Matsayin Mata A Musulunci, Yahudanci Da Nasaranci
Matsayin Mata A Musulunci, Yahudanci Da Nasaranci
Matsayin Mata A Musulunci, Yahudanci Da Nasaranci
Tarjamar
Wanda ya buga Jamiyar Isad da Sakon Musulunci P.O.Box 834 Alexandria, Egypt [email protected] -WWW.islamicmessage.net Registered Charity No. 536
LABARUN DA KE CIKI
Babi na 1 - Gabatarwa Babi na 2 Laifin Hauwa'u Babi na 3 Gadon Hauwa'u Babi na 4 Kunyatattaun Diya Mata Babi na 5 Ilimin Mata Babi na 6 Mace kazamtatta mara Tsarki Babi na 7 Bayar da Shaida Babi na 8 Zina/kwartanci Babi na 9 Bakance/Alwashi Babi na 10 Dukiyar Matar Aure Babi na 11 Saki Babi na 12 Uwaye Mata Babi na 13 Gadon Mata Babi na 14 Shaanin Mata wadanda Mazajensu suka Mutu Babi na 15 Aladar Auren Mata fiye da Daya Babi na 16 Lulluvi/Mayafin Mata wanda kan rufe har Fuska Babi na 17 Cikasawa/Jawabi a Karshe
BABI NA 1
Gabatarwa
Shekaru biyar da suka gabata, na karanta wani labari a mujallar Toronto Star ta ranar 3 ga watan Yuli ta shekarar 1990, wanda aka yi wa suna Islam is not alone in Patriarchal Doctrines (wato Musulunci ba shi kadai ne, hanya wadda a kan bi ta wajen addinai da ke bayar da iko da muhimmanci ga maza kawai ba), wanda Gwynne Dyre ya rubuta. Labarin ya siffanta fusataccen mayar da matanin masu yawa kwarai na mahalarta taron shawarar mata da iko, da aka gudanar a birnin Montreal ta kasar Canada, a kan fadar raayoyin sananniyar matar nan 'yar kasar Masar Dr. Nawal Sadawi. Kasawarta na kauce wa magana, ko hali wanda ya kan jefa wasu jamaa cikin laifi, sun hada da bayanai kamar haka: Jamaar da suka fi dukan mutane takurawa ga mata, an fara samunsu ne, cikin addinin Yahudanci a cikin Littafin Tsohon Alkawari (Attaura), saan nan a addinin
Kirista, kuma saan nan a cikin Alkur'ani; duk addinai suna bayar da iko da muhimmanci ne, ga maza kawai, zama sakamakon alummomi masu bayar da iko da muhimmanci ga maza kawai; kuma Mayafin mata ba takamai mai sabon Musulunci ba ne, amma wani tsohon tarihi, aladu, da ingantattun aladun kabila daya ce, da take dauke da shi shekaru masu yawa, tare da yawan kiyasi addinai iri daya. Mahalarta taron ba za su iya jure wa ci gaba da zama ba, yayin da imaninsu ake tunanin cewa ya daidaita da addinin Musulunci. Ta haka, Dr. Sadawi ta samu babban alkalamin suka. Ba a karbi raayoyinta ba (a cikin zauren). Bernice Dubois ta Kungiyar Mata ta Duniya (World Movement of Mother's) ta furta cewa: Amsoshinta suna bayyana wani rashin hazikanci game da imanin wadansu mutane ne. Alice Shalvi wadda take cikin tsarin sunayen mutane, masu amsa tambayoyi a wagen mahawarar, ta hadaddiyar kungiyar matar Israila (Israel Women Network) cewa ta yi: Dole ne in ki yarda da (fadar raayoyinta), babu wani batun hazikancin ko imani da lullubi cikin addinin Yahudanci. Labarin a mujallar ya ce, ko ya ba da gaskiya da cewa, wadanan fusataccen rashin yarda masu yawa kwarai sakamakon karfaffa wani halin yin wani abu musamman ne, a kasashen Turai ta Yamma, (don) a sa wa Musulunci laifi bisa wasu aladun yi wadanda suke kamar da yawansu wani shashin mallakar tarihin, da aladun da ingantattun aladun kabila daya ce ta kasashen Turai ta Yamma. Gwynne Dyer ya rubuta cewa: Matan Kiristoci da na Yahudawa, ba za su zauna ana yin batu a jinsi daya ba, kamar wadancan mugan Musulmai ba. Ban yi mamakin ba, cewa mahalarta taron shawarar sun riki wani raayin musun Musulunci, saad da (tattaunawar) ta shafi batuttukar mata. A Turai ta Yamma, an hakikanta cewa, Musulunci shine, ya zama alamar kaskanta mata fiye da dukan sauran addinai. Domin a fahinci yadda tabbatacen wannan raayi yake, ya isa zama hujja issashe, mu ambaci cewa munistan ilimi na kasar Faransa, ya yi umurni kwanan nan, na korar dukan yan-mata dalibai masu sanye da lullubi (mayafi) daga makarantun kasar bakidaya! Wata matashiya daliba Musulma mai sanye da dan kwalin kai an hana hakkinta na neman ilimi a Faransa, yayin da matashiya Kirista 'yar tarikar Katolika mai sanye da cross (gicciye), ko kuma Bayahudiya mai sanye da tagiyar Yahudanci, ba a hana ta ba. Ba za a taba mantawa ba da abin da ya auku ko halin da 'yan-sandan kasar Faransa ke ciki dake hana duk yan mata Musulmai masu sanye da yan kwalayen kai daga shiga manyan makarantunsu, domin neman ilimi. Wannan kan sa a zuciya yawan tunanin wani kuma abin babban kunya irin wannan, na gwamna George Wallace da ya auku a shekarar 1962, da yake tsaye a kofar wata makaranta, yana kokarin toshe mashigin bakaken dalibai, domin hana manufar kebe wata launin fata dabam da wata, a wurin da iri na mutane dabam ake waresu, a wuraren na jamaar makarantun Alabama. Bambancin dake tsakanin wadannan abubuwan da suka auku guda biyu, shine, bakaken dalibai sun samu halin taimakawar yawancin Amurkawa da ma mutanen duniya baki daya. Shugaba Kennedy na kasar Amurka, a wancan lokacin, ya tura sojoji masu tsaron kasa su yi amfani da karfin tuwo wajen kau da kofar shigar bakaken dalibai. Yayin da a gefe guda kuma, 'yan-mata Musulmi ba su samu taimako daga wani ba. Maganarsu ga alama tanada dan karamin juyayi, ko a ciki da wagen Faransa. Dalilin kuwa shine, rashin hazikancin mai bazuwa sosai da tsoron duk wani abin da yake da alaka da Musulunci a zukatan mutane a daukacin fadin duniya, a yau. Abin da ya fi jan hankalina, ya bani shaawa fiye da dukan komai, gama da taron shawarar Montreal shine, tambaya guda: Shin, bayanai da Dr.
Sa'dawi ta furta ne, ko kuwa, wata daga cikin masu sukar ta ce, ke dauke da wani tabbataccen abu? A wani bangare guda kuma, shin, Musulunci, Kiristanci, da Yahudanci suna da imani ko hazikanci guda ne game da mata? Shin, sun bambanta a raayoyinsu ne? Shin, Kiristanci da Yahudanci sun kan ba mata kulawa wadda ita ce mafi kyau, fiye da yanda Musulunci ke yi ne? Mene ne gaskiyar lamarin? Ba abu ne mai sauki ba, a nemo kuma a samo amsoshin wadannan tambayoyi masu wuya. Farkon wuyar da zai hana hakan kuwa shine, dole ne mutun (mai bayar da amsar) ya zamo adali mara nuna goyonbaya ga wani, kuma kada son ransa ya yi tasiri a kansa; a kalla, matsanancin akinsa ya zama hakan. Wannan shine, abin da Musulunci ya kan koyar. Al-kurani ya koya wa Musulmai fadi gaskiya ko da kuwa wadancan dake kusa da su sosai ba sa sonta. Allah Ya ce: Kada ku kusanci dkiyar maraya face da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga karfinsa. Kuma ku cika mdu da sikeli da adalci, ba Mu kallafa wa rai face iyawarsa. Kuma idan kun fadi magana, to, ku yi adalci, kuma ko da ya kasance ma'abcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. Wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: tsammaninku, kuna tunawa) An'am: 152. ( Ya ku wadanda suka yi mani! Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Saboda haka, kada ku bibiyi son zciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana ko kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Ya kasance Masani ga abin da kuke aikatawa) Nisa: 135. Wani dalilin wuyar (tambayoyin) kuma shine, girman fadin fannin na ilimin, da yake dauke da shi, yadda za ka tsai da tunkaransa. Don haka, a cikin 'yan shekarun bara, sai na kashe awowi ina karanta Bible (littafin addinin Kirista), da Kundin fannonin addini, da Kundin Yahudanci, domin nemo amsoshin wadannan tambayoyi. Haka kuma na karanta littafai masu yawa wadanda suka tabo batun matsayin mata na addinai dabam-dabam, wadanda malamai, da masu kokarin yin bayyanai da kare raayoyin addini da masu suka (zargi) suka wallafa. Bayanai (wato labarai ko raayoyi) dake tafe a cikin wadanan babuka masu zuwa, suna yin misali da muhimman ganowar wannan guntun binciken asali (abin da na gano) ne. Ban yi ikirarin cewa, son raina ya yi tasiri a kaina ba da gaske, wannan (aiki) ya gagari yawan iyakacin abin da zan iya dauka. Dukan abin da zan iya fada shine, na yi kokari a koina cikin wannan bincike, in matso da kammalallen Alkurani mara aibin, maganar adalci. Zan so na bayar da muhimmanci na musamman a wannan gabatarwa cewa, manufata a wannan karatu ba don in ce Yahudanci, ko Kiristanci ba shi da wata daraja, ko wani muhimmanci ba ne (wato mu gane, karatun bata da wata alaka da cin-fuskar Kirista ko Yahudawa, face nuna gaskiya da adalci). A matsayin mu na Musulmi, mun yi imani da tushen kwarai na dukkan addinan biyu. Babu wanda zai iya zama Musulmin ba tare da yin imani da Annabi Musa (A.S.) da kuma Annabi Isa (A.S.) a matsayin Annabawan Allah masu girma ba. Makasudi na kawai shine, in hakikanta cewa Musulunci gaskiya ne, kuma in yabi abin da ba a yi ba na bin umurni na dogon lokaci a kasashen Turai ta Yamma zuwa ga sako na gaskiya na karshe da Allah Ya aiko zuwa ga dukkan halittu. Haka kuma, zan so na bayyana cewa zan fi mayar da hankali na ne, kawai kan aqida (wato hanya wadda a kan bi ta wagen addini). Galibi, abin da zan fi mayar da hankalina gare shi, shine, matsayin mata a cikin wadannan addinai guda uku, kamar yadda ya kan bayyana a tushensu na ainihi, ba kamar yadda miliyoyin mabiyansu suka saba yi ba a fadin duniya. Don haka, yawancin dalilan da hujjojin da aka ambata kan zo ne daga Alkur'ani, da Hadisin Manzon Allah (tsira da
amincin Allah su kara tabbata a gareshi), da Littafin Yahudawa, da Littafin Kiristoci, da kuma kalaman wasu daga cikin manyan Qissisan (wato Fada Fadan) coci, wadanda suka yi tasiri da yawa akan mabiyansu, wadanda raayoyinsu sun yi taimako da bayyana maana da siffa Kiristanci (wato suna da matukar tasiri wajen ci gaban addinin Kirista). Wannan shaani dake cikin tushoshen kan ruwaito tabbaccen abu da cewa, hazikancin wani addini ta hanyar la'akari da halaye (raayoyi) da dabi'un wasu daga cikin mabiya wannan addini, ta wagen suna kawai, ba dai-dai ba ne, rudu ne, bata ne. Mutane da yawa su na rikita aladun kabila daya da addini, kuma wadansu da yawa ba su san mene ne abin da littafan addininsu ke fadi ba, kuma wadansu da yawa ba su ma kula ba (wato kan nuna halin ko in kula).
BABI NA 2
Laifin Hauwa'u
Addinan uku sun yarda da tabbataccen abu guda na asali: Allah Ya halicci duk mata da maza, Mahaliccin duniya, da rana da wata da taurari duka. Amma dai, sabani ya kunno kai jim kadan, bayan halittar farkon mutum, Adam, da macen farko, Hauwa'u. Hazikancin ko imani da halittar Adam da Hawau na Yahudu da Nasara an bayar da labarinsa daki-daki a Littafin Farawa 2:4 da 3:24. Allah Ya hana dukansu daga cin 'ya'yan itaciyar da aka haramta. Macijin (shaidan) ya lalatad da Hauwa'u ta ci daga gareta, kuma daya bayan daya a cikin wani umurni musamman, Hauwau ta laladad da Adam ya ci tare da ita. A lokacin da Allah Ya yi wa Adam tsawa game da abin da ya aikata, sai ya dora dukkan laifin a kan Hauwa'u, inda ya ce: "Macen da Ka ajiye tare da ni a nan, ta bani yanki na 'ya'yan itaciyar, ni kuma na ci;" sakamakon haka, sai Allah Yace da Hauwa'u: "Hakika Zan kara maki yawan radadi da zogi a wajen haihuwa; cikin zafi za ki haifi 'ya'ya. Bukatar ki zata kasance ga mijinki, sannan kuma shi za ya mulke ki." Dangane da Adam kuma sai Yace: "Sakamakon sauraran matar ka da ka yi har ta sanya ka cin abinda aka hana ka ... tsinuwa ta tabbata a kan kasa saboda kai; sai ka wahala sannan za ka ci daga gareta tsawon rayuwar ka... Hazikancin Musulunci, ko imani da farkon halitta, ana samunsa ne, a wurare dabandaban a cikin Alkur'ani, kamar haka: Kuma ya Adam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci Wannan itaciya, har ku kasance daga azzalumai." Sai Shaidan ya sanya musu waswasi domin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hana ku daga wannan itaciya ba face domin kada ku kasance mala'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama. Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne n, a gare ku, hakka, daga masu nasha ne. Sai ya saukar da su da rdi. Sa'an nan a lokacin da suka dandani itaciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma
suka shiga suna likawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hana ku ba daga waccan itaciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaidan, a gare ku, makiyi ne bayyananne?" Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kanmu. Kuma idan ba Ka gafarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, hakka, Muna kasancewa daga masu hasara. A'raf: 19 23. Idan aka duba labaran da suka gabata game da farkon halitta da kyau, su kan ruwaito wasu bambance-bambancen fannin ilimi. Sabanin Bible (litaffin addinin Kirista), Alkur'ani ya sanya wa duk Adam da Hauwau laifi daidai bisa aikata laifinsu. Ba wani wuri a cikin Alkurani da wani zai samu ko da yin dan ambaton cewa wai Hauwa'u ce ta yaudari Adam har ya ci daga itaciyar, ko kuma wai ita ce ta fara ci kafin shi. Hauwa'un cikin Alkur'ani ba mayaudariya ba ce, ko mai jawo hankali namiji ga aikata abin da ya ki ba ce, ko mai halin lalatad da wani ba ce, kuma, bai kamata a ce an dura wa Hauwa'u da laifin zafin ko ciwon haihuwar 'ya'ya ba. Kamar yadda Alkur'ani ya fadi cewa, Allah ba Ya azabtar da wani saboda zunubin wani. Adam da matarsa Hauwa'u sun aikata laifi, amma sun nemi Allah Ya gafarta musu, kuma Allah Ya gafarta musu.
