba yadda za su yi, sai suka haqura.
Suka aikawa wannan mutum saqon wasiyyar
mamacin. Mutumin ya yi shiruu, sannan ya ce,
‘Kun tabbata haka ya bukata?‘. Suka ce, ‘Haqiqa’.
Da aka zo Salla, mutum ya shige gaba ya fara yi
wa mamacin Sallah, sai jama’ar suka ringa ganin
wani haske har da gizo-gizon Ka’aba a cikinsa,
watau tamkar a Al-Haram suke yin wannan Sallah.
Yawancisu suka ruxe cikin al’ajabin wannan abu.
Bayan Jana’izar, sai suka hanzarta suka dawo gida
domin su ziyarci wannan Waliyyi. Amma da suka
iso, sai suka tarar ya bar gidan; ya bar unguwar; ya
bar garin xungum. Ba su sake ganinsa ba. Suka yi
ta cigitawa, amma Ina!

To, ina masu raina mutane domin ba su da galihu a


idanunsu. Ina masu wulakanta maqwabtansu, ko
masu korar masu nema a gurinsu domin sun zaci
waxannan mutane ba su isa ba?

A xaya gefen kuma, idan ka bar halaye da yanayin


rayuwar wasu, ka ce za ka auna waxansu muqamai
ko darajoji ko adajen duniya da wasu suke da su,
to idan da za ka iya yin zurfi cikin zukatan masu
su, mayiwuwa ne ka tarar cewar su kansu ba jin
daxinsu suke yi yadda ka zata ba. Tara adajen
duniya dabam yake da tara jin daxin duniyar.

240
Tunani da Nazari
Wasu abubuwa kana hangosu ne daga nesa kawai,
sai ka zo kusa za ka san ba haka suke ba. Idan ka ji
masifun da wasu suke ciki, duk kuma saboda
abinda suka tara, to sai ka gode Allah (swt) kai ba
ka tara waxannan abubuwa ba. Wasu masu kuxin,
kuxin ne jidalinsu. Wasu masu sarautar, ita ce wa-
halarsu da tararradinsu. Wani kuxinsa ko mulkinsa
ne za su kai shi kurkuku ko ma lahira. Wasu kuma,
sune su ke jawo masu baqin jininsu. Wasu kuma su
ne hanyar nisartarsu da Allah.

Wasu ga su ana ganin babu irinsu a dukiya, amma


bashin da yake kansu ya fi qarfinsu, ba wanda ya
sani. Wasu sun xauko rigimu iri iri, ba su san inda
za su kaisu ba. Wasu sai sun mutu magada za su
shiga rigima. Wasu masu son sarautar, alla-alla
suke iyayensu ko ’yan’uwansu su mutu domin su
gaje su. Wasu ma su ne sanadin mutuwar iyayen
nasu. Wasu ga kuxin baja-baja, amma talauci ya ci
qarfinsu; wasu ga sarautar buja-buja, amma nagarta
ta fi qarfinsu. Wasu muna ganin ba abinda ba su da
shi, amma su suna ganin ba su da komai. Wasu
kuma hankalinsu na can a kan wasu abubuwa da
suka rasa, sun manta da waxanda suke da shi.
Wasu duk kuxinsu da mulkinsu, ba su da cikakki-
yar lafiya; wasu ma ba mai qaunarsu ko da a cikin
zuri’arsu. Ga wani can ya tara abinci a rumbu,

241
Tunaninka Kamanninka
amma ya kasa cin ko qwaya. Wani ga littattafan
ilmi nan, amma duk xabi’unsa na jahilai ne. Wani
ga sarautar, amma zuciyarsa a quntace. Wani ba
abinda bai mallaka ba, amma kuma ba shi da ko-
mai, ko kuma kullum cikin baqin ciki; zuciyarsa a
qone don wasu dalilan da ba a sani ba.

Wasu da yawa, kai ne abin sha’awarsu, saboda la-


fiyarka, ko saboda ‘yancinka, ko saboda ilminka
da azancinka, ko saboda farin jininka, ko saboda
yakanarka da kyaun zantukanka, ko saboda wani
rufin asiri da suka hango tareda kai, wanda sun san
ba su da shi. Mutum shi kaxai yake iya fassara
kansa daidai, sai dai in zai munafunci kansa da
kansa. Wanda kuwa ya munafurci kansa, to babu
wawa irinsa. Lallai ne mutum ya san ko waye shi,
ya kuma san ya tsakaninsa yake da Allah (swt).
Mutum shi ne kaxai mai iya hangen rayuwarsa ya
shiryata yadda yake ganin za ta fi dacewa da shi.
Mutum shi ne kaxai ma’aunin kansa na gaskiya.
Amma, a yadda wani ke hango wani ko wasu; da
yadda wani yake auna wani ko wasu; da yadda
wani ke zaton wasu abubuwa, duk ya iya tararwa
ba haka suke a ainihinsu ba. Nazarin wani dabam
kuma, ya ba da wata ma’anar dabam. Haka ake
tafiya, har sai cikakken nazari da aunawa sun fiddo
da gaskiyar tsarin mutum da ingancinsa.

242
Tunani da Nazari
Don haka, ya zama wajibi, mutum ya kasance mai
yawaita tunani da zurfin nazari a kan komai,
musammam ma a halayen da ya sami kansa ciki.
Kada mutum ya yi saurin hukumta mutanen da bai
nazarta ba. Kada mutum ya yi saurin qyamar mu-
tane domin a idanunsa ba su cimma awonsa ba.
Masu iya bambance abubuwa cikin haquri ba da
gaggawa ba, sune za su iya sarrafasu su kuma ci
moriyarsu yadda yakamata. Masu iya bambance
abubuwa sune za su iya yin jawabi a kan abubuwa
yadda ya dace da kowannensu. Ko a cikin mutane
ne, ka iya bambance halayensu da bukatansu, to za
ka fi iya zama da su. Hakama dabbobi. Idan ka ce
yadda za ka shaqata a bayan Tunkiya, haka za ka yi
a bayan Jaki, to kuwa wataran ka sha harbi.

Yawancin abubuwa ba yadda suke muke ganinsu


ba. Lallai a duba sosai a yi cikakken nazari.

A wani zamani can cikin tarihi, an tava yin wani


mashahurin Malami mai ximbun ilmi; sannan ga
jama’a da almajirai masu yawan gaske. A kan je
neman ilmi iri iri gurinsa, har da kimiyyar azanci
da hikima, daga ko’ina a wannan vangare na
duniya. Amma, duk lokacinda mutane suka
tambaye shi asalin wannan ilmi nasa, sai ya nuna
masu wani qaton littafi yana cewa duk ilmin nan

243
Tunaninka Kamanninka
nasa yana qunshe a cikin wannan littafi xaya tak,
wanda yake a adane a cikin turakar littattafansa.

Da Allah Ya yi masa rasuwa, sai magada da


xalibai suka yi hanzarin xauko wannan muhimmin
littafi don kwaxayin fahimtar ilmin cikinsa. Suka
fara buxa shafunan wannan qaton littafi xaya da
xaya, amma ba abinda aka rubuta cikinsu. Sai da
suka iso kusan qarshen littafin suna al’ajabin
wannan abu, sannan suka taradda shafi xaya tak da
rubutu bai fi layi uku cikinsa ba. Abinda kawai aka
rubuta a cikin wannan shafi shi ne:

“Duk wanda ya fahimci bambancin da yake


tsakanin kwano da abinda yake cikinsa,
toh ya sami isasshen ilmi.”

Ba shakka wannan abin mamaki ne, kuma wannan


magana tana bukatar zurfin tunani. Kamar yadda
muka fara tun farko, bari mu nanata cewar,
wannan kwano ya iya zama komai. Abinda yake
cikinsa ya iya zama komai. Duk maganar ta
fahimtar bambanci ce. Amma fa ba bambanci cikin
hanzari da rashin tunani da nazari ba.

Misali: Idan ka fahimci bambancin duniya, in ita


ce kwanon, da al’ummun da suke cikinta, ba

244
Tunani da Nazari
shakka ka sami ilmi mai amfanin gaske. Idan ka
fahimci bambancin addinin Islam da musulman da
suke cikinsa, za ka iya riqe addininka komai rintsi,
ka kuma zama musulmi nagari. Ba za ka raina
addininka don ka ga yadda wasu musulmi suka
watsarda shi ba, domin tuni ka bambantasu. Amma
idan ka xau xabi’ar wasu musulmi, ka ce wannan
shi ne musulunci, to ba shakka ba zaka san musu-
lunci ba. Idan kuma ka fahimci bambancin dukiya
da masu kuxi, to rayuwarka za ta fi zama mai
gamsuwa, domin za ka san yadda za ka sarrafata in
ka sameta, da yadda kuma za ka iya ququtawa a
rayuwarka in ba ka sameta ba. Idan ka fahimci
bambancinka da sauran jama’a, to za ka iya zama
da su lafiya, domin za ka san abubuwan qinsu da
na sonsu, da waxanda za su iya yi da waxanda ba
za su iya ba. Haka kai ma dangane da su. Duk ma-
ganar ta nazarin banbanci ce, domin ka da ka haut-
suna tunaninka ka shiga cikin vata.

Idan halayen mutane nagari da qoqarinsu da


fafutukarsu su ne ma’aunanka, ba dukiyarsu ko
muqaminsu ba, to ba shakka, ba za ka yi kuskure a
kansu ba, kuma ba za ka wahaltu a banza a kansu
ba. Wasu sai ka ga abinda kawai suke taqama da
shi shi ne asalinsu, watau su ‘ya’yan wane ne,
amma fa ba su da wata martaba dabam wadda tasu

245
Tunaninka Kamanninka
ce ta kansu daga qoqarinsu. Duk wanda ya jingina
da asalisa, amma shi kansa bai zama komai ba, to
ya zama wawa. Mafi mahimmanci a gareka shi ne,
‘waye kai a zahirinka da baxininka? Me ka ke yi?’
Lallai mutane su yi la’akari da haka.

Idan ka iya bambancewa tsakanin furuci ko


wa’azin da wasu ke yi, da kuma ayyukansu da
halayensu, to za ka fi saninsu a cikin kamanninsu
na ainihi, ka kuma aunasu. Kada kyaun riga da iya
zance su ruxeka ka yi saurin amincewa. A iya
damfararka. Amma kada tsofaffin tufafi su sa ka
kori mai wa’azi, domin watakila shi ne mai faxar
gaskiyar. An fi jin gaskiya a bakin yaro da wawa,
amma ba su ne suka fi kowa hankali ba.

Wasu abubuwa ba shakka, ba yadda suke ake


ganinsu ba. Ko sama ka xaga kanka, taurari kawai
za ka gani. Idan ba ka iya bambancewa da zurfin
nazari ba, ba za ka san hikimomin Allah (swt) ba.
Ba za ka san kai ma a saman kake ba. Ba za ka san
Rana a yadda take minti takwas da suka shige ka
ganta ba. Dá al’umma tana bambamce abubuwa
irin waxannan gameda mutane da sauran abubuwa,
dá an ci gaba yadda ba a zato. Dá yawancin
abubuwa sun tafi yadda ake sonsu. Dá ba haka ba.
Kukan kurciya ma jawabi ne…….

246
Tunani da Nazari

247
Tunaninka Kamanninka

RAYUWA ABAR MISALI

Wata rana, Ali bin Abu-Talib (as), ya tambayi


Annabi Muhammad (saw), cewar, wacce Sunna zai bi
ya zama cikakken mutum? Sai Annabi Muhammad
(saw), ya yi masa bayanai gameda nasa xabi’un.
Ya ce :
**********************************************

*I “SANIN UBANGIJI SHI NE JARINA”


*II “HUJJA ITA CE TUSHEN IMANINA”
*III “SOYAYYA ITA CE GINSHIKINA”
*IV “TUNANIN ALLAH SHI NE ABOKINA”
*V “DAGEWA ITA CE DUKIYATA”
*VI “TAUSAYI SHI NE ABOKIN ZAMANA”
*VII “ILMI SHI NE MAKAMINA”
*VIII “HAQURI SHI NE MADOGARATA”
*IX “WADATAR-ZUCI ITA CE GANIMATA
*X “K’WAZO SHI NE GWANINTATA”
*XI “IMANI SHI NE K’ARFINA”
*XII “GASKIYA ITA CE CETONA”
*XIII “LADABI SHI NE CIKATA MUTUM”
*XIV “FAFUTUKA ITA CE XABI’ATA”
*XV “IBADATA ITA CE FARIN-CIKINA”

248
Rayuwa abar Misali

249
Tunaninka Kamanninka

Rayuwa
Abar Misali

w
‘Mu yi koyi da Manzon Allah’

annan muhimmin Babi ya zama


wajabtacce a wannan littafi namu, domin kuwa
kulliyar darusanmu sun tattara ne a cikin
waxannan xabi’u na shugabanmu, Annabi
Muhammad (saw). Duk gaba xayansu a cikin
Tunaninsa ya saqasu, sannan suka zama
Halayensa. Ba shakka, ba mu da abin bege irin
kasancewa cikin kyakkyawar Halayya irin tasa.
Koyi da shi ya zama wajibi a kanmu duka.

250
Rayuwa abar Misali
Zai yi amfani qwarai idan na yi qoqarin yin
taqaitaccen bayanin kowacce xabi’a cikin
xabi’un nan 15, domin fito da hikmarta, (a cikin
azanci irin nawa) da yadda za ta iya taimakawa
duk mai son inganta rayuwarsa da rayuwarta.

I.
“SANIN UBANGIJI SHI NE JARINA”
*******************************

Haqiqa, duk wanda ya san Ubangiji, Allah (swt),


ya sami tabbataccen jari. Amma fa ba sanin shanu
ba. Ga yawancinmu, sanin Allah yana da ma’anoni
dabam. Yadda wasu suka fahimci Allah, suke
kuma zancenSa, ba haka wasu suka fahimta ba.
Amma a gaskiya, Allah (swt) Ya shige duk yadda
aka fahimce Shi. Sai dai kuma, tilas mu yi qoqari
irin namu, mu sanShi ta yadda yakamata.

‘Sunayen” Allah (swt), guda 99n nan da muka sani,


watau. “Asma’ul Husna”, ba sunaye kaxai bane, ba
kuma alamu ne kaxai ba. Kulliyar Ikonni da
Halaye ne na Allah (swt). Duk zurfin tunaninmu ba
za mu iya qure wadannan laqabai na Allah (swt)
ba, domin sun qunshe komai a cikinsu. Nazarinsu
cikin nutsuwa da saninsu ko fahimtarsu cikin
hikima tareda yadda suka danganci juna, da yadda

251
Tunaninka Kamanninka
suke da iko a kan komai wanda ya danganci
sunansu, su ne suka tattaru suka ba da ma’anar
“Sanin Ubangiji” yadda Yake, ba yadda muke
zatonSa ba. Waxannan ‘Sunaye’ ba shakka suna
da muhimmanci a tareda mu, tunaninmu da yadda
za mu tafiyarda rayuwarmu a kodayaushe. Su ne
kuma suke gudanarda komai a Sararin Samaniya,
da kuma Lahira ita kanta. Da su kuma komai yake
tabbata. Hasalima dai, ta hanyar amfani da su ta
hanyoyin da Ya koyarda su a garesu, Mala’iku
suke cika kowanne umarni na Ubangiji. Wannan
wani babban ilmi ne mai zurfin gaske wanda masu
xinbum ilmi ne kaxai za su iya yin bayani yadda
za a gane. Abin ya shige wannan xan littafi. Sai a
yi bincike a hankali.

Da Allah (swt) Ya ce, “Zan ajiye Khalifa a


Qasa” (duniyar Arx) ( a Baqara: Aya ta 30), lallai
ne mu fahimci abinda ‘Khalifa’ take nufi a cikin
ma’anrarta mafi azanci da dacewa. Ba za mu iya
fassara ‘Khalifa’ tamkar ‘magaji’ ko ‘mai jiran-
gado’ kamar yadda wasu mutane suke yi wa kansu,
ko ake yi masu, laqabi saboda siyasa, ko addini ko
sarauta ba. Hauka ma ba zai yarda da irin wannan
Khalifanci gameda Allah (swt) ba, ballantana
kuma hankali. Tunani mai zurfi gameda Allah
(swt) shi ne zai iya nuna mana ma’anar da ta dace.

252
Rayuwa abar Misali
Lallai ne mu fahimci Khalifancin Allah (swt)
dangane da mutum ta hanyar baiwowin da Allah
(swt) Ya ba wa mutum daga ‘SunayenSa’ a wannan
duniya. Misali: ‘Dauki “Al-Malik” (‘Sarki’). Ko
Jaki ne ya zama sarkin mutane, to sai kwarjininsa
da ikonsa sun canja ta yadda zai fi qarfin duk
mutanen da suke a qarqashin sarautarsa, har sai
sa’inda Allah Ya yaye rigar Khalifancin sarautar
daga gareshi, sannan zai dawo jakinsa. Da farko dai
Allah (swt) Ya ce Shi ne Mai-Mulki ko Mai
Sarauta (Al-Wali). A cikin ‘Sunayen’ nan na Allah
(swt) waxanda suka shafi Mulki akwai ‘Mai
Iko’ (Al-Qadir) a kan komai da komai a duk faxin
wannan mulki naSa. Saboda haka, duk lokacinda
Ya zavo mutum, komai rashin kwarjininsa, ko
yawan qasqancin asalinsa, ko gazawar galihunsa,
Ya ba shi mulki, to nan take Zai yafa masa
alkyabbar Khalifancin Ya kuma tarfa masa kaxan
daga wannan ‘Iko’ a kan komai a faxin mulkin
mutumin. Nan take sai wannan mutum ya zama
abin tsoro a idanun jama’a, har da waxanda suka
raina shi ko suka raine shi kafin ya sami wannan
mulki. Dalilin mai sauqi ne. Yanzu shi ne Khalifar
Allah (swt) a mulkin birnin in shi ne sarkin birnin
ko gwamna, kuma mai iko a cikin faxin mulkin
nasa; kuma haka zai tafi da qasaitarsa har sai ya
zubarda ita ta hanyar kaucewa qa’idojin Allah na

253
Tunaninka Kamanninka
mulkin, kamar dai irinsu ‘Mai Adalci’ (daga Al-
Adl); ko ‘Mai Tausayi’ (daga Al-Ra’uf); ko Mai
Alfarmar Kyauta (daga Al-Karim) da dai sauransu
in an duba sosai.

Saboda haka, ashe, wannan Khalifanci yana xauke


da irin waxannan nauyi tareda shi, kamar yadda
muka gani a cikin waxannan ‘Sunaye’ naSa (Allah
-swt). Akwai kuma xavi’u waxanda suka danganci
kowanne matsayi da Ya sa xan-Adam a kai.
Misali: Da Allah (swt) Ya ce Shi ne mai Mulki a
kan komai, sai kuma Ya ce, Shi ‘Mai adalci ne”,
Shi Mai Jin Tausayi ne’, ‘Shi Mai Gaskiya ne’, da
dai sauran irin waxannan halaye da suka danganci
Mulki da shugabanci. Saboda haka, Yana bukatar
duk KhalifofinSa a Mulki su kasance masu
waxannan halaye; ba azzalumai ba; ba marasa
tausayi ba; ba maqaryata ko macuta ba. Idan ba su
xauki waxannan xabi’u naSa a fannin Mulki ba, to
sun zubar da Khalifancin, sun ci amanarSa, kuma
ko badaxe ko bajima sai sun tarar da wulakancinSa
a tareda su. Ba a cin amanar Allah a zauna lafiya!

A komai ka duba; ko Kuxi, ko Ilmi, ko menene, za


ka tarar masu waxannan baiwa Khalifofi ne kawai
a waxannan fannoni da Allah (swt) Ya ba su
baiwar. Kuma a cikin ‘Sunayen’ Allah (swt) akwai

254
Rayuwa abar Misali
nauyin da ya wajaba a kawunansu, in sun kasance
masu lura da hakan. Idan kuwa suka kauce, to cikin
lokaci Allah Zai xauke KhalifancinSa ya kuma cire
alkyabbar wannan Khalifanci daga garesu. Nan da
nan, sai ka ga wulakanci ya fara isar masu, amma
mutane ba su san dalili ba. Idan masu kuxi ne, sai
su fara tsiyacewa; idan masu ilmi ne, sai ka ga
ilmin ba ya amfanarsu sai ma dulmiyarda su. Idan
malamai ne, sai mutane su fara kauce masu. Idan
masu Sarauta ne, sai ka ga ba Mulkin, ana gudunsu,
ko ma jifansu. Haka dai kowa da abinda ya dace da
shi na tonon asiri daga Allah (swt); nunin Ya tuve
shi daga wannan khalifancin, ko da Ya bar shi da
muqamin saboda wasu dalilan dabam.

Sanin Allah (swt) yana bukatar nazarin waxannan


‘Sunaye’ naSa. A duk ‘Suna’ na ‘Muqami’, toh
kuwa akwai xabi’u da nauyin da suka maqalu da
muqamin, ko na Mulki ne, ko na Wakilci ne, ko na
Arziki ne, ko Ilmi ne, ko na Makiyayi ne, ko na
Alqalanci ne, ko na Amana ne da duk sauransu.
Haka kuma, ga kowacce bukata ta xan-Adam, ko ta
dabbobi da tsiranni, akwai ‘Sunan’ Allah (swt) na
Alfarma mai nunin biyan wannan bukata. Da
wannan ‘Suna’ za a yi ta roqonSa domin Ya kawo
caffa ga masu wannan bukata kowacce iri ce. Haka
duk Mai-aikata kyawawan abubuwa, irin yadda

255
Tunaninka Kamanninka
littafin nan yake ta faxa, shi ma wannan Khalifa ne
shi a wajen wannan alhairi, domin Allah (swt) ya
ce, Shi ne “Al-Barr”. Waxansu ‘Sunayen’ kuwa ba
mai iya sarrafasu sai Shi, amma xan-Adam yana
da damar ya roqe Allah Ya sarrafasu a kansa.
Kamar dai Al-Rahman da Al-Rahim. Haka dai ga
abubuwan nan na ban sha’awa da ilmi gameda
waxannan “Sunaye” idan aka yi nazari mai zurfi.

Yawancinmu a yawancin lokuta muna kallon


halayen Allah (swt) tamkar shigen irin na mutum
ne. Toh, a wasu fannonin ba shakka hakane, domin
a mutumtakarmu muna da Khalifanci ta wasu
hanyoyin ko su waye mu. Amma halaye da
xabi’un Allah (swt) sune maquran aminci a
waxannan fannonin. Namu ne shigen naSa. Kuma
akwai “Sunayen” da za mu kwaikwaye su daga
GareShi dominSa da kuma mu kanmu. Kamar dai
“Soyayya” (Al-Wadud) da “Hakuri” (Al-Sabur).
Ba shakka, Allah (swt) ba Zai halicci abinda ba
Ya so ba. Amma tunda Ya bawa wasu hallitu,
kamar dai Xan-Adam, zavi, to mutum ya iya zavar
ya so Allah, ko kuma ya qi Shi. Amma, qin Allah,
sakamako ne na rashin sanin Allah, domin duk
wanda ya san Allah yadda yakamata a san Shi, to
shi ma wannan mutumin ba shi da zavi illa ya so
Allah da soyayyar da ta kamaci a so Shi.

