Rashid Abdullah Al Nuaimi (راشد عبدالله النعيمي ) tsohon ministan harkokin wajen kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ne.

Rashid Abdullah Al Nuaimi
foreign minister (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1937 (86/87 shekaru)
ƙasa Taraiyar larabawa
Karatu
Makaranta Jami'ar Alkahira
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Nuaimi memba ne na dangin Ajman mai mulki, Al Nuaimi.[1] Yana da digiri na farko a injiniyan man fetur, wanda ya samu daga jami’ar Alkahira a shekarar 1967.[2]

Nuaimi ya fara aikinsa ne’a sashi mai zaman kanta a masarautar Abu Dhabi.[2]Sannan ya shiga ma'aikatar harkokin waje ta Emirati kuma har zuwa shekarar 1975, ya yi aiki a can kan fannoni daban -daban.[2]  A shekarar 1975, an nada shi a matsayin daraktan sashen harkokin siyasa a ma'aikatar harkokin waje.[2]  A cikin shekara ta 1976, ya zama sakataren harkokin waje. Ya rike mukamin karamin ministan harkokin waje daga shekarar 1977 zuwa shekara ta 1990.  Hamdan bin Zayed ya gaje shi a mukamin.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Rashid bin Abdullah Al Nuaimi". APS Review Gas Market Trends. 8 June 1998. Retrieved 15 April 2013.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Profile". ECSSR. Archived from the original on 11 September 2016. Retrieved 15 April 2013.