1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Kwango

Kwale-kwale ya kama da wuta a Kwango ya kashe mutane 143

Abdourahamane Hassane
April 19, 2025

Akalla mutane 143 ne suka mutu, wasu da dama suka yi batan dabo bayan da wani kwale-kwale ya kama wuta a kogin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango a farkon wannan makon kamar yadda hukumomi suka bayyana.

https://p.dw.com/p/4tIzr
Hoto: Junior Kannah/AFP/Getty Images

Gobarar da ta tashi a cikin jirgin ruwan katakon da ke dauke da man fetir   a ranar Talata a wajen Mbandaka, babban birnin lardin Equateur dake a ke arewa maso yammacin Kwangon:

Har yanzu ba a san dalilan  tashinta ba, sai dai ana gani ba za ta rasa nasaba,ba da man fetir din dake cikin jirgin.Tun farko an gano rukunin  gawarwaki 131 a ranar Laraba, yayin da wasu 12 aka ganosu a ranakun Alhamis da Juma'a. in ji Joséphine-Pacifique Lokumu, yar majalisar dokokin kasar da ta ziyarci wurin da lamarin ya  afku.