256
Rayuwa abar Misali
Wanda ya san Allah sosai, shi yake barin
al’amuransa ga Allah. Shi yake iya danqawa Allah
amanarSa, domin ya san Allah Zai kiyaye wannan
amana, domin Shi ne (Al-Mani). Wanda ya san
Allah, shi yake bin Allah ta kowanne fanni a
kowanne hali ya sami kansa ciki, ya kuma yi
“Haquri” da hakan. Shi ne kuma yake iya haquri da
macutansa domin ya barwa Allah ramuwarsa,
domin Allah Shi ne (Al-Muntaqim). Daga
waxannan “Sunaye”, ba shakka, akwai babbar
shiriya ga masu nazari.

A kowanne fanni na rayuwa, mutum yana da zavin


wanne gefe zai tsaya. Gefen Allah ko gefen
shaixan? Wanda ya san Allah sosai, shi ne nan da
nan yake tsayawa a gefen Allah, ba ma sai ya yi
wani dogon tunani ba. Wanda ya yi qaranci a
saninsa na Allah, shi ne yake tsayawa a gefen
shaixan, ba ma sai ya yi wani tunani ba. Ashe, ba
shakka, sanin abinda Allah Zai yi da wanda ba Zai
yi ba, babban jari ne da Manzon Allah yake da shi.
Dukiyarsa ta ‘Sanin Allah’ babbar dukiya ce,
wadda lallai mu yi kwaxayinta ta hanyar nazari, mu
kuma tabbata mun sameta ta hanyar kyakykyawan
tunaninmu gameda Allah (swt). Za mu iya ci gaba
da wannan bayani, shi kaxai ba iyaka, sai dai wan-
nan littafi yana da tasa iyakar.

257
Tunaninka Kamanninka
II.
“HUJJA ITA CE TUSHEN IMANINA”
******************************

Haqiqa, duk abinda ba a yi masa tushe da Hujja


ba, to kuwa ba zai yi qarko ba. Duk mutumin da
yake yin abinda bai tabbatar da gaskiyarsa da
dalilinsa da cancantarsa ba, to bai zai xau wannan
abu da muhimmanci ba, kuma duk sa’inda dama ta
samu na rabuwa da abin, to kuwa nan da nan zai
rabu da shi. Ko dukiya ka samu a banza, to riqon
sakainar kashi za ka yi mata. Haka mulki da
shugabanci, haka aure, haka ‘ya’ya, haka komai
ma. Duk abinda ba shi da hujja a gareka, to kuwa
ba shi da mutumcin da ya dace da shi a gareka.

‘Musulmi’ da yawan gaske a gurare masu yawan


gaske, waxanda har yanzu ba su kafa hujjar
imaninsu ba, su ke wasa da addininsu, suna ganin
wannan zance duk kamar na wasa ne. Tunda ba su
yi wa imaninsu hujja ba, furucin imanin kawai
suka yi, to kuwa ba su iya aikata abubuwan da
imanin ke bukata. Saboda haka ba za a iya ganin
misalan addinin Islam a yawancin ayyukansu ba.
Musuluncinsu a baki kawai yake. Muhimmin
dalilin wannan shi ne: yadda aka haife su
Hausawa, ko Yarabawa, ko larabawa, ko Malay-

258
Rayuwa abar Misali
awa, haka aka haife su musulmi. Watau jinsinsu ko
qabilancinsu sune kaxai hujjar musuluncinsu. Don
haka, wasu lokatan muke ganin waxanda suka bar
wasu addinan suka shiga Islam, sun fi yawancin
musulmin da aka haifa cikinsa riqe addinin da
gaskiya. Wannan kuwa ta faru ne saboda waxannan
‘sababbin tuban’ kamar yadda bahaushe yake
kiransu a wulaqance, sai da suka sami hujja
tabbatacciya tukuna sannan suka karvi addinin
Islam, watau sai da suka ga wata ‘gaskiya’ ta Islam,
ko kuma mu ce, sai da ‘hasken Islam’ ya ratsasu
tukuna, sannan suka yi imani da addinin.

Haka, a inda ka ga yawancin musulmin da aka


haifa cikinsa sun karve shi da kyau suna kuma
aikata shi da kyau daidai qarfinsu, to nazarinsa
suka yi, suka sami hujja wadda za su xora imaninsu
a kai. Ba a banza ko haka siddan suka zama
musulmin kirki ba. Duk wanda bai yi tunani mai
matuqar zurfi cikin nutsuwa a kan Islam ba, to ba
zai sami hujja wadda zai dogara da ita ba. Irin
waxannan ‘musulmi’ su ne suke jawowa Islam abin
kunya, suna vata sunan addinin. Irin waxannan
‘musulmi’ su ne ba sa jin kunyar zunubansu, ko ma
su ringa danganta waxansu miyagun zunubai nasu
da wata daraja da suke nema, ko suka samu.
Waxannan taqadirai sun raina Allah (swt).

259
Tunaninka Kamanninka
Maganar Annabi Muhammad (saw), cewar, ‘Hujja
ita ce imaninsa’, ba qaramar magana ce ta hikima
da azanci ba. Wannan tana nuna mana cewar dama
tun farko, zuciyarsa da tunaninsa tuni suka gamsu
da hujjar Islam, cewar shi ne addini na gaskiya,
wanda ya cancanci a bi, a kuma yi aiki da
shawarwarinsa da gargaxinsa da hukumce-
hukumcensa, musammam kuma, shi aka aikiowa
da addinin don ya yaxa shi a duniya. Musulmin da
ya kafawa imaninsa hujja, ba ya jin kunyar
musuluncinsa duk inda ya shiga. Waxanda ba su
tabbatar da gaskiyar musuluncinsu ba su ne suke
jin kunyar nuna musuluncinsu a wasu gurare, suna
ganin kamar qauyanci ne, ko abin kunya ne su ce
su musulmi ne, ko su aikata wata ibada ko su nuna
wata xabi’a ta musulunci. Amma, mai alfahari da
addininsa, da kuma aikata shi yadda yakamata, shi
ne wanda ya kafawa imaninsa hujja, kuma yake da
xokin ya nuna musuluncinsa a duk inda ya je, da
duk inda ya sami kansa, ba tareda jin kunya ba.

Lallai tun daga yau mu kafa wannan hujja a


zukatanmu, mu san dalilan da suka sa muke cikin
wannan addini na Islam, mu kuma san
bambancinsa da sauran addinai, mu kuma gamsu
da hujjar wannan bambanci. Idan ba mu yi haka
ba, muka karva kawai babu bincike, watau cikin

260
Rayuwa abar Misali
jahilci, don haka muka gada, to ba za mu iya zama
musulmin kirki na qwarai ba. Ko a siyance, aqida
ba ta qarko idan ba a kafa mata hujja ba. Toh,
ballantana kuma a addinance. Wanda ya kafa hujja
shi zai ci riba.

Babu laifi ko kaxan idan mutum ya zauna ya


tambayi kansa, ‘me yasa na karvi Islam addinina?
Don kawai shi na gada, ko kuma don shi ne ya fi
dacewa? Me yasa ya fi dacewa? Lallai ka karanci
Al-Qur’ani da tunani da nazari, ka kuma yi
tambaya a kan abubuwan da suka shigar maka
duhu, ko kuma suka rikitar da kai. Haka gameda
Allah (swt), lallai ka yi tambayoyi a kanSa duk
sa’inda wani abu ya xaure maka kai. Ta haka kaxai
za ka iya saninSa, ka kuma kafawa addininka hujja,
duk a lokaci guda. Daga sannan ne kaxai za ka iya
zama mai cikakken imani ga Allah (swt) da kuma
dogara da Shi, Shi kaxai. Ta haka kaxai za ka iya
zama mai alfahari da musuluncinka, ka kuma iya
kare shi a ko’ina, komai rintsi, ka kuma iya rayuwa
cikin shiriyarsa. Ta hakane kaxai za ka so Allah
(swt), soyayya ta gaskiya, irin wadda muka yi
magana a kai a Babi na 9 da kuma baya kaxan a
wannan Babin. Ta haka kaxai za ka iya gina
soyayyarka da girmamawarka ga ManzonSa,
Muhammad (saw) da sauran Mursalai da

261
Tunaninka Kamanninka
Annabawa da duk na kusa da Shi. Ta haka kaxai
za ka iya fahimtar sauran addinai, ka kuma ba su
damarda ta dace da su, ka kuma kare ’yancinka a
gurinsu. Ta hakane kaxai za ka iya zama jarumi na
qwarai a cikin musulmi. Wanda zuciyarsa da
tunaninsa suka wadata da hujjar imaninsa, ba
shakka, ya samarwa kansa matukar alhairi, ya
kuma shiga layin muminai na qwarai.

III.
“SOYAYYA ITA CE
GINSHIQINA”
******************************

Duk wanda ya kafa rayuwarsa a kan ginshiqin


soyayya, a haqiqa wannan mutum ya kafa rayuwa
a kan ‘tafin hannun’ Allah na Alhairi. Allah (swt)
Shi ne ‘Soyayya’ a ilahirinta; kuma Ya halicci
komai ne domin soyayya. Duk wanda ya yi
soyayya saboda Allah, to kuwa ya yi koyi da Allah
(swt) da kuma ManzonSa.

Babu wani abu da zai tabbata, ya kuma yi amfani


da albarkar da ake so, sai in an jingina shi, ko an
shimfixa shi a kan soyayya. Cikakken Sanin Allah
ba ya tabbata sai da soyayya a gareShi, kamar
kuma yadda soyayyar za ta taimaka wajen qarin
sanin naSa. Haka son Manzon Allah da koyi da

262
Rayuwa abar Misali
shi, waxanda kuma su ne suke qara tabbatarda
imanin mai su. Ba a tava shuka soyayya ta kasa
furanni ba; kuma furanninta ba sa mutuwa. Duk
abinda ka yi, ko aka yi maka; ko ka samu, ko aka
ba ka, ba a sonka ba, to wannan abin ba zai tava yin
martaba a idanunka ba. Idan kai ne makiyayinsa, to
ba za ka kiyaye shi yadda yakamata ba.

“Son Allah”, ba irin son da ya ke tsakanin namiji


da mace bane. Haka kuma ba irin yadda mutum ya
ke son motarsa ko wata kadararsa bace. Haqiqa,
‘son Allah’, irin yadda Annabi Muhammd (saw) ya
ke faxa, soyayya ce wadda take cika zuciya har sai
ta mamayeta gaba xaya, amma ba ta qare ba, ita
kuma zuciyar ba ta qoshi ba. Sai kuma soyayyar ta
kwararo daga zuciyar, har sai mamaye idanu da
kunnuwa da harshe. Sannan ta bi hannaye da
qafafu da sauran jiki gaba xayansa. Don haka, ‘mai
son Allah’ da irin wannan soyayya shigen ta
Muhammad (saw), sai ya ringa jin ba abinda ya ke
son gani, sai abinda Allah Yake so da wanda Ya so
a gani. Ba abinda yake son ji don biyayya, sai
maganar Allah. Ba abinda yake son furtawa sai
sunanSa. Ba abinda yake son ya sa hannunsa a ciki,
sai abinda Ya halarta masa. Ba kuma inda yake son
ya je, sai gurinSa. Wannan ita ce irin soyayyar
Muhammad (saw) ga Ubangijinsa, Allah (swt).

