1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cin hanci ya mamaye yaki da ta'addanci

October 21, 2024

A karon farko gwamnatin Tarayyar Najeriya ta zargi jami'an tsaronta da sai da makamai ga 'yan ta'addar da suka dauki lokaci suna wandaka cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4lxmF
Najeriya | Boko-Haram | Ta'addanci | 'Yan Bindiga
'Yan ta'adda sun jima suna cin karensu babu babbaka a NajeriyaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Can a bangaren manyan hafsoshin tsaron dai, ana ganin karuwar mallakin gidaje da ragowar kayan alatu yayin kuma da ake dada gurfanar da kananan kan laifin sai da makamai ga 'yan ta'addan Tarayyar Najeriyar. Wannan matsala dai, na cikin rawar cin-hancin da sannu a hankali take dada tasiri a batun tsaron kasar a halin yanzu. Shi kansa mashawarcin tsaro na kasar a karon farko, ya tabbatar da tasirin hancin a cikin yakin Najeriyar da ta'addanci. Malam Nuhu Ribadu dai bai boye komai, kan yadda mafi yawa na makaman da ke hannun 'yan ta'addar ke fita daga hannun jami'an tsaron kasar masu yaki da su ba. Wannan ne dai karo na farkon fari da kasar ta fito fili, domin nuna amincewarta kan zargin hancin a cikin yakin na shekara da shekaru. Isa Sunusi dai, na zaman shugaban kungiyar Amnesty International da ta share tsawon lokaci tana bin diddigin jami'an tsaron da ke yaki da ta'adda.

Tsaro: Gwamnan Katsina ya magantu

Yunwa a ciki makami a hannu dai, an dade ana zargin jami'an tsaron da hannu da kafa wajen rura wutar rikicin rashin tsaron Najeriyar da burin neman riba da kila ma neman kudin dare daya. Kabiru Adamu dai na sharhi cikin batun tsaro a kasar, kuma ya ce Najeriyar ta dauki lokaci tana fuskantar matsalar ba tare da nuna alamun daukar mataki a bangaren masu mulkin ba. Tun a shekara ta 2007 ne, Najeriyar ta kaddamar da babban yakin mai tasiri. A shekaru 10 na farkon fari kadai dai, wata kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar ta yi asarar da ta kai dalar Amurka miliyan dubu 97 sakamakon rikicin ta'addancin da ya shafi rayuwa da makoma ta 'yan kasar. Kuma ana shirin ganin tsawon yakin har Mahadi a tunanin Dakta Yahuza Getso da ke zaman kwararre kan harka ta tsaro, in har ba a samar da shugabanci na gari cikin gidan tsaron Najeriyar ba. To sai dai kuma a kokarin neman mafita, Najeriyar ta ce ta shiga sabon babi a cikin yakin na ta'adda, wanda rundunar tsaron kasar ta ce zai tashi daga amfani da kananan makamai ya zuwa sababbin jirage na zamani da ke tuka kansu da kansu.