1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Cin zarafin mata a yankin arewacin Mozambik

Antonio Cascais Zaharaddeen Umar Dutsen Kura/SB
July 16, 2024

Rikici tsakanin kungiyar ‘yan ta‘adda masu alaka da kungiyar IS da dakarun gwamnatin Mozambik na ci gaba da janyo wa matan kasar fyade da auren dole da sauran nau'ika na cin zarafi.

https://p.dw.com/p/4iNf0
Mozambik Dakaru
Dakaru a arewacin MozambikHoto: Delfim Anacleto/DW

Halin da ake ciki a Mozambik din ya yi kamarin da iyaye ke aurar da ‘ya'yansu mata ga ‘yan ta'adda domin samun kudin sadakin da zai ba su damar sayen abincin ciyar da sauran mutanen gidan. Talaucin da rikicin tsakanin kungiyar ‘yan ta‘adda ta IS da dakarun gwamnatin Mozambique ne ke kara jefa magidanta cikin wannan kunci. Wannan na faruwa ne duk da cewa ‘yan ta'adda masu ikirarin jihadi na garkuwa da ‘yan matan da ba a aurar musu da su ba, inda daga bisa sukan yi musu fyade har su dauki juna biyu ba tare da amincewar matan ba.

Karin Bayani:Barazanar 'yan ta'adda a Mozambik 

Mozambik | Save the Children  a Mozambik
MozambikHoto: Save the Chidren

Irin wannan rahoton shi ne ke zuwa teburin kungiyoyin agaji dabam-dabam a Mozambik, dalilin ma ke nan da ya ja hankalin kungiyoyin fitar da rahoto na musamman kan cin zarafin mata a kasar da ke cikin rikici, kamar dai yadda Paula Sengo Timane ta kungiyar bayar da agajin Save The Children ta ce abin takaici ne ke faruwa. Ma'aikatan na ci gaba da samun makamancin wannan labari kusan kullum. Sabon rahoton da suka fitar mai taken ‘'Auren dole a yankin Cabo Delgado'' ya bankado wadannan abubuwa masu muni da ma sauran cin zarafin da ba za su fadu ba.

Mocímboa da Praia, Cabo delgado, Mozambik
Garin Cabo delgado na MozambikHoto: DW

Rikicin da ke gudana a yankin na Cabo Delgado ya shiga shekara ta takwas ke nan ba tare da alamun karewa ba. Alkaluma daga Majalisar Dinkin Duniya na cewa cikin shekarar nan kadai kusan mutane 190,000 suka kaurace wa gidajensu, wasu alkaluma da ba a taba samun yawansu ba, tun farkon fara rikicin.