263
Tunaninka Kamanninka
Wannan ita ce irin soyayyar da muke ta qoqarin
kwaikwayo, domin mu ma, mu so Allah shigen
haka, mu kuma so ManzonSa saboda haka.

Rayuwa gaba xayanta, takan ginu ne a kan


soyayya. Da soyayya ake auratayya, a kuma sami
‘ya’yan soyayya waxanda ake sonsu. Da wannnan
soyayya ta iyaye ga ‘ya’yansu, sai su tabbata sun sa
‘ya’yan a kan hanyoyi nagari, suna yi masu fatan
alhairi da xaukaka fiye da yadda su kansu iyayen
suke. Auren da babu soyayya a cikinsa, ba ya
qarko, kuma in an matsanta, a sami ‘ya’yan da ba a
so waxanda ba za a kula da su ba. Daga nan kuma
tushen iyali ko zuri’a ta-gari ya tunvuke.

Son karatu shi yake haifarda ilmi, a sami al’umma


ma’abociyar ci-gaba. A irin wannan al’umma ake
kafa soyayya wadda za ta iya taimakon kowa, ba a
bar ‘ganin-qyashi’ ya sami gurbi ba, ballantana
uwarsu hassada. Masoyi, ba ruwansa da hassada ga
wanda yake so. Ba ya baqin cikin ci-gaban wanda
yake so. Masoyi, shi yake damuwa da masifun da
mutane suka shiga, ya kuma taimaka ta duk yadda
zai iya. Don haka ashe, wanda ya mayarda soyayya
ginshiqinsa, ba zai kasance maqiyin komai na
alhairi ba. Soyayya ita ta kewaye shi, kuma kullum
a cikinta yake gameda kowa da komai. Wannan

264
Rayuwa abar Misali
mutum shi ne masoyin Allah (swt), masoyin
addininsa, masoyin al’ummarsa da iyayensa da
‘yan’uwansa; masoyin kowa da alhairi. Haka kuma
shi ma za a so shi a sakamako na Allah (swt).

Ba shakka, Allah (swt) Yana son dukkanin


abubuwan da Ya halitta, domin Bai hallicesu da
wasa ko don wasa ba. Don haka, duk wanda ya
nuna soyayya ga wata halitta ta Allah (swt),
wannan ya nuna soyayya ga Allah (swt). Masoyin
abinda ka ke so, ba shakka masoyinka ne. Idan ka
so dabbobi, ko tsuntsaye ko tsuranni, ka kuma
adane su, ka kare rayuwarsu ko lafiyarsu, to ba
shakka, ka yi ibada mai girma a wajen Allah (swt).
Hanyoyin samun rahamar Allah (swt) suna da
yawan gaske, sai dai in ba a yi tunani a kansu ba.
Amma wanda ya azabta jama’a ko dabbobi ko
tsiranni, to ba shakka shi ma zai azabtu a gaba.

Masu tunanin soyayya, ba za su vata lokacisu


wajen qiyayya ba. Tunda soyayya ita ce kewaye da
su, ashe ma babu gurbin qiyayya a kusa da su.
Wanda kuwa ya bar qiyayya ta sami gurbi a
tunainsa da zuciyarsa, wannan mutum ya yi hasarar
rayuwa mai ni’ima, ya kuma yi hasarar babban
maganin maqiya da mahassada. A wannan ’yar
rayuwa taqaitacciya, ina ka ke da isasshen lokacin

265
Tunaninka Kamanninka
aikata duk alhairin da ya kamace ka, balle kuma
har ka vata wani vangare na lokacin wajen shiri da
aikata qiyayya? Wannan hasara da yawa take,
amma fa ga mai lura. Wanda ya cika zuciyarsa da
soyayya, ya gama da masifun duniya da lahira.

IV.
‘TUNANIN ALLAH SHI NE ABOKINA’
******************************

‘Aboki’ tamkar ‘masoyi’ yake, sai dai su ‘abokai’


ma’abotan saduwa da juna ne, watau ma sun san
juna. Za ka iya son mutum, ko wani abu, ko da
kuwa ba ku san juna ba, ko da kuma ba ka tava
ganinsu fuska-da fuska ba. Kamar dai yadda muka
yi zancen soyayya ga Allah (swt) da ManzonSa,
Muhammad (saw). Amma. Aboki, sai wanda ka
sani ya kuma sanka, ku ke kuma da wata alaqa da
juna wadda ta maisheku abokai.

Manzon Allah ya ce, ‘Tunanin Allah’ shi ne abinda


yake yi a kodayaushe, tun da har wannan tunani ya
zama jiki, ya kuma zama abokin zama tare. Da
‘Tunanin Allah’, da ‘Tuna Allah’ abubuwa biyu ne
a qunshe a cikin abu guda. Ba za ka yi ‘tunanin’
abu ba, sai ka ‘tuna’ da shi. Tunawar ita ce Zikri,

266
Rayuwa abar Misali
Tunanin kuma shi ne juyayin al’amuran Ubangiji a
zuci a kodayaushe. Nafsin da ya mai da Zikri (tuna
Allah) davi’arsa, kuma saboda Allah, -zan nanata
“kuma saboda Allah”- to ba zai tava mantawa da
Gaskiyar Allah (swt) ba, ballantana kuma ya
shagala cikin ayyuka ko al’adu waxanda ba su dace
da wannan kyakkyawan yanayi na zuciyarsa ba.
Tunanin Allah (swt) shi ne yake tunasarda mutum
matsayinsa da nauyin da yake kansa da kuma
haqqunan mutane domin ya kiyayesu. Mutanen da
Zikri na gaskiya, ba na nuni ba, ya ratsa zukatansu,
to waxannan mutane masu la’akari ne da abinda ya
dace da wanda bai dace ba. Haka, Tuna Allah (swt)
da TunaninSa sukan tsarkake zuciya ta kasance
cikin yanayin alhairi a kodayaushe. ‘Tunaninka
Kamaninka’ ashe babbar shaidar alhairi ce ga masu
Zikri a lokacin da suke yinsa, kuma albarkarsa ta bi
su ta kare su daga sharri, ko da a cikin barcinsu ne.
Ba jarin da za ka tafi da shi har lahira irin Tuna
Allah (swt) da TunaninSa.

Idan ka haxa lokacin sallolinka, sai ka ga jimlarsu a


ranar ba ta fi ta rabin awa ba. Amma in ka haxa da
yawan Zikirinka, sai ka sami awa uku ko fin haka a
ranar wadda ka ba wa Allah (swt). Shi kuma Ya
saka maka da milyoyin haka. Ba ma ci riba irin
wanda ‘Tunanin Allah’ ya zama abokin zamansa.

267
Tunaninka Kamanninka
V.
‘DAGEWA ITA CE DUKIYATA’
*************************

Jarumi shi ne mai dagewa a kan manufa mai kyau,


ko aqida tabbatacciya, har sai ya cimma nasara.

Kamar yadda muka yi ta nanatawa a can baya, duk


wanda ya gwada sau xaya ya kasa, ya watsar, to
wannan mutum da kyar zai tava samun nasara a
rayuwarsa. Nasara tana ga jarumai waxanda suka
san cewar ba lallai ne su sameta a gwajin farko ko
ma na biyu ba, sai sun dage a kanta har illa masha
Allahu, muddin dai sun yi imanin cewar wannan
manufa tasu muhimmiya ce a garesu, kuma ta
alhairi ce a lokatan yanzu da masu zuwa. Wannan
tunani shi zai sa zuciya ta dake ta kuma himmatu
wajen ababan sha’awarta. Ko addini ne, idan ba ka
dage a kansa ba, sai ya tafi ya bar ka, kana ji kana
gani ka rasa shi, domin ba ka dage ga yinsa ba. Ta
wannan hanya, ba shakka, ‘dagewa’ babbar dukiya
ce ga wanda ya maishe da ita al’adarsa.

Kana yi ana yi maka dariya, ana cewa ‘kai wane da


naci yake’, wataran sai waxannan mutanen sun zo
neman alfarmarka. Duk abinda ba ka dage a kansa
ba, toh wataran sai ka yi hasararsa, ko da kuwa

268
Rayuwa abar Misali
dama can naka ne. Kana ji kana gani za a qwace
maka shi, kuma saboda kai rago ne, ba za ka iya
dagewa ka maido shi gareka ba. Watau, masu
dagewa ne kaxai suke iya kare mutumcinsu da
dukiyarsu da mulkinsu harma da addininsu.
Ragwaye, ko ‘yan aci-bulus’ sune suke rasa
waxannan. Duk wanda bai dage a kan abubuwansa
muhimmai ba, to dama can ba su da muhimmanci a
gareshi. Xalibin da bai dage a kan karatu ba, to
dama bai mayarda ilmin wani abu muhimmi ba,
kuma mun san makomarsa. Xan-kasuwar da bai
dage a kan sana’arsa ba, toh shi zai yi hasara.
Sarkin da bai dage ya kare mutumcin sarautarsa da
jama’arsa ba; ko shugaban da bai dage ya inganta
shugabancinsa ba, duk su za su yi da-na-sani. A
hankali za su rasa sarautar ko kuma martabar
sarautar. Haqiqa mun ga misalai masu yawa.

VI.
‘TAUSAYI SHI NE ABOKIN ZAMANA’
***************************

Mai tausayi shi ne wanda a kodayaushe yake cikin


tunanin halayyar wasu; yake kuma yin iyakacin
qoqarinsa wajen taimakawa domin su sami wasila
a rayuwarsu. Wannan tausayi bai tsaya kan mutane
kaxai ba, har da dukkannin halittu, watau dabbobi

269
Tunaninka Kamanninka
da tsuntsaye da tsiranni, waxanda aka sani. Amma
dai, musammam ma bani-Adam.

Tausayi ya kasance abokin zamansa ne, domin a


kodayaushe a cikin tunanin masu bukatar taimako
yake, da yadda zai taimaka masu. Duk al’ummar
da ba ta da irin waxannan mutane masu tausayawa
wasu, toh kuwa ba za a sami zaman lafiya a cikinta
ba, balle kuma a zaci samuwar arziki da wadata,
balle kuma adalci. Shugabannin da suka shagala
wajen cuta da rashin gaskiya, shugabanni ne
marasa tausayi, domin halayyar jama’arsu ba ta
gabansu. Idan aka sami mai tausayi a unguwa, ko a
gari, to ba shakka an sami jari babba, kuma ta nan
ba abin alhairin da ba zai vullo ba.

Idan Allah (swt) Ya ajiye kayansa a wajen mai


tausayi, to sai Ya yi ta qaro masa ajiyar, domin Ya
san zai ji-qan wasu ne da wannan ajiya taSa.
Amma marasa tausayi, ko badaxe ko bajima, sai su
ma sun zamanto ababan tausayi, kuma a hannun
masu tausayin, ko ma a hannun waxanda yakamata
a tausayawa. Ka ga rimi ya juye da mujiya kenan, a
cikin adalcin Allah (swt). Idan muka yi tunani mai
zurfi, za mu ga irin waxannan misalai da yawa.
Kana zaune, sai ka ga mai tsoratarwa ya zama abin
tausayi ta wasu halaye dabam. Ga tsohon Gwamna

270
Rayuwa abar Misali
yana neman taimako. Amma mutum wanda ya yi
koyi da Manzon Allah, ya mai da tausayi abokin
zamansa, toh wannan mutum ba zai yi lalacewar da
zai zama abin tausayi ba shi kansa.

