Chadi na nan daram a yaki da Boko Haram
Gwamnatin Faransa ta ce, har yanzu kasar Chadi na nan cikin dakarun da ke yaki da 'yan ta’adda a rundunar G5 Sahel duk da ikrarin shugaba Idris Deby na cewar dakarun kasarsa za su janye daga yaki a wajen iyakokin kasar.
Wallafawa ranar:
Ministar Tsaron Faransa Florence Parly ta sanar da haka lokacin da take yi wa kwamitin tsaro a Majalisar Dattawa bayanai, wanda ya kunshi shirin Chadi na tura bataliyan soji zuwa Mali nan gaba.
Shugaba Deby cikin fushi ya ce, zai janye dakarun kasar daga duk wani yaki a wajen iyakokin kasarsa bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa sojojinsa kusan 100, abin da ya sa ya kaddamar da yaki akan su, inda kasar ta sanar da samun gagarumar nasara bayan kashe mayakan kungiyar sama da 1,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu