Wikipidiya
Fayil:Wikipedia Portal Screenshot (2022).svg da Wikipedia pagina principal.png | |
URL (en) | https://wikipedia.org/ |
---|---|
Eponym (en) | Wiki da Insakulofidiya |
Gajeren suna | Wikipédia, Wikipedia, ウィキペディア, Viquipèdia, Wikipèdia, Vicipaedia, Wikipedia, Βικιπαίδεια, ဝီကီပီးဒီးယား, ويكبيديا, Wikipedia, lipu Wikipesija da Wikipédia |
Iri | online encyclopedia (en) , MediaWiki wiki (en) da Wikimedia project (en) |
Slogan (en) | the free encyclopedia that anyone can edit, الموسوعة الحرة التي يستطيع الجميع تحريرها, vapaa tietosanakirja, de vrije encyclopedie, свободная энциклопедия, которую может редактировать каждый, Die freie Enzyklopädie, 人人可编辑的自由百科全书, 人人可編輯的自由百科全書, একটি উন্মুক্ত বিশ্বকোষ, যা সবাই সম্পাদনা করতে পারে, ウィキペディアは誰でも編集できるフリー百科事典です, L'enciclopèdia de contingut lliure que tothom pot millorar, Төрлө телдә яҙылған, сикләүһеҙ ҡулланыуҙа булған ирекле интернет энциклопедия. Һәр кем уны төҙөүҙә ҡатнаша ала, آزاد دائرۃ المعارف جس میں کوئی بھی ترمیم کر سکتا ہے, la enciclopedia de contenido libre que todos pueden editar, a szabad enciklopédia, Ազատ հանրագիտարան, որը կարող է խմբագրել յուրաքանչյուր ոք:, האנציקלופדיה החופשית שכולם יכולים לערוך, Wolna encyklopedia, którą każdy może redagować, 海納百川,有容乃大, la libera enciklopedio redaktebla de ĉiuj da sebuah ensiklopedia bebas yang bisa disunting oleh siapa saja |
Language (en) | multiple languages (en) |
License (en) | Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International (en) da CC BY-SA 3.0 (mul) |
Programming language (en) | PHP (mul) |
Software engine (en) | MediaWiki (mul) |
OCLC, Inc. (en) | 52075003 |
Mai-iko | Wikimedia Foundation da Jimmy Wales |
Maƙirƙiri | Jimmy Wales, Larry Sanger da Wikimedia community (en) |
Mai wallafawa | Al'ummar Wikipedia |
Web developer (en) | Jimmy Wales da Larry Sanger |
Service entry (en) | 15 ga Janairu, 2001 |
Wurin hedkwatar | Tarayyar Amurka |
Kyauta ta samu | Princess of Asturias Award for International Cooperation (en) , FSF Free Software Award for Projects of Social Benefit (en) , Grimme Online Award (en) da Erasmus Prize (en) |
Alexa rank (en) |
13 (4 Nuwamba, 2020) 5 (31 Oktoba 2017) 5 (7 Nuwamba, 2017) 5 (20 Nuwamba, 2017) 9 (2 Oktoba 2019) 10 (1 ga Faburairu, 2020) 14 (ga Augusta, 2020) 7 (4 ga Afirilu, 2009) 13 (18 Disamba 2020) |
Wikipedia | |
Wikipedia | |
wikipedia |
Wikipidiya Insakulofidiya ce ta kyauta da ke tattare da harsuna daban-daban a fadin duniya, wanda al'ummomi masu bada gudummawa ke rubuta mukalai ta hanyar hadin gwiwa a fili (ba tare da ɓoye-ɓoye ba). A turance a na kiran editocinta da suna Wikipedians. Wikipidiya ta kasance farfajiyar nazari mafi girma a tarihin ilimin duniya.[1] Ta kasance daya daga cikin fitattun shafukan yanar gizo guda goma a duniya kamar yadda Similarweb ta zayyano; i zuwa shekara ta 2022 kuwa, Wikipidiya itace ta 7 a cikin jerin fitattun shafuka na yanar gizo a duniya.[2][3][4] gidauniyar Wikimedia Foundation ce ke daukan nauyin shafin wikipidiya. ita kuwa Wikimedia Foundation wata kungiya ce wanda ba'a samar da riba (wato non-profit organization a Turance) na kasar Amurka, kuma suna samun kudadensu ne ta hanyar taimako/gudummawa (donation) daga wasu kungiyoyi ko jama'a.[5]
