Jump to content

Ajami

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 07:06, 4 Nuwamba, 2023 daga Kabirusheshe (hira | gudummuwa)
Ajami
Type
Parent systems
  • Ajami
Rubutun ajami

Ajami (عجمى), tsarin rubutu ne na Hausa ta hanyar amfani da haruffan Larabci. Wannan rubutun ya samo asali ne daga lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa a ƙarni na shida Miladiyya. Sai dai kuma, kasancewar kwayoyin sautin larabci sun bambanta da na Hausa musamman tagwayen baƙaƙe irin su "gy" da "ts", sai kowanne marubuci ya zamo ya na amfani da tasa dabarar wurin rubutun ajami. Sakamakon haka, ajami ya ke da wuyar ganewa har ma ake ma sa kirari da, gagara-mai-shi.

Manazarta