Jump to content

Abdalle Mumin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdalle Mumin
Rayuwa
ƙasa Somaliya
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam da ɗan jarida

 

Abdalle Ahmed Mumin ɗan jarida ne ɗan ƙasar Somaliya, ɗan rajin kare hakkin ɗan Adam, kuma mawallafin littafin Hounded: African Journalists in Exile. A halin yanzu shi ne sakatare Janar na Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Somaliya kuma marubuci ga jaridar The Guardian. [1] [2] [3] A ranar 11 ga watan Oktoba, an kama shi a lokacin da yake jiran jirgin da zai je Nairobi aka kai shi Godka Jila’ow, wurin da ake tsare da shi. Hukumomin Somalia sun tsare shi na tsawon kwanaki uku a can don "kai hari kan mayakan Islama" a yankin gabashin Afirka, daga bisani kuma aka sake shi bisa belin bayan kwanaki 10 a hannun 'yan sanda a ranar 22 ga watan Oktoba. [4]

Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa a farkon shekarar 2015 bayan ya yi wa jaridar The Wall Street Journal rahoto kan kisan shugaban al-Shabaab.

  1. "Abdalle Mumin: A human rights activist and giant of Somali journalism". Amnesty International. May 3, 2023.
  2. Burke, Jason (November 24, 2022). "Journalist under strict bail terms in Somalia after arrest in crackdown" – via The Guardian.
  3. "Somali Journalist Freed in Surprise Move Hours After Conviction". Voice of America. February 13, 2023.
  4. Gonzales, Suzannah (October 11, 2022). "Somali intelligence personnel arrest press rights advocate Abdalle Ahmed Mumin".