BABI NA 3
Gadon Hauwa'u
Kamannin Hauwa'u a matsayin mayaudariya mai jawo hankalin namiji da aikata shaanin mamalar maza da mata, a cikin Bible (littafin addinin Kirista) ya zama sanadin matsanancin tasirin kalmar musun mata mai karfi, a koina cikin hanyar aladar Yahudu da Kirista. An yi imani da cewa dukan mata sun gaji duk alhakin laifi, da kissar uwarsu ce Hawaun dake cikin littafin addinin Kirista. Sakamakon haka, dukansu ba amintattu ba ne, a taikace, ba su kamata a yarda da su ba, masu munanan halaye ne, kuma muga ne. An duba fitar jinin al'ada (wato haila), da daukar ciki, da haihuwar 'ya'ya, a matsayin ukuba da ya dace ga jinsin mace, sakamakon alhakin laifin da uwarta, ta asali ta aikata. Domin fahinta ko gane gaskiyar yadda kalmar musun Hauwa'un cikin Bible yake da shi ga magadanta mata, dole ne mu dubi rubuce-rubucen wasu Yahudawa da Kiristoci da suka fi muhummanci na duk lokuta. Bari mu fara da Littafin Tsohon Alkawari, mu ga wasu gajerun rubutu daga abin da ake kira (Adabin Hikima) kamar haka: "Na kwa tarasda wani abu daya da ya fi mutuwa dachi, watau mache wadda azargiya che, zuciyata azargiya che, da kuma; hannuwanta kuma sarka ne; amma wanda ya sami yardar Allah za ya tsere mata; amma za ta kama mai-zunubi. Duba na iske wannan, in ji Mai-Wa'azi, na yi ta auna wani abu a kan wani, ina gwada su, domin in san baichin komi, abin da raina ke nema har yanzu, amma ban samu ba: namiji guda chikin dubu na samu; amma mache guda ban samu ba chikin wadannan duka." Littafin Mai-Wa'azi
7:26 28. A wani bangaren na adabi (litattafan) Yahudawa wadanda aka samu a cikin Bible din, mabiya tarikar Katolika ya zo kamar haka: "Babu muguntar da ke zuwa daga ko'ina, da ta kai muguntar mache. Zunubi ya fara ne daga mache kuma an gode mata, domin kwa dukanmu za mu mutu" Littafin Ecclesiasticus 25:19 24. Wani limamin Yahudawa ya lissafa la'anoni guda tara wadanda aka yi su a kan mata, sakamakon rashin biyayyar Allah da ya auku na Adam da Hauwau, kamar haka: Ya bayar da la'anoni guda tara da mutuwa ga mace: nauyin zubar jinin haila da na budurci; nauyin daukar ciki; nauyin haihuwar 'ya'ya; nauyin renon 'ya'ya; kanta na rufe ne, kamar na wadda ke yin kukan wanda ya mutu; ta kan hurhurje kunnuwanta kamar dauwamammiyar baiwa ko yarinya wadda ke yin bauta wa mai-gidanta; bai kamata a yarda da shaidarta ba; kuma bayan kome da kome ta cancanci a kashe ta- mutuwa" Har wannan lokacin, Yahudawa maza mabiya tarikar Orthodox (aladun imani da aikin kwarai) a adduarsu ta kullum safiya, su kan fadi Albarka a Hannun Allah take Sarkin duniya da rana da wata da taurari duka, da ba Ka halicce ni mace ba. Su kuwa mata, a gefe guda, kan yi godiya wa Allah kullum safiya da halittarsu gwargwadon (kamar) yadda Yake so. An kara samu wani addu'an a litattafan adduar Yahudawa masu yawa, kamar haka: Godiya ta tabbata ga Allah da bai halicce ni mutumin da ba Bayahude ba. Godiya ta tabbatta ga Allah da bai halicce ni mace ba. Godiya ta tabbata ga Allah da bai halicce ni jahili ba. Hauwa'un dake cikin Bible ta taka muhimmiyar rawa a Nasaranci fiye da yadda ta taka a Yahudanci. Zunubin da ta aikata yanada matukar muhimmanci a duk bangaskiyar Kirista saboda hazikancin ko bangaskiyar Nasara na dalilin aikowar Annabi Isa (A.S.) a duniya, sakamakon rashin biyayar Hauwau ce ga Allah. Ta aikata zunubi kuma ta lalada da Adam har ya biye mata wajen aikata irin zunubin da ta aikata. Sakamakon haka, Allah Ya fitar da su daga Aljanna zuwa Duniya, wadda aka la'anta saboda su. Sun bar zunubinsu ga zuruoinsu su gada musammam baya mutuwansu wanda Allah bai yafe musu ba, kuma ta haka, duk yan-Adam an haife su cikin zunubi. Domin tsarkake mutane daga zunubinsu na asali, Allah Ya sadaukad da Annabi Isa (A.S.), wanda ake dauka a matsayin DanAllah, a kan cross (giciye) Don haka, alhakkin kuskuren da Hauwa'u ta tafka, da na mijinta, da na asalin zunubin yan Adam duka, da na mutuwar Dan-Allah duk ana zargin ta da sune. A wani kaulin kuma, mace daya, mai aiki da raayinta ta yi sanadiyyar rashin girmamawar yan Adam duka. To yaya abin yake ga diyanta mata? Su ma masu zunubi ne kamarta, don haka, bai kamata hukuncin da za a yi musu ya sake zani ba da nata. Saurari furucin mai tsanani da wali Paul a cikin Littafin Sabon Alkawari, inda yake cewa: "Bari mache ta koya a kawaiche da biyayya sarai. Amma ban yarda ma mache ta koyas, ko kwa ta sami mulki bisa namiji ba, amma ta kasanche a kawaiche. Gama Adamu aka fara kamantawa, kana Hauwa'u; kuma ba Adamu aka rude ba, amma machen da ta rude ta fadi chikin zunubi." Littafin Timothawus 1 2:11 14. Maganar Wali Tertullian har ba kewaye-kewaye ba ce game da mata, tafi ta wali Paul a cikin lokacin da ya ke zantawa da 'yan'uwansa mata da yafi so sosai a cikin bangaskiya, ya ce: "Ba ku san cewa kowaccen ku Hauwa'u ce ba? Hukuncin Allah da ya hau kan wannan jinsi naku har yanzu babu abin da ya kawar da shi: alhakin laifin tilas yana nan
kuwa. Ku ne shighifar (kofar hanyar) Shedan; ku ne ku ka falasa haramtacciyar itaciya: Ku ne farkon wadanda ku ka kaurace wa doka ta Allah ba da izini ba: Ku ne ita (Hauwau) wadda ta jawo hankalinsa (Adam) mutumin da Shedan bai kasance mai karfin zuciya issashe da zai fada masa ba. Kun hallakar da kamannin Allah, mutum, cikin sauki sosai. Sakamakon kaurace wa doka ta Allah ba da izini ba har Dan-Allah ya mutu." Wali Agustine, amintaccen mutum ne da ya yi imani da wasiyar wadanda su ka riga shi. Ya rubuta wasika zuwa ga wani abokin, inda ya ce: "Mene ne bambanci ko ga matar aure ko ga uwa, ai bata sake zani ba, har yanzu Hauwa'u ce mai halin jawo hankalin namiji ga aikata shaanin maamalar maza da mata da lalle, za mu yi hankali ga kowace mace ni kam, ban ga wani alfanu da mace ke da shi ga namiji da ya wuce na haihuwar 'ya'ya ba. Bayan shudewar karnoni, Wali Thomas Aquinas har yau yana daukar mata a matsayin marasa hankula ne inda ya ke cewa: Bisa la'akari da yadda dabi'ar mutum take, mace mara hankali ce kuma wadda aka haifa cikin kuskure, domin kuwa karfin kwayar haihuwa dake jikin naminji ne kan sanya a haifi cikakken kamanin namiji, yayin da haihuwar mace kan zo ne daga wani nakasa a cikin karfi mai kuzari, ko daga wasu dan rashin lafiyar kayan jikin mutum dake sa ba su iya yin wani abu, ko ma daga wasu abubuwa masu tasiri na waje. Daga bisani, Ba'amurken nan mai ra'ayin kawo sauyi (gyare gyare) Martin Luther, shi ma bai ga amfani daga wata mace ba da ya wuce na zuba 'ya'ya barkatai a duniya, ba tare da sauraren illa da kan biyo baya ba. Ya ce: Idan sun gaji, ko ma sun mutu, hakan babu komai. Bari su mutu lokacin haihuwa, wannan shine dalilin kasancewarsu. An sha nanata cewa, mata ba su da wani muhimmancin amfani saboda kasancewar kamannin Hawau mai jawo hankalin namiji ga shaanin maamalar maza da mata, mun gode wa labarin da Littafin Farawa ya bayar. Hasali dai, hazikancin ko bangaskiyar Yahudu da Nasara game da mata ya samu gurbata daga imanin da batun cewa, Hauwa'u tana da dabi'ar sabo, da kuma na 'ya'yanta mata. Idan yanzu muka ba da kulawarmu ga abin da Alkur'ani ke fadi dangane da mata, cikin sauri za mu ankara cewa, imani ko hazikancin Musulunci game da mata ya yi matukar bambanta da na Yahudu da Nasara. Bari mu ga abin da Alkur'ani ke fadi: Lalle, Musulmi maza da Musulmi mata da muminai maza da muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata da masu tsare farjjinsu maza da masu tsare farjjinsu mata da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonsa mata Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma Ahzab: 35. Kuma mummunai maza da mummunai mata sashensu majibincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka, kuma suna daa ga Allah da ManzonSa. Wadannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwayi, Mai hikima.Taubah: 71. Saboda haka Ubangijinsu Ya karba musu cewa, Lalle ne N b a zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashenku daga sashe. To, wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu, kuma aka ctar da su a
cikin hanyaTa, kuma suka yi yaki, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana daga karkashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako. Al-Imran: 195. Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a saka masa ba face da misalinsa, kuma wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko mace alhali kuwa sh mmini ne, to, wadannan suna shiga Aljanna, ana ciyar da su a cikinta, ba da lissafi ba Ghafir: 40. Wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko kuwa mace, alhali yana mmini, to, hakka Muna rayar da shi, rayuwa mai dadi. Kuma haqqa Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa Nahl: 97. A fili yake cewa, ra'ayin Alkur'ani game da mata bai bambanta fiye da na maza ba. Duk namiji da mace, halittun Allah ne, wadanda babban makasudin zuwansu a duniya shine, bauta wa Ubangijinsu, aikata ayyuka na kwarai, nisantar (wato kauce) wa ayyukan assha, kuma dukansu za a yi musu hisabi dai-dai gwargwado (ta hanya mai dacewa). Alkur'ani, ko kadan bai ambaci mace da cewa shigifar (kofar hanyar) Shedan ce, ko kuwa ta na da dabiar yaudara ba. Haka kuma bai taba ambatar namiji da cewa kamannin Allah ne ba; abin da kawai ya nunar shine, dukan maza da mata halittunSa ne shi ke nan. Bisa ga maganar Alkur'ani, rawar da mace zata taka a duniya bai tsaya kawai a kan haihuwar 'ya'ya ba. An bukace ta da aikata ayyuka na kirki kamar yanda ake bukatar wani namiji ya aikata. Alkur'ani bai taba cewa babu mata nagari da suka taba rayuwa ba, Sabanin haka, Alkur'ani ya koya wa dukan muminai, maza da ma mata cewa, su yi koyi da wadancan matan wadanda suka dace kamar Nana Maryam da Matar Fir'auna, kamar haka: Kuma Allah Ya buga wani misali domin wadanda suka yi mani; matar Fir'auna, sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna. Kuma Ka tsrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsrar da ni daga mutanen nan azzalumai. Da Maryama diyar Imrana wadda ta tsare farjinta, sai Muka hra a cikinsa daga rhinMu. Kuma ta gaskata game da ayoyin Ubangijinta da LittattafanSa alhali kuwa ta kasance daga masu tawali'u. Tahrim: 11 13.
BABI NA 4
Kirista) game da jinsin mace ya soma ne jim kadan da aka haifi wata mace. Misali, Bible yana bayyana cewa, yawan kwanakin da uwa ke kasancewa cikin rashin tsarkin idan ta haifi mace, yafi tsawo fiye da idan namiji ne, kamar yadda yazo cikin Littafin Leviticus. 12:2 5. Bible din mabiya tarikar Katolika kan ambaci a bayyane cewa: Haihuwar diya mache hasara che. Ecclesiasticus 22:3. Sabanin wannan abin da aka furta mai gigitarwa, 'ya'ya maza, suna da yabo na musamman, kamar haka: Mutumen da ya ilmantar da dansa, za a fa kiransa mai-hassada ga makiyinsa. Ecclesiasticus 30:3. Wani limamin Yahudawa ya tsanya wani takalifi akan mazan Yahudawa, hayayyafar 'ya'ya, domin a haifar da sabuwar kabilar. A lokaci guda kuma, sun kasa boye irin fifikon da suke nunawa ga 'ya'ya maza, inda yake cewa: Komai zai tafi dai-dai ga wadanda suka haifi 'ya'ya maza, yayin da sabanin hakan kan tabbata ga wadanda suka haifi diya mata, kowa na farin-ciki da murna da haihuwar da namiji, yayin da kuma kowa ke bakin-ciki da haihuwar diya mace, kuma zaman lafiya kan zo Duniya da zuwan da namiji, idan kuwa diya mace ta zo Duniya, babu abin da ke zuwa. Ana dubar diya mace a matsayin mai farar kafa (mai mummunar sanadi), kuma mai janyo wa mahaifin ta abin-kunya, kamar haka: Diyarka fa mai tsaurin-kai che? Ka kula da ita da kyau, domin kada ta misheka abin-dariya a idon makiyanka, abin Magana a gari, abin tsegumi da jin-kunya a wurin jama'a. Ecclesiasticus 42:11, Ka fa kula sosai da diya mai-tsaurinkai, ko kwa ta lalata dukan wani abu mai-kyau da ta taba. Ka dubi idanunta na rashin-kunya, kada ka yi mamaki idan ta kunyataka. Ecclesiasticus 26:10 11. Guguwar irin wannan raayi na daukar diya mata a matsayin tushen abin-kunya, ta kai Larabawa, kafin zuwan Musulunci, har suka rika wulakantar da mata tare da kashe su. Alkur'ani ya tabbatad da laifin wannan mugun hali da tsanani, inda ya ke cewa: ( Yana boyewa daga mutane domin mnin abin da aka yimasa bushara da shi. Shin, zai rike shi a kan wulakanci ko zai turbude shi a cikin turbaya To, abin da suke hukuntawa ya mnana) Nahl:59. Abin da za a ambata ne cewa, irin wannan mugun laifi har abada da ba zai taba hanuwa ba (wato a kawo karshesa ba) a kasar Arebiya, ba domin karfin sharuddudin suka masu tsanani da Alkur'ani ya kan suki wannan alada da shi ba, kamar yadda yazo a cikin Alkur'ani Surar Nahl: 59, Zukhruf: 17, Takwir: 8 9. Kuma, Alkur'ani bai sanya bambanci a tsakanin diya maza da yaya mata ba. Sabanin Bible, Alkur'ani ya kan duba haihuwar diya mace da cewa kyauta ce kuma bai wa ce daga Allah, kamar yadda haihuwar namiji take. Alkur'ani ma yana ambaton haihuwar diya mace da farko, kamar haka: (Mulkin sammai da kasa na Allah kawai ne. Yana halitta abin da Yake so. Yana bayar da 'ya'ya mata ga wanda yake so, kuma Yana bayar da diya maza ga wanda Yake so) Shura: 49. Domin hallaka dukkan alamun laifin kissar diya mace wadda ba ta da laifi, a jamaar Musulmi, wadda ta fara kasancewa ba ta cikasa yin girma ba, Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi wa wadanda aka yiwa bai wa da haihuwar diya mata alkawarin samun babban rabo daga Allah, matukar za su basu kyakkyawar
tarbiyya, kamar yadda yazo cikin Hadisi: Duk wanda alhakkin tarbiyyantar da diya mace ke wuyansa, kuma ya kan ba su kyakkyawar tarbiyya, za su cece shi daga shiga wutar Jahannama. Bukhari da Muslim suka ruwaito, Duk wanda ya kula da diya mata guda biyu har zuwa balagarsu, ni da shi za mu kasance kamar haka, sai ya hada yatsunsa. Muslim ya ruwaito.
BABI NA 5
Ilimin Mata
Bambancin dake tsakanin hazakancin ko imani game da mata na Bible da Alkurani ba a iyakace shi a kan haihuwar diya mace jaririya ba, ya kan zarce nan. Bari mu gwada raayoyinsu game da wata mace dake kokarin yin koyon addininta. Zuciyar Yahudanci ita ce Attaurah, dokarta. Amma dai, bisa ga maganar littafin Talmud, An kade (dauke) mata karanta Attaurah. Wasu daga cikin limaman Yahudawa sun furta cewa, Gara a kona kalmomin Attaurah a cikin wuta, da a ce an bayar dasu ga mata, suka kara da cewa, Duk wanda ya karantar da diyarsa Attaura, kamar ya karantar da ita batsa ne. Ra'ayin Wali Paul a cikin Littafin Sabon Alkawari ba mai fasaha ba ne, kamar a jamaar dukan waliyyai, ga abin da ya ke cewa: Bari mata su yi shuru chikin ekklesai: Gama ba a yarda musu su yi Magana ba; amma su zama da biyayya, kamar yadda Attaurat kuma ta fadi. Idan kwa su na son su koyi komi, sai su tambayi mazajensu chikin gida: gama abin kumya ne ga mache ta yi Magana chikin ekklesiya. Littafin Kwarantiyawa 14:34 35. Ta yaya mace za ta samu ilimi ba tare da an bata dammar yin Magana ba? Ta yaya mace za ta girma cikin kwazo da kaifin kwakwalwa (mai wayo) idan aka tilasta mata ci gaba da kasancewa cikin wani halin mika-wuya (yin biyayya)? Ta yaya za ta fadada fahimtarta, matukar mijinta ne kadai hanyarta na samun bayanai, a cikin gida? Yanzu, domin yin adalci, ya kamata mu tambaya cewa: Shin, matsayin Alkur'ani ya bambanta kuwa? Labari guda mara tsawo da aka bayar a cikin Alkur'ani ya takaita matsayin takaitacce. Khaulah mace ce Musulma wadda mijin ta mai suna Aus ya yi lafazi da wannan bayani a dai dai lokacin fushi, kamar haka: Ke, a wuri na, kamar bayan mahaifiyata kike. Irin wannan furuci ne, kafuran Larabawa ke amfani da shi a matsayin sakin macen aure, wanda kan 'yanta miji daga kowane irin shaani na maamalar miji da matarsa ta aure, amma ba zai bar matar ba ta bar gidan mijin, ko ta sake wani auren. Da jin wadanan kalamai da suka fito daga bakin mijin ta, Khawlah ta kasance a cikin wani yamutsattsen hali. Sai ta tafi sak zuwa wurin Anabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) ta yi roko a yi mata wani abu da halin da take ciki (ta gabatar da kokenta gare shi). Sai Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) a ganinsa ya ce, ta yi hakuri tunda a alama babu wata mafita. Khaulah ta ci gaba da jayayya
da Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) a wani yin kokarin ya tsirad da ratayayyen aurenta (wadda ba a sake ta ba, kuma ba a aure ta ba). Gaba kadan, sai Alkur'ani ya sa baki (wato ya yi magana) cewa; an karbi hanzarin Khaulah. Firicin Allah mai yanke Shariaah ta kawar da wannan al'adar ta rashin adalci sosai. Sai aka saukar da cikakkiyar sura guda wadda aka yi wa suna 'Al-Mujadalah' ko kuma 'Mace mai jayayya' a cikin Alkur'ani bayan wannan aukuwa da ya faru, inda take cewa: Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jayayya game da mijinta, tana kai Kara ga Allah, kuma Allah najin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani. Mujadalah: 1. Mace, a hazikancin Alkur'ani, tana da ikon ta yi jayayya, har ma da Annabin (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) da kansa. Babu wanda ke da iko da ya umurce ta da ta yi shiru. Ba ta karkashin takalifi da zata dauki mijinta a matsayin shi ne kadai madogararta wurin batunta na Addini ko shari'a.