Wikipedia shafi ne na yanar gizo wanda masu bada gudummawa ke rubuta mukalai kuma su ke gudanar da ita, ta hanyar shigar da ilimi ko gyare-gyare da sauransu. Ana kuma kiran duk wani mai gyare-gyare ko shigar da ilimi a shafukan Wikipedia da suna "Wikipedian". Wikipidiya tana tattare da harsunan duniya da dama, a shafinta kowa na iya ƙirƙira ko gyara muƙala a kyauta domin taimakawa wajen samar da ilimi kyauta, wannan ne yasa wikipidiya tayi zarra a duk duniya wurin samar da ilimi daga asalin inda ilimin ya fito.
Kowa da kowa na da damar bada gudummawa wajen yada ilimi ta hanyar ƙirƙiran sabuwar muƙala ko gyara ƙirƙirarrun muƙalai da ke buƙatan a ingantasu ta hanyar gyara wasu 'yan kura-kurai ko ƙarin bayani. Harwayau babu wani shafi a duniya baki ɗaya da ya tattara ilimi da bayanai a yanar gizo a yanzu kamar wikipidiya, kuma miliyoyin ɗalibai ne da malamai, da sauran mutane suke amfana daga manhajar a kullum.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An ƙaddamar da shafin Wikipidiya ne a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 2001, Jimmy Wales tare da Larry Sanger ne suka haɗa gwiwa wajen samar da shafin. Suka sanya mata suna ta hanyar hade kalmar wiki da encyclopedia. A farkon ƙirƙirar shafin an kafa tane da Turanci kadai amma daga baya sanadiyar karɓuwa da shafin yayi ne yasa ake samar da ƙarin Harsuna akai-akai har zuwa yanzu. A halin yanzu akwai maƙaloli sama da 6,713,721 a sashen Wikipidiya na Turanci wanda kuma shine sashen da yafi kowanne shahara da tarin maƙaloli. Ayanzu akwai sama da maƙaloli guda miliyan arba'in a mabanbantan yarurruka sama da 301, sannan shafin yana samun masu ziyara mabanbanta sama miliyan 500, adadin duka masu ziyara sunkai sama da biliyan 18 ko wanne wata tun daga watan Fabrairu na shekara ta 2014.
Hausa Wikipidiya
[gyara sashe | gyara masomin]A sashen Hausa na wikipidiya kuma akwai maƙaloli sama da dubu 31 ya zuwa watsn Satumba a shekara ta 2023.[6] duk da yake sashen yana da ƙarancin masu bayar da gudunmuwa amma a hankali sashen yana ƙara bunƙasa cikin gaggawa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Wikipedia is 20, and its reputation has never been higher". The Economist. January 9, 2021. Retrieved February 25, 2021.
- ↑ "Wikipedia is 20, and its reputation has never been higher". The Economist. January 9, 2021. Retrieved February 25, 2021.
- ↑ "Wikipedia.org Traffic, Demographics and Competitors". Alexa Internet. Retrieved October 1, 2019.
- ↑ "Similarweb Top Websites Ranking". Similarweb. Retrieved June 11, 2022.
- ↑ McGregor, Jena (March 17, 2020). "Wikimedia's approach to coronavirus: Staffers can work 20 hours a week, get paid for full time". The Washington Post. Retrieved February 25, 2021.
- ↑ https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi