Dafi
Dafi ko kuma Guba ana kiran dafi da turanci poison/venom dai kamar yadda masu ilimin biology suka bayyana yana nufin duk wani abinda yakeda haɗari wanda har zai iya sabbaba mutuwa ko jin rauni ko raunata wasu sassan jikin Ɗan Adam, misali gaɓoɓi koda kuwa dabbace ko kuma ɓata baki ɗayan jiki. Dafi yana samuwa ne kodai ta hanyar sara/cizon wani dabba misali maciji, ko kuma harbin kunama da ƙarinta (by sting or bite) sai dai shi dafin dabbar da take cizo yasha banban da sauran waɗansu dafin kasancewa shi ta sanadiyyar cizo ne ko harbi kalan wannan dafin na dabbobi ana kiranshi da Turanci da (Venoms)
dafi | |
---|---|
class of chemical substances by use (en) da cause of death (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Abubuwan sunadarai, noxa (en) , makami da Q124326543 |
Amfani | poisoning (en) da makami |
Has characteristic (en) | toxicity (en) da mode of toxic action (en) |
Tarihin maudu'i | history of poison (en) |
Amfani wajen | poisoner (en) |
Dafi/Guba kala-kala ne
gyara sasheGa jerin su da harshen turanci kamar haka kowane tare da bayaninshi:
- Necrotoxins kalan wannan dafin/gubar yana kashe ƙwayoyin halittar bil'adama idan ya samu mutum
- Cytotoxins shima duka illar shi ɗaya daga Necrotoxins
- Neutrotoxins shi kuma yana taɓa ɓangaren hankali (Nervous system) a turance kenan
- Myotoxins shi kalan wannan gubar tana lalata tsokar jiki
- Hemotoxins shi kuma yana tasiri ne a jinin mutum
Tasirin guba a jikin mai rai
gyara sasheDafi ko kuma guba yanada matuƙar haɗari ga duk wani mai rai kamar yadda ya gabata akan cewa kodai yayi sanadiyar mutuwar mai rai ko kuma ya lalata masa wasu gaɓoɓi. Misali binciken da akayi a shekara ta 2013 ya nuna dafi/guba ta kashe kusan mutum 57,000 Sai kuma a shekarar 1990 ya kashe kusan mutum 170,000 wanda kusan duk sanadin cizon maciji kunama da sauran dabbobi masu dafi, idan aka kwatanta da shekara ta 2013 ya ragu akan alƙalumman da aka samu a shekara ta 1990.[1] Duk da cewa a wani ɓangaren ana iya amfani da dafi don yin wani amfani na daban Ana amfani da guba ta hanyar magance ƙwari, haka wasu mutanen marasa imani ko kuma maƙetata suna amfani da guba don halaka abokan hamayyar su wanda wannan ya saɓawa Addinin Musulunci da kuma al'adun Hausawa don a musulunci duk wanda ya kuma kashe wani shima a kashe shi don kisan kai abu ne mai matuƙar haɗari duniya da lahira. Akanyi amfani da guba ta hanyar zubawa ƙwari a abincin su da dai sauran hanyoyin na daban.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Global Burden of Disease Study 2013, Collaborator (22 August 2015). "Global, regional, and national incidence, prevalence, and years lived with disability for 301 acute and chronic diseases and injuries in 188 countries, 1990-2013: a systematic analysis for the Global Burden of Disease Study 2013". Lancet. 386 (9995): 743–800. doi:10.1016/s0140-6736(15)60692-4. PMC 4561509. PMID 26063472.