Hadisin Umm Zar'in Da Darussan Da Cikinsa Ga Ma'Aurata

Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 13

HADISIN UMM ZARIN DA DARUSSAN

DA KE CIKINSA GA MAAURATA

Dr. Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmn


Sashen Koyar da Aikin Akanta, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria
08032989042 ([email protected])
]NASSIN HADISIN UMM ZARIN [1
























o





.

. (1
. (2
. (3
.
(4
. (5
.
(6
. (7

.
(8
. (9

Sunday, March 26, 2017 2


]NASSIN HADISIN UMM ZARIN [2
(10
.


(11











.
.
" .


"


o
"
" :
Sunday, March 26, 2017 3
ABUBUWAN DA HADISIN YA QUNSA [1]
o Mata uku na farko sun yi wa mazajensu kifa xaya qwala
wajen bayyana mugun halinsu da rashin iya zamantakewar
aure
Ba a iya gamsar da shi ballantana a yardar da shi
Mugun hali na bayyane da na voye
Bai ba da damar a bayyana raayi kuma in an yi shiru a cutu
o Mace ta huxu ta yabi mijinta saboda matsakaicin halinsa: ba
tsanani kuma ba sakaci, sannan ba ta tsoron yin maganar da
ta so a gabansa, shi kuma ba ya qosawa da ita.
o Mace ta biyar ta yabi mijinta da rashin yawan sa ido game
da harkokin gida (xabiar a ji, a qi ji, kuma a gani, a qi
gani), da jurumta a waje, da rashin qeqe-da-qeqe.
Sunday, March 26, 2017 4
ABUBUWAN DA HADISIN YA QUNSA [2]
o Mace ta shida ta bayyana mijinta bai rage komai na abinci da
abin sha, saboda ta iya abinci da abin sha; amma ta zarge shi
da yawan barci da rashin damuwa da halin da ta ke ciki.
o Mace ta bakwai ta siffanta mijinta da wuyan shaani, da vata,
da rashin faminta, ga yawan duka.
o Mace ta takwas ta yabi mijinta da tsafta, da taushin jiki da
daxin qamshi.
o Mace ta tara da ta goma sun yabi mazajensu da karamci, da
kyautatawa baqi da maqwafta da kyakkyawar zamantakewa.
o Mace ta sha xaya ta yabi mijinta da kyakkyawar zamantakewa,
da iya mallakar zuciya wanda hakan ya hana ta ganin laifinsa.

Sunday, March 26, 2017 5


DARUSSA DA FAIDODI DAGA HADISIN [1]
1) Manzon Allah (SAW) na hira da iyalinsa kuma yana da
haqurin sauraren maganarsu, ba tare da nuna qosawa ba.
2) Hikiyar da Aisha (RA) ta kawo ta qunshi gulmar da mata
suka yi game da halin mazajensu a zamanin jahiliyya.
3) Hadisin na tabbatar da butulcin mata, kasancewar mafi
yawansu aibobin mazajen suka ambata duk da cewa ba za
su rasa halayen qwarai ba.
4) Mace na da buqatar namiji, kuma ya dace ta yi haquri da
mijinta ko da yana da aibobi matuqar ba su tava addininta
ko mutuncinta ba.

Sunday, March 26, 2017 6


DARUSSA DA FAIDODI DAGA HADISIN [2]
5) Yana daga abin da ke kawo soyayya mace ta ba mijinta
labari mai daxi ba wanda ke tada hankali ba.
6) Ba laifi a buga misali don sauqaqa fahimtar abu.
7) Siffanta mace da kyakkyawar siffa ko kiranta da sunan da
zai faranta mata rai na sa ta qara son mijinta.
8) Barin mace ta ba iyayenta wani abu daga cikin abin da
mijinta ya mallaka, ba tare da almubazzaranci ba.
9) Rashin adawar mace ga surukanta, da yayan mijinta.
10) Mijin kirki matarsa ba ta tsoron yin magana a gabansa,
kuma ba ya gwasale ta ko ta yi kuskure, sai dai ya gyara.
Sunday, March 26, 2017 7
DARUSSA DA FAIDODI DAGA HADISIN [3]
11) Karvar uzuri da yafewa na daga xabiun qwarai ga namiji.
12) Rashin yawan sa ido a kan abubuwan da mace ke yi, da
kau da kai daga abubuwan da ba su taka-kara-sun-karya
ba na daga abubuwan da mace ke so.
13) Qwarewar mace wajen girki na daga dalilan samun
soyayyar mijinta.
14) Cizawa da hurawa na daga dalilan nasarar zamantakewar
aure a haqqin namiji.
15) Dukan mace na daga munanan xabiu.