Mamugunta da azzalumai da maqetata. Varayi da


macuta da maci amana; ba sa cikin rukunin masu
tausayi, domin rashin tausayin ne ya haifar masu da
waxannan miyagun halaye. Amma duk mai tausayi
ba zai kasance a cikinsu ba, domin tausayinsa ya
lulluve zuciyarsa da la’akari da haqqunan jama’a.
Shi banda ya kyautata ba abinda yake son yi saboda
kirkin da tausayinsa ya haifar masa.

Da zarar mai tausayi ya shiga cikin wata masifa ko


wahala, take a nan za ka ga caffa ta zo masa daga
inda ba a zato ba a tsammani. Ba shakka, wannan
caffa daga Allah (swt) take, kuma za ta iso daidai
lokacinda za ta kasance mai amfani. Tausayin duk
waxanda suka cancanci a ji tausayinsu babban
muqami ne na Khalifanci, kuma babban jari ne ga
wanda shi ma ya maida tausayi abokin zamansa. Ba
abu mai daxi a rayuwa irin ka tuna alhairin da
tausayinka ya wanzar ga masu bukatar tausayin. Ka
sha albarka, ka sha addu’a, ka kuma gamsu da
kanka, sanin cewar ka kasance Khalifa na-gari.,
kuma mutumin kirki a idanun mutane. Lallai!

271
Tunaninka Kamanninka
VII.
‘ILMI SHI NE MAKAMINA’
********************

Manzon Allah (saw) ya gama magana a nan. Da


wannan, ba shakka, marigayi Mu’azu Hadejia ya yi
la’akari yayin da yake waqensa yana cewa:

‘Gishiri in ba kai ba miya


Ilimi mai gyaran zamani.

Jama’armu ku jawo hankulanku


Ku lura da halin zamani.
Yadda kaska ke tsotson jini
Haka jahilci gun zamani.

Da tsiya da talauci duk suna


Gun da jahilci ya yi sansani.
Wa’azinmu ga mai karva duka
Masu son gyaran zamani’.

‘Ilmi shi ne Makamina’, inji Manzon Allah (saw).


Wannan ba qaramar magana bace. Haka kuma za
ka gani a hadisai yana cewa, ‘gara dabba da jahili’.
Wannan ba qaramar la’anta bace; kuma lallai ta
dace, domin jahili ko addininsa ma bai sani ba,
balle ya san Allah (swt), balle ya tsara rayuwarsa a
kan hanya madaidaiciya.
272
Rayuwa abar Misali
Kada mu xauka cewar karatun boko ne kaxai ilmi,
ko iya rubutu da karatu. Waxannan sashi ne na ilmi
masu amfani. Amma cikakken ilmi shi ne ilmin
sanin Allah (swt) da yadda za ka tafiyarda
rayuwarka cikin nasara, ka kuma zama shaida a kan
kanka cewar kana cikin datattu. Ba makami irin
ilmi, domin ba za a cika da yaqi ba, ba za a
ha’inceka ba, ba za a yi ba kai ba, ba kuma za ka
qasqanta a cikin jama’a ba, muddin ka ci xamara
da shi, kuma kana amfanin da ya dace da shi.

Bayan ilmin addininka, ilmi mai amfani shi ne


wanda ka koyawa kanka saboda halayyar
rayuwarka. Ilmin da ya shafi sana’arka ko wacce iri
ce, kuma kana mai alfaharin cewar a filin dagarta,
sai an nemeka sannan za a san wasu abubuwa.
Kada rashin ilmin boko ya kasance cikas a gareka,
muddin dai ka gamsu kana da wani ilmin dabam na
rayuwa wanda za ka iya amfani da shi wajen
inganta sana’arka da rayuwarka. Ya rage naka ka
san yadda za ka isarda kanka a cikin masu ilmi na
fanninka ba tareda jin kunya ba. Da ilmi irin naka,
da ilmi irin na wasu dabam, su ake haxawa a gina
al’umma a kowanne zamani. Idan ka shafa ka tarar
lallai kai jahili ne, watau ba wani fanni wanda ka
sani, ba kuma sana’a, to lallai ne ka tashi tsaye ka
nemi ilmi da sana’a yadda za ka iya, domin ka sami

273
Tunaninka Kamanninka
madafa a rayuwarka. Mai ilmin da ba ya amfani da
shi, da mai sana’ar da ya wulakantata, to gara ma
jahilin da ya fahimci jahilcinsa yake kuma yin wani
abu domin ya canja wannan halayya tasa. Ilmin
boko yana da nasa muhimmancin. Ko yi rubutu da
karatu don ka qaru ta wasu hanyoyin.

‘Gemu ba ya hana Karatu’ ba qaramar matashiya


bace a garemu domin mu watstsake mu tashi
haiqan ga neman ilmi yadda za mu iya. Yaqi da
jahilci shi ya tsamo wasu qasashe da al’ummu daga
jujin talauci da takaici, ya aza su a sahun masu
alfahari da kansu saboda nasarorin da suka samu ta
hanyar sabon ilminsu da yawan masu shi a cikinsu.

Ba shakka, ilmi babban makami ne na cin nasara a


duniya da kuma lahira. Manzon Allah (saw) ya
haxa kan nasihu a wannan manufa tasa.

VIII.
‘HAQURI SHI NE MADOGARATA’
***************************

Ko Hausawa ma sukan ce, ‘mahakurci mawadaci’


ko, “Mai haquri shi ke dafa dutse ya sha romo”. Ba
shakka daga azancin Manzon Allah suka samu
wannan magana mai cike da nasiha. Duk wanda ya

274
Rayuwa abar Misali
haqura ya bi abubuwa a hankali, ya kuma mayarda
al’amuran fafutukarsa wajen Allah (swt), to kuwa
ya kafa madogara mai qarfi, kuma wadata tana nan
tafe a kan hanyarsa.

Rashin haquri, shi ke kawo ci-da-zuci, har kuma a


shiga cikin hasarar da za ta tayarda hankali. Rashin
haquri shi yake haifarda fushi, har kuma a watsar
da manufa, ko kuma a tarwatsa tsari. Mara haquri
shi yake vatawa da mutane nan da nan, har ya rasa
abokai. Mara haqurin jin cikakken bayani, shi yake
aikata zalunci, abin kuma ya dawo kansa. Rashin
haquri shi yake hana zuwa, har kuma a yi danasanin
ba a je ba. Mai gajeren haquri mai gajerar zuciya.
Mai gajerar zuciya, mai gajeren tunani. Mai gajeren
tunani mai naqasar nasara a rayuwarsa.

Ashe lallai ne, bayan mun yi shiri mun fara


fafutukarmu ta neman wani abu, mu bi abinda
haquri da dangana. Rashin haquri a kan abinda ake
nema wajen wasu, shi yake quresu har su hana. Ko
Allah (swt) ka roqa wani abu, tilas ka yi haquri sai
sa’inda Ya ba ka, ko Ya musanya maka da abinda
ya fi wannan alhairi a gareka, in alhairin ka ke
nema. Amma idan ka kasa haquri da Allah (swt), to
qarshenta ka watsar da addu’arka. Daga nan kuma
sai ka watsar da addininka. Daga nan kuma ka rasa

275
Tunaninka Kamanninka
madogara kowacce iri ce. Karanta surar “Asr”.

IX.
‘WADATAR ZUCI ITA CE GANIMATA’
*******************************

Lallai kimiyyar rayuwa mai inganci da sauqi tana


daga xabi’un Manzon Allah, kuma don hakama ya
zama abin koyi a garemu duka, ko an yarda da shi,
ko ba a yarda da shi ba. Duk wanda ya yi nazarin
rayuwar Muhammad (saw), kuma ya juyata da
gaskiya ba tareda qyamar addini ba, to kuwa ba shi
da zavi illa ya ji lallai yana son yin koyi da shi.

‘Ganima’, ita ce abar da ake kwasowa in an ci


nasarar yaqi, watau kamar dinare, azurfa, lu’u-lu’u
da yaqutu da su murjani da siliki, da bayi da sauran
ababan adon duniya na mulki da qasaita. Duk
waxannan abubuwan alatu da jin-daxi, su ya haxa
gaba xaya, ya ce, ‘wadatar zuci’ ta fi su.

Zuciya wadatacciya, ita ce wadda ta gamsu hani’an


da ni’imomi waxanda ta fassarawa kanta su a irin
halayyar da ta sami kanta ciki. Watau dai, wata irin
gamsuwa ce da irin yadda Allah (swt) Ya umarta
halayyar mai ita, ta yadda mutum zai ringa ganin
alhairi a cikin duk abinda ya sami kansa ciki.

276
Rayuwa abar Misali
Misali, idan aka yi wa mai wadatar zuci sharri aka
xaure shi, sai zuciyarsa ta ringa faxa masa cewar
zaman kurkukun wata tsarewa ce daga Allah (swt)
daga wasu miyagun abubuwa da za su iya faruwa
ga mutum da yana waje. Daga irin wannan tunani
na imani, sai mutum ya sami kwanciyar hankali, ya
kuma mayarda al’amuransa wajen Allah (swt).
Amma fa mutumin banza wanda illolin rayuwa su
ne adajensa, ba zai tava zama mai wadatar zuci ba,
domin yanayin zuciyarsa ba zai iya yin na’am da
wata irin halayyar ba. Mai wadatar zuci shi ne yake
iya fassara halayyarsa domin kimtsuwarsa, ya
kuma sami biyan bukata daga irin tunaninsa.

Mai wadatar zuci ba ya shiga cikin halayyar talauci


domin tuni zuciyarsa ta riga ta fassara wannan
halayyar ta hanyoyi masu lumananta rayuwa. Mai
wadatar zuci ba ya ganin qyashi, domin a lissafinsa
‘wani hanin ga Allah baiwa ne’. Duk abinda ka zo
masa da shi na taqama ko burga ko nishaxi wanda
ka ke zaton ya rasa, shi yadda ya fassarasu dabam
ne. Idan kuma yana da waxannan abubuwan, shi
yadda yake auna amfaninsu gare shi dabam ne. Ba
yadda za a yi ka husata mai wadatar zuci, ko ka
turnuqa masa wani baqin ciki, ko wata damuwa, ta
hanyar nuna masa wani abu da ya rasa. A gurinsa
wannan abun da ka ke taqama da shi ba muhimmi

277
Tunaninka Kamanninka
bane. Shi ganinsu yake tamkar wasu wahalu ne da
Allah Ya sauke masa su; kuma idan aka yi tunani
mai zurfi, ba shakka, haka xin za a tarar. Ashe
kuwa, ba ganima irin wadatar zuci, domin ita ce
ganimar da take cire maka dulmiyewa cikin
ganimun alatu waxanda suke iya zamewa masifa in
aka samesu, ko in aka rasa su, daidai da yadda
zuciya ta yi son kanta gameda su.

Ba za a tava samun mai wadatar zuci da hassada


ba, domin ba ya baqin cikin abinda ka ke da shi, sai
dai ya tayaka farin ciki idan ya fahimci abin yana
amfanarka da wasu. Ba a samun macuta balle kuma
azzalumai a cikin masu wadatar zuci, domin tuni
tunaninsu ya kore kwaxayin duk irin abubuwan da
suke tunkuxa ragwaye ga cuta ko zalunci. Ba a
samun malalata ko maha’inta a cikin masu wadatar
zuci, domin duk abubuwan da suke yi suna yi ne
cikin amana ba tareda son ran da zai sa su
waxannan munanan xabi’u ba.

