1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Kamaru: Shugaba Biya ya koma gida

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 21, 2024

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya sauka a filin jiragen sama na kasa da kasa da ke Yaounde babban birnin kasar, bayan kwashe makonni da dama a kasashen waje

https://p.dw.com/p/4m4Pv
Kamaru | Shugaban Kasa | Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP/Getty Images

Gidan talabijin din kasar CRTV ya nuna yadda Shugaba Paul Biya mai shekaru 91 a duniya da mai dakinsa Chantal suka isa kasarsa, bayan dawowa da ga tafiyar da aka yi ta yada jita-jita a kan makomar lafiyarsa. Shugaba Biya da ke kan karagar mulki tun daga watan Nuwamba na shekara ta 1982, ya samu tarba ta musamman daga magoya bayansa sanye da riguna da ke dauke da hotunansa suna kida da cashewa domin yi masa maraba.