BABI NA 6
kafafunta ne. Maaikacin addinin Kirista wadda matarsa, diyarsa, ko mahaifiyarsa ke cikin haila, ba zai iya karanta wa mutane addu'o'i masu albarka a cikin dakin ibada ba. Ba abin mamaki ba ne mata Yahudawa da yawa har yanzu suna dubar jinin haila a matsayin laanta. Addinin Musulunci bai dubar wata mace mai haila tana mallakar wani irin kazamta mai yaduwa ba, da ba a taba ta balle a ce laananniya ce. Ta kan tafiyar da rayuwar ta na kulum cikin kunci guda daya ne: An haramta wa maaurata (wato mutum da matarsa) saduwa da juna (tarawar miji da mata) a lokacin da matar ke cikin haila, amma babu laifi su yi kowane irin tabawar jiki kamar wasa, 'yan shafe-shafe a tsakanin su. An haramta wa mace mai haila aiwatar da wasu daga cikin ayyukan ibada, kamar sallolin yau da kullun da azumi, a lokacin da ta ke cikin haila.
BABI NA 7
Bayar da Shaida
Wani kuma muhimmin batu da Alkur'ani da Bible ba su dace ba a kansa, shine, batun bayar da shaidar mata. Gaskiya ne cewa, Alkur'ani ya umurci muminai wadanda ke mu'amala da kudi da cewa, su nemi shaidar mutum biyu maza, ko kuwa namiji daya da mata biyu, kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani Surar Baqarah: 282. Amma dai, gaskiya ne kuma cewa, a wasu wurare Alkur'ani ya kan amince da bayar da shaidar mace dai-dai da yanda ya kan amince da shaidar namiji. A kan gaskiya, shaidar mace kan mayar da shaidar namiji ta banza. Idan mutum yana jifar matarsa da laifin yin jimai (kuma wadansu shaidau ba su kasance a gare shi ba, face kansa), Alkur'ani ya bukace shi da ya yi muhimmin rantsuwa sau biyar a matsayin shaidar alhakin laifin matar. Idan matar tana yin musun (aikata wannan laifin) sai ta rantse kamar yanda ya rantse (wato sau biyar), ba a dubar ta mai laifi, kuma a cikin kowane hali auren ya mutu, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana, Surar Nur: 6 11. A wata fuska kuma, a al'ummar Yahudawa ta farko, an haramta wa mata bayar da shaida. Limaman Yahudawa sun lissafa mata da basu da hurumin bayar da shaida saboda laanoni guda tara da aka yi a kan dukansu, saboda aukuwar kin bin umurnin Allah da Adam da Hawau suka yi, kuma su ka rabu da Aljanna, (duba sashen Gadon Hauwa'u domin karin haske). Mata Yahudawa a Israila ta yau, ba a yarda da su bayar da shaida a kotunar da limamin Yahudawa ke jagoransu ba. Limaman sun tabbatar da gaskiyar don me mata ba su iya bayar da shaida a kutonar limamansu ba, ta hanyar karanto Littafin Farawa 18:9 16, inda aka ambaci cewa Saratu, matar Annabi Ibrahim (A.S.) ta yi karya. Limaman sun yi amfani da wannan aukuwa a matsayin shaidar cewa mata ba su cancanta su bayar da shaida ba. A nan ya kamata a yi tunanin cewa, wannan labarin da aka ba da labarinsa a cikin Littafin Farawa 18:9 16, ya zo a cikin Alkur'ani ba sau daya ba, ba tare da nuna wata yin dan ambaton karya ba da Saratu ta yi, a duba Alkur'ani Surar Hudu: 69-74, Dhariyat: 24-30. A wurin Kiristocin kasashen Turai ta Yamma, da duk tarihin ikilisiya ta cocin Kirista, da shari'ar ta tsakanin mutum da mutum sun hana
mace bayar da shaida sai a karnonin baya-bayan nan suka samu wannan 'yancin. Idan wani miji yana jifar matar aurensa da laifin jimai (fasikanci ko lalata), abin da ta bayar da shaida a kai ba za karbe shi ba gaba daya, bisa ga maganar Bible. Matar auren da aka jifa da irin wannan laifin, zaa gurfanar da ita a gaban kuliya. A wannan gwadawa, macen auren za ta fuskanci wani sauraren koto mai wuyar fahimta da kaskanci, wanda ake tsammani zai hakikanta alhakin laifinta ko mara laifi, kamar yadda ya zo a cikin Littafin Lissafi. 5:11 31. Idan aka iske ta mai laifi ce bayan wannan gurfanarwar, za ta fuskanci hukuncin kisa. Idan aka iske ta ba mai laifi ba, mijinta zai zama mara laifi aikata mugun aiki. Bayan wannan, idan wani mutum ya auri mace, saannan yana jifar ta da cewa bai same ta budurwa ba, ba za a yarda da shaidar da za ta bayar ba. Iyayenta za su gabatar da wata shaidar da zata tabbatar da budurcinta a gaban datibai na birni. Idan kuwa iyayen ba su iya hakikanta da rashin laifin diyarsu ba, sai a jefe ta har ta mutu a kofar gidan ubanta. Idan kuma iyayen sun iya hakikantar da rashin laifinta, za a ci tarar mijin kudi kimanin (Shekel) din azurfa dari kawai ne, kuma ba zai iya saki matar aurensa ba muddar ransa, kamar yadda ya zo: Idan kowane mutum ya amre mache, ya shiga wurinta, ya kita kuma, ya yi tseguminta da miyagun sara, ya kwa sa mata mugun suna, yache, Na dauko wannan mache, amma sa'anda na kusa da ita ban iske budurchi gareta ba: Sai uban yarinyan nan da uwatta za su dauki shaidar budurchin yarinyan, su fito da su wurin datibai na birni a wajen kofa: uban yarinyan kuma za ya che ma datiban, Na ba mutumen nan diyata ta zama matatasa, ama ya ki ta; gashi kwa, ya sa mata laifin al'amura na kunya, ya che, ban iske diyarka budurwa ba; ga kwa wadannan abu su ne alamun budurchin diyata. Su kuma sai su bude zanen a gaban datiban gari. Datiban gari kwa su kama mutumen nan su yi masa foro; su chi shi tara shekel na azurfa guda dari, su ba uban yarinyan, da shike ya jawo mugun suna bisa diyar Israila: za ta zama matarsa kuma; ba shi da iko shi saketa muddar ransa. Amma idan zancen nan gaskiya ne, ba a iske shaidar budurchi ga yarinyan ba; daga nan sai su fito da yarinyan a kofar gidan ubanta, mazajen garinta kwa za su jejjefe ta da duwatsu har ta mutu: domin ta aika mugun abu chikin Israila, da ta yi karuwanchi chikin gidan ubanta: hakanan za ka kawasda mugunta daga chikinka. Littafin Kubawar Shari'a 22:13 21.
BABI NA 8
Zina/Kwartanci
A dukan addinan nan uku zina (kwartanci) ana dubarsa wani zunubi ne. Bible (littafin addini Krista) ya kan yanke hukuncin kisa ga duk mazinaci da mazinaciya, hakan ya zo a cikin Littafin Levitucus 20:10. Musulunci ma kan yin hukuncin kisa ga duk mazinaci da
mazinaciya kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani surar Nur: 2. Amma dai, maanar Alkur'ani na zina ya sha bambam sosai da maanar Bible. Bisa ga maganar Alkur'ani, shine, jibintar wani namiji mai aure ko wata mace wadda take da aure a cikin kwanciya da ita bayan aure. Shi kuwa Bible ya kan duba kwanciyar wata mace wadda take da aure ne, ban da namiji mai aure, a matsayin zina. Duba Littafin Kubawar Shari'a 22:22 da Littafin Misalai 6:20, 7:27. Idan an iske mutum ya na kwana da mache wadda ta ke da mijin amre, duka biyunsu za su mutu, shi mutumen da ya kwana da machen, da ita machen kuma: hakanan za ka kawas da mugunta daga chikin Israila.Littafin Kubawar Shari'a 22:22. Namijin da ya yi zina da matar wani mutum, watau wanda ya yi zina da matar makwabchinsa, da shi mazinachi, da ita mazinachiya, hakika za a kasha su. Littafin Leviticus 20:10. Bisa ga maganar maanar Bible, idan wani namiji mai aure ya kwanta da mace mara aure, wannan ba a dubarsa wani laifi ko kadan. Namiji mai aure da ya kwanta da mace mara aure ba mazinaci ba ne. Kuma mata mara aure da suka kwanta da shi ba mazinata bane. Ana aikata laifin zina ne, kawai idan wani namiji ko mai aure ko mara aure, ya kwanta da mace mai aure. A wannan halin namijin ana dubar sa mazinaci ne, koda bai yi aure ba, kuma macen ana dubar ta mazinaciya ce. A takaice, zina ita ce haramtacciyar saduwa da ya shafi macen dake da aure. Kwanciyar wani namiji mai aure da wata mace mara aure ba wani laifi ba ne a cikin Bible. Mene ne matsayin halin kirki na mutum biyu? Bisa ga maganar Kundin fanonin Yahudawa, an duba matar aure ta zama dukiyar mijinta, kuma zina ya zama wani cin hakkin mijin ne da bai cudanya da mutane ba; matar auren, a matsayin dukiyar mijinta, bata da irin hakki nan a kansa. Wato, idan wani namiji ya aikata zina tare da wata mace mai aure, yana cin dukiyar wani namiji ne, kuma, don haka sai a ladabtar da shi. Har yanzu a kasar Isra'ila, idan wani mutum mai aure ya kwanta da wata mace mara aure, 'ya'yansa da macen nan ana dubar su ba yan halal ba ne. Amma, idan mace mai aure ta kwanta da wani mutum, mai aure ne, ko mara aure ne, 'ya'yanta da mutumin nan ba yan halal ba ne kawai, har ma ana daukar su shegu ne, kuma ba za a yarda da su auri Bayahude ba, ban da sabon tuba (cikin addininYahudanci) da wasu shegu. Wannan haramcin aka bar wa 'ya'yan zurioin mutanen zamunna goma, har sai barnar zina, an dauka cewa ta ragu. A wata fuska kuma, Alkur'ani bai taba dubar mace ta zama dukiyar namiji ba. Alkur'ani, yana bayyana alakar dake tsakanin ma'aurata da fasahar magana da cewa: Kuma akwai daga ayoyinsa, Ya halitta muku matan aure daga kanku domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani). Rum: 21. Wannan shine, hazikancin Alkur'ani ko imani gama da aure: kauna, tausayi, da zamanlafiya ba dukiya ba ne da ninkin kaida na kirki ba ne, saboda yana daukar wata jamaa dabam daga wata.
BABI NA 9
Bakanci/Alwashi
Bisa ga maganar Bible, dole mutum namiji ya cika bakanci (waadin dake kansa) da mai yiwuya ne ya dauka wa Allah. Kada ya karya alkawarin da ya dauka. A wata fuska kuma, bakancin (waadin dake kan) wata mace ba tilas ne ya wajaba gareta ba. Sai mahaifinta ya yarda da shi idan tana zaune a gidansa, ko kuma da yardan mijin ta idan ta yi aure. Idan wani mahaifi ko wani miji bai bayar da goyon bayan bakancin diyarsa ko matarsa ba, dukan kabbarar da ta yi za su zama masu rashin amfani kamar yadda ya zo a cikin Bible: Sa'anda mutum ya yi wa'adi ga Ubangiji, ko kwa ya yi rantsuwa, shi yi wa kansa hani, ba za ya warware maganassa ba; sai shi aika duka abin da bakinsa ya furta. Idan kuma mache ce ta yi ma Ubangiji wa'adin komi tana yi ma kanta hani, tana kwa yarinya a gidan ubanta, idan ubanta ya ji wa'adinta, da inda ta yi wa kanta hani, ubanta kwa ya yi shuru da ita: dukan wa'adodinta za su tsaya, dukan abin da ta rantse za ta hana wa kanta za ya tsaya. Amma idan ubanta ya shaida rashin yardansa a ranan da ya ji, kodaya chikin wa'adodinta, ko abin da ta rantse za ta hana wa ranta, ba za ya tsaya ba: Ubangiji kwa za ya yafe mata, domin ubanta ba ya yarda mata ba. Idan kwa ta yi amre, tun wa'adinta yana bisanta, ko kwa garajen bakinta, idan ta yi wa kanta hani; mijinta kwa ya ji, ya yi mata shuru a ranan da ya ji: sai wa'adodinta su tsaya, da hanin da ta hana ma kanta za ya tsaya. Amma idan mijinta ya shaida rashin yardansa chikin ranan da ya ji; sai shi wofintadda wa'adin da ke kanta, da garajen bakinta, idan ta yi ma ranta hani: Uangiji kwa za ya yafe mata.amma wa'adin amraruwa, ko kwa sakakkiya, watau kowane abin da ta yi wa kanta hani, za ya tsaya a kanta. Idan kwa ta yi wa'adi chikin gidan mijinta, ko kwa ta yi wa ranta hani da rantsuwa, mijinta kwa ya ji, ya kwa yi mata shuru,ba ya shaida rashin yardansa ba; sai wa'adodinta duka su tsaya, kowane abin da ta yi wa ranta hani za ya tabbata. Amma idan mijinta ya wofintadda su a ranan da ya ji su; sa'annan dukan abin da bakinta ya furta a kan wa'adodinta, ko a kana bin da tayi wa ranta hani, ba za su tsaya ba; mijinta ya wofintadda su; Ubangiji kwa za ya yafe mata. Kowane wa'adi ken an, da kowace kakarfar rantsuwa maikuntata rai, au mijinta ya tabbatadda shi, au ya wofinta. Amma idan mijinta ya yi mata shuru kawai yau da gobe, da hakanan ya tabbatadda dukan wa'adodinta da dukan hanin da ke bisanta: ya tabbatadda su ken an, yayin da ya yi mata shuru a ranan da ya ji su. Amma idan ya wofintadda su bayan ya ji su; shi za ya dauki alhakkinta. Littafin Lissafi. 30:2 15. Don me wata kalamar mace bai wajabta gareta ba? Amsar wannan tambaya mara wuya ce: saboda kafin ta yi aure, ita mallakar mahaifinta ce, ko kuma mallakar mijinta ce bayan ta yi aure. Ikon mahaifi da yake da shi a kan diyarsa, ya cika har iyakacin cewa idan ya so yana iya sayar da ita. A cikin rubuce-rubucen limaman Yahudawa an nuna cewa: Namijin mai yiwuya ne ya sayar da diyarsa, amma macen ba ta iya yin hakan; namijin mai yiwuya ne ya yi alkawarin bayar da diyarsa ga aure, amma macen ba ta iya yin hakan. Litattafin limaman Yahudawa kan nuna cewa, aure yana yin misali da canja iko
daga uban ne, zuwa mijin: wata yarda da a aure wani, yana sanya wata mace wadda ake dubar zata zama dukiya mai muhimmanci sosai da zata canja -dukiya wadda lalle, ta isa yabo, ba a kai mata hari, ko hallaka da ta- Alhali, idan an duba matar zata zama dukiyar wani mutum kuma, ba ta iya yin kabara da mai mallakarta bai yarda da ita ba. Yana kayatarwa a lura da cewa, wannan koyarwar Bible na batun bakancin mata ya samu galibi, mugun sakamakon wani aiki ko abin da ya auku na musu da cewa mai yiwuya ne ya faru wani lokaci daga baya a kan matan Yahudu da Nasara har zuwa farkon wannan karnin da muke ciki. Wata mace mai aure a duniyar kasashen Turai ta Yamma, bata da matsayin mutum na biye da doka. Babu aikinta da ya kasance yana da amfani na biye da doka. Mijinta yana da hurumin kin maamular da yarje jeniya, da ciniki, ko akadin da ta kulla. Mata a kasashen Turai ta Yamma (magada masu yawa na abin wasiyyar Yahudu da Nasara), an hana su, ba su iya kulla wata yarje jeniya saboda kusan wani mutum ne ya mallake su. Mata a kasashen Turai ta Yamma sun sha wahala na kusan shekaru dubu biyu, saboda raayin Bible zuwa ga matsayin mata dangane da ubanninsu da mazajensu. A Musulunci, bakancin kowane Musulmi, namiji ko ta mace yana wajabta gare shi ne ko gare ta. Babu wani da yake da iko kin maamala kabbarar kowa kuma. Rashin cin nasarar cika wata muhimmiyyar rantsuwa (da aka kudurta rantsuya a kanta), wadda wani namiji, ko wata mace ta yi, sai a yi kaffarata kamar yadda aka nuna a cikin Alkurani: Allah ba Ya kama ku saboda yasassa a cikin rantsuwoyinku, kuma amma Yana kama ku da abin da kuka kudurta rantsuwoyi a kansa. To, kaffararsa ita ce ciyar da miskni goma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalanku, ko kuwa tufatar da su, ko kuwa 'yantawar wuya. Sa'an nan wanda bai samu ba, sai azumin kwana uku. Wannan ne kaffarar rantsuwoyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyaye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku kuna godewa. Ma'idah: 89. Sahabban Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi), maza da mata, sun kasance suna yin masa mubaya'a baka da baka. Mata da ma maza sun taho wurinsa cikin 'yanci suka yi kabarar rantsuwoyinsu (masa mubayaa) kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani: Ya kai Annabi! Idan mata mminai suka zo maka suna yi maka mubaya'a a kan ba za su yi shirki da Allah ba ga kome, kuma ba su yin sata kuma ba su yin zina, kuma ba su kashe, ya'yansu, kuma ba su zuwa da karya da suke kirkirawa a tsakanin hannuwansu da kafafunsu kuma ba su saba maka ga wani abu da aka sani na shar'a, to, ka karbi mubaya'arsu, kuma ka nemi Allah Ya gafarta musu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jinkai. Mumtahinah: 12. Wani mutum ba zai iya yin ransuwa ba a maimakon diyarsa, ko matarsa. Ko wani mutum ya ki maamala da rantsuwar da mace danginsa ta yi.
