1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: Sudan da Libiya sun dau hankali

Zainab Mohammed Abubakar L
October 18, 2024

Fara allurar riga-kafin cutar Mpox a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da yakin Sudan da kwararar 'yan gudun hijira daga Libiya, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4lxDp
Sudan | Yakin Basasa
Al'ummar Sudan na cikin halin taskun rayuwaHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

A sharhin da jaridar die tageszeitung ta wallafa mai taken "Bayan ruwan sama, yunwa ta zo". Yakin Sudan na kara ta'azzara, ana samun karuwar 'yan gudun hijira daga Darfur zuwa Chadi kuma har yanzu babu tabbaci dangane da kayan agaji ga wannan tarin al'umma da ke fama da yunwa. Jaridar ta ce, kungiyoyin bayar da agaji suna ta kira da gargadi da babbar murya. Yakin da ake yi a Sudan da tuni ya haifar da yunwa mafi girma a duniya, mai yiyuwa ya kara ta'azzara cikin watanni masu zuwa. A yayin da aka kawo karshen damunar bana, ana sa ran za a kara samun barkewar fada tsakanin sojojin gwamnatin Sudan (SAF) da mayakan Rapid Support Forces (RSF). A wannan makon a binin Geneva daraktan Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR na yankin Amadou Dian Balde ya yi gargadin cewa, a cikin makon farko na watan Oktoba kadai kimanin 'yan gudun hijira dubu 25 daga yankin Darfur na yammacin Sudan sun isa kasar Chadi da ke makwabtaka. Baya ga rikicin neman madafun iko, Sudan din ta fuskanci iftila'in ambaliyar ruwa wanda ya kara tsananta lamarin na kaura. Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa, kusan mutane miliyan 11 ne ke gudun hijira a Sudan ciki har da kusan miliyan uku a wajen kasar. Chadi ita ce kasa mafi girma da ke karbar bakuncin 'yan gudun hijirar Sudan wajen dubu 700, amma ita kanta tana fama da matsanancin talauci.

Libiya | Bakin Haure | Mafaka
Bakin hauren Libiya na dakon zuwa cibiyoyin "karba da tantance" masu neman mafakaHoto: Hamza Turkia/Xinhua/IMAGO

"Sabuwar hanyar kaura" da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung ta bude labarin da ta wallafa game da karuwar kwale-kwalen 'yan gudun hijira daga Libya, wadanda ke isa Kreta da kuma Tsibirin Gavdos da ke gabar teku. A cewar jaridar kafofin yada labaran kasar Girka sun sanar da cewa, yankin kudancin Turai na fuskatar karuwar bala'i. Wani jirgin kamun kifi da ke dauke da bakin haure ya nutse a kudancin Tsibirin Gavdos, a daren Larabar mako mai kare wa. Kwamitin da ke da alhakin aikin ceto da kuma kungiyar agaji ta Red Cross ta Girka sun samu nasarar ceto mutane 97, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka bata. Za a kai wadanda aka ceto din nan zuwa Heraklion, babban birnin Kreta. A can da kuma a tashar jiragen ruwa ta Chania da ke gabar tekun ta yamma, 'yan ci-rani sun shafe watanni suna samun matsuguni na wucin gadi kafin a kai su daya daga cikin manyan cibiyoyin "karba da tantancewa" na masu neman mafaka a wannan yanki na Girka. Ga karamin Tsibirin na Gavdos mai mutane kalilan, wannan matsala ce musamman a ranakun da yanayi ya yi muni kuma babu kwale-kwalen zuwa Kreta.

Riga-kafi | Mpox | Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Alluran riga-kafin Mpox, sun isa Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Justin Makangara/REUTERS

Jaridar Welt online ta wallafa nata sharhin ne kan fara allurar riga-kafin cutar Mpox a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Jaridar ta ce hukumomin sun ayyana bullar cutar a kasashen Afirka 16, wanda ke nunar da karin yaduwarta cikin sauri a wannan nahiya mai yawan al'umma. A wani mataki na dakile yaduwar cutar, an fara yin allurar riga-kafi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Har yanzu babu wata babbar nasara da aka samu dangane da yaki da yaduwar Mpox a Afirka, kuma a karon farko a bana ta bulla a kasashen Zambia da Ghana. Adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar a fadin Afirka ya karu daga sama da kaso uku zuwa sama da 36, ya zuwa ranar shida ga wannan wata na Oktoba da muke ciki. A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango cutar ta fi kamari, ita ce kasar da ke da kaso 85 cikin 100 na wadanda suka kamu.