Ranan Salla
Ranar sallah rana ce ta farin ciki ga musulmin duniya bakidaya wacce take gudana sau biyu a kowace shekara.[1]
Sallah ta kasu kashi biyu, akwai babbar sallah da kuma karamar sallah.
Ita karamar sallah ana hidimar ta ne bayan kammala azumin watan Ramadan, Sannan kuma musulmi na yanka dabbobi kamar su shanu,raguna, har ma da kananan dabbobi irin su kaji da zabi da agwagi domin murnar wannan rana. Bayan an gama sallahr Idi Musulmi suna zuwa gidajen 'yan uwa da abokan arziki domin ziyarce-ziyarce.
Babbar sallah ana hidimarta ne bayan kwananki saba'in daga kammala azumin watan Ramadan, wanda hakan yayi dai-dai kwana goma ga watan sha biyu (zul-hijja).[2]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Ita karamar sallah ana yin ta ne bayan an gama azumin watan Ramadana, idan an ga wata a daren Ashirin da Tara ( 29 ) ko 30, to, washe gari za a yi sallar azumi. Ita kuma babbar sallah ana yinta ne bayan azumi da wata biyu da kwana goma. Wato goma ga watan zul-hajji, washegarin Arafa. Ana yanka rago, tunkiya, akuya, taure, saniya, ko rakumi.
Ranar karama sallah wato sallar azumi. Da safe bayan an karya kowa zai yi wanka ya sanya sababbin kaya, a je masallaci domin gudanar da sallar idi. Su kuma iyaye mata za su yi girki na musamman da za a ci a gida da kuma rabawa 'yan' uwa da abokan arziki. Ranar sallah kowa yana samun abin da zai ci. Rana ce ta musamman ga al’ummar musulmai gabaki daya.
Babban Sallah
[gyara sashe | gyara masomin]Ranar babbar sallah/sallar layya. Ranar sallah da safe kowa zai sa kayansa mai kyau, amma an fi son fararen kaya ga wanda Allah ya hore ma wa, amma kuma za ka iya sa kalar da kake so ba laifi ba ne, amma idan mutum yana da halin layya, ana so ya kame bakinsa har sai an sauko daga masallaci bayan babban limamin ya yanka ragonsa. Idan an sauko wato an dawo daga masallaci, sai duk wanda yake da abin yanka ya yanka dabbarsa. A kasar Hausa, ranar za a rataye ragon sai washe gari a yi aiki, shi kuma kayan ciki za su sarrafashi a soya kowa ya taba. Washegari za a sauko da dabbar da aka rataye a yayyanka a bai wa yara su rarraba wa makota da 'yan' uwa. Sauran naman za a dafa shi a soya a rarraba wa mutanen gida kowa ya dauki rabonsa. Shi kuma kai da kafafun dabbar za a babbake a ajiye sai bayan yan kwanaki a yi ragadadarsa a ci. Wasu kan ajiye shi sai lokacin takutaha wanda shi ma wata al-ada ce ta Hausawa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Eid al-Fitr: Abubuwan da ake so Musulmi ya yi kafin Sallar Idi". bbc hausa. 12 May 2021. Retrieved 25 August 2021.
- ↑ {{citenews|url=https://dailypost.ng/2022/06/30/sallah-sultan-declares-july-9-eid-al-adha/