Jump to content

Wq/ha/50 Cent

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > 50 Cent
A yi kudi ko kokarin mutuwa'.

Curtis James Jackson III), (An haife shi a ranar 6 ga watan Yulin a shikara ta 1975) wanda aka fi sani da 50 Cent, mawakin rap ne daga New York.

Zantuka

[edit | edit source]
Ina bukatar in san inda nike nufa, saboda na san daga in nike.
Ina nan yadda nike: kana iya son hakan ko ƙaunar hakan.
Mutane suna son gaskiya. Ko da kuwa ba zasu yarda da ita ba, suna son ta.
  • Ina so in bayyana gari na ga wanda bai taɓa zuwan sa ba fiye da waƙoƙin da suke siya da kuma hotunan da suke gani. Mutane suna son gaskiya, ko da kuwa ba za su yarda da ita ba, suna son ta. Na bari kun sani cewa na sha harsashi guda tara ba wai don in saida waƙa ba, amma don kawai gaskiya ce. A duk lokacin da na zauna intabiyu mutane kan tambaye ni, to 50, ya ake ji idan aka sha harbin harsashi har tara?” Amma hakan ba ya riƙe ni ƙasa, azabar, ko kuma sa ran abunda na fuskanta. Kawai ba zai yiwu ba. Wannan shine tunani na kuma wadannan su ne abubuwan da ke faruwa. Wannan shi ne dalilin nike faɗan baitukan da nike faɗa. Wannan shi ne abunda ya faru a yayin da nike neman arziƙi kafin in mutu a Southside Queens.