BABI NA 10
Yahudawa (duba shashin Kunyatattatun Diya Mata domin karin bayani). Sadakin ya kasance kyautar aure ce da aka gabatar da ita ga ango a karkashin sharuddar haya na gida. Mijin zai yi kamar mai mallakar sadakin ne, amma, bai iya sayar da shi. Amaryar za ta rasa ikon sadakin a daidai lokacin auren. Kuma, an sa rai ta yi aiki bayan auren, kuma dukan ladan aikinta, za su shiga hannun mijinta ne, sakamakon kudin abincinta, wanda ya kasance takalifinsa ne. Tana iya sake samu dukiyarta kawai ne, ta halaye guda biyu su ne: (1) Ta hanyar kashin aure, ko (2) Mutuwar mijinta. Da ita ce ta fara mutuwa, zai gaje dukiyarta. Idan mijin ya mutu, matar auren ta iya sake samun nata dukiyar kafin aurenta, amma bata da hakkin yin gadon rabo daga cikin dukiyar mallakar mijinta mamaci. Sai a kara da cewa, angon ma ya gabatar da wata kyautar aure ga amaryarsa, amma duk da haka kuma, ya kasance mai wannan kyautar ne muddin suna da aure. Addinin Kirista, ya bi irin hanyar aladar Yahudanci sai a kwanan nan. Dukan hukumomin addini da na mazauna kasa daya, a kasashen Kirista dake cikin ikon Rum [Roman (bayan sarki Qostantina)], sun bukaci wani yarjejeniyar dukiya a matsayin wani sharadin shaidar aure. Iyalai su kan mika wa diyansu mata yawaitacen sadakoki kuma, a wani abin da ya tabbata, maza na dan nuna son yin aure da wuri, a yayin da iyalai suna jinkirtad da aurayyan diyansu, sai har daga baya fiye da yadda ya kasance ga alada. A karkashin dokar addinin Kirista, wata matar aure ta kasance mai hakkin samun biya sadakinta ne, ga wasu wahaloli da ta sha idan auren ya kasance ya mutu, sai fa idan an kama ta da laifin aikata zina. A irin wannan hali, ta soke hakkinta na sadakin, wadda ya saura a hannun mijinta. A karkashin dokar Kirista, da sharia ta tsakanin mutum da mutum, mace mai aure a Kiristocin Turai da Amurka ta rasa hakkokin dukiyarta sai har a karshen karni na sha-tara da farkon karni na ashirin. Misali, hakkokin mata a karkashin dokar Turawa, an tattarasu kuma aka bugasu a shekarar 1632. Wadannan hakkoki sun hada da: "Cewa (dukiya) wacce miji ya mallaka tashi ce. Cewa (dukiya) wacce mace ta mallaka ta mijinta ce. Macen ba wai kawai ta rasa dukiyarta a lokacin auren ba ne, ta ma rasa darajanta na mutum da kansa. Babu wani aikinta da ya kasance yana da amfani na biye da doka. Mijinta na iya kin mamalar da sayarwa da ta kulla ko kyautar da ta bayar, kasancewar abin dauren da bai da amfani na biye da doka. Mutumin da ta kulla yarjejeniya da shi, an riki shi a matsayin mai laifin sharakawa a wata zamba (wato algus). Dadin dadawa, ba ta iya kai kara, ko a kai kara da sunanta, kuma ba ta iya kai karar mijinta. Wata mace mai aure ta kasance ana kula da ita kamar jaririya ce a idon doka (sharia). Matar auren ta zama ta mijinta ne kawai, kuma saboda haka ta rasa dukiyarta, da darajarta na mutum da kansa na biye da doka, da sunan danginta, Tun karni na bakwai ne Musulunci ya bai wa mata masu aure 'yancin kai na mutum da kansa, wane Yahudawa da Kirista na kasashen Turai ta Yamma suka hana su, sai har dan kwanan nan. A Musulunci, amarya da danginta, ba su a karkashin wani takalifi ko ta halin kaka, da su gabatar da wata kyauta ga angon. Yarinya a wani iyalin Musulmi, ba dawainiya (bashe) ba ce. A Musulunci wata mace mai halin girma ce da ba ta bukatar gabatar da kyaututtuka don ta jawo hankulan maza da zasu iya zama mazan aurenta. Angon ne, wanda dole ne ya gabatar da kyautar aure ga amaryar. Wannan kyautar, ana dubar ta dukiyarta ce, kuma ko angon ko dangin amaryar basu da rabo a ciki, ko ikon ta. A wasu al'ummomin Musulmi a yau, kyautar auren ta dolar Amurka dubu dari na lu'ulu'u ba na alada da ake ki ba ne. Amaryar kan rike kyautar aurenta ko da daga baya an
sake ta. Ba a yarda wa mijin ya dauki rabo a cikin dukiyar matarsa ba face abin da ta kan mika masa da yardarta. Alkur'ani ya fito fili karara ya bayyana matsayinsa game da wannan lamari, kamar haka: Kuma ku bai wa mata sadakoknsu da saukin bayarwa. Sa'an nan idan suka yafe muku wani abu daga gare shi, da dadin rai, to, ku ci shi da jin dadi da saukin hadiya Nisa: 4. Dukiyar matar auren da ladar aikinta suna karkashin cikakken ikonta ne, kuma na amfaninta ita kadai, tunda daukar dawainiyar kudin abincinta da na 'ya'yanta alhakin (takalifin) mijinta ne. Ko yaya matar ta kai da arziki, ba a tilasta mata daukar dawainiyar gida ba, sai fa in ita ne da kanta, ta kan bugi kirjin yin hakan da son ranta. Ma'aurata kan gaji junansu. Kuma, a Musulunci, mace mai aure kan rike 'yancin kanta na mutum da kansa na biye da doka, da sunan gidan su. Wani alkali Ba'amurke, ya ambata hakkokin mata Musulmi, cewa: "Wata yarinya Musulma mai yiwuya na iya yin aure sau goma, amma mazan nata da ta aura dabam dabam, ba su iya dauke wa kadaicenta da wasu dabam. Ita Duniyar rana ce da kanta tare da wani suna da doka na mutum da kansa.
BABI NA 11
Saki
Addinan nan uku suna da banbamcin raayoyi masu isa a fada na kwarai, game da saki. Gaba daya, Addinin Kirista ya kan kin saki kwarai. Littafin Sabon Alkawari ya kan ba da shawarar fadin raayinsa sosai da sosai cewa aure dangantaka ne da bai iya karewa. An ce Annabi Isa (A.S.) ke da takallifin cewa: Amma dai ina che muku, kowanene ya saki matatasa, im ba domin fasikanchi ba, yana sa ta ta zama mazinachiya: kuma dukan wanda ya amri sakakkiya, zina ya ke yi. Littafin Matta 5:32. Wannan rashin daidaituwar abin da ya dace shine, rashin nunawa ko karba ba tare da wata shakka ba. A kan ji wani halin kirki cikkake ne, da al'ummomin 'yan-Adam ba su taba samu ba. A lokacin da mutum da matarsa su ka gane gaskiyar cewa, rayuwar aurensu ta gagari gyara, haramta saki ba zai masu kyau ba. Tilasta mugun abokan zamar mutum da matarsa, ci gaba da zama tare, ba da son ransu ba, ba ta da ko karfi, ko dama dama. Ba mamaki ba ne, dukan duniya Kirista an tilasta ta da ba da iznin saki. Yahudanci, a wata fuska, ya kan yarda da aiwatar da saki koda kuwa babu dalili. Littafin Tsohon Alkawari ya kan bai wa mijin ikon sakin matarsa, koda ya ki jininta ne, kamar haka: Kadan mutum ya dauki mache ya yi amre da ita, ya kwa zama ba ta da tagomashi a idonsa, domin ya iske wani abin da ba daidai ba a gareta, sai ya rubuta mata takardar saki, shi bata chikin hannunta, shi sallameta daga gidansa. Sa'anda ta fita daga gidansa kuma, in ta so, ta tafi ta zama matar wani mutum. Idan mijin na baya kuma ya ki ta, ya rubuta mata takardar saki, ya bata chikin hannunta, ya sallameta daga gidansa; ko kwa
idan mijin na baya ya mutu, wanda ya dauketa ta zama matatasa; mijin nan nata na fari bashi da iko ya dauketa ta zama matatasa; bayan da ta kazamtu; gama wannan abin kyama ne a wurin Ubangiji: ba kwa za ka sa kasa ta yi zunubi, wanda Ubangiji Allahnka ya ba ka gado ba. Littafin Kubawar Shari'a 24:1 4. Ayoyin da suka gabata sun kawo wasu babbar jayayya a tsakanin maluman Yahudawa, saboda sabaninsu a kan fassarar kalmomin rashin tagomashi da kyama da kuma ki wadanda aka ambata a cikin ayoyin da suka gabata. A kan rubuta raayoyinsu dabam dabam a Talmud (littafin Yahudawa) kamar haka: Mazhabar Shammai tana ganin cewa, bai kamata mutum ya saki matar sa ba, har sai ya same ta da laifukan da suka shafi zina, yayin da mazhabar Hillel ke ganin cewa, ya samu ya sake ta, koda kuwa ta bata masa wani abinci ne da ta dafa da ba ya so. Liman Akiba kuwa cewa ya yi: Ya samu ya sake ta a lokacin da ya ga wata wadda ta fi ta kyau. Gittin 90a-b. Littafin Sabon Alkawari ya kan bin ra'ayin mazhabar Shammai ne, sai dokar Yahudawa ta bi raayin Hillelites da na Liman R. Akiba. Tunda ra'ayin mazhabar Hillelites ce ta rinjaya, ya kasance hanyar dokar aladar Yahudawa wadda ba ta tsinke ba, a bai wa mijin yancin sakin matarsa, ba tare da ta yi masa wani laifi ba. Shi kuwa Littafin Tsohon Alkawari, ba wai kawai ya bai wa mijin ikon sakin matarsa mara tagomashi ba ne, yana dubar sakin wata mumunar mace wani takalifi ne, inda yace: Mumunar mache na kawo kaskanchi, kallon dukuku, da chiwon zuchiya. Sanyin hanu da runin gwiwa sun tabbata ga mutumen da matarsa ta kasa franta masa rai. Mache che asalin zunubi, sa'annan sabili da ita ne dukanmu za mu mutu. Kada ka bari hujajjen tulu ya zudda ruwa, ko kwa mugunyar mache ta fadi dukan abin da ta ke so. Idan kulawarka bai gamsheta ba, to ka saketa kana ka koreta. Ecclesiasticus 25:25. Matar aure da suka tilasta wa mazajennsu da su sakesu an rubuto wadansu kayyadaddun aiyyuka a cikin Talmud (littafin Yahudawa) kamar haka: Cin abinci a kan hanya, shan abin sha da yawa a kan hanya, shayar da jariri a kan hanya, idan ta aikata kowanne daga cikin wadannan laifuka, Liman Meir ya ce, dole ne, ta rabu da mijin ta . Git. 89a. Talmud (littafin Yahudawa) ya sake wajabta sakin bakarariyar mace (wadda ta kai shekaru goma ba tare da ta haihu ba), inda ya ce: Limamin mu na ganin cewa, idan mutum ya auri mace, kuma ya zauna da ita har shekaru goma ba tare da ta Haifa masa da ba, to ya sake ta. Yeb 64a. Matan aure, a gefe guda, ba su iya soma saki a karkshin dokar Yahudanci, Amma dai, matar aure Bayahudiya, tana iya nemar hakki don saki daga wurin mijinta a gaban kotun Yahudawa, da sharadin cewa akwai wani dalili mai karfi da kan kasance. Wani filin raayoyi yan kadan ne, aka yi tanadinsu wa matar auren ta nemi hakkin wani saki. Wannan filin raayoyi su kan hada da: Wani miji dauke da nakasassun jiki, ko cutar fatar jiki, da wani miji da bai iya biya wa matarsa bukata na shaain maamular maza da mata, da dai sauransu. Kotun kan daure wa matar gindin nemar hakkin wani saki, amma ba zai iya raba (kasha) auren ba. Mijin kawai ne zai iya kashe auren, ta hanyar bai wa matar takardar saki. Kotun na iya masa bulala, da cin sa tara, da sa shi kurkuku, da kuma yi masa azabar kora da bayyana cewa, ba zai taba zama cikin kungiyar mutane cocin Kirista ba, don a tilasta shi ya ba da takardar saki na tilas ga matarsa. Amma dai, idan mijin mai tsaurin kai issashe ne, yana iya kin bayar da sakin matarsa, kuma ya ajiye ta a daure, ya ci
gaba da zama da ita mara iyaka (da babu tabbataccen lokaci). Mafi muni duk da haka, yana iya yin kaura daga gare ta, ba tare da ba ta wani saki, kuma ya bar ta babu aure kuma babu saki. Yana iya auren wata mace kuma, ko ma ya zauna tare da mace wadda ba ta da aure, da ba su daura aure ba, kuma ya samu 'ya'ya daga gare ta (wadannan 'ya'yan, a karkashin dokar Yahudanci, ana dubarsu yan halali ne). A gefe guda kuma, yashasheyar matar auren, ba ta iya auren wani mutum dabam, tunda dai har yanzu tana karkashin dokar igiyar aure ne, kuma ba ta iya zama da wani mutum dabam, saboda za a dube ta wata mazinaciya, kuma 'ya'yan ta da ta samu a irin wannan hadaddin zaman, za su zama shegu har na zamunna goma. Macen da ta samu kanta a cikin irin wannan hali, ana kiranta Aguna (macen da aka turke). A yau a kasar Amurka akwai turkakkun mata Yahudawa wadanda ake kiransu Agunot a Turance (wato jumlar Aguna) wajen 1000 zuwa 1500, yayin da kuma watakila yawansu ya kai 16000 a kasan Israel (Israila). Mazaje mai yiwuya su karbi dubannin dololi daga matan aurensu na yaudara (dake cikin tarko) a musayar wani sakin Yahudanci. Musulunci ya kan bayar da tsarin raayoyi, hukunce-hukunce tsakanin Yahudanci da Nasaranci dake kin goyin bayan juna game da saki. A Musulunci, aure wani tsarkakakken kulli ne, wanda ba a warware shi face da dalilai masu tilastarwa. An umurci mutum da matarsa da su bi duk wasu hanyoyin masu yiwuwar magance matsalalolin aure, duk inda aurensu ya fada a cikin hadari. Ba za a koma ga saki ba, sai fa idan an rasa samun wata kofar fita. A takaice, Musulunci ya kan yarda da saki, amma yana nema a hana yin shi, ta kowane hali. Bari mu saurari fitarwar farkon bangaren. Musulunci yana yarda da hakkin dukan abokan tarayya (miji da matarsa) da su kawo karshen dangantakar aurensu, Musulunci yana bai wa mijin hakkin yin Talaq (saki). Kuma, Musulunci, wanda bai yi kama da Yahudanci ba, ya kan bai wa mace hakkin kashe aure, ta hanyar abin da aka sani da suna Khul'i. Idan mijin ya kashe auren ta hanyar sakin matarsa, bai iya dauko abu daga cikin kyautukan auren da ya yi ga matarsa. Alkur'ani a bayyane yana hana wa maza masu sakin matarsu, karbar kyautukan aurensu, ko yaya shaanin tsadar, ko darajar wadannan kyautukan suka kasance, inda ya ce: Kuma idan kun yi nufin musanya mata a matsayin wata mata, alhali kuwa kun bai wa dayarsu kindari to kada ku karbi kome daga gare, shi, shin, zaku karbe shi da karya da zunubi bayyananne? Nisa: 20. A halin da matar auren ke zaben kashe aurenta mai yiwuya ne, ta mayar da kyautukan aurenta zuwa ga mijinta. A irin wannan hali, mayar da kyautar aure shine, arashi mai adalci ga mijin wanda ke son matarsa a yayin da ta zabi barinsa. Alkur'ani ya umurci maza Musulmi da cewa, kada su karbi kyautukan da suka yi ga matansu, sai fa a halin da matar auren ke zabin kashe auren da kan ta, ya ce: Saki sau biyu yake, sai a rika da alheri, ko kuwa a sallama bisa kyautatawa. Kuma ba ya halatta a gare ku maza ku karbe wani abu daga abin da kuka basu, face fa idan su ma'auran na tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba. Idan ku (danginsu) kun ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to, babu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Wadancan iyakokin Allah ne, saboda haka kada ku ketare su. Kuma wanda ya qetare iyakokin Allah, to wadannan su ne azzalumai. Baqarah: 229. Kuma ya zo a cikin Hadisi cewa, wata mace ta zo wajen Anabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) tana neman kashewar aurenta, ta fada wa Annabi cewa, ba ta da kararakin halin mijinta, ko ladabinsa. Alamarinta mai wuya kawai
