Bendtner
Bendtner | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Kwapanhagan, 16 ga Janairu, 1988 (36 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Daular Denmark | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ma'aurata |
Caroline Fleming (en) Julie Zangenberg (en) Philine Pi Roepstorff (en) Sus Wilkins (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 3 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 86 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 194 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm3367902 |
Bendtner (An haifeshi ranar 16 ga watan Junairu, 1988). Tsohon dan wasan kwallon kafa ne na kasar Danish. Ya kasance kwararren dan wasa da ke taka leda a matsayin mai buga gaba.
Bayan nasarori daya samu tun lokacin kuruciya, yayi kungiyoyi da dama kamar kungiyar kwallon kafa ta Tarnby Boldklub, Kjobenhavns Boldklub da kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Bendtner din ya rattaba hannu a matsayin kwararren dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar alif 2005. Dan wasan ya fara bayyana a watan Oktoba shekara ta alif 2005 a wasan kofin lig wanda aka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Sunderland a shekarar. A shekarar 2006 zuwa shekara ta alif 2007, yaje zaman aro a kungiyar dake buga Championship wato kungiyar kwallon kafa ta Birmingham city, Inda ya buga wasanni har guda 48.
Bayan dawowarsa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal din, dan wasan ya shigo cikin sha dayan farko inda ya shigo cikin jerin masu buga wasanni kullum. Sai dai kuma dan wasan ya fara rasa damar sa a shekarar alif 2011 zuwa shekara ta alif 2012. Hakan ne yasa ya kara tafiya wani zaman aron har ya shafe kusan duk shekarar a zaman aro inda ya koma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sunderland inda ya bugama kungiyar wasanni har guda 38. Dan wasan ya shafe duka rayuwar kwallon shi ta shekarar alif 2012 zuwa shekara ta alif 2013 a zaman aro da kungiyar kwallon kafa ta Juventus inda ya bugama kungiyar wasanni guda 10 amma ba tare da ya zura kwallo a raga ba.
Bendtner ya raba gari da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar alif 2014 inda ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Vfl Wolfsburg a matsayin dan wasan kyauta, ya samu nasarar jefa masu kwallo wadda ta basu nasara a gasar kofin Dfl Super Cup. Sun sakeshi a shekarar alif 2016 inda ya koma gasar Premier league a kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest inda suke buga gasar Championship a shekarar. A watan Match shekarar alif 2017 ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafan Rosenberg.[1]
A fannin Ƙasa dan an wasan yana cikin jerin yan wasan da suka halarci gasar kofin duniya. Haka zalika dan wasan ya wakilci kasar tashi a gasar Euro 2012 da aka buga da kuma kofin duniya da aka buga a shekarar alif 2018.[2]
Salon Wasa
[gyara sashe | gyara masomin]Bendtner dan wasa ne mai hazaƙa da zai iya buga ko ina a gaba. Kasancewar shi dan gaba na tsakiya yana amfani sosai wajan buga sauran wuraren suma. Kasancewar shi dogo kuma kakkarfa maji karfi, yana amfani da wannan damar domin danne yan baya kuma yana da tsalle tsalle da tashi, hakan ne ya bashi damar cin kwallaye da kai. Dan wasan yana da kwarewa sosai a saman iska kuma yana da karfin bugun kwallo da kai.[3]
Dukda cewa yana da alkawari, amma dan wasa ne marar tarbiya a yarintar kwallon sa. Dan wasa ne da yake da abubuwa masu yawa a cikin salan wasannin sa. Yana da basira, sauri da zafin nama, taba kwallo sau daya, jajircewa, cin kwallo da kuma taimakawa aci.
Tsohon kwararren kocin dan wasan wato Arsene Wenger, ya bayyana dan wasan a matsayin gwarzo kuma kwararren dan gaba. A cewar tsohon kocin, Bendtner dan gaba ne mai hatsari da ka iya cin ƙwallo ta ko wane hali kuma a inda yake bukata.
Saidai dan wasan yayi fama da raunuka daban daban inda yasha jinya sosai a lokuta da dama wanda hakan ya bada gudummawar hana dan kwallon yakai matakin da yake bukata.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Nicklas Bendtner: A-Landshold (Alle kampe)" [A-internationals (all matches)] (in Danish). Dansk Boldspil-Union. Retrieved 26 August 2018.
- ↑ Biography". Nicklas Bendtner personal website. Bendtner Consulting. Archived from the original on 2 April 2011. Retrieved 15 September 2010.
- ↑ "Player profile: Nicklas Bendtner – Biography". Arsenal F.C. Archived from the original on 26 January 2013. Retrieved 20 October 2010
- ↑ "Player profile: Nicklas Bendtner – Biography". Arsenal F.C. Archived from the original on 26 January 2013. Retrieved 20 October 2010.