Jump to content

Atiku Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Atiku Abubakar
mataimakin shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Mike Akhigbe - Goodluck Jonathan
Rayuwa
Haihuwa Jada (Nijeriya), 25 Nuwamba, 1946 (78 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Fulani
Harshen uwa Adamaua-Fulfulde (en) Fassara
Ƴan uwa
Abokiyar zama Amina Titi Atiku Abubakar
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a customs officer (en) Fassara da ɗan siyasa
Employers Najeriya
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
atiku.org
hoton dan siyasa atiku abubakar
hoton atiku da muhammad buhari

Atiku Abubakar'About this soundAtiku Abubakar  (an haife shi a ranar 25 ga watan Nuwamba shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da shida, 1946)[1] Miladiyya. Ya kasance dan siyasan Najeriya,kuma dan kasuwa ne wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar Najeriya daga shekara ta alif Dari Tara da casa'in da tara , 1999 zuwa shekara ta 2007 lokacin shugabancin Olusegun Obasanjo.[2][3][4] Atiku ya nemi zama gwamnan Jihar Adamawa a shekara ta alif, 1990 zuwa 1996 daga baya kuma, a shekara ta alif, 1998, aka zaɓe shi kafin nan ya zama mataimakin Olusegun Obasanjo[5] a Zaben shekarar, 1999 na shugaban kasar Najeriya an kuma sake zaben su a zaben shugaban kasar Najeriya ta 2003.[6]

Majar Atiku a jam'iyar APC

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Atiku haifaffen jihar Adamawa ne.[7] An haifeshi a jahar Adamawa acikin garin Jada da ɗaya tilo awajen garba Abubakar mahaifinsa da mahaifiyarshi Aisha kande.https://newswirengr.com/2023/02/28/atiku-abubakar-biography-education-career-marriage-net-worth-achievements-and-controversy/

Atiku bayan zabe

Atiku Abubakar yayi rashin nasarar samun zama shugaban kasar Najeriya a lokuta daban daban har sau bakwai. Daga shekarar 1993, 2007, 2011, 2015 , 2019 da Kuma 2023. A shekarar 1993, yayi takara a karkashin Social Democratic Party dan neman zama shugaban ƙasar amma ya sha kaye a wurin Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe. Ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Action Congress a Zaɓen Shugaban kasar Najeriya ta 2007 amma yayi rashin nasara da zuwa na uku a wurin Umaru Yar'Adua na jam'iyyar PDP da Muhammadu Buhari na ANPP. Ya nemi zama ɗan takarar shugabancin ƙasar a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party lokacin Zaɓen Shugaban kasar Najeriya ta 2011 nan ma yayi rashin nasara a hannun shugaba mai ci Goodluck Jonathan.[8] A shekara ta, 2014, Atiku ya koma jam'iyyar APC gabanin Zaɓen Shugaban ƙasar Najeriya ta 2015 kuma ya nemi zama ɗan takarar jam'iyyar amma yayi rashin nasara a hannun Muhammadu Buhari. A shekarar, 2017, ya sake komawa jam'iyyar PDP a inda kuma ya zama ɗan takarar jam'iyyar a Zaben Shugaban kasar Najeriya ta 2019, sai dai har wayau ya sake rashin nasara a hannun shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.[9][10]. A shekarar, 2022 Atiku Abubakar ya bayyana sha'awarsa ta fitowa takarar shugaban kasa a Jam'iyyar PDP mai adawa inda zai kara da Bola Ahmed Tinubu na APC, da Peter Obi na Jam'iyyar Labour da Rabiu Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP da sauran Yan takara na kananan jam'iyyu. Bayan fafatawa mai zafi ta cikin gida da kuma ta sauran abokan karawa, hankula sun kasu gida daban-daban kuma da yawan jama'a sun kyautata zaton Atiku ne zai lashe Zaben. Daga cikin dalilan sa ran nasararsa har da rabuwar kanu a cikin ita jam'iyyar APC. Kari kan wannan, jama'a na cikin tsananin talauci da rashin tsaro a Birane da ƙauyuka. Wani abin damuwa shi ne yanda kwatsam gwamnati ta yi sauyin kudi wanda hakan ya jawo karancinsu a hannun mutane. Hatta da su mukarraban jam'iyyar APC sun zargi cewa an yi haka dan kassara tafiyar Tinubu. Atiku Abubakar ya nuna gamsuwar sa da wannan sauyin kuɗi. Bayan an yi zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu na shekarar, 2023, an kwashe kwanaki huɗu ana tattara sakamakon zaɓen kuma da asubahin wayuwar garin Laraba, shugaban hukumar zaben INEC ya bayyana Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[11]

