1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Vietnam: Tsaurara matakan yakar cin-hanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 21, 2024

Jagoran jam'iyyar kwamunisanci da ke mulki a Vietnam To Lam ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta kara matsa kaimi a yaki da cin-hanci da rashawa a kasar.

https://p.dw.com/p/4m3g1
New York | US-Präsident Joe Biden trifft Präsident To Lam aus Vietnam
Hoto: ANDREW CABALLERO-REYNOLDS/AFP

Sai dai masu fashin baki na yi wa kiran na shugaban Vietman din To Lam kallon wani mataki da ake amfani da shi, domin cimma buri a rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fama da shi. Lam da ya yi jawabinsa na farko ga majalisar dokokin ta Vietnam ya karbi jagorancin jam'iyyar ta Communist ne a watan Agustan bana, bayan rasuwar tsohon jagoranta Nguyen Phu Trong da ya assasa yaki da cin-hancin na ba sani ba sabo. Yaki da cin-hancin a Vietnam dai, ya rutsa da mutane da dama da suka hadar da manyan 'yan kasuwa da jami'an gwamnati ciki har da shugabannin kasa biyu da kuma mataimakan firaminista uku daga shekara ta 2021 kawo yanzu. Shugaba Lam ya dora daga inda wanda ya gada ya tsaya, duk da ana zargin suna yakin ne domin cin dunduniyar 'yan adawa. Koda a makon da ya gabata ma dai, kafar yada labaran Vietnam din ta ruwaito alkalin alkalan kasar Le Minh Tri na bayyana cewa a shekarar da ta gabata an gurfanar da sama da mutane dubu 10 cikin shari'u kimanin 4,800 da Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta gudanar.