Haqiqa, wadatar zuci babbar ganima ce ga duk


wanda ya kasance ya mallaketa. Amma ba ta da
sauqin mallaka, sai ga wanda ya yi tsaf ya kimtsa
tunaninsa, ya kuma fahimci rayuwa sosai, ya kuma
tsarawa kansa zaman lafiya da Mahaliccinsa da
kuma kowa. Wannan tsari na zaman lafiya ba ya

278
Rayuwa abar Misali
tabbata sai kuma mutum ya yarda ya sadaukar da
kansa ga rayuwa mai sauqi ko menene matsayinsa,
dukiyarsa, ilminsa ko mulkinsa, in yana da su, ko
in ba shi da su. Watau dai ya yarda shi mutum ne
sak wanda yake cikin zango zuwa ga rayuwa
tabbatacciya, kuma ba zai yarda ya vata wannan
rayuwa da zai tarar ba, a wannan zango nasa na xan
lokaci mataqaici. Watau dai, ya san komai na
wannan duniya gajeren mafarki ne kawai. Irin
waxannan mutane su ne suke mallakar wannan
wadata ta zuci, shigen wadda Manzon Allah yake
da ita, kuma ta zame masu ganima abar alfahari.

X.
QWAZO SHI NE GWANINTATA
**************************

Wanda bai tashi tsaye da qwazo ba, to kuwa ba


inda za shi, ba kuma inda zai dangana manufarsa.

Masu qwazo su ne abin sha’awa, domin su ne


kuma masu sha’awar duk abinda suka sa kansu ciki
ko suka kuxiri niyyar yi. Da sun fara abu, ko da
abinda wasu suka raina ne, to a cikin lokaci sai sun
zama gwanaye abin sha’awa a cikin waxannan
abubuwa. Qwazonsu a kan waxannan ayyuka ko
manufofi nasu, shi ne abincin zuciyarsu, kuma ba

279
Tunaninka Kamanninka
za su tsaya ba sai sun dangana inda suke son zuwa.
Duk abinda suka sa kansu, da gaske za su yi shi ko
menene abin. A garsu ba hasara irin barin abinda
yakamata ka yi, ko kuma ka yi shi a sassauce, ko a
lalace, ko a ha’ince ko a watse. Gwanitarsu ita ce
su ga sun tashi tsaye sun yi komai nasu daidai
yadda qarfinsu da ikonsu ya kai, ba kuma za su
tava gamsuwa ba idan suka lura da kuskure a cikin
abinda suka sa kansu yi. “Duk abinda ya cancanci
a yi shi, to lallai a yi shi da kyau.”

Duk abinda ka danqa a hannun mai qwazo, toh sai


ka gamsu, watakila ma fiye da yadda kai kanka za
ka yi abin in kai mara qwazo ne. A kodayaushe,
mai qwazo so yake ya faranta maka rai daga
kyakkyawan aikinsa, muddin dai ya yarda zai yi
wannan aikin. Farin-cikinsa shi ne ya ga ka qayatu
ka gamsu daga abinda ka sa shi yi, ko yake yi don
kansa. Idan mai qwazo ya fara abu, ba ya tsayawa
sai ya gama, sai dai inda aka sami wani dalili mai
qarfi wanda ya kawo cikas ga abin. A nan ma za
ka tarar ba laifin mai qwazo bane.

Da jama’a sun fahimci kai mai qwazo ne a kan


wasu abubuwa, toh ba shakka, kai za su dosa da
waxannan abubuwan. In kai mai qwazo ne a
sana’arka, to ba shakka, sana’arka ta sami matakin

280
Rayuwa abar Misali
xaukaka, kai kuma tuni ka hau matakin nasara.
Duk wanda ya maishe da qwazo gwanintarsa, toh
ya gama fassara kansa a matsayin mutum wanda
yake ba wa muhimman abubuwa muhimmancin da
ya dace da su. Irin waxannan mutane ba sa wasa da
abubuwanda aka danqa a hannayensu. Ba sa kuma
wasa da rayuwarsu.

XI.
‘IMANI SHI NE QARFINA’
*******************

Mun yi zancen imani a qarshen Babin na 8, a yadda


ya danganci ‘imani da Allah (swt)’. Mun kuma ga
yadda Imani ya zama hujja ga Manzon Allah (saw).
Ba shakka, imanin da Manzon Allah (saw) yake
magana a kai, irin wannan imanin ne. Abinda
kawai za mu duba a nan shi ne yadda ya zama
‘qarfinsa’. Abinda duk ya zamto shi ne qarfinka, ba
shakka kuma shi ne muhimmin makaminka da
abinda ka ke taqama da shi. Shi ne kuma gin-
shiqinka da makarinka da mutumcinka da tsirarka.

Ba kadarar da mutum zai samu wadda ta fi imani


mai qarfi. Da farko dai, mutane masu qarfin imani
ne kaxai suke iya jurewa da duk halayyar da suka
sami kansu ciki, kuma su ne suke zama jarumai

281
Tunaninka Kamanninka
waxanda ba su tava fidda rai daga samun nasara
ba, domin lallai sun yi imani cewar, ‘nasara tana
daga Allah (swt)’, kuma Shi kaxai ne mai ba da ita
ko mai hanata. Masu qarfin imani ne kaxai suke
iya qyanqyashe wadata a zuciyarsu, kuma wannan
wadatar zucin ta qara qarfafa masu imaninsu.
Waxanda imani ya kasance qarfinsu, su ne kaxai
suke iya tabbatarda gaskiya ko ana ganinsu ko ba a
ganinsu, domin suna sane da cewar Mahaliccinsu
Yana ganinsu, kuma abinda Yake bukata kenan
daga garesu, watau aikata gaskiyar. Suna sane da
cewar Allah (swt) Shi ne Gaskiya, kuma idan suka
yi ta, sun haxe da Shi; idan suka bar ta, sun bar
Shi. Qarfin imaninsu ba zai bar su su tave ba, har
abada domin shi ne madogararsu.

XII.
‘GASKIYA ITA CE CETONA’
***********************

Ba gaskiyar da ta shige wannan magana. Kamar


yadda muka ce yanzun nan a wancan shafin, Allah
(swt) Shi ne Gaskiya. Haka Ya ce a cikin Al-
Qur’ani mai tsarki. Yadda Yake xaya, haka take
xaya. Wanda ya karveta ya karvi Allah, wanda
kuma ya qi ta, ya qi Allah. Wanda ya tsaya gareta
ya tsaya ga Allah, wanda kuma ya nisanceta, lallai

282
Rayuwa abar Misali
ya nisanci Allah. Wanda ya aikatata, ya aikata
abinda Allah Yake so, wanda kuma ya guji
aikatata, toh ya guji aikata abinda Allah Yake so.

Ashe kuwa ba shakka, ‘Gaskiya’ ita ce kaxai za ta


ceci mutum, qarya kuma ita ce kaxai za ta cuci
mutum. Babu wata aba mai fitarda mutum a cikin
mutane irin Gaskiya. Idan ka faxeta sau xaya, sai
ka yi ta faxarta ba canjawa, domin ita kaxai ce, ba
sai ka tuna wani abu ba. Amma qarya ba ta
maimaituwa a yadda aka faxeta a baya, sai ta canja.
Duk wanda aka sani da Gaskiya, toh ko ba a sonsa,
tilas ne a girmama shi domin gaskiyarsa, kuma
idan ya yi magana take an san ba wasa cikinta.

Da wannan siga ta gaskiya aka san Muhammad


(saw). Saboda haka, da ya ce Allah (swt) Ya aiko
shi da Gaskiya, ba a yi shakku ba, duk da wasu ba
sa son abinda ya zo da shin. Dá an san shi da qarya
dá ba wanda zai bi shi, dá addinin Islam a yadda ya
zo da shi bai karvu ba. Dá mun yi hasara babbar
gaske. Amma, ba a san shi da qarya ba, don haka
aka karvi addinin a yadda ya zo da shi, ba gyara.
Wa zai gyara abinda aka san ilahirinsa gaskiya ne?

Gaskiyarsa ita ce ta cece shi, kuma ita ce ta zama


hujjarsa, kuma ita ce ta zama tushen addininsa,

283
Tunaninka Kamanninka
kuma ita ce wadda, ba shakka, za ta ceci shi wajen
Mahaliccinsa a ranar Hisabi. Da wannan Gaskiya
dukkaninmu za mu sami ceto. A duniya: mu sami
ceton mutumcinmu da ‘yancinmu. A lahira: Mu
sami ceto daga kowacce irin azaba da za ta tsimayi
maqaryata a kan tafarkin da Mahaliccinsu Ya
horesu. Duk wanda ya riqi Gaskiya ya riqi dahir.

XIII.
‘LADABI SHI NE CIKA TA MUTUM’
****************************

Mara ladabi ba zai iya biyayya ba. Mara biyayya


kuma tavavve ne shi a cikin mutane. Wannan
gazawa ita ce babbar illa a tareda shi, domin shi
ma ba zai sami biyayyar da yake bukata ba. Wanda
kuwa ba za a bi ba, to kuwa bai cika mutum yadda
ake so ba. Ya gaza matuqa a martabarsa.

A matsayi irin na Manzon Allah, ladabinsa ga


wasu, muhimmin shishshike ne na ladabi a gareshi.
Idan ba a ladabta shi ba, ba za a saurare shi ba.
Idan ba za a saurare shi ba, wa’azinsa ba zai jiwu
ba. Idan ba a ji wa’azinsa ba, ba za a ji labarin
addinin Islam yadda yakamata ba. Ya zamto masa
wajibi ya kasance ma’abocin ladabi ga kowa
domin ya sami biyayyar da shi ma yake bukata, a

284
Rayuwa abar Misali
kuma saurare shi cikin nutsuwa da ladabin, a kuma
fahimci duk abinda yake cewa. Wannan xabi’a,
muhimmya ce ga kowa, musammam ma masu
bukatar su ma a mayar masu da ita. Ka haxa ladabi
da gaskiya, ka ga biyayya da soyayya yadda ba ka
zato. Kana girmamawa, ana girmamaka. Kana ma-
gana, ana sauraronka, ana kuma aiki da ita.

Babbar shiriya a kan wannan dama can mun santa.


Wanda bai girmama wani ba, ba za a girmama shi
ba. Faqat. Saboda haka duk mai son kimtsa
mutumcinsa, to ya kimtsa na wasu. Raina mutane
da yawan galatsi garesu, ballantana kuma ummul-
aba’isinsu “girman kai”, don kai mai muqami ne,
ko wani basarake, toh wataran sai sun mayar maka
da martani duk lokacin da dama ta samu. Ko ma su
zageka, ko su jefeka, duk da muqamin naka.

Rashin ladabi da rashin biyayya suke haifar da


rashin yakana da rashin sanin yakamata. Masu
waxannan halaye ba yadda za a yi su zama mutane
cikakku, har sai sun sabunta tunaninsu sun gyara
halayensu. Mun san wannan tun a Babin baya.

Rashin cika lokaci da alkawari, dangi ne na rashin


ladabi da rashin sanin yakamata. Babu nasara a
al’amuran masu waxannan halaye.

285
Tunaninka Kamanninka
XIV.
FAFUTUKA ITA CE XABI’ATA
*************************

Wannan ko shakku babu gameda Muhammad


(saw), domin dá bai mayar da fafutuka ta zamto
xabi’arsa ba, dá Islam bai bazu yadda ya bazu a
lokacinsa ba. Dá kuma hakane, dá Sahabbansa ba
su kasance masu fafutuka shigen tasa ba.

Kamar yadda muka yi ta nanatawa a gurare da


yawa: Duk qarfin manufarka, idan ba ka ciccivata
da fafutuka ba, to ba za ka sami irin nasarar da ka
ke nema a kanta ba. Mafi muhimmanci gameda
fafutuka shi ne, ita ce kaxai abinda za ka iya yi da
kanka, domin mun san ‘nasara’ tana daga Allah
(swt). Amma mai fafutukar ne kaxai zai iya zaton
nasara. Mara ita ya san dama can ‘hasara’ ce
sakamakonsa. Mai fafutuka yakan sami wata irin
‘nasara’ tun daga gwajin farko, domin ta nan zai
iya nazarin kura-kurensa ya kuma gyarasu don
gaba. Mai fafutuka ne kaxai zai iya himmatuwa a
kan hanyar cin nasarar manufofinsa.

Rayuwar Manzon Allah gaba xayanta, a kan


fafutuka ta ginu, kuma wannan ita ce xaya daga
cikin darussan da ya bar mana waxanda suka

286
Rayuwa abar Misali
cancanci yin koyi da su. Idan sai ya yi fafutuka a
kan abinda Allah (swt) Shi kansa Ya aiko shi da yi,
toh a kan menene kuma ba za a yi fafutuka ba.
Wannan ba qaramin darasi bane ga masu tunani.
Mai fafutuka ba ya lalaci, ba ya hasara, ba ya zama
babu sana’a, ba ya zubarda mutumcinsa. Shi ne
mutum wanda ya san idan ya yi fafutuka a kan
wata manufa tasa ta alhairi, ko badaxe ko bajima,
Allah Zai kawo masa nasara ta wasu hanyoyi. Irin
wannan tunani shi ne abincin zuciyar mutum mai
qwazo a cikin fafutukarsa. Amma mutumin da ya
fara fafutuka ya watsar, ko kuma sam ya qi farata,
toh wannan mutum sam sam ba inda za shi a
rayuwarsa. Duk wanda ya maishe da fafutuka
xabi’arsa, toh kuwa yana tareda nasara. A duk
halayyar rayuwarmu, mukan sami qalubalanta iri
iri. Masu qwazo da son fafutuka ne kaxai suke a
shirye su fuskancesu.

XV.
IBADATA ITA CE FARIN-CIKINA
**************************

Wannan magana haka take a zahiri ga duk wanda


ya yi tunaninta da kyau. Duk lokacin da ka ke cikin
ibada a nutse yadda ake so, toh ba shakka, a
waxannan lokutan duk wani takaici ya kan fice

287
Tunaninka Kamanninka
daga zuciyarka. Ko mutuwa aka yi maka, in ka zo
Sallah, sai ka ji baqin-cikinta ya lafa. In a kurkuku
ka ke, ka shiga ibada, to a waxannan lokutan sai ka
ji wata iska ta ‘yanci tana buso maka, musammam
ma in zaluntarka aka yi aka jefaka cikin ququmin,
saboda ba a sonka ko saboda ba a son ra’ayinka, ko
don wani sharri da zalunci dabam.

Duk masu yawaita ibada take nan za su ga azancin


wannan magana domin sun santa, ba baquwa bace.
Ba maganin masifa da zulumin jidali irin ka tashi
ka shiga ibada: nafiloli, zikri, salatin Annabi,
Istigfari da sauran addu’o’i na girmama Allah (swt)
da neman wanyewar masifu da jidalai. Waxanda
suka maishe da ibada xabi’arsu, ba shakka suna
tareda farin-ciki a kodayause. Wannan yanayin
alhairi na zuciyarsu shi ne kuma zai qarfafa masu
imaninsu har sai sun kasance masu xokin ibada
duk lokacin da suka sami dama. Mutanen da suka
saba jin daxin ibada, to duk lokacinda ba sa amfani
da bakinsu, zikri suke yi. Irinsu ne ma a kowanne
lokaci suke tsimin bakinsu daga zantukan banza,
domin su sami sararin yabon Allah (swt) ko na
salati ga ManzonSa, domin ta nan sukan sami wata
lumana a zuciyarsu. Watau irinsu ne muke yi wa
take: ‘Zikrinsu Lumanarsu’. Allah (swt) Ya sa mu
ma mu kasance haka. Amin.

288
Rayuwa abar Misali

289
Tunaninka Kamanninka

290
Y
Tunani da Hikima

Tunani
da Hikima
‘Kalma xaya tak, ta ishi mai tunani’

Yawancin waxannan shawarwari, ko maganganun


hikima, wasu mutane ne suka rubuta su domin su
taimakawa masu tunani da nazari wajen kimtsa
rayuwarsu. Na rubuta sunayensu a qasan
maganganunsu. Waxanda ba sunaye, yawancinsu
nawa ne; wasu kaxan daga cikinsu kuma, haka
suke ba sunaye a inda na gansu.

Wasu sai ka ga kamar qalubalanta ne, wasu kuma


ka yi mamakin dalilansu. Amma idan aka yi tunani
aka kuma juya al’amuran rayuwa, ba shakka, za a
tarar cewar yawancinsu hikima ce don a sami
rayuwa mai amfani ta hanyar azancin kalmomin.
Sai a duba da lura. Kowa zai sami waxanda yake
so da waxanda za su iya zama jagoransa.

291
Tunaninka Kamanninka

1.
Auna kanka daidai a kodayaushe,
A kan kowacce irin bukata taka,
A kowanne hali ka sami kanka ciki,
A cikin kowaxanne irin mutane.

2.
Kada ka yanke shawara cikin fushi.

3.
Kada ka amsa magana cikin fushi,
Ko ka amsa takarda cikin fushi.
Jinjina sau uku a qalla,
Ka kuma yi tunani mai zurfi.

4.
Tabbatarwa kanka abinda ka ke nema
ya dace da kai,
Kafin ka yi amfani da lokacinka wajen neman.

5.
Kada ka kuskura ka ce sai ka yi abinda wani ya yi,
Ko ka jingina manufarka a kan ta wasu.
Zama mutumin kanka.

292
Tunani da Hikima

6.
Lallai ka yi tunanin abinda zai amfaneka,
Kuma ka yi shi da gaske da qarfinka.

7.
Duk abinda ka ke yi, tambayi kanka:
Me na ke yi?
Daidai na ke yi?
Zai amfane ni?
Zai amfani wasu?
Yaushe zan gama?

8.
Duba damanka: Ka ga Littafai?
Duba hagunka: Ka ga shayi ko lemo?
Duba gabanka: Ka ga fulawa,
ko wani hoto mai kyau?
Duba bayanka: Ka ji shiru?
In duk amsar ba ‘I’ bace, gyara zamanka.

9.
Farkawa daga barci tana da kyau,
Amma motsa jiki muhimmi ne
(Karen Levine)

293
Tunaninka Kamanninka

10.
‘Abinda ya shige tarihi ne.
Abinda zai zo gaibu ne.
Amma ‘yau’ tawa ce kuma a cikinta nake’.
(Tsohuwar maganar hikima a Turai)

11.
‘Gwanitar rubutu da zane
A sauqin fahintarsu take’
(Walt Whitman: 1819-1892)

12.
Mafi qankanci mai ma’ana,
ya fi mafi girma na shirme’
(Carl Jung: 1875-1961)

13.
In ba za ka faxi alhairi ba,
Yi shiru da bakinka’
(Hadith)

14.
Ka iya gafartawa maqiyanka.
Amma kada ka manta sunayensu’
(Pres. John F. Kennedy)

294
Tunani da Hikima
15.
‘Ina son jin daxi mai sauqi.
Shi ne maslahar mutane masu rikitarwa’.
(Oscar Wilde: 1854-1900)

16.
Kada ka jira sai bukatar abu ta tashi.
Neme shi ka ajiye don gaba, in da hali.

17.
Maza binciko baiwar da Allah Ya yi maka,
Ka riritata, ka yi amfani da ita.
In ba ka haka ba ka dankwafe rayuwarka
A cikin abinda bai dace da kai ba.

18.
‘Lallai ka koyi kimtsuwa a cikin hayaniya,
Ka kuma san yadda za ka motsa a cikin shiru’.
(Indira Gandhi: 1917-1984)

19.
‘Wanda ya kauda kwaxayinsa,
Ya ci yaqin rayuwa’
(Charles Dickens: 1812-1870)

20.
Mai wayo shi ne ya san abinda zai sadaukar.

295
Tunaninka Kamanninka

21.
‘Ku tafi ku nemi aikin yi.
Allah ba Ya ruwan dinare’
(Khalifah Umar bin Khattaf)

22.
‘Da-nasani qeya ce’
(Karin maganar Hausa)

23.
‘Duk wanda ya kusanceNi da taqa xaya,
Zan kusantoshi da taqa xari.
Duk wanda ya dosoNi a tafiye,
Zan dosheshi a guje.
Duk wanda ya fuskanceNi da zunubi faxin duniya,
Zan fuskanceshi da gafara mai faxin hakan’.
(Hadith Qudsi, daga Muslim, Ibn Maja da Ahmad)

24.
Ilmi kamar madubi yake in kana da shi,
In ka duba sosai sai ka ganka a ciki

25.
Kilo xaya na aikatawa
Ya fi ton xari na hirar aikatawar’
(Friedrich Engels: 1820-1895)

296
Tunani da Hikima

26.
Cikakken Imani shi ne:
‘Ka dogara da Allah,
Ka kuma san yadda za ka kare kanka’.
(Muhammad Iqbal: a Bal-i-Jibril. Sh.81)

27.
‘Rayuwa dáma ce, ba tilas bace’
(Daga littafin shugabanci na Tao)

28.
‘Sai Rayuwa ta sumbacemu da safe da rana.
Amma kuma ta yi wa ayyukanmu dariya
Da daddare da Asuba’
(Kalil Gibran)

29.
‘Don na kasance ‘ni’,
Tilas ne na xau kasada da ‘ni’.
Na gwada sababbin halaye
Na yadda zan kasance,
Har sai na tararda yadda nake sona’
(Hugh Prather)

297
Tunaninka Kamanninka
30.
‘Rayuwa kamar Mota take.
Za a iya amfani da Mota a je gurare masu nisa.
Amma sai wasu mutane su shige gabanta.
In ta kaxesu sai su fara qorafi,
Suna zarginta da haddasa haxarin’.
(Anthony de Mello)

31.
Hanya xaya da za ka rayu har abada ita ce:
Ka bar wani aiki na alhairi a bayanka

32.
‘Fara komai da Sunan Allah’
33.
Wannan Juma’ar ka yi wani abu na alhairi
Wanda ka daxe kana son yi.
Sannan kuma ka yi qoqari
Ka maimaita shi sau xaya a wata’.
(Denis Waitley)

34.
‘Imani da abu, dabam yake da aikata shi.
Wasu sai su ringa magana kamar Teku,
Amma rayuwarsu a daskare kamar vavarkiya.
Wasu suna saitin idanunsu ga qolin tsauni,
Amma zuciyoyinsu sun maqale a kogon duwatsu’.
(Kalil Gibran)

298
Tunani da Hikima

35.
Idan za ka mutu sai ayi ta yi maka majigi,
Ana nuna maka dukiyar da za ka bari.
Kai kuma kana ta fushi ka yi hasararsu.
To amma, idan dukiyarka…
Zikirin Allah ce fa?’
(Imam Al-Ghazali)

36.
‘Ban da ‘Sauna’, wa zai yi ban ruwa ana ruwa?’
‘Wa ya ce maka ‘Sauna’ ne?
Ka san abinda ya qara a cikin ruwan?’