  1. Atiku Abubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria (entrepreneurs.ng)
  2. "Profile of Atiku Abubakar: From an only child of a father who opposed western education to a political guru". Nigeria Today. 2 October 2018. Archived from the original on 3 January 2019. Retrieved 3 January 2019.
  3. Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Abubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
  4. "Atiku Abubakar - the Nigerian operator who knows how to make money". BBC News (in Turanci). 2019-02-06. Retrieved 2020-09-11.
  5. https://leadership.ng/ex-president-obasanjo-visits-remi-tinubu-for-sallah-celebration/
  6. Podcast, N. L.; Giveaway, N. L. (2019-11-25). "Happy Birthday!! Atiku Abubakar Celebrates His 73rd Birthday (Drop Your Well Wishes) » Naijaloaded". Naijaloaded (in Turanci). Archived from the original on 2020-07-26. Retrieved 2020-05-29.
  7. "The Story of My Life by Atiku Abubakar". PM News Nigeria. 15 April 2019.
  8. Adeosun, Olajumoke (2019-07-17). "Atiku Atiku AbAbubakar - Biography and Life of the 11th Vice President of Nigeria". Entrepreneurs In Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2021-07-09. Retrieved 2020-05-29.
  9. "Atiku emerges PDP presidential candidate". The Punch (in Turanci). 7 October 2018. Retrieved 2019-04-19.
  10. "2023: Where Nigeria's President comes from, not important ― Atiku". Vanguard News (in Turanci). 2021-10-07. Retrieved 2022-02-22.
  11. https://punchng.com/topics/2023-elections Archived 2023-03-01 at the Wayback Machine

Early political career

[gyara sashe | gyara masomin]

Abubakar ya fara shiga siyasa ne a farkon shekarun alif 1980, lokacin da yayi aiki a bayan fage a yakin neman gwamna na Bamanga Tukur, wanda a wannan lokacin shi ne manajan darakta na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya. Ya nemi kuri'u a madadin Tukur, kuma ya bada gudummawa ga yakin.

Zuwa ƙarshen aikinsa na Kwastam, ya sadu da Janar Shehu Musa Yar'Adua, wanda ya kasance na biyu a matsayin Shugaban Ma'aikata, Babban Hedikwatar tsakanin shekarata alif 1976 da shekarar alif 1979. Yar'Adua ya jawo Abubakar cikin tarurrukan siyasa wanda yanzu ke faruwa akai-akai a gidan Yar'Adia na Legas, wanda ya haifar da Jam'iyyar Jama'ar Najeriya. Jam'iyyar People's Front ta hada da 'yan siyasa kamar Umaru Musa Yar'Adua, Baba Gana Kingibe, Bola Tinubu, Sabo Bakin Zuwo, Rabiu Kwankwaso, Abdullahi Aliyu Sumaila da kuma Abubakar Koko .

A shekara ta alif 1989, an zabi Abubakar a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa na Peoples Front of Nigeria a cikin gina Jamhuriyar Najeriya ta Uku. Abubakar ya lashe kujerar wakiltar mazabarsa a Majalisar Dokoki a shekarata alif 1989, wanda aka kafa don yanke shawarar sabon kundin tsarin mulki na Najeriya. Gwamnatin soja ta hana Jam'iyyar People's Front yin rajista (babu wani daga cikin kungiyoyin da suka yi amfani dasu da akayi rajista), kuma sun haɗu da Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) da gwamnati ta kirkira.

A ranar 1 ga watan Satumba na shekarar alif 1990, Abubakar ya sanar da takarar gwamna ta Jihar Gongola. Bayan takarar daya lashe a zaben fidda gwani na SDP a watan Nuwamba na shekara ta alif 1991, amma nan da nan gwamnati ta hana shi shiga zaben.

A shekara ta alif 1993, Abubakar ya tsaya takarar zaben fidda gwani na SDP. Sakamakon bayan zaben fidda gwani na farko da aka gudanar a garin Jos shine: Moshood Abiola tare da kuri'u 3,617 , Baba Gana Kingibe tare da kuriʼu 3,255 da Abubakar Wanda Kiri'arsa takai " 2,066. Koyaya, bayan Shehu Yar'Adua ya nemi Atiku Abubakar ya janye daga kamfen ɗinsa, tare da Abiola yayi alkawarin sanya shi abokin tserensa. Daga baya gwamnonin SDP suka matsa wa Abiola don zabar Kinigbe a matsayin Mataimakin shugaban kasa, a Zaben shugaban kasa na 12 ga Yuni.

Bayan ranar 12 ga watan Yuni kuma a lokacin sauyawar Janar Sani Abacha, Abubakar ya nuna sha'awar yin takara don kujerar Gubnetorial wanda take a Jihar Adamawa a karkashin Jam'iyyar United Nigeria Congress Party, shirin sauyawar ya ƙare tare da mutuwar Janar Abacha. A shekara ta alif 1998, Abubakar ya shiga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma daga baya ya sami gabatarwa ga Gwamnan Jihar Adamawa, inda ya lashe zaben gwamna na watan Disamba na shekarar alif 1998, amma kafin a rantsar da shi ya karɓi matsayi a matsayin abokin takarar dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon shugaban soja Janar Olusegun Obasanjo wanda ya ci gaba da lashe Zaben shugaban kasa na 1999 wanda ya kawo a Jamhuriyar Najeriya ta huɗu.