William Shakespeare (26 April 1564 (baptiza) – 23 April 1616), ya kasance mawaki ne dan kasa Ingila, marubucin wasanni kuma dan wasan kwaikwaiyo, wanda ake dauka a matsayin marubucin harshen Turanci da yafi kowa fice, kuma dan wasan dirama da yafi kowa a duniya.
Maganganu
edit- Duk abinda ba za’a iya watsi da shi ba dole a rungume shi.
- Kyawu da kanshi kan jawo hankali
Na idanun maza ba sai da mai jawabi ba.- The Rape of Lucrece (1594).
- Nasarar zamani shine ya natsar da sarakuna masu jayayya,
Ya fito da karya fili, sannan ya kawo gaskiya zuwa haske.- The Rape of Lucrece.
- Yarinta da tsufa bazasu taba rayuwa tare ba
Yarinta na cike da nishadi, tsufa na cike da kula wa.- The Passionate Pilgrim: A Madrigal; akwai dan kokwanto game da wanda ya kirkiro wannan.
Romeo and Juliet (1595)
edit- Menene acikin suna? Wanda muke kira da rose,
daga nan duk wani suna zai yi daɗi.- Juliet, Act II, scene ii.