ya kasance ne, a gaskiya ba ta kaunarsa, yawancin da ba za ta iya zama tare da shi ba. Sai Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya tambaye ta da cewa: Shin za ki iya mayar masa da lambunsa (wato kyautar auren da ya ba ki)?" Sai ta ce, Naam, za ta iya mayar masa. Daga nan sai Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) ya umurci mutumin da ya karbi lambun sa, kuma ya amince da kashewar auren. Bukhari ya ruwaito. A wasu halayen, akan samu wata matar aure Musulma dake yarda da ci gaba da zaman aurenta, amma ta dai samu kanta tilas ta nemi saki, saboda wasu dalilai masu tilastawa kamar: Taskun (ketar) mijin, kauracewa ba tare da wani dalili ba, wani miji da bai cika takalifin shaanin maamalar maza da mata a wurin saduwa, da dai sauransu. A irin wadannan halaye, kotun Musulunci kan kashe auren. A takaice, Musulunci ya mika wa mace Musulma wasu hakkoki da suka fi wadansu addinai sune: tana iya kashe auren ta hanyar (Khul'i), ko ta hanya kai karar mijinta wagen sharia. Matar aure Musulma, ba za ta taba zama cikin kangin (sarkar) kangararren miji ba. Wadanan hakkoki ne suka rinjaya akan mata Yahudawa, wadanda suka zauna a tsakiyar al'ummomin Musulmai na farko, a karni na bakwai C.E. [(lissafin shekaru daga haihuwar Annabi Isa (A.S)], da su nemi su samu takardar saki daga mazajensu Yahudawa a kotunan Musulumi. Limaman Yahudawa, sun ce wadannan takardu ba su da wani amfani. Domin kawo karshen wannan aikin, sai Limaman Yahudawa suka bayar da wasu sabobin hakkoki da wasu gatanci ga matan Yahudawa, a yunkurin rage wa karfin daukaka kara zuwa ga kotunan Musulumi. Ba a mika wa matan Yahudawa da ke zaune a Kasashen Kiristoci gatanci kamar wannan ba tunda dokar sakin Kasar Roman (Rum), da aka yi aiki da ita can ba ta kasance tana jawo hankali fiye da na dokar Yahudawa. Bari kuma yanzu mu saurari yadda Musulunci ya kan nemi a hana saki. Ya zo a cikin Hadisi cewa, Annabin Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya sanar da muminai cewa: Daga cikin dukan halattattun ayyuka, saki shine, wanda Allah Ya fi ki. (Abu Dawud ya ruwaito). Kada wani mutu Musulmi ya saki matarsa don kawai ya kan kita. Alkur'ani ya umurci maza Musulmi da cewa, su kyautata wa matan auren su, koda a cikin halayen abubuwan da ake jin ba a so sosai ne, ko ana jin rashin son su ne, inda ya ce: Ya ku wadanda suka yi mani! Ba ya halatta a gare ku, ku gaji mata a kan tlas kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka ba su, face idan suka zo da wata alfasha bayyananniya kuma ku yi zamantakewa da su da alheri sa'an nan idan kun k su, to akwai tsammanin ku ki wani abu alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa Nisa: 19. Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi).) ya yi umurni da kamar wannan, a cikin Hadisi, inda ya ce: Mumini namiji lalle kada su ki mumina mace. Idan ya ki wani daga cikin halayenta, zai so wani daga ciki. (Musulim ya ruwaito). Kuma, Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya yi nauyin lafazi da cewa, Musulman da suka fi kowa su ne, wadanda suka fi kowa kyautata wa matansu, kuma Mumunai wadanda suka fi kowa cikakken imani sune, wadanda suka fi kowa halin kirki, kuma wadanda suka fi dukan ku sune masu kyautata wa matarsu. (Tirmidhi ya ruwaito). Amma dai, Musulunci, Addini ne, na aiki kuma yana shaida cewa, akwai halayen shaanin da wani aure zai zama kusan kasa gaba daya. A irin wannan halaye, wata shawarar alheri kawai, ko kamewar kai, ba shine zai zama bayani, ko warwarewar
matsalar auren da zai ci nasara ba. Don haka, mene ne za a yi domin a ceto wani aure a irin wannan halaye? Alkur'ani ya bayar da wasu shawarwari yin aiki dasu ga abokin aure, ko abokiyar aure (miji ko matar aure), wanda abokin tarayya (miji), ko wadda abokiyar tarayya (matar aure) mai laifi ne, ko mai laifi ce. Alkur'ani yana bayar da shawarwari iri hudu filla-filla ga mijin wanda yake tsoron bijirewar matar aurensa inda ya ce: Kuma wadanda kuke tsoron bijirewarsu, (1) To, ku yi musu gargadi, (2) Kuma ku kaurace musu a cikin wuraren kwanciya, (3) Kuma ku dke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku xa'a, to, kada ku nemi wata hanya a kansu. Lalle ne Allah Ya kasance Madaukaki, Mai girma. (4) Kuma idan kun ji tsoron sabawar tsakaninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta. Idan sun yi nufin gyarawa, Allah zai daidaita tsakaninsu ma'auran. Lalle ne Allah Ya kasance Masani Mai jarrabawa Nisa: 34 -35. A fara gwada matakai uku na farko da aka ambata. Idan ba su yi nasara ba, sai iyalan ko dangin miji da mata su shigo domin sasantawa. Sai a lura da hasken da ayoyin da suka gabata suka bayar cewa, dukar matar aure mai yin tawaye, wani mataki ne, wanda ba mai karko ba ne, da aka koma gare shi a matsayi na uku a layin a cikin matsanancin halayen larura, wadda ake sa rai cewa mai yiwuwa ne zai magance laifin matar auren. Idan hakan ya ci nasara, ba a yarda wa mijin ko ta wace hanya ba ya ci gaba da yin fushi da matar auren kamar yadda ayar ta ambata a bayyane. Idan kuwa ba ta ci nasara ba, har yanzu ba a yarda wa mijin amfani da wannan mataki ba, kuma wani zabi ko wata hanyar ci gaba gama da nemar taimakon dangi ga yin sulhu ya kamata a bincika. Ya zo a cikin Hadisi cewa, Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya umurci mazaje Musulmi da cewa, kada su koma ga nuna wadannan nufi (bara), sai a matsanancin halaye, kamar samun mace da laifin fasikanci (wanda ba ta zina ba). A irin wadannan halaye ma, horon mai laifin ya zama karami (mara tsanani), kuma idan matar auren ta daina, ba a yarda wa mijin ya hasalar da ita ba musamman saboda laifin da take ci gaba da yi. inda ya ce: Idan ka same su da laifin fasikanci, ka na iya kaurace musu a wurin kwanciya, sannan ka ladabtar da su, (ladabtarwa mara tsanani). Idan su ka yi maka biyayya, to kada ka yi fushi da su. (Tirmidhi ya ruwaito). Dadin dadawa, Annabin Muhammad (Tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi) ya ce duka da za a yi saboda ba shi da dalili mai kyau ba kyau. Wasu daga cikin matan aure Musulmi sun kai karar mazajensu a gare shi cewa sun dukesu. Da jin haka, sai Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.) ya tabbatar da cewa: Duk wadanda suka aikata haka (suka bugi matansu) ba su zama mafifita a cikin ku ba. (Abu Dawud ya ruwaito). A wannan wuri sai a tuna cewa, Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi).) ya kuma ce: Mafifici a cikin ku shi ne wanda ya fi kowa kyautata wa iyalinsa, kuma ni fiyayye ne a cikin ku a wurin iyali na. (Tirmidhi ya ruwaito). Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.) ya yi nasiha ga wata mace Musulma, wadda ake kira Fatimah diyar Qais cewa, kada ta auri mutumin da ya yi fice wajen dukar mata, kamar haka: Na tafi zuwa ga Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) na ce: Mu'awiyyah da Abul Jahm sun nuna bukatar auren su gare ni. A nasihance, sai Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya ce da ni: Dangane da Mu'awiyyah, shi talaka ne, shi kuwa Abul Jahm an san shi wajen dukar mata. (Muslim ya ruwaito).
A lura da cewa, Talmud (littafin Yahudawa) ya kan ba da izinin dukar matar aure domin horo ga halin yin horo. Mijin ba a takura masa ba, a wasu matsanancin halaye kamar wadancan fasikanci (wadanda ba zina ba). An yarda masa da ya duki matar aurensa, koda kuwa ta kan ki yin aikin gidanta ne. Kuma, ba a iyakace masa amfanin da horon mai laifi da sauki kawai ba (mara tsanani). An ba shi iznin ga kawo karshen taurin kai matar aurensa, ta hanyar tsula mata bulala ko hanata abinci. Ga matar auren da bijirewan mijinta shine, yin sanadin kusan mutuwar auren, Alkur'ani yana nuna nasiha dake biye kamar haka: Kuma idan wata mace ta ji tsoron kiyo daga mijinta ko kuwa bijirewa to, babu laifi a kansu, su yi sulhu a tsakaninsu, sulhu mai kyau. Kuma yin sulhu ne mafi alheri. Kuma an halartar wa rayka yin rowa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi takawa, to, lalle ne, Allah Ya kasance, ga abin da kuke aikatawa, Masani Nisa: 128. A irin wannan hali, ana neman matar da ta nemi sasantawa da mijinta (tare da, ko ba tare da taimakon danginta ba). Ya isa a gane cewa, Alkur'ani ba yana nasiha ga matar auren komawa ga matakai guda biyu nan ba ne, na rashin yin saduwa da (ita) da kuma duka. Dalilin wannan sanya wani rasa sa rai (dokanta), mai yiwuwa ne, ya kare matar auren daga cutarwa ko kissa daga mummunar martanin da ya rigaya na rashin nuna halin kirkin mijinta. Irin wannan cutarwa ko kissa zai yi wa matar auren lahani masu yawa fiye da amfani. Wasu malamai Musulmi sun dauki raayin cewa, kotu tana iya nemar wadannan bara a kan mijin a maimakon matar auren. Wanda da farko koto kan yi wa mijin mai tawaye gargadi, sannan ya kan haramta masa kwanciya akan gadon matarsa, daga bisani kan zartadda da wata sananniyar duka. A takaice dai, Musulunci ya kan bai wa mutun da matarsa shawarwari da zasu kai ga cin nasara da yawa don su tsirad da aurensu a cikin halayen wahala da dauren kai. Idan daya daga cikinsu abokan (zamar auren) na kasadar yin barna, ko hallaka dangantakar auren, Alkurani ya yi gargadi ga dayar abokin da ya yi duk abin da zai iya yi da karfi domin tsirad da wannan aure da aka daura mai tsarki. Idan aka bi dukan hanyoyi da matakan da suka kamata a bi, amma aka kasa samun nasara, to Musulunci kan yi umurni da a rabu cikin kwanciyar rai da tsakanin abokantaka (lumana).
BABI NA 12
Uwaye Mata
Littafin Tsohon Alkawari a wadansu wurare da dama, ya kan yi umurni da kyautatawa da yin tunanin kula koyaushe da iyaye, kuma ya kan tabbatad da laifin wadanda ke yi musu rashin mutunci. Misali: "Gama dukan wanda ya la'antadda ubansa ko kwa uwatasa,
hakikan za a kashe shi: ya la'antadda ubansa ko kwa uwatasa alhakin jininsa yana bisa kans," Littafin Laviticus 20 :9, da Da mai-hikima ya kan faranta zuciyar ubansa: Amma wannan mutum ya kan rena uwatasa. Littafin Misalai 15:20. Koda yake, girmama uba shi kadai ne, aka ambata a wasu wurare kamar yadda yazo: Da mai-hikima ya kan karbi koyaswar ubansa. Littafin Misalai 13:1, faufau ba a ambata uwar ita kadai ba uwar ita kadai ba. Kuma, babu wani nauyin lafazi na musamman a kan yi wa uwar abin alheri sakamakon wata alamar ji dadin babbar shan wahalanta na ba da nono ga yaya da tarbiyyantarwa. Baya wannan, uwaye mata sam ba su gadon 'ya'yansu, yayin da ubanni ke gadon dukiyar 'ya'yansu. Zai yi wuya a yi maganar littafin Sabon Alkawari kamar wani littafi ne, da kan yi kira zuwa ga girmama uwa. Sabanin haka, mutum kan ji cewa Littafin Sabon Alkawari kan duba kyautata wa uwaye mata a matsayin wani abin hani ne daga hanyar Allah. Bisa maganar Littafin Sabon Alkawari mutum ba ya kan zama wani cikakken Kirista da ya inganta ya zama wani sahabbin (mai bin) Annabi Isa (A.S.) sai idan ya ki jinin uwarsa. An ruwaito Annabi Isa (A.S.) na cewa: Idan kowa ya zo wurin, ba ya ki ubansa ba, da uwatasa, da matatasa, da yayanasa, da yan-uwansa, maza da mata, I, har da ransa kuma, ba shi da iko shi zama mai-bina ba. Littafin Luka 14:26. Dadin dadawa, Littafin Sabon Alkawarin, ya kan siffanta hoton Annabi Isa (A.S.) da kamanin mai nuna rashin ruwansa da mahaifiyarsa, ko ma mara ladabi. Misali, yayin da ta zo ta na nemansa a lokacin da ya ke yin wa'azi ga wasu taron mutane, ya ki kula ya fita ya ganta, kamar haka: Ananan uwatasa da yan-uawansa suka zo; suka aike a wurinsa, suna kiransa, suna tsaye daga waje. Taron kwa suna kewaye da shi a zamne; suka che masa, Gashi, uwarka da yan-uwanka suna waje suna nemanka. Ya amsa musu ya che, wache che uwata da yan-uwana? Sa'anda ya dudduba wadanda suna kewaye da shi a zamne ya che, Ga uwata da yan-uwana! Gama iyakar wanda za ya aika nufin Allah shi ne xan-uwana, da yar-uwata, da uwata. Littafin Markus 3:31 35. Wani mutum mai yiwuwa ya yi jayaya cewa Annabi Isa (A.S.) ya na kokarin karantar da masu sauraronsa wani muhimmin darasi ne, da cewa dangantaka ta addini tafi dangantaka ta jinni. Amma dai, da ya karantar da masu sauraronsa daidai darasin, ba tare da ya nuna rashin ruwansa da mahaifiyarsa sosai ba. An bayyana irin wannan halin rashin ladabi a lokacin da ya ki amincewa da furucin da daya daga cikin masu saurarensa ya yi dake sanya wa mahaifiyarsa albarka sakamakon dawainiyar da ta sha da shi na haihuwa da shayarwa, kamar haka: Ananan, yana chikin fadin wadannan abu, sai wata mache daga chikin taron ta tada muryatta, ta che masa, chikin da ya haifeka mai-albarka ne, da kuma maman da ka sha. Amma ya che, Gwamma dai su wadannan da suna jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma. Littafin Luka 11:27 28. Idan wata uwa mai muhimmanci da girmamawa irin na Nana Maryam dake da shi, saboda iyawarta da aiki wanda ya isa yabo wani da mai muhimmanci da girmamawa irin na Anabi Isa (A.S) dake da shi, saboda iyawarsa da aiki wanda ya isa yabo ya yi mata irin wannan rashin mutunci kamar yanda aka nuna hotonta a cikin Litafin Sabon Alkawari to, yaya ke nan mu'amalar matsakaicin 'ya'yan Kirista da uwayensu zata kasance? A Musulunci, daraja, girma, da girma da aziki, dake hadi da uwartaka ba daura da juna suke ba. Alkur'ani ya kan nuna irin muhimmancin da alheri (kyautata) wa iyaye a matsayin na biyu kawai ga bautar Allah Madaukakin Sarki. Kamar haka:
Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kowa face Shi, kuma game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai dayansu ya kai ga tsifa, a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu tir kuma kada ka tsawace su, kuma ka fada musu magana mai karimci. Isra: 23-24. Alkurani a wadansu wurare da dama ya kan nuna babbar dawainiyar uwa na haihuwa da shayarwa na musamman, kamar haka: Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa ta dauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu Muka ce masa "Ka gode Mini da kuma mahaifanka biyu. Makoma zuwa gare Ni kawai take. Luqman: 14. Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) ya bayyana matsayin uwaye mata na musamman da kaifin harshe inda ya ce: Wani mutum ya tambayi Annabi (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.) cewa, a tsakanin iyaye na guda biyu, wa zan fi kyautatwa? Sai Annabi ya amsa masa da cewa: mahaifiyarka. Sai mutumin ya ce, sai wa? Sai Annabi ya ce: mahaifiyarka. Sai ya sake cewa, sai wa? Sai Annabi ya ce masa: mahaifinka. (Bukhari da Muslim suka ruwaito). Tsakanin wadansu dokoki wadanda zasu nuna halin kirkin Musulunci, wadanda har yanzu Musulmi na ci gaba da kiyayesu, sune kyautata wa uwaye mata. Daraja da uwaye mata Musulmi ke samu daga 'ya'yansu maza da mata ya isa abin misali. Danuwantaka da yawa da suke gudana tsakanin uwaye mata Musulmi da 'ya'yansu, da kuma cikakkiyar girma da mazaje Musulmi ke ba wa uwayensu mata, a kullum yana sa mutanen Yammacin Kasar Turai yin mamaki.
