Mintuna 23 da suka wuce Ayyana gwamnatin tawaye da dakarun RSF suka yi a Sudan, ya zo a daidai lokacin da yaƙin basasar ƙasar ke cika shekara biyu, abin da ya ƙara saka shakku kan ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya. Ayyana gwamnatin na haɗin-kai da zaman lafiya da jagoran RSF Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya nuna yadda ƙasar ta rabu