37.
A cikin wasu mutane kafin ku,
Sai wani mutum ya kasa haquri da qurjinsa.
Ya xauko wuqa ya yanke hannunsa.
Allah Ya ce,
‘Wannan bawa Nawa ya yi gajen haquri.
Ba Zan sa shi a AljannaTa ba’.
(Hadith daga Buhari da Muslim)

38.
Duk abinda ya zo daga zuci,
To kuwa zai faranta zuciyar.
(Don Sibet)

299
Tunaninka Kamanninka

39.
Rashin girman-kai shi ne:
Ka yarda wani zi iya koya maka wani abu.
Girman-kai shi ne:
Ka rufe qofar zuciyarka.
(Arthur Deikman)

40.
Wuni-wunin me ka ke yi ne?
Tsoron me ka ke ji ne?
In za ka gwada ka gwada.
Rayuwa cike take da ababan gwadawa.
In ba ka gwada ba, ta yaya za ka iya?

41.
Kashi 80 cikin 100 na nasara
Zuwa gurin abin ne kawai.
(Woody Allen)

42.
Ba wai don abubuwa suna da wahala
Muke kasa yinsu ba.
A a. Kasa yin shi ne wahalarsu.
(Seneca)

300
Tunani da Hikima

43.
Sai an haxa tunani da manufa
Sannan za a sami sakamoko mai amfani.
Yawancin mutane sukan bar tunaninsu
Ya zagwanye a cikin tekun rayuwa.
Kyaun mutum ya qudiri wani buri daidai shi,
Sannan ya yunqura cimmasa.
(James Allen)

44.
Ba kuskure irin ka yi kaxan
Wai don kaxan za ka iya yi.
Tashi ka yi abinda za ka iya.
(Sidney Smith)

45.
In za ka shiga, yi Sallama a kodayaushe.

46.
Ba za ka san daidaituwarka ba,
Sai ka girmama duk waxanda aka haliccesu
Kamar yadda aka halicceka.
(A Course in Miracles)

301
Tunaninka Kamanninka
47.
Ma’anar Rayuwa ita ce ka rayun,
A sanka
A san manufarka
A san ra’ayinka
A san bambancinka da sauran
A san ka Rayu.

48.
Auna bambancin da yake tsakanin
Mutumin da ya ce, ‘sau uku ina kasawa’
Da wanda ya ce, ‘na kasa’.
(S. I. Hayakwa)

50.
‘Ba Na murna da xan-Adam mai vata lokaci…’
(Hadith daga Buhari, Muslim, Abu-Dawud)

51.
In kana son ka san kanka,
Yi tunanin kanka.
(Socrates)

52.
Bishiyar Gamji daga ‘iri’ ta tsiro.
Hasumaya hawa goma daga tubali ta tashi.
Tafiyar mil dubu daga taqar farko ta fara.
(Lao-Tsu)

302
Tunani da Hikima
3.
Lumanar zuci takan samu ne
Daga yawan Gafartawa.
(G.G. Jampolsky)

54.
Duk yawan littattafai masu tsarki da ka karanta,
Duk yawan zancenka gameda su,
Me ye amfaninsu in ba ka aiki da su?
(The Dhammapada)

55.
Duk abinda muke gani
Ko muka zata
Mafarki ne kawai a cikin mafarki.
(Edgar Allen Poe)

56.
Duk abinda za ka iya
Ko ka yi mafarkin za ka iya
Tashi ka yi.
(Goethe)

57.
Jiya, tunanin yau ce kawai.
Gobe kuma, mafarkin yau ce.
(Kalil Gibran: a littafin The Prophet)

303
Tunaninka Kamanninka

58.
Da kyau a zo qarshen tafiya.
Amma ita kanta tafiyar ce muhimmiya.
(Ursula Le Guin)

59.
‘Duk wanda ya tambaya zai karva.
Duk wanda ya nema zai samu.
Duk wanda ya qwanqwasa za a a buxe masa’.
(Annabi Isa, a Matthew– 7:7,8)

60.
Nasara balaguro ce
Ba danganawa ba.
Qarshen tafiyar rabin nasarar ce.
(Gita Bellin)

61.
Yadda muke yau, tunaninmu ne na jiya.
Tunaninmu na yau shi ne yadda za mu zama gobe.
Rayuwarmu daga tunaninmu take.
(The Buddha)

304
Tunani da Hikima
62.
‘Soyayyata tana ga waxanda suka so junansu
Saboda Ni.
Soyayyata tana ga waxanda suka ziyarci junansu
Saboda Ni.
Duk za su kasance a matsayin haske a cikin
inuwaTa’
A Ranar da ba inuwa sai Tawa’.
(Hadith Qudsi: daga Abu Hurayrah, Mushnad Ahmad)

63.
Abubuwa ba sa canjawa.
Mune muke canjawa.
(Henry David Thoreau)

64.
‘Duk wanda bai ji bari ba
Zai ji woho’.
(Karin-Maganar Hausa)

65.
Wani abu gameda rayuwa,
In ka ce komai mai-kyau kake so, sai ka samu.

66.
Qarya fure take yi,
Ba ta ‘ya’ya.
(Karin-Maganar Hausa)
305
Tunaninka Kamanninka

67.
Lokacin da wani ke ja da baya
Don yana jin bai isa ba,
Wani na can yana kura-kurensa
Har sai ya isa.
(Henry C. Link)

68.
Ba abu mai gamsarwa
Irin ka yi abinda aka ce ba za ka iya ba.
(Walter Bagehot)

69.
Idan ka ringa yin abinda kullum ka ke yi,
Za ka sami sakamakon da kullum ka ke samu.
(Anon)

70.
‘Yadda kaska ke tsotson jini,
Haka Jahilci gun zamani’
(Mu’azu Hadejia)

71.
Idan ka kyautata sana’arka
Sai ita ma ta kyautata maka.

306
Tunani da Hikima

72.
Kada ka yi tagumi.
Tashi ka tunkari matsalarka.

73.
Yabo ya tabbata ga Allah
Shi kaxai a MartabarSa da GirmanSa
Da kaxaituwarSa da KasancewarSa
Da rashin qarshenSa,
Wanda ya tauye fukafukan qwaqwalwa
Ta gaza daga hasken xaukakarSa.
Wanda Ya buxe hanyar saninSa
Daga rashin saninSa.
Wanda Ya hana zaqin harshe
Yabon kyaun kasancewarSa,
Sai dai ta hanyar da Shi kanSa Ya yabi kansa.
(Imam Al-Ghazali: farkon bayanin Asma’ul Husna)

74.
Mutane suna son su ji abinda za ka ce,
Amma suna son su ga abinda ka ke yi.
Kuma gani da ido ya kori ji.

75.
Gaskiya ita ce ma’aunin rayuwa

307
Tunaninka Kamanninka

76.
Mutane ba su damu da abinda ka sani ba,
Sai sun san abinda ka damu da shi.

77.
Gaskiya xaci gareta.
Amma sakamakonta zaqi gare shi.

78.
Kiyaye tunaninka
Domin su ne za su zama kalmominka.
Kiyaye kalmominka
Domin su ne za su zama ayyukanka.
Kiyaye ayyukanka
Domin su ne za su zama xabi’unka
Kiyaye xabi’unka
Domin su ne za su zama halayenka
Kiyaye halayenka
Domin su ne za su zama hallayarka.
Kiyaye halayyarka
Domin ita ce makomarka.

308
Tunani da Hikima

79.
Gaskiya qarfi gareta.
Ba ta fashewa kamar vulvuli don an tava ta.
Ka yaqeta da safe,
Ka mangareta da rana,
Ka haureta da yamma,
Amma tana nan damdam da daddare.
Haka kuma za ta farka da safe.
(Oliver Wendell Holmes, Sr.)

80.
In za ka faxi, faxi gaskiya,
Komai ta ka ja maka ka biya.
(Sa’adu Zungur)

81.
Idan zuciyarka ta ce, ‘I’,
Amma tunaninka ya ce, ‘A’a;
Kada ka yi.

82.
‘Gaskiya ita ce Babin Farko
A littafin Hikima’
(Thomas Jefferson)

309
Tunaninka Kamanninka

83.
‘Ya Allah,
Ka tsare ni daga cin haqqi da cin bashi’
(Hadith daga A’isha)

84.
‘Ba wanda zai iya qasqantar da kai
Ba tareda yardarka ba’.
(Eleanor Roosevelt)

85.
Tuntuve zai iya hana faxuwa
(Thomas Fuller)

86.
Masu hikima suna magana ne
Domin suna da abin cewa.
Banzaye suna magane
Domin wai sai sun ce wani abu.
(Plato)

87.
Kada ka yi qoqarin canja duniya.
Canja tunaninka gameda duniyar.

310
Tunani da Hikima
88.
Ba dangantaka mai wahala
Irin taka da kanka,
Domin ba za ka iya yanketa ba.

89.
Duk abinda ka bayar,
Shi za a ruvanya a dawo maka da shi.
Saboda haka, ka yi hankali da abinda za ka bayar.

90.
Akwai hanyoyi biyu na tunkarar wahalu:
Ko ka canja wahalun,
Ko ka canja kanka ka tunkari wahalun.
(Phyllis Bottome)

91.
Abu mai wahalar mu ke yi nan-da-nan.
Wanda ba zai yiwun ba
shi ya ke xaukar xan lokaci.
(Taken sojojin Amerika)

92.
‘Ko ka shige gaba a bi ka,
Ko ka bi,
Ko ka ba da hanya’.
(Rubutu a gaban Teburin Ted Turner mai CNN)

311
Tunaninka Kamanninka

93.
Ba kasada irin rashin xaukarta.

94.
In masifa ta doso
Yi mata waqa.
(Karin-Maganar Larabawa)

95.
Duk sa’inda ka faxi,
Tsinto wani abu.
(Oswald Avery)

96.
In ba ka yi qoqarin yin fiye da abinda ka iya ba,
Ba za ka tava ci gaba ba.
(Ronald E. Osborn)

97.
‘Babbar nasararmu ba ita ce: ‘ba za mu faxi ba’,
Ita ce: ‘duk sa’inda muka faxi za mu iya tashi’.
(Confucius)

98.
Duk tunaninka mai kyau,
Yana da amfaninsa ga rayuwarka.
(Grenville Kleiser)

312
Tunani da Hikima
99.
Ba makara ga abinda za ka iya zama.
(George Eliot)

100
Ba gaggawa ga abinda ba zaka zama ba
Haka, ba gaggawa ga abinda ba zaka samu ba.

101.
Gara ka rayu kwana xaya a siffar Zaki,
Da shekara xari a siffar Jaki.
(Take a azurfar kwabon ‘Lira’ ta Italy)

102.
‘Wadatar Zuci ita ce Ganimata’
(Hadith)

103.
Ba ka da abokin da ya fi ka.
Komai ya rage naka.

104.
Ce:
“La’ilaha Illallah, Muhammadan Rasulullah”
Sannan:
“Subhanallah, Walhamdu-Lillah,
Wala ilaha illallah, Allahu Akbar”
***
313
Tunaninka Kamanninka

314
Tunaninka Kamanninka

“Bismillahir Rahmanir Raheem”

****************************************

“Ga kowane (mutum)


Akwai Mala’iku a jere
A bayansa da gabansa
Suna gadinsa da umarnin Allah.
Haqiqa, Allah ba Zai canja
Halayyar mutane ba
Har sai sun canja kansu
(da zuciyoyinsu)”
Sadaqal-Lahul Azeem
***************************************
Surat: Al-Ra’ad (13)
Aya ta 11

315
Tunaninka Kamanninka

**********

“Alhamdu Lillahi
Rabbil-Alameen”

**********

316
Tunaninka Kamanninka

Mu riqe addininmu da kyau, mu kuma


nazarce shi a hankali da hikima. Ba shakka,
duk abubuwanda muke bukata don cimma
nasarar rayuwar duniya da lahira suna nan
tattare a cikinsa. Amma fa sai mun bincika.

“Mai nema yana tareda samu”

317
Tunaninka Kamanninka

c
318
Tunaninka Kamanninka

319

You might also like