BABI NA 13
Gadon Mata
Daya daga cikin muhimman bambance-bambancen da suka fi duka tsakanin Alkur'ani da Bible shine, raayinsu game da yadda mace za ta gaji dukiyar dangin da ya mutu ya bari. Limamin Yahudawa Epstein ya bayyana raayin Bible sosai a cikin wadansu kalmomi inda ya ce: "Tun kwanukan da ake rubuta Bible al'adar mai ci gaba da ba a sabawa ba ta kan hana mata iyayen gida, matar aure, da diya mata, hakkin gadon iyali ko dangi. A cikin fifikon shirin gajewar gado da aka zana wanda ba a inganta hanyar yinsa ba, mata a cikin iyali, ana dubarsu a matsayin wani yankin dukiyar gado ne. Kuma a matsayin masu nisanta daga magada da kansu na biye da doka, kamar dai baiwar da aka mallaka ce. Yayin da kuma dokar da aka tattaro kadan kadan a wuri daya ta maaikatar hukuma ta yarda da gajewar gado diya mata, idan dai babu rabon namiji da ya yi saura, kuma a irin wannan halaye, ba a yarda da matar aure ta zama mai yin gado ba." Don me ake
dubarsu mata iyayen gida ake dubarsu wani yankin gadon iyali? Liman Esptein ya na da amsar wannan tambayar, inda ya ce: "Saboda tun kafin su yi aure, mallakar mahaifinsu ne, sannan bayan sun yi aure mallakar mijinsu ne. Dokokin gado dake cikin Bible an zana sune a cikin Littafin Lissafi 27:1 11 don bayani. Wata matar aure ana hanata gadon mijinta, yayin da kuma shi ne farkon mai gadonta, kafin ma a zo kan 'ya'yanta. Wata diya mace kan yi gado kawai ne idan ya kasance babu magada maza. Uwa kuwa, ba za taba yin gado ba, yayin da uba kuwa na yin gado. Mata masu takaba (wadanda mazajensu suka mutu) da diya mata, idan akwai 'ya'ya maza da suka saura, su kan yi gadon kayayyakin masarufi a karkashin tausayi (jinkan) magada maza. Wannan shi ya sa matan da mazajensu suka mutu da yan mata marayu, cikin matsiyata fiye da duk mutanen al'ummar Yahudawa. Addinin Kirista ya bi ya dace da (Addinin Yahudanci) da dadewa. Duk Ikilisiya da na sharia ta tsakanin mutum da mutum sun hana diya mata daga yin rabo da 'yan'uwansu maza cikin gadon dukiyar da mahaifinsu ya mutu ya bari. Bayan wannan, matan aure an hana masu hakkokin yin gado. Wadannan dokokin mara adalci sosai sun rigaya ci gaba da kasancewa har zuwa karnin baya-bayan nan. Gabanin zuwan Musulunci, cikin Kafuran Larabawa, hakkokin yin gado an iyakance sune ga dangunar maza ba ya cudanya. Alkur'ani ya zo ya yi watsi da irin wannan al'adu marasa adalci tare da bai wa dangin mata nasu kason na gado, inda ya ce: Maza suna da rabo daga abin da iyaye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mata suna da rabo daga abin da iyaye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya karanta daga gare shi ko kuwa ya yi yawa, rabo yankakke. Nisa: 7. Tun shekaru dubu daya da dari uku (1300), iyaye mata, matan aure, da diya mata, suka sami hakkokin yin gado, kafin Turai su shaida cewa wannan irin hakkokin sun kasance. Rabon gado babban wani katon fanni na ilmi ne, tare da jimloli masu yawa filla-filla kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani Surar Nisa: 7, 11, 12, 176. Doka na kowa ita ce, rabon gadon mace shine, rabin na namiji, face a halayen da uwa kan karbi rabo dai-dai da na uba. Wannan doka na kowa idan aka wareta daga wadansu dokoki batun maza da mata na iya zama wanda ba na adalci ba ne. Domin fahimtar dalilai wadanda ke bayyana hukunci bayan wannan doka, dole ne mutum ya yi batun wadansu halayen shaani cewa, takalifi na kudin maza a Musulunci, ya dara wanda ke kan mata sosai, (duba yankin 'Dukiyar Matar Aure'). Dole ne ango ya yi tanadin kyautar aure ga amaryarsa. Wannan kyautar kan zama dukiyarta ita kadai ce, kuma kan ci gaba a wannan hali, koda kuwa daga bisani auren ya mutu ne. Amaryar ba ta karkashin wani takalifi da zata bayar da kyauta ga angonta. Kuma, miji Musulmi ke lura da kudin abincin mata da 'ya'ya. A gefe guda kuma, ba tilas ba ne matar auren ta agaza masa bisa ga wannan takalifi. Dukiyata da ladar aikinta na amfaninta ne, ita kadai, sai fa abin da ta bai wa mijinta da yardar ranta. Bayan wannan, ya kamata mutum ya ankara da cewa, Musulunci ya kan harshashen ba da shawarar rayuwar iyali da karfi. Ya kan karfafa wa zukutar samarai da su yi aure, yana hana yin saki, kuma bai dauki rashin aure kamar wata nagarta ba. Saboda haka, a cikin alummar Musulmi ta gaskiya, rayuwar iyali wani halin kirki ne da ake tsammani, kuma rashin aure togiya ce wadda ba safai ba ake sonta. Wato, kusan dukan balagaggun maza da mata, za ka samu sun yi aure a al'ummar Musulmi ne. Domin karin haske game da wannan batu, mutum zai ji dadin cewa, dukan Musulmi maza, suna da babbar nauyin na
kudi fiye da ta Musulmi mata, don haka, aka saukar da hukumce-hukumcen gadon da zai dai-daita wannan rashin dai-daitawa, domin al'umma ta tsarkaku daga rigingimun jinsi ko na dukan fanni. Bayan kwatanci mai sauki tsakanin dawainiyar hakkokin kudi da na hidimomin mata Musulmi, wata mace Musulma mutuniyar Ingila ta tabbatar da cewa, Musulunci ba wai kawai ya yi adalci ga mata ba ne, ya ma kyautata tare da karramasu.
BABI NA 14
mazajensu suka mutu kudi don rufa masu asiri (wato ci da ceto) domin su samo iyancinsu. Kafin zuwan Musulunci, kafuran Larabawa, suna da irin wadannan aladu. A wancan zamanin, mace ana dubarta wani yanki ne, na dukiyar mijinta, kuma ta kasance a galibi, ana aurar da ita ga babban dan mijinta, wanda ya haifa tare da kishiyarta. Alkur'ani ya yi soka yaki da kawar da irin wannan mummunar dabi'a, kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani: Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mata, face abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfasha da abin kyama. Kuma ya mnana ya zama hanya. Nisa: 22. A hanyar aladar Bible mata wadanda mazajensu suka mutu da matan da suka rabu da mazajensu ta hanyar saki, an kaskantar dasu da babban Fada ba zai iya auren wata mace wadda mijinta ya mutu ba, ko wata sakakka, ko wata karuwa ba, kamar yadda ya zo a cikin Bible: Za ya dauki mache daga chikin budurchinta ta zama matatasa. Gwamruwa ko sakakkiya, ko batacchiya, ko karuwa, wadannan ba za ya daukesu ba; amma budurwa daga chikin iri nasa za ya dauketa ta zama matatasa. Ba za ya tozartad da zuriyassa a chikin jama'assa ba; gama ni ne Ubangiji wanda ke tsarkake shi. Littafin Levitucus 21:13 15. A yau a kasar Isra'ila, zuriyar Cohen caste [babban Fada Fada na Coci na zamanin Haikali (Dakin Ibada)] ba za su iya auren wata sakakkar mace ba, da wadda mijinta ya mutu, ko wata karuwa. A dokar Yahudawa, wata mace da ta yi takaba har sau uku, ta hanyar mutuwar dukkan mazajenta guda uku da mutuwarsu ta Allah ne, ana dubarta mai sa mutuwa kuma an haramta mata yin wani auren. A gefe guda kuma, Alkur'ani ba ya shaidar Castes [babban Fada Fada na Coci na zamanin Haikali (Dakin Ibada)], ko mutane masu sa mutuwa. Mata wadanda mazajensu suka mutu ko sakakku, suna da yancin auren duk wanda suke so. A cikin Alkur'ani, babu kin goyin baya da mutane ke dauke da shi game da wani ciwo, ko wata hanyar halin cutarwa kamar yadda ya zo: Kuma idan kun saki mata, sa'an nan suka isa ga ajalinsu iddarsu, sai ku rike su da alheri ko ku sallame su da alheri, kuma kada ku rike su a kan ctarwa domin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haqqa, ya zalunci kansa. Kuma kada ku riki ayoyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littafi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kome Masani ne. Baqarah: 231. Kuma wadanda suke mutuwa daga gare ku suna barin matan aure, matan suna jinkiri da kansu wata hudu da kwana goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ada. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne. Baqarah: 234. Kuma wadanda suke mutuwa daga gare ku, alhali suna barin matan aure, wasiyya ga matan aurensu da dadadawa zuwa ga shekara guda babu fitarwa, to, idan sun fita to babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima . Baqarah: 240.
BABI NA 15
amma ba tare da wasu takurawa ba, inda yake cewa: Kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba a cikin marayu, to, akwai yadda za a yi ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata biyu-biyu, da uku-uku, da hudu-hudu. Sa'an nan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to, ku auri guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. Nisa: 3. Alkur'ani sabanin Bible ya kayyade mafi yawan adadin matan aure da za a iya aura, zuwa guda hudu karkashin hali mai tsanani na yin adalci da daidaita tsakanin matan. Kada a fahinta cewa Alkur'ani yana gargadin muminai da cewa su yi aure mata fiye da daya, ko cewa aladar auren mata fiye da daya ana dubar shi wani abu ne wanda ya dace. A wani kaulin kuma, Alkur'ani ya yarda Musulmi su yi auren mata fiye da daya wanda ba ku yarda da shi ba, ko ba ku so, kuma ba wata magana ba, amma saboda mene ne dalilin haka? Don me aka halatta yin auren mata fiye da daya? Amsar wannan tambaya mara wuya ce: Akwai wurare da lokutan da a cikinsu akwai wasu dalilai na zaman jamaa, da na halin kirki masu tilastawa na a yi auren mata fiye da daya. Kamar yadda ayar Alkurani da ta gabata ta kan nuna, batun aladar auren mata fiye da daya a Musulunci, ba zaa iya fahintarsa ba ban da yawancin takalifi zuwa ga marayu da mata wadanda mazajensu suka mutu. Musulunci, a matsayinsa na Addini na kowa da kowa, wanda ya dace da duk wurare da dukan lokuta ba zai yi biris da wadanna takali masu tilastarwa ba. A mafi yawan al'ummomi na yan-Adam, mata sun dara maza yawa. A kasar Amurka akwai, a kalla, mata miliyan takwas (8000000) fiye da maza. A kasa kamar Guinea, akwai mata dari da ashirin da biyu (122) ga kowane maza dari (100). A kasar Tanzania, akwai yawan maza tasain da biyar da digo daya (95.1) ga mata dari (100). Mene ne wata al'umma za ta yi wa irin wannan dangantaka dake tsakanin rukunin jinsin mutane biyu da bai daidai ta ba? Akwai wadansu hanyoyi dabam dabam da za a iya bi domin magance wannan, wasu za su dauki raayin tafarkin zuhudu (kin aure), wasu za su fi son kashe diya mata (abin da ke aukuwa a wasu al'ummomin duniya a yau!). Wasu kuwa za su yi tunanin cewa, hanyar da za ta zama mafita kawai ita ce, al'umma ta yarda da mutane su aikata dukan yardadden shaanin muamalar maza da mata (wato saduwa) wadda ba ku yarda da ita ba kamar su: karuwanci, saduwa da juna ba tare da an yi aure ba, luwadi, da dai sauransu. A wasu al'ummomin, kamar mafi yawan alummomin Afirka a yau, hanyar mafita da tafi girma ita ce, a halatta yin auren mata fiye da daya, a matsayin wani abin da aka yarda da shi na alada, da hanyar girmamawa na zaman jama da jamaa. Maganar da sau da yawa ake kasa fahintata a kasashen Turai ta Yamma ita cewa, mata a wasu al'adun, ba su dubar auren mata fiye da daya a matsayin wata alama ta kankantar da mata ba ne. Misali, yawancin kananan amaren kasashen Afirka, Musulmi ko Kirista, ko ba haka ba, sun fi son auren wani mutumin da ya riga hakikanta kansa zama wani miji mai daukar dawainiya. Yawancin matan aure a kasashen Afirka, kan iza mazajensu da su kara aure wata ta biyu, domin fita daga kangin kadaici a gida. Wani binkice da aka gudanar kan matan da yawansu ya haura dubu shida (6000), wadanda iyakar shekarunsu suke dabam dabam tsakanin 15 zuwa 59, wanda aka gudanar a birni na biyu wajen girma a kasar Nigeria, ya nuna cewa, kashi sittin cikin dari (60%) na wadannan mata sun fi jin dadin zaman aure idan mazajensu suka karo musu wata abokiyar zama (matar aure). Kashi ashirin da uku cikin dari (23%) ne kadai ke nuna rashin gamsuwa da jin-dadinsu idan mazajensu suka karo musu kishiya. Kashi saba'in da shida cikin dari (76%) ne daga cikin matan da aka yi bincike a kansu a kasar Kenya suka hango da ido na yakini aladar auren mace fiye da daya. (waton abin da ya dace suna sonsa). Binciken da aka gudanar a
karkarar kasar Kenya ya nuna cewa, mata 25 daga cikin 27 sun yi maraba da auren mata fiye da daya, suna ganin yin hakan ya fi auren mace daya tal. Wadannan mata sun ga cewa, aladar auren mata fiye da daya wani amfanin ne da jin dadi, matukar aka samu hadin-kai da fahintar juna a tsakaninsu da abokan zamansu. Aladar auren mata fiye da daya a mafi yawancin al'ummomin Afirka wata hanyar girmamawa ce da wasu coci-cocin darikar Protestant (Kirista daga cikin wadanda suka ki ikon Poparuma), ke zama wadanda su kan yarda da yinsa sosai da ba ku sonsa. Limami, Shugaban Majami'ar Coci na darikar Anglican (cocin dake da alaka da cocin Ingila) a Kenya ya furta da cewa, Duk da cewa auren mace daya na iya kasancewa hanyar nuna kauna tsakanin miji da matarsa, ya kamata coci su yi la'akari da cewa, a wasu al'adun sun rungumi auren mata fiye da daya hanu biyu-biyu na zaman jama da jama, kuma imanin da ake da shi cewa irin wannan auren ya saba wa addinin Kirista, yanzu kam ba raayi ba ne mai saukin da za a iya kareshi daga zargi. Bayan kulawar nazari kan irin yadda kasashen Afirka ke gudanar da auren mata fiye da daya, Reverend David Gitari na cocin darikar Anglican (coci dake da alaka da ta Ingila) ya tabbatar da cewa, aladar auren mata fiye da daya, wanda a ke yinsa ya fi dacewa, ya fi zama Kiristanci fiye da saki, kuma da sake (canja) yin aure, muddin aka yi la'akari da yasassun matan auren da 'ya'yan. Ni kaina, na san wasu matan aure 'yan Afirka, wadanda duk da kasancewar sun zauna a kasashen Turai ta Yamma na tsawon shekaru, basu da wani tsargin auren mata fiye da daya. Daya daga cikinsu, wadda ke zaune a kasar Amurka, ta kan yin muhimmin gargadi ne ga mijinta da ya auro mata ta biyu abokiyar zama, wadda za ta taimakata wajen kulawa da tarbiyar 'ya'ya. Matsalar dangantaka dake tsakanin rukunin mutane biyu na jinsin da bai daidaita ba, ya zama matsala da gaske a lokacin yaki. Amerikawa kabilu 'yan kasar Indiya, kan sha wahalar dangantaka dake taskanin rukunin mutane biyu na jinsin da bai daidaita ba, a bayan hasarorin da aka yi a lokacin yaki. Mata a wadannan kabilu, wadanda suka ji dadin wani matsayi mai kyau sosai, sun karbi auren mata fiye da daya a matsayin muhimmiyar kariya daga aukawa cikin ayyukan fasikanci. Mazauna Turawa, ba tare da gabatar da wani canji ba na dabam, sun tabbatad da laifin wannan aladar auren mata fiye da daya na Indiyawan a matsayin rashin wayewa. Bayan yakin duniya na biyu, akwai yawan mata million bakwai da dubu dari uku (7,300,000) fiye da maza a kasar Jamus, [wato miliyan uku da digo uku (3.3) na wadannan matan, wadanda mazajensu suka mutu ne]. Akwai maza dari (100) masu shekaru ashirin (20) zuwa talatin (30) ga Kowane mata 167, a cikin rukunin nan. Wadannan mata masu yawa, sun bukaci wani namiji, ba wai kawai a matsayin abokin zama ba, har ma a matsayin wani mai daukar dawainiyar mutanen gida a wani lokacin wuya da bakin ciki wadanda suka rigaya. Sojojin kawance wadanda suka ci nasara sun sami amfani da rashin karfi wadannan mata ta hanyar ji musu rauni da sauki. 'Yan-mata matasa masu yawa da mata wadanda mazajensu suka mutu su yi riko da wata dangantaka mai kyau tsakaninsu da sojojin mamaya. Sojojin Amurka da na Ingila masu yawa kan biya ladar bukatunsu da suka samu na amfani da wadannan matan ta hanyar basu taba sigari, cakuleti da burodi. Yara kan yi murna sosai da ganin kyautukan da wadannan bakin mutanen suka kawo. Wani yaro dan shekara goma (10) da ya ji labarin irin wadannan kayayyaki daga sauran yara, sai shi ma ya so gaba daya a ce mahaifiyarsa ta samu wani bature da zai rika kawo mata irin wadanan kyautuka, domin kada ta sake ji yunwa gaba. A nan wurin, ya kamata mu tambayi lamirinmu da cewa: Shin mene ne yafi karamci (halin girma) ga wata mace? Wata karbabbiyar abokiyar zama mai ladabi, macen aure da za a aura ta biyu, kamar yadda yake a idan Indiyawa suka dosa, ko wata karuwa,
