Ƙadangare jam'in shi shine ƙadangaru, mace kuma ana ce mata ƙadangaruwa, yana daga cikin dabbobi masu tafiya da ƙafa huɗu a wani bincike kuma ana cewa yana daga dabbobi masu rarrafe. Kuma kusan ko ina a faɗin duniya ana samun shi, sai dai kaɗan daga cikin wasu yankuna irinsu, Antarctica da Island. Ƙadangare da mage. Ƙadangaru suna nan nau'i daban-daban wato kala-kala akwai ja, baƙi mai ratsin fari, yalo da dai sauran kaloli. Haka kuma Nau'ukan ƙadangaru (species) yakai dubu shida (6,000). [1]

Ƙadangare
organisms known by a particular common name (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Reptilia (en) Fassara
ƙadangare akan dutse/jangwalegwada
Ƙadangare da mage

Ƙadangaru suna faɗa da junansu musamman maza daga cikinsu kuma mafi akasari suna faɗan ne saboda mata.

Hoton jangwalegwada

Ƙadangaru suna cin ƙwari ne a matsayin abincinsu amma wani lokacin suna cin abincin da mutane suke ci kamar tuwo, wake da sauran su. Mafi akasarin ƙadangaru ƙanana ne girman su madaidaici ne, kamar tsaka Ko da yake tsaka tana cikin jinsin ƙadangaru. Mafi yawan ƙadangaru ƙwai sukeyi don haihuwa, sukanyi ƙwai kusan ɗari. Haka kuma Hausawa nayin wata karin magana wai "ƙadangaren bakin tulu a ƙyaleshi ya ɓata ruwa a kasheshi a fasa tulu" ma'anar wannan karin magana shine (wato kamar idan wani mutum ya matsawa wani, kuma shi baida ikon rabuwa da wanda ya matsa mashi ɗin), shikenan wannan mutumin ya zame ma shi ƙadangaren bakin tulu.[2] Ƙadangare mafi girma a duniya shine Komodo dragon. [3]

Manazarta

  1. "THE REPTILE DATABASE". reptile-database.org. 10 November 1995. Retrieved 9 July 2021.
  2. "Kenya : Matar da ta zamewa masu aikata laifi a Kenya ƙadangaren bakin tulu". BBC Hausa. 25 January 2021. Retrieved 9 July 2021.
  3. "Komodo dragons". bbc news. 25 January 1956. Retrieved 9 July 2021.