Sunday, March 26, 2017 8


DARUSSA DA FAIDODI DAGA HADISIN [4]
16) Karamci da kyautata wa mutane, da liyafa ga baqi na daga
abubuwan da ke jawo wa mutum matsayi a cikin mutane.
17) Tsaftar jiki da tufafi da muhalli na kyautata rayuwar aure
18) Samar wa mace da kayan qyala-qyalai na sa ta so miji.
19) Girmama mace da mutunta ta na daga xabiun qwarai.
20) Tallafa wa mace da mataimaka a gida idan da hali, ko miji
ya taimaka da kanshi na da muhimmanci.
21) Rashin qiba ko yawan rama na daga siffofin da maza ke
so ga mace.
22) Zaven yan aikin gida amintattu na da muhimmanci.
Sunday, March 26, 2017 9
SHAWARWARI GA MATA [1]
1) Biyayya da xaa cikin abin da ba savon Allah a ciki gwargwadon
iko
2) Tsaftar jiki da tufafi da muhalli
3) Haquri da kaxan (qanaa), da qarfafa gwiwa cikin ayyukan alheri,
da ririta xan abin da ya samu, da rashin ba abin duniya muhimmanci
4) Godewa qoqarin miji, da nuna ana tare da shi cikin samu da rashi; a
lokacin daxi ko wuya
5) Fahimtar sirrin kwanciyar aure: lura da buqatar miji; jawo raayin
miji zuwa ga jimai a lokuta na musamman; ba da kai a ko wa ne
hali matuqar ba bu dalilin hani a Shariah; taqaita yanga ga kafin a
kevewa da miji; fahimtar abubuwan da suka fi motsar da shaawa;
d.s
6) Qwarewa wajen yin nauoin abinci da abin sha
Sunday, March 26, 2017 10
SHAWARWARI GA MATA [2]
7) Nisantar muamala da waxanda ba ya son a yi muamala da su, ko
sanya tufafin da ba ya son a sanya musamman idan za a fita
8) Kulawa da haqqoqin miji dangane da mutunci, da yaya, da
dukiya a ko wa ne lokaci
9) Ba rayuwar aure muhimmanci, da rashin nuna son kai a cikin
alamuran zamantakewa
10) Girmama iyaye da yan uwan miji
11) Yardar da miji a lokacin fushi ta hanyar (1) ba da haquri idan ita
ce mai kuskure (2) rashin nacewa a kan ya amsa laifi idan shi ke
kan kuskure (3) idan ya yi fushi ne saboda wani abu daban, a bari
sai ya huce, daga baya a yi magana.
12) Matsakaicin kishi, da rashin quntata wa miji ko takura shi dangane
da abokiyar zama ko yayanta
Sunday, March 26, 2017 11
SHAWARWARI GA MAZA [1]
1) Kyakkyawar tarba ta hanyar yin sallama lokacin shigowa gida, da
sakin fuska
2) Daddaxar magana
3) Kyakkyawar abota da nishaxantarwa ta hanyan hira, da barkwanci,
da suararen labarinta
4) Wasanni da xaukar hankali
5) Taimakawa a gida gawargwadon hali da yanayi da lokaci, da yaba
wa qoqarinta
6) Neman shawara, musamman cikin abubuwan da suka shafe ta ko
suka shafi yayanta
7) Kula da haqqoqin iyali a lokacin bulaguro, musamman dangane da
abinci da wajen zama da tsaro

Sunday, March 26, 2017 12


SHAWARWARI GA MAZA [2]
8) Taimako da abubuwan buqata, kamar kuxi, gwargwadon iko
9) Tsafta da ado
10) Haxa ta abota da mata na qwarai waxanda za su yi taimakekeniya
wajen samun tsoron Allah da kyautata zamantakewar aure, da
nisantar da ita daga qawayen banza
11) Girmama iyayenta da kyautata wa iyayenta, da yanuwanta, da
qawayenta
12) Qarfafa mata gwiwa cikin ayyukan alhairi, musamman karatu da
daawah da ciyarwa saboda Allah
13) Tarbiyyantarwa da ilmantarwa don sanin wajibanta
14) Matsakaicin kishi, da rashin munana zato ko zargi mara dalili
15) Haquri da juriya da yafewa da nasiha da bi sannu-sannu

Sunday, March 26, 2017 13

You might also like