kamar yadda yake a idan 'wayayyu' abokan juna suka dosa? A wani kaulin kuma, mene ne yafi karamci ga wata mace, abin da Alkurani ya umurta a rubuce, ko kuwa ilimin na karatun addin da wasu imani dake karkashin kasashen da ke cikin ikon Romawa? Zai jawo hankali a kula da cewa a taron matasan duniyan da aka gudanar a Munich ta kasar Jamus a shekarar 1948, an yi batun babbar matsalar dangantakar dake tsakanin rukunin jinsin mutane biyu da bai daidaita ba a kasar Jamus. Da ta bayyana cewa babu wani bayani ko warwarewar matsalar da aka yarda da ita, wasu sun dauki raayin aladar auren mata fiye da daya. Martanin farkon taron shine, wani hade haden motsi mai tsanani da wata kyama. Koda yake, bayan aiwatar da nazari da hankali kan gabatad da shawar, mahalarta taron sun yarda da cewa lallai ne, hakan shine bayani mai yiwuwa ko warwarewar matsalar. Don haka, a cikin takardar yabon taro ta karshe, ta hada da aladar auren mata fiye da daya. A yau, duniya ta kan mallakar makaman kare-dangi masu yawan da ba ta taba mallakarsu ba a baya, kuma coci-coci na Turawa, mai yiwuwa ne ko ba jima ko ba dade su tilasta karbar aladar auren mata fiye da daya a matsayin hanyar mafitar kawai. Fada Hillman ya yi tunanin yarda da wannan batun, inda ya ce: wata shawara da ta fado masa a rai shine, cewa wadannan dabarun kashe-kashen da ake amfani dasu na makaman karedangin (Nuclear, Biological, Chemical) za su haifar da rashin daidaita mai yawa tsakanin jinsin-jinsin da yawaita yin aure zai zama wata hanyar ta tilas na ci gaba da rayuwa Saannan sabanin al'ada da doka wadanda suka rigaya, wani muhimmanci na halitta da halin kirki kwarai fiye da wani abu mai yiwuwa ne ya tashi ya goyin bayan aladar auren mata fiye da daya. A irin wannan hali, masana ilimin addini da shugabannin coci za su yi gaggawan fito da dalilai masu karfi da matani (wato abin da ke cikin littafin) Bible domin yi wa sabon hazikanci ko imani game da aure hujjar kirki. Har wannan lokacin, aladar auren mata fiye da daya kan ci gaba da kasancewa bayani ko warwarewar matsala wadda za ta ci nassara ga wasu cutukan zamantakewar dake addabar al'ummomi na zamani. Wajibobi (talifi masu yawa) na jamaa da Alkurani ya kan ambata tare da yarda da auren mata fiye da daya, a yanzu an fi ganinsu a wasu al'ummomin kasashen Turai ta Yamma fiye da yadda ake ganinsu a kasashen Afirka. Misali, a yau a kasar Amurka, akwai wani hargitsi fannin jinsi mai tsanani a jama'ar bakaken mutane. Mutum daya daga cikin kowane mutane ashirin 20 na bakake maza mai yiwuwa ne, ya mutu kafin ya kai shekaru ashirin da daya (21). Ga wadancan dake tsakanin shekaru 20 da talatin da biyar 35 na haifuwa, kisan kai ne gaba-gaba na sanadiyyar mutuwarsu. Bayan wannan, bakake maza matasa masu yawa ba su da aikin yi, suna cikin kurkuku, ko sun sha mugun maganin mai kawad da hankali. Sakamakon haka, bakar mace daya daga cikin kowane hudu, mai shekaru arbain 40 ba ta taba yin aure ba, idan aka gwadata da daya daga cikin fararen mata goma (10). Kuma, bakaken mata matasa masu yawa kan haihu suna tuzurai (wato ba tare da sun yi aure ba) kafin su kai shekaru ashirin 20 da haihuwa, kuma su kan samu kansu cikin bukatar wadanda za su kula da su. Karshen sakamakon wadannan halayen da ake ciki masu ban tausayi shine, wani adadin mata bakake mai karuwa da yawa suna da hannu cikin abin da ake kira 'tarayya kan namiji guda'. Wato, za ka samu wadannan bakaken mata tuzurai mara saa suna kumshe a cikin alamurar mazajen da ke da aure. Sau da yawa Matan auren ba su san cewa, wadannan mata suna tarayya ga mazajensu tare da su ba. Wasu masu sanya ido
(masu duba) a kan hargitsin tarayya ga namiji guda a jama'ar Amerikawa 'yan asalin Afirka, suna kakkarfa yabo da aladar auren mata fiye da daya da mutane duka suka yarda da shi, a matsayin kayadadden amsa na karamcin maza bakake, har sai an samu wata cikakkiyar fahintar gyara da aka yarda a yi aiki da ita a fadin al'ummar Amurka. Abin nufi da aladar auren mata fiye da daya da mutane suka yarda da shi shine, suna nufin wata aladar auren mata fiye da daya da jamaa ta ba da izini ne, kuma wanda yake dukkan kungiyoyin da ya shafesu, sun yarda da yin kokarin hana tarayya ga namiji guda a boye, wadda take abar cuta ce ga dukan biyu: da matar auren da jama'a gaba daya. Matsalar ta tarayya ga namiji guda a cikin jama'ar Amerikawa 'yan asalin Afirka, ita ce batun shawarar wata jamaar mutanen da aka tattaunata a Jami'ar Temple dake Philadelphia ranar 27 ga watan Janairu, a shekarar 1993. Wasu masu maganar sun yaba da aladar auren mata fiye da daya a matsayin abin da zai iya magance hargitsin. Haka kuma, sun ba mahalarta taron shawarar da cewa kada doka ta hana aladar auren mata fiye da daya, musamman a al'ummar da ta kan yarda da yin karuwanci da kwartunci ga mutane wadanda ba sa sonsu. Fadin raayin daya daga cikin masu sauraron da cewa Amerikawa 'yan asalin Afirka sun bukaci su yi koyi da Afirka, inda aladar auren mata fiye da daya ake yinsa ta hanyar azanci dake nuna cewa amintacce ne, ya samu wani mayar da matani tafin hannu mai ban shaawa da kyar. Philip Kilbride, wani Ba'amurke mutumin da ya koyi ilimin zamantakewar kabilar yan Adam na cocin darikar Katolika ta aladar Romawa, a cikin littafinsa na tsokana, yana cewa: Auren mata da yawa a zamaninmu, kan gabatar da shawarar aladar auren mata fiye da daya a matsayin wani bayani ko warwarewar matsalar wadansu curutukar al'ummar Amurka masu yawa. Ya kan tabbatar da cewa, auren mata da yawa mai yiwuya ne zai iya zama canjin sakin aure a halaye masu yawa, domin a kawar da barnar tasiri nan mai karfi akan 'ya'ya masu yawa. Kuma ya kan kula da cewa, saki da yawa kan faru ne sakamakon alamurar aure fiye da kima, masu watsuwa koina ta hanyar da ba a iya kayyadesu a al'ummar Amurka. Bisa maganar Kilbride , kawo karashen shaanin yin aure fiye da kima zuwa ga yin auren mata fiye da daya, maimakon zuwa wani saki, shine mafi kyau ga 'ya'ya, Za a yi wa yaya hidima mafi kyau, idan aka kara yawan iyali, maimaikon saki kawai da kashewar aure an ganosu a matsayin wasu ganin dama. Kuma, ya kan ba wa mutane shawara da cewa wasu kungiyoyi za su amfana da auren mata da yawa kamar su: mata masu yawan shekaru wadanda suke fuskantar mugun karancin maza sosai da kuma Amurkawa 'yan asalin Afirka wadanda suke da hannu cikin tarayya ga namiji guda. A shekarar 1987, jaridar dalibai ta Jami'ar California dake Berkeley ta tafiyad da jefa wata kuria, ta tambayi daliban ko sun yarda da cewa doka ta yarde wa maza yin auren mata fiye da daya, a jawabin wata fahintar karancin yan takara auren maza a California. Kusan dukkan daliban da suka jefa kuri'ar sun yardar da ra'ayin. Wata daliba har ma ta bayyana cewa, yin auren mata fiye da daya zai cika mata abin da ta ke so da bukatun jikinta sai ya ba ta babban yanci fiye da wani hadadden auren mace daya. A kan gaskiya, Sauran matar Mormon kadan yan asali masu bin addini sau da kafa, wadanda suke yin auren mata fiye da daya har yanzu a Amurka, suna kuma amfani da irin wannan muhawara. Suna yin imani da cewa aladar auren mata fiye da daya hanya ce da ta dace ga wata mace da ta samu duk wata hidima da kuma yaya, tunda dai matan auren kan taimaka wa juna wajen kula da 'ya'ya.
Ya kamata a kara da cewa, aladar auren mata fiye da daya a Musulunci, wata yarjejeniya ce (na bai wa juna yarda). Babu mutumin da zai iya tilasta wa wata mace auren wani namijin mai aure. Bayan wannan, matar auren tana da ikon ta aza sharadi cewa lalle, mijinta kada ya aure mace ta biyu a kanta (wato ba ta son kishiya ko abokiyar zama). Bible kuma a wani bangaren, a wasu lokuta kan koma ga tilasta yin auren mata fiye da daya. Dole ne mace wadda mijinta ya mutu (mai takaba) da ba ta da 'ya'ya ta auri dan'uwan mijinta da ya mutu, koda kuwa yana da aure [duba sashen Shaanin mata wadanda mazajensu suka mutu (masu takaba) Babi na 14, domin karin bayani], ba tare da neman yardam ta ba, kamar yadda ya zo a Littafin Farawa 38:8 10. Ya kamata a lura da cewa, a cikin al'ummomin Musulmi masu yawa a yau, yin auren mata fiye da daya ba safai ba ne, tunda dai tazarar dake tsakanin adadin dukan jinsuna biyun ba kato ba ne. Mutum zai iya, cewa da aminci, bakin auren mata fiye da daya a duniyar Musulmi ya yi mafi kankanta fiye da bakin alamurar aure fiye da kima a kasashen Turai ta Yamma. A wani kaulin kuma, maza a duniyar Musulmi a yau, sun yi nisa sosai da yin auren mace daya fiye da maza a duniyar Turai ta Yamma. Billy Graham, mashahurin Kiristan mai baza addinin Kirista ya shaida wannan batun da cewa: Kiristanci ba zai iya daidaitawa da batun aladar auren mata fiye da daya ba. Idan Kiristancin ba zai iya yin haka ba, to, cuta zuwa gare shi take. Musulunci ya halatta auren mata fiye da daya a maysayin wani bayani ko warwarewar matsala jin dadin mai yawa na jamaa da jamaa, kuma ya ba da izini wani matsayi iyancin zabar abin da za a yi wa dabiar yan Adam, amma a cikin bayyana maanar tsaikon aikin doka mai tsanani kawai. Kasashen Kirista sun bayyana auren mace daya karara, amma a kan gaskiya suna yin auren mata fiye da daya. Babu wanda zai ce wai bai san irin rawar da kwartayye ke takawa a al'ummar kashashen Turai ta Yammaci ba. Kan wannan zance Musulunci addinin gaskiya ne na asali, kuma ya kan ba da izini ga Musulmi ya aure wata matar aure ta biyu, idan lalle ne, ya yi, amma ya kan haramta duk jamiyyoyin da suke saduwa da juna a boye don jin dadi da inganci zama mai gaskiya gaba daya don tsare lafiyar halin kirkin jamaa. Abu mai ban shaawa ne, a lura da cewa, kasashen Musulmi har ma da na ba Musulmin ba a duniyarmu ta yau, sun haramta aladar auren mata fiye da daya. Yin auren wata matar aure ta biyu, koda kuwa da yardarm matar auren farko ne, ya ketare doka. A wani gefe kuma, yin wa matar auren zamba, ba tare da saninta ba, ko yardarta ba halal ne, mara aibi har a idon doka Wai shin mene ne hukuncin hikimar dake bayan irin wannan musu? Shin, an shirya doka ce a kyauta wa aikin hainci, kuma a hori aikin kirki? Wannan abu daya ne daga abubuwa wandanda jamaa ba sa sosu a namu zamanin yanzu ta duniyar 'wayewa'.
BABI NA 16
To yaya abin yake ga hanyar aladar Kirista? Abin da aka sani sosai ne cewa, mata na Kirista masu zaman zuhudi suna dai rufe kansu ga daruruwan shekaru, amma hakan ba shi ke nan ba. Wali Paul a Littafin Sabon Alkawari, ya yi wasu bayanai masu kayatarwa game da mayafin ida ya ce: Amma ina son ke sani, kan kowane namiji Kiristi ne, kan mache kuma namiji ne; kan Kiristi kuma Allah ne. Kowane namiji da ya ke addu'a ko wa'azi, kansa a rufe, yana yi ma kansa kankanchi. Amma kowache mache da take yin addu'a ko wa'azi, kanta ba lulubi, tana yi ma kanta kankanchi: gama da wannan da a yi mata aski daya ne. Gama idan mache ba ta yin lulubi, sai a yi mata kundumi: amma idan abin kumya ne ga mache ta yi kundumi ko aski, sai ta yi lulubi. Gama ba ya kamata namiji shi yi ma kansa lulubi, da shike shi kamanin Allah ne da darajar Allah: amma mache darajar namiji che. Gama namiji ba daga wajen mache ba ne; amma mache daga wajen namiji ta ke: Gama ba a halitta namiji sabili da mache ba; amma mache sabili da namiji aka halitta ta: domin wannan ya kamata mache ta kasanche da shaidar hukumchi bisa kanta, saboda malaiku. Littafin Kwarantiyawa 11:3 10. Kaidodin ko dalilai wadanda ke bayyana wani raayi musamman na lulubin mata na Wali Paul shi ne cewa, mayafin kan yi misali da wata alamar ikon namiji, wanda shi kamanin Allah ne da darajar Allah a kan macen wadda aka halittata domin namiji. Wali Tertullian, a wani yankin sanannen rubutunsa mai tsawo a kan the Veiling of Virgins (Lullubin yara budurai) ya rubuta cewa, Matasan mata, ku na sanya lullubinku a waje a kan hanyoyin cikin gari, don haka lalle ne, ku sanyasu a cikin coci, kuna sanyasu tsakanin baki, sai ku sanyasu tsakanin 'yan'uwanku maza Cikin dokokin addinin Kirista na cocin mabiya darikar Katolika a yau, akwai dokar da take umurtar mata da su rufe kan su a cikin coci. Wasu rasar coci coci Kirista kamar 'Amish' da 'Mennonites', ga misali, har yanzu matansu na yin lullubi. Dalilin mayafin, kamar yanda shuwagabanninsu na cocin suka bayar shine, Rufe kai wata sananniyar alama ce ta mace a karkashin ikon mijin da kuma Allah, wadda itace ainihin hanyar tunani da Wali Paul ya gabatar a cikin Littafin Sabon Alkawari. Daga dukkan shaida ta bisa, a fili take cewa, Musulunci bai kaga lulubin kai ba. Amma dai, Musulunci ya goyi bayan yinsa a cikin jamaa. Alkur'ani yana iza muminai maza da mata su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu kuma saannan yana iza muminai mata su kara tsawon lulubin kansu har ya rufe wuya da kirazansu, inda yake cewa: Ka ce wa mminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu. wannan sh ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. . Kuma ka ce wa mminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nna kawarsu face ga mazansu ko ubanninsu, ko ubannin mazansu, ko diyansu, ko diyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko diyan 'yan'uwansu mata, ko matan kungiyarsu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai wadanda. ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi dka da kafafunsu domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tba zuwa ga Allah gaba daya, yaku mminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo. Nur: 30 31. Alkur'ani ya fito fili karara da cewa lullubin lalle lalle sai ya tsare tsirnci (farjojin mata),
amma me ya sa tsare tsiranci (farjojin mata) ke da muhimmanci? Har yanzu Alkur'ani ya sake fitowa fili inda ya yi bayani kamar haka: Ya kai Annabi! Kace wa matan aurenka da 'ya'yanka da matan mminai su kusantar da kasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauki ga a gane su domin kada a cce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai Jin-kai Ahzab: 59. Wannan ita ce cikkakiyar magana, a cikin Alkurani an umurta tsare tsiranci (farjojin mata) a rubuce don a kange mata daga fitina, ko maanar tsiranci kariya ne, a bayani mara wuya. Ta haka, nufin mayafin mata wanda ya kan rufe har fuska na Musulunci shine kariya. Lullubi, mayafin mata na Musulunci wanda bai yi kama ba da mayafin hanyar aladar Kirista, ba wata alamar ikon namiji ba ne a kan mace, balle wata alamar mace a karkashin ikon namiji. Lullubi, mayafin mata na Musulunci, wanda bai yi kama da mayafin a hanyar aladar Yuhudanci, ba alamar abin marmari ba ne, da bambancin wasu matan aure masu kyakkyawan halaye. Mayafin mata na Musulunci alamar tsare tsiranci (farjojin mata) kawai ne, tare da kange mata, dukkansu. Tsarin imani ko wani raayin rayuwa dake shiryar da halin wani na Musulunci shine, cewa a koyaushe yafi kyau a zama amintacce fiye da yin nadama. A kan gaskiya, Alkurani ya damu kwarai da kange jikunan mata da sunan mata da cewa wani namijin wanda kan nuna rashin kunya, da kushe wata mace da laifin fasikanci, za a hukumta shi, kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani: Kuma wadanda ke jfar mata masu kamun kai, sa'an nan kuma ba su je da shaidu hudu ba to, ku yi musu blala, blala tamanin, kuma kada ku karbi wata shaida tasu, har abada. Wadancan su ne fasikai. Nur: 4. Kwatanta wannan raayin Alkur'ani mai tsanani da matsanancin horon mai laifi mara tsanani na fyade a cikin Bible kamar haka: Idan mutum ya iske yarinya wadda ta ke budurwa amma b a yi tashin ta ba, ya kama ta, ya kwana da ita, har an tarasda su; sai mutumin da ya kwana da ita shi bada shekel hamsin na azurfa ga uban yarinya, za ta kwa zama matarsa, da shike ya kaskantad da ita; ba shi da iko ya sake ta dukan muddai ransa. Littafin Kubawar Shari'a. 22:28 30. Lalle, mutum ya tambayi wata tambaya mara wuya a nan, wane ne tahakikin wanda aka hukunta? Mutumin da kawai ya biya wata tarar yin fyade, ko kuwa yarinyar da aka tilasta wa auren mutumin da ya yi mata fyaden, kuma ta zauna tare da shi har mutuwarsa? Wata tambaya da za a iya yi ita ce: wane halin ne, ya fi nuna kariya ga mata, raayin Alkurani mai tsanani ko raayin Bible mara tsanani? Wasu mutane, musamman na kasashen Turai ta Yamma, ga alama za su so su zama masu halin yi wa dokancin muhawarar tsare tsiranci (farjojin mata) ga kariya baa. Muhawararsu ita ce cewa, babbar kariya ita ce watsa ilimi, halin wayewa, da kamun kai. Za mu ce: Da kyau, amma hakan bai isa ba. Idan har 'wayewa' shine, isasshen kariya, don me mata a Arewacin Amurka, sun kan kasa nuna karfin zuciyar tafiya su kadai a kan wata hanya mai duhu ko kuma ma, su gitta ta wagen da ake ajiye motoci? Idan kuwa ilimi shine, mafita (warwarewar matsala) me ya sa Jamiar da aka girmama kamar Jami'ar Queens take yin hidimar raka daliba gidajen
kwanansu, galibi, ga dalibai mata dake filin Jamiar? Idan kuma kamun kai shine amsar, don me a kowane rana ake samun rahotannin aukuwar laifin fyade a wuraren aiki daga kafofin yada labarai? Wani misalin wadancan da aka yi wa zargin ayyukan fyade a dan shekarun da suka gabata, kan hada da: Hafsosin runduna teku, Manajoji, Malaman Jami'a, Sanatoci, Alkalan manyan kotuna, da kuma Shugaban kasar Amurka. Na kasa gaskata idanuna yayin da na karanta kididdigan dake tafe, wanda aka rubuta a cikin wata kasida wadda Shugaba mai kula da darussar ofishin mata a Jamia Queens ya fitar: 1. A kasar Canada, ana kai wa mace farmakin shaanin muamular maza da mata a kowane mintuna shida, mace daya cikin mata uku a Canada, a wasu lokatu za a kai masu irin wannan farmaki a ruyuwansu. 2. A Canada mace daya cikin mata hudu suna cikin kasadar yin masu fyade ko kuwa kokarin yi mata fyade a rayuwanta. 3. Mace daya cikin takwas za a kai mata farmakin shaanin muamalar maza da mata a yayin da take halartar karatu a kwaleji ko Jamia. 4. Kuma, wani nazari da aka yi ya gano yan Canada maza da shekarunsu ya kai na tafi Jamia kashi sittin daga cikin dari sun ce za su kai farmakin shaanin muamular maza da mata idan suka tabbatar cewa ba za a kama su ba. Wani abu ba daidai ba ne na asali a al'ummar da muke rayuwa a cikinta. Wani sauya shaanin cinkin hanyar rayuwar alumma da alada tilas ne da gaske. Ana bukatar wata aladar yin wani halin kirki sosai, sa riguna da ba su nuna tsiranci ko jawo hankali zuwa aikata zina, tabbacen rashin yin maganar da yawa game da iyawa ko mallakar dukiya, da ladabin kirki na duk maza da mata. In ba haka ba, kididdigan mara dadi zasu karu kullum da ma rashin kyau sosai. A wannan halin mata kawai zasu sha wahala. A kan gaskiya, mu duka za mu sha wahala amma kamar yadda K. Gibran ya ce: wanda kan karbi doka, ai bai yi kama da wanda kan kirga yawan dukan da ake yi masa jin zafi ba. Saboda haka, wata al'umma kamar Faransa, wadda kan kori mata matasa daga makarantu saboda sa kaya da ba su nuna tsirancinsu ko jawo hankali zuwa ga aikata zina, ita a karshe, take yi wa kanta barna kawai, Daya daga cikin habaici masu yawa na duniyarmu a yau shine, cewa wannan daya dayan dankwalin kai wanda ake girmamawa sosai a matsayin wata alamar abu mai tsarki, idan mata na Kirista masu zaman zuhudu suka daura da nufin nuna ikon da maza ke da shi a kansu. Shine, aka zaga a matsayin wata alamar kuntatawa idan mata Musulmi suka sanya da nufin kariya.
BABI NA 17
musu farin ciki na yin tallafi da munanan dabi'un halin zaman kasashen Turawa ta Yamma mai ci gaba, mai wayayyen kai. A wadannan al'ummomi, abin tunani na sashen sama mai muhimmanci sosai, na wata mace mai dauke da fuskar wata mace musamman, ta zamani galibi, shine, kara kyaun ganin jikinta. Saboda haka, sau da yawa ta kan cika hankalinta gaba daya da kula da siffar jikinta, girmansa, da nauyinsa, domin kada ta yi tunani wani abu kuma. Ta kan kula da jikinta sosai fiye da hankalinta, kuma ta kan kula da mafi yawan dadin magagganunta fiye da iyawanta don yi tunani a hanyar majiya, kuma a fahinci abu. Iyawanta na dadin magagganu, da jawo hankali, da ta da hankali (shaawar maza) shine, ya fi daraja a alummar da take rawuya cikinsu fiye da aiyyukanta wadanda suka isa yabo na neman ilimi, yin nema dukiya, ko kokarin a nemi hankalin mutum, da aikin na zaman jamaa. Babu mutumin da zai sa rai ganin wani kofen Alkur'ani a cikin jakarta, tunda tana cike da kayayyakin shafe shafe dake rakata duk inda take tafe. Samun ruhunta a ibada ba mai yiwuwa ba ne a wata alumma, da jawo hankalinta da ta kan yi musamman a hanyar shaanin mamalar maza da mata, duk ya dauke hankalinta. Saboda haka, za ta kare rayuwarta wajen yin kokarin sosai na son tabbaccenta zama mace ya auku fiye da cikar mutuncinta. Me ya sa al'ummar Musulumi su ka karkata daga abubuwan da suka dace a Musulunci? Babu amsar mai sauki. Wani bayanin kutsawa a cikin dalilan da ya sa Musulmi ba su bi raayin shiriyar Alkur'ani dangane da mata, zai gagari wata dama, ko iyawar yi, ko samun wannan karatu. Amma dai ya kamata a bayana, ko ta yaya, da cewa al'ummomin Musulmi sun karkata daga kaidodi masu nuna halin kirki, ko mene ne za a yi tunani na Musulunci, batun harkoki masu yawa na rayuwansu ga tsawon lokuta. Akwai wani gurbi mai fadi tsakanin abin da Musulmi ake tsammani su yi imani da shi, da abin da za su aikata a kan gaskiya. Wannan gurbi ba abin aukuwa na kwanan nan ba ne. Yana nan ga karnonin, kuma yana yin fadi yau da kullum. Wannan gurbi mai yin fadi kullum ya samo masifa da ya kawo wa duniyar Musulumi, ya nuna ta sosai a kusa dukan harkokin rayuwa kamar: mulkin azzalumin sarki na siyasa, da kama karya, da tsimi, mai tanadi ta baya, da rashin yin gaskiya na zaman jamaa, da ilmi irin na zamani wanda ya kasa, da hankali na mutum da bai sakewa, karuwa, ko ci gaba, da dai suransu. Matsayin mata na kyautata zaman jamaa dangane da wasu wanda ba Musulunci ba ne, a duniyar Musulmi a yau shine, kawai wata alamar muhimmin alamari mai wuya kwarai da gaske. Gyare-gyare a cikin matsayin mata na kyautata zaman jamaa dangane da wasu na yau da kullum, ba a sa rai, ta zama mai amfani ba, idan ba a rakata da kusan duk fahintattun gyare-gyaren dokacin hanyar rayuwar alummomim Musulmi ba. Duniyar Musulmi na bukatar farfadowar da za ta kusantar da ita zuwa ga abubuwan da suka dace a Musulunci, kuma ba masu nisa sosai da su ba. A takaice dai, raayin cewa gurbatacen matsayin mata Musulumi na kyautata zaman jamaa dangane da wasu a yau, wai saboda addinin Musulunci ne, wannan magana ba gaskiya ba ce, wata gaya rashin hazikanci ne. Alamura masu wuya na Musulumi masu yawa, ba saboda shakuwa da Musulunci sosai ba ne da suka yi, (amma) sune gaba-gaban goshin janyewa daga gare shi, galibi, mai aukuwa bayan wani lokaci mai tsowo da dadewa. Haka kuma, ya kamata a sake lafazi da cewa, manufar dake bayan wannan karatu mai nuna kwatanci, ba ta wata hanyar yin bata sunan Yahudanci ko Nasaranci ba ne. Lebur halayen karnonin ashirin karshe namu, da ake daukarsu na halin kirki da aka yarda da su, mai yiwuwa ne, ga alama sune ke razanar da matsayin mata a hanyar aladar Yahudu da
Kirista. Duk da haka, sai a dube su a cikin mahallin tarihi wanda ya dace. A wani kaulin kuma, kimantawar makasudin matsayin mata a hanyar aladar Yahudu da Kirista da ake gudanarwa, sai a dube halayen shaanin tarihin a cikin yadda wannan hanyar alada ta girma, saad da ake yanke hukunci game shi. Raayoyin ruwan dare game da mata a alummominsu babu shakka cewa, daga raayoyin Limaman Yahudawa da Fada-Fadan cocin Kirista ne, da suka yi tasiri kan zancen mata. Masu walafa litattafai dabam-dabam ne suka rubuta Bible da kansa, a lokuta dabam-dabam. Darajoji da salon rayuwar mutanen dake kewaye da wadannan mawalafar ba su taba su ba. Misali, dokokin zina a cikin Littafin Tsohon Alkawari masu magudi ne ga mata da cewa, namu hankalin mutum, mai hikima, ya gagari bayani. Amma dai, idan muka duba tabbaccen abu cewa, kabilun Yahudawa wadanda suka rigaya sun cika hankulansu kaf ne da kyautata zamansu na mutane dake iri daya, kuma lalle, masu kosawa ne, da bayyana kansu rabe da kabilun dake kewaye dasu. Kuma da cewa rashin halin kirki na auraron mata kabilu na shaanin muamalar mata da maza kawai ne, da suke aikata shi, kan yi kurari wa wadannan muradai masu karfi da ake son a ga an samesu kwarai. Saannan sai mu iya fahinta, amma, ba tilas ne mu yi jujayin dalilan wannan magudi ba. Kuma, rubutun Fada-Fada na coci masu cin zarafin mata, ko sokar mata, ba abubuwan da za a cire su daga mahallin aladar kin mata na Girka da Romawa ba ne, a inda suke ruyawa. Zai zama abu wanda ba na adalci ba ne, a siffa wani raayin amfani da wasiyyar Yahudu da Kirista bayan a yi tunaninsa ba tare da bayar da wata shawarar abin da ya shafi maganar mahallin tarihi ba. A kan gaskiya, wani hazikanci wanda ya dace da mahallin tarihin Yahudu da Kirista lalle, yana da muhimmanci saboda zai taba hazikanci masu maana na aiyyuka da hidimomin Musulunci zuwa ga tarihin duniya, da halin dan Adam mai ci gaba, mai wayayyen kai. Halayen wuri, halayen zama, da aladun kabilu daya, suna cikin abubuwa wadanda suka kasance sun yi tasiri da siffa hanyar aladar Yahudu da Kirista. Kafin karni na bakwai wannan tasirin ya kara wa sakon Allah na asali, da aka bayyana wa Anabi Musa da Anabi Isa gishiri da ya gagari fitarwa. Mummunar matayin mata na kyautata zaman jamaa dangane da wasu a duniyar Yahudu da kirista kafin karni na bakwai, magana guda ce, da ake nufi kurum. Saboda haka, an bukaci wani babban sabon sako na Allah da zai shiryar da dukan yan Adam zuwa ga hanya madaidaiciya. Alkur'ani ya siffanta aikin karantar da mutane addini na sabon Manzon Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) a matsayin wani sauke wa Yahudawa da Kirista babban nauyin dake kansu, ya ce: (Wadanda suke suna bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke samun sa rubce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjla, yana umurnin su da alheri, kuma yana hana su daga barin abin da ba a so; kuma yana halatta musu abbuwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mnana a kansu. Kuma yana kayar da nauyinsu daga barinsu, da kukummai wadannan da suka kasance a kansu. To, wadanda suka yi mani da shi kuma suka karfafa shi, kuma suka taimake shi, kuma suka bi haske wanda aka saukar tare da shi, wadannan ne masu cin nasara) A'raf: 157. Saboda haka, kada a duba Musulunci a matsayin abokin hamayyar hanyar aladar Yahudanci da Kiristanci. Sai a dube shi a matsayin wanda ya sanya shi mara aibi, cikakke, da kammalallen sakonin Allah da aka bayyana su kafin zuwansa. A karshen wannan karatu, zan so na mika wa al'ummomin Musulmi na duniya shawarar dake tafe. Mata Musulmi da yawa an hana su hakkinsu na asali na Musulunci da dadewa. Sai a
gyara kuskurorin da suka wuce. Yin haka ba wani tagomashi ba ne, (amma) wani abu da ya dace ne ya wajaba ga dukan Musulumi. Jamaar Musulumin fadin duniya sai su ba da takardar sharudda mai ba da iko ga hakkokin mata Musulumi karkashin koyarwar Alkurani da koyawar Anabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabata a gare shi). Wannan takardar sharudda lalle ne, ya ba wa mata Musulumi dukan hakkokin da Mahalicinsu ya ba su. Saannan, duk hanyoyi na wajibi sai a kara yawansu domin a tabbatar da aiki da takardar sharuddar sosai. Wannan takardar sharudda ta dade ba a yi ta ba, a lokacin da ake tsammaninta, amma mafi kyau ne, ta makara fiye da faufau ba a yi ta ba. Idan Musulumi a fadin duniya ba za su yi wa uwayensu, da matan aure, da yanuwa da diya mata lamunin cikakken hakokkin Musulunci ba, wa kuma ne, zai yi? Bugu da kari, dole ne muna da karfin zuciya yin muamala da abubuwan da suka gabacemu, kuma mu ki karbar hanyoyin aladu da dabioi gaba daya na kakannimu, a duk lokacin da doka ko kaida ta Musulunci game yaya za a nuna halayen kirki, ko me za a yi tunaninsa bai yarda da yinsu ba. Ashe, Alkur'ani bai zargi kafuran Larabawa mai tsanani ba, ga bin hanyoyin aladun kakan kakani kamar makaho? A gefe guda kuma, sai mu kara yawan wani raayi mai hadari zuwa ga duk abin da muke karba daga kasashen Turai ta Yamma, ko daga wane aladun kabila dabam. Saduwa (ta sanin juna) da kuma yin karatun wasu aladun kabilu dabam shine, wani hikima mai amfani sosai. Lalle ne, Alkur'ani ya fadi wannan saduwa (ta sanin juna) a cikin yan kalmomi kadan a matsayin daya daga cikin nufin yin halitta, ya ce: Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabiloli, domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda yake mafificinku a takawa. Lalle ne, Allah Masani ne, Mai kididdigewa. Hujurat: 13. Ya kan tafi ba tare da cewa ba, ko ta yaya, wancan makauniyar kwakwaya ita ce tabbatacciyar alamar wata gaya rashin farin jini. Sanarwa ce zuwa ga masu karatu wadanda ba Musulumi ba, Yahudawa, da Kirista, ko in ba hakam ba, da cewa wadannan kalamai na karshe an kallafad dasu ne. Yana da rikitarwa saboda akwai wuya a fahinci cewa, saboda me addinin da ya sauya matsayin mata na kyautata zaman jamaa dangane da wasu kwarai, ake kadaita shi da kuma zarginsa da ba kyau, kamar wanda ya fi takura wa mata. Wannan ilmi don a fahinci gaskiyar halin Musulunci yadda yake shine, daya daga cikin tatsuniyoyin zamanin da, dake bazuwa sosai fiye da duka a duniyarmu ta yau. Adadin litattafai, labarai a jaridu, kafofin watsa labaru da sinima (majigi) na Hollywood masu sa mamakai su kan sanya wannan tatsuniya ta zama wani abu kamar wani mugun hali ne da ake ciki. Natija wadda ba makawarta na wadannan magagganu da ba a daina yinsu, dake sa wani ya bata daga hanya madaidaiciyya, ta zama jimlar rashin hazikanci, da tsoron duk wani abin da ya shafi Musulunci. Kalmar musun siffanta Musulunci a kafofin watsa labarai na duniya da ake yinta, sai a kawo karshenta, har idan zamu zauna a duniyar da babu duk alamomin nuna bambanci, ko wariyya, da son karya maimakon gaskiya tsantsa, da rashin hazikanci. Wadanda ba Musulumi ba sai su (ankara) su gane gaskiyar kasancewar wani gurbi mai fadi dake tsakanin ban gaskiyar Musulumi, da aiyyuka, da tabbataccen magana mara wuya cewa, aiyyukan Musulumi tilas ba su yi misalin da Musulunci ba. A siffanta matsayin mata na kyautata zaman jamaa dangane da wasu, a wata hanya musamman wanda ba na adalci ba, a duniyar Musulumi a yau, ka ce kamar na Musulunci, ya nesanta daga gaskiya, ai, kamar siffanta matsayin mata ne, a kasashen Turai ta Yamma a
yau, ka ce kamar na Yahudu da Kirista. Da wannan hazikanci a zuciya, Musulumi da wadanda ba Musulumi ba, sai su fara ci gaba da wani aikin nemo hanyar tafiya, da na aika labari, da na sadarwa, da tadi (zance) domin a kau da dukan rashin ban gaskiyar addinai, da tuhuma, da yawan tsoro. Kwanciyar rai da ake son samu a lokaci gaba ga iyalin dan Adam, zai sanya irin wannan tadi (zance) ya zama tilas. Sai a duba Musulunci a matsayin wani addini da ya yi matukar kyautata wa matsayin mata na kyautata zaman jamaa dangane da wasu, kuma ya ba su hakokki masu yawa, da duniya na zamanin yanzu, ya shaida kawai a wannan karni. Musulunci har yanzu yanada abubuwa da yawa da zai ba wa macen yau: martaba, girmamawa, da kariya a cikin dukan kamannun, da dukan shaanonin rayuwanta daga haihuwa har zuwa mutuwarta, bayan shaidar da ta yi, da daidaita, da hanyar cikar dukan ruhinta a ibada, da na hankalin mutum, da na halittar jiki, da na abin da a ke so na biyar bukatu. Ba mamaki, da yawa wadanda suka zabi zama Musulmi a wata kasa kamar Burtaniya mata ne. A kasar Amurka mata sabobin tuba, da suka sake addininsu zuwa Musulunci sun yi yawa a adadi fiye da maza wadanda suka sake addinisu da wata dangantaka tsakanin 4 zuwa 1.85, Musulunci yanada abubuwa da yawa da zai ba wa duniyar tamu, wadda ke mutukar bukatar shiryarwa ta halin kirki da shugabanci. Jakada Herman Eilts, a wani abin da ya shaida a gaban kwamitin shaanonin kasashen waje, na gidan wakilai na taron Amurka, ranar 24 ga watan Yuni ta shekarar 1985, ya ce: Jamaar Musulumi dake cikin duniya a yau tana makubtakar (wato ta kai) biliyan daya. Haka wani adadi ne, mai cika fuska. Amma abin da ya fi cika mini fuska daidai shine, Musulunci a yau shine addinin dake kadaita bautar Allah da yafi bunkasa da sauri. Wannan wani abu ne, da za a duba halayensa musamman. Akwai wani abu da yake gaskiya ne, game da Musulunci, kuma lokaci ya yi da za a gano shi. Ina fatan wannan karatu wani mataki ne da zai kai ga wannan bayani.